Idan kaya ya gaji book 3 - Chapter 18
Idan kaya ya gaji book 3 Chapter 18: Idan kaya ya gaji book 3 Chapter 18. ƳAR SHUWA:. "Mama wannan mutane haka danƙam anya kuwa zamu tsaya? Suna fa nace…
4,340 words
Barka da zuwa wannan group me albarka,kina business amma kullin kina yawan ayimiki ,logo, sticker da sauransu
Kiyi joining wannan linki din insha Allah zan koya miki yanda zaki yi da wayan hanninki batare da ko sisin kiba
Ina nufin 🆓🆓🆓🆓! Yes 🆓!
Harma kidinga yima wasu kina samun kudin ki Daga gida
Kawai waya kike nema da datan ki
Kawai kishiga group din for more update Thank you
IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA UKU SHAFI NA GOMA SHA TARA.
Tsallakawa tayi inda suke. Sumy ta kawar da kanta gefe. Ita kuma ƴar Shuwa tayi mata dariyar muguntar da yake ɗauke da fassarar zaki shigo hannune yarinya. "Wallahi tun safe na fito sabida ayi aikin komai dani. To kana naka Allah na nashi ina hanyar zuwa sai ga kira daga gida Mamanmu babu lafiya. Duk wuninnan a asibiti muka yi shi amman da sauƙi na mayar da'ita gida ma. Ga kuma yanayi na ruwa" Murmushi Sa'a tayi ta saki fuskarta tace. "Allah sarki to Allah ya bata lafiya. Ramatu ma bata daɗe da tafiya ba Anty Sumayya ma tafiya zata yi nima gida zanyi ki shiga gidan dai babu kowa gaskiya duk kowa ya tafi sunan baiyi armashi ba sabida ruwa" Sallama tayi ma Sa'a ta shige a tunaninta ruwa ai ta sha. Taje taba maijego abinda zata bata tayi mata irin bayanin da tayi ma su Sa'a. Mintinta arba'in ta kira Samirah akan tazo su tafi. Bata haura minti goma ba sai gata ta iso ƙofar gidan. Sallama tayi da Alawiyya ta fice Samirah taja motarta suka nufi gidan Ƴar Shuwa zuchiyarta cike da tunanin yadda zata yi da B house. Ga yara ta barsu a gidan Mama dan ta kasa tsayawa a fito dasu ta tawo dasu sabida sauri ta dai ce ma Mama gobe a kawo su. Ɗakinta a gurguje ta buɗe hannunsu niƙi_ niƙi da ledoji da fantimoti mai taya suka shiga Samirah ta zauna a kujera tana ƙarema ɗakin kallo. "To bari in yi sallah in zo in ɗaura abinci ko azahar banyi ba gashi har magriba ake kira" "Nima banyi ba bari inyi nima" Ƴar Shuwa ce ta soma shiga banɗaki ta ɗauro alwala a gurguje so take kafin Babangida ya shigo ya zamana ruwan tuwonta na wuta tunda dai tana da miyar kuɓewa ɗanya Ai kuwa ina suna kan Sallah Babangida ya leƙa uwar ɗakin da sallama ganin mata biyu ne yasa ya dawo falo ya zauna ranshi ya ɓaci sosai. Ya rasa sai yaushe zaiyi magana ɗaya a kan abu ne a dena. Idanunshi ya lumshe tunanin chus na ragargazar ruhinshi dama gangar jikinshi. Wayarshi ya zaro ya shiga cikin ma'adanar hotunan dake cikin wayar folda ta musamman shaƙe da hotunan Sabuwa ya shiga yayi ma hotonta ƙur shi kaɗai yana murmushi yana kallon bakinta. Fitowar Yar Shuwa ne yasa ya kashe hasken wayar ya zuba mata idanu. "Sannu da dawowa ka ganni sai yanzu ko? Kasan yanayin ruwa yanzu ma zan ɗaura girki amman kafin isha ma na Kammala in sha ALLAH" tana faɗin haka ta fice ta je ta kunna risho ta ɗaura ruwan tuwo kafin ta dawo taja ta zauna tana son sanar dashi batun yaje ɗakin Ramatu ya kwana. "Amm dama baƙuwa nayi Ƴar uwarmu ce daga Maiduguri tazo shine nace ko zaka je ɗakin Ramatu ka kwana ne tunda ni ina da baƙuwa gobe zata tafi ma" Kallonta yayi kawai yayi murmushin da shi kaɗai yasan fassararshi. Tashi kawai yayi ya fice zuwa can ɗakin su Mardiyya. Yayi zamanshi cikin yaran yaje ya samesu suna cin shinkafa da miya harda latas. Hannu ya saka shima ya shiga ci yana tambayarsu yaya sunan ya kasance da suka je Malama baki abun magana itace ta shiga bashi labari. A haka har suka gama ci ya ja hannun su Aɗɗa'u zuwa Masallaci. A masallacin bayan sun idar da sallah naƙocinsu ya tareshi yake sanar dashi Aɗɗa'u ya tare yarinyarshi a hanya an aiketa ya ƙwace kuɗin dake hannunta. Bayan haka kuma yaran anguwa suna kiranshi da ɓarawo dan har kaji yake sacewa. Hankalin Babangida ba ɗan ƙaramin tashi yayi ba take ya shiga ba wannan bawan haƙuri da godiyar dole kan faɗa mishi halin da ɗanshi yake ciki.. Hmm ranar a ɗakinsu Mardiyya ya kwana a falo a tsakiyar su Aɗɗa'u. Ƴar Shuwa ta kawo mishi abinci yace baya ci. Tayi juyin duniya akan sai ya bar dakin ya koma ɗakin Ramatu sabida tafi kishin yaran Sabuwa fiye da yadda take jin kishin Ramatu da Sumy. "Kije bana son damuwa dan ALLAH. Gobe da safe in baƙuwar taki ta tafi kya bani labarin abinda ya kai ki Ringim ko?" Gabanta ya tattake ya faɗi babu guiwa a jikinta da ƙyar ƙafafuwanta suka iya janta zuwa ciki. Murmushin takaici da baƙin ciki kawai yayi. Ya dubi Aɗɗa'u wanda yake bacci kamar shi sak da Yan gidansu Sabuwa gashi har dabi'unsu ya ɗakko dan dai shi tunda yake bai taɓa sata ba." Yar Shuwa babu guiwa ta shiga ɗakinta ta tadda Samira tsirara haihuwar uwarta da ubanta da sunan tana shafa mai. Zama tayi a kan gadon ba tare data ce uffan ba. Matsowa Samira tayi ta rungumeta ta baya ta shiga mata raɗa a kunnenta. "Tun sanda na haɗa idanuna dake naji a raina kin kwanta kinyi lub. Shuwa ina son zan baki duniya ki juya duniya da mutanen cikin duniya yadda ranki yake so. Ki mallaki gidaje, motoci, duk shekara kije umara dan aikin Hajj akwai wahala sau ɗaya ma ya isheki. Amman in kin bani haɗin kan abinda nake da buƙata a wajenki. Sai dai ina da tarin tulin sharuɗɗan da nake gindayama duk macen da zanyi mu'amala da'ita. Wannan kuma in kin shirya zaki sameni ne a Bamaina." Iska ta hura mata a kunnenta mai sanyi. Tuni ta lumshe idanunta. Abunda yafi komai bata mamaki shine yadda taji ta kwaɗaitu da Samira. Sakkowa tayi daga gadon ta zura rigar baccinta kana ta jawo musu leda mai cike da kaza da gurasa. "Baby sakko muci kinji duk da dai na ganki a damuwa wani abunne?" Ajjiyar zuchiya ƴar Shuwa ta sauke ta sakko suna cin kazar tana faɗa mata halin da take ciki a gidan tsakaninta da kishiyoyinta musamman ma Sabuwa da yaranta. Duk da a tunaninta ta gama da yaran Sabuwa. "Hmm ki dena damun kanki da Ɗa namiji kina tare dani. Duk taurin kanshi nan gaba kaɗan da kanshi zai dinga roƙonki yana so kuyi mu'amalar aure kina ƙi. Daga lokacin babu wata kishiya da zata sha gabanki. Su kam ki dena ma ta tasu baga magani kin karɓo ba? Ai maganin bokannan yankan wuƙa ne Mijinki kuma ai ya baki wata damane da zaki yi nazarin abinda zaki ce mishi ya kaiki Ringim. Ga dabara kice magani kuka je karɓowa da Mama na rashin lafiyarta. Ba lallai bane ya tsananta bincikenshi ba. Ke kofa ya tsananta an gano inda kuka je wajen boka ne. Tuburewa zaki yi akan cewar ku baku sani ba kwatance akayi muku zuwanku na farko kenan" Ajjiyar zuchiya Ƴar Shuwa ta sauke haka ta kwana cike da tunane _tunanen tayin Samira. Ta riga ta jarabtu da soyayyar Babangida tsoronta Allah tsoronta kada ya kamata da wani abun da za'ace har aure ya ƙare a tsakaninsu ji take yi zata iya mutuwa. Gashi tana son kuɗi tana da burin ganinta a cikin sahun manyan matan da akeji dasu. Washegari asussubar fari Ƴar Shuwa duk taje ta zuzzuba magungunan da boka ya bata a ƙofofin ɗakunan waɗanda akeso su taka. Har a ƙofar ɗakinsu mardiyya saida ta barbaɗa Sumy tana kitchen ɗinta zata dafa ruwan zafi taga sanda Ƴar Shuwa take mata barbaɗe a kofar ɗaki. Sai da ta shige ɗakinta tayi dariya kawai. tana shiga ciki tayi fitsari a kofi ta fito ta watsa a ƙofar ɗakinta ta cillar da kofin cikin kwandon shara. Su mardiyya kuwa data basu abinci basu ci ba Mardiyya haka siddan taji jikinta bai bata ba ta ko juye abincin a baƙar leda suka zubar. Su Babangida asubar fari suka fito zuwa Masallaci bayan dashi da yaran duk saida suka yi adda'ar fitowa daga ɗaki kafin suka taka maganin suka yi wucewarsu cikin kariyar Ubangiji. Kafin su fita daga gidanma saida suka yi adda'ar fita daga gida suka nufi masallaci. Ramatu kuwa tana fitowa ta taka wannan maganin taji wani zumm zumm a ƙafafunta yana haurawa a hankali har izuwa kanta. Ta ɗan jima a tsaye saida taji kamar ta dawo daidai saita wuce ɗakin aminiyarta da asussuban dan gulma na cinta na kwanan Babangida a ɗakin su Mardiyya Sai da safen Babangida ya zaunar da Aɗɗa'u ya dinga mishi nasiha yana karanto mishi illar sata da matsayin ɓarawo a musulunci. Daga ƙarshe ya ƙarashe nasihar a kansu baki ɗaya kana ya fita zuwa ɗakin Ƴar Shuwa yana tafe yana ambaton Allah ya tattake asirin baiji ko gezau ba. A falo ya samu Ƴar Shuwa da Samira suna cin ragowar ɗunamen kazar jiya. Samira da shirinta tsab harma ta fito da akwatinta falo. Zama yayi a kujera suka gaisa da Samira yake tambayarta yaya Maiduguri. "Maiduguri alhamdulillah yanzu ma nake shirin inna karya in kama hanya garinmu da nisa. "Allah sarki hakane kam. To Allah ya tsare a gaida mutanen gidan" Miƙewa yayi ya shiga ciki. Samira tace. "Bishi kiyi mishi bayani Baby. Ki tafi mishi da kaza in zaici." Miƙewa tayi ta haɗa mishi kayan kari ta shiga. Ta wuce shi yana wanka bata daɗe da zama ba ya fito da jallabiya a jikinshi zama yayi a gadon yana goge ruwan jikinshi. "Ina kwana?" Ƙur ya ƙura mata idanunshi yayi murmushi tare da cewa. "Me kika je yi a Ringim a iyakar sanina baku da ƴan uwa a ko'ina sai a Maiduguri. Sannan meye ya hanaki zuwa sunan Alawiyya da wuri har saida taro ya watse alhalin da safe kika fita da zummar tafiya gidan sunan?" "Mamace babu lafiya harma asibity na kaita to shine wata ƙawarta ta mana tayin mai maganin gargajiya. Kaji abinda ya kaimu Ringim kuma ko kafin mu isa nayi kiran wayarka bata shiga har a Ringim ɗin na kiraka wayar taƙi tafiya. Ga ruwa ya taremu a hanya kaji dalilin daɗewar da dalilin zuwa Ringim " Ƙur yayi mata yana mata kallon tuhuma sai yaji bai gamsu sosai ba da abinda tace. "Zargina kake yi da wani abun?" Ajjiyar zuchiya ya sauke illar bariki kenan kab matan zarginsu yake yi da zaran sun tambayi zuwa anguwa baya taɓa samun nutsuwa har sai yaga sun dawo. Wannan matsalar ma yanata kaita gaban Allah akan ya nutsar da zuchiyarshi waje guda "Tuwon da kika yi jiya shi zaki kawo mun ɗumamen inci maza in fita kada inyi latti. Da sauri ta fita kafin ta dawo ya gama shiryawa tsab. Yana cin tuwonne ta soko mishi zancan dawowar su Mardiyya wajenta. Ai sai ya ajjiye cokali ya kurɓi ruwan shayi ya miƙe yana gyara zaman hularshi. "Wannan maganar nace dake a barta kada a sake yinta ma. Ai su Mardiyya basu da inda zai ishesu anan a ina kikeso su zauna sabida Allah in ba dai kin shirya son takurama yaran bane amman yaushe uhm dan ALLAH ya ma za'ayi haka?" A ajjihu ya saka hannu ya ciro dubu uku ( bafa ta yanzu bace dubu ukun, ta da ce) "Ga kuɗin cefane nan kiyi shinkafa da miya da latas" Ya fito yayi ma Samira sallama ya fita daidai yaran sun fito zasu tafi makaranta Mardiyya kuma zata tafi koyarwa. Hijabinta har ƙasa kamarshi sak da yarinyar kamar an tsagakara. Samira ma bata daɗe ba ta tafi dubu arba'in ta ƙirga taba Yar Shuwa data rakata mota tana zaune ac na dukanta ta damƙa mata kuɗin. "Baby sai yaushe zan jira zuwan naki?" "To zanyi ƙoƙarin sanin yadda zan ninkeshi baibai. Shi mutumne mai zargi da kulle wallahi gashi baya barin ayi tafiya amman zan san yadda duk zanyi zan zo" Shafa ƙirjinta tayi murya ƙasa ƙasa tace. "Kiyi ƙoƙari kisan duk ƙaryar da zaki yi mishi ya barki ki tawo sabida mu samu mu tattauna kuma in gabatar dake ga manyan mata a matsayin sabuwar Baby na." Da wannan suka rabu Ƴar Shuwa ta dawo Cikin gida. Suna haɗa idanu da Ramatu sai taga tayi saurin sauke kanta ƙasa. Murmushi tayi a ranta ta ayyana magani ya cisu kenan. Anjima in tayi abincin rana zata ma Sumy gargaɗi akan kada ta sake yin girkinta daban duk ranar girkin ita ƴar Shuwan kamar yadda aka saba. Hakan kuwa akayi bayan Ƴar Shuwa ta kammala girkinta na rana ta kira Ramatu ta kawo kularta ta zuba mata sai muzurai take yi mata. Tsulum ta miƙe ta nufi ɗakin Sumy ta sameta a zaune tana shan ƙanzon masara na kwali da madara (cornflakes) "Yayi kyau wato ke an ɗaure miki ƙunƙuru ko duk ran girkina sai ki nemi abun ci sabida baki da mutunci ko?' Da ƙarfi take maganar wai ita ga shugaba. Ai kuwa ranar an kwashi ƴan kallo dan Sumy data miƙe saita watsa mata ƙanzon masarannan a fuskarta ta jawota suka soma dambacewa. Ko da Babangida yazo lefin Ƴar Shuwa ya gani cikin ƙosawa ya raba girki baki ɗaya sabida ya gaji. Kuma kuɗinshi na wajen Alhaji Abubakar Baban bola ya fito miliyan goma sai kawai ya raba girkin abun dai baima Ƴar shuwa daɗi ba sam ga kuɗi da aka narka a wajen boka amman ace Ramatu ce kaɗai ta mallaka. Ai dama Sumy ta mallaka da abun yafi mata sanyi. Haka abubbuwa suka jagwalgwale ma ƴar Shuwa. Gashi duk dabararta Babangida yaƙi barinta tayi tafiya bare ta je ta samu Samira a Bamaina. Suna dai waya, kalaman soyayyar da Samira take yi mata ko namiji albarka Saida biki ya taso a Maiduguri sai tayi amfani da wannan damar. Mama da kanta tazo ta roƙi Babangida akan zasu je biki da Yar Shuwa Maiduguri ba jimawa zasu yi ba kwana biyar kawai zasu yi. Shine Babangida ya amiince ba dan ranshi ya so ba, ba kuma dan ya yadda dasu ba gabaki ɗayansu ba. Idanunshi ya lumshe yana jin zafin rashin Sabuwa a rayuwarshi. Komai nashi ya sukurkuce sabida Sabuwa har koyarwar ma baya wani maida hankalinshi. Gashi yanzu ya kama waje yana siyan kayan baban bola in ya tara sai masu kamfani su zo su siye a kwashe a mota. Kuɗaɗen shiga sai suka ɗan ƙaru mishi,iyali kuma ya ƙara musu kuɗin cefane kuma kullum ko wacce ita da yaranta da shayi da ƙoyi da mummuƙi suke karyawa kunsan dama ta ɓangaren ciyarwa babu wasa mutumin naku Amman kullum zuchiyarshi babu daɗi hoton Sabuwa da tunaninta shine abincin cin shi da shanshi. Wani jirin jarabar sonta da kishinta yake ji. Matanshi kab sun san halin da yake ciki cikinsu babu wacce bata ƙorafin rashin samun lokacinshi da suke yi musamman ma Ƴar Shuwa data damu kanta ta hana kanta sukuni sai bokaye mayaudara ke cin kuɗinta a ƙoƙarinta na ganin ta mantar da Babangida Sabuwa abun ya ci tura. Ita kuma ta lashi takobin ko tsirara zata yi yawo saita cire Sabuwa a zuchiyar Babangida hatta su Mardiyya sai ya koresu a gidan. Ta saka su a gaba da zagi da hantara yarannan. Kullum a cikin azabtar dasu take amman a bayan idanun Babangida. Sai dai labarin na dawowa kunnenshi ta bakin Sumy. Suna ɗauki babu daɗi da yar Shuwa sosai kullum suna cikin faɗa kuma yana faɗa mata ta cuceshi data shigo rayuwarshi dan shigowarta ne ya tunzura Sabuwa har ta dage saida suka rabu. Ya mai nadamar saninta a rayuwa baki ɗaya. MRS BUKHARI. [8/26, 8:43 AM] BADA'AT IBRAHIM: https://chat.whatsapp.com/EEK9H2V5iSOFXz0Xud5Eox?mode=ac_t Yar uwa ta, kin dade kina neman in da zaki samu nighties da lounge wears masu musulmin kyau, saukin farashi da kuma kyan gani? 😍 To ki daina nema! A thrift bae closet, mun bude exclusive group inda za a dinga kawo thrift nighties, lounge wears da sauran su masu kyau, kamar Sabbi kuma farashinsu abin mamaki ne, very affordable 🤩.
A nan ne za ki kasance cikin na farko da za su ga sababbin kaya kafin su kare. Idan kina son kada ki rasa mafi kyawun kaya kafin a sayar da su gaba ɗaya, to shiga cikin group ɗin yanzu kafin ya cika 👇 https://chat.whatsapp.com/EEK9H2V5iSOFXz0Xud5Eox?mode=ac_t
IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA UKU SHAFI NA ASHIRIN CIB😆
SABUWA:.
Chapter notes and social links
ƳAR SHUWA:. "Mama wannan mutane haka danƙam anya kuwa zamu tsaya? Suna fa nace zanje kinsan halin dangin miji yanzu sai su iya faɗama Babangida banzo da wuri ba" Hararata Mama tayi tace. "To saime su faɗa mishin mana. Ke da kike neman yadda zaki kafu da kyau a gidan kuma. Ai ba'a bori da sanyin jiki ni naso ma in kaiki Maiduguri ne ɗungurungum ayi a gama. To mijinki baya barin tafiya ke kuma kina tsoron kada ya sakoki. Ina mamakin irin son da kike yima mijinnan naki shi ba kuɗine dashi irin na da ba balle kice Saifa kin tashi tsaye zaki iya karɓan ƴancinki" Ƴar Shuwa tace. "Wallahi hakane Mama kinsan amaryar da ya kawo itama tazo da nata salon iskancin duk tabi ta tsaneni kofa abincina bata ci shi kuma ya ɗaure mata ƙunƙuru baya cewa uffan sai dai duk ranar girkina tayi nata" Mama tayi tsaki tace. "Ai saiki samu hujjar da zaki saka borin cewar tunda abun hakane a raba girki ko wacce ta dinga yin nata. Dama yanzu wa yake wani yayin girki da kishiya ai kowa yaci nashi gudun kada a barbaɗa maka abinda zai zo ya halaka rayuwarka" Zaman wata matashiya da ba zata haure shekarun Ƴar Shuwan bane yasa suka tsayar da hirar tasu. "Akwai mai waje fa baiwar Allah " Ƴar Shuwa ta faɗa ma wannan matar. Sai tayi murmushi tace. "Nice mai wajen Yar aikinace nasa tazo ta kama mun layi saida na tashi daga bacci shine nazo" Kallonta dukka suka shiga yi. Da gani matar mai kuɗin gaske ne dan komai na jikinta na kuɗine gata da fara'a. Haka kurum ƴar Shuwa taji wannan matar tayi mata wani bala'in kwarjinan da bata ko son dena kallonta. Ita kuma idan suka haɗa idanu sai tayi mata murmushi. Tunda dai suka zauna har azahar basu samu shiga ba saura mutum biyu a gabansu damma sauƙinta bibbiyu ake shiga. Wannan matar ce ta dafa kafaɗar Ƴar Shuwa tace. "Ko zamu je mota muci abinci kafin layi yazo kanmu Mama ta jire mana layin?" Tayi maganar tamkar tana magana da saurayinta. Mama tace. "Kuje mana in layi yazo na kiraku" Ƴar Shuwa ta miƙe tana murmushi tabi bayanta sukaita ratsa taron mata har suka zo wajen da manyan matan da suke zuwa wajen bokan suke ajjiye motocinsu. Wannan mata ta buɗe bayan ƙatuwar motarta fara. "Bismillah ki shiga ta waccan ƙofar ko?" Ƴar Shuwa ta zagaya ta shiga suka zauna tare a gidan baya. Basket ɗin abincin yana kujerar tsakiya. Wannan mata ta buɗe lafiyayyar miyar ganyen da ƙamshinta ya mamaye cikin motar. Da tuwon shinkafan daya tuƙu. "Guda nawa zaki ci?" Ta faɗa tana rausaya idanu" "Biyu zaki saka mun ya isheni" Murmushi kawai tayi ta saka mata ta sa mata colali itama ta saka nata. Motar tayi tsit baka jin komai sai ƙaran cokali kawai, gashi ta kunna musu motar ac sai ratsasu take yi. Irin rayuwar da ƴar Shuwa ta daɗe tana burin kasancewa kenan. Kamar tana karantar zuchiyarta sai ji tayi tace. "Macce tana iya zama duk abinda take son ta zama sai dai in taso ta damkwafe a waje ɗaya. Kin saba zuwa nanne dama?" Ta ƙarashe maganar da tambaya ga idanunta masu kwarjini ta zuba ma Ƴar Shuwa. "Yaune zuwana nan wajen na farko. Mijina nake son mallaka sai kishiyoyina da nake son a saisaitama zama, da kuma tsohuwar matar mijina da yake son dawo da'ita. Kefa kishiyar ko mijin kika kawo?" Dariya suka yi duka. "Ni abinda ya kawo ni ma duk ba wannan bane. Kinsan duniya cike take da abubbuwan ban mamaki. Aini namiji bana mishi kallon ishasshe balle har in kawo shi wajen malami balle kuma kishiya" Ƴar Shuwa tace. "To hala akan kasuwanci ne ko?" "Ashe kin gane in banda abunki ana ta kuɗi wa yake ta ɗa namijin da yanzu zaka iya sakinshi ka auro duk wanda kake so in kana ganin da takura" Ƴar Shuwa sai taji matar ta kuma burgeta. Ƙwanƙwasa ƙofar motar da aka shiga yine yasa suka juya. "Kinga Mama ta biyo mu ƙila layinne yazo kanmu" Ƴar Shuwa ta ɓalle murfin motar ta fita dama ta gama cin abincin. Wannan baiwar Allah kuma ta fito da kula ƙarama a hannunta ta miƙa ma Mama. "Ga naki Mama dama nace in muka gama kema sai a kawo miki naki" Mama ta ƙarba tana godiya. "Ga Ƴata ko zaku yi ƙawance tunda naga kamar kin fita wayewa. Kin ganta mijine yake yadda yaso da'ita kishiyoyinma ba ƙyaleta suka yi ba. Ni auren ma naso in kashe to mijin nata irin almajirannanne ya kafeta a gidan bata ko son ayi batun rabuwa. Kyau iya kyau kin ganta dai tubarkallah mijin nata karayar arzikice ta sameshi yanzu ticha ne fa." Baki ta taɓe. "Ticha fa Mama. Yanzu kamarki mijinki ticha ne? No nasan yadda zanyi Mama. Mu dai jenku" Nan suka rankaya suka koma waɗanda suke gabansu su biyunnan suna ciki sai sun fito zasu shiga Suna fitowa suka shiga dama bibbiyu ake shiga. Ita wannan matar godiya kawai taje yima bokan ta ƙara bashi kuɗi masu yawa duk na godiya. "Ku kuma meke tafe daku. Ke ki dena wannan kalle kallen kar kije ki makance. Mijinki kuma ba zaki iya mallakarshi ba. Sai dai kishiyoyin naki. Sabuwa kuma babu kome a tsakaninta da mijinki. Yaran mijin dai zaki samu nasara a kansu amman sai kin zuba musu magani a abinci sunci da kansu zasu roƙi uban nasu suce zasu dawo wajenku sai yadda kika yi dasu" Ƴar Shuwa tayi mamaki Amman ba sosai ba kasancewar ba wai yau ta saba zuwa wajen bokaye ba." "To amman boka" "Ke iyakar abinda zai yiwu na faɗa miki yarinya duk ma inda kika je sai dai suci kuɗinki Babangida ba zaki iya mallakarshi ba. Kuma bazai taɓa dena son uwar Yaƴanshi ba. Sai dai fa ba zasu sake zaman aure ba." Ƙullin maganine ya faɗo daga sama guda biyu ɗaya a ƙunshe a jar fata ɗaya a ƙunshe a baƙar fata. "Wannan jan maganin shi zaki barbaɗama kishiyoyinki a ƙofar ɗakinsu su taka Muddin suka taka zasu biki zasu miki biyayya tamkar ke kika haliccesu. Wannan kuma yaran mijin naki zaki sama a abinci suma in suka ci zaki samu duk abinda kike so daga garesu. Sai dai akwai wani haske mai gauraye da duhu da yake tunkaroki sai kinyi a hankali. Na hangi tashin hankali, da ruɗani, na hangi nadama, da dana sani. Amman akwai dukiya, ɗaukaka, farin jini duk a cikin lamarin" Kan su Ƴar Shuwa ya ɗaure sosai. Mama taso jin ƙarin bayani amman ya ɗaga mata hannu dole taja bakinta tayi shiru. Kuɗinshi ya faɗa Mama ta kunce bakin zaninta zata ƙirgo. "A_a Mama bari in bayar ai mun zama ɗaya" Kuɗin ta ƙirgo ha da ƙari ta bashi suka fito tare. Ta nemi ta rage musu hanya ai kuwa babu musu suka shiga. Ai suna kama hanya aka ɓalle da wani irin ruwa mai cike da iska, ga garin yayi shegen duhu sosai. Sai samun gefen titi suka yi suka tsayar da motar dan ko gabansu basa iya gani tsabar yadda ruwan yayi ƙarfi. "Baiwar Allah kinga wata ƙudurar Ubangiji ko. Da ba dan ke ba da ruwannan haka zai taremu a hanya. Nace wai me sunanki ne kuma a wacce unguwar kike ne a Dutse?" Mama ta ƙarashe maganar tana mai dariya. Itama dariyar tayi. "Sunana Samirah amman Mama ba'a Dutse nake ba ina cikin jigawa ne cikin garin Bamaina anan nake" Ƴar Shuwa kuwa hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba tana dai zaunene tana tunanin wacce ƙaryar zata yi in taje gidan sunan da tun safe ta fita zata je. Ga kishiyoyinta suna can dole ma su sanar ma Babangida lokacin da taje gidan sunan ko dan gulma. Sanda suke bin layi ma tana ganin kiran Sa'a ƙin ɗauka tayi sabida bata san me zata ce mata ba. "Ƴar Shuwa wannan tunanin na meye haka zaki kashe kanki a banza akan wani talakan mijinki. Muna hira hankalinki baya ma wajenmu yau ga tsiya" Sai lokacin Ƴar Shuwa ta ɗan yi murmushi suka ci gaba da hirarsu. Sai wajajen biyar ruwannan ya tsagaita Samira taja motarta suka wuce. Har ƙofar gida ta sauke Mama ta wuce da Ƴar Shuwa gidan Alawaiyya. A ƙofar gidan suka tsaya har zuwa wannan lokacin ruwan ana yayyafi" "To inaga abinda za'ayi saka number ki anan. Na zama direbanki in kun gama ki kirani a waya zan zi in ɗaukeki in kaiki har gidanki. Ni dama zaki bani wajen kwana ai sai in kwana a wajenki gobe in kama hanyata ban fuye son zaman hotel ba sabida mijina babban mutum ne kuma yana siyasa kinsan hakan ka iya haifar mishi da yarfe irin nasu ƴan siyasa." "Ai babu damuwa duk da nice da miji akanki zan iya sadaukar da kwanan nawa ga abokan zaman nawa ma." Baki ta taɓe tace. "Amman har sai kin sadaukar da kwananki shin baki da ɗakinki daban kike nufi tare kuke kwana a ɗaki ɗaya wai?" Murmushi ƴar Shuwa tayi tace. "A da dai yana da turakarshi ɗakunanmu kuma a yalwace suke suma. Amman tunda karayar arziki ta sameshi shikenan muka daqo gidan haya da zama haka dai aketa haƙuri" Da haka dai ganin su Sa'a dasu Sumy sun fito suna dariya yasa Ƴar Shuwa tayi sallama da sameerah ta fito daga motar. Kallonta Sa'a tayi da mamaki tace. "Wai sai yanzu kika iso ke da akace tun safe kinma riga kowa fitowa shine saida taron sunan ya ƙare tas zaki zo? Kin ganmu fa ko wacce guduwa zata yi ruwane yaƙi ya tsagaita. Da bama zaki zo ki tadda mu ba" MRS BUKHARI [8/26, 8:42 AM] BADA'AT IBRAHIM: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GV5vhgDl7ul6aRQ08xqvVy?mode=ems_share_t