Idan kaya ya gaji book 3 - Chapter 8
Idan kaya ya gaji book 3 Chapter 8: Idan kaya ya gaji book 3 Chapter 8. To kunsan sha'anin gidan haya musamman gidan yawa. Sai ya zamana ko a hira sai kuji…
3,752 words
To kunsan sha'anin gidan haya musamman gidan yawa. Sai ya zamana ko a hira sai kuji suna faɗa mun magana. Ni kuma a lokacin ba kanwar lasa bace ya zamana bana shiri da kowa a cikin gidan sai mace ɗaya Maman Hidaya itama tsohuwar ƙauriyace shi yasa tamu ma tazo guda. Haka dai al'amura suka ci gaba da tafiya. Watana huɗu a gidan Babangida babu abinda ya taɓa shiga tsakaninmu na mu'amular aure. Kuma ya dena kwana a waje sai dai fa sai dare ya raba yake shigowa cikin gidan yaita buga mun ƙofa matan gida na jinmu kullum. Wani sa'inma daya shigo zamu kaure da rikicin da zai iya kaimu har asuba muna abu ɗaya. Dan wallahi in rikicina ya tashi da kaina nake rarumarshi da damben, ko in fasa mishi wayarshi da zaran wata ƴar bajala'u ta kirashi. Daya ga haka washe garin dana fasa wayar da mace ya kwanta a gadona ya jefoni falo a ƙasa na kwana ina kukan baƙin ciki. Mardiyya kuwa bai taɓa ɗaukar yarinyarnan ba kwata_kwata ko kuka take yi a kusa dashi baya ɗaukarta baya kuma rarrashinta sai dai yaita kallonta kawai. A wata biyar ɗinnan sau biyu naje gida, shima da ƙyar Babangida ya barni. Saida na sauka a ƙofar layinmu na gane ashe Babangida na biye dani a machine. Bai gushe ba har saida yaga na shige gidanmu tukunna. Yau dai tun sassafe nake ta aikace_aikace sabida gobe akwai biki a gida na Adama da Ƴar Shuwa kuma duk a gida za'ayi anko ma iri ɗaya muka yi .Ankon da sai da Baba malam ya saka baki kafin Babangida ya yarda yayi mun. Kuma ya saka shi ya bani kudin gudunmawa. Ina zaune Malama Babba ta korani a waya ta zage ni tas ta inda ta tsikara ba tanan take jawowa ba duk akan kuɗin ankon da akasa Babangida ya bani ne kuma. Tana tsaka da maganarta ma na kashe wayata a hakanma nayi mata da ƙauna tunda dai ban faɗa mata magana ba. Da daddare ina kwance a kan kujera ina kallo. Mardiyya kuma tana ɗan wasanta a ƙasa ta rarrafa can in kamota ta sake komawa. Tunda dai ta soma rarrafe da mikewa tsaye kullum bata da aiki sai rigima da fasa mun abubuwa. Na tashi zan kamota a gaban tv Babangida yayo sallama ya shigo. Juyowar da zanyi naga ni yaketa kallo idanunshi cike da ruwan sha'awa. Dogon baƙin wandone a jikina sai farar top da na saka matsattsiya kaina babu ɗankwali sai sabon kitson da wata mai kitso tazo ta yarfamun shuku da na gaba. Ga ƙunshi nayi dai haka. Haɗe rai nayi na dawo na zauna. Kujera ya samu ya zauna "Sabuwa babu ko sannu da zuwa"" Rijalu kenan in suna son abu sun iya kwantar da kansu. Ai Rakiya bata koya mun ba ka tuna?" Nayi maganar idona na kan tv. Murmushi yayi wanda in ba dan yana buƙata ba sai dai mu hau sama mu duro. "Toh a kawo mun abincina ko shima Rakiyan bata koyar dake yadda ake ba miji abinci ba?" Banza nayi mishi na nuna mai abincin akan tebur na ajjiye mishi komai da komai. Hatta akan abinci saida Baba Malam ya kirani yayi mun faɗa kafin na soma yin girki dashi. Ko da gara ta ƙare babu laifi ya siyo abinci ya jibge har nama da kifi da kayan miya masu yawa ya siyo na adanasu a gidan ƙanƙara. Sai dai fa baya bani ko asi komai dai ya siyo ya ajjiye, ko kitso nake son na sabumta dole saina tambayeshi. A nanne yake yin yadda yaso kafin ya bani. Ko zai bani kai da kai yake bani, koma ya bani bai isa ba. Ɗaukar Ƴata nayi a ƙasa harta soma bacci muka shiga ciki. Dan saƙon da Babangida yake miƙo mun ya soma tasiri a jikina. Nima dauriya kawai nake yi. Ina shiga ciki na shinfiɗe Mardiyya da baccinta yayi nisa a gefe. Ina da burin siyan gadon yara amman ina bani da kuɗin haka dole na haƙura. Shirin bacci nayi na yi kwanciyata na ba ƙofa baya. Can Babangida ya shigo shima ya gama abinda zaiyi ya kwanta. Sai da dare ya kusan rabawa naji yana lalubena. Hannunshi na ture tare da juyowa cikin tsiwa nace. Meye wannan kuma kake yi.?" "Halalina nake nema wasu ƴan iska ma aka basu balle ni da aka ƙaƙabamun ke ƙaddara mai munin gaske" Ai ku ake rabama ƴaƴan iska sai ƴan iska irinku" Ina faɗan haka ya ruƙunkumeni dambe sosai ya kaure a tsakaninmu duk na yakusheshi, shi kuma yai mun wulakancin da wallahi da safe da ƙyar na shiga cikin ruwan zafi. Kafin na samu salama. Ina zargin maganin ƙarfin maza ya afa duk da dai dama a wannan fagen bashi da tamka a cikin mazajen da nayi mu'amala dasu. Haka raina a jagule na isa gidanmu aka shiga hidimar biki. Kwanana hudu a jere ina sunturin zuwa gida dan Babangida yaƙi fur in je gida in an gama bikin in dawo. Ƴar Shuwa dai Allah yasa nan Dutse suka soma zama mijin nata ya samu aiki a jigawa sai ya tattago matarshi ya siya musu ƙaramin gida can muka kaita dai. Muna gama bikinsu ƴar Shuwa kuma aka shiga bikin gidansu Babangida za'ayi bikin mutum biyar Alawiyya da Sauwama sai maza uku biyu ƴan dakin Malama ƙarama ɗaya ɗan ɗakin su Babangida. Daga lokacin na soma sanin ashe ma gidan babu wani haɗin kai na azo a gani. Dan dai suna da ilimine shi yasa suke yin abun na hankali. Biki dai rana ɗaya akeyi amman ko wanne ɓangare da ankonsu, abinci ma bambamcewa akayi. Surukan gidan kuwa sai lokacinne nasan adadinsu da kalarsu. Sai dai fa ko wacce wani irin kallon gani_ gani take yi mun. Duk inda na gilma ni da Sadiya dake riƙe da Mardiyya sai inga ana zunɗena. Ƙanne da yayyen Malama Babba kuwa sai da suka ci mun mutuncin da duk taurin raina saida na zubar da hawaye. Nima na farfaɗi maganganun da ya jawo rikicin da Malam Baba yace in koma gidana washegari buɗar kai bama sai nazo ba. Gaga gaga Wata na takwas da aure Babangida yayo aure wata ranar juma'a. Ina kwance naga ya shigo da magriba abunda bai taɓa yi ba kenan. Saye ya shigo da farar malum_malum sai ƙamshi yake zubawa. Ban isheshi kallo ba naga ya ɗebi kayanshi a jaka ya jejjera ya kwashe turarukanshi daya jera a gaban mudubi. "Kizo ki kulle ɗakinki ni yau aka ɗaura mun aure da budurwa tiya leda ba irinki tokumbo ba. Gangariya ba irinki oshele ba. Yarinya ƴar gidan malamai ba irinki ƴar gidan kawalai ba. Dan haka ni na tafi saina gama dandalar romo tas." Ficewa yayi. Sabida tsabar zafin kalmominshi, da kishin da banyi tunanin zanyi akanshi ba yasa idanuna suka rufe. Ganin zai fita ya barni da cizon yatsan ban mayar mishi da martaniba yasa na duro a guje naje na sha gabanshi. Ai wallahi baka isa ka faɗa bam mayar maka ba" Dariya yayi tare da buɗe baki zai yi magana nayi wuf na rigashi. "Da kake kirana tokumbo. Ai ire irenku suna numfashi a doron ƙasa ba za'a taɓa dena samun mata tokumbo ba. In kuma juninka neman matan banza ne da sannu zaka tadda wacce zata zama ajalinka. Aure da kayi ko a jikina. In sha ALLAH ba zaka taɓa samunta yadda kake tsammani ba. Murhu sai tukunya ɗan banza sai ƴar banza. Ina gama faɗin haka na koma ciki da sauri na kulle ƙofar uwarɗakin na shiga aikin zurga zurga. Wallahi kishi masifa ne mata. Kar kuyi mamaki dan nayi kishin Babangida. Har ga Allah ai ina sonshi sosai kuma dai kun sani Kuma ko auren dole aka ma mace da mijinta ranar da zai kawo mata batun ƙarin aure dole sai taji babu daɗi a ranta. Nasan masu kishiyane zasu biya wannan karatun. Marasa kishiya sai dai suce Sabuwa tayi asara ko menene na kishin Babangida oho. A wannan daren sabida tsabaragen masifa ji nayi kamar in ƙona kaina in huta. A ranar na gane dare da tsawo yake. Washegari sassafe ina gama aiyukana na wuce gidan ƴar Shuwa takwas a ƙofar gidanta tayi mun. Dama munyi waya da'ita a daren jiya ta sanar dani miji ba'a ɗakinta yake ba. Kuma itama tana cikin matsala babba. Ina ƙwanƙwasa ƙofarta kishiyarta ta wani leƙo tana cewa. "Waye haka sassafe dan rashin hankali. Mai gidanma ba za'a barshi yayi bacci ba" Tana leƙowa muka haɗa idanu irin kallon dana watso mata ya tsoratata sosai. Tana dai tsaye har Ƴar Shuwa ta buɗe mun ƙofa. "Aisha baƙuwa da sassafe haka kika yi. Kamar Sabuwa ƙawarki ko?" Kuji gulma wato dai kishiyoyi akwai gulma wallahi ɗaiɗaikune masu iya ɗauke kansu ga sha'anin kishiya. "E wallahi ai Sabuwa zata iya kawo mun ziyara a duk sanda naga dama sabida ƴar uwatace" Hannuna ta figa muka shige ciki. A kujerarta na zauna. Ita kuma ta shiga ɗan kitchen dinta da kamar karin kumallo take haɗawa. Jinta shiru yasa na shiga kitchen ɗin na sameta a gaban doyar da take soyawa a zaune ta gasa tagumi tayi shiru. Bata san na shigo ba har saida na dafata tukunna ta juyo da sauri. Ƙurama juna idanu muka yi dukkanmu muna cike da damuwa. Doyar zata ƙone ki kwashe tukunna sai mu nutsu muma juna bayanin matsalalolinmu. Doyar tayi maza ta kwashe ta toya mana ƙwai guda biyu da ruwan tea. Muna kan karyawa take zayyyanu mun irin matsalolin da ta soma fuskanta daga kishiyarta na makirci da haɗata faɗa da miji duk ran kwananta. "Kinga jiya a ɗakina yake wallahi har tsirara nayi a gabanshi amman ko gezau da kika sani. Duk wata hanyar maɗe da hilatar ɗa namiji kinsan na iya Sabuwa ni gangarance a wannan babin. Amman ace kayi aure miji kuma ya ɗaukeka da kai da banza baku da maraba. Shikenan duk soyayyar dana iya a bariki zata ƙare kenan. Duk yadda nake tafiya da imanin maza ace nawa mijin na kasa tafiyar dashi. Shikenan tarairaya da nuna kulawa an barma mazan bariki kenan? Kai na jinjina ina taɓe bakina. Ni duk wani iskancin Babangida wallahi baima taɓa damuna ba wallahi. Nifa jiyane kaɗai Babangida ma ɓirɓishin sonshi da kishinshi suka tashi mun da yace yayi aurennan. Tunda haka yake miki ki share shi kawai kiyi harkokin gabanki. Tunda naga matar tashi in jeraku za'ayi ko sisi babu mai siyanta." Dafa mun cinya tayi tace. "Sassauta murya dan kamar tana laɓe wallahi. To ai inna barta ta samu galaba a kaina kenan. Ni haihuwa nake son nayi tunda ita kanta albarkacin yaran take ci. Kuma dasu take yi mun gadara. Akan ƴarta ta goye fa sai ya sauka a kaina muna mu'amalar aure ya tafi sabida kawai yaji kukanta mafiya yawan lokuta shiryawa kawai take ta saka yarinyar kuka dan ya baro ɗakin nawa. Wani sa'inma baya dawowa sai in yayo sallar asuba. Sabuwa babbar matsalata fa shine matar tashi wallahi duk bala'ina kamar tsoronta nake ji. Kinsan Allah ko haɗuwa muka yi gabana yata faɗuwa kenan. In naji muryarta a tsakar gida bana fitowa sai dai in ta kama dole. Gashi yana cewa zai mayar damu maiduguri kawai can kuma a gidan gandu suke kinga in muka koma yaya zanyi? " Mun jima sosai muna tattaunawa da Yar Shuwa nice har la'asar kafin na baro gidanta. Sai naji na ɗan samu sauƙi babu laifi dai Haka naita zuba ido yau Babangida zai dawo a_a gobe ne shiru har saida ya kwana ashirin cib da magriba sai gashi lokacin ina kaɗa miyata ta yauƙi nayi tuwona na alkama. Ƙurama juna idanu muka yii kowanne cikinmu da abinda dai yake saƙawa a zuchiyarshi. Nice na soma kawar da kaina. Dana gama girkina bayan ya dawo sallahr isha na zuba mishi yaci. Haka zaman yaci gaba da tafiya babu daɗi cin mutuncin iyayena da cin zarafina babu wanda Babangida ya fasa saima abinda ya ƙaru. Ya tsani yaga su Adama a gidana, ya kuma tsani ince zanje gida ganin gida. So da yawan lokuta yana korar su Adama haka dole suke fita zukatansu a jagule kuma suna ƙyaleshine dan gudun kada su turguɗe mun auren nawa. Har Maigogul Babangida ya taɓa kora wallahi a nanne Maigogul ya zazzare mishi idanu ya nuna baifa isaba. Inaji sun daɗe suna faɗi in faɗa. Cin fa mutunci da cin kashi babu wanda Babangida bai mun ba, babu wanda danginshi basu yi mun ba. Wata haihuwa da Sa'a tayi ne da naje suna ananne farkon haɗuwata da matar Babangida mai suna Zahiya fara kyakkyawar gaske mai hijabi da niƙabi. Abinka da dangin miji an gama faɗama kishiya sirrinka ko gaisawa yarinyarnan taƙi muyi sai feleƙe take ta faman yi tayi nan tayi can. Ni da Adama data rakani sai ido muka ɗauka muka zuba mata har habaici take zubarwa. To ananne da naji ta ambaci sana'ar kawalci na dira a bakin mitsiyaciya nai mata kafirin duka na tarwatsa taronnan tsab. Aurenma bai daɗe ba suka rabu da ciki a jikinta daga baya cikin ya zube. Kwatsam Babangida yace in shirya gobe gobe zamu tashi a wannan unguwar zuwa wata unguwar. Cikin dare yasa naita haɗa kaya ina ɗaurewa a buhu. Sassafe su Labbai suka zo suka taya ni harhaɗa kaya mota na waje anata loda kaya. Muna gamawa naima matan gida sallama babu wacce tace zata rakani face maman Zahira kawata. To Babangida ya gama shafeni da baƙin fenti. Hmm muna zuwa ƙofar gidan da aka tsaya sai muka ga motar kayan Amaryar a ƙofar gidan akata aikin saukewa gasu Sa'a da su Gudidi da sauran maza ƙannen Babangida. Ga ɗaki ga ɗaki ni da sabuwar Amaryar Babangida wacce za'a ɗaura auren a ranar. Mu da su muka cakuɗa akaita jera kayan ɗaki matan gida kuma suna ta kallon ikon Allah dai. Su Adama sai rarrashina suke yi sabida yadda suka ga na damu ainun. Da daddare muna zaune ni da Rahama da naita roƙonta ta tayani kwana sai ga Babangida ya leƙi. Ganin Rahama ne yasa ya koma. Ni dai a wannan dare da ƙyar nayi bacci. Masu karatu na barku da hasashe ku hasaso duk wani wulaƙanci da za'aima mace ta muzanta wallahi babu irin wanda Babangida bai mun ba. Cikin ƙanƙanin lokaci na lalace na fige na fice a hayyacina. Abinci fa akwai a gidana babu wannan yinwar hakama sutura. Amman baƙin cikin ba Babangida suke cusa mun yana da yawa sosai. Gaga gaga haka rayuwa taita garawa matsaloli ta ko wanne ɓangare gana Babangida gana matarshi, gana danginshi, ga mai dungurungum na ƴan gidanmu. Ko da yaushe a cikin zuwa beli muke. Wannan ya yi sara, a_a wancan yayi sata, wancan yayi ma mace ciki muke nan a haka zamu ƙare. Ga ƴar Shuwa sabida tsabar damuwar da take ciki ko gidanta bana zuwa daga baya ma suka koma maiduguri can dangin mijin duk da danginsu ɗaya. Gaga_gaga Ina zaune da tsohon cikin Aminu a kan gadon Rakiya anata taɗin bikin Sadiya ni dai bana cewa uffan sabida tun jiya nake jina wani iri dai. Toh ni kam Rakiya zan tafi gida. Jikinne nake jinshi babu daɗi inaga haihuwarnan tana hanya dab take da isowa" Adama ta miƙe tace. "Ni kaina tafiya zanyi Lolo. Allah ya kaimu asabar ɗin duk abinda ake ciki kafin masu kawo kayan su zo zamu haɗa abinda ya dace. Ina mota a zaune zani gidane na tuno mai zai hana in dinga duba tunda babu wahala Maigogul a gabana yake yin abubbuwa da yawa. Murmushi nayi dana tuno ba ƙaramin kuɗi zan samu ba kuwa. Ina isa gida naƙuda ta kamani matan gidanmu ne suka tsaya mun hardai na haifo ɗana namiji naci azaba har sau biyu na suma bayan yaron ya duro duniya. Ko da aka kira aka sanar ma Baba Malam batun haihuwar shiru har washegari babu wanda yazo barka. Babangida ma yana ɗakin sabuwar Amaryarshi da bata fi wata biyu da tarewa ba. Jiya dai ya leƙo ina kwance bayan mun dawo asibiti. Amman fa baice mun sannu ba. Ya dai leƙa fuskar yaron a gaban Adama yace. "Wannan dai nawa ne. Amman ita waccan a nuna mata ubanta tun wuri" Mardiyya na kalla sai ta bala'in bani tausayi sai kallon uban take yi. Ƴar Shuwa ma sai sake tabbatarmun take yi Mardiyya ba Ƴar Babangida bace duk da kamanninsu, ni dai ce mata nake yi ta bar wannan zancan yarinya dai tashi ce. To shima bai yadda tashin bace. To yau da muka wayi gari babu wanda ya leƙo mu tsakanin Babangida da matarshi. Ga jariri bashi da sutura sai kayan Mardiyya na jinjirantaka ake saka mishi a hakan A cikin kwana na uku da daddare Baba malam yazo yayi mun barka ya ɗakko dubu ashirin ya bani. A cikin kudinne na samu na bayar da ɗinki, su ƙunshi da kitso duk a ciki nayi. Ranar suna da safe sai ga Amarya ƙebe_ƙebe ta shigo da atamparta a leda ta tarar dasu Labbai harda Uzairu zuchiyata sunata ƙulla zoɓo da kunun aya. Ta yi mun barka ta bani wannan Atampa ta fita. Haka akaita zuwa suna ƙawayenmu na makaranta, maƙota da ƴan gidanmu. Da rana can wajen azahar tawagar gidansu Babangida suka iso. Daga lokacin taron suna ya watse aka rabu tsiya_tsiya dambe har maƙota Adama ta kwaɓe ma Sa'a hijabi a ƙofar gida akaita karawa. Zagi ta uwa ta uba sabida Aminu yaci sunan mahaifin malama Babba bisa umarnin Baba malam, shine fa wannan rikicin. Ni kuwa sabida tsabaragen baƙin ciki ɗaki na shiga na kulle sai kuka. Da la'asar gidan suna babu kowa duk kowa ya watse. Ga ubn tulin aiki da ragowar abinci da ba'aci ba. Sabida tsabar haushi haka na goya Aminu a baya Mardiyya na biye dani na fito naita aiki. Abinci kuwa matan gidanmu babu wacce tayi girki abinci faca faca har maƙota. Maman Abdul ce tai ta tayani aiyukannan zuchiyata kamar zata fashe dan baƙin ciki. Malama Babba har gida tazo washegari ta tusa ni a gaba da Ɗanta akan sai dole dole ya sake ni tana yi tana kuka. Ana cikin haka Babangida da biro da takadda a hannunshi sai muka ji shigowar Baba malam yazo akan faɗan da aka gwabza jiya dan Sa'a ma tana asibiti sabida mahangurɓan data dinga sha. "Yayi kyau Babba ashe da kika ce asibiti zaki je nan kika tawo kin tusashi gaba yayi saki ko? To kai kaji matsawar hannunka ya saki yarinyarnan to tamkar ka saki gyatumarka ne wallahi, kuma bazan yafe maka ba. Zaɓi ya rage gareku. Ramadan wuce ka mayar dani. Ke Sabuwa Allah ya raya Baba Aminu. " Jiki a sanyaye malama ta fita, Babangida ya dinga dukana gani da ɗanyen jego babu ƙarfi a jikina Take jini ya ɓalle mun, kusan wata guda nayi a asibiti dan na daku sosai. Haka aka kuma kwatantawa a sunan Aɗɗa'u sabida shi kuma sunan mariƙin Malama Babba ne yaci ƙanin mahaifinta wanda a hannunshi malam ya auri Malama Babba. Sai dai shi wannan ba'a watse ba dangin dai Babangidanne suka watse. Amman fa rikici harda zubar da jini dattijan unguwane suka yayyafama ƙurar ruwa a lokacin Babangida yayi kuɗi yana da mota kuma naji labarin yana gini ma, ya saki mace ta biyar yana shirin zai ƙaro ta shida zuwa bayan ƙaramar sallah nima a bakin Alawiyya naji da bazan sani ba sai dai inga ana shigo da Amarya. Ni kuma a lokacin na zama mai duba mata na zuwa cikin sirri ina musu duba kuma suna samun biyan buƙatarsu, ni kuma ina amfana da kuɗaɗen hannunsu harda ma kaji da turamen zannuwa. Yadda harkar take duk bige ce gaskiya. Babu komai a cikin duba face ƙarya da suddanaru. Bugun ƙasa dai anayi ne dan a duba tauraron mutum a cikin waɗannan taurarinne ake duba abinda zai iya faruwa, misali kaga mutum a gidan bakwai ko huɗu, ko gidan tara. Ko kaga wata guguwa, ko wani duhu, ko wani irin haske mai tsanani. Siddabarune mara wahala sai dai in baka koya ba. Iyakar abinda kaɗai na iya kenan tunda ni nasan laƙanin da ake amfani dashi wajen duba. Magunguna kuma duk bige ne, kuka, munjirya, rawaya, sabara, itacen kuka, sassaƙen mangoro babu abinda bana bayarwa ince mace tayi amfani dashi. Kuma sai kuga an dace dake shi dama tsafi gaskiyar mai shine na yarda da wannan hausar. Amman bana aiki da aljanu, damfara ce kawai. Yanzu dai kun gane ina fata? (Bana son fito da haƙiƙanin sahihin bayaninne dan gudun matsala) Gaga_gaga Haka abubbuwa suka ci gaba da faruwa bayan Sallah kuwa sai ga Amarya Hamida an kawota. Kafin a kawota nayi muku tsallake kusankwana Babangida yakke yi waya da Hamida akan gadona ina ji ina kuma gani. A lokacin na soma sanyi na saduda da duk wani rashin kunya hankalina ya dawo kan tarbiyyan yarana musamman da Mardiyya ta soma zuwa makarantar boko da islamiyya. Babangida sai ya sake samun damar ci mun mutuncina yadda ranshi yaso. Abubbuwa da suka ci gaba da faruwa suna da yawa, tunda kuɗi ya zauna ma Babangida sai ya sake buɗe faifayin neman matan baza, da yawan yin ɗinkuna, da yawan zage_zage da gore_gore dai. A cikin wannan wahalar Allah ya ƙaddara na haifi Malama haihuwar da tafi ko wacce haihuwa bani wuya kenan. Haihuwar da bazan mance rikice_rikicem dake cikinta ba. Haihuwar da ko awo ban taɓa zuwa ba. Allah ya ƙaddara aka sama yarinya suna Saratu. Sunan da har gobe mai sunan na nadamar da ɗiyata aka saka ma wannan sunan take yi. Cikin yarannan guɗu dana haifa in aka cire mardiyya basu taɓa saka daidai da wando ace na ubansu bane har saida suka girma da abun duniya ya isheni shine nayi tattaki na sanarma Baba Malam duk halin da nake ciki tun daga farkon auren har zuwa lokacin da nakai ƙarar. Shine Baba Malam yaci mutuncin Babangida sosai da sosai kuma ya zamana yana yawan tuntuɓata halin da nake ciki da yaran. Bayan Hamida Babangida ya auri mata biyar sune Zainabu, ita tana da ɗa dashi yana hannun Kawu manga. Farida itama ta haifi ɗiya mace dashi, sai Abida basu da rabo, Ƴar shuwa, Ramatu. A taƙaice iyakar abinda zaku samu kenan a cikin haiwayen da akayi. Ragowar na barku da hasashe. Amman kuimun adalci wajen nazari mai kyau kafin ku yanke hukunci. Inci gaba da zaman ƙasƙanci da auren Babangida. Ko in matsa in gina sabuwar rayuwa?
Mrs Bukhari [8/14, 7:22 AM] +234 802 205 9556: IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA UKU SHAFI NA TARA
DAWOWA DAGA LABARI
Babangida:.