Idan kaya ya gaji book 3 - Chapter 12
Idan kaya ya gaji book 3 Chapter 12: Idan kaya ya gaji book 3 Chapter 12. Babangida:. Yana tafe su Mardiyya na binshi a baya ya riƙe hannunshi da ɗankwalin…
4,854 words
Babangida:. Yana tafe su Mardiyya na binshi a baya ya riƙe hannunshi da ɗankwalin Sabuwa wanda ya jiƙe da jini sharkab. A guje ƴar Shuwa ta biyosu lokacin har sun hau abun hawa. "Baban faty ashe dama zaka iya zuwa wajen Sabuwa matar da tabi tsohon saurayinta. Bayan data dawo kuma ta wuto gida kai tsaye. Inaga dai bokancin Sabuwa da mahaifinta yayi tasiri a kanka dan bokace ita da ubanta nasan baka san wannan ba" Kallonta a matsayin mahaukaciya Babangida yake yi. Idanunshi a mugun rine ga yaranshi jikinsu duk yayi sanyi . "Malam ja abun hawannan mu tafi kaji ba hankali bane da'ita" Ƴar Shuwa tace. "Tafiya zaka yi ka barni wai?" "Ke in kinga dama kema kiyi zamanki a gidanku. Ba Sabuwa ba ko wacce macen ma ta fice mun a raina gayyar tsiya" Da faɗa yake maganar dan a mugun hasale yake. Fuu abun hawan ya wuce ya bar Ƴar Shuwa tana sheƙa dariya a titi. "Ai wallahi Babangida ko tsirara zanyi yawo dolen dole saika rabu da Sabuwa har shegiyar ƴarta sai ta bar gidanka domun ba Yarka bace. Ai tunda Sabuwa ta kwace mun Khalid to dole ta rabu da Babangida. Kuma saina saka mata baƙin jinin da ko kallonta wani ɗa namiji bazai kuma yi ba wallahi sai dai ta dawwama a gaban shegun iyayenta Khalid kuma saina rabasu ya dawo hannuna domin tun kallon farko ni Khalid naso ba abokinshi ba." A titi Babangida yasa aka sauke su Mardiyya shi kuma ya wuce kemis aka wanke mishi wajen yankan a can layinsu. Kai tsaye gidam Kawu Manga ya nufa. Yana shawo kwana ya hango Kawu Manga tare da Baba Malam a ƙofar gida harda Sa'a tana gurfane a gabansu. Baiso Baba Malam ya ganshi a wannan halin da yake ciki ba amman babu yadda ya'iya haka ya nufesu. ",ina wuni Baba Malam yaya kufan jikin naka?" Baba Malam sai ya yinƙura da ƙyar ya miƙe. "Manga zan shiga daga ciki in kwanta. Ke kuma Sa'a duk bijirewar da zaki yi daidai ne. Sauban ai ɗanki ne kina da ikon zaɓa mish mace ta gari kam ai naki da sauƙi akan abinda ƙaninki ya aikata ai duk wata ɓaraka daga wajen mahaifiyarku ne" Yana kaiwa nan ya shige. Ai kuwa yana shigewa Sa'a tace. "Duk Babangida ne ya ja mana bala'innan. Ni kuma taya ina kallo ɗana zai auri yarinyar da aka sameta bata hanyar aure ba. Da uwar ƴar da uban ƴar duk gasu ga kamarsu. Inace ita uwar wajen saurayinta ma ta gudu da aurenta..." "Yafa isheki Sa'a. Ki sani nima daga yau na soke maganar auren Sauban da Mardiyya. Ƴata ko zata rasa miji ni ni kaɗai ubanta na isa in sanyata a farin ciki. Kawu zan koma dama nazo in sanar muku Sabuwa ta dawo, amman gidansu ta wuce kuma ta sake mayar dani kotu" Yana gama faɗin haka ya wuce yana jin tsabar jiri tamkar ya faɗi. Da ƙyar ya iya kai kanshi gida. Ɗakin Sabuwa kai tsaye ya shiga bai zarce ko inaba sai kan gado ya kwanta yana shaƙar ƙamshinta wani al'amari na bijiro mishi a zuchiyarshi game da sabuwa shi ba ƙiyayya ba kuma ba jin haushi ba. Kiran wayar Sumy ce ta dawo dashi hayyacinshi wanda yayi daidai da kiran sallah azahar da aka soma a masallacin unguwar. Ɗaga wayar yayi a sanyaye. Yana ɗauka yace. "Sumayya bari inje masallaci inna fito zan kiraki" "To shikenan ina fa jiran kiranka ato dan ina da magana fa ato." Kai kawai ya gyaɗa ya kashe wayar ya mayar aljihunshi ya fito falo. "Aminu kuyi alwala bari in sake kaya sai mu je masallaci ko?" Sai da ya sake taɓa jikin Malama kafin ya fita har zuwa lokacin da zazzaɓi kau a jikinta. Shi sai yake jinma kamar zazzaɓin ƙaruwa yayi. Dole ma ya ƙaru ai irin wannan jafa'in daya faru a gabansu ai dole ya sake assasa hauhawar zazzaɓi. Ɗakin Ramatu ya shiga ya ko tadda ɗakin maƙil da mata. Sabida haushi kawai sai ya fita ya nufi ɗakin Ƴar Shuwa ya saka ki ya buɗe ya shiga. Yana tsaye a cikin uwar ɗakinta zai cire kaya Ramatu ta shigo. "Haba ranka ya daɗe ya zaka shigo nan kuma alhalin kasan nice nake dakai har sai anyi la'asar girkina zai fita.?" Ƙur yayi kawai yana kallonta yama rasa mai zaice mata. Sai a lokacin ne taga yankan dake tafin hannunshi dana wuyanshi mammanne da filasta. "Subhanallahi wannan ciwon kuma fa daga ina haka?" Wucewarshi banɗaki yayi ya sakar ma kanshi ruwan sanyi kawai idanuwanshi a lumshe yana hango Sabuwa a gaban Dr Kamilu harma da yaranshi. Kanshi a mugun ɗaure yake ga tambayoyi cike a bakinshi ko ya fesar babu mai bashi amsarsu. "Wato Sabuwa dai na lura ajalina take so tayi ta huta. Ko wanne ɗan iskan ta kuma samowa oho. Kuma iyayenta da ƴan uwanta suka mara mata baya. Ni Sabuwa zata ci ma amanar Aure?" Lafiyayyen hannun ya doka a bango yana jin wani irin ƙaikayi a zuchiyarshi. A gaggauce ya dauro alwala ya fito. A zaune fa a bakin gadon ƴar Shuwa ya fito ya tadda Ramatu. "Ki tashi ki fice mata a ɗaki. Ai da tana nan ko labulen ɗakin baki isa kin riƙe ba balle har kima kanki masauki a kan gadonta ko? Bana son neman jarfa ki barni da damuwar dake damuna dan ALLAH" Jikinshi ya goge harya sauya kaya Ramatu bata fita ba tana kallonshi baki a taɓe. "Wai shin har sai zuwa yaushe zuchiyarka zata dena wahalaka akan Sabuwa ne. Oho wato wannan ciwon ma ƴan gidansu ne suka sake ji maka amman ka saketa kaƙi sakinta. To ma dame tafi ragowar matan daka dinga saki in banda farar fata. Tsinka mata mari yayi mai zafi A ɗakin ya barta a tsaye yayi ficewarshi. Shine dai ta biyoshi ta fito tana riƙe da kunci Masallaci suka wuce da yaran ana idar da Sallah ya dauki Mardiyya da Malama a mashin sai asibiti. Ai kuwa suna zuwa akace ciwonta ne ya tashi babu shiri aka basu gado da gaggawa. Daga shi sai Mardiyya a asibitin har zuwa bayan la'asar kuma ya kira Malama Babba ya sanar mata a tunaninshi zata turo a zo a zauna dasu a asibitin shi kuma ya tafi neman kuɗi sai yaji shiru. "Mardiyya ki zauna da Malama ina zuwa yanzu ɗaya daga cikin Ummanku zata zo ta zauna da Malama su kwana ke kuma inna dawo sai in mayar dake gida" "Toh Baba sai ka dawo Allah ya tsare" Har wani tashi kan Babangida yayi sabida tsantsar daɗi. Yana tafe yana lissafi har ya karasa gida. Bai shiga gidan ba sai da akayi magriba tukunna. Ɗakin Ƴar Shuwa ya nufa kai tsaye ya taddata a kitchen tana tuƙa tuwo. Bai kulata ba ya shige ciki, itama babu abinda tace mishi har saida ta gama tuƙa tuwonta kana ta shiga ta sameshi yana waya da Mustapha yana labarta mishi an ba Malama gado. Sai da ya gama wayar tas ya sauke kana ya dubi Yar Shuwa da tayi ƙuri tana kallonshi. "Ki haɗa abinci a kula zan kaima su Mardiyya a asibiti Malama aka ba gado. Sannan inason ki zuba ruwa a filas" "Kash gashi abincin daidai cikinmu da yarana na girka sai kuma naka. Ruwan zafin dai tunda da wuta bari in ɗaura a hita yanzu." Ficewa tayi ta jona ruwan a ƙaramar robar fenti tana tsaye tana jiran ruwan tana magana a zuchiyarta ko kuma ince saƙa mugun saƙa. Biyota yayi ya dubeta suka haɗa idanu tayi kwalliya da ƙananun kaya tayi kyau sai ƙamshin humra take yi. "Ki haɗa nawa abincin a kula bari in samu Ramatu dan ita zata kwana dasu." Nanma bai jira abinda zata ce ba ya shiga ɗakin Ramatu ya taddata suna cin abinci ga TV suna kallo ko ina kaca_kaca ga kayan ɗaki har kaya amman Ramatu irin matannanne da ba ko yaushe suke gyaran daki ba. Duk randa taso gyara wa dai zata gyara komai ta ajjiye komai a muhallinshi. Jallof ɗin shinkafar manja da alaiyawo suke ci da ruwansu ɗan kamface a gabanta. "Lafiya naga ka shigo ɓangarena kaga kar kasa jarababbiyar matarka ta biyoka" Murmushin takaici kawai yayi. "Ki gama cin abincin zan kai ki asibiti zaki zauna da Malama bata da lafiya an bata gado." Idanu ta ware amman da suka haɗa idanu taga ya murtuke fuskarshi tamau bata ga fuska ba dole ta hadiye maganarta ta kora da ruwan sanyi " Sallar isha da aka soma kirane yasa ya tashi tsaye. "Ki tsimtsa kafin in dawo sallah sai mu wuce. Su kuma yaran ki miƙa su wajen Aisha ko ki miƙa su ɗakinsu Mardiyya" Yana faɗin haka ya saka kai ya fita. Tare suka je masallaci da su Aminu. A cikin masallacinne yake sanar musu Mardiyya na asibiti tare da Malama. "Amman kunci abinci.?" Aminu yace. "E na dafa mana farar shinkafa dama muna da miya" "To akwai ragowar abincinne ka zuba sai a kaima ita Mardiyyan? Kafin Aminu yayi magana ma yace ya barshi kawai tunda a gida Mardiyyan zata kwana. Suna shigowa ya karɓi abinci da filas ɗin ruwan zafin a cikin basket ƙarami. Tun daga tsakar gidan Ramatu ta hau mashin ɗin tana riƙe da basket ɗin abincin aminu ya buɗe musu get suka fita. Mardiyya na zaune ƙwalam ta hango Babansu da yadikkonsu ajjiyar zuchiya ta sauke. "Mardiyya yaya jikin na Malama ta farka kuwa?" "Ta farka Baba tana ta kuka tana kiran Ummi ni kuma wayata babu kati ban kira mata Ummin ba. Likita ma yace in ka dawo yana son ganinka." "To shikenan bari naje. Ramatu bata abincin taci sai in zo mu tafi." Ficewa yayi. Mardiyya kuma ta tusa wannan tuwo a gaba malmala ɗaya ƙarami da nama tsoka ɗaya ta cinye. Ramatu kuma ta hakimce a bakin gadon jinyar sai hararar Mardiyya take yi. Sauban ne ya shigo da kaya kici_kici harda su lemu da ayaba da abinci kula guda, da ruwa katon guda. "Baba Ramatu ina wuni ya mai jiki?" Sauban cikin girmamawa yake gaishe da Ramatu. A gatsine ta amsa tana ƙarema ledojin daya jibge a gaban Mardiyya ido. Ledar da kular take ciki ya buɗe mata. "Kici abincin kince mun yinwa kike ji ko? Kai ta ɗaga mishi kafin daga bisani tace. "Baba ma ya kawo mun tuwo naci. Sai dai tunda wannan kai ka kawo bari inci kafin mu tafi" Abincin ta zuba a plate lafiyayyar jalof ce wacce taji ɗanyen kifi. Ramatu kanta saida ta haɗiye yawunta. Mardiyya na cikin ci Babangida ya shigo da sallamarshi. Sauban ya kalla ya dubi ledojin daya kawo ya kalli abincin da Mardiyya take ci. Idanunshi ya lumshe yaji wani abu na tafasa mishi ranshi. "Baba ina wuni yaya jikin Malama?" "Lafiya Sauban. Jikinta da sauƙi za'ace. Kaine da wannan hidimar?" Kai Sauban ya sosa tare da cewa. "Ah ai wannan ba komai bane" Zama Babangida yayi a farar kujera. "Mardiyya zubo mun in ɗanci kafin mu tafi" Mrs Bukhari
#Team Babangida #Team Sabuwa #Team Gaza #Team Maigogul [8/19, 7:41 PM] BADA'AT IBRAHIM: IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA UKU SHAFI NA GOMA SHA UKU
Harta ciro kwano zata zuba mishi sai yace ta zuba mishi a cikin kwano da taci. Ko data zuba mishi bai wani ci sosai ba. Ta miƙa mishi ruwa yasha sai yace. "To Sauban mu fa tafiya zamu yi Ummansu ce zata zauna a wajenta. In kaje gidan ka gaishe da Sa'a" Tare suka fita dashi Mardiyya ta hau mashin ɗin Babangida Sauban ya shiga motarshi kowanne ya nufi gida. Saida Babangida ya jima tare da su Mardiyya a ɗakinsu kafin yayi musu sai da safe ya nufi ɗakin Ƴar Shuwa yana murɗawa yaji ta kulle ɗakinta saida yaita bugu kafin tazo ta buɗe mishi ya shiga. Yana zaune a bakin gado tunani yayi mugun yi mishi yawa sai ya jiyo muryar Ƴar Shuwa a kanshi. "Aina ɗauka acan dukka zaku kwana a wajen ita yarinyar shi yasa ma na kulle dakina. "Zauna muyi magana ɗake" Fuskarshi a mugun murtuke take babu ko wasa dis a fuskarshi, sai jikinta ya mutu. Zama tayi a kusa dashi tana saurarenshi. "Da farko inaso in tambayeki ki tabbatar kin faɗa mun gaskiya in kikai mun ƙarya ranki zai ɓaci kuma zan saɓa miki" A sanyaye tace. "Ina saurarenka" "Kulolinki ina suke danna lura kin dena saka mun abinci a kula. Sai yau naga wata koɗaɗdiyar kula a ciki kenan kika zuba mun abinci, sannan ina kika samota dan ni ban sanki da wannan kular ba naga kuma ba sabuwa bace." Gabanta ya faɗi ras da jin abinda yake tuhumarta akai. Dama tasan za'a rina shi yasa tun kafin azo hakan taso ta samu kula ta siya ko sakan ko sabuwa mai ɗan rangwamen kuɗi. Ita kanta jin Ramatu ta sai kula mai tsada ya matuƙar ɗaga mata hankali. Gashi shima ya tare ta da maganar. "Kulolin suna gidanmu ne da ragowar kayan wutana sabida kaga kitchen ɗina babu kanta ga ƙanƙanta kulolina manyane ba zasu zauna a kitchen ɗin bane." Ƙur yake kallonta. "Sai kuma kika kasa cire mun kular da zaki dinga zuba mun abinci a ciki? Sannan har sai kin kai kuloli gidanki ga ƙarƙashin gado ga store naga tarkace ne a ciki me yasa baki ajjiye a ciki ba" Tsuru_tsuru tayi mishi. Shi kuma bai yadda da abinda ta faɗa mishi ba. Shi zarginshi siyarwa tayi tayi hidimar bikin ƙanwarta dasu dan yaga ta dinka kayayyaki manya harda su takalmi da jaka. Kuma hakanne a dalilin bikinne ta harhaɗa ta kaɗar dasu sabida ta fita kunya dangi suna ganin tana auren mai kuɗi ace an tashi bikin ƙanwarta ba'aga tayi bajinta ba har ƙaramin zobenta na gold saida ta siyar duk a bikin dan kawai tayi bajinta. "Hmmm ki kira waya gobe a dawo miki da wasu kulolin na faɗa miki kenan. In kin fahimta ni namijine mai son kula ɗebi da kanka wannan tsarinane kuma kin sani ba tun yau ba. Magana ta biyu itace me yasa inna bada kuɗin gawayi sai in dawo in same ki kina girki da risho." "Ai Ramatu ma a rishon naga take yi" A tsawace yace. "Yanzu dake nake yi ba Ramatu ba. Ko so kike mu kafa teburinta a ɗakinki? Wato na fahimci rayuwar ƙarya daga ke har ita kuke son yi. Bazai yiwu kuje ku jawo mun jarfa ba. Ni na rungumi ƙaddarata ace ku matana kun kasa ɗaukar ƙaddararku kullum ƙorafinku kifi nama, ko ban bada kudin kifi ko nama ba sai in dawo in gani a girkinku alhalin nasan ba sana'a kuke yi ba. To wallahi in kuna son zamanku lafiya ya zame muku dole ku dawo cikin taitayinku. Duk da a cikinku duk sabida kuɗi kuka aureni Sabuwa ce kaɗai a lokacin dana aureta ƙarma ƙarma kawai nake yi. Kuma daga yau dole a haɗe girki duk wacce take da miji zata yi girki na dukka gidan har da su Mardiyya" Baki zata buɗe tayi magana a zafafe ya nuna mata yatsa. "Kimun shiru maras kunya fitsararriya kawai sai in fasa bakin ki Allah. Bar ganin nayi sanyi ki zaci zan ɗauki take_ taken iskanci wallahi ƙaryane. wallahi baku isa ku juya ni yadda kuke so ba wannan doka ce na kafa daga gobe ki ɗaura girkinki da kowa." Yana gama wannan maganar ya haye gado yayi kwanciyarshi. Shinfiɗa ta fita falo tayi ma yara ta dawo ta juya mishi baya a gado. Cikinsu babu wanda yayi bacci sai tubkewa da warwarewa suke yi. Ita ta ƙuduri niyyar gobe sassafe zata je ta kai ƙaranshi wajen Malama Babba dan tayi rantsuwar ba zata taɓa haɗa girki da kishiya ba har taci abincin kishiya ba Shi kuma Babangida da tunani biyu ya kwana tunani na farko na sabuwane da wannan namiji daya gansu tare. Sai kuma Malama dake gadon asibiti. Har mafarki yayi Sabuwa ta dawo cikin rayuwarshi suna ta zuba soyayya harma sun sake samun karuwar ɗiya mace mai kama da Mardiyya sak. Farkawa yayi da asuba sai yaji zuchiyarshi ta sake yin nauyi sosai. Yana dawowa sallar asuba sai yayi wanka ya kintsa Ƴar Shuwa tana gado tana baccin asara. "Aisha ki tashi ki dafa shayi zan siyo kayan tea" Cikin magagi ta amsa mishi amman harya dawo bata tashi ba. Ga yara a falo sai kawai ya juna ruwa a hita ya tafasa ruwan tea ya soya musu ƙwai. Ya zuba nasu Mardiyya ya cika musu jug da tea ƙwansu ya zuba a kwano ya kira Aminu yazo. Daidai futowar Ƴar shuwa daga ɗaki tana muƙa. Da kallo tabi Babangida da Aminu da aka miƙa mishi jug. Yawu ta haɗiye muƙut bata ce uffan ba ta koma ciki. Da kanshi ya sallami yara tsab, ƴan asibiti kuma ya ware musu nasu harya zuba a basket. Yana gama karyawa ya miƙe ya ajjiye mata kuɗi nera dubu biyar. "Ga kuɗin cefanen rana dana dare dukka ayi da ƴan asibiti" Ficewarshi yayi baibi ta kanta ba. Itama ko a dawo lafiya bata ce mishi ba. Ta zauna tana ta tunanin ƙila lokacin rabuwarta da Babangida ne yazo dan ita bata tsara rayuwar gidan aurenta a haka ba"
SABUWA:.
Washegari
Sassafe Mardiyya tayi kiran wayar Adama take sanar mana Malama a asibiti ta kwana ba lafiya. Abunka da sha'anin ƴa da uwa sai hankalina ya tashi ba shiri su Labbai suka soma girkin asibiti. Taliya da kifin gongoni suka dafa sai shayi mai kayan ƙamshi ko basket bamu dashi a leda muka zuba komai. Jikina babu ƙarfi nayo wanka tas na zura doguwar rigar kanti daga cikin rigunan da Dr Kamilu ya sai munne. Labbai sai ta saka ɗaya doguwar rigar tawa, Adama kuma ta saka lace muka fito sai ga motar Dr Kamilu a ƙofar gidan isowarshi kenan. Gilashin motar ya zuge yana mun murmushi nima murmushin nayi mishi. Ya ƙurama Adama idanu yana ɗan murmushi. Yaya kaine sassafe haka?' Na tambayeshi" "Kin ganni dai dake na kwana cikin raina. Yaya Adama ina kwananku yaya Lolo da jiki?" Nan dai suka gaggaisa. "Dama nazo in duba jikin nata ne sannan in gaishe da su Mama'" Gabana ya yanke ya faɗi Adama tace. "To sakko mu ƙarasa gidan. Dama asibiti zamu je dubiyar ƴar gidan Lolo karamar jiya a asibiti ta kwana. Ai kuwa ya ajjiye motarshi muka ɗunguma zuwa cikin gidanmu Shigarmu da sallama wallahi sai ji mukai an jefo bokitin roba tabb ya sauka aƙirjin Dr Kamilu. Gaza ne suke damben Allah tsine a tsakar gida shi da madamcy. Ga su Rakiya a tsakar gidan kowanne harkan gabanshi yake yi. Babu wanda ya damu da abinda su Gaza suke yi. Hauwa na gaban murhu tana dumame, gasu Qamriyya a tsakar gidan duka. Rakiya kuma wasu jemammun kayan gado aka kawo mata tana siye. Ga Maigogul a kan turmi yana brosh. Uzairu zuchiyata yana zaune akan kujerar tsugunno yana ta aikin goge ƙafarshi. Su Sadiya kowa na zazzaune babu wanda ya shiga faɗan su Gaza. Illahirin kunya ta kamani da mugun gudu Gaza ya biyo madamsy ita kuma ta nufo kanmu ai kuwa ta bangajeni sai gani a ƙasa jiki dama duk ciwo ya cinyeshi. Gaza sai ɗuma zagi yake tayi. "Ke Rakiya ga baƙo munyi fa" Cewar Maigogul daya nufo mu da sauri. Ni kuma a sanyaye Sadiya ta ɗaga ni na miƙe ina kaɗe jikina. "Bawan Allah kayi haƙuri ka shigo gidan ka tarar anata hatsaniya. Shaye shaye kasan babu abinda baya sawa shi yasa. Wannan rikicin tun dare ake yi da sassafe suka ci gaba da faɗansu duk kamar a bige suke sun ci kai shi yasa. Yanzu da zaka goyi bayan ɗaya sai cibi ya zama ƙari, ƙari ya zama ƙababa shi yasa kaji munyi kurum. Labbai surikinne aka kawo shi Allah yayi kenan? To madallah" Da sauri ya koma da kanshi ya ɗauko tabarma ya shinfiɗa ya riƙo hannun Dr Kamilu suka zauna. Gaza kuwa ya kama madamcy sai dukanta yake yi sai da ya daketa son ranshi kana ya rabu da'ita yayi ficewarshi ma a gidan. A sanyaye Dr Kamilu ya gaishe da su Rakiya da Maigogul kafin Adama ta gabatar musu dashi. Baki Maigogul ya washe. "Allah sarki munfa gode da ɗawainiya wallahi Allah ya saka maka. Itama muna ta lallaɓata ta daure ta koma ɗakinta wallahi kaga taƙi shi wannan mahaukacin wan nasu daya fita ya ɗaure mata baya akan ba zata koma ba. Ƴan uwanta mata duk sun goyi da bayanta. Kafa gansu cike da gidan duk zawarawane zaman auren ya gagaresu dama itace ta samu... Carab Adama tace. "Sauri muke yi Maigogul ƴar wajen Lolo ce babu lafiya zamu je asibiti mu dubota dama gaisheku yazo yayi. "Assha to ai sai mu tafi tare. Kai Uzairu zuchiyata maza sako kaya muje asibiti. Malam Kamilu da mota kake ne?" "E Baba da mota ai sai in sauke ku" "To to shikenan Allahu Akbar bari in shirya ai sai mu tafi baki ɗaya." Ya ƙarashe yana wannan dariyar da in yayi sai inji kamar in haɗiyi zuchiya in mutu. Da sauri ya shiga ɗaki ya bugo kwalliya ya fito yana ta baza ƙamshi yayi kyau tabbas tamkar wani minista ko ɗan majalisar jaha fa haka yake ado komai nashi mai daraja ga kyau Allah ya huwace mishi idanunshi farare tar_tar gashi da suma mai laushi da furfura jefi_jefi. Uzairu zuchiyata shima ya bugo nashi wankan dama dai jirgi ɗaya ne ya kwaso su yasa wani ƙaton takalmi sai sheƙi yake yi hmmm. "Dama nace akwai kayan abinci Yaya Adama a mota ko yara zasu shigo dashi?" Dr Kamilu ya yi maganar yana kallon Adama. Maigogul yayi carab yace. "Muje kaji in kwaso in dire musu sai mu tafi" "A_a Maigogul su Sadiya kuzo muje ku shigo da kayan. Anfa gode sosai" Nan su Rakiya da Hauwa suka shiga godiya. Dubu goma_ goma yaba Rakiya da Hauwa. Ga ƙaton buhun shinkafa da katan na taliya da mangyaɗa an dire a kofar Rakiya. Mu kuma muka shige mota Maigogul yana gaba sai labarai yake ba Dr Kamilu marasa ma'ana, daga yace ƙawarshi ta gari kaza, sai labarin sunje bikin Ƴar gwamnan gari kaza haka dai dama salon hirarshi suke. idanuna na lumshe wasu siraran hawaye suka gangaro mun. Gashi Maigogul sai ƙoƙarin saka su Labbai a hirar tasu yake yi. Suma suka biye mishi sukaita hira har muka karasa asibiti. Muna sakkowa a motar muka haɗa idanu da Babangida. Dr Kamilu kuwa dama bai fito ba yace bazai shiga ba dan gudun fitinar Babangida. Gaba muka yi ni kunya tasa na kasa tsaiwa muyi sallama ma. A guje Maigogul ya biyo bayanmu yana cusa kuɗi a ajjihu bakinshi kuwa har kunne. A cikin ɗakin da Malama take muka tadda Babangida fuskarshi a mugun murtuke gashi ya shigo ya tadda Malama sai kuka take tana kiran umminta. Muna shigowa nayi saurin isa bakin gadon na zauna na rungumi diyata ina shafa bayanta. Sai tayi tsit tana ta sauke ajjiyar zuchiya ta ƙanƙameni sosai yarinyar tamkar tana tsoron kada in gudu. Ana kan gaggaisawa muka jiyo sallamar Baba Malam da Malama Ƙarama da Wawo sun shigo suma da abincinsu niƙi _niƙi. Har ga Allah banso muka haɗu da Dattijon ba domin bana so ya bani wani umarni in saɓa mishi. Yako nuna farin cikinshi da ganina duk da yayi mun faɗa sosai akan kada in kuma tafiya ko'ina duk abinda ya dameni in garzayo in faɗa mishi. "Babangida kaida waccan ku fice ku bamu waje" Babangida dama a takure yake da sauri ya fice. Ramatu tabi bayanshi sum_ sum_ sum. "Maigogul gaka ga Sabuwa dama nayi niyyar zuwa gidan daga asibitinnan sai gashi mun haɗu. A gaskiya roƙo dama zanyi Sabuwa ta dawo ɗakinta tunda labarin ƙarar data kuma shigarwa ya iso mun. Tayi haƙuri in Allah ya cika mata burinta sai ta tafi gabaki ɗaya. Amman yanzu ai ba daidai bane ace tana zaune a gida ba ko ba gaskiya ba?" Maigogul yace. "Wannan gaskiya ne ni da Rakiya munyi munyi da'ita amman taƙi komawa. Kuma tun ranar data bar gidan nata tana asibiti babu Lafiya" Nan ya kwashe labari ya ba Malam Baba harda ɗorawa da cewa. "Yaronne ma ya kawo mu asibiti yanzu yaje gida dan mu gaisa sai dai fa Babangida yazo har ƙofar gidan anyi ɗauki babu daɗi daga zuwa ya runtuma a wuyan wannan bawan Allah ya kamashi da kokawa akaita turzawa. Yaita rantsuwar dai bazai yadda ya saketa ba. In sha ALLAH daga nan in aka sallami yarinyar zata koma gidanta kai tsaye in yaso sai a tafi da Adama da ita Labbai ɗin zuwa yadda shari'ar ta kaya. Har cikin raina bana goyon bayan mutuwar auren Lolo wallahi " Ni dai bance komai ba kuma bana jin a wannan karon zanyi ma Malam Baba biyayya nifa na baro gidan kenan. Kuɗi ya ɗakko masu yawa yace in riƙe a hannuna ya ba Maigogul ma harda su Adama. A taƙaice dai kwanan malama biyar a asibiti muna jinya. Kullum Babangida yana zuwa amman ko ga miciji bama yi ma juna yayi yinƙurin samun damar magana dani nice ban bashi damar ba nace mu haɗu a kotu kawai. Tunda matarshi ta fice a asibitin ranar da muka je babu wacce ta sake tako ƙafarta. Daga dangin Babangida matan babu wanda yazo mazan dai sun zo Sauban ma yanata hidimar kawo abinci dasu lemo da ayaba. Dr Kamilu kuma kullum sai munyi waya ya tambayi jikina. Rana na shida aka sallamemu kuma a ranar ne zamu yi zaman kotu na farko. Ni dai kai tsaye gida muka wuto da Malama dasu Adama duka. Sunyi juyin duniya akan in koma ɗakina naƙi fur. Su Sadiya ma nasa suka je suka tattaromun suturuna da duk wani abu muhimmi suka kawo mun ai kuwa ɗakin dama ba girma ba duk saiya cike. Sha ɗayan rana a kotu tayi mana ni da su Adama da Rakiya Maigogul yace ba zashi wani kotu ba. Sai gani gasu Malama Babba da Sa'a a harabar kotu sun zo suma. Kafin mu shiga cikin kotun Dr Kamilu shi da lauyana suka ƙaraso. Sha ɗaya dot muka shiga ɗakin shari'a. Nan aka gabatar da dalilin ƙarana lauyana ya zayyano hujjojinmu, Alƙali ya buƙaci shaiduna uku. Baba Malam yayi mun shaida, Adama ma haka, sai Ramadan da ake yawan aikowa. Aƙali yayi musu tambayoyi dangane da abbuwan da suka sani, suka amsa gwargwadon saninsu. Akaita turzawa. Lauyan Babangida ya kakkkareshi da hujjojinsu na ƙarya. Alƙalinnan yayi shiru bayan ya gama sauraren dukkan bayani daga ɓangare biyun. Sai ya buƙaci in fito cikin ɗan akwaku. Na fito na tsaya zuchiyata a bushe. Tambayoyi ya dinga jero mun ina amsawa cikin rashin tsoro ko na misƙala zarratin. Alƙali sai rubutu kawai yake yi. Lauyan Babangida ya tashi a zabure ya dinga mun sharri irin wanda sukaita mun a kotun baya dai. Haka aka ɗage sauraren ƙara akan nan da wata ɗaya mu dawo domin yanke hukunci zuwa lokacin an gama bincike domin tabbatar da adalci. Alƙali ya nemi Babangida ya sake ni ya nuna shi a sake bashi dama. Ni kuma na nuna wallahi bazan sake zaman aure dashi ba abadan. Da haka zaman kotun ya ƙare muka fito zuchiyata fes har wani murmushi nake yi dan daɗi. Babangida da su Malama Babba kuwa hankalinsu a matuƙar tashe yake. Baba malam ne ya tare mu. "Sabuwa kizo gobe ki same ni a gida da safe zamu yi Magana dake." A kunyace na amsa mishi Washegari sassafe kuwa na isa. Kuɗi dubu ɗari shida ya ƙirgo a baƙar leda ya damƙa mini. "Ga kuɗi ko alƙali zai ce ki fanshi kanki da kuɗi, duk da shima da kanshi yana da damar da zai iya sakin ki kuma kin saku bisa ga dalilai masu yawa da kika gabatar. Na fahimci shi wannan alƙalin yana alƙalanci da gaskiya da amana zai raba auren naku ne kuma alƙali yana da damar da zai saki mace na sanshi tare muka yi karatu dashi. Amman dai Sabuwa kin yadda har cikin zuchiyarki zaki rabu da Babangida dai ko?" Cikin ƙarfin guiwa na amsa mishi ba wasa yaita mun nasiha akan kada in sake in koma kan rayuwata ta baya yaita mun nasihu har saida naji haka kurum tsohon ya bani tausayi. Haka kwanaki sukaita shuɗewa a kwana a tashi har lokacin shiga kotu ya zagayo. Muka je amman Babangida da lauyanshi basu zo ba. Aka sake saka lokacin sati guda. Muka sake zuwa amman Babangida bai zo ba, kuma anata aika mishi ɗan aike daga kotu. Sai a zama na uku da aka aika mishi da takaddar gargaɗin ƙarshe dan kotu ba sa'arshi bace shine suka tawo dashi da lauyan nashi. Babangida yaƙi amincewa ya sake ni aka kaɗa aka raya. Ni dai duk zaman da akayi ina kan bakata. Har sai da akayi zaman kotu na ƙarshe. Bayan alƙali ya gama tattare bayanai ya jima yana nazarin can sai yace. ( الطَّلَاقُ مَرَّتَانِ ۖ فَإِمْسَاكٌ بِمَعْرُوفٍ أَوْ تَسْرِيحٌ بِإِحْسَانٍ ۗ وَلَا يَحِلُّ لَكُمْ أَن تَأْخُذُوا مِمَّا آتَيْتُمُوهُنَّ شَيْئًا إِلَّا أَن يَخَافَا أَلَّا يُقِيمَا حُدُودَ اللَّهِ ۖ فَإِنْ خِفْتُمْ أَلَّا يُقِيمَا حُدُودَ اللَّهِ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْهِمَا فِيمَا افْتَدَتْ بِهِ ۗ تِلْكَ حُدُودُ اللَّهِ فَلَا تَعْتَدُوهَا ۚ وَمَن يَتَعَدَّ حُدُودَ اللَّهِ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الظَّالِمُونَ )