Kenza eBookz

Idan kaya ya gaji book book 4 - Chapter 1

Idan kaya ya gaji book book 4 - Chapter 1

Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 1: Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 1. 10/4, 10:30 PM] +234 810 593 2041: IDAN KAYA YA GAJI.... GAMMO MA YA GAJI…

4,352 words

10/4, 10:30 PM] +234 810 593 2041: IDAN KAYA YA GAJI.... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA HUƊU (4) SHAFIN FARKO.

BARKANKU DA JUMURIN JIRA INA GODIYA SO.

TEAM BABANGIDA TEAM SABUWA INA MIƘO SAƘON GAISUWA DA JINJINATA GAREKU MADALLAH DA ƘARFAFAN HUJJOJI.

Canada😆

Abu kamar wasa bacci ya ƙauracema idanuna. Duk wani motsi da tunanin Alhajin da ban sanshi ba nake yi. Murmushinshi da cikar kamalarshi kawai nake hange. Dana tuno wacece ni da irin gidan dana fito sai jikina yayi sanyi sosai. Siraran hawayene suka surnanomun hakan saiya haifar mun da ciwon kai. Haka dai na samu na yi baccin marar daɗi. Da muka tashi aka taremu da ƙanzon masara da madara a matsayin abuncin rana. Da daddare kuma shinkafa basmati da wata miyar kabewa niƙaƙƙiya zaƙi zoi. Ni wallahi na kasa ci. Uzairu zuchiya kuwa duk abinda aka bashi kaiwa yake yi. Na fahimci Uzairu zuchiya baima zo da wando dogo ba, duk gajerun wanduna da amles ya kwaso, naga kuma hakan ya burge Felisha sosai. Da dare yayi ni dai ban ban jima ba nayi bacci mai cike da mafarkai barkate. Bani na farka ba saida gari ya waye tangarangan abinka da gidan kirista, su ba sallah ba bare su tasheka kaima kayi. Su ba kusa da masallaci ba bare kaji kiran sallah. Alwala nayo na fito na gabatar da Sallah. Nayi shiru a inda nayi Sallah ina tunanin da ni kaɗai na barma kaina sani. Da wasa_wasa har sai sha biyun rana muka soma jin hayaniyar jama'ar gidan lokacin yinwa ta jigatani na shiga ɗakin Uzairu zuchiyata na sameshi riƙe da cikinshi yinwa zata kasheshi, gashi ya kwana gudawar gamje_gamjen da yake ta ɗirkama cikinshi. "Ke lolo Kwana nayi cur ina gudawa ga yinwa na neman halakani, yanzu kaje cin abincin ma a kawo maka taliya mai madara kuma ƙila tunda munci mai sikari, munci mai zumar ma. " To Uzairu zuchiyata kai da kake mijin Baturiya ai zaka saba da kunyi aure shikenan " "Wa lolo? Babu sabo. Kinga muna kumawa zan sake zagewa in koyi girki da kyau duk da dai ina iya dafa taliya, taliyar ƴan yara. Zagewa zanyi Dad ya koya mun abincinnan nashi nima in dinga mana girki ko kuma uban kowa yaci nashi" Felisha ce ta shigo daga ita zai ƙaramin wando iya cinya da rigarta iyakarta ciki. Tana zuwa ta zauna kusa da Uzairu Zuchiyata tana faɗin yayi kyau sosai. Gaggaisawa dai muka yi sai wajen sha biyu da rabi muka hallara a teburin cin abinci Muna cin abincin iyayen Felisha suna kafa ma Uzairu zuchiyata sharadi akan aurenshi da Felisha tunda dai taji ta gani. Duk sharuɗɗan da aka kafa mishi duk ya ɗaukesu suka gama tsayar da lokaci akan nan da wata uku me kyau sai su tawo najeriya ayi biki. Ƙwarewa Uzairu zuchiyata yayi ya dinga tari anata yi mishi sorry sorry. Saida tarin ya lafa ne yake cewa. "Ai mu da Dad ɗina yace nan zamu tawo ayi bikin kawai in aka gama sai su koma" Baban Felisha yace "Bazai yiwu ba ya zama dole muga iyayenka da danginka kaima kamar yadda yau Felisha zata zagaya daku kuga nata dangin dukkansu suna nan Calgary." Yawu ya haɗiye yace . "To shikenan Dady" Nan dai muka karya sai kuma muka shiga shirin fita. Ananne muka kira su Maigogul a waya aka gaggaisa, su a Najeriya lokacin dare ne kasancewar akwa bakwai ne a tsakaninmu. "Lolo ya kika ga Canada kyanta dan ALLAH?" Dariya nayi nace. Ai Rakiya wallahi ba'a cewa komai. Gashi iyayen Felisha mutanen kirki ne gasu masu kuɗi." Maigogul ya fisge wayar inaji Rakiya na maganganu. "Ke Lolo ina shi Uzairu zuchiyata yake bani shi inji yayi amfani da kwalli da turaren dana bashi kuwa?" Uzairu zuchiyata ya karɓi wayar yana dariya yace. "Ai Maigogul ko babu kwalli da turare na riga dana sace zuchiyar Felisha ballema turare da kwalli wallahi naga amfaninsu kwallinnan yanzu haka na sake rambaɗashi da kyau. Mun samu tarbar mutunci. Yanzu ma haka zamu jene ganin danginta a nuna ni kuma tunda kunsan ba jinawa zamu yi ba kwana bakwai ne kacal. Bikin dai wata uku aka saka su Rakiya sai a soma shiri" Su Labbai duk saida aka basu waya daga ƙarshe ma kashewa muka yi nan Felisha ta ɗauki mota muka wuni munata zagaye a gari da kuma gidajen ƴan uwansu. Ni dai da zaran wayarta tayi ƙara sai inyi tunanin wannan Alhaji ne yake nemana sai inga ba haka bane. Sai da muke dab da dawowa gida lokacin dare ya rufa sai kuwa gashi ya kirani Felisha ta miƙo mun wayar. Muna daidai wani kanti na cin abinci mai shegen kyau da ƙara ma jijiyoyin ido lafiya wajen kallo. Assalamu alaikum " na furta a ƙasan maƙoshina. Kafin yace wani abun sai naji ya sauke wawuyar ajjiyar zuchiya kafin yace. "Shalele barka da dare. Da fatan kin wuni lafiya ko. Sannan ina fatan kinyi waya da Alhaji Baba kun sanar mishi isowarku lafiya ko?" Murmushi nayi da naji ya kira Maigogul da Alhaji Baba yaga wanka kayan girma ya ɗauka aljihunma da girma. Lafiya lau gamu nan a waje muna ta zagaya CALGARY muna kallon gari. Yanzu haka ma ina gaban wani gidan cin abinci mai suna. Casino blactfoot. Ƴan gida kuma munyi waya dasu" Sai muka yi shiru na ƴan sakanni shi ya katse shirun ta hanyar cewa. "To ni yaushe za'a bani dama in zo a zagaya garin dani ko dai nayi tsufa? Kinsan nace inaso in ganki dan mu tattauna ko? " Murmushi kawai nayi bance uffan ba. "Uhm baki ce komai ba ko dai bakya son inzo ne? " A_a ba haka bane. Zaka iya zuwa duk lokacin da ka shiryama hakan. " "To nagode. Yaushe zaku koma najeriya amman" Nan da kwana shida in Allah ya kaimu. " "To shikenan zuwa jibi zan shigo da safe amman da yamma ne zanzo wajen naki" Da mamaki na tambayeshi. Dama kana da ƴan uwa a nanne? " Dariya yayi mun tunda yasan inda na dosa. "A_a ni bamma taɓa shiga Calgary ba wajenki kawai zan zo. Hotel zan kama in mun gama yawon sai in koma in kwanta wayewar gari kuma in kama hanya. Gobe zan gama abinda ya kawo ni in sha Allah. " A haka dai mukai sallama ya kashe wayarshi. Zuwa can sai gasu Uzairu zuchiyata da ledoji rigi_rigi. Muna shiga gidan muka tarar babu kowa suma sun tafi shaƙatawa. Ni dai abincin da akayo oda naci na rama sallolina nabi lafiyar gado. Abincin dai mun samu shinkafa fara da kaza gashin injin, wai miyar ɗanyen tumaturi da gishiri. Kai munga duniya Washegari sai da daddare wajajen tara ma muka fita hmm club ta kaimu. Anan muka ga ainihin watsewa irin ta turawa. Wasu ma tsirara_tsirara gasunan. To daga su sai rigar Mama da gwari na tsuma. Rawa kuwa sai tiƙarshi akeyi, Uzairu zuchiyata a wannan waje ya ƙona mun kaina tas wallahi hiye wai ku kunga rawa kuwa hmm. Felisha dai a bige muka dawo da'ita gida danma Uzairu zuchiyata ya iya mota kuma yana da ƙwaƙwar gane waje. Sai fa biyun dare muka shiga gida. Amman a titi yadda kuka san rana. Washegari sai na jini na tashi da farin ciki wanda ni kaina bansan musabbabin hakan ba. Wajajen yamma ina ɗaki Uzairu zuchiyata ya leƙo "Lolo zo ga waya Rakiya zata yi magana dake. Cewar Uzairu zuciyata. Karɓar wayar nayi na kara a kunnena. " Lolo mutan turai ya kuke ya surukar tamu?" Lafiya lau Rakiya turai gata nan muna shanta. Ina su Labbai? " "Uhm suna gidan Adama kishiya ta watsa mata talge a hannu shine suka je dubata. Amman kinsan Adama a ƙonen wallahi saida tayi mata kafirin duka ita a kwance Adaman ma a kwance. " Hankalina take ya tashi na shiga salati. Uzairu zuchiyata ya shiga tafa hannaye dake yana jiyo mu. "Tayi daidai Rakiya amman duk yadda akayi Gaza bai sani ba nasan da saiya mata yadda ake saɓule gashin kaza ko? Ni wannan Aure na Adama babu sa'a" Cewar Uzairu zuchiyata. Rakiya tace. "Baya gidan gangar siyasa ta doka kaima kasan Gaza bazai zauna ba. Yana aiko yaran nashi da cefane dai a ba matarshi amman bama iya sakashi a idanunmu. Ga wannan Yarinya Salma ƴar ɗakin Hauwa itama ta dawo babu auren ita kam harda goyo ta dawo abu goma da ashirin. Maigogul babu ruwanshi ya shiga ya fita ko a jikinshi wallahi ya dai barmu da damuwa. Kai Allah wadaran naka ya lalace. Kunga ga ma su Adamannan sun tawo raɓe raɓe da hannu duk magani, ashe ƙunace bata wasa ba fa. Adama shine kika biyosu kuka dawo gida a wanne dalili da ba zaki zauna a ɗakinki ba. Wai shin gidannan daɗi yake yi muku ne? " Ina jiyo Hauwa ta na magana. "Haba Rakiya bakya ganin irin mummunan ƙunan dake hannunta ne, ai gara dai ta dawo ta zauna ta warke tukunna Allah bashi daga baya ta koma" Wayar Rakiya ta datse tana ta faɗa. "Kin gani lolo shi yasa nake son ki karɓi tayin maigogul kiyi aurenki gidan arziki. Amman naga kamar wannan Alhajin da muka haɗu a jirgi sonki yake yi ko. Kun yi wata maganane? Naga dai yana da kamala kuma da gani akwai kuɗaɗe a hannunshi gaskiya " Ajjiyar zuchiya na sauke jikina duk ya mutu nace. Yau dai muka yi dashi zamu haɗu yace zamu tattauna to bansan me zaice dani ba. Amman biri yayi kama da mutum. Uzairu zuchiyata na gaji da rayuwar ma gabaki ɗaya wallahi ji nake kamar in kashe kaina ko in gudu in tafi wata duniyar daban inda zan dena jin labarin kowa" "A_a lolo kin soma gudu da ƙyamar tsatsonki ne? Ƙaddararmu ce a haka shine dalilin da yasa muka fito ta tsatson maigogul da Rakiya har fa gara Maigogul akan Rakiya wallahi. Ni a hakan dai bana sha'awar dena jinsu. Zan dai matsa ganina zaiyi wuya. Yana daga cikin dalilaina da yasa na zaɓi Felisha sama da Hajiya Zara Abuja duk da Hajiya Zaran ta fita jini a jika. Ki dai daure a cikin waɗannan biyun ki fidda gwani aike ƴar baiwa ce ma a cikin gidanmu yanzu na yadda ƙashin arzikine dake wallahi Allah. Zagewa zaki yi kita narkewa kina firirita har wannan Alhajin ya furta yana sonki. Lolo kwallinnan in Maigogul ya baki ki zizara, turarennan in Maigogul ya baki ki shafa, jubi idanuna kamar tsuhuwar karuwa yaji kwalli, amman ko a jikina ko da Felisha ta tambayeni ce mata nayi kwalco ɗinmu ne saka kwalli. Lolo kada ki sake wannan Alhajin ya suɓuce miki barikin da kika buga a baya dan Allah yayi aiki anan" Ya noƙe kafaɗarshi yana wani kashe mun ido kamar tsohuwar karuwa." Ficewa yayi da wayar a hannunshi ni kuma na faɗa banɗaki zanyi wanka. Saida naci kukana na gode ma Allah kana nayo wankan na fito, tausayin Adama nake ji sosai shikenan mu ko da muna son zaman auren babu damar yi, ga Salma ma ance an sakota, ita kanta Adama na dai san ƙarshenta auren ya mutu ya gama. Mai na shafa na ɗan murza hoda sama sama na saka tozali yaji sosai a idanuna dan nasan tozali na yi mun kyau kuma yana daga cikin adon mata. Man baki na murza na zura abayata mai ruwan jinin kare saina tayar da sallah. Ina sallah Uzairu zuchiyata ya shigo. "Au sallah take yi" Sallama nayi na dubeshi. "Ke lolo baƙonki ya iso yana waje cikin lambun dake bayan ɗakinnan. Muma muna can ni da zuchiyata. Sai kiyi saurin fitowa zuchiyata tasa a kawo mishi lemu. Lolo kifa nutsu wallahi da ganin fatar dake shinfeɗe a jikin wannan dattijo kinga mai kuɗi hutu ya ratsa shine irin eh. Wallahi ko ba cewa yayi yana sonki ba ki maƙale mishi har sai kin kaishi bango, iya wuya kada ki bari ya kubce. Wallahi mu munga waje. Kina dai ganin su Labbai anyi bandaro Adama ma data shiga kina gani kishiya ta ƙonata suna gida. " Miƙewa nayi jikina duk a sanyaye. Rauni da karyewar zuchiya nake ji tun da naji labarin abinda ya faru da Adama. Turarukana na fesa na fita ina takawa a hankali ga faɗuwar gaba da yake ta damuna. Daga nesa can cikin korayen fulowowi masu adon furanni farare na hangoshi akan wata farar kujera ga kayan motsa baki a gabanshi. Yana saye da riga polo fara da wandonshi na jins mai ruwan baƙin bulu. Ga tsabtaceccen farin gemunshi sai sheƙi yake yi. Tsintsiyar hannunshi ɗaure da baƙin agogon fata. Daga gefenshi can na hango Uzairu zuchiyata tsuntsun soyayya anata guje_guje a lambu ya samu waje sai iya shege yake yi. Murmushi nayi mishi kawai. Shi kuwa Alhaji tun daga nesa yake ta bina da ido harna ƙaraso na zauna a farar kujerar dake fuskantarshi kai tsaye. "Barka da isowa Shalele kin saje a cikin turawan ƙasar duk da fatarki tafi tasu kyau da murjewa. " Dariya kawai nayi muka gaisa sai shiru ya biyo baya ina jiran me zai faru gaba kuma. Ya jima yana ƙarema fuskata kallo harda taguminshi, bansan hakan ba saida naji shirun yayi yawa na ɗago sai idanunmu ya sarƙe ana juna, kallon da yake mun ya nuna ya daɗe yana kallona dan ya shagala sosai. Murmushi ya sakar mun kafin yace. "To maganganun bakina suna da yawa. Da fatan ba zaki ƙosa da tambayoyina ba ko? " Babu komai in sha Allah. Na faɗa a sanyaye a taƙaice Zamanshi ya gyara tare da furzar da iska. " Alhaji Baba ya faɗa mun aurenki mutuwa yayi. Ko zaki sanar dani dalilin mutuwar auren. Mijinne bai riƙeki yadda ya kamata ba. Ko daga danginshine matsalar, ko kuma daga kene? Nasan ba zaki taɓa faɗamun abinda ba shi kenan ba." Duk sai naji na ruɗe to ni mai zance mishi ni kaza? "Ke nake saurare. In kuma kina ganin wani abune da kike ganin ba dole sai naji ba sai muje tambaya na gaba" Murmushi nayi cikin salon wayancewa nace. A_a ba wani abu bane da har za'a ɓoyeshi ba. Hirarshi ne ma ban fiye son ana yi mun ba. Amman kasan aure raine dashi lokacin mutuwarshi in yayi babu tsimi babu dabara. Kawai yawan saɓanine da rashin kwanciyar hankali a gidan auren. Sanadin haka harma na kamu da hawan jini, da dai ciwon damuwa da ake cewa ina dashi. To kaga kuwa akwai cutarwa sosai haƙurin da juna shi yafi alkhairi dan har yanzu ina ganin likita, kuma ina shan magunguna " Kallonshi nayi domin in karanci yanayinshi. Sai naga labarin kamar ya taɓa mishi zuchiya sosai sai girgiza kai yake yi. "Allah shi kyauta yaranku nawa dashi, kuma suna ina yanzu yaran? " Saida na sauke ajjiyar zuchiya kafin nace. Yaranmu huɗu biyu maza biyu mata babbar ɗiyarmu ma harta kusan aure, tana koyarwa a makarantar Islamiyya ta gidan mahaifinta. Suna hannun matan mahaifinsu basa hannuna." "Allah sarki. To bayan nan da kuka rabu karatu kika koma, ko kasuwanci kike yi. Ya batun zawarawa za'a nema mun matsuguni ko ko dai nayi tsufa in koma gefe? " Ya ƙarashe da dariya. Nima dariyar nayi. Mishi kawai ba tare da nace komai ba. Jus ya tsiyaya ya sanyaya maƙoshin shi, ga wata sassanyar iska mai shiga jiki tanata ratsamu hakan saiya tsundumamu a cikin wani yanayi mai taushi da tsaiwa a rai. Sai murmushi muke yi ma junanmu. Ni dai na riga na kamu bani data cewa. Fatan kawai Allah yasa abun ya ɗore. Muddin dai zaiyi bincike babu aure tsakaninmu. Ko zuwa taɗi yayi ƴan gulma suka ganshi dole zasu rusa abun. To ya zanyi ne ni Sabuwa baiwar Allah. Katseni yayi da soma yi mun bayanin daya shafeshi. "To ni dai Sunana Alhaji Zaidu Rano ɗan fuloti. Ni haifaffen garin Rano ne dake jihar kano family house ɗinmu acan yake, mahaifina Allah yayi mishi rasuwa, sai iyayena mata da ragowar ƙanne da yayyu. Iyalan matan ƙanin Babanmu ne suke cikin family house ɗin a yanzu. Gidanmu gidan almajiraine mahaifina malamin tsangaya ne, anan gabanshi mukai karatun Allonmu. Har yanzu makarantar tananan ƙannenshi na kulawa da'Ita, kuma har gobe a kwai almajirai da suke karatu a gidan sama da su Ɗari biyu. Gidanmu gidan malumtane sosai kuma gidanmu sananne gidane haka mahaifinmu ma sanannene, dan mun samu alfarmomi da dama a wajen manya da zaran mun ambaci sunanshi. To cikin ƴan uwana nine kaɗai na fito irin ciraninnan ko kuma ince fatauci. Muna shigo da kayan hatsi Kano, sai mu sai kaya mu koma gida. A haka nayi ta nema ni nasa kaina a makarantar boko har matakin jami'a. Nayi aiki a ƙarƙashin gwamnati na kusan shekaru takwas kafin daga baya na ajjiye aikin na shiga harkar canjin dala, da harkar siyar da feguna fuloti kenan kinji inda na samo inkiyar ɗan fuloti. To nakan gina gidaje na siyarwa ma Sosai. Ina da mata ɗaya Hajiya Munubiya. Ina da yayye da ƙanne a gidanmu mu arba'in da tara cib mahaifinmu ya haifa. Wannan shine a taƙaice shekaruna sirrinane na barki da hasashe ke da masu karatu" Murmushi nayi mishi tare da cewa. Yaranka nawa banji ka ambaci ko ɗaya ba? " Sai naga take fuskarshi ta sauya daga annuri zuwa akasin hakan. Ya sauke kanshi ƙasa yayi shiru. Nima sai naji babu daɗi ina tunanin to mena faɗa da zafi haka. Mun ɗauki lokaci mai tsayi kafin yace dani cikin murya mai sanyi. "Allah bai taɓa bamu haihuwa ba ni da maiɗakina. Munyi maganin harmun gaji. Har india, Saudiyya munje ƙwararru a wannan fannin sun duba ma anyi duk wani bincike. Amman basu gano matsalar komai ba ni da'ita duk lafiya. Sai dai haihuwar bata samu ba" Allah sarki take naji tausayinshi ya dirarmu gashi dattijo dashi, Allah yayi mishi arziki sai dai bashi da magaji. " "Ƙila jin wannan ya ture alaƙarmu kamar yadda ya tutture wasu alaƙoƙin a baya. Duk da su ƴan mata ne ba zawarawa ba. Naga ke kina da yara ban sani ba ko Allah zaisa a dace ba" Shiru nayi ina nazari ni haihuwar bawai ta dameni bane, yara kuma gaskiya ya faɗi ina dasu har huɗu bana jin ina da buƙatar ƙari in samu ma in auru ai shine ribar. Sannan Alhaji Zaidu wani irin nutsattsen dattijone wanda kwarjini da hankali suka mishi ƙawa yanayin haibarshi da nutsuwarshi tayi kama data Baba malam Adalin dattijo. Nasan ma nesa ba kusa ba in dai binciken asalina za'ayi ni dashi babu dacewar haɗuwarmu, gashi daga tsatson malamai yake shima gashi ɗan dangi. Ina tsoron amsarshi daga baya mu rabu in shiga damuwa ni ba ishasshiyar lafiya ba. "Kina tunani ko? Ai ba dole sai yanzu zaki bani amsa ba zan baki lokaci har zuwa ki koma Najeriya kiyi shawara da Alhaji Baba da ƴan uwanki abinda kika yanke a zuchiyarki sai ki sanar dani karki damu. Kuma kada ki zurfafa tunani da damun kanki. Amman kada kiyi hukunci cikin gaggawa akwai yiyuwar ki haihu akwai yiyuwar baza ki haihu dani ba to kinga yana da kyau ki nemi zaɓin Allah. Nima zan nemi zaɓin Allah muyi istikara." Kallonshi nayi na rasa tacewa sabida haƙiƙa naji tausayinshi sosai da sosai, kuma ni tuni na amince dashi Haihuwa ni bazai zama matsala a wajena ba sam. To shikenan Ubangiji Allah ya zaɓa mana abinda yake mafi alkhairi." Murmusawa yayi ya ƙura mun idanunshi masu kaifi yana mun kallon so dan yayi farin ciki sosai da furucina. Nima wallahi yayi mun ai dole ma yayi mun ni ɗin banza. Ƙurama junanmu idanu muka yi ga iska dake kaɗa fulawowin lambun suna sakar mana ƙamshi mai daɗi sai yanayin ya zama na musamman lokaci guda wani irin sanyi ya soma busowa sai lumshe idanunmu muke yi. Isowar uzairu zuchiyata ne ya katse mana daddaɗan yanayin da muka tsinci kanmu aciki. "Alhaji ina ganin muje ko magriba ta kusa" Agogonshi ya kalla yace. "To shikenan muje ma samu masallaci a hanya sai muyi Sallah. Amman ita gimbiya ba zata samu sallah ba. Abinda zamu yi mu jira muyi sallah kawai in yaso sai mu fita kawai. " Yanayi yana kallona. Ni dai ina cikin wani irin sabon yanayin da ban taɓa shiga irinshi ba. Ga wani irin mugun sanyi da yake ta ratsani har kaɗawa hanjin cikina suke yi,. Uzairu zuchiyata Baban ƙarya rigarshi babu hannu amman ko a jikinshi sai dai duk tsigar jikinshi ta tashi ina kallonshi. " Ciki na tashi na shiga ni da Felisha. Su Uzairu zuchiyata muka barsu zasu yi Sallah a cikin lambun. Bayan na idar da sallah nayi gurum inata tunani ni dai tsorona guda ɗayane kada mu soma daga ƙarshe mu rabu. Kai ina wannan ma yaudarar kaine lolo wannan ba kalarki bane gaskiya kada ki yaudari kanki. Ajjiyar zuciya na sauke hawaye suka zubo mun. Wato kamun kai a rayuwa akwai daɗi kaico da irin yadda muka tsinci kanmu. Ubangiji Allah ka kawo mana ɗauki ka kawo mana hanyar shiriya ta inda zato bai zata ba. Shigowar Felisha ya katsemun tunanina. Tana murmushi ta miƙo mun ƙatuwar jaket fara mai gashi a wuyan irin na ( mage, kuliya, ƴar mussa) Ina murmushi nima na amsa na zura na ƙara fesa turare ta ja hannuna muka fito. A mota muka tarar dasu Uzairu Zuchiyata su suka zauna a gaba mu kuma muna baya lokaci zuwa lokaci muna haɗa idanu mu sakarma juna murmushi na musamman. Wannan daren ya kasance daga cikin dararen da suka tsaya mun a raina gaya. Munyi yawo sosai a wannan birni mune gidan cin abinci mune siyayyar kayan sakawa da kayan ciye ciye dai. Shima Alhaji Zaidu a nan yayi ma iyalinshi tsaraba mai yawan gaske, nima haka yace in ɗauki duk abinda nake so. Da ƙyar dai aka rabu har bakin hotel ɗinshi muka je muka saukeshi mu kai sallama da godiya muka nufi gida. A cikin kwana bakwai ɗinnan sau uku muka haɗu da Alhaji Zaidu, waya kuwa kullum sai ya kirani mun fi sama da awa guda muna hira duk da bai kasance mai yawan magana ba, amman yafi so dai ni ya tursasani in bashi labari. Ranar da muka cika kwana bakwai a ranar jirginmu ya tashi zuwa Najeriya. Felisha da iyayenta har filin jirgi suka rakomu munyi rabuwa ta mutunci sosai. A cikin jirgi kuwa kujerar can bayana sosai Alhaji Zaidu ya zauna. Uzairu zuchiyata kuma kujerarshi a jere take da tawa. Idanuna na lumshe sai nake jin wani iri wanda ina kyautata zaton bazai wuce sabida Rabuwa da Alhaji Zaidu bane. A wannan kwana bakwai mun yi wata iriyar shaƙuwa ta ban mamaki. Kuma na sake karantarshi sosai ɗabi'unshi da irin yadda yake lallaɓani abun yana yi mun daɗi. Haka muka kwana a jirgi washegari da misalin ƙarfe goman safe sai gamu jirgi ya diremu a najeriya. Ina tafe daga ni sai akwatin kayanmu. Uzairu zuchiyata da Alhaji Zaidu suna ta faman jan akwatunan namu kiyy_kiyy gaskiya mun lodo tsaraba sosai. Muna fitowa dan zuwa inda zamu samu tasi muka hango Maigogul tare da wani hamshaƙin mai kuɗi suna tsaye a gaban wata farar mota. "Lolo ga Maigogul can yana ta washe bakinshi" Cewar Uzairu zuchiyata. Saida gabana ya faɗi dan tsorona Allah tsorona kada maigogul yaje yaita sakin layi a gaban Alhaji Zaidu. Ƙarasowarmu ke da wuya maigogul yace. "Ka ganta Alhaji Maina ɗaya kenan tamkar ya dubu lolo ikon Allah. Mai sunan ummana kenan. " Ni dai sai nayi turus nama rasa abun cewa. "Ahh Alhaji ashe kuma zamu sake haɗuwa, ahh ko kaima can canada ɗin kaje ne? " Maigogul ke tambayar Alhaji wanda sai yanzu ya ƙaraso hannunsu na cikin na juna Alhaji Zaidu yace. "Ai kuwa Alhaji can muka je. Harma naje can inda ita Shalelen taka suka sauka mun gaggaisa. Mun sameku lafiya? " A cikin ladabi sosai yake maganar Maigogul kuwa sai rawar kai da ɓarin zance yake yi. "Ab kace kaga surukar tawa ma kenan? Allahu akbar amman naji daɗi sosai. A wanne hotel kake a nan Lagos ɗin ko dai a yau zaka wuce arewa? " Ya tambayeshi kafin ya bashi amsa yace. "Lolo gafa Alhaji nawa da nake faɗa miki. To shine da muka yi magana yace bari ya bar duk abinda yake yi mu tawo mu tarbeki kinga kwa ɗan zanta ma hahaha" Ya ƙarashe yana dariya. Alhaji Zaidu na kalla, shima ni yake kallo yayi mun ƙur ƙila yana son jin abinda zance ne. "Masha Allah tabarakalla. Kai yanzu Maigogul kana da Ƴa kamar wannan shine ko hirar ba'a taɓa yi mun ba duk surutunnan naka" Uzairu zuchiyata na kalla. Yayi saurin cewa. "Maigogul muje masauki wallahi yinwa nake ji sosai a jirgi muka kwana duk munyi tulus. Alhaji a wanne hotel zaka sauka?" Ƙur nayi mishi da idanu ina son in karanci yanayinshi. Fara'ar fuskarshi dai ta ragu sosai. Yana kallona ya faɗa ma Maigogul hotel ɗin da yake sauka, ya sake lumshe idanunshi kafin yace. "Kufa Shalele? " Na ɗago muka haɗa idanu sai lokacin naga asalin yadda ya canja. "Muma can ɗin muka nufa yanzu abinda za'ayi mu shiga mota Alhaji sai mu je dukka kawai" Faɗin maigogul. Kai Alhaji Zaidu ya girgiza yace. "A_a Alhaji Baba ai abokina yana hanya zai tawo ya ɗaukeni kuma ma gidanshi zan soma sauka. Nagode sosai" "To to shikenan. Zan kiraka a waya in mun nutsa dukkanmu in ka shigo hotel ɗin mayi magana kuma munfa gode Alhaji Babba. " Maigogul ya shiga yi mishi fadanci. Ni sabida tsabaragen haushi harna shige motar da shi wannan mai ƙaton cikin ya nuna mun. Ta gilashi naga Alhaji Zaidu ya ciro kuɗin amurka ya dunƙulawa Maigogul a hannu. Take hawaye ya zubo mun shar _shar. Shigowarsu motar baisa na goge hawayena ba. Ta gaban Alhaji Zaidu muka wuce idanu muka haɗa dashi ya ɗan sakar mun murmushinshi na kamilallun dattijai. "Toh fa Alhaji Babba sai fa mun haɗu akwai wata haja da zan tallata maka ne" Rass gabana ya yanke ya faɗi. Shikenan maigogul zai tallatama Alhaji Zaidu sana'arshi sabida gani yake yi kowa watsattsene. Muryar wannan Alhajin ce ta katsemun tunanina".

[10/4, 10:29 PM] +234 810 593 2041: IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA HUƊU SHAFI NA BIYU

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull