Kenza eBookz

Idan kaya ya gaji book 3 - Chapter 11

Idan kaya ya gaji book 3 - Chapter 11

Idan kaya ya gaji book 3 Chapter 11: Idan kaya ya gaji book 3 Chapter 11. Mardiyya:. Suna zaune tana ba Malama maganin da Babansu ya kawo mata na mura tana…

3,918 words

Mardiyya:. Suna zaune tana ba Malama maganin da Babansu ya kawo mata na mura tana sha. Ƴar Shuwa tayo sallama ta shigo tare da tsayawa a kansu.." "Ba wanki kike mun ba ubanme yasa kika barmun wanki kika dawo wajen wannan makirar yarinyar. Ke ga mai ƙanne ko?" Aɗɗa'u yace. "Ita ba makira bace wallahi. Kuma in ummin mu ta dawo saina faɗa mata duk dukanmu da kike yi" Ai kafin Mardiyya tayi magana tuni Yar Shuwa ta makanta ganin Aɗɗa,u da wani zazzafan gigitaccen marin da sai da ya shiɗe. "Kaji mun ƙaramin marars kunya. Ko da yake barewa ba zata yi gudu ɗanta yayi rarrafe ba. Tunda ka Tsotsi nonon Sabuwa kuma jinin Maigogul da kayi nayi yana yawo a jikinku dole kayi. Ke kuma dan abu ta kazanki zaki wuce ne ko saina ɓallaki?". Da sauri Mardiyya ta dure Malama ta fita ta koma kan tulin wankin da Ƴar Shuwa ta tula mata dana Fati dana Babangida ma. Zuwa tayi ta dasa kujera tana kallon Mardiyya tana zage_zage. Wayar da Babangida ya mallakama Mardiyya dan ya dinga jin ya suke in baya nan. Da kum su riƙa magana da Sauban itace ta shiga ruri. Ganin number Labbai yasa ta ɗaga da sauri. Ai tana jin abinda Labbai tace sai ta miƙe. "Kika ce Umminmu ta dawo? Alhamdulillah" Iyakar abinda tace kenan ta kwashi gudu sai ɗaki. Su Aminu suna kan Malama da take ta faman kukan ciwo. Mardiyya ta shigo sa gudu ta ɗauki hijabinta ta saka. "Ku taso muje wajen Babanmu ya bamu kuɗin mota Umminmu ta dawo. Ai nan suka shiga murna a gaggauce suka fito Ƴar Shuwa sai kwaɗama Mardiyya kira take yi amman ko waige. Da wani bawan Allah suka ci karo yana neman ɗan aike. Ganinsu yasa ya tsaidasu. "Ku shiga cikin gidannan kuce ana sallama da Babangida kacigari " "Ai Babanmu ne. Baya nan yana makaranta" Aɗɗa'u ne yayo maganar. "A ina makarantar take dan Allah?" Mardiyya tace. "Babu nisa can ƙasan layinnan ne yanzu ma wajenshi zamu je" Ai kuwa wannan ma'aikacin kotu yabi su Mardiyya har makaranta wajen Babangida. Mai gadin makarantar ne ya shiga ya kirawo musu shi. Tun daga nesa daya hango su Mardiyya tsaye da wani mutum sai yaji faɗuwar gaba. Hakan yasa ya ɗago ƙafa ya ƙaraso. "Baba Ummi ta dawo zamu je wajenta" Ƙuruci dangin hauka. Malama ce ta tari Babanta da wannan maganar. Sai kan shi ya ɗaure ya shiga rarraba idanu tsakanin yaran da wannan mutumin. "Assalamu alaikum bawan Allah kaine Babangida kacigari ko?" Hannun daya miƙo mishi dan suyi musabaha shima ya miƙa mishi tare da amsa sallamar. "Nine Babangida Allah yasa lafiya?" "Sai alkhairi dama naje gidanka nemanka ne to sai yaranka suka ce dama wajenka zasu zo suma shine na biyo su. In babu damuwa mu ɗan keɓe mana" Yaranshi ya kalla yayi jim daga bisani yace. "Mardiyya ku shiga ku zauna a waccan barandar ku jirani" "To Baba" Ta ja yaran zuwa ciki. Wannan mutumi ya miƙo ma Babangida sammaci. "Wannan sammacine daga kotun musulunci matarka Sabuwa ce ta shigar da ƙaran Akan abinda take ƙaran, da kuma ranar halartar kotun yana jikin takaddar zaka gani. Dama Abinda ya kawo ni kenan na barka lafiya " Musabaha suka kuma yi har wannan mutumin ya wuce Babangida na tsaye kanshi na jujjuyawa ya shiga zurfin tunani. Duk da ta ƙasan ranshi yayi matuƙar farin ciki da jin kalmar Sabuwa ta dawo, sai dai wannan sammacin ya danne mishi murnar tashi. "Sabuwa uwar rigima da taurin kai. Mu zuba muga waye zaiyi nasara a tsakaninmu. Babangida shine mijinki tilo a duniya, babu ɗan abu ta kazan daya isa yasa in sake ki" Muryar su Aminu ce tasa ya juyo da sauri ya kallesu. "Mardiyya Ummanku wai ta dawo da gaske tana gida yanzu haka?" "E Baba ta dawo Labbai ce ta kirani take sanar mun. Acan ta sauka shine muka zo ka bamu kuɗin mota muje wajenta" Tashin hankalin da yake ciki ai sai ya kuma nunkuwa duk da yana da yaƙinin su Rakiya zasu iya dawo da'ita ko Baba Malam ya kirata yace ta koma ɗakinta. Da wannan dalilin ya sauke ajjiyar zuchiya. Ya shafi kan Malama zafi rau. "Mamana jikin har yanzu da zafi. Inaga zansa zuwa yamma a kai ki asibiti" Kuɗi ya zaro a aljihunshi dubu ɗaya ya basu suka kama hanya suka tafi. Shi kuma ya koma class amman ina ya kasa koyarwar sam dole ya nemi izinin cewar baya jin daɗi zai koma gida. Yana tafe yana juwa. Su Ramatu ana tsakar gida an barbaje magungunan mata matan unguwar sun cika tsakar gidan anata batsa Babangida ya shigo. Karab a kunnenshi yana jin sanda Ramatu take ba da labarin jiya data yi amfani da wani magani waishi kurman namiji wai saida Babangida yaita ihu tana rufe mishi baki."Kai kawai ya girgiza dan ƙarya take yi shi salab ma ya jita musamman jiyan. Kanshi a ƙasa yazo ya wuce su ya shiga ɗakin Ramatu kwananta ne. Zubewa yayi a kujera baƙin ciki goma da ashirin ya haɗe mishi. Sai da Ramatu ta ƙaraci surutunta kafin ta shigo ɗakin. "Lafiya ka dawo alhalin lokacin dawowarka cin abincin rana bai yi ba? Kaga ni ko cefanen banyi ba ma wanda zan aika ya siyo mun kayan miya na rasa kuma yaran waccan matar naga basa gidan. "Wacce matar kike magana akai Ramatu?" Yayi tambayar cikin tuhuma jin kamar muryarshi a ɓace yasa ta haɗiye maganarta. Ɓurum Ƴar Shuwa ta shigo ɗakin da shirinta tsab na fita uunguwa. Zama tayi a kujera. "Sannu da dawowa?" "Hmm yauwa sannu" Sai ta ɗanyi murmushin dole kafin tace. "Dama yanzu na fito zan leƙa makaranta in sanar maka Mama ce ta kirani wai tana son ganina da gaggawa shine dama" Ƙur yayi mata da idanunshi kamar yana karantar wani abu daga motsinta. "Amman bana hana a dinga biyo ni makaranta ba. Shin wayar hannunki meye amfaninta da ba zaki kirani ba?" "Allah ya huci zuchiyar mijina da girman kujerarka. Wayarce babu kati shi yasa wallahi. Aimun afuwa" Sassautowa yayi kaɗan. Hannu yasa a aljihu ya ciro dubu guda ya miƙa mata. "Kar kiyi dare kinsan ke zaki karɓi girkin dai yau ko?" Murmushi tayi harda wani kallon gefen da Ramatu take tako tsume. Sai ta saki murmushin kissa. "Ni ko nasan ni zan karɓi girki Jannati. Ai kamar yadda kake zumuɗin zagayowar kwanana nima inayi. Ko zaka bani kuɗin cefanen nayo a gida dana dawo girki kawai zan ɗaura"? Hannu yasa a ajjihu ya ciro dubu biyu ya bata. "Me kake so to a girka?" Saida ya ɗan yatutse fuska kafin yace. "Tuwo zaki yi miyar kuɓewa ɗanya kisa nama kona ɗarri biyar ne na gaji da cin shinkafa shinkafa " Miƙewa tayi tana dariya. "An gama harda kifi ma zan haɗa in saka maka. Ni saina dawo. Ramatu na fita" Ciki ciki Ramatu tayi mata saita dawo. Ledarta data ajjiye a ƙofar ɗakin ta ɗauka yara na biye da'ita taima matan gida sallama. Gidan dillaliya ta shiga. Tako yi katari babu kowa a gidan dillaliya kamar ma fita zata yi. "Ƴar Shuwa kece da hantsi haka ta samu kenan?" "Uhm dillaliya duk wanda kika gani a gidanki ai siya ko siyarwa yazo yi. Tukunna ma dan Allah an samu kulolin kuwa?" Dillaliya tace. "Bana kuloli sunyi wuyar samu waɗanda na samu gaskiya masu tsada ne irin na ƙarfennan dubu har ɗari da goma. Jiyannan kishiyarki ta siye su wallahi. Idanu Ƴar Shuwa ta zare harda dafe ƙirji ta furta. "Na shiga uku. Kikace fa dubu ɗari da goma kuma Ramatu ta siye dama Ramatu na da kuɗi haka?" Dillaliya ta fashe da dariya tace. "Ki dai zauna ta fiki fada. Kinga tun lokacin da kika haɗo kan kulolinki duk kika siyar ɗayar mai shegen tsadan saida nace miki kada ki siyar amman kika ƙi ji. To ga kishiyarki tasai waɗanda suka fi naki tsada kuma babu mamaki dan tasan kina da sune. Waɗannan fa in sababbine zasu iya yin ɗari huɗu ma" Ƴar Shuwa duk saita ruɗe abubbuwa suka caɓe mata goma da ashirin. Atampopi biyu ta zaro ta miƙa ma dillaliya tana haɗiyar yawu. Bayan dillaliya ta gama jujjuyasu saita buɗe jakarta ta zaro dubu sha uku ta ba Ƴar Shuwa. "Haba dillaliya bafa kayan sata bane. Ya atampopina masu tsada zaki mun haka?" Kuɗin ta miƙa ma Dillaliya ita kuma ganin haka yasa tace. "Kai daɗina dake gajen haƙuri yanzu iyakar abinda ke wajena kenan. In kika dawo ki biyo Allah bashi na sama miki wasu kulolin kinga sai mu wanye. Dariya Ƴar Shuwa tayi tace. "Dillaliya kin yarda dai ina binki bashi ko?" Dariya suka saka duka. A tare suka fito har titi daga wajenne kowacce ta kama gabanta. Rai babu daɗi Ƴar Shuwa ta shiga gidansu da sallama an je munafurci.

MRS BUKHARI

Gobe bazan samu zarafin turowa ba haka jibi ma sai zuwa talata in Allah ya kaimu cikin masu rai Aimun afuwa bani da lafiya ne yanzu haka ma daga asibiti muka dawo. Nagode sosai son so💪🏼 [8/18, 7:50 AM] BADA'AT IBRAHIM: IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA UKU SHAFI NA GOMA SHA BIYU

*KUYI HAƘURI BA KULLUM ZAKU DINGA SAMU BA HAR SAINA SAMU LAFIYA NAGODE SOSAI*

SABUWA:.

Idanuna ban buɗesu ba har saida na jiyo amon muryarsu Mardiyya. Malama ta faɗo jikina tana kiran sunana. Naji jikinta kau da zafi. Da sauri na miƙe zaune kaina ya wani mugun sara mun har saida na dafe. Mardiyya bata da lafiya ne Malama?" Dawowa suka yi kusa dani dukkansu sai tattaɓani suke yi. "E Ummi bata da lafiya mura da zazzaɓi take yi amman Baba ya siyo mata magani. Yace ma da yamma zai kaita asibiti. Ummi ina kikaje dan ALLAH kada ki sake tafiya ki barmu" Murmushi kawai nayi musu. Aɗɗa'u yace. "Maman Fatima kullum saita dake mu kuma taita tsine miki Ummi." Adama tace. "Zata rina. Ƴar abu ta kazan... Zan rakaku gidan in zaku koma wallahi sai munyi kare jini biri jini da'ita dan Yar Shuwa zuma ce sai da wuta." Nan wannan yace wannan wannan yace wancan. Ni dai ina maƙale da yarana. "Ummi baki da lafiya ne kin rame sosai?" Mardiyya bani da lafiya tun ranar dana barku ina kwance ne a asibiti ko gane wanda yake kaina bana yi." Nan yaran suka shiga aikin yi mun sannu da jikina. Rakiya ce ta aiko ai kiranmu dukkanmu. Miƙewa mu ka yi muka ɗiba yuu zuwa gida. Gaza na tsakar gida ya gwafe sai wanke kaya yake yi. Ga wasu lesuka ya dauraye harya shanya. Naga ga wata mata mai kama da ƴan daba taci riga da wando ta ɗame a zaune a gefenshi tana ta shafa kan Rahine. Ga magina a cikin gidan sun tayar da ginin ɗaki harma an gama zance dan baifi bulo ɗaya za'a ɗaura ba a kashe ginin. "Allahu Akbar kaga Lolo Sabuwa mai sabon aiki ba ehh ashe kin samu kanki yarinya kin waiwayo gida? Bafa zan ɓoye miki ba gara da kika dawo duk tsiya ku mata ne kar ku sake ku shiga bariki gara ku zauna ehh a gabansu Rakiya kuyi duk wacce zaku yi. Duk da ehh na sani da gabansu da Bariki duk ɗaya amman ko yayane zasu yi muku garkuwa dai" Maigogul dake zaune akan turmi yana yanka nama yace. "Loko kizo ki shirya su Adama sui miki rakiya gidanki dalilin kiran da Rakiya tayi miki kenan tun kafin uban mijinki yazo kinsan zaice miki ki koma ɗakinki dai kafin a gama shari'ar da kika nace" Na buɗe baki zanyi magana Gaza ya daga mun hannu tare da tsame hannunshi a wankin. Wuƙa ya zaro a kugunshi ya shiga kartawa a wani ƙaton dutse da muke zama. "Inaaa wallahi Allah daya ne Lolo ba zata koma gidan wancan ɗan akuyar ba. Ko abinda ya faru a kotu wallahi Ni Gaza dan bana gidannane da bazai faru ba. Nifa zan kashe Babangida uban kowa ma ya huta wallahi. Ehh jibi yarinya yadda ta fita hayyacinta har ta gudu ta bar gida yanzu ta dawo ace zata koma. Ai ko shine autan maza ehh gara ta zo ta zauna tunda ba dole bane sai tayi auren ba. Dattijo a wannan karon fa Babangida zai iya rasa ranshi in baiyi sakinnan ba, wai anya kuwa ba'a caca aka ciyomu ba kuwa? Ƙiyayyar da kuke ehh mana tun muna yara ai ta isa. Ke Lolo ki shiga ki zauna ki bararraje." Maigogul yace. "Inta bararraje kai zaka ɗauki nauyinta ashe ko?" "To saime tunda kai ba iyawa zaka yi ba saita rataya ai a wuyana. Su kuma waɗannan yaran su bar gidannan tun kafin in yankasu Wallahi kar su sake zuwan mana gida. Ku kuzo ku fice kafin in yanke ku ehh" Da sauri ya nufo kanmu. Matar dana gani a gefen Gaza da bansan wacece ba itace tayo carab ta riƙe wuƙar tana magana da muryan dabanci. "Ahh huce Gaza ai su yarane kuma basu da lefi a kan komai. Zasu koma shima ubansu bazai bari su dawo nan ba. Eh su Maigogul a dinga sassauta musu iyayene koma yayane eh ba zaka so mu haifi Maigogul ƙarami yazo yana sa'insa damu ba" Kaina a ɗaure cikin rashin kuzari nace. Gaza wacece wannan ɗin?" Ihu yayi da wuƙa a hannunshi yana jujjuyawa kafin yace. "Wallahi aure nayi fa Lolo da aurena na baro gidan yari ma kinji rabo. Kin ganta nan ƴar amana ake faɗa miki mace mai haƙuri da kulawa. Kayanta nake wankewa ma kuka shigo. Wallahi baki ga kulawa ba lokacin ina kotu harda nama take kawo mun. Allah kin ganta da aikinta gandiroba ce mai tsaron ƴan balaja'u. Idanu na zare kawai ina mamaki. Rakiya tace. "Ai sai ku koma tunda Gaza ya ɗaure miki baya zaki bijire mana." "A_a kada ki ja magana Rakiya a bijire take fa dama. Wai yau aka saba wannan rikicinne. Ku dan abu ta kazan... Kuzo ku bar gidannan nan ai ba gidan ubanku bane" A gigice Mardiyya ta riƙe hannun ƙannenta suka fita. Juyawa nayi na bisu a baya na jasu zuwa gidansu Adama. Ina jiyo ihun Gaza yadda kuka san mahaukaci wallahi. Yaushe ma dan Allah ƙwaƙwalwata zata huta a gidanma. Maigogul sai donna zagi yake yi shi kuma, girki ma yake yi yau a gidan. Ku zauna anan nima yanzu zan dawo" Nan na barsu na koma ciki na tadda matar Gaza a cikin su Adama a ɗakin Rakiya harda Gazan sai labari suke ana dariya. "Lolo kinga gini inayi ko? Madamsy nake ma gini kinsan bata tare ba har yanzu tana kwana dasu Rakiya ne." Allah sarki Allah ya baku zaman lafiya" Murmushi tayi tare da cewa. "Ameen ai Lolo tun a gidan yari Gaza yaita bani labarinku Sai bayan da mukai aure ya fito sai muka zo muka tarar ba'asanma inda kike ba. Amman yanzu me ake ciki dangane da makomar auren naki?" Adama ce ta basu labarin na sake shigar da wata ƙarar harma an kaima Babangida sammaci. Gaza yace. "Bana wallahi in dai Babangida bai bini a hankali ba saiya rasa rayuwarshi. Nifa Lolo da zaku yarda sawa zanyi a kamosho in saka mishi wuƙa a wiyanshi wallahi sai ya sake ki. Ko in kasheshi kya yi idda ne ko takaba oho dai. Uban kowa ya huta. Su su Maigogul babu abinda suka saka a gabansu sai son kudi. Ku duba yadda duk muka zama ƴaƴa duk babu na gari" Rahama ce tayi carab tace "Gara ka bari abi matakin Shari'a tukunna. Yaci albarkacin ubanshi da ƴaƴanshi Gaza. Na roƙeka kada ka aikata abinda zaka sake komawa gidan yari ga madamsy nan ka barta da wa?" "Ahh in barta da Allah mana. Wai ke Rahama an faɗa miki tsoron gidan yari nake yi? Naci dubu wallahi sai ceto. Wallahi ke wuya a Lagos wuya a kwatano, wuya a tafa wuya a mararraba, wuya a shagamu fa." Madamsy ce ta shiga yi mishi kirari yana ƙara botsarewa da ƙyar suka harhaɗu aka bashi haƙuri daya tsaya abi matakin kotu tukunna in hagu ta ƙiya a wannan karon dole ayi dama. Ni dai da ba daɗin jikina nake ji ba na miƙe na fito ni dasu Labbai zamu koma can ɗakinsu. "Lolo zan samu dubu uku a hannunki zanyi kuɗin motane wallahi kun ganni baƙi zanje tasha in taro zan kaisu ges house ƴan kuɗaɗen jikina dasu nayi girki." Maigogul ke magana yana gaban murhu yau dai shi yake girki a gidan duk da ba wani sabon abu bane. Yayi gwafe_gwafe a gaban wuta jallof sai ƙamshi take zubawa wallahi saida yawuna ya tsinke" To zan aiko maka dashi" "Allahu Akbar kaga ƴar albarka wacce aka haifa tsiya na bacci. Lolo ta Maigogul Allah yayi miki albarka. Ba zaku tsaya kuci abincin nawa bane? Duk da baƙi na dafama. Bari in zubo miki ke kaɗai zaki samu arzikin cin abincinnan Lolona uhm bana so kina damuwa Lolo kin ganni nan Hamshaƙin garnaƙaƙin mai kuɗi nake miki fatan ki aura. Lolo kika auri mai kuɗi dani zaki tafi ai bazan iya zama ba" Ya tashi harda ɗan gudunshi ya zari kwano a kwando ya zuba mun da dama kuwa ga nama an yayyanka ƙanana abinci sai ƙamshin kori yake yi. Hawayene masu zafi suka zubo mun daya tawo da sauri ya bani kwanon. Madadin in amsa sai na faɗa kafaɗarshi na fashe da wani irin kuka mai tsuma zuchiya. Shiru Maigogul yayi yana riƙe dani da hannu ɗaya ga abinci a ɗayan hannun nashi. "Aikin banza da wofi yanzu nan har Maigogul ya kai irin wannan uban a wajenki Lolo? " Cewar Rakiya. Ɗagoni yayi yana share mun hawaye da gefen malum malum ɗinshi yana wani irin murmushi. "Lolo kiyi haƙuri ki dena yawan kuka ni Maigogul ina tare dake har abada. Zaki yi albarka zaki samu rayuwa mai kyau a gaba. Amshi abincinki kije kici ki ƙoshi" Amsa nayi na kalleshi muka yi murmushi. Sai kawai ya amshi kwanon ya sake zuba mun abincin na karɓa na fita Rakiya sai shewa take yi. Da muka isa ɗakin su Labbai saina buɗe kayana na zaro dubu shida naba Sadiya ta kaima Maigogul dubu huɗu Rakiya dubu biyu. Abincin daya bani kuma nasa su Mardiyya a gaba suka ci. Saida suka gama na aiketa ta siyo biredi suka kara da shayi. Ganin lokacin shan maganina yayi ne yasa nima na sha shayin na warwatsa magungunana na jingina da bango ana ɗan hira ina saka baki sabida in ƙwarara kaina. Hmmm wajajen huɗun yamma muka jiyo sallamar yaro wai ana sallama da Sabuwa inji wani mutum a ƙofar gida. Ina kyautata zaton Yaya Kamilu ne. Wanka na fito da sauri na soma saka kayana. "Mardiyya kije ki ce ma mai kirana ganinan fitowa likitane shi ya taimakeni a asibiti kuma shi yaita biyan komai na maganina" Na faɗa mata ne tun kafin su zargi wani abun su soma tuhumata ko in bar ƙwaƙwalensu da hasashen da bansan wanne iri bane. Fita tayi a nutse nima na samu zarafin shiryawa na zura hijabina na ja hannun Malama muka fito. Ai kuwa shi ɗinne yana jingine a bakin motarshi Mardiyya na gabanshi yana mata tambayoyi tana amsawa na isa da sallama. "A_a Sabuwa har kin warware an shiga cikin ƴan uwa ko?" Dariya nayi mishi kawai. Ya yafito Malama halamun taje. Sakinta nayi taje suka gaisa yake tambayarta ita izufinta nawa tunda yaji Mardiyya tayi sauka" "Sabuwa ashe yaran namu malamai ne dan ko ni babu sittin a kaina akwai dai arba'in." Murmushi kawai nayi Mardiyya ta kama hannun Malama zasu koma ciki yaa kirayi sunanta. "Mardiyya tsaya ku shigarma da Ummi kaya" Both ya buɗe ya zaro manyan fararen ledoji ya miƙa mata. Tana kan karɓa na hango Babangida yana daidai ƙofar gidanmu yana tawowa idanunshi a kaina ƙem. Har su Mardiyya suka shige bai ƙarasoba. Isowarshi ke da wuya sai cewa yayi "Sabon farka kika samu shine kika yi ƙaryar kurumcewa kika gudu kika bar gidan aurenki da yaranki, kika tafi kika barni da kewarki da tunaninki ashe? Malam dan abu ta kazan ubanka... Bata faɗa maka tana da aure bane? Ko da yake son zuchiya bazai barka ka tuno wannan ba. Nine mijinta wanda zamu ƙare rayuwarmu tare" Kawai saiya cukume Kamilu. "Ki shige gida Sabuwa wallahi ko in miki dukan tsiya na rantse tunda baki da mutunci matar ƙaddara maras kamun kai ko ki koma ciki ko ni dashi muyi mutuwar kasko wallahi" Kamilu yace. "Sabuwa shige gida abunki zanyi mishi bayani" Ina Babangida da dambe ya kama Kamilu Ni Ko nasa hannu aka na kwarmata ihu dan na fahimci Babangida ranshi yayi mugun ɓaci sosai yafi ƙarfin Kamilu. Ai kuwa jama' a kamar jira suke yi suka fiffito ciki harda su Adama. "Tabb Lallai Babangida abun naka yakai Labbai maza kirawo Gaza yazo ya raba wannan faɗan. Ina gefe ina kallo kukanma yaƙi zuwa mun dan nasan bama a soma komai ba. Ina buɗe idanuna na hango Ƴar Shuwa na tawowa wajenmu. Gaza kuwa a guje ya tawo matarshi na biye dashi. Su Rakiya ma sai gasu afujajan babu ko mayafi. Yana isowa yasa hannu ya ɓanɓare Babangida a jikin Kamilu faɗa ya koma a tsakaninsu. Babangida ya naushi Gaza 'Gaza ya rama. "E lallau yau sau nayi ajalinka wallahi wai ni ka fasama baki Tabb yau zaka gane waye Gaza" Wuƙa ya zaro kamar ƙibtawar idanu ya yanki Babangida, Babangida idanunshi sun rufe da kishi sai tijara yake yi. Madamsy ce tayi saurin shiga tsakaninsu. Ƴar Shuwa ganin jini na fita a jikin Babangida yasa ta dinga danna ihu kowa da kowa ya fito. Da ƙyar faɗan ya lafa da taimakon mutane, da taimakon su Rakiya da suke ta cakume Gaza. Maigogul dai baya nan. Sun sha naushi in nausa da Babangida sosai shi kuma Gaza ya yayyankeshi a waje kusan huɗu ga jininshi nan kaca kaca. Kamilu yana riƙe da hannun Gaza ga dattijai anata bashi haƙuri. "To naji amman ya bar unguwarnan kuma kada ya sake zuwa layinnan da sunan zuwa wajen ƙanwata wallahi ko yaranshi na gani sun zo gidanmu saina illatasu. Ai kai ƙaramin dan abu ta kazan ubane mu iyayenka ne yaro a iskanci." Babangida na ɗaure hannunshi da ɗan kwalina daya faɗi yace. "A fito mun da yarana to. Kuma wallahi ko mutuwa kuke yi kuna dawowa Sabuwa tawace ina son matata sonta a jinin jikina da jijiyoyina suke yawo bazan saki Sabuwa ba sai dai duk abinda za'ayi ayi Kai kuma wallahi bazan taɓa yafe maka hakkina a kanka ba." Gaza sai ihu yake yi ganin matarshi shi ya hana ya kai Babangida ƙasa. Labbai ce ta tarkato yaran ta turasu gabanshi. Shine ya ja hannayensu suka bar layin. Gaza ya ja hannun matarshi suka tafi. Su Rakiya suka bishi Rakiya sai ɗebo zagi take tana dura ma Gaza. Shi kuma yana faɗa yana sake rantsuwar faɗanma yanzu aka soma. "Kinga ƙanwata kiyi haƙuri zuwanane duk yaja wannan abun. Ki shiga gida ki tabbatar baki ɗauki damuwa kin ɗaura ma kan ki ba. Kinsan ba lafiya gareki ba. Ashe Babangidan naki mahaukacin zaki ne. Duk da naga halamun makauniyar soyayyar da shi kanshi bai gane soyayya bace a tattare da amonshi ba, amman tabbas yana mutuwar sonki. Ki je zamu yi waya kinji ko?" Kai kawai na ɗaga Adama ta ja hannuna muka shige ciki. Naci kuka kamar raina zai fita har saida ciwo ya bigeni sai Dr Kamilu Adama ta kira bai jima ba ya dawo yaita rarrashina yana bani kalma har dai raina ya ɗanyi sanyi amma fa ba sosai ba gaskiya.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull