Idan kaya ya gaji book 3 - Chapter 3
Idan kaya ya gaji book 3 Chapter 3: Idan kaya ya gaji book 3 Chapter 3. Cikin dakewa da rashin wasa yayi maganar. Dama wannan ɗabi'ace ta Malam ba Mutum…
4,186 words
Cikin dakewa da rashin wasa yayi maganar. Dama wannan ɗabi'ace ta Malam ba Mutum bane mai sakewa a cikin gidanshi ba. Hakan yasa ko kara ya gindaya babu Wanda ya isa tsallakewa yaranshi ashirin da uku da Allah ya bashi kowanne cikinsu yana kiyaye ɓacin ran Baba Malam Kuma umarni sau ɗaya rak yake bayarwa babu wanda ya isa tsallake wannan umarnin. Har iyayensu mata babu wanda ya'isa yaji dalili madamar bashi yaso sanar dasu dalilin ba. Da haka Sa'a ta koma a sanyaye ta mayar ma Malama Babba abincin tare da zayyana mata a yadda ta shiga ta sameshi da kuma saƙon daya bata. "Kudidi ni kam tafiya gida zanyi tsoro ya kamani sabida bamu san Abinda zai biyo baya ba. Ko meye haɗin Babangida da waɗannan mutanen sai Allah" Cewar Sa'a data zura dogon hijabinta tana tsaye tana ɗaura niƙabi. Malama Babba tace. "Ni kaina jin sunan Babangida a cikin Maganar yafi komai tayar mun da hankali. Gashi wayarshi sam bata shiga sam ko ina yau ya shige oho. Allah yasa ba wani babban abun bane. To ma me Babangida zai yi?" Sa'a tace. "Ai da ganin yanayin Baba Malam lamarin fa da girma. Ke dai kiyi ta adda'a kawai. Yarinyar da ta zaro wuƙarnan tana gidan Kawu Manga fa Baba Malam yace a ajjiyeta acan har zuwa Babangida ya dawo. Ni dai zan tafi koma menene gobe da safe in nazo naji. Bana so Baba Malam ya fito ya same ni a gidannan." Ai duka suka miƙe ko wacce ta kama gabanta. Bayan Sa'a ta sanar da yaran ɗakinsu Alawiyya, suma wasu abinci ma suke ci, amman duk suka suri hijabansu. Suka bar Malama Babba tana tubka da warwara. Ta jima sosai a zaune har Autanta ya shigo ya zauna bata sani ba. "Malama Babba lafiya kuwa inata magana amman baki ma jini ba?* Ajjiyar zuchiya kawai ta sauke ta fuskanci Autanta. Kafin tace wani abun suka jiyo sallamar Malama ƙarama a kofar ɗakin. Amsawa tayi tare da bata izinin shigowa. Labule ta ɗaga ƙafarta ɗaya a waje ɗaya a ciki. "Babba dama batun girkin dare ne tun ɗazu Sahura tazo harfa ta gama jajjagen kayan miya amman baki fito ba shine nace bari in zo inga ko lafiya?" Tsakankanin Malama Babba da malama karama ana gwabza kishi da gasa sosai fiye da tunanin masu karatu. Sai dai dake ba faɗa suke yi a tsakankaninsu ba yasa Baba Malam ya zuba musu idanu kawai amman yana sane da irin zaman da suke yi. Haka in wani abunne na jaje ya samu ƴan wasu ɗayan ɗakin koƙarin ɓoyema ɗayan ɗakin akeyi. Abun alkhairi ne dai suke shelar sanarwa a tsakar gida. Baba Malam ya haɗe kan yaranshi ne tun suna ƙananu ta hanyar zaunar dasu duk asubar duniya yayi musu nasiha tare da jaddada musu mahimmancin zumunci da haɗin kai. Har yanzu yana irin wannan zaman dasu duk Sallah sakamakon abubbuwa da suka sha kanshi da yawa. Malama Babba ta taɓe bakinta ta miƙe. "Kin ganni yanzu zan fito sai ga Auta ya shigo shine kuma na zauna. Kice mata ganinan" Da "Toh" Malama ƙarama ta amsa tare da sake labulen ta fita. "Auta kaga Babangida yau dinnan?" "E na ganshi ɗazu a can majalisarsu da abokanshi su Mustapha. Amman lokacin ma mota suke shiga naganshi da ƙananun kaya..." Da sauri Malama Babba ta rufe bakin Auta. "Kul naji wannan maganar a bakin kowa Auta duk wanda ma ya tambayeka yayan naka kace baka ganshi ba faƙat" Miƙewa tayi ta fice daga ɗakin zuchiyarta cike da tsoro. A babban kitchen ɗin tsakar gidan ta tadda Sahura. "Sahura ga kabewa can ki fereta baki ɗaya miyar kabewa zamu yi. Akwai tantaƙwashi a rufe a kwano ki zuba a tukunya. Zanyi Sallah yanzu zan dawo mu kwaɓa alkubus" Tana faɗin haka ta fito a kitchen ɗin ta nufi bakin rijiya ta ɗauki buta cike da ruwa tayi Alwala ta koma ɗakinta tayi Sallah tare da roƙon Allah yasa Babangida ya dawo kadayayi dare asirinshi na yawo ya tonu tasan in wannan asirin ya tonu kashinta ya bushe maƙiya zasu yi dariya sosai, za'aga Babangida da Baba Malam a rana. Tana shafawa ta fice suka shiga aikin girki ita da Sahura har zuwa magriba kafin suka kammala yau aikin yayi musu dare kasancewar Malama Babba bata fito da wuri ba. Gidauniyar abincin Baba Malam ta ɗakko ta soma zuba mishi, kafin ta zuba na ƴan ɗakinta, dana ƴan ɗakin Malama ƙarama, sai na Sahura, da almajiran Baba Malam Saida ta kammala wannan rabon ta samu tayo wanka tare da alwala ta shigewarta ɗaki. Tana idar da Sallah ta nutsu taita adda'a a zaune a inda tayi Sallah tasan Baba Malam inya fita tun yamma sai bayan isha yake shigowa. Ita tsoron haɗuwa dashi ma take yi. A sanyaye ta tashi tayo sallar isha ta ɗakko zaninta na super ta saka harda sabon ɗankunnen zinaren data siya ta saka tana shafa turarenta na mai da ƴar baƙar humrarta mai ƙamshin asali ta jiyo sallama a ƙofar ɗakinta. Izinin shigowa ta bayar. Sumayya Ɗalibarta ce ta shigo da goyo a bayanta yarinyar sai kuka take yi. "Ah Malama Babba kinyi kyau sosai" Dariyar dole tayi tace. "Toh mu mata duk tsufanmu sai da gyara musamman in kaine da kwana. Kune yara_ yaran mata baku ɗauki gyaran jikinku a bakin komai ba" Sumayya tayi dariya tare da cewa. "Gaskiya ne Malama Babba. Amman ai ku na musamman ne dama ku kuke koyar damu dabarun da zamu riƙe miji. Littafin ahalari nazo siya dama na bar yara su kaɗai, yanzu sai kiga kafin ka koma sun yi ma ba daidai ba." Littafin ta ɗakko ta miƙa mata, ta bata kuɗin suka fito tare. Ita ta nufi waje, ita kuma ta nufi kitchen ta ɗauki gidauniyar abincin malam Baba ta nufi ɓarayin nashi gabanta na ta faɗuwa. Gashi taga Malama ƙarama ta kafa ta tsare tana son gani da jin gulma. Wannan a faɗar malama Babba ne. Da sallama Malama Babba ta tura ƙofar ta shiga. A hankali Baba Malam ya amsa sallamar yana zaune a bakin gado ya cire hularshi. "Sa'a bata faɗa miki saƙona bane, ko kuwa mantawa kikayi ne?" Ya jefo mata wannan tambayar tare da ƙare mata kallo. Jikinta a sanyaye ta nemi waje ta zauna. "Ta faɗa mun asalima shi yasa ban shigo na gyara maka ɗaki ba. Naga baka ci abincin rana ba, ya kamata kaci abincin dare kaima Allah kayi haƙuri" Hannu ya ɗaga mata halamun tayi mai shiru. Kafin ma yayi Magana suka jiyo sallamar Malama Ƙarama a dokin ƙofar. Malama Babba bata so ya bata uzinin shigowa ba. Amman dake macece mai kissa da son mulki sai tayi sauri ta koma kan gado kusa da Malam. A haka Malama ƙarama ta shigo ta taddasu. Tsugunnawa tayi a gefen ƙafar Malam Baba tare da cewa. "Baƙine da kai amman magajin Malam ya shimfiɗa musu tabarma a zaure na uku kamar yadda yace. Shine nace bari inzo in sanar maka afito lafiya" Tana dasa Aya ta fice abunta. Hular daya cire a kanshi ya saka ya fice yabar Malama Babba a zaune cikin bugun zuchiya. Yana fitowa tsakar gidan yaci karo da Wawo yana gaisawa da Malama ƙarama. "Kai me kake yi a cikin gida? Maza wuce makaranta ka bar ɗalibai na jiranka" Da sauri Wawo ya juyo ya fice harda ɗan haɗawa da gudu. A hankali Baba Malam ya shiga ratsa zaurukan gidan nashi, yana jiyo yanda su Maigogul ke ɗaga muryoyinsu har ya iso cikin zauren da sallama ɗauke a bakinshi. "Sannunku da zuwa. Ina zuwa bari a kawo muku abinci" "A_a ba abinda ya kawo mu kenan ba. Kawai munzo ne muji ba'asin Magana." Cewar Maigogul kenan. Kallonshi Baba Malam yayi yace. "Toh shikenan ina zuwa bari in sa yara su dubo Babangidan" Yana kaiwa nan ya fice ya kirawo magajin Malam. "Ka kirawo mun Babangida yana makaranta. In baya makaranta ka duba shagon kwanansu kace yazo" shi kuma Talle kace mishi nace yaje gidan Manga ya kirawo Manga da baƙuwa haka kawai zaka ce mishi. In kuma ka haɗu dashi Mangan a makaranta sai ka faɗa mishi kuyi maza. Ku same ni a zaure na uku." Umarnin daya bayar kenan ya dawo ya zauna suna jiran ƴan aike."
SABUWA:. Haka na wuni a ɗaki cur ga azabar ciwo na cina, ga baƙin cikin Babangida na cina shima. Azahar nayi wannan matar tazo ta tasheni na ɗan samu bacci kenan "Baiwar Allah muje in koyar dake yadda zaki yi alwala sai ki bini muyi Sallah tare" Ina miƙewa na cabke kuguna na dubeta da kyau. Kin ganni nan? Da musulunci aka haifeni. Ni musulmace gabana da bayana, sabida haka kada ki sake mun kallon arniya" Ina faɗan haka na koma na kwanta. "Ikon Allah. Toh Allah ya kyauta" Iyakar abinda tace kenan ta fice. Bata daɗe ba ta kawo mun abinci. Shinkafa da miya harda kaza da fanta. Zagewa nayi na cinye tas na kakkarya ƙasusuwa yadda ya dace. Sai da akayi sallar la'asar yamma sakaliya na haɗa azahar da la'asar. Tunda dama tazo ta ajjiyemun hijabi a gefena. Inata waye_waye da Ƴar Shuwa ina sanar mata halin da ake ciki" "Wai ko in zo ne ƙawata?" "A_a kiyi zamanki ai ni warki ce daidai ƙugun kowa kema kin sani. Ni da Babangida shege ka fasa" A haka muka gama wayarmu ta karshe. Tafe_tafe nice har wajajen taran dare kafinnan aka aiko wai inzo. Ajjiyar zuchiya na sauke na fito na tadda wannan mutumin daya kawoni a tsaye. "A_a ki koma ki saka hijabi. Ba mutunci bane mace ta dinga tawo tsirara ba" Ai ba da hijabin nazo ba. Babangida kuma ya kamata ku tusa gaba kuna ma wa'azi ba wai ni ba" Ina gama fitsarata na yi waje ai zan iya gane gidan tunda hanyace fetal babu wani kwana. Ina jiyo takunshi a bayana har muka isa zaure na uku a inda su Maigogul suke da zama. Waje na samu na zauna bance komai ba. Wani almajirine ya ƙaraso da sallama. "Malam duk inda ya kamata a samu Babangida ba'a sameshi ba" Kai Baba Malam ya girgiza tare da cewa. "Magajin Malam dama Babangidan yana kaiwa haka a waje ne kaine ɗakinku yake kusa, ka faɗa mun gaskiya" Ƙasa magajin Malam yayi da kanshi halamun babu amsa. A raina nace . Ashe Babangida ƙaramin ɗan balaja'u ne ma a gidama ba'asan waye shi ba. Baki na taɓe. Ana kan mayar da zance sai ga Babangida ya shigo saye da dogayen kayan farar shadda harda zanna bukar a kanshi. Idanu muka haɗa dashi ya kalleni cike da maɗaukakin mamaki, ni ko gajeren tsaki na saki kawai na juya kaina. Baba malam yayi tsam yana kallonmu tare da nazari. Shigowar Mazan gidanne wajen yasa Baba Malam yace. "Kai Babangida nemi waje ka zauna. Wawo kaima haka. Ashiru shiga gida ka kiraqo iyayenka mata su zo su samemu ka biyo su. Ku kuma Ramadan kuna iya shigewa ciki" Duk wannan jawabin da yayi kanshi na ƙasa jikinshi yayi wani irin mugun naushi. Jiki a mace Babangida ya nemi waje ya zauna a ɗarare. Cikin mintunan da basu wuce biyar ba Malama Babba da malama karama da ɗan aike suka dawo. Daga gefe can su Malama suka rakuɓe a tsugunne. "To ga mai gayya mai aikin ya iso. SABUWA zan baki dama ki mana bayanin alaƙarki da Babangida. Ke muke saurare. Ku kuma ku buɗe kunnuwanku ku zama shaidu. Dukkannin abinda Babangida ko Sabuwa zasu faɗe ku yi nazari akai" Cike da rashin sanin girman manya nace. Saurayinane da muka haɗu a gidan rawa dashi. A takaice ina ɗauke da cikinshi na wata kusan huɗu. Na kirashi na sanar dashi yau kwana biyu kenan wayarshi a kashe. Shine Babanmu ya rakoni muzo gidansu domin asan da zaman cikin, wannan shine dalilin eh zuwan namu" Ina magana ina ciccije leɓe ina karkace bakina, irinna yaran da basa ganin uban kowa da gashi " Salati kafatanin ƴan wajen suka saka banda ni da su Maigogul da suke zaune Cicib na yatsina "Sannan yaronnan kwararo_ kwararo babu inda baya ɗaukar ƴata su tafi, hotel _hotel babu wanda baya kaita suje su kwana. Ya ɗirka mata cikin kuma ace kada mu kwato mata ƴancinta. Yaro a gidan malamai amman gashi ƙwallon shege" Cewar Maigogul kenan. Malama Babba dai kuka take yi sautin kukan na fita a hankali. Wawo yace "Amman Baba malam wannan lamarin n" Hannu ya ɗaga mishi dole yayi shiru. Manga ma yaso yin magana amman shima an tsayar dashi. Dubanshi ya mayar wajen Babangida wanda yake ta zare idanu tamkar mazarin tsire. Ya jima yana ƙare mishi kallo kafin ya girgiza kai. "Kai Babangida. Kasan wannan yarinyar? Ka ɗago kai ka kalleta da kyau ka buɗe bakinka kowa na ji" Babangida da ƙyar ya iya ɗagowa ya dubeni. Idanunshi tab da ruwan ƙwalla gabaki ɗaya zufa ta jiƙa mishi fuskarshi. "Ka shaidata?" Baba Malam ya sake jefo mishi tambayar" "E nasanta" Idanu Baba Malam ya runtse tare da jan wawuyar ajjiyar zuchiya ya karanto wasu addu'o'i kafin ya buɗe idanunshi kanshi a ƙasa yace." "Kenan duka abinda tace gaskiya ne ko?" Yayi maganar muryarshi na rawa. Malama Babba tayi carab tace. "Ai wannan ko a mafarki bazai taɓa zama gaskiya ba. Waɗannan mutanen kawai sun zo ne domin su ci mutuncinmu su zubar mana da darajar gidanmu, amman in ba haka ba yaushe Babana zai iya aikata wannan aika....." Idanu Baba Malam ya zuba mata. Kaifin idanunshi da rashin ɗaukan warginshi yasa tayi shiru. A hakanma daurewa tayi furta abinda ƙila zai zama kariya, ko ɗaura ma Babangida magana a bakinshi. "Kar ka bari in sake magana. Kada ka sake kayi mun ƙarya. Duk da mazinaci babu abinda bazai iyayi ba, tunda har baiji nauyin Ubangijinshi ba ni kuma waye" Babangida na share zufa yace. "Ba cikina bane wallahi " Wani kallo Baba Malam yayi mishi" "To cikin waye? Muna jinka bamu labari" Kawu Manga yace. "Yaya duk wannan tashin tashinar yafa kamata ace an barta. Batun tone tone baima taso ba. Babangida dai ya riga da ya jajiɓo mana abun kunyar da zaita yawo kan haula, abin kunyar da har abada bazai taɓa goguwaba, kuma ya rasa yarinyar da zaibi sai ƴar daba tatacciyar maras kunya. Haƙiƙa girma da darajar gidannan ta zube" Kai Baba Malam yaita girgizawa. "Babangida kayi mu'amala da yarinyarnan ko bakai ba?" Da mugun sauri ya ɗago kanshi hannunshi a saman bakinshi. Da halama tambayar ta matuƙar gigitashi kuma ta matuƙar yi mishi girma. Amman gudun kada ya hasala Baba Malam dole haka ya runtse idanunshi muryarshi na rawa yace. "Na na na na yi? Da gudu Malama Babba ta shige gida. "Shikenan tashi kaje. Wawo, Bashiru, Manga duk kuje na sallameku zan gana da iyayen Sabuwa " Ba dan rai yaso ba, sai dan biyayya da rashin yin jajayya da iyaye yasa duk suka bi umarninshi. Bayan sun shige Baba Malam yace. "Maigogul yanzu me kuke so ayi? Sabuwa zata koma gida tare da kune zamu ɗauki nauyin cinta, shanta, suturarta, kulawa da lafiyarta har Allah yasa ta sauka lafiya kafin mu ɗaura dana shayarwa?" "A_a a gabanku Sabuwa zata zauna. Kasan Allah duk barikancin yarana babu wacce ta taɓa haihuwar shege a gabana. Ba kuma za'a soma akan Sabuwa ba. Malam Baba ko? Na fahimci kai babban malamine rufin asirinka dole kake nema. Ni daka ganni taceccen kawaline abun kunya gaba na bashi ba baya ba. Tunda kai kake neman rufin asiri da rashin zubewar daraja babban rufin asirinka shine riƙe Sabuwa a gidanka ka haɗata aure da ɗanka kaga shikenan sai asiri ya rufu. Har abinda za'a haifa shima anyi mishi sutura. Amman fa shawarace kyauta muddin kana son in tafi da'ita to zan tafi da'itamman a cikin ƙwaryar garinnan sai kab sun san waye uban cikinnan. Ai zancan gaskiya ne saina fallasa maka asirinka uban kowa sai yasan ka haifi baragurbi " Baba Malam ya ja numfashi yace. "Shikenan Allah ya rufa mana asiri baki ɗaya. Sabuwa zata zauna kamar yadda aka buƙata. Shikenan ko?" Cicib yace. "Ciki lafiya baka lafiya. Maigogul tashi maza muje kasan su Lantana suna Hotel suna jiranmu zamu kaisu Ges house din Mai nasara. Da gayya yayi wannan maganar domin Baba Malam ya san da gaske su kawalaine." Miƙewa suka yi sukai ficewarsu ni kuma na bisu da idanu sama da ƙasa Allah bai bani ikon nayi musu ko na tanka ba. Nima naji daɗin hakan ta wani ɓangaren ko dan in cunkusama Babangida baƙin cikin da abadan bazai mance dani ba. Ta wani ɓangaren kuma zuchiyata cike take da taraddadin abinda zai je yazo. "Ke tashi muje ciki" Miƙewa nayi ina biye dashi har zuwa cikin gidan. Ganinmu yasa mazan gidan duk suka daddare kowa ya nemi hanyar waje. A ƙofar ɗakin Malama Babba yayi sallama ya shiga nima nabi bayanshi. Babangida yana ɗakin ya riƙe ƙafafuwan mahaifiyarshi yana bata haƙuri ita kuma ta haɗe kanta da guiwarta tana sharɓar kuka. Jin shigowar Baba Malam yasa duk suka juyo a firgice. Ganina yafi furgitasu fiye da ganin shi a toh. "Tashi ka fitar mun a gida yanzunnan, mutumin banza mutumin hofi. Da mugun sauri Babangida ya fice har yana buga kanshi a ƙofar fita. "Ke kuma ki zauna tare da Surukarki. Sannan ki buɗe kunnanki da kyau ki jini. Ba'a yawo a gidana, ba'a saka ƙananun kaya, ba'a shaye_shaye, ba'a harkar dabanci. Wannan wuƙar dake soke a jikinki ki miƙo mun ita yanzunnan" A_a nifa gaskiya ba zaka wani tusani a gaba da irin wannan faɗan ba gaskiya. Dan wallahi ko a gida ba'a haka dani" Wata tsawa naji daga kaina. MRS BUKHARI "
Hmm abun ba'a cewa komai sai dai muce Allah yasa mu dace Ameen [8/14, 7:22 AM] +234 802 205 9556: https://chat.whatsapp.com/IUKFTeul76p2VaAvQ5nk0U?mode=ac_t
IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI LITTAFI NA UKU SHAFI NA HUƊU
INA MIƘA SAƘON GAISUWA A GAREKU MASOYANA NA FAƊIN DUK DUNIYA. HAƘIƘA INA ALFAHARI DAKU SON SO💪🏼
Ina godiya ga Allah daya bani damar rubuta muku wannan littafi mai cike da ɗumbun darasi. Wannan littafin ya haɗani da manyan matan da zatona bai zaci ko kusa dasu zan iya zuwa ba. Amman sai gashi sanadin rubutu Allah ya haɗamu Hajiyoyi son so.
LABBAI TACE TANA GAISHE DA ƳAN ƊAKIN SHARSHI SON SO💪🏼
"Kul kika sake buɗe bakin ki kice zaki yima mahaifinmu rashin kunya. Duk fitsararki ki tabbatar kin ajjiyeta zuwa ranar da Allah zaisa ki bar gidannan. Bar ganin Babangida ya zubar da mutuncinshi a idanunku mu masu mutuncine. Kuma ko banza ya fiki da tarbiyya daga ke har uban naki" Wawo ne yake faɗamun waɗannan maganganun cikin muryar kuka da hargagi. Baba Malam ya dubeshi bai iya cewa uffan ba shi dai. Ni kuwa sai hararar Wawo nake yi ina ƙunƙunni harda murguɗa bakina. "Sabuwa nace ki kawo wuƙar jikinki ki kuma nutsu nan ba gidanku da kika saba rayuwa babu burki bane" Ba wai dan tsoro ba wallahi na dai ga damane na zaro wuƙar na miƙa mishi. "Wawo karɓa ka ajjiyeta a wajenka tukunna" Yana faɗan haka ya saka kai ya fice ba tare da ya kalli kowa ba. Daidai lokacin Malama Babba ta zuba guiwoyinta a ƙasa ta fashe da sabon kukan tashin hankali da baƙin ciki. "Allah ya isa tsakaninmu daku. In sha Allah kamar yadda kuka tona mana asiri sai kunyi wulaƙantaccen ƙarshe mai munin kwatance. Tana kaiwa haka numfashinta ya ɗauke. Wawo dake kaina a tsaye ba shiri ya yarda wuƙar hannunshi. Ya shiga jijjigata yana ambaton sunanta. "Wawo Lafiya meke faruwane?" Malama Ƙarama wacce ta iso a gigice take tambayarshi tun kafin ta iso. Tana shigowa taga irin halin da Malama Babba take ciki. "Ohh wannan lamari ya kwaɓe. Bari in kirawo Ramadan maza a kaita asibiti." Da sauri ta fita. Ni dai ina tsaye ƙerere ina ƙare musu kallo ko a kwalar rigata, haka maza biyu suka shigo suka kinkimeta suka fita da'ita. Na saka hannu na ɗauki wuƙata na mayar da'ita ƙuguna. Sai a lokacin na nemi kujera na zauna shiru. Na waiga ina neman soket ai kuwa na hango shi ta bayan ƙofa harda chaja a jiki na maƙala wayata dan a mace take mus ina son kuma inyi kira.
Malam Baba:. Da ƙyar ya fito daga cikin ɗakin har wani duhu yake gani. Yana zuwa tsakar gida yaga Babangida ya tsugunna a daidai ƙofar ɓarayinshi yana dakon fitowarshi. Malama Ƙarama tana zaune ita da Alawiyya da Ma'u ƴan matan da suka rage a gidan kenan. Turus Baba Malam yayi ya shiga ƙarema Babangida kallo yana haɗiɗiyar zuchiyarshi. Babangida ya rasa da irin gwalagwalan kalmonin da zai soma ba Baba Malam haƙuri dan yasan mutumme shi mai zafi, gashi da kafiya, da mugun riƙo. Ganin tsaiwar tayi yawa yasa Malama ƙarama ta ƙarasa wajen. "Malam lafiya kake tsaye baka shige ba?" Sai lokacin yayi ajjiyar zuchiya. "Kinga Babangida ya fitarmun a cikin gidana ya tarkata duk komatsanshi ya fitarmun a gidana. Wannan gidan ya zama shi da shi sai hange, na cireshi daga yarana na barranta kaina dashi babu ni babu shi har gaba da abada" Kafin Malama Ƙarama tace wani abunne ta jiyo Wawo na ambaton sunan Malama Babba a gigice shine taje taga halin da take ciki. Babangida na riƙe gam da ƙafafuwan Baba Malam har aka fito tiri_tiri da Malama Babba. Da idanu Babangida da Baba Malam suka bisu ko wanne da abinda ke zuchiyarshi. Malama ƙarama ta sake dawowa da sauri wajen hannunta riƙe da hijabi. "Malam ya kamata in bisu ina neman izinin ka" "Babu inda zaki je yaranta zasu kula da'ita. Ki aiki Alawiyya ta kirawo mun magajin malam da Jamilu, da ja'afaru suzo yanzu " A sanyaye ta bar wajen ta aiki Alawiyya kiransu magajin malam bisa umarnin da aka bata. Har suka zo Babangida na riƙe da ƙafar Baba malam sai kuka kawai yake yi amman ya kasa furta kalma. "Magajin malam ku kinkimi Babangida ku jefar dashi a waje. Ka haɗa mishi kayanshi ka jefar mishi" Baba malam ya faɗa a raunace tamkar baya son abinda yace a aikatan. Malama ƙarama tana gani tana ji bata da ikon cewa uffan. Sai korar su Alawiyya ciki tayi kawai. Haka gardawannan suka ɓamɓare Babangida a ƙafar Baba malam da ƙyar suka fice dashi. Baba malam har da zai shiga ciki sai yayi waje shima. To kunsan gardawa babu wanda ya fisu shaƙiyanci da ƙeta, suna fitowa suka cillar da Babangida kamar Yadda Baba malam ya umarcesu. Malam Baba da kanshi ya shiga shagon kwanan su Babangida su Ashiru da su Abubakar suna kwance Baba malam ya shigo ya ce. "Waccece jakar Babangida Habu?" Jikin Habu na rawa ya nuna mishi jakar tashi a gefen katifarshi. Baba malam ya kinkima ya fice da'ita ya cillama Babangida dake wajen da aka jefar dashi Kawu Manga yana roƙonshi akan ya tashi. Jakar ta sauka a kusa da ƙafafuwanshi yana ƙoƙarin juyawa ya shiga gida kawu Manga ya tareahi. "Yaya wannan tonan sililin kuma da kanka zaka yi. Yanzu daka koreshi ina kake son yaje. Hannunka baya ruɓewa ka yanke ka yar, duk lalacewar Babangida naka ne dole sunanka na maƙale a sunanshi." Kallonshi Baba malam yayi tare da dafa kafaɗarshi. "Manga kenan. Har tsohon ɗan bariki mai shan sigari da zuwa gidan rawa, da zango baƙi a ce in an koreshi ina zashi? Ga ƴan mata nan birjik a bariki irinsu Babangida suke nema. Tonan silili kuma da kake faɗe har ya wuce wanda iyayen yarinyar da yaima ciki sukai mana ɗazu? Yarinyar fa tana cikin gidana damu da ita mun haɗu har abada ko munƙi ko munso tarihi bai isa ya goge wannan lamarin ba" Hawayene suka zubo a guraben idanun Baba malam lamarin daya gigita ƙanin nashi kenan. Sai rirriƙeshi yayi ya shiga dashi ciki. Duk da yana ta cewa. "Manga zan iya ka rabu dani tuni na amshi ƙaddarar ai tunda har yarinyar na amsheta zata zauna damu." "A_a Yaya muje dai in kai ka" Sai da ya ajjiyeshi a bakin gadonshi kana yace. "Zan riƙe Babangida ya dawo hannuna ya zauna da su Ƙasimu." Malam bai ko kulashi ba, dole ya fice. A cikin wannan daren a cikin gidansu Babangida babu wanda ya runtsa tun daga kan yaran dake gidan, almajiran malam da akayi komai a gabansu, har zuwa waɗanda suke da aure ko wanne yana kwance a gado yana tubkewa da warwarewa. Malama Babba kuma tana gadon asibiti ana mata ƙarin ruwa, kukan da take ta faman yi ne yasa akai mata allurar bacci dan ta samu nutsuwa. Sa'a da Wawo, da Ramadan ne a wajenta Sai faman waye_waye suke yi a tsakankanin junansu. Hatta jefo Babangida da Malam Baba yasa akayi tuni labarin ya isarma dasu Sa'a. Baba malam kuwa da ƙyar malama Ƙarama ta dinga rarrashinshi da bashi kalma da tunasar dashi haƙuri da rungumar ƙaddara duk muninta kana ya sauke nannauyan ajjiyar zuchiya ya amshi abincin yacinye kamar yadda dai ta buƙata. Amman dai maganar bacci babu a sallayarshi ya kusan kwana ga zazzaɓi mai ɗan karen zafi a jikinshi da ƙyar yake janyo numfashi daga huhunshi, kanshi ya ɗauke akwai tulin tambayoyi daya adanasu yana jiran Babba ta bashi amsarsu.