Kenza eBookz

Idan kaya ya gaji book 3 - Chapter 5

Idan kaya ya gaji book 3 - Chapter 5

Idan kaya ya gaji book 3 Chapter 5: Idan kaya ya gaji book 3 Chapter 5. SABUWA:. Ni kam ta ɓangarena ina komawa ciki nayi baje_baje akan katifa sai bacci.…

4,059 words

SABUWA:. Ni kam ta ɓangarena ina komawa ciki nayi baje_baje akan katifa sai bacci. Sai daf asuba Alawiyya ta tasheni. Da ruwan sanyi na tsarkake jikina ina idar da Sallah na yi komawata gado. Abuna, bani na farka ba sai wajen bakwai da minti goma, shima ɗin Adama ce ta kirani a waya. Adama da sassafe kira haka kin tashe ni a bacci" Sai cewa tayi. "Wallahi kuwa kinga dama dai yau zamu sake zuwane Maigogul ne ma yace zai kawo mu ke harda magazin babu wani shege ko shegiya da zasu hanamu shiga yau. A shirye sosai zamu tawo" Dariya na saka. Kice unguwa yau zata ɗauki harami ga Maigogul ga Mazagin kinga ai babu magana. Sai kun zo dan ALLAH Adama in zaku tawo ki kawo mun littattafan hausa zan ɗan kakkaranta nifa zaman ya isheni ban saba da haka ba. Jiya ma na fita ai. Nan na labarta mata duk yadda fitar da dawowar ya kasance. Dariya tayi. "To zan yo miki rentin amman ina kawo miki zaki lale kuɗaɗen mutane ki basu dan mai rentin ɗin bata da mutunci ko na misƙala zarratin dan ko daɗewa littafinta yayi saita yi rashin mutunci kuma sai an ƙara mata kuɗi. Baki na taɓe ganin shigowar Alawiyya da masa da miya da kunun tsamiya. To shikenan sai kun karaso baro in karya sai zuwa anjima" Datse wayata nayi na karɓi abincin dake hannun Alawiyya. Tana bani ta fita. Ni dai ina daga ɗaki matan gidan masu aure duk wacce tazo sai ta ɗaga labule ta ganni ta taɓe bakinta. Ko wacce da irin nata salon da take leƙowa dashi. Ni dai inata harkokin gabana ko in kula dasu har dai suka gaji suka gama. Gidan cike da hayaniyar muryoyin maza da mata, harma da yara ƙananu. Ƙila wani taron akeyi a gidan yau. Ina gama faɗar haka a zuchiyata na miƙe na fito tsakar gidan na yi zamana a kan turmi ina yanke farce, ina kallon yadda suke ta shigewa ɓarayin Baba Malam. Murmushi nayi ni kaina nasan ba ƙaramin saka Babangida da iyayenshi nayi a uku ba.

BABA MALAM:.

Manya manyan taburmaine malale a farfajiyar shayyar Baba Malam. Yana zaune a kujera wan sita. Yaranshi maza da matan suna ta shigowa kamar dai yadda ya buƙata. Sai daga can kusa da ƙarshe can sosai kafin Malama Babba ta tawo Yaya Hanne na biye da'ita. Baba malam yayi ƙur ya zuba ma Yaya Hanne idanu, ya mayar da idanunshi tsakiyar idanun Malama Babba. Sai da suka nemi waje aka zazzauna kana Baba malam yayi gyaran murya ya soma da sallama. Duk suka haɗa bakunansu wajen amsa sallamar tashi. "Kafin in soma magana a kan abinda ya tara mu anan. Hanne inaso ki yi haƙuri ki jira Babba a ɗakinta. Wannan taron na cikin gidane" Yaya Hanne ta dubi Baba malam ta dubi Kawu manga kafin tace. "Zamu tafi ni da Manga ƙaninka kenan? Dan in ni bare ce a cikin wannan maganar to Manga ma ai bare ne ko?" Baba malam bai yi mamakin abinda Hanne tayi mishi ba. Dan a baya ma babu irin zigin da bataima Malama Babba ba akan dole saita ɓokare mishi. Har anyi lokacin da ya dakatar da ita Malama Babba zuwa duba Hannen sai dai ita tazo ta dubata. Gadararta shine mijinta hamshaƙin mai kudine kuma su ƴan boko ne sosai. Kuma tana matuƙar son Malama Babba tana taimaka mata. Duk wani kwancen kayanta masu tsada tsada Malama Babba take bama ita ta soma bata kwancen gwal, ita kuma ta soma bata kwancen atampa supa da aura. "Babba kisa Yarki ta tafi ta jiraki a can falonki" Bata da yadda zata yi tasan halin mijinta ba daɗi gareshi ba yana da bauɗaɗɗen hali. Da ƙyar ta jaye Yaya Hanne ta fita zuwa falonta. "Ke Saratu haka mijinku yake tsinkaki a gaban kishiya?" Ta faɗa tare da ƙanƙance idanunta irin na masifarnan. "O_o _o_o ɗanki ne ya jawo mun. Kinsan tunda ya aikata wannan abun wallahi in faɗa miki Malam bai sake sakin fuskarshi dani ba." "To meye naki ke a ciki halin ɗan yau? To ni dai ki cire tsoro ki sanar mishi ciki bana Babangida bane faƙat. Kuma kiyi ƙoƙarinki cikin ya zube ki tabbatar yarinyarnan taci maganin dana kawo miki. Ji yarinya a tsakar gida tanaima mutane kallon ɗaɗɗaya almura idanta kamar soyayyar gyaɗa" Malama Babba da sauri ta fita ta koma wajen taron. "Wawo a buɗe taro da adda'a" Wawo yana daga zaune ya buɗe taron da adda'a kafin Baba malam yace. "Dangane da batun wancan shashashan ɗan iskan yaronne Babangida. Shine dalilin taruwarmu anan sabida tunda abun ya faru inata aikin nazari da binciken duk daya dace. Kuma naga saka hannun mahaifiyarshi ta ɓangarori manya wanda hakan ba ƙaramin mamaki ya sanya ni a ciki ba. To abu na farko dai shine. Kamar yadda nace Babangida ya bar gidana, to ina nufin ko bayn raina ban yadda yaronnan ya dawo cikin gidannan ba zaici gaba da zama tare da Manga. Kai Manga" Baba malam ya dubeshi. Cike da tsantsar ladabi ya amsa. "Na'am Yaya" "Sai kasa idanu sosai akan su Ƙasimu dan gudun kada ya lalata maka tarbiyyarsu ya rusa maka ginin daka daɗe kana ginawa. Ni da a so nane ma yabar gidan naka ya shiga uwa duniya. Amman dana je Ringim nake labartama Kawu da Goggo Amfana halin da ake ciki. Suma sai suka ce lallai Babangida ya zauna a wajen naka tunda dai kai kaji zaka iya. Wannan itace maganata ta farko. Maganata ta biyu kuma itace. Sabuwa zata ci gaba da zama a gidannan har saita haihu zata bar gidannan. Sannan na saka doka duk wanda a cikinku ku mata matannan kuka sake takalar yarinyarnan tazo tana mana rashin mutunci a gida zan saɓa muku. Idan ta haihu zata bar gidan izuwa gidan Babangida zan sa a ɗaura aurensu ta tare a matsayin matarshi suje can su reni abinda suka haifa yafi ace suna yawo gidan rawa_ gidan rawa, dan wani cikinma sai ya sake ɗirka mata ba komai bane." Shiru yayi yana nazarin fuskar kowa. A cikinsu babu wanda yaji daɗin hukuncin daya yanke musamman mata_matan. Malama Babba kam hawaye ma take ta sharewa. "Dangane da batun ɓata tarbiyyar da nace Babba na da saka hannu ciki shine. Na daɗe da hana Babangida mu'amalar abota da yaronnan Mustapha ɗan gidan Baba na shago. Sabida yarone da sunanshi yayi ƙauri a unguwa. Bincike ya tabbatarmun da sahalewar Babba yaci gaba da abotarshi da yarannan ba tare da sanina ba. Sai abu na biyu tana sane da yawon dare sarai da Babangida yake yi. Da saninta yake yin wannan yawon daren. Sabida bata son ɓacin ranshi ita a kullum ta saka Babangida farin ciki. Wanda daga tsakiya ga abinda yaje ya jajiɓo mana jibi yanzu ba hawaye take yi ba? To in dai Babangida ne kukanma banyi tunanin in an soma ba. Sabida a cikin wannan halin da ake ciki har rashin kunyar Babangida ta kai ya kira Sabuwa su fita zuwa gidan rawa har yana iya rungumeta a layi wa'iyazubillah Tarbiyya, da ilimin addinin dana ɗaurashi akai bai amfaneshi da komai ba kaico. Magajin malam sunji tsoron sanar dani fitar dare da Babangida yake yi dan gudun su jefani a mawuyacin hali. Wai ashe har ƙananun kaya yake sakawa yaita yawonshi a gari ma. Kuma ita Babba tana sane sarai" Duk waɗanda suke cikin wajen taron hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi akan lamarin Babangida ba, dama abinda ya aikata jiyan. Wannan wani sabon lamarine a cikin wannan zuriyar mai ɗauke da ɗumbun tarbiyya da ladabin yi nayi bari na bari. Malama Babba taji tsoro da fargaba irin wanda bata taɓa ji ba a rayuwarta. Shikenan ashe ma duk abinda suka Tsara da Yaya Hanne babu aikin da zaiyi anan. Bata da kalmar da zata iya dawo da martabarta da kimarta a idanun Baba malam ko Qur'ani zata haɗiye tana aman surori bazau kuma yadda da'ita ba. Ita yadda ɗaya ce a wajenshi, baya kuma bayar da wata dama ta biyu bare har aje ga ta uku." Kai Baba malam ya girgiza yace "Ko akwai wanda yake jin yana da magana ko wata shawarar?" Babu wanda yace shine ba dan basu da abinda suke son faɗe ba. Sai dan kawai gudun fishin Baba malam da faɗin abinda ka iya tunzurashi yayi fishi da mutum" "To shikenan tunda babu mai magana na sallameku dukka, banda kai Manga " Kafin su soma yinƙurin tashi suka jiyo hayaniya mai ƙarfi a tsakar gidan harda ihun wani almajirin Baba malam da halamar wata muguntar akai mishi. Ɗuu suka fice matan harda ɗan gudunsu dan son ganin menene ke faruwa. Suna fitowa suka tadda ƴan uwan Sabuwa ne a tsakar gidan Almajiran Malam Baba na ƙoƙarin hanasu shiga shine har aka yanki magajin malam a hannunshi."

SABUWA:. Ina zaune a tsakar gida na jiyo hayaniya daga nesa tanata tahowa. Murmushi nayi dan nayi imani su Adama ne suke shirin zuwa ganina. Ai kuwa ban aune ba sai gasu a tsakar gidan almajirai nata faman tattaresu. Magajin malam magazin ya riƙe yana ja ai kuwa kamar ƙibtawa da bismillah Magazin ya zaro wuƙa ya yanki tsintsiyar hannunshi ya sake shi babu shiri, tare da yin wani ihu. Ihun da yayi sanadiyyar fitowar su Sa,a Ɗuu. "Meye haka ke faruwa. Me zan gani?" Cewar Malama Babba wacce dama a cikin baƙin ciki take. "Abinda kika gani shi kika gani. Ku dai kuna da neman fitina wallahi. Babu damar azo ganin Lolo sai ku hana Malam ya hana Malam ya hana. To ko makawuyane yau dai dole yayyen Lolo su ganta" Maigogul ke magana cikin ɗaga muryarshi akan Malama Babba." Tare da Kawu Manga Baba Malam ya ƙaraso wajen. Zuwanshi yasa yaranshi suka soma zamewa, ko wacce na jaye ɗanta. Malama Babba tace. "Allah ya wadaranku ku dai baku da kunya ban taɓa ganin marasa kunyar iyaye kamarku ba. Ace kana uba amman kaine jagora..." Da mugun kallo Baba malam ya kafeta ƙirjinshi na sama da ƙasa. "Hattara Dattijuwa bari kul Wallahi. Kin ganni nan na sari mutane sunfi dubu, har kisa nayi an kulleni amman na fito. Wallahi ko a barmu muga Sabuwa ko in tsigema wata kunne a gidannan" Kafin suce wani abun Babangida da shigowarshi kenan ya ruƙunƙune Magazin ta baya yana ƙoƙarin fitar dashi. Ai kuwa nan kokawa mai haɗari ta shiga gudana a tsakankaninsu. Magazin ya samu Babangida ya dinga naushinshi a duk gaɓoɓin da yasan zai karya mishi kuzarinshi. Baba malam yana tsaye ya hana su Wawo raba wannan faɗan. Sai gwabza dambe akeyi. Zaro wuƙar da magazin yayi ne Babangida ya danna a guje magazin yabi bayanshi. "Kuje Wawo ku raba faɗan maza" Yayi maganar cikin ba da umarni. "Maigogul na fahimci dukkannin take takenka burinka yin fito na fito da nine. Burinka ka kunyatani a idanun duniyane. Ku matan ku shiga ku ga Sabuwa, amman duk abinda zaku ce mata sai dai kuce mata ayau. Wallahil azeem babu wacce zata sake shigowa cikin gidannan da zummar ganin Sabuwa In kuma da'ita zaku tafi gata nan. Kuje ku yi duk shelar da zaku yi. In aka sake kawo mata ziyara abinda kuke tunanin yiyuwarshi bazai yiwu ba. Ya kamata ka gane jama'a na ganin ƙimata" Juyawa yayi zai bar wajen. Maigogul yace. "Ai na faɗa na maya muddin muka tafi da Sabuwa to tabbas sai abinda kake son burnewa ya fito" "Saime ya fito mana. Nima bari kaji duk ranar da wani ko wata daga ɓangarenka ya sake zuwa da zummar ganin Sabuwa to tabbas ɗana bazai taɓa aurenta ba ka sani bana magana biyu. Ka kuma fice mun daga tsakiyar gida babba dakai a shekaru a ido gaka babu laifi sai dai kash hauka da hauragiya su sukai maka ado Ke kuma ki shige ɓarayinku" Fuu Baba malam ya fice a gidan yana faɗan maganganu domin ranshi yayi matuƙar ɓaci ainun. Jinshi yake yi kamar ba shi ba. Hatta gidan da mutanen gidan gani yake ba su bane. Jin wannan furucin sai jikkunanmu dukka suka mutu. Maigogul babu shiri ya fita. Ni kuma na ja su Adama muka shige ciki. Yaya aka ƙare da magazin da Babangida oho. Muna daga ɗaki muka jiyo kukan Malama Babba sai bata haƙuri akeyi. Fuu ta shigo cikin ɗakin da nake ta rufeni da shegen duka. Banyi niyyar ramawa ba sabida inason sake jefata cikin uku. Ɗauke numfashina nayi da ƙarfin tsiya wanda hakan yasa nayi suman dole. Su Adama kuma suka fasa ihun Malama Babba ta kasheni. Da ƙyar na yarda na farfaɗo harma ana shirin kaini asibiti kafin na yarda na farfaɗo. Baba malam ya dinga faɗa a tsakar gidannan tare da gindaya sharruɗa masu zafi. Ranar gaskiya an fusata Baba malam sosai. Gaga_gaga al'amura sukaci gaba da tafiya ranaku suna shuɗewa. Abubbuwa marasa daɗi sun faffaru ciki harda yinƙurin zubarmun da ciki da Malama Babba tayi har sau biyu bata samu nasara ba Na biyun saida nayi sati biyu a asibiti kafin aka sallamoni. Malam yayi faɗan yayi rikici sosai sai da akaita zuwa bashi haƙuri daga dangin Malama Babba kana ya hakura. Babangida kuma bai ganni ba balle yayi nashi yinƙurin. Su Maigogul kuwa an ɗauke ƙafa gudun kada a fasa aurena. Sai dai su kirani a waya mu gaisa kawai. Da lokacin daya kamata na soma zuwa awo yayi Baba malam ya haɗani da malama ƙarama ta rakani muka je. Duk wata hidima Baba malam ke yi mun. Duk abinda nake so zanje in sameshi a makaranta in faɗa mishi in sha Allahu kuwa zaisa a aiko mun dashi. Babangida dai ya samu da ƙyar an roƙi malam ya yarda zai dinga shigowa gaishe da mahaifiyarshi amman shi baya buƙatar gaisuwarshi. Ƙiyayya babu irin wanda ba'a nuna mun a gidansu Babangida ba. Ni kuma zaman gidan ya dameni nayi yinƙurin guduwa har sau biyu Baba malam yana hanawa. Kuma koma dai yayane ina ganin girmanshi kwarjini gareshi bana wasa ba. Ranar da cikina ya cika wata tara cib na haifi diyata mace a asibiti Nasha baƙar wahala dan anyi tunanin ma na mutu Baba malam duk ya shiga damuwa ainun MRS BUKHARI [8/14, 7:22 AM] +234 802 205 9556: https://chat.whatsapp.com/IUKFTeul76p2VaAvQ5nk0U?mode=ac_t

IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI LITTAFI NA UKU SHAFI NA SHIDA 6

Na sha wuya sosai, abun har ya gagara ansa hannu za'ai mun aiki sai kuma na sauka da kaina. Ana haihuwar kuma duk wahalar sai ta wuce. Sai washegari na samu kaina Duk da yarinyata ƴar gaba da fatiha ce sai naji duk duniya babu abinda nake so sama da wannan yarinyar. Gashi babu ta inda ta baro Babangida Kunji wata ƙudurar Allah. Yarinyata tana gadon jarirai a kwance Malama Babba data iso yanzu da malama karama da muka tawo tare duk sun ƙi su ɗauketa har sai da Baba malam ya ƙarasone yasa hannu ya ɗauketa. Ya daɗe sosai yana kallon yarinyar. Nasan dai bazai wuce tsantsar kamanninta dashi yake mamaki ba. "Allah mai yin yadda yaso, yarinya ta raba duk wata kaddama. Sabuwa sannu ko. Akwai abinda kike buƙatane?" A_a so nake dai ƴan gidanmu su san halin da nake ciki" Kai ya gyaɗa. "Nasa a sanar musu zasu zo nan asibiti su sameki. Mahaifiyarki zata zauna ta kwana dake anan zuwa gobe a sallamemu sai mu koma gida" Malama Babba tace. "Nayi tunanin ai a gidansu zata yi wanka. Kasan haihuwar fari tana buƙatar kulawa daga ita har jaririyar. Sannan duk wannan kamannin ai yana da kyau a sake tabbatarwa ko? " Kallo mai ɗauke da tuhuma yayi musu du su biyun. Sai da yayi ma jaririyar adda'a kana ya dubeni yace. "Akwai wani suna da kike so a saka mata ne. Ko Babanta ya riga da ya zaɓa mata sunane?" Dukkansu su ukun ni suke kallo. Ni kuma sai numfashi nake saukewa. Babu sunan da muka zaɓa mata" Kai ya gyaɗa yayi. Mata huɗuba da suna Mardiyya kana ya miƙo mun yarinyar na rungume abata ina jin motsin sonta a zuchiyata. "Yarinya nayi mata huɗuba da sunan kakarta mahaifiyar Babba wato mardiyya. " Daga malama Babba har malama Ƙarama sun kaɗu sai dai babu halin tankawa. Ramadanne ya shigo da abinci. Malama Ƙarama ta zuba mun, farfesun kayan ciki ne sai kunun gyaɗa. Nasa hannu na amsa dan dama ba ƙaramin yinwa nake ji ba. Ga jikina babu ƙarfi kwata_kwata har rawa yake yi nasha wahala fa sosai. Fita Malam Baba yayi. Ni kuma jinjirata na jikina na cinye wannan farfesun tas na kora da kunun. Take bacci ya yanko mun. Na daɗe sosai ina baccin wahala ina farkawa naga Rahama da Labbai Sai naji wani sanyi a raina da naga ƴan uwana. "Sannu Lolo kin tashi? Ai kinsha baccin gajiya haihuwa ai ba wasa ba. Allah dai ya raba lafiya saura haramar yin aure kuma. Boyeki ya ƙare ai. Cewar Rahama dake shan tea Labbai kuma na riƙe da Mardiyya. "Kinga Lolo yarinya kyakkyawa sak ubanta babu inda ta baro shi. Sai dai mun zo muka tarar babu kowa a wajenki ga jaririya a kwance kunata sheƙar bacci." Hmm ai basa zauna ba. Gara da Allah ya kawo ku dan ni kam daga nan sai gidanmu. Na gaji da wannan kullen da suke yi mun." "A_a kada ma ki soma Lolo. Gara ki koma can ɗin dai kinga kar maganar Auren naku ya rushe kuma. Za dai ayi magana zan zauna dake acan ɗin sabida a kula dake yadda ya kamata. Ki ɗan haɗa da shan magungunan mata dana gyaran jiki tunda yanzu batun aurenku ne abu na gaba. Adama ce taso tazo ta zauna dake to bata jin daɗine a kwance take babu yadda take, ga babu kuɗin zuwa asibiti. Lusarin mijin nasu kuma baya ma garin yabi babbar mota wai zuwa Inugu. Shi Babangidan yazo yaga yarinyar?" Bai zo ba. Kuma nasan bazai zo ba. Ai hatta kayan jaririya, da duk wani kayan haihuwa Baba Malam ne yayi. Babangidan da har yanzu ba'a amsa gaisuwarshi" Ƴar Shuwa ce ta katse mana hirarmu. Ina ganinta nayi murmushin farin ciki nayi kewarta sosai duk da dai a rana ma mukan yi waya takai sau uku inma ta kama har fi. Haka muka kwana mu uku ma a asibitin daga mu sai mu, an dai kawo mana abincin dare lafiyayyen tuwon shinkafa da miyar shuwaka har da man shanu. Washegari sassafe su Rakiya da su Maigogul da ƴan ɗakinmu dukka suka zo ganin yarinya. Anan Baba Malam ya tarar dasu aka dai gaisa babu yabo babu fallasa A hakan Maigogul ya nemi Rahama zata zauna dani ta kula dani acan. Allah cikin ikonshi sai tace . "Dama ko baku buƙaci hakan ba ni zan buƙata. Sabida Sabuwa na yin arba'in a ranar za'a ɗaura aurenta a ranar kuma zata tare a gidanta in sha ALLAH" Murmushi Maigogul yayi yace. "To hakan yayi kyan alƙawari cikawa. Sai dai wani hanzari ba gudu ba. Ni ina zanga kuɗin kayan gado nan da kwana arba'in? Ka gansu nan dukkansu lokacin aurensu su suke yima kansu kayan ɗaki. Ƙarya da ciwo bani da kuɗin da zanma Lolo komai. Sai dai a ɗan ƙara mana lokaci" Rakiya tace. "Gaskiya kam muna buƙatar ƙarin lokaci. Dan inta wannan za'a daka ma auren bazai yiwu ba in dai da kudinshi za'ayi bikin." Ai da faɗin haka Maigogul ya hau nuna ma Rakiya hannu tana faɗa yana faɗa har sai da ma'aikatan jinya suka zo suka musu magana akan su fita. Baba Malam yana tsaye motsin kirki ya kasa yi sai zuwa can yace "Ya yara ba zasu lalace ba ace yarinya ita zata ma kanta kayan ɗaki ita ba aiki ba ba sana'a ba. Shin waɗannan waɗanne irin mutanene Babangida ya kwaso mana wai? Hmm babu damuwa. Sabuwa ku shirya ga mota a waje an riga an baku sallama" Yana gama fadin haka ya fice. Su Labbai ne suka haɗa mana kayayyakinmu. Suka kawo mu har bakin mota. "To Rahama duk yadda ake ciki mayi magana ko ta wayane" "To Rakiya. Amman fa ni ina ganin babu bukatar a ɗaga aurennan. Bari dai in muka isa can ɗin zamu yi waya" Da wannan muka rabu. Muna shiga gidansu Babangida Malama Babba dake tsaye a tsakar gida rike da bokiti ganinmu yasa ta sau bikitin. "Ohh ni Saratu yanzu Malam ashe da gaske yake yi wannan yarinyar a nan ɗin zata yi jego? Babu komai ai zata gama jegonne" Rahama tace. "To da a ina kike son tayi? Akayi renon cikin da haihuwarshi ma sai wankan jegone ba za'ayi ba. Ke Lolo inane ɗakin da zamu zaunan yake?" Nuna mata nayi da hannu muka wuce muka bar Malama Babba na sababi a tsakar gida. Ina kwance Rahama tace. "Kinga Lolo tashi ki ba yarinyarnan mama tasha sai mutsu mutsu take yi. Ko ruwan nonon bai zo ba ki bata in tana ɗan zuƙa zai zo da kanshi." Miƙewa nayi nasa hannu zan karɓeta Malama ƙarama tayi sallama ta shigo da gaushi ta dire ta fita, bata daɗe ba sai gata da ruwan wankan jinjira a sabon bawon na cikin seti da Baba malam ya bayar aka siyo. "Gama bata Maman sai ki miƙota ayi wanka. Rahama ko? Sai kuje kiyi mata wankan yamma. Ni na dunga mata na safe" Baki Rahama ta taɓe tare da miƙewa. "Lolo kafin ta gama sha bari in wanke kayan jinin da muka dawo dashi. Baiwar Allah sabulu da omo fa" Malama ƙarama tace "Zan je in tambayo Malam duk yadda akayi ya manta ne bai siyo a siyayyar haihuwar ba. Bari a gama ma Mardiyya wanka tukunna" Tayi maganar babu annuri kamar a yadda Rahaman tayi mata kenan. Miƙa mata jinjirar nayi na fita Rahama ta bi bayana zuwa banɗakin tayi mun wankan tawul ta gargasa mun jikina, in tasa tawul dinnan a ƙasan marata ta danna sai jini yaita zuba. Naji daɗin jikina sosai ana kiran sallar muka fito daga wankan. Mun shiga mun samu Malama ƙarama harta gama yima Mardiyya wanka tayi mata gashin cibi tana wanke kayan da aka cirema yarinyar ne a cikin ruwan wankan. Muna shigowa ta suri bawon ta fice tana faɗin. "Allah ya sauwaƙe wallahi ko a cikin labaran hikayoyi ban taɓa jin labarin da yayi kama da wannan ba. Wannan abun kunyar da yawa yake" Tsaki muka ja ni da Rahama. Ni dai tsabar daɗin wanka har wani bacci_ bacci nake ji. Ina gyangyaɗi Rahama na gyaran ɗakin Alawiyya ta shigo da ƙaton filas na ruwan zafi sabo fil. Bayan ta ajjiye ta kuma shigowa da ƙatuwar leda shaƙe da kayan tea komai na gongoni sai sikari ne kaɗai na kwali mai zaki ce, wasu na kiranta mai iyali. Data sake shigowa sai ta dure ƙatuwar kular abinci da wata babbar farar leda. "Ga sabulun da omo Baba malam yace a kawo muku. Allah ya raya Mardiyya " "Ameen in da gaske kike yi. Shi zakaran da Allah yaso sai yayi cara ko ana shawo ana muzuru sai yayi caranshi." Rahama na gama faɗin haka ta buɗe ledar ta suri ƙaton omo ta fice zuwa tsakar gidan. Ni kuma tea kakkauta na haɗa cikin ƙaton kofi, na saka lokaci a cikin kular da aka shaƙo mun da lafiyayyar jallof mai nama da kifi. Sosai na zage ina cin abincin. Na jiyo Rahama tana ta dura ashariya a tsakar gida. Ban dai ji muryar kowa ba halamu ya nuna wani abun ta gani shi yasa. Muryar Baba malam naji yana gargaɗinta akan ba'a mishi hayaniya bare ashariya a gida, ta kiyaye in ba haka ba zata koma inda ta fito. Daga nan na jiyo takun tafiyarshi zuwa ɗakin da nake. A bakin ƙofa ya tsaya. "Sabuwa an kawo miki kayan shayi da sabulai?" E an kawo gasu nan" "Akwai wani abu ne da ake buƙata wanda ban siyo ba?" Shiru nayi ina nazari gaskiya yayi ƙoƙari ya sai komai da komai ko ɗan halak albarka. A_a babu a yanzu dai" "To shikenan gobe za'a soma miki naman gashi. Ki zauna da shirinki kina yin arba'in zaki tare a gidanki. Allah zai rufa asiri ko babu yawa ni zanyi miki kayan ɗakin sai ki sanar ma iyayenki" Nan ya tafi ya barni da mamaki baki a hangame jin wai zai mun kayan ɗaki. A idanunshi kaɗai inna kallla ina hango ƙiyayyar da yake yi mun, amman duk da haka yana ƙoƙarin lallai sai Babangida ya aureni. Murmushi kawai nayi naci gaba da kora tea.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull