Idan kaya ya gaji book 3 - Chapter 13
Idan kaya ya gaji book 3 Chapter 13: Idan kaya ya gaji book 3 Chapter 13. البقرة (229) Al-Baqara
3,224 words
البقرة (229) Al-Baqara
Saki sau biyu yake, sai a riƙa da alheri, ko kuwa a sallama bisa kyautatawa. Kuma ba ya halatta a gare ku (maza) ku karɓe wani abu daga abin da kuka ba su, face fa idan su (ma'auran) na tsoron ba za su tsayar da iyakokin Allah ba, Idan kun(danginsu) ji tsoron ba za su tsayar da iyakokin Allah ba, to, babu laifi a kansu a cikin abin da ta yi fansa da shi. Waɗancan iyakokin Allah ne saboda haka kada ku ketare su. Kuma wanda ya ƙetare iyakokin Allah, to waɗannan su ne azzalumai. Fasali ya ja kafin ya ɗaura da cewa " A bisa hujjoji kamar haka *Imam al-Dasuqi ya rubuta cewa:* للزوجة التطليق على الزوج بالضرر وهو ما لا يجوز شرعا كهجرها بلا موجب شرعي وضربها كذلك وسبها وسب أبيها *Matar tana da damar samun saki daga mijinta saboda cutarwa (wadda ba ta halatta ba a shari'a), kamar barin ta ba tare da hujja ta shari'a ba, ko duka ta haka, ko yi mata zagi, ko zagin mahaifinta.* *Asali:* al-Sharḥ al-Kabīr wa Ḥāshiyat al-Dasūqal-Dasūq Saboda haka, mace Musulma na da cikakken iko ta nemi saki daga alƙali idan mijinta yana cutar da ita (*at-tatliq bil-darar*) - ko cutarwar tana da nasaba da duka ne, maganganu, ko ciwon zuciya (emotional abuse) - ba tare da wajabcin ta mayar masa da sadakinta ba ko wani diyya. Ko da ba a samu shaidu ko hujjar gani ba, *shekarar da mace ta bayar cewa tana cikin cutuwa* na iya wadatarwa ga alƙali ya yi la'akari da sakin - musamman idan akwai wasu alamu ko yanayi da ke goyon bayan hakan. *Imam Khalil ya rubuta cewa:* *ولَهَا التَّطْلِيقُ بِالضَّرَرِ ولَوْ لَمْ تَشْهَدِ الْبَيِّنَةُ بِتَكَرُّرِهِ وعَلَيْهِمَا الإِصْلاحُ وإِنْ تَعَذَّرَ وإِنْ أَسَاءَ الزَّوْجُ طَلَّقَا بِلا خُلْعٍ*
Ma'ana: *Mace na da damar samun saki saboda cutuwa, ko da kuwa babu bayyanannen shaidu na cewa abin na faruwa sau da dama. Dole a fara yunƙurin sulhu, amma idan hakan ya ci tura, kuma mijin yana da laifi, za a iya sakinsu ba tare da neman yardar miji ko mayar da sadaki (khul'i) ba.* *Majiya: Mukhtaṣar Khalīl 1/111* Idan aka zo ga magana, halayen rashin da'a daga miji-irin su duka, barin mata, ko zina-suna daga cikin hujjoji masu ƙarfi da za su iya ba wa mace damar neman saki daga alƙalin shari'ar Musulunci. Manzon Allah ﷺ da kansa ya taɓa shiga tsakanin wani miji da matarsa da ake bugunta da ƙarfi, inda ya kafa misali na doka cewa shugabanni su gyara irin wannan hali. Aliyu ɗan Abi Ṭalib ya ruwaito: *Matar Al-Walid ibn 'Uqbah* ta je wurin Annabi ﷺ tana kuka tana cewa, "Ya Manzon Allah! Al-Walid yana buguna ni!" Sai Annabi yace:
*قُولِي لَهُ قَدْ أَجَارَنِي* *"Ki ce masa: 'Ya ba ni kariya.'"* Bata daɗe ba sai ta dawo tace: "Bai yi min komai ba sai ƙarin duka!" Sai Annabi ﷺ ya yayyanka wani yanki na rigarsa ya ce:
*قُولِي لَهُ إِنَّ رَسُولَ اللَّهِ قَدْ أَجَارَنِي* *"Ki ce masa: Lalle Manzon Allah ya ba ni kariya!"* Bata daɗe ba ta dawo tace: "Bai yi min komai ba sai ƙarin duka!" Sai Annabi ﷺ ya ɗaga hannuwansa yana cewa: *اللَّهُمَّ عَلَيْكَ الْوَلِيدَ أَثِمَ بِي مَرَّتَيْنِ* *"Ya Allah! Ka hukunta Al-Walid, domin ya yi mini laifi sau biyu!"* *Majiya:* *Musnad Ahmad 1257 - Ingantacce (Sahih)* Dangane da yadda mijin Sabuwa ke zuwa kan shinfiɗarta kuma *Shaykhul-Islam Ibn Taymiyyah ya ce:*
*يَجِبُ عَلَى الرَّجُلِ أَنْ يَطَأَ زَوْجَتَهُ بِالْمَعْرُوفِ... *Ya wajaba ga namiji ya kusanci matarsa ta hanyar da ta dace da al'ada. Wannan yana daga cikin manyan hakkinta a kansa, ma fi girma fiye da ciyar da ita. An ce wajibi ne akalla sau ɗaya a cikin kowane watanni huɗu. Wasu kuma sun ce ya danganta da buƙatarta da ƙarfin mijin, kamar yadda ciyarwa ke zama bisa buƙata da iyawarsa. Wannan ra'ayi na biyu shi ne mafi inganci.*
*Majiya:* *Majmu' al-Fatawa 32/271* *- Ya kamata mijin ya kusanci matarsa ta hanya da za ta gamsar da sha'awarta, ba wai kawai ya tsaya kan jin daɗin kansa ba, kuma ba da tsauri ko tashin hankali da zai cutar da ita ba.* *- Shari'ar Musulunci ta gane cewa watsi da buƙatar jima'i ba matsalar jiki kawai ba ce, sai dai tana shafar nutsuwar zuciya da lafiyar kwakwalwa, waɗanda su ne ginshikan zaman lafiya a aure.*
*Imam Ibn Qudamah:*
*ويُسْتَحَبُّ أَنْ يُلَاعِبَ امرأتَه قبلَ الجِمَاعِ لتَنْهَضَ شهوتُها فتنالَ مِن لذَّةِ الجماعِ مثلَ ما نالَ* *- An so (miji) ya rika wasa da matarsa kafin jima'i, domin sha'awarta ta motsa, ta ji daɗin jima'i kamar yadda shi ma yake ji.*
*al-Mughnī 10/232* A bisa waɗannan hujjojin da waɗanda lokaci ba zai bani damar zaiyanosu ba Sabuwa na sake ki, in kin gama idda kin samu miji kiyi aurenki na rufe wannan shari'ar ta ƙare. Sakin yana nufin babu damar kome har sai kin yi wani auren kin fito. Kina da damar riƙe ƴaƴanki in kina so. Kuma ratayayyen hakkine a kan ubansu ya ɗauki ɗawainiyarsu bisa daidai samunshi da kotu zata duba ta ayyana mishi kuɗin da zai dinga baku duk wata. Bugu da ƙari su saurara kuji abinda Allah yace. ( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا نَكَحْتُمُ الْمُؤْمِنَاتِ ثُمَّ طَلَّقْتُمُوهُنَّ مِن قَبْلِ أَن تَمَسُّوهُنَّ فَمَا لَكُمْ عَلَيْهِنَّ مِنْ عِدَّةٍ تَعْتَدُّونَهَا ۖ فَمَتِّعُوهُنَّ وَسَرِّحُوهُنَّ سَرَاحًا جَمِيلًا )
الأحزاب (49) Al-Ahzaab
Ya ku waɗanda suka yi imani! idan kun auri muminai mata, sa'an nan kuka sake su a gabanin ku shafe su, to, ba ku da wata idda da za ku lissafa a kansu, kuma ku yi musu kyautar jin daɗi kuma ku sake su saki mai kyau.
( لَّا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ إِن طَلَّقْتُمُ النِّسَاءَ مَا لَمْ تَمَسُّوهُنَّ أَوْ تَفْرِضُوا لَهُنَّ فَرِيضَةً ۚ وَمَتِّعُوهُنَّ عَلَى الْمُوسِعِ قَدَرُهُ وَعَلَى الْمُقْتِرِ قَدَرُهُ مَتَاعًا بِالْمَعْرُوفِ ۖ حَقًّا عَلَى الْمُحْسِنِينَ )
البقرة (236) Al-Baqara
Kuma babu laifi a kanku idan kun saki mata matuƙar ba ku shafe su ba, kuma ba ku yanka musu sadaki ba. Kuma ku ba su kyautar daɗaɗawa, a kan mawadaci gwargwadonsa, kuma a kan maƙuntaci gwargwadonsa; domin daɗaɗawa, da alhari, wajibi ne a kan masu kyautatawa.
( وَإِن طَلَّقْتُمُوهُنَّ مِن قَبْلِ أَن تَمَسُّوهُنَّ وَقَدْ فَرَضْتُمْ لَهُنَّ فَرِيضَةً فَنِصْفُ مَا فَرَضْتُمْ إِلَّا أَن يَعْفُونَ أَوْ يَعْفُوَ الَّذِي بِيَدِهِ عُقْدَةُ النِّكَاحِ ۚ وَأَن تَعْفُوا أَقْرَبُ لِلتَّقْوَىٰ ۚ وَلَا تَنسَوُا الْفَضْلَ بَيْنَكُمْ ۚ إِنَّ اللَّهَ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ )
البقرة (237) Al-Baqara
Kuma idan kuka sake su daga gabãnin ku shãfe su, alhãli kuwa kun yanka musu sadãki, to, rabin abin da kuka yanka fãce idan sun yãfe, kõ wanda ɗaurin auren yake ga hannunsa ya yãfe. Kuma ku yãfe ɗin ne mafi kusa da taƙawa. Kuma kada ku manta da falala a tsakãninku. Lalle ne Allah ga abin da kuke aikatãwa Mai gani ne.
Alƙali ya tambayeni na yafe ko ya bani kuɗin. Darajar Baba Malam yasa nace nayafe mishi. Alƙali ya ɗaura da cewa "Shi kuma Babangida kotu zata ci tararshi na ƙin amsa kiran da kotu tayi mishi dan kotu ba sa'arshi bace" Na sanar ma alƙali bani da buƙatar riƙe yaran yaje ya riƙesu. Ina gama faɗin haka. Alƙali ya rubuta takadda tare da buga hatimi a jiki yasa magatakarda ya miƙo mun. Guduma ya buga duk muka miƙe. Da gudu na fita waje nayi sujjada a ƙasa ina godema Allah har da kuka dan murna. Su Labbai ne suka ɗaga ni. "Cau cau wallahi kunsan Allah dama yau nayi niyyar saka kan Babangida gabas in mishi kisan mummuƙe dan naga shari'ar taƙi ƙarewa ashe zata ƙare, na Allah basa ƙarewa." Cewar Gaza da yake taya ni murna. Duk ƴan uwana suna bayana abinda yake sake ƙarfafa mun guiwata kenan. Maza muka shige motar Dr Kamilu muka fice a kotun. Mahaifiyarshi kuma tata motar ta shige ta tafi wata kotun dan tsaya ma wata matar itama, aikin fa kenan zamani ya lalace da gaskiyarka in baka da hanya ba lallai ka samu adalci ba. Inajin wani irin daɗi marar misaltuwa na ratsani jina nake tamkar an sauke mun dala da gwauron dutse a kaina. Team Babangida kuma ya jikin naku?
BABANGIDA:. Babangida kuma da ƙyar aka jawoshi daga kotun ya fito dan ji yake duniya na juyawa dashi ga ba guiwa😆. Take yaji wani irin matsanancin son Sabuwa ya shigeshi so mai girman da bai taɓa yima mace makamancinshi ba. Gashi gobe asussubar fari zasu wuce garinsu Sumy ɗaurin aure tare da su Sa'a da zasu tafi da akwati. Ya ƙuƙuta yayi ma matan nashi kaya kala bibbiyu da ƙyar da kuɗin ɗinki. Kawu manga ne ya iso kusa da Babangida ya dafa shi suka haɗa idanu. "Mustapha kayi ƙoƙari ka tawo da Babangida can gidana akwai zama da zamu gudanar na family. Babangida ita fa rayuwa da kake gani haka take juyawa da duk wanda yayi wasa da'ita duk wanda yayi guga da zummar ɗiban duniya ƙarshe inya jawo bazai tadda komai ba. Ba kai bane baka ɗauki saki a bakin komai ba? Sai gashi yau kaine alƙali ta sakar maka mata kuma ta saku har a wajen Allah gashi harma ka shiga mawuyacin hali akan haka. Nifa na ɗauka farin ciki zaka yi naga gobe_gobennan zaku wuce wajen ɗaurin aure. Danni ba zuwa zanyi ba tunda dai munje an ganmu mun gabatar da kanmu da sadaki ai magana ta ƙare" Su Sa'a dasu Wawo ne suka zo suka wuce su Kawu manga ko wanne zuchiyarshi babu daɗi. Babangida na bayan motar Mustapha yayi shiru kana ya takure waje guda ya shiga wani irin zurfin tunani. Irin diramomin da sukaita yi da Sabuwa, da Cus da yake kiranta, da irin yadda ya hanata saƙat yake ta tunowa. "Babangida yafa kamata ka sararama kanka akan batun Sabuwa. Ni dai wallahi tun daga farkon haɗuwarku kawo yau da Allah ya ƙaddara ƙarshen zamanku bansan wata riba da zance kunci a aurenku ba. Tunda dai yarinyar ta shigo rayuwarka kake ta karo da matsaloli manya. Shin Babangida ko dai kana son Sabuwa ne mu bamu sani ba ka barmu a duhu?" "Wallahi Mustapha nima ban san sonta nake yi ba ashe mugun sonta nake yi. Amman ina jin wani irin yanayi a jikina akan Sabuwa sosai. Nafi yawan tunaninta fiye da duk matan dana aura a rayuwata. Mustapha ina ga fa soyayya da kishin Sabuwa ne ya lulluɓemun zuchiyata ya haifar mun da muguwar tsanarta. A yau dai naji duk duniya babu macen da zan iya rayuwa da'ita sama da Sabuwa. Mustapha wallahi badan kada a saki Malama Babba bane yasa na dage naƙi sakin Sabuwa ba. Sonta nake yi naga Ƴan taskar Badiat suna ta bina da bita da ƙulli tuban nawa ma sun kasa yadda dashi" Dariya Mustapha yayi yace "Kaga wannan Ummin Maman hum yarinyar akwai daɗin murya ko ita zata maye gurbin Sabuwa ne? " Da harara Babangida ya bishi kawai daidai isowarsu ƙofar gidan Kawu manga can suka baro Kawu Manga tare da Baba Malam. "Ni shawarar da zan baka kawai ka mance da Sabuwa a cikin rayuwarka kayi tsayuwar daka wajen ganin Baba Malam ya yafe maka. Ga mata nan birjik a bariki waɗanda suka fi Sabuwa kyau yara masu asalima. Naga gobe ɗaurin aurenka ma zamu tafi. Sumy kam ai tayi kuma duk wani taro zaka iya shiga da'ita ba tare da anji kunya ba yarinya ga turanci." Buɗe murfin motar Babangida yayi ba tare da yace dashi ci kanka ba ya wuce cikin gidan. Ga takalman ƴa uwanshi nan a ƙofar falon yana jiyo hargagi da maganganu marasa daɗi da Sa'a da Kudidi suke fesarwa. Idanu ya lumshe shikenan shi kullum a kanshi ake zama a falimi? To shikenan ta faru ta ƙare zama ya ƙare tunda dai har Sabuwa ta fice a rayuwarshi ai. Sai hankalin kowa ya kwanta Allah ya isan da mahaifinsu yayi mishi ta hau kanshi. Babban abu mafi ciwo sakin Malama Babba da Baba Malam zaiyi a matsayinshi na ɗa ace shi yai sanadiyyar tsinka igiyar auren data riƙa ta haure shekaru sama da sittin kaico. A hankali ya zame takalminshi ya shiga da sallama. Uwa kenan itace kaɗai ta iya amsa sallamar Babangida har tana nuna mishi wajen zama kusa da ƙafarta. Sai yaji tamkar yayi wayyo. Jikinshi har rawa yake yi ya tsallake su Wawo ya zauna adaidai inda ta nuna mishi. Kannan nashi a ƙasa duniya tayi mishi atishawar tsaki, sai tamaule zuchiyarshi take yi a ƙirjinshi son Sabuwa na neman rayuwarshi."
MALAM BABA:. "To Yaya mu fa roƙonmu a madadin ni da ƴaƴanta shine ka daure ita Babba ta dawo ɗakinta dan ALLAH. Wannan al'amarin ya faru mu barshi a ƙddarar da bawa bai isa kauce mata ko nuna wayonshi ba." Hannu Baba Malam ya saka a aljihu ya ciro takaddar saki ya miƙa ma Kawu manga. "Wannan takaddar sakin Babba ne. Tuni na rubutata ina jiran irin wannan ranar domin nasan zata zo. Babba in tana so taci gaba da zama a gidana wallahi bazan hanata ba ai itama gidanta ne. In kuma a gidanka zata zauna in ta gama iddarta ka aureta ni zanfi son haka. Wala Allah ka gane wacece Babba daga lokacin da zata tarwatsa maka ahalinka. Maganar yafiya ma Babangida Manga mu jingineshi a gefe. Yaron da bai gaji da neman Magana da saka mutane a uku ba shi kake nemama gafara? Ince gobe zaku naushi hanya aje a ɗauro mishi aure ko? A hakanne kake godona saina janye furucina akanshi ko? To inanan akan bakana in bai gaji ba nima ubanshi ban gaji ba. Ni zan shiga gida" Ya shige gida ta bar Kawu Manga a tsaye da takaddar sakin Malama Babba. Ɗan kuka kenan mai jama uwarshi jifa. Da sallama ya shiga cikin gidan har zuwa babban falon nashi. Da Malama Babba suka haɗa idanu ko wanne cikinsu da abunda yake saƙawa a zuchiyarshi. Waje ya samu ya zauna ya jima a zaune kafin ya miƙa ma Malama Babba wannan takaddar wanda bata da buƙatar buɗewa balle tasa a karanta taji saki nawa ne. Haƙiƙa tasan tayi rashin masoyin da babu wanda zai iya maye mata gurbinshi abadan dan malam guda ne harda ɓari. Kuma tasan cewar Malam yayi haƙuri da'ita kuma yayi mata gata daya ɗaurata a gwadaben karatu yau gashi malamace ta addini. Gauron numfashi ta ja data ga halamar tunaninta na son ya mayar da'ita baya. "Allah yasa hakan shine mafin alkhairi. Amman ya janye furucinshi akan shi Baban nawa?" Buɗar bakin Sa'a sai cewa tayi. "Mu muna ta taki. Ke kina ta wannan marar kirkin yaron wanda baisan mutuncinki ba. Harfa yanzu bai daina halinshi ba. Ni bikinshi ma bazanje ba dama ke kika tursasani tun farko amman tunda har yayi miki sanadiyyar aurenki da mahaifinmu nifa na fita sha,aninshi dana iyalanshi kuma. Sannan kai ka sani Babangida na tsani dukkan abinda ya shafeka da iyalinka. Kuma ko ana ha maza ha mata Sauban bazai taɓa auren Mardiyya ba narantse maka da Allah bazan haɗa iri da Sabuwa ba a rasa wa za'a liƙa mana sai ƴar gaba da fatiha? Yarinyar da sanadinta uwarmu ta rasa aurenta, girmanta, gidanta, dama lafiyarta mrs Bukhari
Aimun afuwa ba zaku jini ba sai ranar asabar ko monday in sha Allah Dan Allah aimun Uziri dole ce tasa [8/21, 2:25 PM] BADA'AT IBRAHIM: IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA UKU SHAFI NA GOMA SHA HUƊU
Saukar mari taji a kuncinta Kawu Manga ya falla mata. "Wai Sa'a baki da hankaline ina kike barin iliminki da tarbiyyar da aka baki ne? Ya ɗan uwanki ido da ido ki dinga nuna ƙin kininshi. A tunaninki dan bata hanyar aure ya samu Mardiyya ba zai ƙita ne? Ki bar ganin yana zafafa ƙiyayyarshi ga uwarsu dasu kansu. Nayi imanin a yanzu da Sabuwa zata dawo cikin rayuwarshi zai fi kowa farin ciki da samun nutsuwa kuma in faɗa muku soyayya zai nuna ma matarshi sosai. Ai abinda ya faru tuni ya riga daya faru harma ya wuce tunda yau ina Sabuwan take? . In Sauban bazai aureta ba ai shikenan sai a haɗa auren da Mahadi yaron Wawo ko kuma Surajon Kudidi ba shikenan bane? Mardiyya ai ba zata rasa mijin aure ba a haularmu ba. Ki guji ɓacin ran Yaya a kanki ina gargaɗinki" Malama Babba tace. "Shikenan wallahi Mango. Abinda Sa'a take yi sale_salin ɓata zumunci ne tunda shi Sauban ai yana son Mardiyya so mai tsanani sosai. Sannan ai ba wannan maganar ake yi ba" Wawo ne yayi gyaran murya kana ya ɗaura da cewa. "Ni kam wannan maganar a barta tukunna ayi batun inda Malama Babba zata zauna tukunna. Dan Mahadi yana da wacce yake so ɗiyar Ƙanwar mahaifiyarshi zai aura shekararsu guda suna nema" Wani yawun baƙin ciki da takaicine ya taru a bakin Babangida da ƙyar ya haɗiye yawun dan baƙin cikin yadda Ahalinshi suke zuƙewa kan Auren Mardiyya. A zuchiyarshi ya ƙudurce Mardiyya zata auri bare a waje can inda za'afi gane darajarta kuma kome za'ace sai dai ace amman bazai taɓa cusa yarinyar a inda zata sha wahala ba zumuncine zai lalace a banza. "Ke Babba ki daure ki koma ɗakinki kiyi zamanki Malam yayi miki wannan alfarmar. Yarannan zaki duba ko ba gaskiya ba Wawo?" "A_a Kawu ni ina ganin kawai mu haɗu mu siya ma Malama Babba gidan da zata zauna a cikin layinnan, su Nusaiba sai su koma hannunta islamiyyarta da take koyar da mata sai ya koma cikin gidan kawai. Amman zaman ba daɗi zaiyi mata ba. Ƴaƴa kam ai Auta ne kaɗai a gabanta shima kuma mata zai fito dashi yayi aurenshi a huta" Kudidi tace. "So samu a sai gidan da shi Auta zai iya zama tare da matar tashi in yaso sai su dinga ɗebe mata kewa tunda su Nusaiba ɗakin miji zasu tafi suma." Nan suka tsayar da matsaya akan hakan. Babangida kuma Malama Babba da Kawu Manga da Wawo sukai tayi mishi nasiha kanshi na ƙasa hankalinshi gabaki ɗaya baya ma wajensu yana dai jin abinda suke cewa fahimtace dai baya wani yi Sabuwarshi kawai yana tunowa a inda tayi sujjada a harabar kotu na godiya ga Allah bisa rabuwarsu. Idanunshi ya lumshe kawai. Da wannan taron ya watse akan Malama Babba zata zauna a gidan Wawo kafin a samu gidan da za'a siya mata ta koma. Bayan Babangida sunyi Sallah a masallaci sai ya wuce kai tsaye majalisarsu data soma taruwa da abokanshi. Nan daga masu tsine ma Sabuwa albarka sai masu ganin gara da aka saketa uban kowa ya huta. Daga haka suka shiga tsara yadda tafiya ɗaurin auren gobe zai kasance. Ƙasimu yace. "Ohh Allah dai yayi cewar dole_dole sai Sumy ta zama matarka. Wane karsashi ko zumuɗi angon da yasan amaryarshi ciki da bai zaiyi? Ai nasan babu wani marmari ko misƙala zarratin tattare da kai dubi sauran aurarrakin da kayi a baya irin zumuɗi da abubbuwan da kake yi." Musbahu yace. "To wannan auren ai auren dole ne za dai a yishi ne sabida rufin asiri. Bawai dan ana so ba" Babangida dai sai ido duk wanda yake magana idanunshi a kanshi. Shi kaɗai yasan irin zafaffakin da yake ji a zuchiyarshi dukane kawai tako ta ina bashi da ma hannun karewa. Bashi ya nufi gida ba sai sha ɗayan dare sabida gidanma baya ƙaunar ya koma. Da ba dan ya tuba ba tabbas da yau a Club zai kwana ko dan ya samu sauƙin zuchiya. Amman dake ya tuba yana tafe a lifan dinshi yana rera karatun Qur'ani hakanne ma ya haifar mishi da ƴar nutsuwa kaɗan.