Heedayah complete Novel - Chapter 60
Heedayah complete Novel Chapter 60: Heedayah complete Novel Chapter 60. Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... 9/12/21, 8:04 PM - ,:…
1,986 words
Heedayah isn't free, you read for free 馃し馃徎鈥嶁檧锔忦煠佛煆烩€嶁檧锔�
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Chapter notes and social links
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... 9/12/21, 8:04 PM - ,: Driving Zayyad yake yi carefully yana kirga manyan gidajen da yake wucewa a layin, har ya tsaya a dai dai gida na biyar kamar yanda Khaleel yace masa, a hankali ya bude motar ya sauka ya nufi gate din yana kare ma gidan kallo, da zoben hannunsa ya kwankwasa gate din, bayan few seconds ya kuma kwankwasawa, dai dai nan aka bude gate din, wani ne sanye da khaki hannunsa rike da bindiga ya gani, sai ga Mai gadin gidan ma ya taho da sauri, Zayyad ya d'an sosa kansa yace "Erm don Allah tambaya nake" Me sanye da khaki na kallonsa fuska a murtuke yace "Go on..." Zayyad yace "Na xo wucewa ne daxu na hadu da wata yarinya bakin hanya, she was almost unconscious, so being the good Samaritan that I am na nemi gefe nayi parking na sauka coz she looks responsible, nan kuma na tambayeta abinda take yi bakin hanya da daren nan, I have to listen with both my heart kafin in fahimce me take ce min, that dumping dinta wai wasu suka yi a wajen suka wuce, I asked her wani anguwa take, and she mentioned here with both the address, daga haka kuma she passed out, wato ta suma, I hate police cases snn ni matafiyi ne ba d'an Abuja ba, bana son kuma duk wani abu da xai hadani da Yan sanda su bata min lkci, to tunda dai ta bani address din inda take shine na dai sakata a mota na kawota nan din da tace min gidansu ne, ina kuma fatan shine gidan nasu" daga Mai gadi har masu khaki biyu dake tsaye bakin gate din kallon Zayyad that is speaking confidently suke suna sauraronsa da kyau, daya daga me khakin sojan ya fita xuwa gun motar Zayyad holding on to his gun, ya leka cikin motar yana kallon Heedayah dake bacci gently, komawa yyi yana duban Zayyad yace "I think it's better ka kai ta police station din for police report ba yar gidan nan bane, kuma shi xai fi maka sauki" Mai gidan ne da matarsa ke tahowa xuwa parking space alamar xa su fita don makullin mota na hannunsa, kuma dama jiransa sojojin suke ya fito kasancewar su excort dinsa na nan garin, ganinsu tsaye bakin gate din gidan har yana hango Zayyad yasa Mai gidan yace "Allow him, if he wants to see me, let him plss" Sojan ya koma gefe Zayyad ya shigo compound din yana kallon Mai gidan almost shocked, walking calmly Mai gidan ya iso har gabansa ya tsaya ya basa hannu with smile a fuskarsa suka yi musabaha, Mai gidan yace "Kana son ganina ne gentleman, kaga kuma xan fita yanxu but in sha Allah ka dawo gobe da safe xan ganka" Zayyad dake ta kallonsa ya fara kame kame yace "Noo, A'a dama yarinya na kawo, i was thinking gidansu ne nan, tace min nan ne gidansu, Kuma address din nan ta bani, I saw her almost unconscious a hanya and decided to help her" da mamaki Mai gidan yace "Yarinya? Ina yarinyar take yanxu?" Zayyad yace "Tana cikin motana" gaba daya Zayyad a daburce yake ya ma ki yarda su hada ido da Mai gidan, Mai gidan yace "To shigo da motar taka" Zayyad ya juya da sauri xai fita and dama yyi niyya idan ya samu ya fita to fecewa kawai xai yi abunsa, daya daga sojan ya dakatar da shi, snn shi sojan ya fita kamar yasan abinda ke ransa, Mai gadi ya bude gate din gidan sojan ya shiga motar Zayyad snn ya shigo da motar cikin compound din, matar da suka fito tare da Mai gidan ta karaso gun me gidan nata tace "Abiey Ina jin yarinyar da Mum Islam tace ake nema a gidan makotan mu ce fa, kilan bai gane kwatancan nata bane, nan makotan mu ya kamata ya kai ta" Zayyad dai sai keto masa xufa yake yana sharewa with swag, Mai gidan ya nufi motar da sojan yyi parking a tsakar compound yana duba cikin motar, Tana kwance har snn sai da kusan rabin fuskarta rufe yake da mayafin abayarta kamar yanda Khaleel yayi mata tun daxu da ya kwantar da ita a motar, sojan ya bude motar ya yaye mayafin daga fuskarta bayan ya kunna wutan motar, kallonta kawai Mai gidan ke yi without blinking, ita dai matar na tsaye taki leko cikin motar tace "Ko a kira Mum Islam nasan baxata rasa sanin yarinyar ba tunda tana shiga gidan sosai" Sojan dake tsaye bakin motar shi dai ya kalli Heedayah snn ya sake kallon matar Mai gidan nan, yyi hakan yyi sau uku, Jin shirun da Mai gidan nata yyi, matar tace "Abiey Ina magana, nace should they call Mum Islam ayi alerting din neighbors din namu" Can dai ta gaji da magana ganin mijin nata ya ki cewa komai, ita ma ta leka cikin motar tana kallon Heedayah, Dafa ta Alhaji Ahmad yyi xai janyeta daga motar ta fixge hannunta da sauri, ta fi minti daya tana kallon Heedayah da idanuwanta kamar xa su fito, can ta xaga daya side din motar da sauri har tana neman faduwa, da mamaki ta sa sojoji da Zayyad da suke tsaye wajen ke kallonta, ta bude motar tana sake kallon Heedayah kirjinta na Heaving, har wani rawa hannunta yake ta kamo hannun Heedayah na dama ta daga rigar Abayarta tana duba hannun, ta kara xaro ido sosai snn ta juya wuyar Heedayah nan ma ta ga black dot din da take son gani, wani kara me karfi tayi da ya farkar da Heedayah daga nan kuma ta sulale wajen, Heedayah ta kara lumshe idonta sbda har sannan maganin bai saketa ba nan ta kuma komawa duniyar bacci, da sauri Mai gidan ya xaga xuwa inda matarsa ta fadi sojojin ma duk suka bi sa da Mai gadi, Zayyad dai was extra confuse, ga wayarsa dake ta vibrate a aljihunsa ya san kuma Khaleel ne ke kiransa, Mum Islam da ta ji karan uwargidan nata ta fito da sauri daga bangarenta, Tuni Mai gadi kuma ya tafi dauko ruwa daga dakinsa da gudu, Daya sojan sai fifita yake ma Madam din Mai gidan nasu da hularsa, Alhaji Ahmad dai ya dago matar tasa yana kiranta amma ta suma, a rikice mum Islam tace "Abiey lafiya?? what happened, jikin nata ne ya tashi?" Ta amshe ta hannunsa ita ma tana mata fiffita da gefen dankwalinta tace "Asibiti xa mu tafi yanxu" ganin hawaye fuskan mijin nasu ya sa Mum Islam tayi still tana kallonsa, a hankali tace "Subhanallah is everything alright Abiey, wani abu ya faru ne ta fadi" Daukar matar tasa kawai yyi yana kallon Zayyad yace "Bring the girl in" daga haka ya wuce ciki yana rike da wife din tasa, duk sai mum Islam ta ji ba ddi tayi jigum tana bin su da kallo bata mike daga durkushen da take ba, Zayyad ya fiddo Heedayah daga cikin motar, da ido Mum Islam ta bi Heedayah da kallo tace "Wacece wnn kuma?" Sai kuma ta wani xaro ido ganin kamar da Heedayah ke yi da co wife dinta, lkci daya ta mike ita ma jikinta ya dau tsuma tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un...." Ta furta haka ya fi a kirga, sai kuma ta bi bayan Zayyad da yabi bayan Mai gidan nasu da sauri, Mai gadin ya girgixa kai shi ma dai har da hawayensa yana kallon sojojin that all look confused yace "Sai gashi har gida an dawo mata da 'yar ta da ta bace yau shekara kusan biyar kenan, bbu tantama wnn yarinyar 'yar uwar gidansa ce" Zayyad ya kwantar da Heedayah nan tsakiyar lallausan carpet dake parlon, Alhaji Ahmad kuma ya kwantar da matarsa saman kujera wanda a nan take ta bude idonta, ta mike xaune weakly, da kyar ta fashe masa da kuka tana rike da hannunsa tace "Wllh Heedayah na gani Ahmad, wllh Heedayah ce, daughter na ce, tana Ina yanxu? Ina ku ka bar ta" Alhaji Ahmad ya koma gefenta yanda xata ga Heedayah dake kwance parlon, Kukan da Mum Islam take kai kace ta ta6a ganin Heedayah ko ta ta6a saninta, Kuma har xuciyarta take farin cikin bayyanar 'yar kishiyar tata bayan an fidda rai da dadewa, Kuka sosai Mahaifiyar Heedayah take tace "Ahmad idan mafarki ne wnn Allah ubangiji kada ya bani ikon farkawa, idan na farka naga mafarki nake nasan kilan karshen rayuwata ne ya xo coz I won't be able to stand it, let it not be a dream plsss, baxan iya ci gaba da rayuwa ba idan na farka naga mafarki ne" Mum Islam ta durkusa kusa da ita ta rikota tace "You are not Dreaming Mum twins.... We all are not Dreaming, Heedayah ce ba mafarki bane" Zayyad was so emotional at that time, ga confusion da ya dabaibayesa ta ko ina, but Khaleel yace masa a jiya ya dauketa daga gida, then why are they acting kamar sun yi shekara da shekaru rabonsu da ita, and wnn ai shine Mutumin da suka so kidnapping shekaranjiya, shine Alhaji Ahmad dake neman takarar gwamna how is this girl his daughter..... Mahaifiyar Heedayah ta rungume kishiyartata tana kuka sosai tana cewa bata son farkawa daga wnn mafarkin da take yi don tasan ba gaskiya bane, she is just dreaming, meeting with her daughter can't be just like a film to her. Khaleel ya kira Zayyad ya fi a kirga no response, hankalinsa ya tashi ba kadan ba, ya ma rasa tunanin da xai yi, gidan ne bai kai ta ba deceiving dinsa yyi duk da yasan Zayyad just can't do that, ko kuma ya kai ta aka kamasa, he don't know which to keep in mind, he don't know which to imagine, gashi ya ki komawa gida duk da ciwon da yake ji a xuciyarsa yana dai ta xaune inda suka yi xa su hadu idan Zayyad ya ajiyeta a address din da ya basa, ganin this is almost an hour hakurin Khaleel ya kare gaba daya, da kafa ya koma har layin, sai dai he is really not fine, at anytime he can fall sick ya sani, tafiyar ma daurewa kawai yake yi, yana isowa dai dai gate din gidan Deenar ya tsaya thinking of what next to do, gaba daya bbu alamar motar Zayyad a layin sai dai ga wata bakar mota a dai dai kofar gidan Dinar din, ya sake ciro wayarsa ya kira layin Zayyad for the countless time no answer, har ya kai hannu xai buga gate din dai dai nan aka bude, At first baya Khaleel ya koma da sauri ba tare da ya bari ya ga ko waye ba, bayan few seconds ya dago kansa ya ga ana pointing dinsa da bindiga, kallon Shuraim kawai Khaleel ke yi, da mamaki Abba ya kalli Shuraim yace "Hey, What's that u are doing Shuraim, I told u bana son kana bi na da bindiga, meye hakan...." Asp na Yan sanda dake wajen shi ma don duk tare suka fito Calmly yace "Drop that Shuraim, sure everybody is a suspect now, but...." Shuraim yyi wani murmushi yana kallon Khaleel da kyau yace "Shine saurayin da ya tafi da ita, he is the main suspect" yana fadin haka ya isa dai dai gaban Khaleel ya mayar da bindigan aljihunsa yana kallonsa fiercely nan take yyi masa naushi har biyu a ciki, lkci daya idanuwansa suka sauya kamanninsu just as the soldier he is yace "Ina ka kai Heedayah???" Junaid was just still a bakin gate din yana kallon Khaleel, Asp ya kwace Khaleel daga damkar da Shuraim yyi masa, da ido Khaleel ya bi Shuraim da kallo ko kiftawa bbu, Asp ya xaro handcuff din aljihunsa yana kallon Khaleel yace "You are under arrest"