Heedayah complete Novel - Chapter 84
Heedayah complete Novel Chapter 84: Heedayah complete Novel Chapter 84. Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... 9/12/21, 8:04 PM - ,: Shiru…
2,735 words
Heedayah isn't free, you read for free 馃し馃徎鈥嶁檧锔忦煠佛煆烩€嶁檧锔�
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Chapter notes and social links
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... 9/12/21, 8:04 PM - ,: Shiru Ammi tayi tana kallonta, Heedayah ta kasa kallon Mahaifiyartata sai fidgeting din yatsunta take, mika mata wayar Ammi tayi, ta karasa ta amsa ta juya ta bar parlon ta kulle mata kofa ta koma dakinta, gefen gado ta xauna tayi dialing number Khaleel, yana fara ring ya daga, a hankali tace "Ina yini?" Cikin Husky voice dinsa yace "Lafiya lau, ya gida?" Tace "Alhmdllh, ya kowa da kowa" Yace "Fine....." D'an murmushi tayi tace "Do you like it in there?" Ya d'an yi shiru sannan yace "Nop, not when u are not here Heedayah" Tace "Uhn you need to get use to ur relatives, and nasan Sumayya xata dinga keeping dinka company ai" Yace "Wace haka?" Tace "Cousin dinka mana" yyi shiru, tace "Ko ba haka ba?" Yace "Haka ne" turo baki tayi kamar xata yi kuka tace "Haka xaka ce min?" Yace "Toh yi hakuri, ba haka bane..." Knocking kofarta aka yi, tayi kasa da murya tace "Hold on pls xan bude kofa ana knocking" a hankali yace "Ohk dear" ta mike ta bude kofar taga Maid dinsu ce Amina, gaisheta Amina tayi tace "Hajiya kin yi bako a parlor yana jiran ki" Da mamaki Heedayah tace "Bako?" Amina ta gyada mata kai tace "Ehh" Juyawa tayi ta koma dakin, Amina ta bar bakin kofar, Khaleel yace "Wani bakon kika yi?" Heedayah tace "Nima ban sani ba wllh, let me go and check idan na dawo daki xan kiraka" A hankali yace "Alright..." Tace "Bye..." Daga haka ta katse wayar, ta dau mayafinta ta yafa snn ta fita, parlon baki ta nufa ta bude a hankali ta shiga da sallama tana leka ciki, Shuraim ta gani xaune idonsa a kan screen din wayarsa, ya dago kai suka hada ido, ta turo baki tace "Toh kai ne bako?" Bai ce komai ba har ta karaso cikin parlon ta xauna kujeran dake kusa da nasa tace "She told me nayi bako" Shuraim yace "Ohk to kilan bakon ki ka yi a waje, ki je ki samesa" Ta buda ido tace "I tot kai take ce ma bako?" Yace "Nima ban sani ba, na dai san nace ta kira ki ki amshi laptop dinki" Heedayah ta langwabar da kai tace "Ohk... A xubo maka abinci?" Yace "I'm not hungry" Tace "Good evening" Yace "How are you" tace "I am fine" ta wara ido tace "Two minutes plss" Daga haka ta mike da sauri tanufi kofa ya bi ta da kallon gefen ido har ta fita, can dakinta ta koma ta dauko wayar Ammi ta fito, tana kusa parlon da Shuraim yake ta tsaya tayi dialing Number Farida, yana fara ring Farida ta daga, Heedayah tace "You know what sweetheart?" Farida tace "No, what?" Heedayah tace "Ya Shuraim ya xo ya tambayeki bari in kai masa wayar ku gaisa ynxu" bata saurari Farida ba ta shige parlon da sauri ta isa kusa da Shuraim dake kallonta, ta mika masa wayar hannunta murya can kasa tace "Xa a gaisa da kai" Bata jira yace komai ba ta kai masa wayar kunne ganin sai kallon wayar yake, ya kama wayar da mamaki, ta xauna arm din kujeran murya can kasa tace masa "Toh kayi magana mana" A hankali yace "Assalamu Alaikum" Murmushi kawai Heedayah ke yi tana kallonsa, Farida da taji gabanta ya fadi daga daya bangaren ta amsa a hankali ita ma tace "Ina yini Ya Shuraim" Shuraim ya kalli Heedayah da mamaki, ta wara masa ido, dauke idonsa yyi yace "Lafiya lau ya kike?" Farida tace "Alhmdllh, ya kano? Ya aiki?" Yace "Fine, ya su Mami?" Tace "They are all fine" Yace "Maa sha Allah, ana ta lectures?" Tace "Aa exams xa mu fara next week" Yace "Toh Allah ya bada sa'a, ayi karatu sosai" Murmushi Farida tayi tace "In sha Allah...." Xai cire wayar a kunnensa Heedayah ta mayar da sauri ta wani tsuke fuska murya can kasa tace "Kace yaushe xata xo kano joor" Kallonta kawai Shuraim ke yi, can dai yace "Yaushe xa ki xo Kano?" Farida tace "After my exams In sha Allah" Yace "Toh Allah ya kai mu muna jiran ki" Farida na murmushi tace "In sha Allah, ya kano weather?" Shuraim ya wani hade rai ya sake kallon Heedayah, wara masa ido tayi tana washe masa hakora, can dai yace "Alhmdllh" Farida tace "You like it there?" Yace "Sure it's cool, ki gaida su Mami" Heedayah ta turo baki ta matsa kusa da kunnensa kuma, murya can kasa tace "Kace kana son ta fito da first class" Hannu yasa ya ja bakin nata, tayi wani kara ta rufe bakin da hannunta da sauri, Shuraim dake sauraron Farida dake masa sai da safe yace "In sha Allah, thank you" Daga haka ya katse wayar, Heedayah ta bar wajen da sauri ganin Fixgota yake son yi, ta fashe da dariya har da kyakyatawa, kallonta kawai yake, tayi me isarta ta koma kujeran da take xaune ta xauna tana wani murmushi tace "Kasan me ya Shureen?" Ya hade rai yace "What's the meaning of what u just did?" Turo baki tayi taki cewa komai, ganin kallon da yake mata tace "Toh muna magana da ita ne shine take tambayata Ina ya Shureen shine na baku ku gaisa, is there anything wrong with that?" jingina yyi da kujera bai ce mata komai ba, ta ta6e baki tayi shiru, bayan few minutes yace "Abba yace xa a siya maki waya, wani iri kike so" Kallon wayarsa dake ajiye tayi ta mike ta karasa ta dauka tana duba wayar sannan tace "Irin wannan" Kallonta kawai yake, can yace "Toh sai ki rike wnn din kawai" Ta xaro ido tace "Ba sabo Abba yace a siya min ba" Yace "Wnn ma sabo ne ai" Ajiye masa tayi ta koma inda take tace "Bana son irinsa kuma" Murmushi kawai yyi bai ce komai ba, can ya kalleta yace "Ban taho maki da laptop din ba sai gobe" tace "Ohk, in kawo maka chargern?" Yace "Ehh" Mikewa tayi ta wuce dakinta ta dauko masa chargern ta dawo ta basa ya amsa yace "Thanks" Mikewa yyi yace "Sai da safe, kar ki ce ma kaka na xo" Tace "Baxa ka sha shayi ba?" Yace "Na koshi" Tace "Ohk, ina son xan maka magana, can I escort you say in gaya maka a waje" Ya kalleta yace "As u wish" bin bayansa tayi suka fita parlon.... Tafiya suke a tare tana gefensa, baka ta6a cewa dare ne don ko ina tarr da hasken fararen fitilu ga shukokin dake kewaye na ta bada Iska me dadi, bayan wani lkcn Shuraim ya kalleta yace "Har gida xa ki rakani kenan?" 'yar dariya tayi tace "Aa, ai parking space din da nisa, but idan na rakaka sai ka sake rakoni rabin hanya sannan ka koma" Bai ce komai ba, jin taki magana ya kalleta suka hada ido, tace "Ya Shuraim ka gaya min irin qualities din da kake so a wajen mace?" Tsayawa Shuraim yyi yana kallonta yace "Why did you ask that?" Tace "No just tell me" Dauke idonsa yyi daga kallonta, ta kalli wani thatch me kyau dake dauke da kujeru tace "Mu je can mu xauna sai ka gaya min" Bata jira cewarsa ba ta nufi Thatch roofing din ta hau stairs dake wajen snn ta xauna kan daya daga kujerun, bin bayanta yyi xuwa wajen, ya xauna saman kujera, ta tallabi chin dinta tana kallonsa tace "Ina jin ka?" Ya shafa beard dinsa bayan few second yace "Ohkk... ina son mace me tsafta, me kuma rikon addini" Jin yyi shiru ta xaro ido tace "Shi kenan?" Yyi murmushi yace "Aa Ina son 'yar doguwa fara, me manyan idanuwa da dogon hanci with cute lips" Heedayah ta wara ido tace "Dimples fa?" Yyi shiru yana kallonta, can yace "Yi dariya mu ga" Bata san lkcn da ta kwashe da dariya ba, yyi murmushi yana kallonta, ta gaji don kanta tayi shiru, bayan few seconds yace "Bana son dimples" Ta marairaice tace "Why" yace "Kawai haka nan" Tace "Toh baka son me gashi har gadon baya?" Ya d'an yi shiru, can yace "Toh ai ban san ya gashi yake har gadon baya ba, do you mind showing me?" ta d'an yi shiru kafin tace "Toh ai ni nawa bai kai gadon baya ba" Yace "Ehh xan iya measuring with my eyes ai" ta fara bin inda suke da kallo ganin sojoji ne can nesa da su bakin daya daga many gates din building din ta sauke mayafin kanta snn ta cire hulan gashinta ta cire ribon din da ta daure dogon gashinta da shi, tuni kamshin gashin nata ya cika wajen, kallonta kawai Shuraim yake, ta juyo tana nuna masa bak'in gashinta da ya sauko kasan shoulders dinta bai karasa gadon bayanta ba, jin bai ce komai ba ta juyo, sauke idonsa yyi tace "Have u finish measuring?" Yace "Yeah" ta daure gashinta ta mayarda hulan snn ta daura mayafinta a kai tana kallonsa, flowers ya tsura ma ido, tace "So?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Ban son gashin da ya kai gadon baya" Da mamaki tace "Me yasa?" Ya juyo yana kallonta a takaice yace "Haka nan" Ta langwabar da kai tace "Toh kana son me wushirya?" Yace "Meye hakan?" Tace "Gapped teeth" Yace "How? In ga naki wushiryan?" Tace "Aa bani da shi ni" Daga haka ta bude masa fine set of teeth dinta, Kallonsu ya dinga yi tace "Uhm??" Ya girgixa kai yace "No, bana son wushirya" Tace "Ohk hips fa?" Yace "Meye shi?" Tayi dariya tace "Hips ne baka sani ba?" Yace "Ehh" Tace "Ohk forget that" yace "Aa nuna min" tace "Aa forget that" Shiru yyi yana kallonta, tace "And don't you want a girl that can cook all sort of varieties" Yana mata wani kallo yace "As if you can cook varieties" tace "Ni daban warce xaka so daban, nasan I don't have much cooking skills, but you will need a girl that can cook many type of food" Shuraim ya tabe baki yace "Ko ruwan xafin da xata hada min shayi kadai ta iya tafasawa ta isheni a hakan, I have never been a foodie" Dariya Heedayah tayi sosai, sai kuma tayi shiru, kallonta ya dinga yi, a hankali tace "Ya Shureen you know what?" A hankali ya matsa kusa da ita yana kallon lips dinta yace "Repeat the name again" Xaro ido tayi ta matsa daga kusa da shi tayi dariya tace "Yaya" Jin bai ce komai ba tace "Why haven't you ever thought of dating Farida? She is pretty, nice, good hearted, even her flaws are lovely, all the qualities i mentioned above tana da su, and beside all this... she loves you wholeheartedly, she's been admiring you from day one, tun jiya take min xancen ka shi sa na hada ka da ita yau a waya, I am telling you Yaya Shureen you won't regret it, she's a wife material wllh..." kallonta kawai Shuraim yake ko kiftawa baya yi, tana kallonsa a hankali tace "Kayi shiru Ya shureen" Dauke idonsa yyi kafin yace "Me yasa kike mata sha'awana?" Tace "Sbda every lady will love to have you, ka ga na farko you are handsome, sannan kana da hali me kyau duk da baka sakewa da mutane kuma baka da yawan magana, but I know you are not bad, you are just being who u are, most important of all u are religious, kana respecting Mum dinka sosai.... Ur flaws are odd and unique...." Shuraim yace "Toh me yasa ke baki yi ma kanki sha'awar inyi dating din ki ba sai ita" Dariya tayi sosai ta girgixa kai tace "Kai yayana ne bbu wnn tsakaninmu, kaga kai da Ya junaid da ya Sudais I can never imagine dating you 3, sannan ma ni ina da wanda nake so da aure" Yace "Wa kenan?" Tace "Khaleel" Ya gyada mata kai bai ce komai ba, bayan few seconds tace "I have never asked for a favor from you, ni bamu wani saba ba ma balle in tambaya, so plss do me this favor, wllh Farida na sonka sosai, na dade da sanin haka, Ina son in hada ku pls..." Shuraim yace "Toh kamar yanda kema kike da wanda kike so, nima haka nake da warce nake so" Heedayah tayi shiru lkci daya jikinta yyi sanyi, a hankali tace "Wacece ita ya Shureen?" yace "When the time comes idan baki riga ni aure ba xan kai ki wajenta" Daga haka ya mike yace "Sai da safe" Ta mike ita ma kamar xata yi kuka tace "You are rejecting my frnd ya Shureen??" Ya juya yana kallonta yace "Kema ki hakura da saurayin da kike so in hada ki da wani da ya dade yana son ki, in har kin yarda da hakan wllh wllh xan amshi soyayyar kawarki, I will date her" da wani irin mamaki take kallonsa, ya sauka stairs din yyi wucewarsa ta bi sa da ido har ta daina ganinsa. A hankali ta sauka ta koma cikin gida, Tana komawa dakinta cire kayan jikinta tayi ta shiga bandaki tayi wanka ta dauro alwala snn ta fito, bayan tayi sllh tayi shirin kwanciya ta kashe wutan dakin ta hau saman gado ta dau wayar Ammi, missed calls din Farida ta gani uku sai na Khaleel guda daya, kallon agogo tayi taga tara har ya wuce, shiru tayi tana tunanin abinda Shuraim ya gaya mata, can ta shiga contact din Ammi tayi dialing Shuraim taga bbu numbersa a wayar, mikewa tayi ta sa Hijab dinta ta fita dakin, bangarensu kaka ta nufa ta bude kofar parlon da sallama ta shiga, suna xaune sun cika parlon da hayaniya, ta xauna ta gaishesu gaba daya, kaka na mata wani kallo tace "Sai yanxu garin ki ya waye Deedaya? Tun safe sai yanxu xa ki shigo gaishe mu?" Heedayah tace "Toh na shigo kuna bacci" Tana fadin haka ta dau wayar kaka bata sake sauraron surutan da suke mata ba, ta shiga call log ta duba number din Shuraim cikin kankanin lkci ta kwashe a kanta ta ajiye wayar ta mike tace "Sai da safen ku" Daga haka ta fice daga parlon ta kulle masu kofa, tana komawa dakinta ta dau wayar Ammi, miss call din Farida ta sake gani, ta saka number Shuraim a wayar snn tayi dialing, har ya gama ring bai daga ba, sake kira tayi no answer, ta tsura ma wayar ido, can ta kira Farida kawai, Farida na dagawa tace "Wayar na wajen Ammi ko?" Heedayah tace "Aa na bar shi a daki ne?" Farida tace "ke kina ina?" Heedayah tace "Ina parlor, ya Mami fa" Farida tace "Tayi bacci, Ya Shuraim din ya tafi?" Heedayah ta d'an yi murmushi don dama ta san kiran da take ta yi mata kenan, Farida tace "Hello" Heedayah tace "Tun daxu ya wuce dama kawai xuwa yyi in kira ki a waya ku gaisa, bayan kun gaisa kuma ya wuce" Farida tace "Me yasa ya gaisa da ni to?" Heedayah tace "Uhn nima dai ban sani ba" Farida tayi shiru, Heedayah tace "Yace in basa number ki nace sai ya biya kuma ya ki biya" Farida tace "Nawa xai biya?" Dariya Heedayah tayi tace "Kudi me yawa na yankar masa shine ya ki" Farida tace "How much" Heedayah ta wara ido tace "Just 100k" Farida tace "Uhm, to turo account number" Dariya Heedayah tayi tace "Xa ki biya masa?" Farida tace "Ehh" Heedayah tace "Hm to xan turo gobe, yanxu xan maida ma Ammi wayarta" Farida tace "Toh don Allah send it tomorrow, I will call in sha Allah" Heedayah tace "Allah ya kai mu, byee" Daga haka ta katse wayar, lkci daya jikinta yyi sanyi, is she suppose to pull Farida's leg this much, tausayinta ya cika Heedayah, a hankali ta ajiye wayar don dama bata son su ci gaba da magana tana bata hope ne yasa tace xata kai ma Ammi waya, bayan wasu mintuna ta dau wayar ta shiga Kiran Khaleel, har ya gama ringing bai daga ba, ta sake kira bai daga ba, ajiye wayar tayi a gefenta ta kwanta ta lumshe ido, tunani iri iri ta dinga yi kafin bacci ya dauketa, can cikin bacci taji vibration din wayar ta bude ido a hankali ta jawo wayar tana kallon screen din....