Kenza eBookz

Heedayah complete Novel - Chapter 90

Heedayah complete Novel - Chapter 90

Heedayah complete Novel Chapter 90: Heedayah complete Novel Chapter 90. Heedayah isn't free, you read for free 馃し馃徎鈥嶁檧锔忦煠佛煆烩€嶁檧锔�

2,030 words

Heedayah isn't free, you read for free 馃し馃徎鈥嶁檧锔忦煠佛煆烩€嶁檧锔�

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... 9/12/21, 8:04 PM - ,: Heedayah na xaune daki tana kallonsu Farida dake fiddo ankonsu daga cikin akwatin da aka kawo har an dinka kayan wanda kala biyar biyar ne, kallonsu kawai take amma gaba daya hankalinta ba a kansu yake ba, tayi nisa tunanin da take aka kwankwasa kofar dakin, Farida ta mike ta nufi kofar ta bude don duba waye, Heedayah ta kalli agogo dake nuna tara saura na safe, ta koma ta kwanta a hankali saman gado, yau kwanansu biyu da dawowa kano, a kwanakin nan biyu a ko wani second cikin faduwar gaba take, duk ta rame abincin ma bata iya ci sosai sai tunani, babu wanda ke tambayarta don me a gidan da ya fara cika da jama'ah daga wajaje daban daban sai step mum dinta dake kokarin kwantar mata da hankali ko da yaushe sanin it's always like that for a new bride to be, Farida ta dawo dakin tana kallonta tace "Aunty na kiran ki Heedayah" Heedayah tayi shiru, kafin ta mike ta sa hijab dinta ta fita daga dakin ta tafi bangaren Mom Islam, Tsaye ta sameta dakinta ta fiddo da wasu tsadaddun atamfofi da laces da aka dinka kala goma daga wani sabon akwati, tana kallon Heedayah tace "An kawo kayan dinkin ki for the week" a hankali Heedayah tace "Toh" Mom islam tace "Me maki gyaran jiki tana jira a can bangaren Ammin ki, ki wuce can yanxu" A hankali Heedayah ta sake ce mata "Toh" Juyawa tayi xata fita, Mom Islam tace "Kin ci abincin kuwa" Heedayah tace "Na ci" Mom Islam tace "Okay anjima xa a kawo kayan lefen ki idan Allah ya yrda" Heedayah dai bata ce komai bata juyo ba kuma bata tafi ba, jin step mum dinta tayi shiru ita ma, ta juyo tana kallonta, Murmushi step mum din ta sakar mata tace "Haka kike son a kai ki duk a rame Heedayah, ba nace ki kwantar da hankalin ki ba?" Heedayah ta kasa ce mata komai, Step mum din ta nufeta tace "Tell me meye damuwar ki yanxu?" Lkci daya hawaye ya kawo idonta tace "Aunty kawai ni dai ina tsoro" Stepmum dinta tace "Ki kwantar da hankalin ki xaki daina, it's like that with some, yanxu ki fara tafiya kiyi ma Abbanki godiya kafin ya bar part dinsa..." Heedayah ta gyada mata kai snn ta nufi kofa ta fita, bangaren Abban nata ta tafi ta bude kofar babban parlonsa a hankali ta shiga, yana xaune parlon tare da Sudais da Shuraim, duk suka daga kai, ganinta Shuraim ya dauke kansa, karasawa parlon tayi a sanyaye ta xauna kasa ta gaishesu, suka amsa... snn ta kalli Abbanta tace "Abba Aunty ta bani kaya, I really appreciate it" Abba yace "U are wlcm Fatima" Sudais ya mike tare da Shuraim, yace "Mun gode ur Excellency Allah ya kara girma" Abba na murmushi yace "Ameen, yanxu xaka koma Kadunan?" Sudais yace "In sha Allah" Abba yace "Toh Allah ya tsare, Allah ya maku albarka...." Duk suka amsa da Ameen, suka nufi kofa... Abba da ya bi Shuraim da ido yace "Don't forget you meet me at office later Aliyu" Shuraim yace "In sha Allah" Daga haka suka fita da Sudais, Abba na kallon Heedayah yace "Hope no problem dear?" Ta girgixa kai tace "Aa babu" Abba yace "Toh Allah ya maki albarka" a hankali tace "Ameen" bayan few seconds tace "Abba me su Yaya suka xo yi?" Da mamaki yake kallonta yace "Me suka xo yi kuma?" Bata ce komai ba, yyi murmushi yace "Na ba Sudais appointment ne, shi kuma Shuraim dama a nan yake ai...." Heedayah ta ji dadin abinda Abbanta ya fada har xuciyarta, tace "Allah ya kara girma Abba, I am happy with that, I stayed with them from the beginning because of Ya Sudais, he didn't reject me even for a second, he supported my Abba and convinced everyone I stay.... Shine silar xamana tare da su" Abbanta ya girgixa kai yace "Kuma ban sani ba, I just saw his dad is nice also, shi ma naga yana da hankali" Heedayah ta gyada kai, Abba yace "Toh Allah ya saka masa da alkhairi, amma ya kamata yyi aure shi da Shuraim..." Murmushi Heedayah tayi tace "Toh ai shi ya kusa haka kaka tace mana" Abba ya girgixa kai yace "Aa we just talked about that now, yace his mum was against the marriage, bata son auren" Shiru Heedayah tayi mamaki ya cikata, can tace "Toh did you talk to Ya Shureen also?" Abba yace "Sure I did, yace min soon" Heedayah tace "Allah ya kai mu" Abba yace "Shi kuma Junaid his uncle called yesterday, yace jiya aka kai nasa gaisuwar Yola" Heedayah ta buda ido tace "I am happy for him" Abba ya gyada mata kai yace "Sure" A hankali tace "Toh Abba why didn't you give Ya Junaid appointment also?" Abba yace "He is working... Haka Mum dinku tace" Heedayah tace "Ya Shureen fa?" Abba yyi murmushi yace "He is now my assistant family doctor" Murmushi kawai ita ma tayi, Abba na kallonta yace "Baki tambayar ma Khaleel ba?" Sunkuyar da kanta tayi tana murmushi Abba yace "I appointed him first, after the wedding in sha Allah, he will report to work" A hankali Heedayah tace "Allah ya kai mu" daga haka ta mike ta sallami Abban nata ta bar parlon tunawa da tayi Mom Islam tace ana jiranta a bangaren Ammi. Sai da ta fara tafiya parlon baki ta tadda Shuraim and Sudais, Sudais na shan shayi shi kuma Shuraim na danna wayarsa, murmushi Sudais ya sakar mata yace "Amarya" ita dai bata ce komai ba ta karaso cikin parlon tace "Yaushe ku ka xo Yaya?" Yace "Yesterday, ya shirye shirye?" A hankali tace "Alhmdllh" kallon Shuraim dake ta danna wayarsa tayi tace "Welcome ya Shureen" ya d'an kalleta yace "Thanks, ya komai?" Tace "Fine ya karin hakuri" yace "Mun gode Allah" Tace "Kai baxa kayi breakfast din ba?" Yace "No I am okay" tace "Okay sai anjima" Yace "Alright" daga ma Sudais hannu tayi ya sakar mata murmushi ta bar parlon da sauri. Ammi na parlonta da frnds dinta da wasu mata uku that are wedding planners, Ammi na kallonta tace "Ki je spare room upstairs ana jiran ki" Heedayah tace "Toh" Da yammacin ranan motoci hudu suka xo daga garin gombe kawo lefen Heedayah government house, Aunts din Khaleel ne da matan uncles dinsa sun kusa su goma, aka masu tarba me kyau na mutunci da girmamawa, akwatuna set shidda sau biyu, sai set uku makil da tsadaddun kaya suka kawo matsayin lefen Heedayah, a cikin akwatin jewelries har da sarkan zinari da dankunne da rings, kowa ya6a kayan yake don ba karya sun yi, Yayar Ammi na kallon Ammi bayan duk an gama bude kayan tace "Daga gidan uwar rikon nata aka kawo wannan kayan?" Ammi tace "Aa daga dangin mahaifinsa ne" Hajiya Salamatu tace "Allah sarki, toh Allah ubangiji ya sa gidan xamanta ne, Allah ya basu xaman lafiya, ni ko angon ma ban gani ba har yanxu...." Ammi ta d'an yi murmushi tace "Ameen" Heedayah na bangaren Stepmum dinta da su Farida an gama mata gyaran jiki na ranan, wani kyau na musamman tayi skin dinta sai glowing da sheki yake kana ganinta kaga amarya, amaryar ma 'yar gata, tun da taji an kawo kayanta take kukan da bata san dalilinsa ba, babu irin lallashin da Farida da su Zainab basu yi mata ba amma kamar suna dada tunxurata, Stepmum dinta ta ja ta xuwa bedroom dinta tana mata wani kallo tace "Wani iskanci ne wnn kuma Heedayah, kukan meye haka kike yi ma mutane kamar warce aka doka? Kinsan idan bangaren Amminki kike sai ta 6ata maki rai ko?" Ta fashe da kuka sosai tace "Aunty kawai ni dai gabana faduwa yake, wllh tsoro nake ji" Mom Islam ta xauna gefenta cikin kwantar da murya tace "Toh kiyi ta addu'a, babu abinda xai faru my daughter, ko wacce amarya kan ji hakan ki kwantar da hankalin ki kin ji?" Heedayah ta gyada mata kai da kyar hawaye na sauka idonta, Mom Islam tace "Kun yi magana da Khaleel din?" Heedayah ta girgixa mata kai, Mom Islam tace "Toh ina wayar taki?" Cikin sanyin murya Heedayah tace "Yana can daki na" Mom Islam tace "Bari Farida ko Rabi'ah su dauko maki, kilan ma ya kira ki" daga haka ta juya ta fita, Heedayah ta koma ta kwanta hawaye na sauka idonta a hankali, ba a dau lkci ba Farida ta kawo mata wayarta ta amsa Farida ta fita dakin, miss call din Khaleel daya ta gani sai na Shuraim daya, a hankali tayi dialing number Khaleel, yana fara ring ya katse sai gashi ya kirata, cikin sanyin murya ta amsa sallaman da yyi mata tace "Ina yini?" Cikin cool voice dinsa yace "Alhmdllh Heedayah, how are you?" a hankali tace "I'm fine" yace "Noo, ur voice isn't, ko kuka kika yi?" ta turo baki tace "umm" yace "Why" mikewa xaune tayi tana goge idonta tace "I am just afraid" sai kuma ta sakar masa kuka, ya d'an yi shiru kafin yace "Afraid of what Heedayah?" Cikin rawar murya tace "Nima ban sani ba" Yace "Toh kiyi addu'a" tana hawaye tace "Ina yi" yace "Pls ki kwantar da hankalin ki, don't stress ur self much" Ta gyada masa kai kamar yana ganinta, yace "Kina cin abinci?" Tace "Bana iya ci" yace "Aa ki dinga ci, kina son ki kara ramewa ne? You are making me feel sick also" Ta girgixa masa kai bata iya ta ce komai ba, yace "Tell Farida to get you something to eat now idan kin gama ci sai ki kirani yanxu" Cikin sanyin muryarta tace "Toh" Daga haka ta katse wayar ta ajiye, mikewa tayi ta nufi kofa ta bude tana kallon su Farida dake parlon Mom Islam tace "I want a cup of tea plss" Murmushi kawai mom Islam tayi, Farida ta mike tace "Ohk dear" daga haka ta mike ta fita daga parlon Heedayah ta koma dakin ta xauna. Daukar wayarta tayi ta shiga kiran Shuraim da yyi mata miss call, har ya gama ring bai dauka ba ta ajiye wayar, Farida ta shigo dakin da cup of tea and pepper soup ta ajiye mata, saukowa Heedayah tayi kasa a hankali tace "Thank you" Murmushi Farida tayi mata tace "U are welcome Aunty Heedayah" Heedayah ta wani hade rai, da sauri Farida ta juya ta fita dakin tana dariya, Heedayah ta dau shayin ta fara sha a hankali, pepper soup din bata wani ci da yawa ba ta rufe snn ta tafi bandakin Auntynta ta wanke bakinta ta fito, daukar wayar tayi ta shiga kiran Khaleel, katsewa yyi ya kirata ta daga ta kai kunne, yace "Har kin ci abincin?" Ta gyada masa kai tace "Uhm" yace "Aa ban yarda ba" Tace "Wllh na sha shayi with pepper soup now" yace "Good dear, how are you feeling now?" Cikin sanyin murya tace "Alhmdllh" Yace "Now tell me, what's making you afraid or disturbed?" Shiru tayi, yace "Talk to me dear, feel free" A hankali tace "That I am getting married" Murmushi ya d'an yi yace "And whats making you afraid because u are getting married?" Ta d'an yi shiru kafin tace "Nima dai nan sani ba" Yyi kasa da murya yace "In dai kina sona you need not to be afraid, I am not a beast, or am I?" Ta sauke idonta kamar yana ganinta bata ce komai ba, yace "Talk to me" A hankali tace "Baxa ka dinga bani tsoro ba?" Sauraronta yake da mamaki, can yace "Wani irin tsoro?" Tace "Nima ban sani ba" Ya d'an yi murmushi yace "Baxan baki tsoro ba wife" Sun dade sosai suna magana da Khaleel har kusan la'asar, a dai dai lkcn kuma frnds din Mami da sisters dinta da su Hajiya Zuwaira da step mum din Sudais suka iso daga Kaduna da Boxes set shidda cike da kaya.....

Heedayah isn't free, you read for free 馃し馃徎鈥嶁檧锔忦煠佛煆烩€嶁檧锔�

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull