Idan kaya ya gaji book 3 - Chapter 7
Idan kaya ya gaji book 3 Chapter 7: Idan kaya ya gaji book 3 Chapter 7. SABUWA:. Gaga gaga abubbuwa sukaita faruwa, ni dai hankalina kwance daga ni har…
3,235 words
SABUWA:. Gaga gaga abubbuwa sukaita faruwa, ni dai hankalina kwance daga ni har Rahama mun yi ƙiba sabida cin daɗi, haka ma jajiriyata tayi kiba duk wanda ya ganta sai ta bashi sha'awa. Saura kwana ɗaya in yi alba'in wanda yayi daidai da gobe ɗaurin aurena. Ni da kaina da safe naje na samu Malam a waje cikin almajirai. Yana ganina ya girgiza kanshi ya taso ya same ni a zaure. "Lafiya Sabuwa me kuke da bukata?" Babu kunya dan a lokacin bamma santa ba nace. "Kitso da ƙunshi nake son ayi mun. To ina da me kitso kar tazo a hanata shigowa" Hannu yasa ya rufe baki da dukkan halamu maganar ta matuƙar bashi kunya. Da ƙyar yace. "Jeki zan turo Ƙarama" Na wucewata ina mamakin dalilin da yasa ya buɗe baki. Na koma ciki Rahama tace. "Ya ake ciki me yace miki?" Uhm wai in dawo zai aiko kishiyar babar su Babangida " Bamma rufe baki ba sai gata ta shigo. "Ke Sabuwa ƙunshi da kitsonne ba zaki iya faɗa mana ba sai Malam kika tsallake mata a tsakar gida kika sameshi shi. Dake ku a gidanku babu manya. Uban naki ma bai kama kanshi ba bare ku. To kul a gidannan mu ba'a haka. Duk abinda kike buƙata ki sanar mun ni zan isar miki wajen Malam ɗin dan ba sa'anki bane. Ƙunshi da lallai kuma zan turo Yahanasu tayi miki maras kunya" Ahh to naga ai zamanshi nake yi" Na faɗa ina ƙunkunni. "Au zaman Malam ɗin kike yi?" "E mana to da zamanki take yi? Ku dai gidannan akwaiku da tsurfa kaiii kuna da zuzuta ƙaramar magana ta zama babba. Wai dama haka malaman suke ne?" Rahama ta faɗa tare da juya kai tamkar ba ita tayi maganar ba. Haka dai Malama ƙarama ta fice. Ba'afi awa biyu ba mai kotso tazo. Mune har bayan isha muna abu ɗaya. Kitso dai sai da akayi guda ɗari da hamsin. Ƙunshi kuma salateb aka jeramun suffa. Sai takwas na dare aka gama. Washegari na fito fes dani. Tun asuba muke ta harhaɗa kaya ni da Rahama, muna kan tattare kayan Malama ƙarama tayo sallama ta shigo hannunta riƙe da baƙar leda cike dam da alawa da goro na ɗaurin aure. "Gashi ke goron ɗaurin auren ne. Malam kuma yace ku shirya bayan la'asar za'a kai ki." Wani sanyi naji a raina jin wannan aure ya ɗauru. Murmushi nayi dana tuno rantse_rantsen da Babangida ya dinga mun akan bazai aureni ba. Rashin sani yafi dare duhu ashe daga ranar da zan tare a matsayin mata a gidan Babangida da ranar matsalata ta buɗe sabon shafi mai wuyar biyawa. Yamma nayi akace mu futo ba ai taro ko ɗis ba asalima ko yaran gidan basu zo ba. Mardiyya na bayan Rahama ta goyata muka fito tsakar gida da kayayyakinmu. Malama ƙarama, da Goggo, sai Larai sai kuma ni da Rahama aka ɗauke mu a mota zuwa gaba can da unguwarmu. Gidan gidane mai cike da jama'a. Da sallama muka shiga sunata hada _hada a tsakar gida, yaran gidan sunata tsalle tsallensu akwai yalwar tsakar gida sosai a gidan. "Sannunku fa da aiki matan gida. Ga abokiyar zama kun sake samu" Cewar Larai kenan. "Ayya sannunku da zuwa. Ai mu da muka ga irin dukiyar da aka zuba da gyaran da akayi mun zaci amaryace munga idanta a bude tangararan" Cewar wata zabiya uwar rawar kai ta ci wani pink din janbaki baki sai kace babanin akuya. Goggo tayi dariya tace "Ba Amarya bace ga ƴarta a baya ma. Allah dai ya baku zaman lafiya" Suka amsa da ameen . Ni dai ina tsaye a gefe. Malama ƙarama ce tai mana jagora zuwa ɗakina. Lallai Baba Malam ya zuba mun dukiya ko diyarshi ce ni iyakar gatan da zai yi mun kenan. Goggo dai saida ta lalleƙa ko'ina tana girgiza kai. "Ƙarama tashi mu tafi kinji." Tashi suka yi suka fita babu wanda suka kula, muma bamu ce dasu uffan ba. "Ke Lolo yanzu duka wannan aljannar duniyar wai naki ne? Uhm cikin shege yayi miki rana, mu ne dai muka hadu da jar masifa Adama dai Allah ya yanke mata wahala." Tashi nayi na cire mayafina harda ɗankwalina muka shiga kitchen ga kayayyakinan a jejjere, wasu ma suna kwalinsu, ga gara tubarkallah Baba Malam yayi mun. Muka tafi ɗakin gado shima yayi kyau, ko ina kefet ne mai laushi. Zama nayi a bakin gadon nayi shiru haka suddan kuma sai nake jin faɗuwar gaba mai tsanani. Har Rahama ta gama jera kayana dana Mardiyya ban ko motsa daga inda nake ba" "Lolo kinji magriba ake kira bari kiga in yi Sallah sai in kama hanyar gida kuma" Kallonta nayi tana shimfide Mardiyya a kan gado.. Gidanki zaki koma?" "Wa? Can gida zanje gobe zamu zo muyi namu bikin ai, kuma a gyara miki wajen da kyau" Tana bayan gida aka aiko yara biyu ko wanne da kwano a hannunshi na abinci. Toh kuce musu an gode ko?" Na amshi kwanukan da fara'a na ajjiye akan teburin tsakiyar falon. Na koma ciki ina ƙara ƙarema ɗakin kallo. Rahama ta shigo daga banɗaki ta sameni a tsaye ina riƙe da labule ina duba kyansu. "Uhm Lolo anyi ɗakin kai. Kinsan Allah ke kam haɗuwarki da Babangida alkhairi ne. Jibi waje Lolo komai mai tsada.. kab cikinmu babu ma wacce ta taɓa samun arzikin irin gidan hayarnan da aka kama miki. Dan wallahi da gani tsada zaiyi in kika duba yanayin tsarin ginin. Kitchen ɗinki jibi shaƙe da kayan arziki ga su kayan kallo a falo." Dariya kawai nayi mata na shiga banɗakin ita kuma ta tada Sallah. Na fito na sameta a tsaye ta gama shiryawa tsab. Rahama nace ko zaki farke katan din taliyar dake kitchen ki tafi muku da ko uku ce kwa karya dashi?" "Sosai ma muje to in buɗe kinga har su maggi da mai na ɗiba. Ai kuwa hakan akayidan mangyaɗa ma da muka rasa a ina za'a zuba Rahama ta buɗe ruwan gora na swan ta kwankwaɗeshi tas muka cika da mangyaɗa. Abincin da matan gidan suka kawo ma a leda na juye mata nace ta kaima Rakiya. Mardiyya na goya na ɗauki jakata na kalle ɗakin na rakata har bakin titi saida ta samu abun hawa kana na dawo. A hanyata ta dawowa na tsaya na sai biredi da ƙwai a shago da taliyar ƴan yara dan ba ƙaramar yinwa nake ji ba." Babu kowa a tsakar gidan sanda na shigo ko wacce tana ɗakinta da iyalanta. Nima ina shiga na rufo ƙofata na kwantar da Mardiyya a kujera na shiga kitchen ɗin na kunna gas na ɗaura ruwan zafi. Sannan na fito na yi Sallah a falo. Taliyar ƴan yars na dafa da kwai sai tea mai kauri dana haɗa dama muna da kayan tea da mika tawo dashi a kaya. Nayi ƙat na shiga da kwanukan kitchen na wankesu na mayar dasu inda na ɗauka Ƴata na ɗauka muka shiga ciki muka hau shirin bacci. Kaya masu sauƙi obarol na saka ma Mardiyya ni kuma wata doguwar riga mai sauƙi na saka wacce nake bacci da'ita tunda na koma gidansu Babangida. Na kashe hasken ɗakin nayi baccina raina ɗaya Wani irin bacci nayi wanda ban taɓa yin irinshi ba. Bani na farka ba sai bakwai na safe shima sabida bugun da aketa ma ƙofatane yasa na bude idona a hankali gari tangararan. "Lolo kizo ki buɗe mana ƙofa" Na jiyo muryar Maigogul ta windon uwarɗakin nawa. Da sauri na duro na zo na buɗe musu. Dukka ƴan gidanmu ne suka zo harda ƴan ɗakin Hauwa. A mazan dai daga Uzairu zuchiyata sai Ma'aru ne suka zo. Daman sune basu fiye yawo ba a gidanmu bar Uzairu zuchiyata dai da yaudarar mata, shi kuma Ma'aru ɗan yankan ajjihune ranar cin kasuwannin ƙauye yafi fita. "Kai kai kai Lolo haka Allah ya kashe ya baki, irin wannan kaɓakin arziki haka? Masha ALLAH " Cewar Maigogul dake tsaye yana karema ko'ina kallo su Adama kuma duk sun zazzauna wasu a kujera wasu a kasan kafet. "Ai kasan itafa Lolo tun tasowarta ta zama daban komanta ya bambamta dana ƴan uwanta" Cewar Rakiya tana yi tana kallon Hauwa. Dariya Hauwa tayi tace. "Gaskiya mana ta haifi ƴar shege, kuma taje ta haihu a gidansu Baban shegen kinga ai ita kaɗaice hakan ya faru a kanta" Nan cacar baki da habaice_habaice ya soma. Ni kam suna cikin mayar da zance nayi komawata ciki su Adama suka biyoni dukkansu. Zuwanku ne ya tasheni ma a bacci. Bari in yi Sallah sai mu shiga kitchen. Adama ashe haka abu ya faru?" "Ke dai je kiyi Sallar tukunna dai akwai labarai ai" Cewar ƴar Shuwa kenan wacce ta ɗauki Mardiyya tana taɓa mata kumatu. Ina cikin Sallah, su Adama sunyi baje _baje wasu a gado wasu a ƙasa Adama babu ko riga a jikinta daga ita sai bireziya da dogon wando hijabi ta ziro kawai. Ina cikin sallah Sai kawai Babangida ya ɗaga labulen uwar ɗakin. Daidai nayi sallama muka haɗa idanu dashi. Wani irin wulaƙantaccen kallo ya watso mana na raini. Yayi tsaye riƙe da labule shi bai shigo ba, shi bai koma ba. Su Adama duk suka miƙe tsaye suna neman hanya. Ina jiyo Maigogul yana gaishe da Babangida amman bai ko yi gezau ba. Ai saika basu waje su wuce ko?" Na faɗa cike da tsiwa. Shigowa yayi yana muzurai su kuma suka fice ɗaya bayan ɗaya. Mardiyya na kafaɗar Sadiya. Zama yayi yana ƙarema ɗakin dani kallo. Miƙewa nayi na ninke sallayata na cire hijabina ina shirin ficewa a ɗakin naji yace. "Ke Sabuwa" Juyowa nayi ina kallonshi. "Me mutanen gidanku suke yi a gidana haka cikin falo? Ohhh nagane" Sai naga ya miƙe ya iso har inda nake yana wani zazzare idanu. Daf dani ya tsaya har ina shaƙon kamshin jikinshi wanda yake cakuɗe da warin hayaƙin sigari. "Sun zo ne a cinye garar da ubana ya hadoki dashi ba. Ai kab ƴan uwanki babu wacce ta samu gida irin wannan. Shine akazo za'aci banza harda tsohon najadun ubanki" Maganar ta dira a zuchiyata sosai Wallahi duk lalacewar iyayena da ƴan uwana ina son kayana, kuma ina jin zafin a zagesu. Murmushi nayi nace. Ai ko sunci bakai ka siya ba. Da kake kiran ubana tsohon najadu, naka uban ko bai zama tsohon najaduba ya haifi ɗan duniya hayaƙin..." Marin bakina yayi bub yana zare idanu. "Ke ni zaki zaga dan iyayenki? Ko da yake babu tarbiyyar bin miji a tattare da sha'anin gidanku. Uwar da uban sa'insa suke yi ko shigowata. Amman ki sani zan koya miki hankali kuma wallahi sai na gigita duniyarki. Na tsanake ke da yarinyar da kuka haifa kike ikirarin tawace. Kuma na lashi takobin sai da kanki kun yi nadamar aurena kin kuma nemi hanyar rabuwa danni kije ki sallamesu kizo ki sauke nauyin da Allah ya ɗaura miki" Narantse da Allah sai dai mu gigita duniyar juna. Babangida bari kaji in faɗa maka nima fa ba sonka nake yi ba kaddararmu ce kawai a haɗe. Kaga ai ko babu komai ka samu ribar bariki kuma ko na fita a rayuwarka har gaba da abada ba zaka manta ni ba" Tsaki naja nayi ficewata na barshi yana ta kwaɗa mun kira da ƙarfinshi na gaske. "Ke Lolo ba kina ji mijinki na kiranki ba?" Cewar Maigogul daya biyo mu kitchen. Ƙyaleshi Maigogul rigima yake ji ina daidai dashi ni kuma." "A_a Lolo yanzu dai duk tsiyar Babangida mijinki ne kije kiji menene" "Rabu da'ita ai dama ƴar balaja'u ce yaushe zata iya biyayyar Aure ko da yake bata da laifi kai ka koyar da'ita" Babangida ne fa ya rike labule ya dubu tsabar idan Maigogul yake faɗa mishi hakan. Shi ko wallahi ko gezau sai ma wannan dariyar mai sani baƙin ciki ita yayi. Uzairu zuchiyata ne yace. "Ai ko mutuwa tana jin kunyar mahaifa ka duba taronmu nan duk ƴaƴanshi ne amman ji irin furucin da kake furtawa" Harara Babangida ya zabgama Uzairu zuchiyata yace. "Kai kuma mai zubin ƴan daudu ba dakai nake yi ba. Cin abinci ne dai ya kawo ku da sassafennan sabida dama tun asali maiƙon gidanmu da darajar gidan namu kuke bi. In ba haka ba meye naku na zuwa da safe haka kusan ku ashirun wannan rashin kaine fa" Tsaki yaja ya koma ciki a hakanma bai isheshi ba yaci gaba da maganganu yana ta yaɓo musu. Su dai kowa yayi shiru Hauwa kuwa sai cewa tayi. "Uhm ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta. Dama shi bariki iyakar ribarta kenan" Rakiya ta dubeta tare da ƙanƙance idanu. "Me kike nufi da iyakar ribar bariki kenan?" Maigogul dake ƙofar kitchen yace. "Toh zaku ci gaba da raba hali a gidan yarinya salan mijinta ya sake fitowa yayi mana tijara ko?" Yana gama faɗa haka yace. "Adama ku ƙara sanwar naga taliya huɗu kuka ciro yaushe zata ishemu fisabilillahi?" "Zamu ƙara da makaroni leda ɗaya Maigogul. Kaga kaje ka zauna bai kamata fa kana cikin kitchen ɗinnan ba gaskiya. Kana jin wancan maras mutuncin abinda yake cewa." Labbai bata gama Magana ba muka jiyo Hauwa na cewa. "Abinda nake nufi ai kin sanshi. Ke da kikai aure a barikin baga mijin naki ba har gobe kuna cukume_cukume ba? To ga kuma ƴarki mijinta ya leko yana gargasa mana Magana." Kafin Adama ta fito Maigogul ya tsallako kitchen ɗin ya kama taliya yana bude mana. "Hauwa dan ALLAH bama son neman fitina ku daure in kuka koma gida sai ku ɗaura daga inda kuka tsaya." "A_a fa ya za'ai ta faɗa mata magana irin haka?" Cewar Labiban Hauwa. Adama tace. "Na ci ubanki wallahi in haɗaki da bango in shaƙeki. Ji yarinya figigiya da'ita wai ni zataina rashin mutunci." Da ƙyar dai fitina a falon ta lafa sakamakon kallo da na fito na saka musu. Uwar ɗaki na koma inaso zan dakko kuɗi in ba su labbai a samo kayan miya ko da da kifin gongonine muyi girkin dashi Babangida yana banɗaki dan ina jin saukar ruwa daga cikin banɗakin. Jakata na dauka na fita. Dubu biyu na ba Labbai da Sadiya. Basu daɗe ba sai gasu da kayan miya harda kifi ɗanye. "Lolo ai a gidannan naku ana saida kifi ashe kala kala kin gansu manya. Kayan miyanma gida biyu ne tsakaninku mai kifin ce ta kwatanta mana muka siyo. Maigogul yasa hannu ya karɓi ledar kifin yana dubawa. "Babu laifi yayi kyau. Kinga kin huta gya dinga siye. Uhm Aisha matsa kiga in yanka muku kifin sai in soya muku." Matsa mishi Aisha tayi ya karasa inda wajen wanke_wanken yake ya soma yanka mana kifin. Mu kuma muna ta hira. Duk da zuchiyata a cunkushe da maganganun da Babangida ya zubo ma su Rakiya take. Hakan bai hana mu wasa da dariya ba. Babangida ne ya leƙo kitchen ɗin ko me zaiyi oho. Ganun Maigogul a bakin famfo yana wanke kifi yasa ya buɗe bakinshi galala yana kallonshi Shi kuwa Maigogul sai ya hau dariya. "Uhm kifine nake yanka musu ba iyawa zasu yi ba baka jiba da ƙanƙara sosai wai nace inna soya musu ai na taimaka musu. Kasan lokacin suna yara wallahi ni nake yin girkin gidana safe rana dare, sai dai ranar da bananan sai iyayensu suyi. Kasan nayi girki a hotel gashi na iya haka siddan akaimun maƙarƙashiya aka koreni ina kan ganiyata" Tsaki Babangida yayi yace. "Ni Babangida na shiga ukuna wannan wacce iriyar ƙaddarace ke bibiyata haka?" Aikin banza aikin wofi" Na faɗa da tsiwa tare da hararar Babangida na ja dogon tsaki. Ta gefenshi Maigogul yake so ya raɓe ya fita. Ni ko dan in ƙara baƙanta ma Babangida sai cewa nayi. Dama kayi mana miyar kifin Maigogul yaushe rabon muci girkin da kayi mai daɗinnan" Yana jin haka ya washe bakinshi yana farin ciki. Sai naji tausayinshi ya kamani. Babangida na tsaye na kunna ma Maigogul ɗayan gas ɗin. "Miƙo abun tuya da mangyaɗa. Lallai yau zaku ci miya ƴar kwatano takumbo kenan" Babu shiri Babangida ya koma ciki fu. Da harara na bishi, su Adama kuwa sai ƙunshe dariyarsu suke yi. Haka muka gama dafa farar taliya da makanoni sai miyar jajjage wacce ta wadatu da kifi. Maigogul da kanshi ya rarraba mana shima ya zuba nashi, Uzairu zuchiyata ya dinga rarraba musu. "Lolo wannan ki kaima mijinki" Ya miƙo mun abincin a plate. A_a yadda yake ciki da rashin mutuncinnan nasan ko na bashi ba ci zai ba. Ku dai kuci ku ƙoshi kawai" "A_a Lolo ke dai kai mishi koma baici ba kin bashi. Kinga irin wannan daular da Allah ya huwace miki samunta? Kada ki sake Babangida ya sake ki duk wuya duk rintsi. Kai mishi dai ki zo kuci abinci da ƴan uwanki" Karɓa nayi na shiga uwar ɗakin. Yana kwance yana waya da mace dan naji ya ambaci baby. Baki na taɓe tare da ajjiye mai abincin a durowar gefen gado ina ƙoƙarin wucewa ya riƙo hannuna. Da sauri na juyo ya wani kashe mun idanu. "A_a Baby zamu haɗu da yamma. Yanzu ina gidane inaso nayi bacci. Amman baccin ma ya gagara jama'a ce cike da gidan nawa ma" Tsaki nayi tare da fusge hannuna ina shirin fita yayi saurin kashe wayar ya cabkeni ya jefa a gado yana nunani. "Wai dame kike taƙama ne. Ni kike ma tsaki dan uwarki?" Ba dai uwata ba kasan uwar da kake zagi dai" Ina faɗan haka ya duro a kaina. Muka shiga dambe da gaske. Da ƙyar na kwace kaina na fito. Muna gama cin abinci ba'a daɗe ba su Maigogul da su Rakiya, da su Ma'aru sukai mana sallama. Kafin su tafi saida maigogul yayi mun miyar sutu mai daɗin gaske taji soyayyen kifi. su Adama kuma muna gama hutawa. Adama taima Mardiyya wanka na shiga na ɗakko mata kaya lokacin Babangida yana bacci. Wankan nima nayi na saka atampata daga cikin kayana da suka kawo mun daga gida. Duk da ƴar Shuwa ta kwashe rabi da kwatan kayanma. wanke_wanke da gyaran kitchen da bubbuɗe wasu kayayyakin da ba'a buɗe ba muka soma. Muna ajjiye komai a muhallinshi bamu muka kammal ba sai azahar. Lokacin Sallah nayi Babangida ya fice. Allah ya taimakeni bai dawo gidan ba. Abincin dana kai mishi kuwa ko taɓawa bai yi ba. Ƙwafa nayi na ɗauki plate ɗin nakai na rufe abincin a kitchen. Labbai na kitchen ɗin tana mana jallof mai kifi ƙamshi duk ya kaure ko'ina kunsan kifi da ƙamshi. A taƙaice dai sai magriba su Labbai suka bar gidana. Na ɗibar musu abinci mai yawa musamman ma Rahama. Babangida bai tashi dawowa ba sai wajen biyun dare yazo yana buga mun ƙofa. Cikin bacci na jiyoshi haka nazo na buɗe mishi. Nayi komawata gado na kwanta. Shi kuma yana tsaye yana jera kayan sawarshi daya tawo dasu cikin jaka. Gaga_gaga haka rayuwar taci gaba da garawa. Babu daɗi sam zaman gidan Babangida. Dan bamu da aiki sai faɗa, har dukana yake yi duk da nima bawai barinshi nake yi ba. Matan gida bamu daɗe ba suka gane Babangida maras kirki ne ta ɓangaren iyalinshi. Mu'amalarshi mai kyau da mutanene da kuma sakin fuskarshi, ga yawan larabci da kawo hujjoji da hadisai yasa ake ganin kamar nice marar kirki ba shi ɗin bane. MRS BUKHARI [8/14, 7:22 AM] +234 802 205 9556: IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA UKU SHAFI NA TAKWAS 8 BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI.