Kenza eBookz

Idan kaya ya gaji book 3 - Chapter 6

Idan kaya ya gaji book 3 - Chapter 6

Idan kaya ya gaji book 3 Chapter 6: Idan kaya ya gaji book 3 Chapter 6. Malam Baba:. Daga wajen Sabuwa kai tsaye ɗakin Malama Babba ya wuce. Suna zaune ita…

2,882 words

Malam Baba:. Daga wajen Sabuwa kai tsaye ɗakin Malama Babba ya wuce. Suna zaune ita da Yaya Hanne suna tattaunawa dangane da batun haihuwar Sabuwa suka jiyo muryarshi da ma abinda suke saƙawa mummuna. Basarwa yayi tamkar bai ji ba dan ko a fuska bai nuna ba, Malama Babba kuma sai tasha jinin jikinta. Ganin babu damuwa a fuskar Malam yasa ta fito da fara'arta shi kuma ya riga da yaji komai murmushi kawai yayi. "Yauwa Babba batun auren Babangida da Sabuwa ne. Ki faɗa ma ɗanki ina neman dubu ɗari biyu a hannunshi kafinnan kafin sati uku. Kafinnan kuma ya kawo kuɗin ragon da za'aima Ƴarshi hakika nera dubu talatin cib. Ku kuma mata ta ɓangarenku sai ku soma shirye_shiryen biki" Mamaki yasa Malama Babba ta kasa rufe bakinta data hangameshi hangangan. Har Malam ya kusan barin ɓarayin sai taga ya juyo. "Af Babba na mance. Zai soma iya fara neman gidan haya tun yanzu kinsan gidajen haya tsada suke yi" Dole ta haɗiye malolon daya tokare maƙoshinta murya a dashe tace. "To Malam zan faɗa mishi saƙonka." Ɗaki ta shiga ta zauna daɓas a kusa da Yaya Hanne. Sai salati kawai suke yi a cikin wannan yanayin Babangida ya shigo da sallama ya samesu. Yasan baya raba ɗayan biyu shi yasa ma bai tambayesu meke faruwa ba. "Babangida kaga dai abinda ka jawo mana yanzu muna ji muna gani zaka auri wannan yarinyar maras tarbiyya ta zamema uwar ƴaƴanka. Wannan wanne tarihi Malam yake son kafa mana mai zafi haka. Yaya Hanne duk wani shirinmu ya rushe ki duba sunan uwarmu ya saka ma yarinyarnan sabida ya nuna ma Ƙarama iyakata" Babangida ya razana sosai da wannan labari daya riskeshi. Har ƙasan zuchiyarshi baya jin ko ɗigon son Sabuwa face zallar sha,awarta. Manufarshi shine cin moriryar ganga kawai kamar yadda akema duk wata karuwa. Sai gashi yaci biredi yana tunanin ya yaga leda ashe ledar bata yagu ba. Yafi kowa sanin rashin tarbiyyar gidansu Sabuwa shi a iyakar saninshi ma bai taɓa ganin gida maras tarbiyya da kowa ɗan iskan kanshi bane kamar gidansu Sabuwa ba, wai ashe Malam Baba zai yarda a auro Sabuwa a matsayin surukar gidan malamai gaba da baya? Tunaninsu duk barazanace duk da sun san malam kaifi ɗayane amman duba da tarbiyyar gidansu Sabuwa yasa suke tunanin ba za'ayi auren ba" Iska ya busar yana jin wani zazzaɓi_zazzaɓi na buso mishi. "Saratu ku kwantar da hankalinku. Gobe ki tambayi Malam zuwa ƙauyensu in ya barki zamu je a motata. Inma hagu taƙi yi zamu koma dama. Kinsan Allah Babangida bazai Auri wannan yarinyar ba. Kuma dena damun kanku" "To Yaya Hanne ai bazai taɓa barina zuwa ƙauyansu ba sabida yasan abinda zai kaini. Kuma kinsan kafiyar Malam kuwa? Balle wannan abun yadda ya ɗaukeshi da zafi. Kuma duk ya fimu tsanar Sabuwa da danginta ma." Yaya Hanne ta dafa Malama Babba tace ."zanzo gobe zaki ji zuwa da dawowan Saratu. Kai kuma saika kiyaye gaba kana ganin halin da kasa mahaifiyarka a ciki. Gata da kishiya sun samu abun goranta mana marar goguwa." Shi dai Babangida yama kasa cewa komai, zuchiyarshi sai tuƙa mishi take yi. Duk duniya babu wanda yake so sama da sabuwar budurwarshi wadda a lokacin ita ce a gaba. Duk da baya jin aurenta, amman tana da dukkan abinda yake buƙata a jikin mace. "Ka fasa bankinka ka ciro dubu talatin zan kaima Malam kuɗin sayen rago kamar yadda ya buƙata" Cewar Malama Babba. Haka dole Babangida yayi abinda Malam yace musu. Malama Babba taje ta sameshi ta bashi kuɗin. Ta ɓangaren Babangida yamma nayi ya isa majalisarsu nan akaita kacancana zancan masu zugashi ya aureta ya koya mata darasi sunfi masu cewa kada ya aureta yawa. Ya gamsu da ya aureta yai mata wulaƙanci na fitar hayyaci yai mata sakin wulaƙanci. Murmushi mugunta yayi da ya hango irin rashin mutuncin da zaiyi mata. Sai yaji hankalinshi ya kwanta a sauwaƙe zai koyar da'ita darasin rayuwa. Washegari." Malama Babba tai ta jiran Yaya Hanne ba ita tazo ba sai wajajen sha biyun rana. Abunda tazo mata dashhi yafi ƙarfin tunaninta bata taɓa zatin haka ba. "Kinga wannan maganin ? Kina zuba ma Malam a abincinshi wallahi zancan wani aure ya ƙare. A taƙaice duk taurin kanshi sai yadda kika yi dashi Allah" Jikinta da hannunta har rawa suke yi ta amshi maganin. A ranta ta gamsu kota wanne irin haline da dai a auro Sabuwa gara ta kauce hanya. "Amman Yaya Hanne babu abinda zai sameshi ko?" "Babu abinda zai sameshi. Ke dai ki saka mishi maganarnan a kasheta kowa ya huta" Haka ta amsa akan nan da kwana biyu in girkinta ta zago zata zuba mishi."

SABUWA:. Sassafe Malama ƙarama tamun wankan jego, tayi ma jinjira wanka, Rahama kuma ta wanke kayan da muka cire har da nata. Ina daga gado ina cin tuwo Rahama kuma tana waya dasu Rakiya tana sanar dasu halin da ake ciki biki saura kwana talatin da bakwai kenan. "Rakiya inaso kije ki samu Zahira ta gidansu Malam Bala ta haɗo mana magunguna zamu biyata daga baya sabida a tari abun da wuri kunga bamu da lokaci" "To ba zuwan bane matsalar ba. Kuma nasan Zahira zata baku bashi. Waye zai kawo muku gida babu kowa sai Uzairu zuchiyata kuma kun dai san halin wannan kafaffen tsohon." Rahama tace. "Aba Uzairu zuchiyata ya kawo in yazo ƙofar gidan ya ba almajiran gidan zasu kawo nana." "Rakiya tace. "To shikenan zanje yanzu, dan dama gyalena na hannuna inaso zanje dubo Adama ne jikin dai yaƙi ance kishiyoyinta sun rarrafa sun kaita ƙaramin asibiti kuma ga ba kuɗi. Da ƙyar na haɗa dubu biyu su Sadiya suka harhaɗa mun shine zanje. Zan soma zuwa wajen Zahiran tukunna" Da haka sukai sallama. "Lolo kinji jikin Adama yayi tsanani kishiyoyinta nema suka kaita asibiti. Ni dama gida Rakiya ta dawo da'ita duk da gidanma babu daɗi. Inma ta dakkota abinda zata ci shine aiki. Amman wallahi da kashe auren akayi da sai yafi. Kwananta nawa dama a gida tayo yaji da kanta yinwar gidan da rigimar gidan yasa ta kwashi jiki Aisha ta rakata ta koma ɗakinta." Ai da tana jin magana da tuni ta kashe wannan ƙaddararren auren. Allah dai ya bata lafiya. Amman Rahama ni da an bar wani maganin matan. Ni ba auren soyayya ba ba komai ba ina ni ina wani shan magunguna azo a barni da biyan bashi." Rahama tace. "Ai ko ba aure zaki yi ba yadda kika haihunnan yana da kyau kiyi gyara sosai. Ki bar ganin irin auren da zaku yi kenan. Sanda zai lallaɓo ya biyo dare mu muna ina? Su Labbai su Adama da Layuza duk ba irin auren da suka yi ba kenan?" Haka dai mukaita hirarmu muna daga ɗaki. Da yamma sai ga kunun kanwa da naman gashi shaƙe da kwano naci naci har saida na ture. Ina samun kulawa a gaskiya fiye da tunani. Kullum sai naci naman gashi, ga magunguna Rahama sai durkamun take yi harda nasu tsugunno a gaushi duk inayi. Ranar suna aka yanka mun katuwar tinkiyata a soye marau aka kawo mun halamu sun nuna ko tsoka ɗaya basu ɗauka ba. Ni dai nasa Rahama ta raba nama gida biyu aka kira Uzairu zuchiyata yazo ƙofar gida Rahama ta bashi ya kaima Rakiya harda dubu biyar na bashi dan Adama tana gida auren nata ya mutu ga jinya har yanzu bata warke ba."

Malama Babba:. Ta ɓangaren Malama Babba tayi iyakar yinta Malam yaci wannan maganin a ranar da yaci sai batai mishi maganar ba sai washegari ta tareshi da maganar suna kwance. "Malam yanzu wai da gaske kake yi yaronnan Babangida shi zai auri wannan yarinyar ƴar marasa tarbiyya? Ka duba watan yarinyarnan ta shiga na gomaa kenan a gabanmu mahaifinta kawaline kuma maras mutunci yanzu duk girma da darajar wannan gidan namu mai daraja da surukan da yaranmu suka auro daga gidan malumta a rasa wacce za'a gaiyato cikin haular sai Sabuwa?" Tsam yayi yana kallonta. Tunda ta iya tunkararshi da wannan maganar tabbas yasan akwai abinda take saƙawa abinda yaji suna faɗa ta aikata kenan. Sai yayi ƙoƙarin gwadata ta hanyar cewa. "To yaya za'ayi ɗanki ne ai ya jajiɓo mana ita. Sai nake ganin kamar dashi da ita ƙwaryar sama ke dukan ta ƙasa. Ko wacce ƙwarya da abokin burminta, in banda abinki mugu ai shi yasan makwancin mugu, ba'a abota sai hali yazo ɗaya" Yayi shiru tare da kafeta da idanu yana karantarta "Malam bambamcinsu a fili yake. Kai mai mutuncine, malami mai koyar da al'umma. Ka duba makarantarka ɗalibai nawa garemu muna ba mutane karatu harda tarbiiya. Nima Malama ce da taimakonka na zama hakan. Ƙarama ƴar gidan malamai ce. Kaf surukanka daga gidan malumta suka fito. Taya zamu haɗa iri da Sabuwa" Dariya yayo sosai wanda ya daɗe bai yi irinta ba. A baɗini kuma zuchiyarshi ji yake tamkar zata faɗo dan raɗaɗi. Yafi kowa ƙin Sabuwa yafi kowa ƙunsan baƙin ciki da takaici in yaganta, ko yaji muryarta da duk danginta da abinda ma ya shafeta baki ɗaya. Shi ta ɓangarenshi zai aurama Babangida Sabuwa ne sabida ita yarinyar da aka haifa, an riga da an haɗu ko ba'a soba. Dalili na biyu zai aura mishi itane a matsayin horarwa dan yayi imanin Babangida zaifi son ya auro ƴar mutunci, ƴar manyan mutane, ƙila ma ƴar malamai kamar yadda sauran ƴan uwanshi suka yi hakan. Na uku, zaiyi hakanne a matsayin hannunka mai sanda ga sauran yaran gidan. Duk da baya fatan a sake samun Babangida kashi na biyu, amman kashi na farkon ma ai baisan za'a samu ba. Hausawa suka ce gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah. Dalilinshi na huɗu shine ita kanta Sabuwan ai mata adalci a taimaki rayuwarta a tsamota daga cikin duhun da take. Ƙila ta sanadinta ƴan uwanta su shiryu. Domin har ga Allah duk yadda yake ƙin Sabuwa yafi ƙin Babangida fiye da'ita. Ita gaskiya gaskiya ce baya bayan kowa sai bayan adalci. Waɗannan sune manyan dalilinshi. "Yanzu dai mu kwanta da safe ma ƙarashe maganar na gaji, gashi ina da raɗin suna da asuba" Yana faɗin haka ya juya mata baya. Zuchiyarta fes ta kwana amman da asuba kafin ta bar turaka Malam ya kankare mata hadda ta hanyar wasu kalmomi marasa yawa sai firgitarwa da sare guiwa. "Babba ki sake sanar da Babangida batun kuɗaɗennan lokaci nata gabatowa, sannan ya tabbatar a satinnan ya nemi inda zai zauna sabida ayi fenti da komai. Za'aje ayi mata jere ranar talata mai zuwa rana ita yau kenan." Yana gama faɗin haka ya nufi hanyar waje saida ya fita ya girgiza kai yace. "Mata kenan mai ilimi ma kenan ina ga jahila kuma?" Haka dole ƙanwar naƙi Malama Babba ta saduda, ita ta sai da sarƙarta ta danƙama Malam Baba dubu ɗari biyu daya buƙata a wajen Babangida. Shi kuma Babangida ta barshi da neman haya. Harma an samu ciki da falo da bayan gida da kitchen sai dai gidan gidan yawane sosai. A haka aka kama akayi duk gyare_gyaren daya dace kamar yadda Baba malam ya buƙata dai. Ta nashi ɓangaren kuma Malama Ƙarama ya kira ya bata dubu ɗari biyu da hamsin. Da wasu dubu ɗari uku daban. "Ɗari biyu da hamsin ɗin kayan lefe zaki haɗo mun ke da Larai. Wannan ɗari ukun kuma kayan gado da kayan kitchen nake son a sai ma yarinyarnan kina ganin zasu isa ?" Sai da Malama ƙarama tayi murmushi kafin tace. "Na lefen dai ya isa zata samu kaya da yawa. Ammman kaga na kayan ɗakin a gaskiya ba zasu isaba in dai kaya masu kyau za'ayi mata. Sai dai in irin kayannan na bakin kasuwa za'a sai mata" Kai ya girgiza yace. "A_a ayi mata komai mai kyau. Kamar yadda kuke ma yaranku. Yanzu to kawo ɗari ukun ki gani. In yaso duk abinda ake buƙata a rubuta komai da kudinshi da jumulla. Yanzu ku gama na lefen tukunna" Ai kuwa haka akayi a cikin kwana biyu da Malam Baba ya basu suka haɗa akwatuna guda biyu da kit shaƙe da kaya masha Allah. Malama Babba tana zaune tana lissafin yadda ta zama bora a gidan mijinta sai ganin Larai da akwati kici_kici tayi. "Waɗannan akwatunan kuma daga ina Larai"? "Kayan auren Babangida ne Baba malam ne ya bamu kudin muka haɗa" Da mamaki ta kalli Larai ta dubi Wawo dake zaune yana dama ma Baba malam fura. "Kuma sai baki kai ɗakin uwarki ba tunda itace uwar bikin ba?" " Baba malam ne yace a kawo miki" Kafin ta kuma cewa wani abun sai ga Malama Ƙarama ta shigo da sallamarta. Sai da ta nemi waje ta zauna kafin tace. "Babba ga akwatin Babangida nan na haɗo. Toh Malam yace da magriba Wawo da Bashiru su kaimu gidansu Ita Sabuwa mu kai musu akwatin. Sai ki ma Yaya Hanne Magana. Goggo ma tana kan hanya tare zamu je akai." Sai da Malama Babba ta hadiye yawu muƙut kafinnan tace. "Toh shikenan. Allah ya kaimu da rai da lafiya." "Ameen Babba Allah ya albarkaci auren kawai zamu ce" Tana gama faɗin haka ta fice. Malama Babba tace. "Har fishin da Malam yake yi dani yayi irin wannan ƙamarin? Taya zan ƙaunaci wannan yarinyar ai har gaba da abada" MRS BUKHARI " [8/14, 7:22 AM] +234 802 205 9556: IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI LITTAFI NA UKU. SHAFI NA BAKWAI 7

"Ai muma Malam Baba ya tutsiyemu na harhaɗo kan mazan gidan dubu ɗari uku muka haɗa mishi. Babangida ma saida ya bayar. Bai faɗa miki bane?" Kai ta girgiza tace. "Bai sanar dani ba. Damuwar dake damunshi yaushe zai bashi damar sanar mun da wani abun. Yau bamma saka shi a idanuna ba. To me Malam zaiyi da kudi?" "Sai Allah bazai wuce duk akan bikin bane" Haka dai sukaita tattaunawa ta ɗaga waya ta sanarma Yaya Hanne duk abinda ake ciki. Kafin magriba sai ga Goggo ta iso dama dai ƴar ɗakin Malama Babba ce anan take sauka. Ta sauka ko samun damar tattaunawa basui ba. Suna yin sallar isha suka wuce kai kayan lefe.

GIDANSU SABUWA:. Tun yamma Maigogul ya kafa ya tsare a ƙofar gida domin tarbar masu kawo akwati. A cikin gidan kuma Rakiya jallof ɗin shinkafa da kifi tayi ma ƴan kawo akwati sai lemun kwalba da aka siyo guda biyu rak sai ruwa guda biyu shima. Da ƙyar Maigogul ya bayar da dubu uku wai kuɗin salala. Rakiya ta bi kan yaran ɗakinta kafin su fita gantalinsu da ƙyar ta haɗa kudi suka kama dubu biyar. Suna zaune a tsakar gida takwas daidai suka jiyo sallamar mata daga zaure. Maigogul ne ya soma shigowa riƙi _riƙi da akwati a ka su Malama ƙarama na biye dasu. Dama tun magriba Rakiya ta shiga gidansu Ƴar Shuwa ta sanar ma da mahaifiyarta to ta shigo tananan sai matar ƙanin Maigogul itama tananan tazo. "Ku shiga ga ɗakin uwar Lolon nan, kunga ma uwar tata nan.' Ya faɗa yana dariya tare da shigewa da akwatin a kanshi. "Marabanku ku shiga" Rakiya ta faɗa tare da miƙewa tabi bayansu. Goggo sai taɓe bakinta take yi. Bayan an gama gaggaisawa a zatonsu Maigogul kuma zai basu waje ne amman sai Goggo taga zama dam. Ita to bata san waye ba kuma irin matannanne ita masu faɗa da yawa. Sai cewa tai "Hala kaine Babban wan Amaryar dai ko?" Maigogul ya gyara zaman gogul dinshi yace. "Ni ubanta ne nina haifeta. Baiwar Allah kuyi abinda ya kawo ku ina da wajen zuwa dama isowarku nake jira" Baki Goggo ta rike tana mamakin wannan abu. ."Toh kayane ai gasu na Sabuwa. Sai a bubbuɗa a gargani bisa al'ada ko? Duk da banga jama'a masu tarbar masu kawo kaya ba kamar yadda al'ada ta tanadar." Babu dai wanda ya kulata Mama ta miƙe ta bubbuɗe akwatin ta shiga ɗaɗɗaga kayayyakin ana gani harda Maigogul a ɗadɗaga kayayyakin bacci da aka zuba haɗe da kayan kwalliya." "Tabarakallah kaya sunyi an gode. Maigogul sai ka fita ko zasu ci abinci" Mikewa yayi tare da bibbige malum_malum dinshi a kansu, su dai mamaki ya ishesu. "To ni kam na tafi. Rakiya bikine damu ni kam sai jibi ma zaku ganni. Baƙi munga kaya Sabuwa tayi goshi ba'a taɓa wata yarinya rabin abinda akaima lolo ba, lallai da sa'armu muke tafe kafaɗa da kafaɗa" Ya saka kai ya fice yana dariya. Goggo tace. "To Malama ƙarama inaga ai sai mu tafi ko?" Umma tace "Abincin fa?" "Zamu tafi dashi kar muyi dare" Cewar Goggo tayi hakanne danta kuresu domin a kallo ɗaya da taina gidan ta gane suna cikin talauci" Ai kuwa kwanon da suka gani na abincin ya tabbatar da zarginta. Har gaban mota Mama da Tani suka rakasu suka danƙa dubu Biyar ɗinnan a hannun Malama Ƙarama dan sunga tafi Goggo sauƙi."

Gidan Malam:. Ai fa suna dawowa aka buɗe sabon faifayin surutu abinka da mata. Wannan kuɗin salala da wannan abinci akaita maganar a tsakar gida har dai yaje kunnen Baba malam sai da ya tsawatar. Washegari Malama Ƙarama da Larai suka wuce kasuwa cikin kwana biyu suka gama siyan komai aka jibge a gidan Kawu Manga . Baba malam da kanshi yasa aka je aka sanarma da su Rakiya ranar da zasu zo a debi kaya aje jere.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull