Idan kaya ya gaji book 3 - Chapter 2
Idan kaya ya gaji book 3 Chapter 2: Idan kaya ya gaji book 3 Chapter 2. "shikenan Lolo yanzu duk jan hankalinki da nake yi saida kika sake yadda wani…
4,026 words
"shikenan Lolo yanzu duk jan hankalinki da nake yi saida kika sake yadda wani shegen ya durka miki wani cikin. Kin mance da jar wahalar da kika sha, da gargaɗin da likita ya bayar akan ki, ke da kamar ba ma zaki rayu ba. Ai shikenan, ke kuma Hauwa hankalinki ya kwanta, kai kuma me son ji Lolo to cikine da'ita sai kayi abinda zaka yi akai." Tana faɗan haka tayi shigewarta ɗaki. Tana kutuntuma zagi. Maigogul ya daɗe a tsaye yana nazari kamar ma bazai ce komai ba. Hauwa kuwa sai shewa take yi tana faɗin. "Bana dai ƴar so za'a wuce gidan miji tunda ita ba sai tayi ciki sau uku da namiji ɗaya yanzu duk cikin daya shiga dole a haifeshi. Uhm lallai nagode Allah da yasa a ɗakin Rakiya za'a soma kafa tarihin ɗan kuka, Maigogul da Rakiya za'a sha raino. Mai arzikin dai da ake nema ake fata ba'a samu ba Alhamdulillah. Yadda yaranmu aka cusa su kema dole a cusa ki." Da ido maigogul yake ta bin Hauwa abun al'ajabi baice uffan ba. Waya Maigogul ya zaro a ajjihunshi ya danna kira, jim kaɗan aka ɗauki wayar. "Cicib kazo ka same ni a asibiti zaka raka ni wani wajen daga asibitin" Iyakar abinda ya faɗa kenan ya kashe wayarshi. "Ke Lolo ki shirya dan ubanki zamu je asibiti daga asibiti kema kinsan sauran zancan. Ke kuma Hauwa ki kaimun ruwan wanka yanzunnan in watsa mitsiyaciya mai neman maganar tsiya yau dai in baki bi Rakiya a sannu ba tana iya dandaƙaki" Ɗakin Rakiya fuu ya shige. Hauwa kuma ta juye mishi ruwan wankan tana ta waƙen baka. "Lolo kije ki shirya kafin ya fito. Ki dena ɗaga ma kanki hankali cikin shege ba kan ki barau ba kuma ba zaki zama ƙarau ba. Wanne irin cikin shege ne ba'ai a gidannan ba?" Cewar Adama. Labbai tace. "Kuma ba'a ɗakko shirin denawa ba. Shima Maigogul faɗan gan_gan kawai yake yi. Kuna zuwa aka bashi kuɗi shikenan fa zancan ya ƙare duk da naki lamarin ya dakeshi ya sha bambam da namu" Ni dai zama nayi a cikin ƴan uwana nayi shiru babu uhm banu uhm_uhm. A wannan ranar Rakiya da Maigogul ba karamin rikici suka yi ba. Tun suna yi a daki har suka fito tsakar gida Rakiya na cukume da wuyan Maigogul. Da dai yaga Rakiya na neman ta kwashe mai ƙafafu ta zuba shi da ƙasa ai sai dambe ya kaure Rakiya na Kururuwa. Abun kunya matan maƙotane da Malam Habu maƙocinmu mutumin Labbai suka raba wannan rikicin. Kuma akaimun terere akan nayi cikin shege ne. Ni kam a lokacin ko a jikina dam bamu san wata kunya ba. Har Maigogul ya fito wanka ya shirya su Labbai nata godona akan in shirya nima naƙi fur. "Taso muje Lolo asibiti a tabbatar mun cikin ne in shine kuma wata nawa" Carab Hauwa tace. "Wannan cikin zai iya kaiwa wata biyar ko huɗu" Buɗar bakin Maigogul yace. "To da shike ke kika yi mata ko? Hauwa ki kiyayi Rakiya a gidannan yau." Rakiya ce ta fito mayafinta a kafaɗa. "O_o batta tayi ai duniya ce. Ƴaƴa gasu nan jibge a ɗakinta. Lolo kuma ita ta siyo mun abinda Hauwa ta samu nasara a kaina. Sana'ar kayi nayi na ta fiye mun wannan kaddararren gida, da ƙaddararren miji, da ƙaddararriyar jar makirar kishiya wallahi dukkanku bakwa gabana" Tana kaiwa nan ta wuce. "Ke Adama tawo muje ki raka mu ayi komai a gabanki." Tasowa Adama tayi muka rankaya asibiti. Muna kan bin layi Cicib ya ƙaraso yana rausaya mu uku muka shiga ɗakin Adama aka barta a waje. "Ku kuje daga waje Baba inna gama dubata zan kiraku" Wannan likita ta faɗa ranta a ɗaure. Haka su Maigogul suka fita. Likita ta gama aune aunenta ta tabbatarma da su Maigogul cikine na wata huɗu babu sati ɗaya a jikina. "Lolo ina fatan kinsan wanda yayi miki cikinnan, sannan kinsan gidanshi ina nufin gidan da matarshi da yaranshi suke ko?" Maigogul ne yayi mun wannan tambayar cikin dakewa da kakkafeni da idanu. Saurayine bashi da aure. E nasan gidan amman".. Dakatar dani yayi da hannunshi. "Wuce ki kaimu gidansu tunda dai kinssn gidan. Saurayine, magidancine, talaka ne, ko mai kuɗi wannan kuma ke ta shafa" "A_a Maigogul me zai hana shi yaron a kirashi tukunna ya sameka in yaso in yayi musu sai a dangana da gidan iyayen nashi. Kaduba abubbuwan da suka faffaru a baya. Sannan Lolo kes ɗinta ya bambamta ita dai babu halin zubar da ciki ya kamata a nemeshi ayi magana ta nutsuwa dashi, in aurenta zaiyi sai ya aureta su rufama juna asiri" Maigogul ya dubi Adama data gama magana ya dubi Cicib dake tsaye yana gyara mayafinshi. Nima ya kalleni tsab. Cicib yace. "Yarinya tazo da hanzari. Yanzu Maigogul abi a hankali din. Ita Lolo ta kirashi ta sanar dashi mu muna nemanshi zuwa da daddare ƙarfe takwas. Barsu su yi tafiyarsu kasan na baro baƙi ." Sai da naga su Maigogul sun ɓace kafin na sauke ajjiyar zuchiya mai ƙarfi. Muna cikin abun hawa Adama taga nayi shiru ina tubkewa ina warwarewa. "Ke Lolo da mun koma gida sai ki kira shi saurayin naki ki sanar mishi halin da ake ciki. Amman ina ganin zaifi kyau ki sanar mishi cewar ana nemanshi a gidanku. Duk da dai nasan babu alƙawarin aure a tsakaninku. To yaya zamu yi a haka muka tsinci rayuwarmu. Maigogul da kanshi yaita ingizamu zuwa shiga duniya sabida kyan da Allah ya huwace mana. Gashi duk kyanmu ya zama kyan ɗan maciji. Ajjiyar zuchiya na sauke duk abinda ta faɗa babu gyara a cikinshi Amman Adama kai tsaye sai inga kamar in nace mishi ana nemanshi ba tare dana sanar dashi dalilin neman ba. Ba lallai bane yazo, amman in yaji akwai ajjiyarshi a jikina zai iya zuwa ko dan tsoron tonuwar asirinshi tunda gidansu gidan malamai ne." "Toh hakane kam kince wani abun kuma. Shikenan ki sanar mishi yayi ƙoƙari yazo in ba haka ba sai yayi dana sanin saninki a rayuwar baki ɗaya dan wallahi Maigogul suka je gidansu za'ayi ɗauki babu daɗine." Haka mukaita tattauna matsalolin kanmu da kanmu har abun hawa ya saukemu a kofar layinmu. Gidan ko da muka shiga Hauwa ce kaɗai a gidan sai ƴar Shuwa dake ta shafa hoda halamun fita zata yi ita mahaifiyarta ta sama mata miji wani ɗan uwanta zata aura harma magana tayi zurfi yazo ya ganta sau biyu kuma ya yaba, itama Ƴar Shuwa tayi na,am dashi. Yanzunma shine yace zai zo daga Maiduguri bai wuci kwalliyar tarbarshi akeyi ba dan a ɗakin Rakiya suke zancan. A tsakar gida Adama tayi zamanta mu biyu ne a ɗakin. "Sabuwa anya kuwa cikin dake jikinki kuwa na Babangida ne? Ni sai nake ganin kamar na wannan Alhajin da yazo Jamus ya haɗaki dashi ne. Ko dai kin mance ne? Gashi shi ba'asan ma a ina yake ba. Ko dai a hakan kike so ki ƙaƙabama Babangida? Kinsan dai mitsiyacine baida wani kuɗi ke rayuwarsu Layuza bata zame miki abun duba ba, yama kika yi sake ciki ya shiga ne? " Ras gabana ya faɗi nama rasa ni kam mai zance dan shab na mance da batun Alhajin da Jamus ya haɗani dashi, kuma cikin yayi daidai da lokacin da muka haɗu. To amman Yaya zanyi? Tunda dai wannan Alhajin ni bansan inda zanma sameshi ba. Shi kanshi Jamus in wuƙa za'a saka mishi baisan inda yake ba kuma baida lambarshi, duk da dai babu tabbacin cikin nashi ne gaskiya. To Ƴar Shuwa yaya zanyi ni dake kaɗai muka san wannan ƙullin inaso mu haɗu mu binneshi a tsakankaninmu. Dole Babangida zan liƙama cikinnan. Tunda bamu da tabbacin ba nashi bane tunda shima ai muna tare dashi a lokacin." Shigowar Adama tare da Rahama da tazo yanzu tana tafe raɓe_raɓe da yara yasa dole muka rufe shafin nan aka buɗe sabon shafi. "Lolo kiyi ƙoƙarin kiran saurayinki tun yanzu ni dai na faɗa miki" Kafinma ta haɗiye yawo kiran Babangida ya shigo wayata. Ɗanewa nayi ƙuryar katifar Rakiya. Allah ya taimaki mai martaba sarki a cikin zuchiyata. Koda yaushe zuchiyata da gangar jikina cike suke da kewarka. Dama ko baka kirani ba daman ni zan kira akwai abinda ya taso ne" "To bari in gama sauraren sarauniyar dake da babbar fada a zuchiyata. Lokacina naki ne ke nake saurare" Kai tsaye nace dashi. Cikine dani, kuma kasan cikinka ne tunda bana kula kowa. Shine Maigogul yace kazo yana so ya ganka zaku yi maga.." Ƙit Babangida ya kashe wayarshi. Da mamaki na zare wayar a kunnena da gaske katsewa yayi? Sake kira nayi sai ga wayarshi a kashe abun almara. A karon farko dana taɓa jin wayar Babangida a kashe kenan. Hmm bariki kenan alalan gero kunun wake, ni Babangida yake so yaima akuyanci? Ashe baisan wacece Sabuwa ba labarin Sabuwa yake ji? Ni da na zauna a kango na kwana na tashi a cikin ruƙaƙƙun shegu. Na taka duk ubanda naso. Naba Babangida kwana biyu matsawar bai neme ni ba kuma bai zo ba zan nuna mishi nawa kalan barikin" Ƴar Shuwa ce ta duro gadon, na kalleta kawai ina harare_harare, gasu Adama sai mayar da zancan cikin suke yi." Labartama yar Shuwa nayi tare sa ɗaurawa da cewa. Wallahi saina kuikuyama Babangida rashin dajarar da sai yayi dana sanin shiga bariki. Waini Lolo yau ni namijin bariki zai nuna ma bariki ni da tsabar yagewan idanuna dayan ya haɗe da ɗayan." Dariya muka saka harda tafiwa. "Tabb ustaz ya taro mach ɗin da bazai iya bugawa ba. Da yasan waye Sabuwa da Maigogul wallahi bazai kashe wayar ba, kuma bazai ƙi amsa wannan gayyatar girman da babuma wanda ya taɓa samu ba." Da daddare sai ƙaryar Babangida yayi tafiya zuwa jibi zai dawo nayi musu. "To naji jibin kaɗai kike dashi wallahi. Ko ya dawo ko kar ya dawo zamu je gidansu dan asan da ajjiyarshi a jikinki tunda haihuwar cikin za'ayo dole ƙanwar naƙi." Da haka muka rabu dasu ina cike ni kuma da mamakin Akuyancin Babangida. Duk sanda zan kira wayarshi a kashe take har Allah ya kawo mu kwana biyun wa'adin sharaɗin da Maigogul ya gindaya. "To Lolo taso muje rana bata ƙarya. Cicib yana waje yana jiranmu" Riga da wandone a jikina a haka na miƙe na warware gyalen dake ɗaure a kaina na yafa, wuƙa na soke a ƙunƙuruna muka fito. Har munzo bakin ƙofar gida Rakiya ta tawo da sauri. "Maigogul wai yanzu in kunje me zaka cema mahaifan yarannan?* Kafaɗa ya ɗaga tare da cewa. "Me kuwa zan faɗa musu daya wuce abinda ya faru. Ke kinga mu sai mun dawo" Haka suka sakani a gaba abun hawanmu har kofar gidansu Babangida. Ai kuwa almajirai cike da makaranta anata karatu. Ga wani farin dattijo mai cike da kamala da haiba. Yanayinshi kaɗai ya tabbatar da yana da managartan halaye Albasa ce kawai batai halin ruwa ba. Wallahi ko ku kuka ga mahaifin Babangida sai kunji inama wani ɗan uwanku ne. Ga gidannan. Inaga wannan shine mahaifin nashi." Na faɗa ina kallon Maigogul. A cikin abun hawan muka fito ga Cicib harda ɗankwali a kanshi duk da ma ba'a rabashi dashi. "Abinda za'ayi Maigogul bari inje in karawoshi gefe muyi abinda ya kawo mu. Ikon Allah ko meye kuma haɗin kifi da gaska? Uhm yau za'a yita ashe da dukkan halamu" Yana rausaya. Ya isa gaban Dattijon yana tsaye babu wargi ko wasa sam a tattare dashi. Bama jin abinda suke faɗi amman dai munga Cicib ya nuno mu Dattijon ya juyo ya kallemu. Yaro ya tayar daga cikin gardawa ya shiga zauren gidan, shi kuma Cicib ya tawo wajenmu da rausaya. "Maigogul muje an mana iso zuwa cikin zaure. Naga tsohon babu wasa daidai da fara'a yaƙi yayi." "Ai sai ki shige muje. Ki rasa wanda zaki bi kema sai talaka duk samarinku masu kuɗi yanzu jibi gidan malumta kika kawo mu, yaushe za'a wanye lafiya ke da gani" Cewar Maigogul. Ni dai bakina shiru inata binsu a baya har muka shiga zauren muka samu Dattijonnan a zaune a tabarma yana tsumayarmu. Ɗagowa yayi ya kalleni tare da saurin sauke kanshi. Zama muka yi dukkanmu muna fuskantarshi. Sai daya sauke gauron numfashi kana yace. "Toh Assalamu alaikum tunda ku bakui sallama ba" Maigogul yace. "Adana sallamarka domin ba ita muka zo ansaba" Murmushi yayi irinna takaici tare da raina wayon Maigogul. "Malam ai wajibine amsa sallama ga duk musulmin da akaima. A ƙa'ida ku da zaku shigo ai ku yafi dacewa da kuyi sallamar. Amman nayi muku ma kun kasa maidomun da'ita? To meke tafe daku haka?" Ya ƙarashe maganar yana nazartarmu. "Kaine mahaifin Babangida kacigari?" Cikin alfahari yayi murmushi yace. "Uban masu gida kenan. Nine mahaifinshi meke tafe daku?" Zama Maigogul ya gyara shima cikin alfaharin yace "Wannan Ƴa tace ta cikina. Wannan kuma amininane wanda baida tamka. Kar in cika ka da surutu a taƙaice Babangida Ɗanka yaima ɗiyata cikin shege. Kaga cikin ai a jikinta harma ya bayyana ko? Wata huɗu ne gashinan. Ga takaddar shaidar tana ɗauke ma da cikin ke lolo buɗe cikin ya gani" Salati Baba Malam ya shiga yi a hankali. Haƙiƙa kaɗuwa da damuwa sosai sun bayyana a fuskarshi ainun. Cike da mamaki yace. "Babangida kace fa? Bana jin ko cikin mafarki Babangida zai iya neman mace da fasiƙanci balle har ace tana ɗauke da cikinshi. Kamar yadda kuka gani nan gidan gidan malamai ne. Shi kanshi Babangidan Malami ne. Sabida haka ba Babangidan wannan gidan kuke magana a kai ba. Nawa Babangidan ya ƙoshi da tarbiyya. Jibi Ƴar da kake ikrarin taka ce, ji da irin shigar data biyo ka ta tsuke jikinta tamkar ba yarinyar musulmai ba. Kai da kake a matsayin mahaifinta baka ji kunyar ɗakko ɗiyarka a tsirara ba, wai ashe har lalacewar al'ummarmu ta kai haka?" Ai kuwa daga haka Maigogul da Cicib suka miƙe nan suka shiga ɗaga murya da zagin Malam akan shine marar tarbiyya dashi da mazinacin ɗanshi. Yana ta basu haƙuri kan in maganar tayi zafine. Hankalinshi ya tashi yadda yaga su Maigogul suna ɗaga murya Cicib sai tattafa hannaye yake yi. Lamarin daya tunzura almajiran Malam suka zo sukayi waje damu. Dan ba ƙaramin ɗaukar zafi su Maigogul suke yi ba. Abunda su Maigogul suke nema kenan suka hau ihu da tafe tafen hannaye jama'a suka taru aka shiga basu haƙuri Maigogul nata ƙoƙarin sai yayi ma mutane bayanin dalilin zuwanmu. Amman dai baici nasaraba sabida yadda suka ƙi saurarenshi suke ta bama Malam haƙuri. Yaran Malam daga cikin makaranta mata_matan duk suka fito. Harma dasu Malama Babba. Malam ko a fuska yayi mamakin abinda su Maigogul suka yi. A tunaninshi duk abinda ya faɗa mana si gaskiya ce sai dai muƙi karɓa. "Kuyi haƙuri ni ban zaci ranku zai ɓaci ba. Amman a inda babu ƙasa anan ake gaddamar kokawa. Kuzo muje zan aika a kirawo Babangida a duk inda yake, kada ku zubar mun da mutunci a unguwa na rokeku ana mugun ganin darajata.." Jin an ambaci Babangida Malama Babba tace. "Wai to su ɗin su waye Malam da zasu zo da irin wannan hayaniyar. Ko da yake ko a shigarsu banga wata kamala ba ballantana tarbiyya ba ina namiji ina kallabi" Ina jin haka nace. A_a fa Dattijuwa ki kiyaye harshanki, dan bazan tsaya ina gani ku dinga aibata mun iyayena ba. Dan haka wallahi ku kiyaye" Nayi maganar ina ciccijewa irinna mata ƴan daba." Sa'a ce ta matso kusa dani ta daki kafaɗata. Nayi mata wani mugun kallo tace. "To in bata kiyaye harshenta ba me zaki yi mata?" Dariya nayi mata tare da ɗaga rigata suka ga Sharɓeɓiyar wuƙa a cikin gidanta a soke a ƙuguna. Baki Malam ya buɗe su Malama Babba duk suka bude baki. Itama maras kunyar babu shiri ta matsa baya. "To duk dai mu jira wanda ya haɗa wannan fitinar. Ku mu koma daga zaure. Ku kuma ku koma makaranta kuci gaba da koyarwarku. Ke Sa'a ki kirawo mun wayar Babangida kice ina nemanshi maza, duk a inda yake yazo. Kome yake yi ya bari yazo zasu tabbatar da ɓatan kai suka yi" Haka muka sake ɗungumowa muka shigo zauren. Tunda aka zauna Maigogul yake ta mita da farfaɗan maganganu. Sama da ƙasa Baba Malam ko ɗago kanshi baiyi ba bare har ya kalli Maigogul. Shigowar Sa'a zauren da sallamane yasa Dattijon ya ɗago kanshi. "Yaya akayi Sa'a ince an sameshi dai?" "A_a Baba Malam wayarshi a kashe take. Mun kira kiran duniya tana rufe" Jim yayi yana nazari, can ya dubu Maigogul yace. "Ko zaku dawo da daddare dan ALLAH sai ayi komai a gaban shi Babangidan. Tunda yanzu baya nan. Shine kaɗai zai tabbatar mun da gaskiyar lamarin?" Maigogul yace. "Zamu tafi mu biyu. Amman ita wannan tazo kenan ba zamu koma da'ita ba ehe wannan furucin cewar babu tarbiyya tattare damu naka ɗan shine mai tarbiyya wallahi zan nuna maka ni bansan ma me ake nufi da tarbiyya ba" Malam Baba ya dubi Sa'a yace. "Kiyi tafiyarki Sa'a. Amman in kin fita ki kirawo mun manga lallai inason ganinshi" Sai da Sa'a ta fita kafin Malam Baba yace. "Bawan Allah ban gane me kake nufi da cewar Ƴarka tazo kenan ba. Ko za kai mun bayani?" Cicib ya karɓe yana tafi yace. "Nufinshi shine Sabuwa zata zauna a wajenku har Allah yasa ta haife abinda ke cikinta. Inta ajjiye muku ɗanku sai ta dawo gida. Ko ba hakan kake nufi ba Maigogul Aminina ?" Gabanane naji ya take ya faɗi a raina na furta. A nan gidan za'a barni har saina haihu fa? Tabɗi jan hakanma ba mai yiwuwa bace nasan sun faɗane dan kawai su tsurar da iyayen Babangida aure ayishi dole. Murmushi Baba Malam yayi tare da girgiza kai. "Toh shikenan zata zauna ɗin har zuwa dare zuwa lokacin Babangida ya dawo, kuma kun dawo in aka ƙarƙare magana sai ku tafi da'ita babu wani dalilin da zaisa ta zauna damu a nan ina mai tabbatar muku wannan yarinyar bata san Ɗana ba. Sannan in zaku dawo shi wannan mai kallabin yayi haƙuri kada yazo dashi" Miƙewa su Maigogul suka yi Cicib yace. "Kar ka shiga inda zaka kasa fita Malam" suka ficewarsu suna sambatu. Baba Malam ya dubeni ya maya idanuna a tsaitsaye a cikin nashi. "A ina kuke haɗuwa da shi Babangida yarinta ki gayan gaskiya?" Cikin halin ko in kula nace. Ranar farko dai a Club muka haɗu dashi. Daga lokacin mukan haɗu a Hotel, ko a shagon abokinshi dai" Idanu Malam Baba ya lumshe yace. "Menene Club ɗin da kuka soma haɗuwa shima Hotel ɗin fa? " Ina taunar cingam nace. Gidan rawar dare wanda ake cakuɗuwa maza da mata ayi rawa ayi shaye_shaye dai haka. Shi kuma hotel zango baƙi" Kai ya girgiza yana jinjina lamarina. Ni kuma a irin rashin tarbiyyar mu bansan cewar yin wannan bayanin kaɗai ba ƙaramar fitsara bane. "Kin tabbatar cikin dake jikinki na Babangida ne?" Ah sosai ma. Ko shima ya sani. Daga ranar dana sanar dashi ina da cikin. Tun lokacin har zuwa yanzu wayarshi ma a kashe take." "Babangidan shima yana shaye_shayenne ko ko dai bayayi?" Yana shan taba. Baya ga wannan baya shan ko wanne nau'in kayan maye ƙarya da ciwo" Kai kawai Malam Baba yaita girgizawa har wani bawan Allah mai kama dashi ya shigo ya gurfana a gabanshi. Rauni linkib ya nuna a idanunshi harda muryarshi, izuwa motsinshi. "Manga yarinyarnan ka tafi da'ita gidanka ta zauna. Zan nemi ka kawo mun ita zuwa bayan isha. Sabuwa ko? Tashi ki bishi. A bata hijabi ta saka in zata dawo" "Amman Yaya meke faruwa ban taɓa ganinka a cikin irin wannan yanayin ba. Meke faruwa dan ALLAH ka barni a duhu. Ita wannan musulunta tazo yi ne?" Hannu Malam Baba ya ɗaga ma Manga cikin dakiya da dauriyar da ya aro ya yafa yace. "Babu wata damuwa Khairan in sha ALLAH. Ku je kawai" Haka Kawu Manga ya tusani a gaba har zuwa gidanshi. Ya danƙani a hannun uwargidanshi a matsayin wacce tazo zata musulunta. Ɗaki ta shigar dani, ta kawo mun ruwa da abinci. "Ga abinci kici baiwar Allah. Allah sarki na taya ki murna sosai gaki kyakkyawar gaske. Allah ya haɗaki da miji na gari wanda zai koyar dake addini da kyau" Uhm bance mata ba. Ina zaune na faɗa zurfin tunani.
Baba Malam:.
Da idanu yabi bayan Sabuwa. Sai da yaga fitarsu ya miƙe tsaye tare da sauke numfashi. Leƙawa yayi wajan almajiran ya yafito babban Almajirinshi wanda almajirai ƴan uwanshi sukai mishi ƙalani da magajin Malam. Da sauri ya iso hannunshi riƙe da bulala. "Magajin Malam ka kula da almajiran ni zan shiga gida akwai abinda zanyi" Cike da girmamawa magajin Malam ya amsa. Baba malam ya shige cikin gida izuwa turakarshi. Zama yayi a bakin gado yayi shiru yana nazarin maganganun su Maigogul. Tare da tunanin irin tarbiyar da ya bama yaranshi da irin gwadaben da ya ɗaurasu a kai. Babangida shine ɗa tilo mafi soyuwa a zuchiyar Baba Malam wanda har ya kasa ɓoye son da yake yi mishi tun yana yaro balle daya girma asalin kamanninsu ta sake bayyana. Ko Magana Babangidan yake yi yana mamakin tsantsar kamannin muryarsu. Haka inya hango Babangida daga nesa yana tawowa kamar harta ɓaci. A ranshi yasan shi ba kuɗi ba, ba ɗan siyasa ba, babu wani dalili da zaisa su Maigogul su zo da nufin sharri. Wani ɓarayi na zuchiyarshi na faɗa mishi kuskure suka yi ba gidan suke nufi ba, ba kuma Babangidan gidan ake nufi ba. Wata zuchiyar tana sanar dashi cewar. Girman lamarin da suka zo dashi yafi ƙarfin ace wai ɓatan kai suka yi. Amman tambayar anan meye haɗin Babangida da wannan ƴar barikin. Meye haɗinshi da Hotel, meye haɗinshi da Club, meye hadinshi da karar sigari? Waɗannan tambayoyin su suka hana wannan Dattijo sukuni. Ya shafe tsawon awannin da suka haura uku yana karanta wasiƙar jaki. Har Malama Babba taima kanta masauki a kusa dashi baida wata masaniya har saida ta ambaci sunanshi kana ya ɗago idanuwanshi da babu wasa cikinsu ya sauke a kanta. "Yaya akayi har makaranta ta tashi kenan?" Ya faɗa cikin magidanciyar kamilalliyar muryarshi mara wasa. "E Malam amman abunda ya bani mamaki shine a karon farko tunda ka kafa wannan tsangayar ban taɓa ganinka a zaune a ɗaki alhalin makaranta nayi ba. In ba'a ganka a makaranta ba to kana wajen karɓan ɗaurin aure, ko raɗin suna, ko jana'iza, ko kuma alƙalanci. Amman yau abun mamaki kaine kayi zaune tunaninka ya tafi wani wajen. Na tabbatar hakan baya rasa nasaba da waɗannan mutane marasa tarbiyyar islama da suka zo wajenka ko?" Murmushi yayi kawai tare da cewa. "Babba kenan. Hakane damuwar dana shiga tana da halaƙa da zuwan nasu. Amman wannan damuwar ba komai bace akan damuwar da zamu shiga dukkanmu in abinda suka zo dashi gaskiya ne" Shiru tayi tana son tambayarshi abinda ke tafe dasu, amman tasan halin mijin nata da ace yaso faɗa mata da kai tsaye zai soma maganar. Tasan bai shirya faɗa mata ba. Kawai dai tunda taji harda Babangida a cikin maganar ta kasa samun nutsuwa. Haka ta tafi ta bama malam Baba waje domin a ƙa'idar gidan da rana haka basa shiga turaka sabida kunya da sakayawa kasancewar almajirai ko da yaushe cikin shige da fice suke a gidan, yaransu ma dake gidajen mazajensu kullum suna gida kasancewar sune malaman makarantar Malam Baba dasu akeyin abincin rana tamkar yadda da gidan yake cike da yara. Da Baba Malam da Malama Babba haka suka wuni a cikin damuwa. Ko da akayi abinci da rana Sa'a ta kai mishi abincin. A tsaye ta sameshi ya kai mari ya kai gwauro "Sa'a ki mayar da abincin. Ko wacce cikinku da kunci abinci ku koma gidajenku. Sannan ki sanar ma iyayenku mata kada wanda aka bari ya shigo ɗakinnan har su kaɗaici kawai nake so. Babangida ne kaɗai in ya shigo za'a yi mun Magana. Ku hanzarta kuci abinci ku tafi" MRS BUKHARI
Tabb wannan lamari da girma yake [8/14, 7:22 AM] +234 802 205 9556: https://chat.whatsapp.com/IUKFTeul76p2VaAvQ5nk0U?mode=ac_t
IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI LITTAFI NA UKU SHAFI NA UKU 3