Kenza eBookz

Heedayah complete Novel - Chapter 85

Heedayah complete Novel - Chapter 85

Heedayah complete Novel Chapter 85: Heedayah complete Novel Chapter 85. Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... 9/12/21, 8:04 PM - ,: Karfe…

3,311 words

Heedayah isn't free, you read for free 馃し馃徎鈥嶁檧锔忦煠佛煆烩€嶁檧锔�

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Chapter notes and social links

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... 9/12/21, 8:04 PM - ,: Karfe goma saura Heedayah ta farka daga baccin da ta koma da safe, kallon sabuwar wayan da Shuraim ya kawo mata dake ajiye gaban mirror tayi, ta mike xaune, sai kuma ta tashi ta tafi ta dauko ledan ta dawo ta xauna ta ciro wayar daga kwalinsa, ta dau sabon sim card da ya siyo tare da wayar tana jujjuyawa, can dai ta saka cikin wayar ta duba ko da kudi a layin taga dubu biyar, number Khaleel ta yi dialing ta kira, har ya katse bai daga ba, can ta kara kira ya dauka, tayi masa sallama, ya amsa yace "Whose line?" Tace "Nawa" Yace "Ohk okay, an kawo maki wayar ki daga Kaduna?" Tace "Aa sabuwar waya ce" Yace "That's good, ya mutanen gida?" Tace "They are fine, are you still leaving gombe today?" Yace "Ina hanya" Ta wara ido tace "Amma ban ji hayaniya ba" Yar dariya yyi, tayi shiru tana sauraronsa, his laugh was unique, bata ta6a jinsa yyi dariya ba, yace "Motar haya kike son ki ji na hau?" Tayi murmushi tace "Aa ni bance haka ba" Yace "Ohk, motar kawu na ne... And i am together with his driver" Heedayah tace "Toh Allah ya tsare, kun kusa?" Yace "Obviously" tace "Toh Allah ya kawo ku lafiya" Yace "But...." Sai kuma yyi shiru, tace "But what?" Yace "Is it necessary sai mun tsaya kano?" Bata fuska tayi tace "Ni ba necessity dinka bace ai... It's not necessary" Ya wara idanuwansa yace "Sorry ba haka nake nufi ba, anyway in sha Allah xa mu tsaya kano" Jin ta ki cewa komai yace "Kin yi shiru" Kamar xata yi kuka tace "Wato xa ma ka iya wucewa baka tsaya ka gan ni ba" Yace "Noo, baxan iya ba" Tace "Toh Allah ya kawo ku lfya" yana murmushi yace "Ameen" Daga haka ta katse wayar, Har xata ajiye sai tayi dialing number Shuraim da ta haddace, yana fara ring ya katse, sai ga shi ya kirata, dauka tayi amma bata ce komai ba, yace "How was ur night?" Tace "Fine, good morning" Yace "Morning" Tace "Ya Shureen me yasa baka ce min so kake in bar maka laptop dina gaba daya ba..." Shiru ta ji yayi, can yyi murmushi yace "Saboda nace maki bani da nawa?" Tace "Toh ai ban sani ba" Yace "Toh xan kawo maki anjima" Ta wara ido tace "Aa wasa nake, you can use it har lkcn da ka gaji da shi" Yace "Okay kin kira ne just to hear from me kika fake da laptop?" Ta turo baki tace "Sbda laptop na kira ka" Yace "I see, ya kawarki?" Tace "She's fine, why do u ask?" Shiru yyi bai ce komai ba, ita ma tayi shiru, can tace "Ya Shureen me kake son gaya min da na raka ka jiya kuma ka fasa?" Yace "Naga ke yarinya ce shi sa na fasa" Dariya tayi sosai tace "Yarinya?" Bai bata amsa ba, tace "Meye ka sani wanda ni ban sani ba har yanxu??" Shiru yyi, can yace "Allah ko?" Tace "Eh mana, ni din ce yarinya?" Murmushi yyi yace "Ohk, xan nuna maki abinda ni nasani wanda ke baki sani ba" Ta ta6e baki tace "Babu wannan abun, nice ma nasan abinda kai baka sani ba" yyi shiru.... Can yace "Da yake ke har gidan da ba naku ba kin ta6a kwana ko?" Shiru tayi ita ma kafin tace "Ban gane ba" Yace "Ohk leave it" Ta hade rai yace "Wani gidan ne na kwana da ba namu ba?" Yace "Ni xa ki tambaya?" Tace "Toh ai dai naga ba gidan wani daban na kwana ba gidan saurayina ne" Yace "Haka ne, dole ki san abinda ni ban sani ba kam, i will hang up now ina wajen aiki" daga haka ya katse wayar, ta kalli screen din snn ta ajiye wayar tana hararansa, mikewa tayi ta fita dakin ta tafi bangaren Ammi, ganin tana da baki ta wuce bangaren Mum Islam, Mum Islam na kallonta tace "Sai yanxu kika tashi?" Ta xaro ido tace "Aunty sai karfe takwas da rabi fa na kara wani baccin bayan nayi wanka, mun fa gaisa da Abba tun sassafe" Mom Islam tace "To xauna dama ina nemanki" Heedayah ta xauna gefen makeken gadonta tana kallonta, Mom Islam ta xauna gefenta tace "Ki gaya min gaskiya Heedayah..." Sosai gaban Heedayah ya fadi ta dinga kallonta, Mom Islam tace "Heedayah tell me, ke a xuciyar ki wa kike so, but kar ki manta xaman aure fa ba abinda xa ayi na shekara daya ko na shekara biyu bane, xama ne na dindindin, xama ne na har abada, ba a fatan rabuwa sai in mutuwa" Heedayah ta sauke kanta kasa, Mom Islam tace "Ina jin ki, wa kika ji xuciyar ki ya kwanta da" a hankali tace "Aunty ni Khaleel nake so" Mom Islam tace "Kin tabbatar?" Ta gyada mata kai, Mom Islam tace "Me yasa baki son kaninsa?" Heedayah tace "Aa ni bance bana sonsa ba, kawai baxan iya aurensa bane, Ya junaid is among the people that did good to me, yana da kirki sosai, kuma ya nuna min kulawa yanda xai yi ma Farida, amma ni i can't marry him" Mom Islam tace "Shi kuma Khaleel me yasa kike sonsa?" Heedayah ta d'an yi shiru, Mom Islam tace "Ina jin ki" A hankali Heedayah tace "Ina sonsa sbda shi ne mutum na farko da ya fara taimakona a rayuwa, Ina sonsa sbda yana da hali me kyau if not of the situation he found himself, kuma na ga yana da rikon addini duk da haka, kuma ina tausayinsa sosai, I don't want anything to happen to him ta dalilina, Aunty ai kinsan condition dinsa" a sanyaye ta kare maganar, Kallonta kawai Mom Islam take kafin tace "Anya ba tausayin Khaleel kike ba Heedayah?" Heedayah ta kalleta tace "Ehh ina tausayinsa kuma Ina sonsa" Mom Islam ta girgixa kai tace "Aa tausayin ya fi yawa nake kaga" Heedayah tace "Aa, bayan tausayinsa nasan ina sonsa, tun daga sanda muka fara waya da shi, Aunty kinsan fa har gidansa na ta6a kwana, his ways of life is perfect, yana rikon addini sosai, kuma in sha Allah nasan ya daina abinda yake har abada...." Mom Islam tace "Eh nasani" a hankali Heedayah tace "Wllh ina sonsa Aunty" Mom Islam tace "Toh shkkn Allah ya tabbatar da alkhairi dear" Heedayah ta sauke idonta kasa tace "Ameen, Yana hanya ma Aunty" mom Islam tace "Xai xo nan?" Heedayah ta gyada mata kai tace "Ya ma ce min ya kusa" Mum Islam tace "Shine baki sanar ma kowa ba?" Heedayah ta kalleta tace "Yanxu muka yi waya da shi ya gaya min, naje xan gaya ma Ammi naga tayi baki, shine na xo nan" Mom Islam tace "Toh Allah ya kawo sa lfya" Heedayah tace "Toh Aunty me xa a dafa masa?" Mom Islam tace "Abinci ba matsala bane ai masu aiki suna can ma suna yin na rana, kawai xuwa xa muyi ayi masa sabon snacks coz wanda ke da akwai aren't fresh" Heedayah tace "Toh Aunty" Mikewa Mom Islam tayi tace "Ki tafi nawa kitchen din Ina sakkowa yanxu" Heedayah tace "Aunty kitchen nawa ne gidan nan?" mom Islam tace "Kitchen hudu ne" Heedayah tace "Ohk" daga haka ta fita. Sai da suka kusa gama snacks din da suke yi Mom Islam tace "Nasan bakin Amminki sun tafi yanxu ki je ki sanar mata" Heedayah ta wanke hannunta ta fita kitchen din, bangaren Amminta ta tafi, Kawar Ammi daya ce a parlon, Ammi na kallonta tace "Ya aka yi?" Heedayah tayi shiru bata ce komai ba, Ammi ta mike ta wuce bedroom dinta ta bi bayanta, Ammi na kallonta tace "You want something?" Heedayah ta girgixa kai tace "Aa Ammi ya Khaleel ne xai xo?" Shiru Ammi tayi tana kallonta, can tace "Daga ina?" Heedayah tace "Daga wajen relatives dinsa a Gombe" Ammi tace "Toh ni bani xaki fadi ma ba ai, sai ki sanar ma Babanki" Daga haka Ammi ta fita daga dakin, Heedayah ta fi minti biyar tsaye kafin ta juya ta fita, kitchen ta koma gun stepmom dinta, Step mum din na kallonta tace "kin sanar mata?" Heedayah ta gyada mata kai tace "Amma tace ba ita xan gaya ma ba Abba xan gaya ma" Mom Islam tace "Bari mu koma daki sai in kira private number dinsa yana gunsa idan ya daga sai ki sanar masa" Heedayah tace "Toh" har suka gama jikinta a sanyaye yake suka fita kitchen din tare xuwa bangaren Mom Islam. Mom Islam ta kira Abban Heedayah ta mika mata wayar bayan ya daga, nan Heedayah ta sanar masa Khaleel na hanya, Abba yace "Yau?" Heedayah tace "Ehh" Abba yace "To maa sha Allah, Allah ya kawo sa lafiya" Heedayah tace "Ameen" Amsan wayar Mom Islam tayi tace "Toh xaka sanar da xuwansa ne kar ya samu matsala wajen shigowa tunda bashi da wani appointment?" Abban Heedayah yace "In sha Allah" Daga haka suka yi sallama ta katse wayar ta ajiye, a sanyaye Heedayah tace "Aunty me yasa kamar Ammi bata son ya xo?" Mom Islam tace "Aa tana so mana, tunda kince ya kusa ki tafi ki shirya sabbin kayanki na can wajenta da tailor ya kawo last week, ki kawo akwatin gaba daya in xabar maki wanda xa ki saka" Heedayah tayi shiru, can tace "Nawa ni kadai Aunty?" Mom Islam tace "Aa ke da Farida da kannin Shuraim biyu, amma bai kawo nasu ba tukun" Heedayah tace "Toh a ina aka samu measurement dinmu?" Mom islam tace "Mami ce ta turo naku, kannin Shuraim kuma Uwarsu" Heedayah tace "Ohk" mikewa tayi ta fita xuwa gun Amminta, nuna mata trolleyn kayan kawai Ammi tayi, Babban trolley ne sosai, ta ja sa har xuwa bangaren Stepmom dinta, Mom Islam ta kwantar da akwatin ta bude, kaya ne duk a goge kala ashirin da biyar masu tsada sosai ko wanne kuma da mayafinsa, duk laces ne da atamfa, mom Islam na duba kayan a nutse tace "Ba su kenan ba ma, kilan basu gama ba tailors din" Wani ubansun lace me tsada ta fiddo ta ajiye mata, Heedayah ta dinga kallon lace din, Mom islam ta dauko wani akwatin cikin press dinta ta kwantar ta bude duk takalma ne da jaka kusan kala goma, Mom Islam tace "Naki ne, tun da aka kawo ban kai gun Ammin ki ba" Takalmi da jaka da xai tafi da lace din ta fiddo ta ajiye gefen gadonta inda ta ajiye kayan, Heedayah na murmushi tace "Nagode" Mom Islam tace "Ki shiga bandaki ki sake wanka ki fito" Heedayah ta cire doguwar rigar jikinta, ta shiga bandakin, ba a dau lkci sosai ba ta fito daure da towel din step mum dinta, a nan dakin tayi sllhn azahar sannan ta shirya, kallonta kawai Step mum dinta ke yi tana murmushi don sosai kayan su amsheta, Heedayah ta sunkuyar da kanta, Mom Islam tace "Kinyi kyau sosai my daughter" Murmushi Heedayah tayi tace "Nagode Aunty" Mikewa Mum Islam tayi ta dauko kit din kayan make up dinta, nan tayi mata very light make up, Heedayah ta dawo kamar ba ita ba, tayi kyau sosai kamar wata amarya, Mum Islam ta kara fesa mata turarurrukanta iri iri sannan ta dauko mata wani dankunnen zinari da zobe ta bata ta saka, mom Islam tace "Two month ago wata kawata ta kawo na daukar maki" Heedayah na murmushi tace "Nagode Aunty" Mom islam tace "Toh kuma ina kika bar wayar kar yyi ta kira" Heedayah ta xaro ido tace "Lahh yana dakina" daga haka ta fita da sauri ta tafi dakinta dauko wayar, miss call dinsa daya ta gani, ta shiga kiransa, bayan ya daga tace "Sorry bana kusa wllh, kun iso ne" Yace "Ehh mun ma shigo" Tace "Okay no problem ko?" Yace "Sure, tare da wani soja" Tace "Toh sai kun karaso" tafiya tayi da wayar ta koma gun Mom Islam, nan ta sanar mata sun shigo, mom Islam tace "To mu je in hada maki abinda xaki kai masa kar kiyi shirme" Tare suka fita xuwa kitchen dinta, dama ta sa yan aiki su debo duk abinda suka dafa a different cooler su kawo mata kitchen dinta su ajiye, mom Islam taga warmer din a jere, ta shiga budesu one by one, shinkafa da miya with cow meat, sai tuwo da miyar assorted egusi, da garnished cous cous da ya ji hanta, pepper soup na kaza sai xuba kamshi yake, last bowl din ta bude taga coslow ne ciki, Mum Islam ta kalli Heedayah dake tsaye gefenta tace "What's his favourite?" Heedayah ta bude hannu tace "Nima ban sani ba" Mom Islam tace "Toh a kai masa shinkafa da miya da coslow da pepper soup din, sai a debi cous cous kadan a plate a hada ko?" Heedayah tace "Toh" Nan Mom Islam ta fara hada abincin a tray, ta dauko ginger and zobo drink da tayi tare da snacks tace "Shi xa ki fara kai masa" Heedayah tace "Toh" kallon wayarta da ya fara ring tayi tace "Aunty kilan sun shigo" Mom islam na kallonta tace "Toh ki fita ki shigo da shi" Heedayah ta koma ta dauko mayafinta ta sa takalminta snn ta fita, har wani walwali take kamar amarya cikin kayan jikinta, a hankali take tafiya, ta gansa xaune inda suka ta6a xama tare da Shuraim, kallonsa take tun daga nisa don kaftan ne a jikinsa da hula, bata ta6a ganinsa da manyan kaya ba sai yau, sai yyi mata kama da balarabe da yyi dressing din hausawa, sosai kayan suka yi masa kyau, shi ma kallonta yake kamar yanda take kallonsa har ta isa inda yake, murmushi tayi ta sunkuyar da kanta a hankali tace "Sannu da xuwa" Yace "Uhn baki gane ni bane?" Ta boye fuskarta tace "Ya hanya" yace "Alhmdllh" Tace "Toh ka shigo ciki" Yace "Bari in huta kadan" Ta kallesa tace "Toh a ciki ma ai xa ka huta" Mikewa yayi ta dinga kallonsa, a hankali tace "Kayi kyau" Yace "A'a ke dai kika yi kyau" Murmushi tayi ta fara tafiya ya bi bayanta, parlon baki ta kai sa tace "Bari in kawo maka ruwa" Daga haka ta wuce can kitchen din Mom Islam ta dauko tray din ginger drink da zobo sai bottle water da snacks ta fita ta koma parlon, xaune ta gansa ya jinginar da kansa da kujera idonsa a lumshe, a hankali ta durkusa ta ajiye tray din hannunta tana kallonsa ya bude idonsa yace "Thank you" ta xuba masa ruwa a glass cup ta mika masa ya amsa, Mikewa tayi tace "Ina xuwa" daga haka ta fita parlon, Bangaren step mum dinta ta tafi, tana kallonta tace "Aunty ya na parlor" Mom Islam tace "Ohk to bari in je mu gaisa, ki je ki sanar ma Ammin ki" Heedayah tace "Toh" fita tayi ta koma bangaren Amminta, cikin dakinta ta sameta, ta kasa kallonta gabanta na faduwa tace "Ammi ya iso yana parlor" Ammi tace "Wa ya iso?" Heedayah tace "Khaleel" Ammi tace "Ohk..." Bayan few seconds Heedayah ta juya ta fita dakin, a parlon da Khaleel yake ta tadda Mum Islam xaune suna gaisawa, Heedayah ta shigo ta xauna kasan carpet, Mum Islam na kallon Heedayah tace "Ki kai sa ya gaisa da su Yakumbo" Heedayah tace "Toh" Mikewa tayi tace masa sai anjima sannan ta fita daga parlon, Heedayah na kallonsa tace "Mu je yanxu?" Yace "Aa let me rest first" Shiru tayi bata ce komai ba, bayan wani lkci tace "Toh baxa ka ci snack din ba" Xaunawa yyi kan lallausan Carpet din parlon yace "Mun ci abinci a nan kano fa Heedayah, wllh I am not hungry" Lkci daya ta 6ata fuska, yyi murmushi ya dau samosa daya yace "Ke ma xo ki dauka idan kina son in ci" D'an murmushi tayi ta mike ta koma inda yake xaune leaving a little distance between them ta dau samosa daya, kallonta kawai yake har ta kai baki, sai a snn ya ci na hannunsa, kadan ya ci yace "Ban iya cin abin nan ba, yau na fara ci sbda ke" Heedayah ta xaro ido tana kallonsa, ya dau ruwa ya sha, yace "Ya isheni wllh" Shiru tayi tana kallonsa, can tace "Me kafi so cikin abinci?" Yace "fried rice, rice and stew, meat ko wani iri na halal Ina ci, I love pizza, shawarma, sausage, burger, milk drink, tea.... I think that's all" Xaro ido Heedayah tayi tace "Tuwo, wake, taliya, macaroni, egg, fish, different soups...." Katse ta yyi yace "Hell No, abinda na lissafa maki kadai nake ci a duniya" da mamaki Heedayah ke kallonsa, Sallama aka yi a kofar parlon, Heedayah ta juya da sauri, Ammi ta shigo parlon, Khaleel ya sauke idonsa kasa, xaunawa Ammi tayi saman kujera tace "Sannu da xuwa" da ladabi yace "Ina yini" da murmushi fuskarta tace "Lafiya lau ka xo lafiya?" Yace "Alhmdllh, ya gida" Tace "Alhmdllh, daxu mun yi waya da Barrister tace min tana kano" Khaleel yace "Ehh tana nan" Ammi tace "Kun hadu da ita kenan?" Yace "Aa ba mu hadu ba" Ammi tace "Ohk anjima xa mu je da driver sai in daukota in sha Allah" Khaleel yace "Allah ya kai mu" Ammi tace "Ameen, you are welcome" D'an murmushi yayi yace "Nagode" Mikewa tayi ta fita parlon, Heedayah ta wara ido tana kallonsa tace "Ashe Mami ma ta xo?" Yace "Ehh ta xo" Heedayah tayi murmushi tace "Xan bi ku mu koma" Ya wara ido bai dai ce mata komai ba, tagumi tayi tana kallon dogon hancinsa, ya shafa kansa ya bude goran ruwan ya diba a glass cup, a hankali tace "Zayyad fa?" Yace "Yana gombe mun hadu ma" tace "Wajen wa a Gombe?" Yace "Shi ma Yan uwansa na can gomben" Heedayah tace "Ohkkk" wayarta dake hannunta ne ya fara ring ta kalla ta ga Shuraim ke kiranta, a hankali tayi silencing wayar, Khaleel dake kallonta yace "Pick ur call" tace "Aa ban san waye ba" Wani samosan ta dauka ta fara ci tace "Me yasa baxa mu je mu gaida su kaka ba yanxu?" Yace "Xan je anjima kadan" Mai aiki ce ta shigo parlon ta gaida Khaleel da ladabi tana kallon Heedayah tace "Aunty tace ki je" Heedayah tace "Toh" mikewa tayi tana kallonsa tace "Bari in je in dawo" Ya gyada mata kai ta wuce, tana Isa bangaren Step mum dinta, tace "Abbanki ya kira yanxu yace yaje office ya samesa" Heedayah tace "A ina office din?" Aunty tace "Government house" Heedayah tace "Toh wa xai karasa da shi?" Aunty tace sojoji suna waje suna jiransa, Heedayah tace "Ohk" daga haka ta fita dakin, bayan ta sanar ma Khaleel abinda Aunty tace, ita ta rakasa har inda soldiers din suke snn ta koma ciki. Sai bayan la'asar Khaleel ya dawo, Heedayah har ta canxa kayan jikinta xuwa wani sabon atamfar me tsada, xaune ta samesa a parlor, ta xauna kasa tana kallonsa tace "Sannu da dawowa" yace "Thanks dear" mikewa tayi tace "Bari in kawo maka abinci" yace "Na ci abinci" tace "A ina" murmushi yyi yana kallonta a hankali yace "Wllh na ci" Tayi shiru, shi kam kallonta kawai yake, murya can kasa tace "Mami ta xo tana sama wajen Ammina" Yace "Ohk..." Bude kofar parlon aka yi suka juya a tare, Shuraim ne ya shigo Heedayah ta dinga kallonsa, ya ja gefe ya tsaya, Sudais ya shigo parlon, wara ido Heedayah tayi ta mike tana kallonsa tace "Ya Sudais" murmushi ya sakar mata yace "Cutie..." Bata san lkcn da ta nufesa da gudu ba, saura kiris ta rungumesa lkci daya ta ja baya, sai kuma ta fashe da dariya tana kallonsa, shi kam murmushi yake, Khaleel ya dauke kansa, Shuraim dama tuni yyi hakan....

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull