Kenza eBookz

Idan kaya ya gaji book 3 - Chapter 10

Idan kaya ya gaji book 3 - Chapter 10

Idan kaya ya gaji book 3 Chapter 10: Idan kaya ya gaji book 3 Chapter 10. Ta jima a kaina kafin daga bisani ta tambayeni. "Yanzu da me dame kike ji a…

5,107 words

Ta jima a kaina kafin daga bisani ta tambayeni. "Yanzu da me dame kike ji a jikinki" Jiri da ciwon kai. Sai kuma ina ji kamar in kashe kaina" Na faɗa harshe da nauyi. "Subhanallah. Kiyi ta adda'a in sha ALLAH komai yayi tsanani sauƙi na nan zuwa." Amman waye ya kawo ni asibitinnan dan Allah?" Na tambayeta muryata ta sake yin sanyi. "Dr Kamilu ne ya bani ke dai. Amman sanda aka kawo ki bani ce da duti ba ranar. Shi kuma yanzu baya nan sai zuwa dare yake da duti. Sai dai yace in kika tashi duk abinda kike buƙata a kawo miki. Me zaki iya ci ko sha a kawo miki?" Idanuna na lumshe ina hamdala a zuchiyata da akace wani ne daban ya kawo ni asibiti ba Babangida ko ƴan gidanmu ba. A kawo mun ruwan zafi kawai" Na faɗa ba tare dana buɗe idanuna ba. Tunanin ko a wanne hali ƴaƴana suke shi ya jani har wannan ma'aikaciyar jinya ta dawo ba tare dana sani ba. "Tashi ki sha shayin ko saina taimaka miki ne" Ajjiye shayin tayi a durowar gefen gadon ta cire mun ruwan daya ƙare a hannuna. Taimaka mun tayi na zauna tare da jingina a fuskar gadon. Shayinnan kakkaura zafinshi daidai da sha. Dana kafa kaina ban sauke ba saida na shanye tas. Ba dan yinwa ba ba kuma dan daɗi ba. Sai dan Allah Allah nake yi in gama bakina babu komai face ɗaci. Sai nake ji kamar in doka kofin da ƙasa, ko in jijjige gadon da nake kai. Bayan kamar minti goma ma'aikaciyar jinyarnan ta dawo da bokitin ruwan dumi a hannunta zuwa banɗakin dake cikin ɗakin jinyar. Sai da ta kai ta dawo inda nake. "Ga ruwan wanka can na kai miki ko zaki daure kiyi wankan kafin Dr Kamilu ya kawo miki kayan sawarki?" Dan gudun kada in gwasale bajintarta yasa na amince da taimakonta na isa banɗakin tsabtatacce tamkar ba asalibiti ba sai dai warin izal da yake yi kamar ko wanne asibiti. Ina kwara ruwan duminnan a jikina hawaye na wanke mun fuskata tunanuka cunkushe fal kaina. Gurina shine gina sabuwar rayuwa a duniya Sabuwa. Da haka na gama wankan na ɗauro alwala na goge jikina da farin tawul ɗin dana ga ta rataye mun a bakin ƙofar banɗain. Saina maida kayana da wari ma suke yi. Da bin bango na fito majinyatan dake kwance sai sannu suke yi mun da jiki. Kai kawai nake ɗaga Musu ji nake dama in mutu in huta, ko kuma in ɗaura hannu aka in kwarmata ihu, ko kuma in kashe kaina zanfi samun farin ciki. Wani irin ƙaiƙayi ƙwaƙwalwata take yi mun kwatanta muku ne bazan iya ba, zuchiyata tayi duhu kuma a cunkushe nake jinta. Duniyar ganinta nake yi kamar mitsitsiyace kuma kamar ni kaɗai nake rayuwa a cikinta. Iyakar kwatancen da zai kwatantu ya ɗauki hankalin mai karatu kenan. Amman sanin haƙiƙatan ɗin yadda nake ji sai macen da ta taɓa kamuwa da ciwon damuwa, ko kuma likitocin da wannan fannin suka karanta ne kaɗai zasu gane mai nake ji. A haka nayi Sallah daga zaune inayi ina kuka. Na dai yi ne ko zan samu nutsuwa amman abinda nake karantawa a cikin sallar ban sani ba. Banma gama ramawa ba na hakura kawai. Wannan ma'aikaciyar jinyar ce ta kawo mun maganguna na hadiya na sha ruwa. Ban jima ba bacci ya ɗaubeni. Bani na farka ba sai wajajen taran dare. Abokan jinyata duk bacci suke yi, sai masu kula dasu da suke zaune wasu a kujerar roba wasu a ƙasa kan dadduma. Durowar gefen gadona na kalla sai naga kular abinci, da filas din shayi da kayan shayi da wasu ruwa. Kawar da kaina nayi, wanda yayi daidai da buɗe ƙofar ɗakin namu. Wani irin razana nayi da jin ƙaran ƙofar har ƙanƙame jikina nayi idanuna na runtse su da ƙarfi inata adda,a a fili. Na daɗe sosai a haka da dabara na buɗe idona ɗaya sai naga mutum da fararen kaya a zaune a gaban gadona yayi tagumi yana kallona. Da sauri na buɗe ɗayan idon na gyara jikina tare da sauke kai ƙasa. Baice komai ba, nima ko tari naƙi yi, sai can ya sauke ajjiyar zuchiya tare da cewa . "Yaya jikin naki?" Da sauƙi lafiyata ƙalau" "Zan iya sanin sunanki? Ni dai sunana Dr Kamilu nine mutumin daya kawo ki asibitinnan. Mun haɗu dake ne a zangon baƙi. Muka ganki a cikin wani hali shine muka ɗaukoki zuwa asibiti, yau kwananki huɗu za'ace a kwance" Hawaye na soma zubarwa can saina soma shessheƙar kuka. "Kiyi haƙuri in tambayar ita ta saki wannan kukan. Bari. In zuba miki abinci kici zaki sha maganine" Bance komai ba amman na tsagaita kukan. Miƙi mun kwano yayi da farfesun kayan cikin saniya. "Amshi ki daure ko bakya jin daɗinshi ki cinye. Magungunanki suna da ƙarfi kuma sister ta faɗa mun shayi kawai kika sha." Kwanon na karɓa na soma ci a hankali a hankali har na gama. Karɓan kwanon yayi ya ajjiye ya haɗo mun shayi a nanne nace mishi na ƙoshi. Magunguna ya ɓallo ya miƙa mun ya ɓalle murfin ruwa ya miƙo mun. Watsa magungunan nayi a bakina na bisu da ruwannan. "Allah ya ƙara sauƙi. Ga kaya nan na tawo miki dashi. Zan turo sista zata zo ta taimaka miki. In kina buƙatar ganina ki mata magana. In kina buƙatar wayarki ma tana hannuna. Ya kamata a kira wani naki ko?" Da sauri na ɗago na kalleshi. Dan Allah in a kunne wayar take ka kashe. In a kashe take na roƙeka ka sakata a bola bana buƙatarta, kuma bana buƙatar kowa" Jin na fadi haka saiya lallaɓani har saida ya tabbatar hankalina ya kwanta kafin ya tafi. Da taimakon sista na sake kaya. Sabuwar doguwar riga yar kanti ce a ledar da mayafinta. Sakawa nayi nawan dana cire na mayar cikin ledar. Saida na ɗauro alwala na sake biyo bango na dawo gadona. A lokacin ne na samu zarafin ƙarashe biyan bashin sallolun da ake bina. Sun cika, a_a nayi sun wuce wallahi a lokacin ban sani ba. Bani na sake gane kaina ba sai washegari.

Babangida:. Bayan an sallamesu daga ofishin ƴan sanda kai tsaye gidan Mustapha suka wuce yaje zai ɗauki mashin lifan da Mustapha ya bashi kyauta da yaƙi karɓa. Yaƙi shiga gidan Babangida yana jingine a bakin get ɗin gidan har Mustapha ya fito jaye da mashin jin. "Bari in fito da mesa a wanke kaga tayi ƙira dake ba hawa nake yi ba." Mashin jin sabone sosai dake siyan jin daɗine, haka hawanma na ra'ayine. Mustapha da kanshi ya wanke mishi lifan din ya danƙa mishi kin. "Gashi bafa aro na baka ba kyauta ne. Babangida me zai hana ka koma sana'arka ta baban bola. Shi kanshi Alhaji Abubakar Baban bola ya kamata a sake tuntuɓarshi kan kuɗaɗenka dake wajenshi, inta kama ma sai mu koma kotun kome kake gani?" Idanu ya lumshe saida ya haye mashin ɗin kana yace. "Yanzu batun Sabuwa shine abunda yafi komai mahimmanci a wajena Mustapha. Nagode da kyautar lifan. Sai ka jini." Mashin ɗin ya tayar ya bar wajen zuwa gidanshi kai tsaye domin yaga a wanne halin su Mardiyya suke. A tsakar gidan ya tadda su Ƴar Shuwa suna ta hira. Yaji duk munafurcin Sabuwa da Ƴar Shuwa take yi da irin watsar mata da daraja da take yi. Ba ƙaramin shaƙa yayi ba. Wucewa yayi da mashin dinshi ɓangaren Sabuwa ya ajjiye a bakin ƙofar ɗakin. A kitchen yaga Mardiyya a tsaye tana musu girki. Aminu kuma wanke wanke yake yi. Aɗɗa'u da Malama suna zaune su kuma suna ɓare Maggi. Turo ƙofar yayi ya shigo. "Sannu da dawowa Baba" Cewar yaran dukka. "Baba anji labarin inda Ummi take kuwa?" Mardiyya ta tambayeshi muryarta na rawa. Kafaɗarta ya dafa yayi ƙasa da muryarshi. "A_a Mardiyya. Amman ku kwantar da hankalinku umminku tana cikin ƙoshin lafiya a duk inda take. Kuma zata dawo ɗakinta tayi fishine dani, amman zata sakko ta dawo mu yi rayuwa mai kyau" Shiru Mardiyya tayi kawai shi kuma Babangida ya dubi tukunyar dake kan gas kayan miya take soyawa. Agogon hannunshi ya kalla azahar tayi. "Ba'a baku abinci bane naga kina girki, ko ummomin naku basu san kunanan bane?" Ya tambaya da mamaki. "Sun san munanan sun shigo ma ɗazu suna tambayar ko munji labarin anga Umminmu" Kai ya girgiza kawai. "Ku sauke tukunyarnan zansa a kawo muku abinci. Ku shiga ciki. Ku kuma Aminu ku yo alwala mu je masallaci." Yana tsaye har su Aminu suka fito. Sake wuce matan gidan suka yi dai a inda ya barsu. Ganin zai fita da yara yasa Ƴar Shuwa ta miƙe ta biyo shi da sauri. "Baban Fati ina kuma zaka je, kazo ka wuce alhalin kasan a ɗakina kake?" Kallonta yayi kawai tare da girgiza kanshi kawai bai samu zarafin ce mata uffan ba. Wucewarshi yayi ita kuma tana tsaye har saida taga sun shiga masallaci. "Allah ya soka wallahi. Ita kuma Sabuwa ta fita a rayuwarka kenan. Ko banza nayi galaba a kanta. Nasan ko aure zata yi a gaba ba dai ta samu irinka ba. Inma ta aurun kenan. Dariya ta kwashe dashi ta koma cikin gida. Babu Sallah sai sake share wajen zaman gulma da suka yi harsu Babangida suka dawo. "Ku shiga ciki ina zuwa zan kawo muku abinci" Wucewa yayi ɗakin Ƴar Shuwa ya nemi kan kujera ya zauna. Atampopi guda biyu da leshi ɗaya ya gani a ajjiye a hannun kujera. Tabbas atampar ankon ƙanwarta ya gani leshin ma anko ne da yace bazai iya siyan mata ba bashi da kudin. Bai gama tunanin ba sai gata ta shigo ta nemi waje ta zauna. "Sannu da shigowa. Yaya na ganka da sabon mashin siya kayi, shine da nace kayi mun ankon gidanmu kaƙi kayi ko? Ai babu damuwa gasunan ka gansu ɗazu Mama ta aiko amaryar dashi ta karɓo mun bashi a wajen dillaliya tace za'ayi mata biya biyu zuwa bayan biki" Baƙin ciki kamar ya halakashi haka yake ji. "Baki yi girki bane?" "Nayi aina ɗauka bama zaka iya cin abinci ba sabida Sabuwa data gujeka. Ashe duk yaudararmu kake yi kana son matarka bariki kawai kake yi mana. Hmmmm bari in ɗauko maka abincin. Mikewa tayi tana wata tafiyar iskanci ta ɗakko mishi abinci a plate abinda yafi tsana kenan shi a rayuwarshi yana son food flaks ( ɗibi da kanka) sosai. "Ga abincin bari in kawo maka zoɓo" Yawu ya haɗiye kawai ya buɗe abincin shinkafa da wake da mai da yaji ne, sai maggi star guɗa ɗaya a ciki harda lemun tsami ƙarami aka yanka mishi. Yatsa yasa ya taɓa abincin tarara babu ko ɗumi. Da kallo ya biya harta kawo mishi zoɓon ta ajjiye mishi a gora da kofin roba. "Nace wai baki san abincin da sanyi bane kika kawo mun a haka?" Da faɗa yayi maganar dan ya zo wuya. Ita kuwa cikin salon sake cunkusa baƙin ciki tace. ",kasan ba kuɗin gas ka bani ba, baka bani na kalanzur ba gawayine. To ni wallahi bana iya kunna gawayi kalanzir na siyo gora ɗaya kuma tas ya ƙare." Ƙur yake kallonta yana ji kamar ya rufeta da ɗan banzan duka. "To naji kulolinki kuma me ya same su, kinsan bana cin abincin da aka kawo a plate. Kai da gidanka ba za'a kawo ma abinci a kula ka ɗebi da kanka ba. Sannan ya na bayar da kuɗin kayan miya zaki dafa shinkafa da wake har talaucin nawa ya kai wannan matakinne?" Baki ta zumɓure kawai bata ce mishi uffan ba. Miƙewa yayi yana tsaki yayi ficewarshi zuwa ɓarayin Sabuwa. Gas ya kunna ya tsayar da sanwar Taliya dama Mardiyya ta riga ta soya jajjage. Firiza ya buɗe yaga suna da komai kifi guda ɗaya ya ɗakko ya daddatsa. Murmushi yayi dsya tuno Maigogul sanda yake yanka ma su Sabuwa kifi a Kitchen washegarin aurensu. Jin wannan datsar yasa yaran suka leƙo. "Baba bari in dafa." Da sauri Mardiyya ta amshi kifin shi kuma ya shiga ciki. Kai tsaye banɗakinsu ya shiga. Bayinnan tsab tsab dashi sai ƙamshin sabulun wankan Sabuwa na ruwa yake yi. Idanunshi ya lumshe ya sakarma kanshi ruwan sanyi. Tunanin Sabuwa na sake bujiro mishi da irin maganganun banzan da Khalid yayi mishi shi da matarshi. Yayi mamakin yadda rashin Sabuwa da gaske ya dakeshi kuma yana mamakin irin yadda yake fata da burin sake ganin Sabuwa. Harma a ranshi ya gama yanke in Sabuwa ta dawo zai yi zama na mutunci da'ita zai sauke duk wani ratayayyen hakkin daya rataya a wuyanshi nasu. Kuma zai mayar da Sabuwa ta daban cikin matanshii, zai nemo daraja ya lulluɓeta dashi lib. Ƙaran wayarshi dake cikin bayan gidan ya dawo dashi kan hankalinshi. Kawu Manga ne Babu shiri ya kammala wankan ya fito. Maimakon ya fita saiya shige uwarɗakin Sabuwa. A nan ya tadda yaran suna cin abinci a faranti. Yana zaune a bakin gadon yana waya da Kawu Manga Mardiyya ta kawo mishi abinci a kula ta ɗauro plate da cokali da abun diba irin yadda Sabuwa ta koyar da'ita. Gaga_gaga haka abubbuwa sukaita tafiya wasane gaske ne Sabuwa dai babu ko labarin wanda yace ya ganta ma. Duk wani neman daya dace ayi duk anyi amman ba'a samu labarinta ba. Ta ɓangaren Baba Malam bai san da ɓacewar Sabuwa ba har saida ta cika kwana uku cib da ɓacewa a ranar ma Maigogul ne yazo duba jikin nashi shine ya fasa maganar har Baba Malam yaji. Yaji damuwa sosai ya kuma yi alƙawarin da zaran jikinshi ya warware zai duƙufa roƙon Allah akan ya dawo da tunaninta ta dawo cikin ahalinta. Hakan ma yasa magajin Malam ya tattaro kan almajirai akaita adda'a har sauka Malam Baba yasa akayi. Malama Babba kuwa labarin ɓatan Sabuwa kusan shi yasa ta samu lafiya kwananta uku aka sallamota sai tace Wawo ya kaita gidan Yaya Hanne ta gaji da zaman kaɗaici da take yi a gidanshi. Hakan kuwa akayi Malama Babba ta koma gidan yarta da zama tana jiran tsammanin ranar da Baba Malam zai huce ya bata izinin dawowa ɗakinta tunda wacce ake taƙaddamar a kanta ta tafi yawon duniya a cewarsu.

Ta ɓangaren gidansu Sabuwa kab ƴan ɗakinsu cike suke da damuwar rashin sanin inda Sabuwa take. Amman Rakiya da Maigogul ko gezau basu saduda ba. Gara ma Maigogul wani sa'in in yaran suka mishi baƙar rowa yakance. "Allah ya jiƙan Lolo ba dan ta mutu ba. Kai Alkhairi Allah ya kai mata a duk inda take" Ranar data cika kwana huɗu da ɓata sai fa abun duniya yabi ya ishi Maigogul shine harda zazzaɓi, ranar a gida ya wuni a kwance sunata tabka rikici da Rakiya. Ya kuwa zageta ta uwa ta uba akan halin ko in kula data nuna akan lolo. A lokacin tabbas kab ƴan gidan sun yadda matsayin lolo ya bambanta da nasu a zuchiyar Maigogul. Adama kuma Allah dai ya nufa bazawarinta ya kawo sadakinta amman yace ta jirashi har sai ya kammala gina ɓarayin da zai ajjiyeta kafin ayi auren. Ita gudun ma kada ya kuɓuce mata gaskiya taso a ɗaura auren taci gaba da zama a inda suke haya dan ita tsoronta kada ya fasa aurenta. Duk da Maigogul ya baje tabarmar tsubbu ya haɗa mata turaren muhibba dan a binciken da Maigogul yayi ya gano ba ƙaramin dukiya Allah ya huwace mishi ba. Gabaki ɗaya hankalinshi ya dawo kan Adama. Yayin da su Labbai da su Sadiya suka ci gaba da zawarci Qamriyya ma har anci talatar laraba a gidansu tayi mata da ciki ma karami aka fafarota uwar mijin ashe ba'ai bincike ba sai daga baya uwar mijin taji shine fa tasa ɗanta gaba saida yayi sakin. Ke Qamriyya jin zafin an sakeki yasa ta zazzage uwar miji tas har tana mata barazanar duka a haka dai tsiya tsiya aka rabu ta dawo taci gaba da yawonta ga ciki a jikinta. Uzairu zuchiyata kuma kusan abun nema ya samu ya samu wata baturiya da suka hadu a yanar gizo kamar dai wasa suke abota har abun yakai da sun mallaki number juna suna magana ta manhajar WhatsApp. Uzairu sosai ya zage yake bama Felisha kulawa duk da dai ba'a kai ga soma furta love you_love you ba. Amman da dukkan alamu Uzairu zuchiyata yayi kasuwa. Kuma bashi da wani burin daya wuce Felisha ta Aureshi ya bar najerian ma baki ɗaya ya huta ma ranshi. A ko da yaushe bashi da mafarkin daya wuce na barin ƙasa. Wannan kenan.

Mrs Bukhari [8/16, 9:11 PM] BADA'AT IBRAHIM: IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA UKU SHAFI NA SHA ƊAYA (11)

*AKWAI WATA BAIWAR ALLAH DAKE FAMA DA CUTAR SANKARA WATO KANSA A TURANCE* *SUNA BUƘATAR TAIMAKONKU KASANCEWARSU MASU ƘARAMIN ƘARFI YANZU HAKA TANA GADON ASIBITI CIKIN MAWUYACIN HALI GASHI ƳAN UWANTA BA MASU ƘARFI BANE GA MAI SON TAIMAKA MUSU A LAMBAR ASUSUN BANKINSU DA LAMBAR WAYARSU 8168309714,HAUWAU ABDULLAHI,OPEY, PHONE NUMBER 08055695830 ALLAH YASAKA DA ALJANNAH

Sabuwa:.

*Bayan wata guda harda ɗoriya*

Ina zaune a bencin ƙofar ɗakin dana gama jinya dan yau aka sallameni kuma alhamdulillah jikin nawa da sauƙi. Kuma na samu sauƙin damuwa sosai dan Dr Kamilu ya haɗani da terafi Dr mace, da farko dai duk yadda taso dani ta kasa shawo kaina. Sai da muka soma sabawa ne har na saki jiki da'ita dake Allah yayi musu wata iriyar baiwa sosai. Sun iya tarairayan marar lafiyansu kuma suna da hanya da salo_salo sosai na dukan cikin mara lafiya, da bashi misalai wanda har sai mara lafiya ya gamsu ɗari bisa ɗari dasu ya fasa cikinshi sun san matsalarshi. Duk da akwai abubbuwa da yawa wanda na sakaye ma Dr Fatima ban fayyace mata ba. Iyakar irin rayuwar da nake yi a gidan Babangida da dalilin fitowata kaɗai na sanar mata. Amman ban faɗa mata a Club muka haɗu da Dr Kamilu ba sabida ya gabatar dani ne a matsayin ƙanwa ta jini. Sai ta fahimta a matsayin auren dole kawai akayi mun. Duk da a cikin zuchiyarta wallahi bata yadda da labarin dana bata ɗari bisa ɗari ba. Kuma tana yawan tambayata in dai nutsu in faɗa mata gaskiya dan a magance matsalar dake damuna. Dolen doliya na fasa mata cikina taji duk sirrina, tayi mun rantsuwar wannan sirrin a ofishinta za'a birneshi babu mai ji. Uhm bayin Allah makaranta wai ku kunga matan auren da suke zuwa wajen terafis kuwa? ( Allah yasa ina faɗan sunansu daidai. Ayi haƙuri ban iya turancin bane amman nasan kun gane😆) Hmm Allah yayi yawa dasu, wasu iyayensu ke kawo su, wasu kuma ƙannensu, ko yayyensu ke kawosu. Mata ana cikin damuwa da jarabawa gaskiya. "Sabuwa kin gama haɗa kayan naki har kin fito?" Cewar Dr Kamilu dake tsaye a kaina. E Yaya na fito asibitin duk ya isheni wallahi" Dariya yayi harda tuntsurawa. Ya tsugunna ya debe mun kayana dana haɗa nima na ɗebi wasu muka wuce har zuwa wajen motarshi. Saida muka kama hanya yake sanar mun wajen mahaifiyarshi zai soma kaini saina murmure kafin su rakani gida. Kuma zasu yi tsayuwar daka kan kes ɗina tun ina asibiti yayi mun wannan alƙawarin. Nagode sosai Yaya da irin taimaka mun da kayi. Itama Umma ina godiya sosai a gareta." Dariya yayi kawai. Bamu tsaya a ko ina ba sai a gidansu Dr Kamilu. Gidane na mutane tsaka tsaki su ba za'a kirasu talakawa ba, ko za'a kirasu masu kuɗi sai dai irin masu ƙudin da ɗinnan. In kayi la'akari da irin ginin gidan na jan bulone tagogi da ƙofofin gidan duk mada'in dane. (made in da) A rabkeken tsabtataccen falon gidan muka samu Umma a zaune da wata ƴar mata haka dan da gani ba budurwa bace suna ɗan hirarsu harda dariya. "Ahh masha Allah Kamilu marar lafiyanka ta samu kenan? Sabuwa maraba da zuwa" A gabanta na zube na kwashi gaisuwa wannan yar mata da suke tare na juyo muka gaisa sai lokacin na gane ashe yawan fara'ar Dr Kamilu gadon gidansu ne. "Allah ya kara sauƙi Sabuwa. Sannan nasihar da zanyi muku ke da Mariya itace ku kama Allah ku kasance masu taurin zuchiya domin ku fuskanci duk wani kalubalen da zai bijiro muku. Kin ganta itama ta shiga halin da yafi naki ma muni. Da taimakon Allah da kuma ita wannan terafi da nasa Kamilu ya haɗa ku har ta samu kanta. Ku riƙa haƙuri da ƙwarara xuchiyoyinku ku zama jarumai. Sannan kamar yadda nayi alƙawarin kafin ki koma gida inaso ku zanta da lauyanki ku tattauna da kyau. In yaso sai ki koma gida da sammacinki a hannunki na ɗaukaka ƙara. A matsayina mai rajin kare hakkin ɗan adam zan tsaya miki irin tsaiwar da nayi ma Mariya. Kuma kada ki sake tunanin gudu ki bar danginki ki shiga duniya ko da wannan auren bai mutu ba. Ballantana ikon Allah ne kaɗai zaisa yaƙi mutuwa, ko kuma ke kice kin janye" Ni dai sai godiya kawai nake yi nama rasa godiyar wacce iri zanyi musu dukkansu. Ɗakinmu ɗaya da Mariya kuma shekarunta ko ya haura nawa zai zama da kaɗanne. Gidansu gidan karamci ko shara sun hanani, duk abinda na tashi zanyi da zummar taya aiki sai Umma da Mariya su hanani fur. Ana gobe zan koma gida ina kwance shiru, Mariya da Umma sun sun tafi umara, asalin tafiyar ta Mariya ce ta kaita ne domin ta roƙi Allah ya cire mata son tsohon mijinta a zuchiyarta. Sun yi mun alƙawarin da sun dawo zasu sa Kamilu Ya kawo su har inda nake. ina tunanin yadda zan koma mu kwashe da su Maigogul. Ga sammaci har an yanka goben magatakarda zai kaima Babangida sabon sammacinshi. Ni da lauyana kuma duk abinda ya kamata ya sani dole na sanar dashi kuma ya ajjiyeni akan magana ɗaya babu gargada. Idanuna na lumshe Ko yaya su Mardiyya suke, kuma yaya suka ji lokacin da labarin ɓatan dabo na ya bayyana musu oho. Ƴar Shuwa na tuno nayi wani murmushi wanda ni kaina bansan ma'anarshi ba, girgiza kaina kawai nayi ta yi. Washegari da wuri na shirya Baba Haule mai aiki ta kawo mun abincin karin kumallo. "Mai sunan Malam yace in kin gama ki fito yana jiranki" Gabana ya tattake ya kuma yankewa. Tunda dai na tashi nake cikin faduwar gaba. To Haule nagode sosai. Sannan na gode da kulawarki gareni. In sha Allah zan dinga kawo muku ziyara lokaci zuwa lokaci." A sanyaye nayi karinnan na sha magungunana. Ƙarfe goma dot muka tsaya a daidai gidan da su Adama suke haya. Tun kafin mu tsaya na hango Adama a tsaye a dokin ƙofar da tsohon mijinta ga ƙatuwar leda a hannunshi yana miƙa mata. "To ki sauka ki soma shiga sai ai mun iso ko? Sai mu tafi gidan naku" Ajjiyar zuchiya na sauke dan tun muna hanya na sanar dashi wajen yayyena zamu soma zuwa. Tukunnan Toh bari inje gama ya ta can a tsaye da mijinta" Idanu ya ƙura ma Adama har yana sauke tangaran ɗin jikin tagar motar tashi. Daidai Adama ta dumo wani ashariya ta lailayama mijinta kenan. Idanuna na runtse shi kanshi na fahimci zagin ya kiɗimashi. Abinda nake gudu ƙila fa saiya faru, shi yasa tun farko nake ta neman hanyar zillewa amman dana lura bani da wata hanya dole sai Dr Kamilu ya haɗu da su Rakiya yasa dole muka tawo. Tunda ko basu hadu a gida ba zasu haɗu a kotu ai. A hankali na sakko sai kawai Adama ta ganni. A guje ta shige cikin gidan Sai gasu tare da su Labbai harda Uzairu Zuchiyata. Gam muka rungume juna ni da Adama da Uzairu zuchiyata dukkanmu muka saki kuka ni ko da gaske nake rerashi kamar wata ƙaramar yarinyar goye. "Iko sai Allah Lolo kece kika dawo ashe zaki dawo garemu mu har mun cire ƙauna da sake sanyaki a idanunmu. Duk rintsi kada ki sake tunanin guduwa mu tsaya ma kanmu da kanmu" Cewar Uzairu zuchiyata dake tsaye kusa daf da mijin Adama. "Ya isa haka Adama ido ya soma yawa." Labbai tayi maganar tare da ɓanɓareni a jikin Adama Tare muke da baƙo Adama. Yana so yaga su Rakiya" Kafin ma in rufe baki har ya ƙaraso inda muke da sallamarshi. "Allah sarki bawan Allah kaine ka tsinceta kenan? Tawo mu shiga daga ciki. Su Maigogul basa nan Hauwa ce kaɗai a gidan." Kallonshi nayi nace. Yaya mu shiga kaji basa nan. In ka sake dawowa ka gansu" Muna gaba yana biye damu har cikin ɗakin su Adama wanda naga sun samu arzikin gyarawa har da gas ƙarami, ga ɗan kayan abincinsu a gefe. Waje muka bashi akan kujerar ya zauna shi da Uzairu zuchiyata wanda hankalinshi yana kan wayarshi ma. Mu kuma muna kan katifa. Gaggaisawa akayi Dr Kamilu ya kwashe kab halin daya same ni ya basu kabari da dai irin jinyar dana sha duka komai dai. Ajjiyar zuchiya Adama ta sauke. "Tabb ashe daman akwai bayin Allah irinka? Bawan Allah mun gode maka da iyayenka baki daya Allah ya saka da alkhairi. Ni na tashi daga bacci na tarar bata gidan cikin dare ta fice. Kuma ta fita ne a cikin wani irin mawuyacin hali mai muni. Alhamdulillah data faɗa hannu nagari. Jiya jiyannan naje na dubo su Mardiyya inata dai basu haƙuri kan rashin uwarsu da irin zaman da suke yi a hannun matan uba. To iyayenmu har yanzu suna kan bakarsu akan ba'a isa an kashe wannan auren ba. Ita kuma Lolo dama tauri gareta inta botsare kamar gandar kai haka take. Amman dai zamu kuma tuntuɓarsu Allah bashi in suka ji irin halin data shiga fitar data yi ko zasu sassauto" Dr Kamilu ya gyara zama yana kallon agogonshi. "To a dai fahimtar dasu ba'a zaman aure da zalunci. Haka zalika ba'a aure dole balle irin nata auren mai cike da zalunci. A irin kondishon ɗin da take ciki ba'a buƙatar ko tunani ta yawaita balle shiga wata damuwa. Inaga Sabuwa ni zan tafi ko zuwa dare sai in dawo inaso shi Baba mu gana dashi ko zai fahimceni" Da sauri na ɗago Labbai tayi carab tace. "Ai shi tafiya yayi Allah kaɗai yasan yaushe zai dawo ma. Sai dai in ya dawo ko a waya ne saita sanar maka" Muka haɗu muka rakashi har bakin motarshi muna mishi godiya marar iyaka. Kayana ya sauke mun Muna shiga ɗakin sai ga Maigogul ya faɗo ɗakin afujajan babu ko sallama. Tsaye yayi hannunshi riƙe da ƙugu yana kallona tar. "Lolo kece ashe da gaske ashe zaki dawo garemu?" Nice Maigogul " Sai kuma naga ya zauna yana ƙare ma ɗakinsu Adama kallo Labbai na gaban tukunya tana zuba abinci, Uzairu zuchiyata ko hankalinshi na kan waya sai murmushi yake yi. "Lolo sabida mun hana mijinki ya sakeki sabida ke ƴar abu ta kazan ubace shine kika tafi wajen shi Khalid mai hure miki kunnen gabaki ɗaya ayi duk abinda za'ayi ko? Ai kin bamu mamaki kuma baki cika ƴar duniya ba da kika dawo. Sannan da kika tawo wajensu Adama kin kaso auren ne hankalinki ya kwanta ko?" "Haba Maigogul wai me yasa baku damu da rayuwarmu bane, ku dai kan ku kawai kuka sani?" Faɗin Adama kenan. Daƙuwa yayo mata. "Ohh sabida kuna zawarci shi Dakacin da yake zuwa wajenki yana baza ƙaryar kaya ya kasa turo iyayenshi. Mijinki yanzu haka yana gida amman kin ƙi bashi haɗin kai shine ita kike so ta kaso auren nata. In ta kaso kika san waye zai zo ta aureta? Sannan in hakane baga can mijinki yana ta godonki ki koma kin ƙi ba sabida kina neman maiƙo ba. Shine ita kike son rabata da nata maiƙon da yake hannunta ko? Kuma ai ko dan Mardiyya ai ta daure tayi haƙuri. Lolo mufa dukka wannan akan sonki muke yi wallahi Allah" Adama tace "Shikenan tunda haka kace a mayar da auren shi Alhaji in yazo zan faɗa mishi na koma gidan mijina shikenan ai. Inata faɗa muku saki ukune aure ya ƙare a tsakaninmu ƙaryace kawai yake yi muku" "Ni dai bance miki haka ba Adama. Ba haka nake nufi ba ehe" Sai naji yayi ƙasa da muryarshi. Harma da bagarar da zancan ta hanyar cewa. "Labbai miƙo mun inci in tafi. Hiye harda kifin gongoni kuke girki ni ubanku kun barni cikin wahala" Kai kawai na girgiza ina jin baƙin ciki tamkar yayi ajalina. Saida ya zuba loma a bakinshi kafin yace. "Kici yanzu in mayar dake ɗakin ki tun kafin kayi nayi ta dawo." A_a Maigogul wallahi Allah na gama auren Babangida bazan sake zaman aure dashi ba. Na gwammaci in kashe kaina kowa ya huta tunda ba ƙaunata kuke yi ba" Na ƙarashe maganar cikin tartsatsin kukan baƙin ciki. Adama ta shiga labarta mishi halin da na shiga da duk labarin da Dr Kamilu ya basu. Uzairu zuchiyata ya ɗaura da cewa. "Yarinyarnan tana fa da ƴancinta a wannan karon mu ƴan uwanta wallahi sai inda ƙarfinmu ya ƙare daga nan har kotun Allah ya'isa. Wannan karon har ku in bakui wasa ba wallahi a kotu zamu maka ku a cire mana hakkunmu. Yanzu fa da a ƙasar wajene hukuncin ma kisa za'ayi muku" Labbai tace. "Tabbas kuwa a wannan karon dole sai Lolo ta rabu da mijinta tunda dai tace bata yi. Bari ma in kira su Rahama in sanar musu da dawowarta. Mardiyya ma akwai waya a hannunta bari in kira su roƙi Babansu suzo" Nan da nan ta kira su Rahama. Tana kashewa ta kira Lambar Mardiyya ihun yaran naji suna karanto adda,ar godiya ga Ubangiji Ai sai kukana ya tsananta." "To ai shikenan. Na tsame hannuna a kan sha'anin Lolo. Ai kowa rai yaima daɗi ba kamar maishi ba. Kuma duk daɗin inuwar gemu taba kai ga maƙoro ba. Allah ya baku sa'a mu ƴan kallo ne. Nauyin ki ba a kaina zai ƙare ba inma kin fito yawon tazubas kike sha'awar komawa gaki ga duniya. Har ku koma ga Allah ba ku isa kunyi abinda ni ko uwarku tayi ba. Kai kuma da kake cewa a yanke mana hukuncin kisa Bismillah. Lolo kiyi haƙuri ki dena kukan haka kukanki na dafani kinsan sonki" Kwanon daya ci abincin ya jefo ma Adama a fuska ya fice. Hmm kaɗai na iya cewa. Idona kawai na runtse na kwanta na juya bayana kawai. Ina jinsu sunata hirarsu har Rahama ta ƙaraso, su Sadiya ma duk suka shigo da suka dawo. Harda Hauwa saida ta rarrafo tazo ganin ƙwab. Rakiya ma tun kafin ta dawo gida labarin dawowata ya isheta. Itama ansha tababa da'ita su Adama ke Magana ni ko bana ko buɗe idona ma. Maƙota sukaita shigowa munafurcinsu ni dai sai dai ace musu bacci nake yi. Idanuna biyu ras.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull