Kenza eBookz

Idan kaya ya gaji book 3 - Chapter 9

Idan kaya ya gaji book 3 - Chapter 9

Idan kaya ya gaji book 3 Chapter 9: Idan kaya ya gaji book 3 Chapter 9. Yana zaune a benci shi kaɗai. Maza masu majinyata a asibitin wasu suna kwance a…

3,743 words

Yana zaune a benci shi kaɗai. Maza masu majinyata a asibitin wasu suna kwance a tabarma, yayin da wasu suke zaune a tabarmar. Babangida dai sai aukin kiran lambar Sabuwa yake yi, abinda yafi komai ɗaga mishi hankali jin wayar tata a kashe yanzu_yanzu. "To mutuwa wayar tayi, ko kuwa kashe wayar Sabuwa tayi ne?" Shiru yayi yana tunanin yadda ya damu akan son jin jikin Sabuwa. Kwatsam yaji wayarshi tana ruri ƙur ya ƙurama baƙuwar lambar idanu. Tabbas yasan kiran na dole ne in aka duba lokacin da akayi kiran lokacine da mafiya yawan al'umma baccinsu tuni ya jima da yin nisa. A kasalance ya ɗaga wayar kirjinshi na dokawa "Babangida Adama yar Lolo ke Magana" Babu shiri ya bude baki har yana harɗe harshe wajen furta. "Adama kaddai jikin na Lolo ne yaƙi?" Zaka iya fuskantar tashin hankali sosai a muryarshi "Uhm Babangida dama jikinne da sauƙi. Lolo fa ta gudu bata gidanka. Kuma bata gidanmu ma dan yanzu muka gama waya da ƴan gida" Baisan sanda ya miƙe tsaye ba sai jirine ya dawo dashi ya zaunar da karfi. Cikin rarrabe kalma yace. "Adama kika ce Sabuwa ta gudu fa ba'a san inda take ba? Hasbunallahi wa ni'imal wakil. Gani nan zuwa gidan yanzu" Ƙit ya kashe wayar tare da dafe gefen zuchiyarshi da yake jin tamkar zuchiyar tsaga ƙirjin zata yi ta faɗo. Ashe Sabuwa haka ta tasirantu a rayuwarshi shi yananan yana haukarshi baisan itace cikon numfashinshi ba? Miƙewa yayi cikin dauriya duk da dai jiri na dibarshi amman dole yaje gida yanzu abi duk inda za'abi dan ganin matarshi ta dawo gida cikin ƙoshin lafiya " Ɗakin jinyar ya shiga ya tarar Sa'a bacci take yi a zaune. Malama Babba kuma yana da tabbacin sai zuwa gobe allurar baccin da akai mata zata saketa juyawa kawai yayi ya futo bakin asibitin zuchiyarshi cike da ciwo da tunanuka. Duk shi kaɗai sai bama mutane wahala yake yi duk sabida shi kaɗai iyayenshi na kwance basa iya gane kansu shi ko wanne irin son kaine dashi haka ne? Kai ya girgiza yanata aikin istigifari a fili da zuchiya ga kukan zuchi da yake yi wanda yafi na zahiri ciwo da duka. Titi tamkar an share shiru babu gilmawar ko mota ɗaya. Babangida ganin wankin hula na shirin kaishi dare yasa dole ƙanwar naƙi ya kira Mustapha a waya dan ya kawo mishi ɗauki. Wayar dai ta shiga sai ruri take yi, Babangida na adda'ar Allah yasa Mustapha ya ɗaga. Ai kuwa Mustapha ya ɗauki wayar muryarshi tarwai ga sautin kiɗa na tashi a inda yake da dukkan halamu baya ma gida yabi dare yana shuka tsiya tare da ƴaƴan iska. "Ustaz kaine a cikin darennan ko dai ruwa ka koma ne?" Girgiza kai Babangida yayi irinna wanda yayi nadamar gaske yace. "Allah yaimun tsari da komawa wannan ruwa mai cike da ƙazanta. Kaima bazan gushe ba ina maka nasiha akan kaji tsoron Allah ka tausayama iyayenmu, matanmu, da ƴaƴanmu. Mustapha ko a ina kake kazo bakin asibiti ka kaini gida. Sabuwa ce akace mun bata gida ana zargin guduwa tayi" Mustapha yace. "Guduwa kuma? Wani abun ya sake faruwane banda wanda ya faru a kotu?" Sai da ya lumshe idanunshi da suke mishi yaji kana yace. "Shidinne kasan dole abun ya jijjigata. Kai dai tawo dan ALLAH " Murmushi Mustapha yayi yace. "Kaci sa'a ina kusa bani minti goma in sallami Ruda" Ƙit ya kashe wayarshi. Kafin ya kashe Babangida yana jiyo ƙaran summatar Ruda da Mustapha yake yi. Shi kuwa dake a cikin damuyoyi yake masu girma tare da lissafin rayuwa da kusakuren daya yai ta tabkawa Sai yaga Mustapha ya iso da wuri alhalin saida yaci mintuna ashirin masu kyau. Zama yayi a gaban motar ya rufe idanunshi zuchiyarshi na dokawa da ƙarfi. Mustapha yayi juyin duniya su ɗan tattauna Babangida yaƙi fur. "Allah ya kyauta. Ka kwantar da hankalinka babu inda zata je fa. Inma zata gudu taje wani wajen bafa zai wuce wajen Khalid ba. Kum.... "Ya'isheka Mustapha kada ka sake jifan Sabuwa da wannan kalmar. Bana jin Sabuwa zata hugu taje wajen wani ɗan balaja'u da aurena a kanta. Yaya kake son nayi ne in haɗiye zuchiya in mutu kaima ka huta ko? ".. Ya ƙarashe maganar cikn haki. Hakiƙa Mustapha ya sake jefa rayuwar Babangida a cikin garari ya kunna mishi wutar kishi bisa wutar da take ta tafasa jini da tsokar jikinshi. Suna isowa ƙofar gidan Babangida bai jira Mustapha ya gama gyara tsaiwa ba ya dire kawai. A baya Mustapha ya bishi da sauri sai a falon Sabuwa suka haɗu. Su Adama suna zazzaune a falo sunyi shiru ciki harda Mardiyya. "Adama kika ce Sabuwa bata nan. Kuma bata gida?" Babangida ya tambaya a kidime" "Wallahi kuwa Babangida. Ni ko dana farka nayi tunanin tana banɗaki ne. Ashe Sabuwa ta hau dokin zuchiyar abinda su Rakiya sukai mata, da irin tashin hankalin da ka jima kana jefata a ciki. Ta yanke hukuncin tunda ba zaka saketa ba ta shiga duniya. Mu faɗa ma kanmu gaskiya Babangida kayi ma Sabuwa cin zarafin da ba duk mace ba. Ko mu ƴan uwanta ka wulaƙantamu. To Sabuwa dai ta tafi" Da mugun sauri ya wucesu zuwa uwarɗakin Sabuwa. Yayi tsaye kawai dan baisan abunda ya shigo dashi ba. Idanunshi suka sauka akan akwatin data haɗa kayanta ta barsu. Babu shiri ya isa ya buɗe akwatin yana kallon kayan data gwamutsa a ciki. A haka ya bar akwatin a buɗe ya isa gaban sib duk ya bubbuɗe ji yake tamkar zaiga Sabuwa a ciki. Rigar baccinta ya zaro ya ƙanƙame a hannunshi tare da rufe idanunshi yana tuno ranar da yayi mata wani fyaɗe a lokacin tana sanye da rigar a jikinta. A duk yawon biye biyenshi da duk samfurin matan daya aura haƙiƙa Sabuwa tayi fice ɗanɗanonta daban yake dana sauran matan daya sani. Wannan yana daga cikin dalilan da yasa duk yadda yake nuna ma Sabuwa ƙiyayya a fili a can ƙasan zuchiyarshi akwai sha'awarta wadda ashe cakuɗe take da wata iriyar soyayya mai haɗe da kishinta wanda shi baisan wannan motsin soyayya bane sai a cikin kwanakinnan. A tunaninshi motsin sha'awarta ne. Buɗe idanunshi da suka rine yayi ya ajjiye rigar ya fito jikinshi a mace. "Babangida inaga tunda da mota a darennan mu garzaya gidajen ƙanne ko Allah zaisa Sabuwa taje can ɗin sabida zukata su samu nutsuwa." Cewar Labbai Kamar wasa suka soma zagaye cikin dare tare da buga gidajen mutane. Abu kamar haɗin baki dai har suka gama karaɗewa ko wanne gidan ƙawayen Sabuwa har gidan Layuza suka je zancen ɗaya ne Sabuwa bata zo ba. Zuwa lokacin yaci in asibiti aka kai Babangida a bashi gado tare da bashi kulawar gaggawa. Amman Mustapha ke riƙe dashi a masallacin layin gidansu Sabuwama sukai sallar asuba. Su kuma su Labbai suka shiga gida. Saida suka idar da sallar sannan sukai sallama a ƙofar gida aka basu izini, sai ga Babangida a tsakar gidan su Sabuwa. Yana shiga kiran wayar Sa'a na shigowa wayarshi sai lokacin ya tuno da batun Malama Babba ma. "Assalamu alaikum Yaya Sa'a?" "Babangida kana inane na futo Sallah ban ganka ba. Kaddai kace mun baka kwana a asibitinnan ba. Ko kuma Club ɗin ka zame jikinka ka tafi tunda ka saba jawo mana maganar da zata hanamu bacci?" Idanu ya lumshe yana jin wani abu mai tauri a maƙoshinshi yana tokare mishi harshe. Yana ji tana ta Hello Hello amman ya kasa buɗe baki ma yayi magana. Ita a nata tunanin network ne yasa bata ji maganar Babangida ba. Sai ta kashe wayar. A hankali ya sauke wayar a kunnenshi cike da girma Babangida ya gaishe da Rakiya da Hauwa. Nan aka shiga kiran ƴan uwa na ƙauye ko Lolo taje wajensu. Babu labarinta sam. "Babangida kaje ka nutsu Lolo ba ɓata tayi ba ba kuma saceta akayi ba. Babu mamaki Khalid ne ya hure mata kunne shi yasa ta gudu taje wajenshi. A babban asibiti yake ko zaku je mishi da yan sanda a kamashi zai fito da Lolo nayi imani tana can." Cewar Rakiya kenan. Wata ƙatuwar ajjiyar zuchiya ya sauke yana jin duniya na juyawa dashi kamar gajimare zai sakko mishi a ka. Matarshi wani ƙato ya ɗauketa ta koma wajenshi bacin da aurenshi a kanta uwar ƴaƴanshi. Wai dama haka bariki ƙazantarta take ne?" Kai ya riƙe kawai Mustapha ya riƙeshi suka fita. "Mardiyya ja ƙannenki ku shiga ciki" Cewar Adama kenan. Amman kafin ta rufe baki Mustapha ya dawo.."Mardiyya ku tattaro mu tafi a kaiku gida" Labbai tace "Na zaci za'a barsu anan na ɗan wani lokaci ai?" Rakiya tace. "Su tafi maza. In aka barsu Hala ke zaki ɗauki nauyin basu abinci ko? Komu da Allah ya kawo mu wayewar garin yau munyi farin ciki da muka ga yau da rayuwarmu ruwane kaɗai amman a gidannan muma shi zamu kamfata kowa ya kama gabanshi. Gidansu da gidan kakaninsu akwai abinci suje can su ƙarata. Ita kanta uwarsu dadine yayi mata yawa dan banga haka a gidan ubanta ba. Kinsan in daɗi yaima mutum yawa sai yace Allah ya kasheshi ya huta." Kai Mustapha ya girgiza ya tarkata kan yaran suka fice. Babangida fa jiki yayi tsanani dauriya ce kawai da addu'o'in da yake ta jerowa yasa ya kai war haka. "Kaini asibiti Mustapha yaran sai a mayar dasu gida wajen Aisha ko Ramatu. Mardiyya mamanku bata faɗa miki inda zata je ba, ko kinji tana waya haka?" "A_a Baba bata faɗa mun komai ba. Abinda na sani shine jiya bata ko magana har muka dawo daga islamiyya " Ido ya lumshe kawai yana dafe da kanshi har suka ƙarasa asibiti. A ƙofar asibitin suka ga Kawu manga da matan su wawo isowarsu kenan. "Mustapha ya zamu yi da naso ka rakani asibitin inaso inga Khalid ne?" Shiru Mustapha yayi yana tunani can kuma sai yace. "To yanzu abinda za'ayi muje mu duba Malama Babba sai mu futo mu sauke yaran in yaso sai mu wuce." Fitowa kuwa suka yi dukkansu. "Ai ga Babangidan ma ya iso" Cewar Safiya matar Bashiru. A tsanake ya isa wajensu aka gaggaisa duka. Kawu manga yace. "Ina ka shiga Sa'a ta kirani a waya ta kawo ƙarar baka kwana a asibiti ba?" Kafin yace wani Abu su Safiya suka wuce tare da yaran zuwa ciki. Wajen ya rage daga Kawu manga sai Mustapha sai shi mai gayyar. "E ban kwana a asibiti ba gaskiya " Kura mishi idanu yayi kafin yace. "To me yasa?" "Sabuwa ce akai mun waya jiya da daddaren wai ta gudu. Wannan dalilinne yasa na bar asibitin. Tun jiya muke nemanta cikin dare har izuwa safiyar yau babu labarinta. Yanzu ma nazo in duba jikin Malama ne inaso Mustapha ya rakani mu kai report ofishin ƴan sanda, mu ba da cigiyarta a gidan TV " Kawu manga shiru yayi baice komai ba. Bai kai ga cewa uffan ba su Wawo suma suka iso asibitin tare da dukka mazan gidan baki ɗaya. Nan aka shiga gaggaisawa nan kuma suka dunguma zuwa ciki. Bibbiyu bibbiyu ake shiga sabida bazai yiwu su shiga fin haka ba. Kuma da sun fito sai su nufi hanyar waje, dan tsaiwar ba zata yiwu ba sabida yawansu. Babangida sai kallon su Mardiyya yake yi da suke zaune a takure a kan benci. Mardiyya itama uban nata take kallo ta saka fuskar tausayi. Sai da ya rage saura Babangida da Mustapha ne kaɗai a tsaye suna jiran Kawu Manga ga Wawo su futo su su shiga shine ya dubi Malama Babba ya miƙo mata hannunshi. Allah sarki yarinyar ta taso ta riƙe hannun Baban tana mishi murmushi. Sai yaji tamkar hawaye zasu sakko mishi. "Mardiyya ku kun shiga kun duba jikin Malama ne?" A sanyaye yayi maganar linkib da rauni. Itama a sanyayen tace. "Bamu kai ga Shiga ba Goggo Sa'a tace kar mu shigo bata son ganinmu shine nace musu mu zauna anan" Wani irin abune ya soki ƙirjinshi jin abinda Sa'a ta faɗama yaran. A zuchiyarshi sai yafi ganin lefinshi da bai tabbatarma da ƴan uwanshi cewar su Mardiyya sunfi mishi ko wanne yara soyuwa a zuchiyarshi ba. Sai yasa ƙafa ya shure yaran yake nuna musu ƙiyayya duka hantara, kyara duk shi kaɗai. Baima kamata yaga laifin Sa'a ba sam. Sai dai yayi tunanin hanyar da zaibi dan ganin ya siyo musu martaba da kima a idanun duniya baki ɗaya. Isowar su Ƴar Shuwa da Ramatu, da Sauban ne ya dawo da Babangida daga cikin hayyacinshi. Wawo na fitowa Babangida ya ja hannun Mustapha suka shiga ciki. Malama na kwance amman idanunta biyu. "Sannu Malama ya ƙarfin jikin naki?" Kai ta ɗaga da hannunta halamar da sauƙi. Babangida tsoro ya shigeshi yace. "Yaya Sa'a Malama bata magana ne?" "Da tana yi ai da tayi. Kai da kake son ma ta mutu ka huta? Saboda fasiƙar matarka ta gudu tabi namiji shine dalilin da zaka fice a asibitinnan babu ko sallama ga mahaifiyarka kwance babu lafiya silarka. Ita dai wannan soyayya da Malama take nuna maka bata da wani amfani ma tunda ka kasa tsaya mata a lokacin da bata da lafiya " Kallonta Babangida yayi. Ya dubi Malama Babba da take ɗaga ma Sa'a hannu akan tayi shiru. "Lafiyanki ƙalau kuwa Sa'a da irin waɗannan maganganun da kike fesarwa a gabana. In a gaban Yayane kin isa ɗago kaima bare har ki dinga wannan kalami haka? Dame kuke so mutum yaji ne. Babangida inya tsaya a kanku shine samun lafiyarne koka sai akayi Yaya? Duk lalacewar Sabuwa ai matarshi ce Uwar manyan yaranshi dole. Sannan kufa sani Sauban ne zai auri Mardiyya fa" Shiru Babangida yayi yana nazari. A yanzu ne yake jin in sama da ƙasa haɗewa zata yi bazai bari Sauban ya auri Mardiyya ba. A yaune ya gano zata rayune cikin ƙunci da tsangwama ƙila har a wajen Sauban ɗin. Yafi taje waje ta auri bare ba Sauban ba. "Kayi haƙuri Kawu Manga bazan sake ba." Ya jiyo muryar Sa'a tana ba da haƙuri. Kawu manga yace. "Babangida muje daga waje in ganku tukunna" A baya suka bishi zuwa waje. Sauban na zaune a kusa da Mardiyya suna hirarsu cike da girmama juna. Kuka ma take yi shi kuwa ya rage murya sai aikin rarrashinta yake yi. Ganin futowar Babangida ne yasa su Ƴar Shuwa da Ramatu suka tashi. Gaishe da Kawu manga suka yi tare da tambayar mai jiki. Ƴar Shuwa ta ɗaura da cewa. "Ashe da abubuwan da muka tashi kenan. Naji labarin Mamansu Mardiyya ta tafi wajen khalid tunda Baban Mardiyya yaƙi sakinta" "Ke baki da hankali ne kinsan abunda kike faɗa kuwa?' Matsowa yayi gabanta cikin zafin nama kamar zai kifa mata mari. Take fa har hawaye ya taru akan fuskarshi. Kawu Manga ne yayi saurin riƙeshi ya dawo baya. Ƴar Shuwa ba ƙaramin mamakin yadda Babangida ya birkice tayi ba. Duk da zuchiyarta a cike take da farin cikin tayi nasara akan Sabuwa, sai da taji kishin yadda Babangida kishin Sabuwa ya baiyana ƙarara a abinda ya aikata mata kuma taji ciwon hakan. "Assha Babangida ashe dai baka dena halinka na dukan mata ba wai? Ke kuma Aisha menene wannan wacce iriyar magana kike furtawa haka ke haka ta faɗa miki wajenshi zata je?" A zuchiyarta tayi murmushin mugunta ta kuma samun wata dama. A zahiri sai ta sau fuskar tausayi tare da cewa. "Ayi haƙuri Kawu manga amman yadda Sabuwa take da Khalid ba zata taɓa iya rayuwa babu shi ba. Shima Baban Mardiyya baisan tsakanin su bane nice nasan komai shi yasa nace haka amman ayi haƙuri tunda maganar tayi zafi" Idanu Babangida ya rufe yana jin juwa tare da wani yaji a idanunshi. Allah yasa ma su Mardiyya tuni sunyi gaba da a gabansu za'ayi wannan abun. Mustapha da yasan haƙiƙanin irin kishin Babangida babu shiri ya riƙeshi dan ya fuskanci yana cikin mawuyacin hali. Kawu manga yayi kasaƙe yana kallonta kafin yace. "Allah ya kyauta ku shige kuje kuyi abinda ya kawo ku. Kai kuma kuzo mu tafi" Har suka shiga mota babu wanda yayi magana. Wawo da yaga tahowarsu Kawu manga ya buɗe mishi mota sai yaga ya shige motar Mustapha. Karasowa bakin motar yayi. "Wawo ku ku tafi wajen nema. Zamu je wani wajennne da su Babangida." "To shikenan yaran ma dasu za'a tafi ko su fito in ajjiyesu a can gida?" Kawu manga yace. "A_a barsu tare da ubansu kai dai jeka Allah yayi albarka" Saida suka hau titi kafin Kawu Manga yace. "Mu je can wajen nashi a asibitin Dan ba ace an barku ku kaɗai kunje za'a iya yin ɓatacciya." Har aka iso babban asibiti Babangida bai buɗe idanunshi ba saida Mustapha ya dafa kafaɗarshi kana ya buɗe idanunshi da suka zama tamkar garwashi ko kuma tasshi dan ja. Sakkowa yayi ya yafuto Malama ta futo. "Mardiyya ku jiramu muna zuwa ko?" Ya faɗa yana gyara riƙon da yaima Malama. Da tambaya aka kawosu har bakin ofishin Khalid. An kuma ci sa'a ma yananan. Izinin shiga aka basu suna shiga Malama ta saki hannun Babanta ta isa wajen Dr Khalid tana dariya halamun ta sanshi tayi sabo dashi. Tsawar da Babangida ya dako mata ne yasa ta dawo da sauri ta riƙe hannunshi da suke ta rawa. Illahirin jikin Babangida rawa yake yi. Kenan yaranshi ma sun sam Khalid kenan. To Sabuwa ko dai tana shigo da Khalid gidanshi ne ya kwana ma shi bai sani ba. Shima yana can yana lalata yaran mutane, ko yana tare da daduronshi?' "Yaro kaine Khalid tsohon saurayin Sabuwa ko?" Kawu Manga ya tambayeshi. "Baba nine ku zauna ga kujeru" Yayi maganar ko a jikinshi. Mustapha da Kawu Manga ne suka zauna. Babangida na tsaye jikinshi na rawa. Wai yau shine suka tawo wajen saurayin matarshi nemanta. Wannan tashin hankali da yawa yake. Kawu Manga ya yi ma Khalid bayanin zuwansu kab. Babu shiri ya cire gilashin dake idanunshi cikin nuna damuwa yace. "Guduwa Sabuwan tayi? Wallahi Allah bansan inda take ba kuma bama waya da'ita Baba ka yarda dani da Sabuwa na hannuna ko bazan bayar da'ita ba zan sanar muku tana hannuna ko dan ku samu nutsuwa" Ai sai ji suka yi Babangida yayi kukan kura ya ɗale jikin Khalid ya hau naushin bakinshi dan baƙin ciki. Khalid shima ingarma ne kuma ba baya ba wajen karfi sannan a kule yake da Babangida da kuma faɗan da sukayi kwanaki har Babangida ya samu galaba a kanshi. Dambe da zagine ya kaure a ofishin. Babu shiri Kawu Manga ya ja hannun Malama ya fita da'ita ya zaunar da'ita a benci inda mata ke jira dan shiga ganin likita. Shigar da yayi ne ya samu Babangida ya caka ma Khalid almakashi a tafin hannu Allah yaso bai shiga da yawa ba sai dai wajen ya fashe. Tsakiyansu ya shiga gashi Babangida ya kawo naushi ganin Kawu Manga a tsakiyansu yasa ya sauke hannun nashi idanshi ɗaya na zubar da hawayen kishi mai zafi. "Ku barni dashi bakwa jin abinda yake faɗa da gadara wai da tana hannunshi ko bazai bamu itaba. Dan uwar ubanka kai an faɗa maka ni kanwar lasa ne. Wallahi sai nayi shari'a da kai akan keta mun haddin aurena daka yi" Babangida ke magana maganar cikin rufewar idanu yake yi. KHALID dake riƙe da tafin hannunshi ya danne inda Babangida ya caka mishi almakashin da babban yatanshi yace. "Sabuwan da kake son kaga ta mutu ka huta. Matar da ka ɗaura ma cutar hawan jini da ciwon damuwa a kanta kake haka? Ai babu namijin da zai so Sabuwa sama dani. Ka zauna kananan zamu yi aure ni da ita" Ai ashe ba'ai komai ba ɗazu. Babangida baisan sanda ya janye Kawu Manga ba shi da Mustapha suka shiga aikama da Dr saƙon naushi. Kafin kace me aka soma cika har saida aka kira ƴan sanda suka wuce dasu dukkansu. An dai ci sa'a dpo yasan Kawu Manga yasan Malam Baba shi yasa ƙurar cikin awa uku ta lafa akai musu tsakani tare da tuhumar Khalid inda Sabuwa take . Zancan ɗaya ne baisan inda take ba. Yara kuma tun sanda za'a tafi dasu Babangida ofishin ƴan sanda Kawu Manga ya kirawo Wawo a waya yace ya zo ya ɗaukesu a asibiti ya kaisu gidansu Hakan kuwa akayi aka maidasu gida, sukaita kuka a ɗakin Mamansu. Maƙota sai shigowa suke yi suna musu jajen ɓatan Mamansu. Ga Babansu a ofishin ƴan sanda, ga kakanninsu a kwance babu Lafiya "

SABUWA:. Sannu kan hankali idanuna suka buɗe tarwai. Wani irin sarawa da kaina yayi ne yasa babu shiri na ɗan runtse idanuna. Jijiyoyin gefen kaina sai aiki suke yi tamkar an kunnasu. Abubuwan da suka faru a kotu da baro gida dana yi izuwa ɗakin hotel kaɗai na iya tunawa. Da sauri na sake buɗe idanuna sai na ganni a asibiti harma hannuna a saƙale da robar ƙarin ruwa. Gefe da gefena na waiga matane da ko sun ɗarani a shekaru kaɗanne ko wacce tana kan gadonta. Macen dake hannun dama na idanta ita biyu. "Baiwar Allah yau kin farka kenan masha Allah. Sannu kinji Allah ya bamu lafiya baki ɗaya." Na buɗe baki zanyi magana sai naji na kasa ɗaga harshena. Ko dana yinkura zan miƙe izuwa zaune shima sai naji na kasa jan jikin nawa. Ga kuma jiri dana soma gani ɗakin ma a wani hargitse nake ganinshi. Wasu hawayen baƙin cikine suka soma zubowa daga kwarmin idanuna suna gangarewa ta gefe da gefen fuskata. "Yauwa Baban Adam ko zaka yima ma'aikatan jinya magana. Kaga matarnan da aka kawota kwana uku da suka shige itace ta farka." Na jiyo amon muryar matar dake hannun damana. Kwana uku, kenan har kwana uku nayi a kwance bansan inda nake ba. To wama ya kawo ni nan. Kaddai Babangida dasu Adama sunsan inda nake su suka kawo ni nan?" Duk waɗannan tambayoyin da nake ma kaina a zuchiyata nake yi. Take naji ɗan ƙarfi ya shigeni harna yinƙura zan tashi zaune kuma jikin ya motsa jirine dai yasa na koma. Wanda aka kira da Baban Adam bai jima da fita ba sai ga wata ma'aikaciyar jinya biye dashi turyan_turyan har izuwa bakin gadona. "Sannu baiwar Allah kin farka yaya jikin naki?" Kafin in bata amsa ta shiga dubani tare da aunani da wannan abun awon nasu da suke maƙewa a wuya da kunne. Da jima sosai a kaina tana duba lafiyata MRS Bukhari

Sai kuma Allah ya kaimu Ranar Asabar. Son so💪🏼 [8/16, 5:47 AM] BADA'AT IBRAHIM: IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA UKU SHAFI NA GOMA

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull