Kenza eBookz

Idan kaya ya gaji book 3 - Chapter 19

Idan kaya ya gaji book 3 - Chapter 19

Idan kaya ya gaji book 3 Chapter 19: Idan kaya ya gaji book 3 Chapter 19. Yau dai sassafe muka fito da akwatunanmu zamu wuce garin kano. Dani sa Uzairu…

3,895 words

Yau dai sassafe muka fito da akwatunanmu zamu wuce garin kano. Dani sa Uzairu zuchiyata da Maigogul daya tubure shi sai yayi mana Rakiya har izuwa Lagos kafin ya dawo. An yi juyin duniya yaƙi yarda haka Uzairu zuchiyata ya haƙura. "To Rakiya Hauwa mufa arziki ya kiramu dama dai ance kashine to ni dai na tako nawa. Kuma ko babu komai ta sanadiyyata Sabuwa zata keta hazo." Baki Hauwa ta taɓe ba tare da tace uffan ba. Maigogul bai ce uffan ba sai gyara zaman hularshi yake yi ya caɓa adon burgewa. Gaza da madamcy suka fito muka yi sallama muka kama hanyar zuwa kano bayan mun yi sallama da ƴan uwa, dan Adama ma a gida ta kwana sun samu saɓani da mijinta. Layuza ma dai auren ya ƙare dama igiya ɗaya ce jol take yawo a kanta to ya tsinke igiyar da yaga ya soma samun faraga. Gata da goyo amman a hakan ya korota Maigogul dai yace yana dawowa daga Lagos zai tusa Layuza a gaba a mayar da goyon ɗan nata. Da misalin ƙarfe sha ɗayan rana muka shiga Kano. Kai tsaye daga tasha muka yi shatar tasi ta kaimu har Airport na kano dan jirginmu na zuwa Lagos ƙarfe biyu cib zai tashi. A Airport muka yi sallah muka ci abinci. Maigogul sai waye_waye yake yi da jama'arshi ta Lagos dan baya rasa mutane a ko wanne jaha yanda kuka san wani mai babban muƙami a hannu." "To Shikenan mun samu an kama mana babban Hotel a Lagos ɗin ɗaki biyu Lolo naki ɗaya, sai ni da Uzairu Zuchiyata mu riƙe ɗaya. Amman lolo akwai wani Alhaji da matarshi ta mutu yana ta son ya sake aure shine nake son in tambayeki in Khalid bai shirya ba me zai hana in haɗaki dashi?" Wani irin kallo nayi ma Maigogul wanda shi kanshi saida ya dibibice mamakine ƙarara a fuskata da abinda naji yace. "To Shikenan na fahimci bakya so. Amman ni sonki da arziki nake yi babban hamshaƙine Lolo shi kanshi ma ba lallai fa ya amince da tayin nawa ba dan babbane a muƙami abokin hulɗata ne" Idanuna na lumshe kaina ya wani sara mun. Uzairu zuchiyata ne yace. "Maigogul ai daka bar Lolo ta nutsu ta fitar da wanda ya dace ya kuma yi daidai da rayuwarta. Sannan shi mutumin da kake so ka hadasu ya yanayin ƙarfin kuɗinshi yake?" Dariyar da Maigogul da Uzairu Zuchiyata suka saka abun mamaki sai kawai naga sun tafa. Nan Maigogul ya dinga ɓarin zance yana ba Uzairu zuchiyata shi kuma tuni yai na'am da wannan mutumi har hotonshi ya nuna ma Uzairu zuchiyata a waya. "Wallahi ke Lolo da sa'arki ma dai aka haifoki wallahi irin wannan mai arziki haka a rayuwarnan wa yake son wahala? Jibi Adama fa yadda a lokaci ƙanƙani tabi duk ta lalace har ta yo yaji. Ni dama Maigogul ne ya dage saita auri ɗan ƙauyannan amman wallahi ni nasan dama ba za'ayi abun arziki ba. Shifa ɗan ƙauye baifa san cima mai daɗi ba fa kuɗinshi ba bana ci bane na cizo ne" "Ai in faɗa maka wallahi a lokacin da aka haifi Sabuwa mun samu alkhairai da yawa fa. Ai a lokacin ne Alhaji tsalha ya biya mun kujerar umara fa naje, shi yasai ragon sunanta. Wani maigidana Marigayi Alhaji muttaƙa shima ya sai rago tiƙeƙe ya bani. Ya ɗakko dubu ashirin ta zamanin baya ya bani. Uzairu zuchiyata a sunan Lolo shinkafa da miya aka ci saida kowa yaci ya ƙoshi shi yasa take da sa'a" Uzairu zuchiyata yace. "Amman ni lokacin da aka haifeni fa? Gara inji insan wacce iriyace sa'ata ya ƙarfin taurarina suke na zahiri?" Harara na zabgama Uzairu zuchiyata na baƙin ciki da takaicinsu su duka biyun. A jirgi ya ƙarashe mishi labarin yadda sunanshi ya gudana, ya dinga soki buritsun zance Uzairu zuchiyata yana ƙara turashi dama shi haka halinshi yake. Karfe uku cib muka sauka a Airport dake garin Lagos. Ni dai dana shiga jirgi na sake gane Allah da girma yake. Ashe jirgi haka yake da girma amman a sama a hangoshi ƙarami? Isarmu titi ke da wuya muka tare abun hawa zuwa hotel ɗin da aka turama Maigogul adireshin a waya da lambar ɗaki kamar haka uku sifili da uku ɗaya (30 da 31) Eco Hotel Banana Island. Wannan hotel ɗin a tsada in akwai wanda ya fishi tsada a Lagos to tsadar da kaɗanne amman abinda na sani hotel ne wanda yawanci turawa da hamshaƙan ƴan kasuwane suka fi iya kamawa sabida bala'in tsadarshi. "Yauwa Sabuwa ke shiga mai uku sifilin kiyi odar duk abinda kike so akwai abinci kyauta ko sau nawa zaki ci. Kuci ku ƙoshi banza ta faɗi. Ni dana huta zan shiga garine" Ni dai ɗakin na buɗe na shiga na shiga ƙarema haɗuwar ɗakin kallo. Zamana nayi akan gado ina ajjiyar zuchiya. Ni bana ma jin yinwa tunda munci abinci a Airport. Mayafina na zare kawai na haye gado inaso inyi bacci. Sai nayi shiru kawai ina kallon yadda ac yake buso hayaƙin sanyi, sanyin na ratsa jikina. Fuskar Alhajin da Maigogul ya nuna ma Uzairu zuchiyata ce ta faɗo mun na lumshe idanuna. Ina tunanin da ba dan bansan wanne iri bane shi dana amshi tayin Maigogul. Abu ɗayane yake sani tunani da tsoron komawa gidan jiya. Nasan abune mai wuya in ba mazinaci bane tunda har Maigogul ya sanshi. Ƙila mata yake kai musu tunda yace abokin cinikaiyarshi ne. To inma nace ba shi ɗin ba waye zai aureni wai? Bana tunanin akwai nutsattse kamammen da zai iya neman aurena in dai gaskiya zamu faɗama kanmu tunda ubanmu ma kawaline. Sannan maza da yawa suna cikin harkar zinace_zinacennan in dai zai riƙeni da mutunci ba gara in aureshi ba me ku kuke gani amma? In kuma na tuno da kuɗurar Allah sai in ji a raina nagartaccen miji kintsattse yananan zuwa lokacine bai ba. Tunda Allah ya sani na tuba nayi nadamar gabaki ɗaya ma rayuwata ta baya wallahi Allah kenan. Dan na gaji da irin rayuwar gidanmu Allah ya sani so nake in nesanta dasu sosai ko zam samu nutsuwa a rayuwata. Kuma nafi ƙaunar auren gudun sake tsundumawa rayuwar dana tsinci kaina a baya. Lumshe idanuna nayi a hankali banfi minti goma da rufewa ba bacci ya kwasheni.

Maigogul Suna shiga ya cire babbar rigarshi ya faɗa banɗaki yayo wankanshi ya fito daga shi sai wandon shaddarshi da tawul a wuyanshi. "Uzairu zuchiyata kirasu a waya su kawo mun farfesu mai zafi in sha ni fita zanyi." Uzairu zuchiyata daya ƙyafe a gado yana waya da Felisha ya gyaɗa mishi kai tare da ɗaura yatsanshi a saman labɓanshi ma'ana yayi shiru. Shiru Maigogul yayi harda kama bakinshi. Zama yayi a kujera ya ciro manshi ya shafa ga shadda ya zarota ya kintsa tsab wanka iyakar wanka ya feshe jininshi da turaruka masu ƙamshin daɗi ya ƙarama yatsanshi zobe guda ɗaya mai baƙin dutse kasancewar agogon hannunshi cikinshi baƙine yana son kwalliyar ta fita da kyau. Uzairu zuchiyata saida ya sallami Felisha kana ya kira Hotel ya faɗa musu saƙon Maigogul cikin minti sha biyar suka kawo farfesun naman akuya lafiyayyen gaske suka dire mishi yana ci yace. "Uzairu zuchiyata ka shawo kan Lolo ta amince da batun dana kawo mata sabida naga tafi su A'isha wayewa ne kuma turancinma babu laifi tana kwaciɓawa shi yasa nayi mata wannan tayin fa. Ƙarshe in nace su Labbai zan bashi kaga harkar ta lalace kuma Lolo ce zata samu samunta ya zama namu babu kokonto. Wallahi ta aureshi munfa yi bankwana da talauci fa, gaka zaka auri baturiya kaima kaga fa harkar kawalcinma sai in dena Alhaji ya bani jari ko na motocine in dinga zuwa kwatano ina shigo dasu tunda a baya mun ɗan taɓa harkar" Uzairu zuchiyata yace. "Wai Maigogul kai ko wacce sana'a kayi ta ne?" Dariya yayi mishi kamar bazaai magana ba saida yasha romo sosai kafin yace. "Hmm har kwasar kashi nayi. Uzairu zuchiyata har angola munje munyi kasuwanci abunne yaƙi karɓarmu shi yasa muka koma harkar kawalci kuma muka shigeta da ƙafar dama shi yasa bana wasa da aikina. Har a cikin kwata mun kwana. Ni dai dan Allah tunda Lolo ƙawarka ce kama zaɓeta sama dani ubanka to ka shawo mun kanta ko Allah yasa makkannan mu sake komawarta." Da haka Maigogul ya gama shan farfesunshi ya saka kanshi ya fice. Uzairu zuchiyata kuma ya koma dakin Lolo.

SABUWA:. Ina baccina Uzairu zuchiyata yazo ya tasheni da bugun ƙofa jiki a mace na tashi naje na buɗe mishi. Saida muka yi Sallah yayo mana odar lafiyayyen abinci muna ci ne yace dani. "Lolo in kikayi la'akari da gidanmu da irin mazajen da ƴan uwanmu suke aure ni sai inga kamar riba zaki ƙirga. Ga shawara kyauta wannan Alhajin ta ɓangarenki ki amince dashi ki barma Maigogul sauran. Ni dai shawarar da zan baki kenan a taƙaice. Kinga nima abinda zai fissheni nayi kina ganin shekarun dana kwashe ina neman irin abinda raina yake so da sannu ba gashi kusan nakai ga cimma abinda nake so ba?" To zanyi nazari akai kafin mu dawo zan yanke hukuncin amincewar ko akasin hakan" Mardiyya na kira a waya ta haɗani da su Malama a waya duk muka gaggaisa suna makarantar islamiyya lokacin suna jiran Babansu ya gama ya ɗaukesu su koma gida. Nan na faɗa musu zamu yi tafiya ni da Uzairu Zuchiyata zuwa ƙasar canada su taya mu adda'a. Uzairu zuchiyata yayi carab ya fisge wayar. "Mardiyya da bakinku na karatu mai albarka ki roƙa mana Allah yasa in samu nasarar abinda zai kaimu. Ita kanta uwar taku ku sakata a adda'a" Mun ɗan jima muna waya tana faɗa mun matsalolinsu ni dai a kullum abinda nake cewa dasu suyi haƙuri duk runtsi su dinga tsayama junansu suna gani duk lalacewar gidanmu muna iya tsayama kanmu a kan duk wani abu duk girmanshi. Gaga_gaga washegari tun ƙarfe goma muka fito zuwa Airport sai ƙarfe uku jirginmu zai tashi amman ana jiye mana turmutsutsun dake titin Lagos shi yasa aka bamu shawarar mu tafi da wuri mu jira lokacin a Airport. Mun fita tun goman amman sai karfe ɗaya muka isa Airport sabida turmutsutsun titin Lagos ( go slow) kai tsaye muka wuce inda ake duba kaya a na'ura domin tantanewa. Sannan muka wuce wajen jira ga kujeru nan shaƙe da mutane. A wata kujera muka zauna da wasu mata da miji. Maigogul kuma na kusa da wani Alhaji ya zauna shima ya tsaɓa kwalliya. Hannu Maigogul ya miƙa mishi suka gaisa daga haka ya soma yi mishi surutu kai kawai na girgiza. Muna zaune aka kira fasinjar Dubai duk suka. Miƙe suka hau kan layi in suka miƙa takaddar hannunsu aka duba sai su bi wata ƙofa su fita a haka har suka ƙare. Sallahr azahar muka yi muka dawo Uzairu zuchiyata nifa yinwa nake ji. Ya kamata mu nemi abinda zamu ci gaskiya. Kai kaga Maigogul ya samu mutum sai surutu kawai yake ta zuba mishi babu kamun kai babu komai" Baki Uzairu zuchiyata ya taɓe kawai. "Kinga ga wani windo can muje muga me suke dashi ko zamu iya siya kinsan Airport kayansu tsada ko ruwane" Kafinma mu miƙe Maigogul ya iso inda muke. "Lolo muje sama akwai gidan cin abinci wannan bawan Allahn da muke tare dashi yayi mun tayi zuwa cin abinci shine nake faɗa mishi tare da yarana nake." Kallonshi nayi na bi bayan Alhajin da kallo da yake kan ƙafar bene yana haurawa. Jikina a sanyaye nabi bayansu har zuwa saman ni da Uzairu Zuchiyata teburinmu daban, Maigogul da Alhajin teburinsu suma daban ga jama'a anan ɗaiɗaiku suna zaune suna cin abinci. Dafadukan soyayyar shinkafa mai ɗauke da kayan lambu wadatacce aka kawo mana da kaza akai muka ci muka ƙoshi muka kora da lemun limka na kwalba. Godiya muka je muka ma wannan Alhajin. "Wannan sunanta Sabuwa ƴar gaban goshina kenan yarinya ƴar albarka mai tausayi. Ta rabu da mijinta tana da yara huɗu. Wannan kuma wanta ne Uzairu zuchiyata" Da sauri muka katse Maigogul ta hanyar sake yima wannan Alhajin godiya gudun kada Maigogul ya sakar mana ɓera a yayi. Ai kuwa sai muka ji an soma sanarwa a amsa kuwa cewar fasinjan Canada su hau layi jirginmu yana jiranmu. Sakkowa muka yi cikin hanzari zuwa ƙasa muka shiga layi. "Sabuwa Uzairu zuchiyata ni zan koma zamu haɗu a Lagos ranar da zaku dawo zan tawo in tarbeku. Duk abinda na baka ka tabbatar kayi amfani dasu kada kayi mana asara" Alhajinnan yana bayan Uzairu zuchiyata sai ya dube ni yayi mun murmushi ni ina layin mata. Na lura tun muna wajen cin abinci yake ta mun murmushi. Kaina na sauke kawai. "Alhaji ni zan nufi jigawa kuma in babu damuwa ka bani lambarka mana" Cewar Maigogul yana dariya. Katinshi ya zaro a ajjihu tare da littafin rubuta kuɗi ( check) ya rubuta ma Maigogul kuɗin da mu bamu san nawa bane Maigogul yaita runtuma godiya ya nufi hanyar fita. Da ido kawai na bishi yadda yake tafe bagajan_bagajan ina juyowa muka haɗa ido da Alhajinnan fuskarshi dai ɗauke da murmushi da wani irin kallon tsan da yake yi mun. A haka dai har muka fito aka duramu a bus zuwa bakin jirgi duk muka shiga kowanne ya zauna a inda lambarshi ta fito. Idanuna a runtse har saida jirgi ya saisaita a sararin samaniya kana na buɗe idanuna na sauke ajjiyar zuchiya wai yau mune a jirgi zamu tafi wata ƙasar Allah mai yin yadda yaso. Tafiyar ashe ba tafiya bace mai sauƙi ba. Wasane_gaskene saida muka yi tsawon awanni goma sha bakwai a zaune. Muyi bacci mu farka, muci abinci, muje muyi fitsari haka dai haka dai bamu muka iso Canada ba sai wajajen ƙarfe takwas na dare. Tafiya yankin azaba wai damma jirgi akwai daɗi babu gajiya babu galabaita sam. Hannun Uzairu zuchiyata na riƙe gam dan wallahi Allah ina sauke ƙafata a ƙasa bayan mun sakko daga ƙafar benen jirgin sai naji tsoro ya kamani. Jakata Uzairu zuchiyata ya riƙe mun sai dariya yake yi mun. "Lafiya Uzairu zuchiyata wani abunne ya samu shalelen Baba? Naga ka riƙeta ga jakarta ka riƙe?" Cewar wannan Alhaji da muka shiga jirgi tare. Kaina kawai na sauke Uzairu zuchiyata yace dashi. "Babu komai rigimace kawai Alhaji" Sai ya ɗanyi dariya irinta dattijai. Mu dai muna ta bin mutane a baya a baya har muka shiga wata ƙofa. Ananne akwatunanmu suke suna yawo akan wani ƙarfe mai sulu, in jakarka tazo gabanka Sai ka zare, in kayi sanya ta wuce saita sake dawowa zaka ɗauka. Uzairu zuchiyata ne ya ɗakko mana akwatunanmu wannan Alhaji yana biye damu ƙafa da ƙafa. Uzairu zuchiyata ya zuge jakata ya ciro tabarau ya saka, ya feshe jikinshi da turare ya saka namijin goro a baki sabida ya ɗauke mishi bashin da bakinshi yake yi. Muna shiga wata ƙofar tangaran sai muka jiyo ihu daga can nesa na wata baturiya da fararen fulawowi shaƙe a hannunta har tana kuka. Watsarmun da jakata Uzairu zuchiyata yayi ya kwasa a guje yana ambaton "My Heart ( zuchiyata_ zuchiyata) Ni kuma na tsugunna zan kwashe kayana da suka zubo a jaka wannan Alhajinma ya tsugunna zai kwashe mun. Ganin ya rigani tsugunnawa sai ni na miƙe inata kallonshi hardai ya gama kashewa. A tsanake cikin nutsuwa ta jini ya ke komanshi hatta murmushi ɗan gayu yake yi. "Ga jakar taki shalele. Amman dai tunda hakane ki saka mun lambarki ta najeriya Allah bashi in muka koma gida sai in kiraki in kawo miki ziyara ma har gida. Alhaji Baba ma nasan zaiyi farin ciki da wannan haɗin ko? Allah dai yasa ban yi miki tsufa ba kinganni da furfura" Murmushi kawai nayi mishi gabana na tsananta faɗuwa na karɓi jakata. Wayarshi ya miƙo mun na amsa na rubuta mishi lambata na miƙa mishi. Sai ga Uzairu zuchiyata da Felisha sun ƙaraso hannunsu sarƙe dana juna abinka da turawa. Rungumeni Felisha tayi tana farin ciki tare da yi mun sannu da zuwa ƙasarsu mai albarka. Aka sumbaci gefe da gefen kuncina dai Ni dai sai murmushi kawai nake yi. Alhaji ya tambayi Felisha ina zamu je ta faɗa mishi har adireshin gidansu naga ta bashi sai ya dubeni yace. "To shalele abinda zaifi zan zo in sameki a gidansu Felisha sai mu tattauna dukkan abinda ya dace ayi a gama kawai uhm?. Felisha can i have your number? ( Felisha zan iya samun lambarki)" Ya tambayeta tare da ƙare maganar da murmushi. "Yeah of course " ( E sosai ma) Nan ta bashi lambarta ni dai ina tsaye Uzairu zuchiyata sai kashe mun idanu yake yi. Dala ya ciro a ajjihunshi ya zura mun a cikin jakata yana murmushi yana kallon cikin idanuna ya suri akwatinshi ya wuce mu. Takunshi na bi da kallo har sai da Uzairu Zuchiyata yace. "Lolo muje kin kafe bawan Allah da idanu. Nifa dama tun a gidan cin abinci naga hakan wallahi. Tabbb wannan ba dai maiƙo ba, naga dala ya dunbuzo ya cunkusa miki ke mu dai watanmu ne ya tsaya ƙyam ya maman maza. " Dariya muka yi harda Felisha da bata sam me muke cewa ba sai dai muna tafe inaji tana tambayar Uzairu zuchiyata waye wannan Alhajin. Uhm wai kunji Uzairu zuchiyata yadda yake karya harshe irin na turawa kuwa? Sai ku rantse da Allah yayi digiri da digirgir lallai karanta ƙamus yayi rana. A madadin mu fita a Airport sai muka zagaya ɗakin jira ashe jirgi zamu sake shiga daga nan Canada zuwa Alberta. Ƙarfe goma dot jirginmu ya tashi. Awanmu huɗu a zaune a jirgi dan masifa Felisha sai nan nan take yi damu gata kyakkyawa duk da dai ba yarinya bace, amman dai shekarunta sunyi daidai a matsayin matar Uzairu zuchiyata tunda dai ba na yau bane shi ɗinma. Mun sauka a jirgi a cikin Airport ɗin YYC CALGARY INTANATIONAL AIRPORT. da misalin ƙarfe biyun dare kai tsaye muka wuce gidan cin abinci dake cikin Airport ɗin. Dan Uzairu zuchiyata yace yana jin yinwa sosai dan ta faɗa mishi daga nan Alberta kai tsaye birnin CALGARY zamu wuce a mota sai mun yi tafiyar awa huɗu da rabi. Dole muka ci abinci muka rama sallolin da ake binmu ni dai duk na gaji ma wallahi. Anan Airport ɗin muka samu masu tasi suka ɗaukemu. Ananne muka sha kallo muka kashe ƙwarƙwatar idanunmu. Kai an tafi anyi mana nisa najeriya sosai. Gari tsab komai akan tsari ga shukoki masu ban ƙawa a hanya takota ina simintinnan a lailaye wasu titinan ma da muka wuce su intalock ne ba kwalta ba. Ga lantarki tako ta ina gari kamar rana Ba dai mu muka shiga cikin gidan iyayen Felisha ba sai da safe. Danƙari ai tun daga bakin ƙofar shiga muke taka jajayen fulawowi da muka shiga cikin babban falon gidan kuwa balambalone sunfi ɗari kala kala duk an watsar dasu. Uzairu zuchiyata yana tallafe da Felisha har gaban iyayenta da mutanen gidan nasu. Mun sha runguma da sumba a kumatu tako ta ina anata waƙoƙin tarbanmu abinda yafi komai bani mamaki shine wato Uzairu zuchiyata ba karamin taƙadarin baduniye bane hannu ta saka a ajjihu ya ciro wani ɗan akwati mai ɗauke da zoben daimon ya durƙusa a ƙasa yana nuna ma Felisha zobennen tare da kakkafeta da idanunshi. Bakinta ta rufe tana kuka iyayenta da ƴan uwanta suka shiga tafi. "Will you marry me ( zaki Aure ni?) Ya furta. Nan ɗakin yahau sowa anata ambaton " Yes_yes ( E_E) "Yes ( E) ta furta tare da miƙo yatsunta ya zura mata wannan zoben ya miƙe ya rungume kayanshi. Hmm ni naga fitsara a wajen turawa saida komai ya lafa aka nuna mana ɗakinmu na saukar baƙi ɗakin da aka bani yana kallon na Uzairu zuchiyata. Banɗaki na faɗa da sauri gudawa nake ji sosai, ina zama akan sita na soma yi ina sauke numfashi sai lokacin na samu zarafin ƙarema banɗakin kallo komai na ciki kalan sararin samaniya ne, ga tsari harda kafet a shimfiɗe a bayan gidan, wajen wanka kuma ƙatoton bawone na wanka a lokacin shi ake yayi mu a Najeriya ma sai gidan wane da wane ko gidan masu kuɗin da ɗinnan. Saita ruwan wanka nayi daidai yadda zan iya na gargasa jikina sannan naji daɗi alwala na ɗauro na fito na zauna akan kujerar doguwa. Kai turawa sun iya tsara waje marar hayaniya. Ɗakin ƙaramin gadone sai kujera sai madubin bango da tebur a ƙasan mudubin inda anan mai da su turare suke, ga kafet mai laushi malale a ɗakin, sai wani ƙaton taga kusan bango guda babu labule a jiki daga ciki kuna hango waje wasu fulawowine koraye shar masu sanya mai kallo nutsuwa a bayan tagar. Man dana gani a gaban mudubin shina shafa na ɗauki doguwar rigata na zura ni dai bana ce ga gabas ba ƙofa kawai na kalla na gabatar da sallolin da ake bina ina sallama ta ƙarshe Felisha ta buɗe kofar bata shigo ba tace dai in fiti muci abinci. Uzairu zuchiyata mutuminku yana kan tebur daga shi sai gajeren wando da riga amles da wata hula yana ta hira da mahaifin Felisha suna dariya. Waje na samu a gefen wata ƴar budurwa na zauna muka sake sabuwar gaisuwa turancin nawa da suka lura babu ƙarfi sai suka fi mayar da hankalinsu a kan Uzairu zuchiyata. Soyayyen dankalin turawa da soyayyar kaza mai zuma aka zuzzuba ma kowa da wata iriyar miya ita bata siga ba ita bata mazar ƙwalla ba dai Ni dai dankalinne na ɗanci babu laifi amman kazar da ƙyar na cinye yanka ɗaya zaƙi ne cau a jikinta na kora da wani lafiyayyen jus ɗin kwakwa dake cikin wani kwali mai daɗi. Uzairu zuchiyata kuwa ranshi fes Felisha take bashi abinci a baki yana amshewa harma da tambayarta wanda yayi girkin. An ɗan jima ana hira daga bisani iyayen Felisha da ƙannenta suka tafi suka basu waje. Nima wajen na basu nayi komawata ciki. Rigar baccin da Uzairu Zuchiyata ya sai mun itace a jikina ina kwance na rufa a lallausan bargo Felisha ta turo ƙofa ta bani wayarta wai ana son magana dani. Karɓa nayi tare da kara wayar a kunnena sai naji muryarshi mai sanyinnan yace. "Shalele da fatan kun sauka cikin ƙoshin lafiya ko?" Idanuna na lumshe nace. Lafiya lau gani ma a kwance inaso in ɗan yi bacci duk na gaji" Murmushi yayi mun tare da cewa. "To babu damuwa ki kwanta kiyi bacci. Gobe zan kira ki ki saka mun ranar da zanzo in ganki domin mu tattauna wata muhimmiyar magana" Idanuna na buɗe tare da cewa. "To shikenan nagode ƙwarai sai munyi magana a huce gajiya" Da haka muka yi sallama na mayar ma da Felisha wayarta na dawo ɗaki. Murmusawa kawai nayi mrs Buhari

Tofa mutanen Canada dai an sauka lafiya. Ga kuma wani Alhaji ya ɓullo Ga Alhajin da Maigogul yayi ma Sabuwa tayi shima. Ga Ƴar shuwa dai ta faɗa harkar maɗigo.

Anan littafi na uku yazo ƙarshe. Littafi na huɗu dana biyar zai soma zuwa muku bayan mun gama dogon hutun da zanje.

Akwai sauran labari sosai a gaba. Akwai cakwakiya masu yawa fa a gaba

Dan Allah na roƙeku a wannan karon aimun uziri zan tafi hutu mai tsayi kafin in dawo sabida idanuna sun tasanma ciwo sosai To dole sai nabi a hankali da fatan za ku daure kuyi mun uzuri dan Allah?

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull