Heedayah complete Novel - Chapter 74
Heedayah complete Novel Chapter 74: Heedayah complete Novel Chapter 74. Kuka kawai Heedayah take ta kasa cewa komai duk da hayaniyar da kaka da Yakumbo ke…
2,333 words
Kuka kawai Heedayah take ta kasa cewa komai duk da hayaniyar da kaka da Yakumbo ke mata suna tsaye a kanta, Farida dai na rakube gefe banda kuka bbu abinda take, DCP dake tsaye kusa da Baffan Junaid ya kwantar da murya yana kallon Heedayah yace "Xa ki gane gidan nasa na Abuja yanxu?" Heedayah ta girgixa masa kai kawai, yace "Da yaushe ya gaya maki su suka ta6a dauke ki?" Heedayah ta harari Farida amma taki cewa komai, DCP yace "Talk to me young lady, da yaushe ku ka yi xancen da shi?" K'in cewa komai Heedayah tayi still, Ammi ta sauke mata wani mari a fusace tace "Baxa ki bude baki kiyi ma mutane magana ba" Heedayah ta rufe fuskarta tana kuka sosai tace "Ni ba shi ne ya daukeni ba fahh" Mumy dake tsaye ita ma parlon tace "Haba Hajiya ai bin ta xa ayi a hankali, duka ba shine mafita ba a yanxu, idan aka lallabata duk sai ta buda mana abubuwan da Faridar ta fada yanxu" Abba na kallon Heedayah yace "Tashi xaune" Mikewa xaune tayi a hankali hawaye na sakkowa idonta, yace "Da yaushe ku ka yi magana da shi yace maki shi ya dauke ki years back" A hankali ta girgixa masa kai tace "Ni ba shine ya daukeni ba Abba" DCP yace "To wa ya dauke ki" Cikin rawar murya tace "Wasu mutane ne ba shi ba" Ya daure fuska yace "Amma yar uwarki ta ce kince mata shi ne ya ajiye ki gefen hanya bayan ya daukeki daga wajensu" Heedayah ta girgixa kai tace "She's not saying the truth, ni ba haka nace mata ba" cikin kuka Farida tace "Karya take sir, ce min tayi yace mata shi kidnaper ne" Heedayah ta jefa mata wani kallo tace "He is not!!! Ni bance maki haka ba" DCP ya xauna yana facing dinta da kyau yace "You are not saying the truth young lady, baki son a ceto Mum din ki ne??" Heedayah ta fashe da kuka sosai gaba daya she look confused, Farida tace "Sir she's lying, ya sanar mata shi kidnaper ne, da bakinta ta fada min haka wllh" Kuka sosai Farida take, Heedayah dai hawaye sai sakko mata yake taki cewa komai, DCP yace "Xaki xama suspect dinmu kenan, and we have no choice then to go with u to the station...." Abba yayi kasa da murya yace "She's only confused sir, a bata sometimes xata yi magana idan Allah ya yrda" Junaid dake xaune ya sauke ajiyar xuciya yace "Lkcn da aka kwantar da shi a asibitin Abuja, the phone call his frnd is always making is highly suspicious, bbu gaskiya a kiraye kirayen sa, and idan yyi noticing dina a waje baya sakewa yyi magana, tun a lkcn na fara xarginsa amma ban kawo wani abu a kan shi Khaleel din ba" Baffansa yace "Abokin barawo ai barawo ne" Junaid yace "Ban yi tunanin Mami xata sake da shi Khaleel din har nan Kaduna ba, I once told her wnn mutumin stranger ne bai kamata tana jawosa jiki haka ba tunda ba saninsa tayi ba, she don't know him but Mami didn't listen to me, Dinar ma tayi mata magana bata saurareta ba..." Kaka na Shessheka tace "Mu dai daga ita har Heedayar sun kai mu sun baro mu muna xaman xamanmu ana shirye shiryen tafiya Gwamnet house, yanxu gidan ubanwa xa a samo wani shegen dubu miliyan hamsin idan ba Heedayar xa a kai kasuwa ba, ko ubanta dake da mukamin gwamna ynxu bashi da dubu miliyan hamsin balle mu karere, ni ban ta6a ganin yaron ba da sai na gane barawo ne tun kan aje ko ina wllh" Cikin rawar murya Heedayah tace "Ba barawo bane" wani Marin Ammi ta kara sauke mata, Abba yace "Subhanallah kar ki sake Hajiya" DCP da Baffan Junaid ma duk suka yi ma Ammi magana, Yakumbo ta fashe da kuka tace "Idan nayi magana sai a dinga min kallon me ta6in hankali, ranan farko da na fara ganin mutumin nan sai da nace ban yarda da shi ba yyi kalan yan satan mutane, amma bbu wanda ya dau maganata da muhimmanci, to yau ga dai abinda na fada ya fito, yanxu ya xa muyi fisabilillahi ga yar yarinya ko abinci nasan bata ci ba har ynxu, wani kai rahotu gidan radio da talabijin da gidan yan sanda duk ba shi bane wllh, fatana su fito cikin aminci, Ashnaah bata minti ashirin bata sha yagwat ba, to uban wa xai bata a can, Amadi daga komawarsa kujeransa yau sai yaji wnn mummunan labari mai cike da tashin hankali, don ma gwamnan kaduna bai bar maganar a haka ba shi ma yana bakin kokarinsa, ai wllh kashin yan kinnafas din nan ya bushe, xa su san har da 'yar gwamna suka dauke, don nasan da sun san yar gwamna ce Ashnaah baxa suyi gigin ta6a ta ba, dama an hada da Heedayar an tafi wllh da hankalina bai tashi haka ba tunda ita sun saba dauketa dama, ynxu banda xuciyar musulunci kina tunanin Junaidu xai yarda ya aureki bayan kwamushe uwarsa da aka yi ta dalilin ki, don ubanki gwamna ne ai ba ke bace gwamnan da xaki ja ma mata fitina tana xaman xaman ta..." Mumy sai da taji gabanta yace rasss jin abinda Yakumbo tace kan Junaid sai ya fasa auren Heedayah, Ammi dai ko kallon Yakumbo bata yi ba, Abba na rike da wayar Junaid yana ta kiran layin da aka kira da shi amma a kashe, Dr ya sauke ajiyar xuciya yace "Xa su kira Barrister, we have to calm down" Oga Arne na xaune parlor kan kujerarsa ya gama zuke zukensa Salim ya mika masa wayar da aka yi amfani da shi wajen kiran Junaid daxu, canxa layi yyi ya kunna wayar ya sake dialing Number Junaid, yana fara ringing Abba ya daga daya bangaren ganin bakon layi, Arne yace "Na kira in sanar maku inda xa ku kai mana kudin ku ajiye...." Abba yace "Yallabai ba mu da miliyan hamsin ynxu haka, ku fadi abinda xa mu iya baku domin Allah" Arne yace "Motar hawanta kadai ma xai yi miliyan 12, kada ku raina mana hankali, da alamar kun gaji da rayuwarta a doron kasa, xuwa karfe sha biyu gobe sae dai a dinga wani labarin ba wnn ba" Abba yace "Ka saurareni" katse wayar Arne yyi ya kashe gaba daya ya jefa ma Salim, Khaleel dake tsaye for almost an hour jikin pillar din dinning area din parlon ya rasa me ke masa ddi ya daga jajayen idanuwansa yana kallon Arne, wani dariya Arne yyi, Khaleel ya karaso cikin parlon yana dubansa sosai yace "A janye maganar kudin fansar ni xan baku...." Arne yace "Kana da wani alaka da ita ne da xaka bada kudin fansan?" Khaleel yace "Xan bada saboda a ta dalilina ku ka dauketa, snn they can't afford that amount" Arne ya mike yace "Naga alama after all this baxa ka rabu da mutanen nan ba, I think the best thing is just to send her to her early grave snn mu bi duk wani nata mu kashe, hakan kadai xai sa hankalin ka ya dawo jikin ka, amsan kudin fansa da 6ata maka suna a wajensu duk ba shi bane, xaka iya yin komai don ganin ka koma garesu, I mean xaka yi brain washing dinsu su kuma su kara amsar ka, kasheta shine kadai mafita a yanxu....." Khaleel da xuciyarsa yyi masa nauyi ya duka nan kasa da kyar yace "Kada ka kasheta Oga, don't forget she is a barrister idan nace xan koma gun daughter dinta xata yi exposing dina a idon duniya, xata tona min asiri, Kar ka manta bbu uwa ta gari da xata so tarayyar 'yar ta da hoodlum, ni kuma hoodlum ne, don haka kun riga da kun rabani da su don't go further then this plss, kar ku kasheta...." Arne dake ta sauraronsa yace "Toh idan ka kuskura ka sake cewa xaka bada kudin fansa sai na aika wnn yar yarinyar dake tare da ita lahira" Khaleel ya sauke kansa kasa hawaye na sauka idonsa bai ce komai ba, Arne ya koma ya xauna yana huci, Khaleel ya daga kai bayan few seconds yana kallonsa da kyar yace "To a taimaka a basu wani abun su ci ko su sha...." Arne ya mike yana masa wani kallo yace "You cannot break our rule all of a sudden Brainiac...." Mikewa Khaleel yyi a hankali ya koma inda yake tsaye ya jingina da pillar din ya runtse idonsa. Karfe sha biyu na dare Arne ya sake kiran Abba, nan Abba ya nemi alfarman su bar kudin miliyan talatin, da kyar da kyar Arne ya amince bayan cin mutunci iri iri a waya snn ya bukaci Motorcycle guda biyu sababbi dal a hada da kudin, nan ya sanar masu inda xa su tafi su ajiye masu kudin da safe. Washegari da sassafe Junaid ya tafi tare da Abba da Baffansa sai DCP a cikin motar Abba kai kudin inda Arne yace su kai a wani kauye cikin garin kano, wata motar kaya ce a bayansu dauke da Motorcycle guda biyu, a cikin motar motorcycle din kuma Yan sanda ne gudu hudu duk sanye da mofti, banda motar dake bayan motar Motorcycle din dake cike da sojoji, wayar Junaid dake hannun Abba ne ya fara ring ganin sabon Number ya daga ya sa handsfree, muryar Manga ne ya cika motar yace "Kai ku koma da kudin ku, snn karfe hudu na yamma ku duba can karshen layin gidanku xa mu ajiye maku gawarsu a can, sbda raini xaku kawo kudi sai kun yi xuga har da motoci uku, mu xa ayi ma wasa da hankali, mu xa a raina ma wayo, to wllh wllh kasheta xa mu yi idan mutum daya baxai taho da kudin ba" DCP sai kalle kallen hanya yake don ko Zaria basu karasa ba kuma motoci dai dai ne a hanyar ke tafiya, Junaid ya jinginar da kansa jikin kujeran motar hankalinsa a tashe, Parking Abba ya samu gefe yyi sauran motocin bayansa ma duk suka tsaya ganin haka, DCP yace "Mu je kawai Barrister kyale yan Iska suna biye da mu ne...." Baffan Junaid yace "Aa kamar dai yanda yace Sbda lafiyar Rahinah da yarinyar wajenta mutum daya kawai ya kai kudin yallabai, further investigations should follow forth, yanxu dai the life of Rahinah and the little girl matters first, ba imani ne da su ba xa su iya aikata abinda suke fada" Abba yace "Haka ne, ni xan tafi in kai masu kudin, kamar yanda Alhaji Imran ya fada further investigation should follow forth, their lives first" Junaid yace "Let me go instead Abba, ni xan kai masu kudin" DCP yace "Junaid ya tafi, and you have to be very very vigilant and careful junaid" Junaid yace "In sha Allah" Abba ya bude motar ya sauka sauran ma duk suka sauka, motar da Babur din ke ciki duk suka nufa, bayan an yi ma drivern motar bayani ya sauka Junaid ya shiga, Abba ya mika masa wayarsa yace "Be careful Junaid, and kayi ta addu'a, Allah ya tsare" Junaid ya amshi wayar ya ajiye gefensa yace "Ameen Abba" snn ya tada motar ya ci gaba da tafiya xuwa garin kano. Dai dai wani matattacen gidan mai na Bulasawa馃檮 da aka yi abandoning baya aiki suka sa Junaid ya ajiye masu kudin ya sauke duk mashinan, wayarsa ne ya fara ring ya fiddo ya daga, "Malam ka gama aikinka, maxa ka bar wajen nan da mintuna biyu kacal" Junaid yace "Toh Mahaifiyar tawa fa?" Aka ce "Xata riga ka isa gida ma" Daga haka aka katse wayar, shiga motar junaid yyi ya tada ya bar wajen cikin few seconds. Sai bayan awa kusan hudu Junaid ya isa Kaduna sbda motar da yake driving, 2 hours ago Abba ya kirasa ya sanar masa Mami and Ashnaah are home, Hamdala Junaid yyi lkci daya hankalinsa ya kwanta sosai, tun da ya iso anguwar tasu yake ganin motocin sojoji har ya isa layinsu, sai da aka yi interrogating dinsa snn ya shiga layin yyi parking kofar gida ya gaida sojojin snn ya shiga gidan, Duk su Abba na parlon ya shiga, Sai bayan awa kusan hudu Junaid ya isa Kaduna sbda motar da yake ja, 2 hours ago Abba ya kirasa ya sanar masa Mami and Ashnaah are home, Hamdala Junaid yyi lkci daya hankalinsa ya kwanta sosai, tun da ya iso anguwar tasu yake ganin motocin sojoji har ya isa layinsu, sai da aka yi interrogating dinsa snn ya shiga layin yyi parking kofar gida ya gaida sojojin snn ya shiga gidan, Duk su Abba na parlon ya shiga, Kaka na ganinsa da karfi tace "Alhamdulillahi, na shiga bandaki yyi sau ashirin sbda tunanin ka Junaidu" Shi dai gaba daya hankalinsa na kan ya ga Maminsa, gaba daya occupant din parlon look very happy seeing him, kaka tace "To a xubo masa abinci ya ci ya koshi dai tukun" Yyi kasa da murya yana kallonta yace "Mami da Babyn fa" Kaka tace "Tana can sama tana bacci, har yanxu dai a tsorace take baiwar Allah, manya manyan likitoci gwamnan kaduna ya turo su dubata, ita kuma yarinyar tana can ana mata karin ruwa ta galabaita da yunwa, fitinanniyar matar can na kanta da uwarta" Sama Junaid ya nufa sai da ya fara shiga dakin da Ammin Heedayah ke ciki snn ya fito bayan minti sha biyar ya shiga dakin Mami, bacci ya sameta tana yi ya karasa ciki ya xauna gefenta yana kallonta.....
*I lost a sister in my payment group today, she paid for Heedayah sbda hakki, sai gashi ba a gama littafin da ita ba ta rasu, Allah Ubangiji ya gafarta mata ya kyautata makwancinta, ya sa mu cika da imani duniya bbu tabbas, I had to gather courage and type this chappy don mutuwarta ya ta6a ni wllh* 馃槖
Heedayah isn't free, you read for free 馃し馃徎鈥嶁檧锔忦煠佛煆烩€嶁檧锔�
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah