Kenza eBookz

Heedayah complete Novel - Chapter 75

Heedayah complete Novel - Chapter 75

Heedayah complete Novel Chapter 75: Heedayah complete Novel Chapter 75. Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... 9/12/21, 8:04 PM - ,: Mami…

1,900 words

Heedayah isn't free, you read for free 馃し馃徎鈥嶁檧锔忦煠佛煆烩€嶁檧锔�

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Chapter notes and social links

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... 9/12/21, 8:04 PM - ,: Mami na xaune parlor bayan Magrib da hijab din da tayi sllh har kasa da carbi a hannunta, gaisawa suka yi da DCP dake parlon shi ma wnda sbda shi ta sakko downstairs, Abba na xaune parlon kusa da DCP shi ma, kaka da Yakumbo na xaune daga gefe daya su ma ko wannensu na kallonta, sai Ammi dake rungume da Ashnaah dake bacci, matar Baffan Junaid na rike da Ashfah, sai wata colleague din Mami a kusa da ita, Heedayah dai na bayan kujera ta ki yarda ta hada ido da kowa tun dawowar Mami, Junaid na tsaye yana kallon Mami da gaba daya tayi sanyi, DCP yace "Hajiya xaki iya gane gidan da aka kai ki jiya?" Mami ta girgixa kai tace "Aa" DCP yace "Tun farkon fara tafiyar taku baki lura da anguwar da ku ka shiga ba ko wajejen da ku ka bi??" Mami tace "Duk ban lura da hakan ba don hankalina baya jikina a lkcn" Shiru yyi na wasu sakwanni sannan yace "Toh su nawa ne Kidnappers din?" Tace "Ban kirga su ba amma suna da yawa" Yace "A cikinsu akwai wanda kika sani?" Mami bata ce komai ba, kowa na parlon kallonta yake, DCP yace "Feel free to talk to me Madam, akwai idon sani a cikinsu?" Ganin Mami tayi shiru, Kaka tace "Yau naga bala'i ana tambayar ki abun arxiki kin yi shiru" firgit Mami ta dawo daga duniyar tunanin da ta lula tunda DCP ya jefo mata tambayar, DCP yace "Kada ki damu Hajiya bbu wani abun da xai sameki you are safe, ki gaya min a cikinsu akwai wanda kika sani?" Mami ta girgixa kai a hankali tace "Babu" Idanuwa aka xuba mata a parlon barin junaid, DCP yace "Kina nufin bbu wanda kika sani ko kika ta6a gani a cikinsu?" Ta gyada masa kai tace "Duk ban san su ba" Yakumbo tace "Ya xa ki ce baki san su ba, nan nan Farida tace wnn rusheshen mutumin dake xuwa gidan nan wajen Heedayah d'an kinnafa ne, kuma Heedayar ce ta sanar mata hakan, hatta Junaid ya shaida hakan shi ma, to wa xai dauke ki idan ba Mutumin ba? Wllh shi ne, idan ma tsoro kike ji ga dai jami'an tsaro duk an watsa a anguwar nan, lungu da sako" Mami ta kalli Junaid dake ta kallonta tace "A ina ka shaida hakan??" Junaid ya kasa cewa komai, can ya girgixa mata kai yace "Aa I was talking of his frnd" Mami tace "To babu wanda na sani cikinsu" Kaka tace "Toh ai dama mutumin baxai yarda ki gansa ba, hauka yake xai bari ki san har da shi cikin kinnafas din, mu dai ba ya cucemu ya raba bayin Allah da basu ji ba basu gani ba da miliyoyin kudinsu, daga karshe ma sai ni na cika kudin wllh, Allah dai ya isa, tunda kuma abu ya xama haka ayi maza gaskiya a sa ma Deedayah rana da Junaidu kowa ya huta don duk dalilinta wnn tashin hankali da asaran ya faru, Kuma wllh a yanda Farida ta nuna Mutumin sonta yake yi.... Kuma tun da yana shigowa gidan yana ganin baja baja ai dole yyi cuta" DCP yace "You need rest Madam, ki tafi sama gobe sai ku taho station da Barrister" Kamar Mami jira take ta mike tace "Nagode yallabai, sai da safe" Tana kallon Abba tayi masa sai da safe shi ma sannan tayi hanyar stairs, ido hudu suka yi da Heedayah dake bayan kujera har snn, Heedayah ta sauke kanta kasa, Mami ta wuce sama. Bayan kwana biyu da faruwan lamarin Ammi suka koma Kano tare da Kaka da Yakumbo, bbu wanda yace Heedayah ta bi su, Yakumbo ma cewa tayi ita ba ruwanta su tafi da ita a sake biyowa a kwashesu gaba daya, kana ganin Heedayah kasan tana cikin damuwa sosai, gaba daya ta rame, bata da aiki sai xaman bayan compound, ko abincin kirki bata ci, har lkcn taki yrda xaman waje daya ya hadata da Mami, iyakarta da ita gaisuwa, duk da Mamin ma tana bedroom dinta always ko fitowa parlor bata yi, har snn kuma a sanyaye Mami take, Bayan tafiyarsu Ammi Farida na parlor tana danne danne a system dinta aka yi knocking kofar parlon, ganin mai aikinsu na dakinta yasa ta mike ta isa kofar ta bude, Shuraim ne tsaye bakin kofar, tun faruwan incident din sai ranan ya xo, he look pale, kana ganin sa kasan he just recovered, ta basa hanya tace "Good evening" ya shiga parlon yace "How are you?" Tace "I'm fine" yace "Mami fa?" Tace "She's sleeping, ta sha magani ne" yace "Ohk" xaunawa yayi saman kujera, ta tafi gun system dinta ta xauna ta ci gaba da abinda take, lkci lkci take kallonsa ta gefen ido, bayan few minutes ya juyo suka hada ido, dauke idonsa yyi yace "Heedayah fa?" Tace "She's outside" Yace "What is she doing outside?" Tace "I don't know" Bayan few minutes yace "Outside where?" Tace "Ta backyard" Mikewa yayi ya fita daga parlon, can bayan gidan ya sameta xaune a karamin garden din tana xane da karamin iccen hannunta a kasan dake shimfide wajen, jin taku ta juya da sauri, suna hada ido ta dauke kanta ta ci gaba da abinda take, ganin bata ga ya karaso ba ta d'an saci kallon hanyar taga ba kowa, juyawa tayi tana kallon wajen, can ta ci gaba da xanen da take a kasa, Farida na ganin Shuraim ya dawo parlon yyi xamansa ta mike ta wuce kitchen, ruwa ta kawo masa a tray ta ajiye nan gabansa, ta koma gun system dinta, yace "Thank you" Ba tare da ta kallesa ba tace "You are wlcm" Xuba ruwan yyi a glass cup ya sha ya ajiye snn yace "Wani course kike yi a schl" Ita dai idonta na kan system sai taji kamar ba da ita yake ba, can ta juya ganin kallonta yake tace "Biochemistry" Ya d'an buda ido yace "Why biochemistry?" Tace "Kawai" Yace "Xa ki iya kuwa?" Ta kallesa ta d'an yi murmushi tace "Gashi ina yi" Ya daga kafada yace "Allah ya bada sa'a" Tace "Ameen" Bude kofar parlon aka yi, Heedayah ta shigo, ba tare da ta kallesa ba ta wucesa snn ta gaishesa ta haura sama. Da daddare Heedayah ta fito daga wanka Mami ta shigo dakin, tunda Heedayah ta kalleta sau daya ta kasa ci gaba da kallonta, Mami ta xauna gefen gadon tana kallon Farida tace "Excuse us dear" Mikewa Heedayah tayi ta fita, Mami na kallon Heedayah ta nuna mata gefen gado, a sanyaye Heedayah ta karaso ta xauna gefen gadon tana kallon Mami, lkci daya hawaye ya kawo idonta cikin rawar murya tace "I am sorry Mami I caused you everything, I don't know......" Sai kuma ta fashe da kuka sosai ta rufe fuskarta da gadon, Mami ta dagota tace "You caused me nothing, now tell me, me da me Khaleel ya gaya maki a kansa" Hawaye na sauka idon Heedayah tace "Ce min yyi shi ya fito da ni daga wajen Kidnappers" Mami tace "So he told you he is also a Kidnapper" Heedayah ta girgixa kai tace "Aa he wasn't straight, but I suspect that" Mami tayi shirun Wani lkci snn ta sauke ajiyar xuciya cikin sanyin murya tace "Khaleel Kidnapper ne Heedayah, he is a hoodlum with large gang, but this should be between just I and you, kada ki fada ma kowa koda Farida kuwa" Heedayah ta fashe da sabon kuka tace "Mami shi ya dauke ku ko? Shine yyi kidnapping din ku ko?" Mami dake kokarin ganin hawaye bai kawo idonta ba tace "Shi yasa aka dauke mu Heedayah, Shuraim ya ta6a gaya min he don't trust him not even for a second, haka ma Junaid amma duk ban dau xancen su da muhimmanci ba, sai gashi, Khaleel is beyond ur thought dear, he is thug..." Heedayah ta fada jikin Mami tana kuka sosai tace "I am happy he didn't hurt you Mami, ni na jawo maku kiyi hakuri ki yafe min, I don't know why I trusted him all of a sudden" Mami ta goge hawayen da ya sakko nata idon a hankali tace "I don't think we are safe together anymore a gidan nan Heedayah, nayi ma Amminki magana xaki koma can kano cikin satin nan, don bana son wani abu ya sameki, Kar ya ci gaba da bibiyarki ya cuce ki..." cikin rawar murya Heedayah tace "Mami mu tafi kanon gaba daya plss, kema u are not safe anymore" Mami tace "Aa... am going no where dear, ke kam xaki koma wajen Amminki, I don't want you to be here" Heedayah ta shiga goge idonta bata dai ce komai ba, Mami tace "And ki fada min gaskiya do you have any feeling for Junaid, bana son a shiga hakkin ki, don matsayinki daya da junaid a wajena" Heedayah ta dago da sauri tana kallon Mami, Mami tace "Yes, tell me" Sauke idonta tayi ta kasa cewa komai, mamaki ya cikata, Mami tace "Kar ki ji komai ki gaya min gaskiya" Heedayah dai ta ma rasa abinda xata ce, Mami tace "Sbda incident din nan da ya faru Yakumbon ki tace xa ayi maki aure kada ya ci gaba da bibiyanki, I think ana komawa xa ayi magana, so tell me ur mind now...." Jin Heedayah ta ki cewa komai still, Mami ta kamo hannunta tace "Toh ki gaya ma Farida gobe ta gaya min kin ji??" Heedayah dai sai kallonta take ko kiftawa bbu, Mami ta mike tace "Good night dear" daga haka ta fita dakin ta kullo kofar, Heedayah ta fashe da wani kuka tana imagining wai Junaid, da wani idon ma xata iya cewa Mami bata son Junaid, she just can't, kuka take sosai sai dai ba xancen Mami na karshe ne ke sata kuka ba, taji xuciyarta yyi mata xafi she wish this is a dream na cewa Khaleel Kidnapper ne..... Khaleel ya sauka kan napep ya ba mai napep din kudinsa snn ya karasa layin walking calmly, karfe takwas da yan mintuna ne na dare, sojoji ne bakin layin a xaune, ga motarsu daga gefe a tsaye, ya fiddo ID card dinsa ya nuna masu snn ya shiga layin a hankali yake tafiya har ya isa bakin gate din gidan, sojoji ne tsaye a gate din, suka tambayesa wa yake nema, yana kallonsu yace "My aunt..." yana fadin haka ya ciro iD dinsa ya nuna masu su ma, daya sojan ya bude gate din Mai gadi ya taso da sauri, Khaleel ya dake yana kallon Mai gadin dake kallonsa shi ma yace "Wa kake nema?" A nutse yace "Mami" Bai jira cewar Mai gadin ba ya shiga ciki yana maida ID dinsa aljihu, dai dai nan aka bude kofar main parlor, Shuraim ya fito tare da Junaid, lkci daya Khaleel ya juya ya fiddo wayarsa ya nufi parking space ya kara wayar a kunne kamar me receiving din call yana tsaye parking space din, Shuraim ya karaso compound din tare da junaid yana kallon Khaleel da ya juya masu baya wayarsa a kunnensa har lkcn, ya kalli sojojin dake tsaye bakin gate snn ya sake kallon parking space din, ta madubi Khaleel ya ga Shuraim ya nufo sa.....

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull