Kenza eBookz

Idan kaya ya gaji book 3 - Chapter 4

Idan kaya ya gaji book 3 - Chapter 4

Idan kaya ya gaji book 3 Chapter 4: Idan kaya ya gaji book 3 Chapter 4. Babangida:. Tunda ya shiga ɗakin kwanan su Ƙasimu yaron Kawu Manga yayi shiru akan…

4,473 words

Babangida:. Tunda ya shiga ɗakin kwanan su Ƙasimu yaron Kawu Manga yayi shiru akan katifa yana tunanin yadda yayi alalan gero ya kwaɓe mishi a bariki. Wai yau duk mutuncin gidansu da kamalar da yake arowa ya yafa amman shine yaima wata macen ciki har asirinshi ya tonu bama a idanun iyayenshi da ƴan uwanshi zallah ba. Harda almajiran Malam Baba da ɗaiɗaikun jama'ar unguwa ƙila sun san abinda yake faruwa. Gashi sanadiyyar wannan lamarin ga Malama Babba can a kwance a gadon asibiti, shi kuma an koreshi a gidansu. A tunanunshi irin ƙololuwar son da Baba malam yake yi mishi bazai taɓa iya tunanin korarshi ba, duk da shi kanshi yana jin girman abinda ya aikata ya wuce misalin kwatance. "Hmmm Sabuwa kin taɓo tsuliyar dodo. Kin taɓo gidan rina zan nuna miki ke ba bariki kike yi ba daga ke har iyayenku. Saina kuikuya miki akuyancin da baki taba cin karo dashi a bariki ba. Yadda kika cire ma iyayena yarda dani suke mun kallon mazinaci. Ni rayuwarki zan tarwatsa wallahi" Duka waɗannan sambatun cikin zuchiyarshi yake yi. A fili dai ajjiyar zuchiya kaɗai yake saukewa. Kawu Manga ne ya buɗe ƙofar ɗakin ya shigo. Babangida yana daga kwance kawai baƙin ciki da guguwar ɗaukar fansa na cin ƙasan zuchiyarshi. Zama yayi a bakin katifar, ya dubi Ƙasimu yace. "Ƙasimu fita waje ka bamu waje" Cike da ladabi Ya fita. Kawu Manga yafi minti arba'in yana zazzagowama Babangida nasihu da tunatarwa ya ɗaura da cewa. "Zuwa nan da ƙura ta lafa zaka ci gaba da zamanka anan. Babban abinda nake so dakai shine kaji tsoron Allah kada ka sake aikata kuskuren daka aikata. Na tabbatar shaiɗanne yayi wasa da imaninka. Kaita istigifari Allah zai yafe maka. Gobe da safe kaje ka duba mahaifiyarka. Wannan sirrin zamu yi iyakar bakin iyawarmu wajen ganin mun birneshi bai tashi ba. Kaima saika riƙe bakinka kuma kaci gaba da walwalarka sabida kada mutane su fahimci wani abun" Haka dai yai tayi mishi nasiha daga ƙarshe Babangida yayi godiya tare da sake jaddada cewar sharrin shaiɗanne kuma in sha ALLAH haka bazai sake faruwa ba"

SABUWA:. Bayan wayata ta ƙoshi da caji saina kunna ina kwance a doguwar kujera na kira Ƴar Shuwa a waya bata ɗauka ba. Sai zuwa can sai ga kiranta ya shigo. "Ƙawata sai kuma muka ji kina gidansu Babangida acan zaki zauna ki haihu. Nayi ta kiran wayarki ma a kashe. Wai ke kinga irin rikici da tashin hankalin da Rakiya da Maigogul suka yi yau a gidannan duk akan barinki da akayi acan? Wallahi ƙawata kab unguwarmu babu wanda baisan abinda yake faruwa ba. Rakiya taso ma tazo ta dubaki to wayarki a kashe mu kuma bamu da adireshin gidan. Yau Rakiya saida ta yar da Maigogul har ƙasa Uzairu zuchiyata ne ya rungumeshi suka faɗi tare duk suka kukkuje" Ajjiyar zuchiya kawai na sauke. Ke dai bari nima na yarda na zauna ne saboda Babangida. Sannan iyayenshi basu da kirki kinji yadda suke aibatamu yadda kika san su tun a duniya aka basu tikitin shiga aljanna. Alhalin gasu da ƙaton rikakken ɗan iska sun haifa a gida. Inanan kane kane a ɗakin uwarsa, ita kuma ranga_ranga aka wuce da'ita asibiti." Dariya muka saka dukkanmu, mun jima muna hira sai daga ƙarshene na bata adireshin gidan dan tace gobe zata zo da yamma zamu fita. Ina ajjiye wayar Alawiyya ta shigo da sallamarta. "Dama Malama ce tace inzo in kai ki ɗakinmu ki kwana acan" Wani kallo na watsa mata tare da cewa hmm kafin nace. Ke kuma daga ina? Ai naga Babanku ne ya kawo ni, in dai so ake in koma wani ɗakin sai dai yazo ya faɗa mun" "Ke ki kama kanki wallahi. Baba malam ne zai taso da kanshi yazo inda kike? Ke in ma banda ƙaddara yaushe zaki shigo ko zauren gidanmu balle har ki yi kane_kane a cikin ɗakin Sunnah " Dariyar manna hauka kawai nayi mata. Dole data gaji da tsayuwarta ta fice fuu nabi banza da harara. Inata kwance ni ba bacci ba, ni ba abokin hira ba. Sai naji ina kewar gidanmu. Da ina gida da ana can ana zuba cabta. Ko kuma muna Club muna jijjigewa, ko kuma muna kwance dai. Murmushi nayi tare da shafa cikina Da tunane tunane bacci yayi awon gaba dani Asubar fari ko kiran sallah ba'aiba naji ana tashina har ana dukan kafaɗata. Ina buɗe idanu naga mata a kaina. "Wai dana turo Alawiyya cewar ki bita kuje ɗakinsu ashe baki je ba anan kika kwanta?" Banza nayi da'ita. Inaji ta kwaɗa kiran Alawiyya tazo da sauri ta shiga tuhumarta. Ita kuma ta mayar mata da yadda nace. "Uhm Lallai Babangida ya ɗebo mana abinda yafi ƙarfinmu. Ke yarinya kibi duniya a hankali. Ke abinda ke cikinki ma kaɗai bai isheki yasa kin rusuna ba? Taso to muje ki bita kiyi alwala kiyi Sallah a ɗakinsu acan zaki ci gaba da zama" Har zanyi raddi sai kawai na fasa. Nabi Alawiyya ta nuna mun banɗaki dai. Nayi duk abinda zanyi na shiga ɗakin duk su biyun Sallah suke yi. Bakin karifarsu na hau na zauna ina ƙarema ɗakin kallo. Harda sib suke da'ita. Mu kam ina iyayenmu ma suka samu kamar haka balle kuma mu. Ji waje ko ina tas. "Ga hijabi da goduwar riga kiyi Sallah" Na jiyo muryar Alawiyya a kaina. Ta idar har ta tashi ta bani waje. Hijabin dai na saka banko kalli doguwar rigar ba na tayar da Sallah. Kafin in idar har sun kwashi littattafai sun fice. Niko ina idarwa na haye katifa na baje harda ɗora kai a filo gida babu. Bani na tashi ba sai tara da rabi na safe. Wayata na jawo naga na rasa kira kusan sau ashirin ( missed calls) Kafinma in kai ga dubawa wayar ta sake ruri, sai dai kafin in ɗauka aka buɗe labulen ɗakin Sa'a ce tana tsaye tana ƙare mun kallo. "Allah wadaran wannan abun kunyar. Sai kace wasu tubabbu ace budurwa ta dawo gidan saurayinta da zama da cikin shege a jikinta. Tur da wannan tarihi da kuka ajjiye mana mummuna." Kallonta kawai nayi tana cikin niƙab idandunanta kaɗai nake kalla. "Ke Sa'a kul kika kuma zuwa kusa ma da ɗakinnan doka ce Babanku ya saka. Kuma ya haneku da faɗan maganganu marasa kyau akan wannan lamarin. Wuce ki bar nan" Dole ta wuce. Ita kuma ta shigo ta kawo mun abinci na. Amman jaraba na cina sai zage_zage nake yi ni kaɗai akan maganganun da Sa'a ta yaɓa mun ban samu damar ramawa ba." Wajajen sha biyu na jiyo kamar muryoyinsu Rakiya a tsakar gida kuma da halama hayaniya akeyi. Zuruf na fice ai kuwa ilai rigimarce akan danme Uzairu zuchiyata zai shigo gidan matan aure. Rakiya kuma tayi ram dashi a hannunta tana rantsuwar dole sai ya shiga tunda nice a cikin gidan. Akan wannan aketa jayayya. "Kunga malamai wannan yaron dai wallahi saiya shiga gidannan. Ai dalili kesa a zagi malami kuma naji kina wani maganar rashin tarbiyya. Ai rashin tarbiyyar ɗanku shine babban maras tarbiyya daya iya yima yarinya ciki sabida ƙin gaskiya da ƙin ALLAH kuke iya buɗe baki kuna cewa wasu basu da tarbiyya Sa'a kuka ci akan Uzairu zuchiyata kuke wannan maganar da Gaza ne ko Magazin ba kwa soma ba." Sa'a na shirin mayar da martani, ni kuma ina shirin zaro wuƙar ƙuguna muka jiyo fitowar Baba malam wanda hayaniyar data fito dashi daga ɗakinshi kenan. Babu shiri Sa'a ta wuce sum_sum kai a ƙasa. Malama ƙarama ma wucewa tayi tana yi mishi sannu da fitowa. Bai kulata ba hankalinshi na kaina. "Lafiya meke faruwa anan. Bawan Allah daga ina zaka shigo har tsakar gidana ka tsaya. Ke Sabuwa maza wuce ki sake kayan jikinki kada ki sake fito mun tsakar gida da ƙananun kaya ko babu ɗankwali" A mugun tsawace yayi maganar. Juyawa nayi Rakiya tayi carab ta riƙoni. "Zo amshi kayan naki." Amsar kayan nayi a karamar jakata nayi komawata ciki. "Malam nice mahaifiyar Sabuwa. Wannan wanta ne laifine dan munzo ganin ƴarmu? Naga sai wani jijji da kai kuke yi kuna faɗa. Wannan al'amarin daya faru daga mu har ku babu wanda zaice abune mai daɗi. Uzairu zuchiyata wuce mu shiga" Rakiya ta riƙo hannun Uzairu zuchiyata zasu wuce Baba Malam ya riƙe hannunshi carab. Idan ranshi yayi dubu ya ɓaci musamman dake bai saba Magana ya maimaita ba. "Hajiya wannan yaron bazai shigar mun gida ba. Kema dan mahaifiyarta ce amman bazan laminci aita kawo mata ziyara ba bazai yiwu ba in dai ba tozartamu kuke son yi ba." Ni dai ina daga ɗaki ina sake kaya nake jiyo su Rikici ya kai har Baba malam yasa anyi mishi kiran samarin gidan daga waje suka shigo. Nan suka kori Uzairu zuchiyata shi kuma ya fita yanata zage_zage. Rakiya kuma aka barta ta shigo inda nake. "Lolo wannan uban miji naki haka yake maras mutunci? Dama Maigogul ya sanar dani yadda suka kwashe. Amman ke kinji kin gani zaki iya zama a cikin wannan gidan, bakya gudun faruwar wani abun?" Ina girgiza kai nace. Bana jin taoron uban kowa. Babu fa abinda zai faru. Ni kam nazo kenan Rakiya kinsan Allah daga nan sai gidan Babangida. Ke kina ganin in ba hakan muka yi ba yaushe iyayenshi zasu yadda ya aure ni. Shikenan fa in bai aureni ba an cuceni an barnu da ɗan shege" Rakiya ta jinjina kanta bata dai ce komai ba mu kai shiru na wani lokacin. "Nan ɗakin na yaran gidanne?" E nasu ne ji ɗaki mai kyau ba irin na gidanmu ba." "Hmm ita wannan duma dumar itace uwar Babangidan kinga yadda tayo kaina kamar zata dakeni. Harfa cewa take yi wai bata taɓa ganin marasa tarbiyya kamar mu ba. Ke ki ji mun mata da ɗiban albarka. Ai kuwa Lolo ko mutuwa zasu yi sai kin zama surukar wannan babban gidan. Kinga bari in tashi in tafi Su Adama da tare zamu zo dasu, sai nace su dai bari mu soma zuwa muga kamun ludayin abun. Ke kina ganin da mun tawo duka ai da anyi ɓatacciya" Har ƙofar gida na rakata. Naso in fito amman gardawan Baba malam suka tare hanya bisa umarnin Baba malam akan kada su sake ko leƙe in yo. Dariya kawai nayi na koma ciki. A zaure na huɗu muka ci karo da shi zai fita ko kallo bai isheni ba na ɗage kaina sama. A haka dai na kwana biyu a gidan nan yaran gidan sai zurubtun zuwa suke yi A kwana na huɗu ne aka sallamo Malama Babba daga asibiti.

Babangida:. Washe garin ranar da Sabuwa ta kwana a gidansu da safe dai asibiti yaje ya duba jikin Malama Babba yai ta bata haƙuri shine harda kuka akan sharrin shaiɗanne kuma shi wallahi ba cikin shi bane. Take Malama Babba da jin haka ta sauke ajjiyar zuchiya taji har ƙasan ranta ta gamsu da abinda yace. "Na yarda da kai Babangida. Amman ta yaya zanyi ma Malam magana ya yarda da kai? Kasan Malam yadda ɗaya ce a wajenshi. Amman zan yi iyakar yina dan ganin na wanke ka. Ita kuma baƙar dagar yaya za'ayi ta bar gidannan? Bazan iya zama a gidannan muddin tana ciki ba" Sa'a tace. "Babu fa yadda muka iya amman zama dole kinsan tunda Baba malam yace ta zauna Magana ta ƙare. Tananan tana zuba rashin kunya, ƴan uwanta ma marasa mutunci suna nasu. Wawo dake tsaye duk yana saurarensu yace. "Malama Babba baifa kamata kima yarda da Babangida ba. Ai ya amsa cewar yayi mu"amala da'ita a gaban Baba malam." Malama Babba dake fama da jikinta tace. "Amman kasan yaso yayi Magana bayan ya amsa hakan malam ya ƙi bashi dama. Wawo ɗana bafa zai aikata irin wannan ɓarnar ba" Murmushi kawai yayi shi yasan dama Babangida bazai taɓa zama mai laifi a wajenta ba. Asalima son da take nuna mishi da yawa ƙila shi yasa ya jawo musu wannan abun kunyar da za'aita zancan har abada. Daga asibiti Babangida majalisar abokanshi ya wuce ya nemi waje ya zauna shiru anata hirar mata Babangida dai sai dai in wannan yayi magana ya kalleshi har dai Mustapha ya ankara Babangida baya magana ga majalisa ta hautsine da musun wasu mata biyu kan waccece tafi kyau kowa na tofa albarkacin bakinshi. "Babangida kacigari tunda ka shigo majalisarnan baka ce ci kanku ba. Meke faruwa ne. Ko sabida rashin lafiyar Malama Babba ne?" "Uhmm ku dai ku bari Wai kunsan Sabuwa a cikin gidanmu ɗakin mahaifiyata ta kwana dan bura'ubanci?" Zare idanu dukkansu suka yi, ai sai kallo ya koma sama. "Kamar ya a gidanku ta kwana. Kaddai akan cikin da tace tana dashine?" Nan Babangida ya kwashe labari yake ta basu. Yasan akwai yadda mai ƙarfi a tsakankaninsu. Cikinsu babu wanda baima mace ciki an zubar ba abokaine su irin na cin mushennan. Tuni Malam Baba ya daɗe da rabashi dasu. Amman halin ɗan yau yasa Babangida yayi biris da gargaɗin Baba malam malama Babba kuma ta goyi bayanshi. "Tabb amman Sabuwa ta kuikuya maka akuyanci. Amman zata ga bunsuranci. Kai wanne mataki kake ganin yafi dacewa ma da'ita ne?" Cewar Mustapha dake tsaye yana ta hargagi da zage_zage" "Wallahi ban sani ba. Tun jiya nake tubka da warwarar hukuncin da zan yi mata amman ban tuno ba. Mustapha wallahi saina koya ma Sabuwa hankali. Sai taji a cikin ranta ta tsaneni ta kuma tsani bariki. Cikin da take takama dashi saina zubar dashi dan ubanta ko zan mutu ba zata haihu ba." Haka dai sukaita tattaunawa tare da jinjina girman matsalar da Sabuwa ta saka abokinsu a ciki. Babangida ya buɗe fitar dare da neman mata a cikin kwana biyunnan sosai. A tunaninshi hakanne kaɗai zai wanke mishi damuwar da yake ciki. Dan ba ƙaramin matsala yake ciki ba.

Baba malam:. Dama jira yake yi a sallamo Malama Babba daga asibiti ya tara zama yayi musu aman abubbuwan da suke cin ranshi da irin binciken da ya saka akayi mishi akan Babangida da ita kanta malama Babban lokaci kawai yake jira yasa a zauna yayi musu amai. Bincikenne bai kammala damuwa kuwa sai cin ranshi take yi a kwana bakwai da zuwan Sabuwa Dattijon saida yayi rama. Kallo ɗaya zaka mishi ka gane baya cikin nutsuwarshi

Sabuwa A kwana bakwai da nayi a gidan anyi rikice_rikice masu yawa. Dan duk waɗanda suka zo ganina ba'a barinsu ma su shigo tun daga waje ake taresu a hanasu. Daga haka sai rikici ya tashi. Nima nayi yinƙurin fita kusan sau uku abun yaci tura, a yinƙuri na huɗunne na samu nasarar ficewa da misalin ƙarfe ɗayan dare motar su Yar Shuwa na bayan layin suna jirana. A guje na ja motar muka wuce fuu sai Club. Ina bayan mota sai sigari nake sha ina jina fayau dani tsabar jin daɗi Kwanana bakwai cib babu sigari babu yawo ƙafafuna sun gaji har ƙaiƙayi suke yi mun. Ai kuwa muna shiga club na faɗa filin rawa na shiga tiƙar rawa ina aikin shan sigari. Ban jima da shiga Club ɗin ba Babangida ya shigo carab idanuna suka sarƙe a cikin nashi duk da wuta mai kalar dake kunnuwa ta ɗauke kanta bamu kasa gane juna ba. Kamar mahaukacin zaki haka yayo kaina a lokacin wani namiji na shafa jikina. Fisgata yayi zuwa waje ina turjewa yana jana cike da mugunta. Bayan motarsu ya buɗe ya jefa ni ya rufe. Ina hangoshi ta taga dafe da kanshi yayi shiru Nasan Babangida mutum ne mai mugun kishi akan abinda yake so Nayi mamaki daya nuna kishinshi a kaina a tunanina ai ya tsananeni shi da na farkema laya.. Ƴar Shuwa da saurayinta ne suka ƙaraso wajen motar. "Lafiya zaka jawo yarinya ka turata a mota. Tare nake dasu fa" Cewar saurayin Ƴar Shuwa. "Dan abu ta kazanka zaka san tare kake dasu. Ba ni kake cema tare kake dasu ba? Ina zuwa. Nan Babangida ya soma nannaɗe hannun rigarshi Ai kuwa ya ɗane wuyan saurayin Ƴar Shuwa faɗa harda fasa kwalba da yankan juna. Ni dai ina mota inata aikin bubbuga murfin motar ga zafi kamar zai kasheni. Da ƙyar abokan Babangida suka jayeshi suka turashi a mota. Mai motar ne ya cilla mishi keyn mota a cinyarshi. "Kuje ka mayar da'ita gida ka dawo ka same mu." MRS BUKHARI

Sai mun haɗi ranar litinin in sha Allah [8/14, 7:22 AM] +234 802 205 9556: https://chat.whatsapp.com/JmCasXpUuuT0J6dfLTWFNk?mode=ac_t . 18066696785. Hussaina Bello

HAJIYA KAYAN KITCHEN KIKE SO MASU SAUƘI DA KYAU. KO KUMA SARIN KAYAN KITCHEN KIKE SO KI SOMA KIN RASA INA ZAKI SAMU AKAN FARASHIN DA KEMA ZAKI SAMU ALKHAIRI? H@H AVAILABLE WHOLESALE AND RETAIL DUNIYA NE MAZA TUNTUƁE HUSSSAINA BELLO KAI TSAYE A LAMBAR WAYARTA. KO KUMA SHIGA CIKIN ZAURENTA DOMIN KASHE ƘWARƘWATAR IDANU

IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI

LITTAFI NA UKU SHAFI NA BIYAR 5

*SON SO MASOYAN ALƘALAMINA* *WANNAN SHAFIN DOMIN SOYAYYARKU NE MASOYAN ASALI INA JIN DAƊIN YADDA KUKE NUNA ƘAUNA GA ALƘALAMINA. YA ZAME MUN DOLE IN FARANTA MUKU KAMAR YADDA KUKE FARANTA NAWA RAN SON SO💪🏼*

Ai kuwa da mugun gudu ya figi motar saida kaina ya gwaru. Haka yaita watangaririya da rayuwarmu a titi. Yana yi yana kutuntumo manya zaguna yana ɗumamun. Nima bakina kunsan bazai taɓa yin shiru ba yana zagina ina ramawa. Wallahi sai kawai ya faka a gefen wata unguwa ya fito ya dawo gidan bayaa ya kama wuyana ya shaƙeni sosai. Taimakona ɗaya akwai wuƙa a jikina jin ina kiciniyar zareta a gidanta yasa ya saki wuyana. Na shiga sauke numfashi. Gashi ya haye kaina yayi kane_ kane. A cikin motar ya tumurmusheni tas har saida ya samu biyan buƙatarshi. Yana haki yace. "Wallahi saina sa da kanki kinyi nadamar zuwanki gidanmu Kin ga wannan tsinannen cikin da bama nawa bane kika liƙa mun? In sha ALLAH shine ajalinki tare zaku mutu dake da tsinannen ɗan dake ciki saina zubar da cikinnan wallahi. Sabida ke tacacciyar Ƴar balaja'u ce shine har zaki fito kuzo Club wani ɗan iska na shafa ki. Kuma kike tunanin ni Babangida zan yarda cikin jikinki wai nawa ne?" Sauka yayi a kaina ya dawo gidan gaba yana gyara zaman wandonshi. Duk da jikina yayi laushi marata har wani zargewa take yi sabida ba ƙaramar mugunta Babangida yayi mun ba. Amman baisa na ragama Babangida ba. Ai kuwa sai di mu mutu mu uku dani da cikin da kai ribar ƙafa ƙila harda mahaifinka Wallahi na tsanake bana ƙaunar in buɗe idanu in ganka a duniya . Sabida kana ganin kai ɗan iska ne. Ni zakaima ciki kayi tunanin kaci biredi ka yaga leda kuma Maigogul ya barka? Kayi kuskure ƙaramin ɗan iskan dake ɓoye shi ɗan iskane a gidansu. Ciki saina haifeshi kuma a cikin gidan da aka haifi ubanshi. Shima shegen sai ya taka doron ƙasa yayi adawa da ubanshi. Wallahi in bakai wasa ba wannan shegen sai ta zama ajalinka" Haka yaja motar har muka iso bayan layinsu muna farfaɗama juna maganganu. Inya faɗi goma zan faɗi ashirin dan bana tsoronshi sam. "Fitarmun daga mota Ƴar balaja'u kawai ke da Club har abada duk inda kika je zan kamaki dan dole zan ganki."

Baba Malam:. Yana zaune akan sallayarshi yayi raka'a biyu a sallar data zame mishi jiki. Ya jiyo sallamar Malama ƙarama a hankali tare da ɗan doka ƙofar shima a hankali. Miƙewa Baba malam yayi tare da sake duba agogo. A hankali ya iso bakin ƙofar "Ƙarama lafiya a cikin darennan zaki tawo?" Kafin ta bashi amsa Malama Babba ta ƙaraso wajen. "Me zan gani ni da kwanana Karama na son ƙwace mun miji?" Ta faɗa ba'a faɗa ba, ba da wasa ba amman. Dan tasan halin mijinsu sarai. Kuma tasan a cikin halin da Babangida ya saka gidan. Kallonta kawai yayi ba tare da yace mata uffan ba. "Ina jinki ƙarama menene?" "Uhm dama Alawiyya ce tace mun wannan yarinyar da take zaman Babangida bata nan ta gudu. Na dudduba cikin gidannan kab har banɗaki amman malam bata nan" Kai Baba malam ya shiga jijjigawa yatsanshi ɗaya saye akan leɓenshi ya ɗan ciza. Malama Babba babu shiri tayi ƙasa da kanta tana jinjina girman munafurcin Ƙarama. Da kuma kalar rashin tarbiyyar Sabuwa. "Ya zame mun dole in san menene mafita. Duk da Yaya Hanne tace in bar komai har zuwa gobe ta iso" Malama Babba a zuchiyarta take maganar. Wucewar Baba malam ne ya dawo da'ita hayyacinta. Taji dai sun yi magana amman Allah cikin ikonshi bata ji me yace ba. A tsaye a wajen ya barsu. Yana ƙulewa Malama Babba ta sha gaban Ƙarama dake ƙoƙarin barin wajen. "Wato sabida dama kina hassada da irin son da Malam yake yima Babangida shine kika tawo sanar dashi halin da ake ciki sabida ya sake tunzura ki kara mishi wutar tsanar Babangida ko?" Murmushi Malama ƙarama tayi tace. "Wallahi ko ɗaya a tunanina dukka kuna nan tare tunda nasan kece da miji. Kuma a gabana kika zo kika wuce zuwa turaka. Babba babu dalilin da zaisa in yi hassada da soyayyar da Malam yake ma Babangida. Babangida ɗanane, kuma son da Malam yake yi mishi ai baya nufin su ragowar yaran baya sonsu. Sannan hatta ni dake ko wacce tana da ɗa mafi soyuwa a gareta wanda tafi ƙauna. Babu kyau dai nuna fifikone domin ina tunanin yana daga cikin kuskuren da aka aikata har aka samu wannan matsalar ma data afku" Tana kaiwa iyakar nan tayi tafiyarta. Malama Babba dake jan numfashi da ƙyar sabida ciwo da kuma nauyin kalaman da Ƙarama ta faɗa mata yasa ta kasa ma magana. Wannan itace rana ta farko a cikin tarihi da Ƙarama ta mayar ma da Babba martani a iyakar tsawon rayuwar da suka yi tare. Da ƙyar ta daddage ta shiga ɗakin Baba malam ta kwanta a kan doguwar kujera tare da shiga dogon tunani da fargaban abinda zai biyo baya. Ta wani ɓangaren na zuchiyarta tana roƙon Allah yasa kada Sabuwa ta sake tako gidannan. Baba malam kuwa yana fita ya leƙa ɗakin samarin yaranshi su shida da sukai ragowa. Auwalu, Ramadan da Magajin malam ya taso suka soma zagayen neman Sabuwa cikin tsakiyar dare unguwar babu motsin kowa da komai. Suna shan kwanar layin dake bayan layinsu daidai lokacin Babangida ya faka motarshi kenan. Kashe fitilun motar da yayi yasa bai hasko su Baba Malam ba. Sabuwa ce ta fito tana kunƙunni Babangida ya biyota tare da matseta a jikin motar. "Babu shakka Babangida" Cewar Malam daya iso inda suke"

SABUWA:. Da mugun sauri Babangida ya sake ni jikinshi har rawa yake yi. Baba malam kuwa sabida tsabar tashin hankali da ruɗu kusan faɗuwa yayi daga tsaye. Da sauri magajin malam da Ramadan suka tareshi. Babangida kuwa kanshi ya sauke ƙasa jikinshi na wani irin kakkarwa. Ni kuwa sai tsilli_tsilli nake yi da idanuna" Baba Malam ya kafe mu da idanunshi kallon ƙyama da tsana yake watso mana. "Daga ina kuke Sabuwa?" Ya tambayeni murya a kausashe. Daga gidan rawar dare muke" "Shi ya nemi kuje kenan. Dake ke shashashace wacce bata da hankali baki san inda yake miki ciwo ba shine kika bishi? Mutumin da yayi miki ciki ya kafa tarihi mai muni a rayuwarki ya nemi ya tsere miki shine har kika kuma bashi yadda. Kuma a gidana za'ayi wannan iskancin ni Baba Malam?" Ni dai ban tanka ba. "Yayi kyau ki wuce mu tafi. Daga yau in kika kuma fita wallahi zan yi mummunan saɓa miki zaki yi mamakina sawa zanyi a banƙareki" Iyakar abinda ya faɗa kenan ya juya magajin malam da Ramadan na riƙe dashi Bayansu na bi muka bar Babangida a tsaye a wajen. A tsakar gida kuma Alawiyya da Malama ƙarama muka tadda "An ganota kenan Malam?" Kai kawai yake girgizawa ba tare daya iya furta wata kalma ba. Malama Babba tana kwance taji shigowar Baba malam ya tsaya a kanta yana kallonta. "Kin cutar dani sosai Saratu. Amman ki sani abinda kika aikata sai yafi damunki fiye da ni. Za kuma kiga matakin da zan ɗauka wanda daga ke har Baban naki bazai muku daɗi ba." Zama yayi yana huci kawai. Ji yake yi tamkar ya cire zuchiyarshi ko ya huta da irin zugin da take yi mishi. Vidiyon Babangida da Sabuwa sai sake haska kansu da kansu suke yi a ƙwaƙwalwar Baba malam. Tunda yake bai taɓa ganin mace dana miji a rungume da juna a cikin gida ma ba a waje ba. Amman sai gashi yau yaga Babangida ido da ido rungume da mace a tsakiyar layi. Idanunshi kawai ya lumshe. Tsugunnawa tayi a gabanshi tana hawaye. Tayi magana ta kasa sabida ba tasan me zata ce ta kare kanta ba. Tasan bata isa ta iya fahimtar da Malam har ya sake yadda dasu ba, shi sau ɗaya tak yake yadda da mutum. "Ai dole Saratu ki kasa furta kalmar da zaki kare kanki da Ɗanki. Ki fitarmun a ɗaki bana ko ƙaunar in buɗe idanuna nayi tozali dake. Babangida kuma har abada ya fita a raina kenan. Kinsan Allah ba shi kaɗai ba hatta da zuriyar da Babangida zai tara bazan taɓa jin na ƙaunacesu ba abadan. Tashi ki fita, ki fita nace ko in bar muku gidan baki ɗaya" Ya ƙarashe maganar cikin ɗaga murya. Cikin ɓacin zuchiya ta saka kai ta fice tana rausa kuka tamkar yarinya ƙarama. A wannan dare haka wannan iyaye suka sake kwana idanunsu biyu ras. Asubar fari Baba malam ya sanar da ya dawo da zaman da za'ayi yau. A kira yaran duk a sanar musu takwas na safe za'ayi zaman."

Babangida:. Su Baba Malam na juyawa ya runtse idandunanshi gabaki ɗaya babu laka a tattare dashi. Bawai tsoron dan an gansu tare yake yi ba, tsoronshi a yadda aka gansun, dakuma irin tashin hankali da zai ƙara saka Malama Babba a ciki su suka fi komai ɗaga hankalinshi. Da ƙyar yayi da gaske ya shiga motar ya ja zuwa Club ɗin. Da ba dan mai motar na can yana jiranshi ba bazai koma ba. Amman ko da yaje bai wuce uku da rabi na dare ba suka saukeshi a bayan layi ya shige gidan Kawu Manga ta hanyar haure katanga. Ko da ya shiga ɗakin ya tarar da Ƙasimu yana kan dadduma yana ta tilawa da halama sallah yayi ma. Haɗe girar sama data ƙasa Babangida yayi dan ko da Ƙasimu ya juyo da nufin tuhuma fuskar Babangida saita tsoratashi sosai Babu shiri ya mayar da hankalinshi kan abinda yake yi. Babangida ya miƙe ya fita tsakar gida dan bacci ya gagareshi.. Ruwa ya diba a randa a bokiti ya shiga banɗaki ya tsarkake jikinshi kana ya dawo ya ta da Sallah. Da asubar Fari Malama Babba tayi kiranshi akan za'ayi zama yau ba gobe da Malam Baba yace ba. Amman bata san ko za'a buƙaci yazo ayi zaman dashi ba. A sanyaye Babangida ya sauke wayar a kunnenshi tare da sauke gwauran numfashi.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull