Heedayah complete Novel - Chapter 86
Heedayah complete Novel Chapter 86: Heedayah complete Novel Chapter 86. Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... 9/12/21, 8:04 PM - ,: Kallon…
2,763 words
*Wlh nayi busy fans ayi min uxuri, it's just for sometimes plss...*
Heedayah isn't free, you read for free 馃し馃徎鈥嶁檧锔忦煠佛煆烩€嶁檧锔�
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Chapter notes and social links
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... 9/12/21, 8:04 PM - ,: Kallon agogon jikin wayar dake nuna karfe sha daya da rabi tayi ta daga kiran ta kai kunne ba tare da tace komai ba, sallama ta ji yyi ta amsa snn tace "Ya hanya?" Yace "Alhmdllh" Shiru tayi daga haka, yace "I missed your calls" Ta turo baki tace "Eh ni ban gane maganganun da ka min daxu ba" Yace "Au haba?" Tace "Ehh mana" Yace "Then isn't it better to forget it?" Tace "Noo, sai ka gaya min me yasa xaka wani ce kai kana da budurwa bayan baka da ita, ance maka Faridar bata da class ne? Ai dai bata ta6a nuna maka tana sonka ba, kuma ynxu kana nufin na xubar da class dinta na gaya maka kenan da xaka wani ce A'a?" Yace "Tare muke yawo da ke da kika san banda budurwa?" Tace "Ko ba tare muke yawo ba ni dai nasan baka kula mata, to me ma kke ce masu idan ka kulasu" murmushi yyi yace "Accept my frnd and I will accept ur frnd also, isn't the equation balanced?" Ta marairaice tace "Amma dai kasan ni ina da wanda nake so and I made a lot promise to him..." Shuraim yace "Really?" Tace "Eh" Yace "What sort of promise?" Tace "That's between I and him" Yace "Fine, nima I made lot of promises to my girl..." Shiru tayi bata ce komai ba, lkci daya taji wani haushinsa, calmly yace "Can I go off ur line now?" Bluntly tace "Noo, ba mu gama magana ba" Yace "Ohk Ina jinki gobe da safe xan fita aiki" Kamar xata yi kuka tace "Don Allah ya Shuraim kar ka mana haka, tell me is there anything wrong with Farida da kake tunanin you won't love her?" Yace "Look, kema kiyi tunani, there is nothing wrong with my frnd dat will stop you from loving him, idan har da gaske kina son Farida you can sacrifice ur so called love for her, in har kika yi hakan wllh I am giving you my words gobe ma sai in kai maganarta gun Abbana" Kasa cewa komai Heedayah tayi mamaki ya cikata, jin ta kasa cewa komai yace "You just think about it, sai da safe" tace "Wait, waye mutumin da kake cewa" yace "Idan kince in kawo maki shi sae in kawo maki shi" Ta wani hade rai tace "Ka kawosa in masa me? Why don't you want to understand ina da wanda nake so??" Yace "Fine, Kar ki sake kawo min maganar Farida nima" Daga haka ya katse wayarsa, ta6e baki tayi ta jefar da wayar tana tunanin maganganunsa, can ta kara ta6e baki a ranta tace "Lallai ma" d'an tsaki tayi ta kwanta, bayan kusan minti biyar ta sake jawo wayar, number Khaleel ta kuma kira bai daga ba har ya katse ta ajiye wayar ta lumshe ido tana karanto addu'ar bacci a xuciyar ta. Washegari da safe Heedayah ta gama duk abinda xata yi har karfe tara Khaleel bai kirata ba, daukar wayar tayi ta dialing numbersa amma har ya katse bai daga ba, lkci daya jikinta yyi sanyi, tana ta xaune dakin aka kira Ammi a wayar, mikewa tayi a hankali ta fita xuwa bangaren Ammi, da yake tun asuba ta fito ta gaisheta da Abbanta da step mum dinta, mika mata wayar kawai tayi tace "Ammi ana kiran ki" Amsar wayar Ammi tayi tana duba me kiranta, can ta ajiye tace "Ohk xan kirata, kinyi breakfast din?" Heedayah ta gyada mata kai, Ammi tace "Kin je gaida su kaka?" Tace "Yanxu xan tafi" Ammi ta ci gaba da abinda take, Heedayah tace "Ammi su Ashnaah fa?" Ammi tace "Yanda baki damu da su ba su ma ba damuwa suka yi da ke ba ai" Shiru Heedayah tayi tana kallonta, can ta juya a hankali xata fita, Ammi na kallon wayarta da ya hau vibrate tace "Wa ke kira?" Heedayah ta juyo ta dawo da sauri tana kallon wayar, Ammi tace "Waye?" A hankali tace "Ammi Khaleel ne" Ammi tace "Kiran me yake maki haka ne?" Heedayah ta kasa cewa komai, Ammi tace "Tambayar ki nake" Heedayah ta sunkuyar da kanta still bata ce komai ba, Ammi tace "Dauka ki fita" Daukan wayar Heedayah tayi ta juya ta fita daga dakin, nata dakin ta koma ta xauna gefen gado ta yi dialing numbersa don tuni kiran nasa ya katse, sai da ya kusa katsewa ya daga, ta wani hade rai tace "Why ain't you picking my call tun jiya?" Yace "Na jira baki gama tadi da bakon naki ba shine na kwanta, daxu da kika kira kuma I was together with my uncle, is there any thing wrong with that?" Tace "Tadi kuma?" Yace "Ehh" Tace "Ya Shureen ne fa ya xo" Bai ce mata komai ba, tace "Toh da shi din xan yi tadin?" Calmly yace "Na sani??" Shiru tayi bata ce komai ba, bayan few seconds yace "Xan fita yanxu, later..." Bata ce masa komai ba still taji ya katse wayar, sosai gabanta ya fadi ta dinga kallon screen din, ta fi minti goma xaune a haka kafin ta ajiye wayar, lkci daya ta ji jikinta yyi sanyi sosai, ta kasa ma fita daga dakin, knocking aka yi bakin kofar dakin ta kalli kofar kamar baxata tashi ba sai kuma ta mike ta isa kofar ta bude, Amina ce tsaye bakin kofar ta gaisheta snn tace "Hajiya tace ki kai mata wayarta yanxu" Heedayah ta juya ta koma daki ta dau wayar ta tafi ta kai ma Ammi, Ammi na amsar wayar Heedayah bata yarda sun hada ido ba ta juya ta fita daga dakin, dakinta ta koma ta fada kan gado ta fara kukan da bata san dalilinsa ba, tayi me isarta ta hakura tayi shiru, tana ta kwance dakin aka bude kofar, Kaka ce ta shigo Amina da tayi mata jagora ta juya ta bar bakin kofar, kaka na washe baki tana bin dakin da kallo tace "Ba shakka, ke kuma nan ne bangaren ki kenan, wnn makeken daki haka kamar parlon gidan Amadu, ashe kina nan kusa kusa da uwarki mu kuma an ke6e mu can gefe tunda cin arxiki ne, to ae dai ya fi babu wai d'an agwai da bak'in d'a...." Heedayah ta mike xaune a hankali tace "Ina kwana kaka" Kaka tace "Aa ba ruwana, meye kuma ina kwana, da ban kwana ba xaki gan ni? baki san inda nake bane da xaki wani gaisheni da na shigo dakin ki? ke dai ba kinga na xo gidan ubanki ina ta xama ba dole ki tsiro wani shakiyanci daban, amma baxan biye ta taki ba tunda ba ke kika rokeni in xauna ba" Heedayah dai bata ce komai ba, Kaka ta mika mata wayar hannunta tace "Tun daxu Farida ke son magana da ke, gashi nan kiyi mata flashing don nima ba katin gareni ba, dubu biyar ce jiya Babanki yace ya sa min, gwara inyi ta cancana kayana Ina jin muryar 'ya yana da jikokina" Heedayah tace "Toh na ji" Kaka tace "Idan kun gama ki maido min da wayata yanxun nan" Daga haka ta fita, Heedayah ta duba balance din Kaka taga kusan dubu sha biyar ce a ciki, Kiran Farida ta shiga yi, yana fara ringing Farida ta daga, Heedayah tace "How are you doing Farida?" farida tace "Am fine dear, na kira wayar Ammi baya wajen ki koh?" Heedayah tace "Eh na mayar mata tun daxu, and kilan bata kusa ne" Farida tace "Ohk, kin fasa turowa ne in sa maki?" Heedayah tayi murmushi tace "Ki bari da daddare xan turo maki" Farida tace "Uhn but tell me, why did he even ask of me all of a sudden" Heedayah tace "Kawai yana son gu gaisa ne" Farida tayi shiru, lkci daya jikin Heedayah yyi sanyi tace "Bari idan na gama abinda nake xan kira ki ynxu" Farida tace "Ohkk" daga haka Heedayah ta katse wayar, ta fi minti talatin a ynda take, damuwarta biyu a lkcn, na farko abinda Khaleel yyi mata har da kashe mata waya, na biyu kuma hope da ta fara sa ma Heedayah alhalin Shuraim din isn't even interested, gashi Farida har ta fara farin ciki, can dai ta mike jiki ba kwari ta fita dakin, bangaren Ammi ta koma, a hankali ta lallaba ta isa gun wayar Ammi ta dauka ta kwashe number Khaleel a wayar kaka ta fita da sauri ta koma dakinta. Kiransa ta shiga yi bayan ya daga tace "Shine ka kashe min waya?" Yace "To save you from struggling for words, ya gida ya kike?" Kin cewa komai tayi, yace "don't you want to say anything?" Ta fashe masa da kuka, lkci daya ya rikice yace "Kuka kuma Heedayah? to ki yi hakuri don Allah, I am really sorry" Cikin rawar murya tace "Sbda na damu da kai ma shine xaka wani katse min waya, kuma nake ta kira ka ki dauka" Ya kwantar da murya yace "Wllh bana kusa, kiyi hakuri...." Jin tayi shiru yace "Kin hakura?" Tace "Nima ban sani ba" yace "Wahala xaki bani ko?" Ta turo masa baki, yyi kasa da murya yace "For the love you are having for me kiyi hakuri pls" A hankali tace "Nayi..." Yyi murmushi yace "Good gal, ya su mama?" Tace "Suna lafiya" murya can kasa yace "But kar ki sake ce min kinyi bako plss, that hurts..." Shiru tayi bata ce komai ba, bayan few seconds yace "Gobe xan bar gombe, am tired" Da sauri tace "Da gaske?" Yace "In sha Allah" tace "Kai da wa?" Yace "Driver...." Tace "Toh plss just drop at kano pls" yace "Kano?" Tace "Yes plss" yace "Why?" Tace "Ka xo ka gaida Abbana da Ammina" Yace "That's idan Mami ta amince, and ita ma tace gobe xata shigo kano tana da case" Da sauri tace "Xata amince ai, plss tell her you will drop there too" Murmushi yyi yace "Ohk Allah ya sa.... You know what karfe nawa xan kira ki ynxu xa mu d'an fita ne" Tace "Ina xa ka?" Yace "Gidan Gwaggwo na" tace "Toh xan kira ka anjima" yace "Alright dear" a hankali tace "Take care of ur self" yace "In sha Allah" daga haka ta katse wayar, tana ta kallon wayar kafin ta nemo number Shuraim, Har xata kirasa sai kuma ta fasa ta ajiye wayar. Yau ma da daddare Amina ta kwankwasa kofa ta sanar mata tayi bako, Heedayah dake kwance tana waya da Khaleel a hankali tace "Ya Khaleel wai Ammina tana kirana" yace "Ohk, should I wait for you or I should go to bed?" Tace "Aa ba dadewa xanyi ba ynxu xan dawo, idan na dawo xan kiraka" yace "Ohk then" katse wayar tayi ta ajiye ta dau hijab dinta ta sa ta fita, visitors palor ta tafi, xaune ta samesa tana kallonsa ta karasa cikin parlon ta xauna tace "Ina yini ya shureen" ya d'an daga kai ya kalleta yace "Looks like da gangan kike 6ata min suna" Tace "To ya xan ce maka?" calmly yace "Aliyu" murmushi tayi tace "Ni dai ya Shureen na sani" ya gyada mata kai bai ce mata komai ba, kallon ledan dake gefensa tayi tace "Wayana ka kawo min" yace "Ehh" ta mike ta dau ledan ta fiddo kwalin ciki, wara ido tayi tace "Waow..." Ta kallesa cike da farin ciki tace "I really like it ya Shureen, irin wanda nake so ne wllh" ta isa kusa da shi ta xauna arm din kujera tana murmushi sosai tace "Thank you...." Ta gefen ido ya kalleta amma bai ce komai ba, ta turo baki tana kallonsa tace "Nace thank you" yace "I prefer a cup of tea to that thank you" dariya tayi tace "Ohkk" daga haka ta mike ta dau hanyar kitchen ya bi ta da ido.... Shayi ta hada masa ta xubo masa pepper soup din offals a bowl snn ta fito, har ta shigo parlon kallonta yake ta isa gabansa ta durkusa ta ajiye bowl din offals din da cup din shayin ta wara masa ido tace "Is the thank you enough?" Yana kallon pepper soup din yace "Sure you are wlcm" ta dau spoon ta deba ta xai baki ya cafkota, xaro ido tayi, yace "Mayar ciki" da sauri ta fiddo a tafin hannunta tace "Toh xan karo maka sakeni..." yace "Wnn za ki ajiye" ganin ba saketa xai yi ba ta mayar da naman cikin bowl din, a hankali ya saketa yana kallonta, da mamaki take kallonsa ita ma, ya sauke idonsa ya dau cup din shayin ya fara sha snn yace "So what have you decided?" Tace "About?" Yace "Our talk yesterday" Shiru tayi na d'an lokaci, sai kuma ta kallesa tace "I've decided discard my request, cause ba a forcing soyayya, I will console Farida in ce mata may be kai din ba alkhairi bane gareta Allah xai bata wanda ya fi ka" kallonta kawai yake ko kiftawa bbu, can yyi murmushi yace "That's because you are soo self centered, kanki kawai kika sani, you can never sacrifice ur love for her, nasan kuma da ita ce she will gladly do that for you" Heedayah tace "I am not being self centered, kaga kai ba sonta kake ba, ni ma kuma I will never agree to ur so called frnd, to ae hakan ba shi da amfani, ita ya kamata tayi hakuri tunda ba wai sonta kake ba" Shuraim dake ta kallonta yace "Haka nace maki bana sonta?" Tace "To tunda kana sonta snn ita ma tana sonka, ni me yasa xaka min dole, you are not being fair to me kenan?" Wani murmushi yyi yana ci gaba da shan shayin hannunsa, Khaleel ne ya fado mata ta xaro ido gabanta ya fadi, ta san yana can yana jiran kiranta, a hankali tace "Ya Shureen can I go now ina yin wani abu ne a sama" ya d'an kalleta kafin yace "Noo, wait in gama sai ki wuce" bata ce komai ba, bayan ya sha shayin ya ajiye yana kallonta yace "Take them back to the kitchen" tace "Pepper soup din fa?" Yace "I am full" tace "Ai baka ci ba" yace "Na sani" mikewa tayi ta dauka ta wuce da su kitchen gaba daya..... Tsaye ta gansa parlon yana kallonta yace "Mu je waje xan maki magana" Ta kalli agogo kamar xata yi kuka bata ce ma Khaleel xata dade haka ba, kofa ya nufa ta bi bayansa har suka fita parlon..... Abban Heedayah na xaune parlonsa tare da Ammi sai mom Islam, Abba ya kalli Ammi da gaba daya mood dinta ya canxa lkci daya kuma tayi shiru, yace "Say something Aisha" Ammi ta girgixa kai a hankali tace "But ur Excellency what's wrong with the Junaid da xa a biye mata don tace bata so? Idan ma bata sonsa ga Shuraim dama ni hankalina ya kwanta da shi" Abba yace "Ke dole kike son ayi mata? snn still wanda tace take so ai d'an gidan ne shi ma naga" Ammi ta kallesa da sauri tace "Wa kenan??" Abba yace "Wan Junaid din, Khaleel..." Da mamaki Ammi ke kallonsa, can tace "Haba ur Excellency, ni gaskiya ban amince da wnn xancen ba, me yasa xa a biye mata kamar ita ta haife mu??" Abba yace "Abinda yyi Junaid shi yyi yayansa, haka ko ba haka ba?" Ammi tace "Aa wllh, his past..." Sai kuma tayi shiru, Abba kallonta kawai yake, Mom Islam tace "His past is nothing to write home about.... And kina duba reputation na gidan nan ko?" A hankali Ammi tace "Exactly Maimuna" Murmushi Mum Islam tayi sannan tace "Amma kar ki manta Aunty, Mahaifiyar wnn mutumi bata san wacece Heedayah ba, bata san 'yar wacece ita ba, bata san daga inda take ba amma ta yrda ta amince ta riketa bayan shi wanda ma ya tsinceta an ki rike masa ita cikin iyalinsa" Kasa cewa komai Ammi tayi, Mum Islam tace "It isn't Khaleel's fault he found himself in such life, kar ki manta yau da Heedayah ba hannu na gari ta fada ba Allah kadai yasan wani irin rayuwa xata yi, Allah kadai yasan abinda xata xama, albarkacin wnn bai kamata ki kyamaci d'an wannan baiwar Allah da ta inganta rayuwar 'yar ki ba ba tare da hakan ya bata wahala ko shakku a ranta ba...." Murmushi kawai Abban Heedayah ke yi bai ce komai ba, Ammi dai ta kasa cewa komai.....