Idan kaya ya gaji book book 4 - Chapter 2
Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 2: Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 2. Maigogul inaga bari mu kaisu wajen cin abinci su ci su ƙoshi tukunna.…
4,338 words
Maigogul inaga bari mu kaisu wajen cin abinci su ci su ƙoshi tukunna. Amman lolo me kika ce.?" Ɗan murmushi nayi nace. Naga Hotel ɗinma abincinsu yana da kyau ai gara muje can ɗin kawai." Maigogul yayi dariya yace. "Hakane Lolo suma abincinsu ƙarshene. Uzairu zuchiyata ince dai kayo mun tsarabar abinda na bayar sallahu, kema Lolo ince dai kin siyo mun wani abun dai ko? " "Ai dole Maigogul nayo ma kowa tsaraba. Taka tsarabar data Rakiya ma ta dabance" Baki maigogul ya washe yana ta dariyar jin daɗi. Ni wallahi tausayi ma ya bani Oh shi maigogul babu abunda ya dameshi shi dai burinshi kawai ya samu abinda yake so. Da waɗannan tunane tunanen muka isa Hotel ɗin. Ni dai tunda aka nuna mun ɗakinmu nayi shigewata dan mun gaji sosai. Banɗaki na faɗa nayi wanka na ɗauro alwala dan azahar tayi. Ina fitowa na buɗe akwatina na zaro goduwar riga na zura, mayafin rigar na zaro sai katin Alhaji Zaidu ya faɗo. Ɗauka nayi nabi numbobin da kallo na sake adanawa a cikin akwatin. Wayar da ya siyamun sabuwa na ciro na jona a chaji kana na tada kabbarar sallah. Ina zaune akan sallaya ina adda'ar Allah ya zaɓa mun mafi alkhairi a cikin waɗannan maneman nawa biyu. Duk da a zahirance Alhaji Zaidu yafi nagarta sai dai sanin baɗini sai Allah masanin komai. Amman ni dai hankalina yafi nutsuwa da Alhaji Zaidu. Na jiyo an danna ƙararrawar ɗakin. A hankali na miƙe na je na buɗe ƙofar wata ma'aikaciyace ɗauke da abinci a tire ta diremun a ƙaramin teburin ɗakin ta fita. Farfesun kaza ne sai shayi mai zafi. A tsanake na cinye shayinma na shanye shi tas nayi kwanciyata domin in huce gajiya. Bacci nayi mai daɗi cike da mafarkan Alhaji Zaidu. Ko dana farka naga ashe mafarki nayi ba zahiri bane sai kawai nayi murmushi tare da furta. Allah yasa abinda na gani ya tabbata a gaske in dai kaine mafi Alkhairi" Miƙewa nayi na ɗauro alwala dan ƙarfe fa biyar lallai kuwa nayi bacci sosai. Kafin in kai ga soma sallah naji ƙararrawar ɗakin tayi ƙara ashe Maigogul ne. "Lolo bacci kike yi ne haka wai? " E yanzu na tashi zanyi Sallah kenan. "To kinsan fa jirgin ƙarfe bakwai zamu hau mu koma gida ko? Ba kwana zamu yi ba. To Alhaji yana son ku ɗan fita yace dani zai miki siyayya kuma yana so ku samu keɓewa dashi sabida ku zanta. Lolo dan Allah ki daure dai ki amsheshi zaki huta a gidanshi matanshi suna fantamawa wallahi gasar zuwa umara da Dubai kawai akeyi a gidanshi kafin ɗayar Allah yayi mata rasuwa ɗayar kuma sata ta kuntuka da dalolin amurka shine ya saketa. Ungo wannan kwallin ki goga in zaku fita kada ki kuskure ki ambaci sunanshi in zaki shafa sunanshi Bilya muna kiranshi Bili maina sunane da ake kiranshi na gidansu. " Hannu nasa na karɓi kwallin. Maigogul dan Allah wacce haja zaka tallatama wannan Alhajin da kace ne? " Kallona yayi sai yayi murmushi. "Lolo ki kwantar da hankalinki babu abinda na tallata mishi. Ba sana'ata na tallata mishi ba. Wasu motoci na tallata mishi sabida ƙulla alaƙar arziki. Shine yake sanarmun ashe shima yana da gonar motoci ashe hamshaƙin mai kuɗin gaskene. Yazo ai munfi awa guda muna hira. Ni lolo dama zaice yana sonki mana da mun caɓa amman nasan ina bazai ce ba. Dan hamshaƙine sosai fa na fahimci haka a ɗan bayanin da yayi mun. Amman har hirarki nayi mishi wallahi na cusaki da dabars " Me kace mishi to a kaina? " "Me kuwa na sake jaddada mishi ke bazawarace mana da yawan yaranki, sai son taimakon ƴan uwanki da kike dashi. Lolo na faɗa mishi hakanne wala Allah ko zaiji wani abu a kanki. Ina sonki dai da arziki dan nasan kece zaki shiga cikin arziki mu kuma mu shiga cikin alkhairi dumu dumu. " Dariya muka yi a tare daidai lokacin Alhaji Zaidu yazo wucewa. Muka haɗa idanu haka siddan nake jin kunyarshi harma nake ganin tamkar na aikata mishi wani gagarumin laifi. Kuma ace ankai awa guda da Maigogul ana hira shikenan ai Maigogul ya kama tuɓe mun zani nasan tas. "Alhaji Baba kana ji da wannan shalele taka ni abun har burgeni yake yi" Ya faɗa a ladabce yana ɗan murmushin da a ƙasanshi akwai magana. Ai firit maigogul ya juyo yana washe bakinshi. "Ai wannan itace duniyata ita da ɗan uwanta Uzairu zuchiyata. Yarane masu son iyayensu da tausayin kowa Alhaji. To ina dai sake lallashinta ne kan sha'anin zawarci kasan na faɗa maka iddar bata daɗe da gamawa ba. To ita tsoronta waye zai tausaya mata..... Ni dai illahirin kunya bata barni na tsaya na gama jin abinda Maigogul zaice mishi ba. Ya suka ƙare ban sani ba. Kwallin daya bani na ajjiye a kan gado na tada kabbarar sallah. Na ɗan jima ina nazari har saida Uzairu zuchiyata aka aikoshi wai in fito Alhaji Bilya yana ƙasa a mota yana jirana. A yadda nake haka na fice sai kwalli dana zizara dan gudun kada Maigogul ya gane naƙi saka kwallin daya bani. Bani da burin kowa ya soni, ko in jawo hankalin wani ta hanyar asiri. Na fiso so yayi aiki da kanshi. Kuma a cikin su biyunnan wallahi duk wanda ya nuna da gaske yake yi zan aureshi in sha Allah. Alhaji Zaidu ma nasan zuwa yanzu ya tsinke da lamarinmu. Ficewa nayi sannu kan hankali na sauka ƙasa har zuwa wajen mota. Alhaji Bilya da kanshi ya buɗe mun gidan gaba na zauna ya ja muka lula munyi tafiya mai nisa ba tare da yace dani kanzil ba. Nima bance ci kanka ba sai can dai ya ɗan dubeni kaɗan tare da washe bakinshi. "Ai Sabuwa ban taɓa sanin Maigogul yana da ƴa tsaleliya irinki ba wallahi ai da tuni na lallaɓo. Duk da dai ya faɗa mun auren naki bai jima da ƙarewa ba kuma a kotu ma aka raba auren. " Wani ƙududune ya tokare mun maƙoshina jin abinda yace. Shi dai maigogul yafi sha'awar yaita bayani. Yanzu ina shi ina bama Alhaji Bilya labarin yadda aurena ya mutu domin Allah fa? Nasanma ya riga da yasan komai ma. Ɗan murmushi nayi nace. Kasan komai kamawa take yi yanzu gashi data kama mun haɗu" Dariya yayi yace. "Hakane Sabuwa. Ai gaskiya inna sameki na rufe ƙofa da kyau. Wannan ke ai duk wata semina dake za'aje su Hajiya sai dai suyi haƙuri kawai tunda babu ƙasar da basu zagayaba adai ƙasashen da nake hulɗa dasu. Wani sa'inma nakan rasa mai mun rakiya dake duk suna kasuwancinsu a lokacin muna tare. To ita ɗayar rasuwa tayi. Ɗayar kuma da mun rabu amman Allah cikin ikonshi an mayar da auren sai dai bata tare ba. Ke in munyi auren me kike so ki riƙa da zaki juya taro ya dawo sisi? " Idanuna na lumshe a hankali na buɗe sai nace. To wannan maganar ai inaga a barta har sai zuwa in anyi auren a tattauna. Kenan yanzu matarka ɗaya ko? " "Ƙwarai kuwa matana ɗaya yarana ashirin cib kuma duk suna raye. Amman kada fa ki damu a gidana hatta gadon da kika kwanta masu aikine zasu gyara miki. Kar kizo kiji tsoron shiga dan kinji tulin yara ai gaskiya ne ko? " Murmushin dole nayi kawai Nasan a cikin raina Alhaji Bilya yayi ma ƙoƙari da har yaji yana son aurena a irin rayuwata dai. Kuma nasan in baisan labarin rabin rayuwata ba. Tofa yasan kwata in dai Maigogul ne. Haka dai na sake mukaita hira har muka iso wani ƙaton kanti dake ƙunshe da komai. Da kanshi ya buɗe mun murfin mota na fito. Ya tusani gaba muka shiga kantin ga ciki a gaba him. Mata da maza anata kai kawo na siyayya a kantin kowa ka gani da kwando a hannunshi. Wani layin turaruka da mayamayai da sabulai ya soma kaini. A dai taƙaice yayi mun siyayya mai yawa danma ina noƙewane shi ba haka gogan naku ya so ba. Mun dai tattauna babu laifi kafin muka dawo Hotel. Saida muka isa filin jirgi muke jin cewar jirgi sai gobe bakwai na safe zai tashi sakamakon babu jirgi a ƙasa. Haka muka kuma dawowa Hotel Da daddare ina kwance ga sabuwar wayata ga katin da Alhaji Zaidu ya bani. Ina kwafe number wani shashe na zuchiyata yana nuna mun kada fa ace nayi azarɓaɓi da yawa tunda shima yana da lambata amman bai kira ba. Wani shashen kuma yana jana da in kira. Take nabi shashen da hankalina yafi raja'a a kai na danna kira tare da karawa a kunnena ina kuma dafe da ƙirjina. Wayar kamar dai zata tsinke sai kuma aka ɗaga. Da kuma naji muryarshi ya ratsa dodon kunnena saina kasa sarrafa harshena yana sallama amman da ƙyar na iya amsawa. Sautin murmushinshi da ajjiyar zuchiyarshi suka sake sani faɗuwar gaba. "Shalele kin kuwa kirani a daidai. Dan ɗazu kasa mallakar kaina nayi har da zanje in tambayi Uzairu lambarki sabida na rasa lambar taki a wayata. to kunyar Alhaji Baba ce tasa har naje ƙofar ɗakin na juyo na dawo nawa ɗakin. Yanzunma a kwance nake zuchiyata nata ƙara burunƙasamun ke. Murmushi nayi mishi mai sanyi tare da cewa. Allah sarki nima ina kwance ne shiru shine nace dai bari in taɓoka to gashi ka sake samu lambar wayata" Murmushi yayi yace dani. "Kin kuwa kyauta sosai yanzu zan saka ma lambar sabon suna. In kuka koma gida yaushe ni za'a bani damar zuwa inji amsata kar daga kallon ruwa kwaɗo yayi mun ƙasa. Naga wani Alhajin nason ya kasani a hannun Shalele. Duk da a jikina nake jin shalele dai tawa ce" Mun jima muna hirarmu ta mutunci da dattijantaka da natija. Ni na zaci saurayi da budurwa, ko ince ma'abota soyayya dole sai sunyi batsa shine soyayya ashe sam ba hakan bane. Duk samarina in banda Madubala in sun kirani a waya maganganune na tayar da hankula kawai muke aikema juna, sai yau da naji wani sabin abun Daga ƙarshe mukaima juna sallama. Zukatanmu suka kwana a cike da farin ciki. Ni dai a ranar nayi mafarkai da yawa daga wannan mafarkin in ɓulla wancan sai dai kash ba irin mafarkan da in aka wayi gari zaka iya tunasu turyan _turyan bane sai dai ka tsinci na tsinta. Da sassafe muka wuce Airport da niƙi niƙin kayayyakin tsarabarmu. Ƙarfe bakwai da rabi jirginmu ya ɗaga zuwa Kano ta dabo tumbin giwa gari in ba Kano ba dajin Allah. A Aiport muka tarar da motar da Alhaji Bilya ya turo azo a ɗaukemu tana jiranmu. Kai tsaye jigawa muka dosa muna tafe Maigogul nayi ma Alhaji Bilya hira bashi yayi shiru ba har saida bacci yayi awon gaba dai dashi kana ya samarwa da kanshi lafiya. Wajajen sha biyu da rabi muka tsaya a ƙofar gida. Rakiya muka gani saɓe da mayafinta zata fita ga zoɓo tana sha a leda. Ganinmu ne yasa ta tsaya tayi turus tana kallonmu da fara'a ɗauke a fuskarta. Uzairu zuchiyata kuwa yana fitowa Rakiya ta soma tafi tana kiran sunanshi. Da gudu Labbai ta fito ko mayafi babu a jikinta ta rungumeni muka saka dariya. Uzairu zuchiyata sai wani dariya da ƙwanbo yake yi. Maigogul kuma yana cikin mota bai fito ba har saida muka sauke kab kayanmu kana suka fito da Alhaji Bilya. "Kayi nayi gafa surukinki ki matso ku gaisa" Alhaji Bilya yace. "A_a Maigogul wai ya kake magana haka kamar ba'a farsa maka bakinka bane. Ni ai ya kamata inje in gaisheta ka fiye katoɓara" Wannan kalmar daya faɗama Maigogul da daki zuhina sosai. Amman nasan bashi da laifi babban mai laifin Msigogul ne. Da haka na ja akwatina kiii zuwa cikin gida nan na tarar da Hauwa dasu Layuza da Aliya suna zaune suna cin taliyar murji da manja da yaji. "Ahh kaga mutan turai ashe kuna tafe ai tun jiya muke saka rai daku" Ayya Hauwa dake jiya an samu matsala jirgin bai samu damar tashi ba sai yau." Shigowar su Adama dasu Uzairu Zuchiyata ne ya katsemu. Adama kece kika ƙone haka a hannunki ashe har abun ya kai haka Adama?" A gigice na ƙarasa gabanta ina kallon hannun. Buɗar bakin Hauwa tace. "Gaza ai yaje ya rama mata tunda Allah ya hore muku Gaza ai saiku taka uban kowa. Miji kuwa tunda ta dawo gida ko ƙyeyarshi bamu... " "Munafuka kai Hauwa halinki sai dai abar miki. Anya Hauwa zaki dena munafurci kuwa? Ba zaki ga Annabi ba" Shewa Hauwa ta saka. Uzairu zuchiyata har dashi a shewar ɗan yi. "To ƙarya nayi ne ko yazo? . Ƙila ma auren ai mutuwa yayi ake rufe mana. " "To a rufe miki kewa. Naga Aliya ce gata ta dawo daga yawo karuwanci da ciwo ya kamata aka dawo miki da'ita. Binta fa tana ɗaki an sakota, ga Layuza da kike taƙamar itace mai gasa da Lolo itama an sakota. To na me zan ɓoye miki dan an saki Adama aikin banza a kab ɗakina babu wata mace data tafi yawon karuwanci har ba'a san inda take ba saida ciwo ya kawota" Bakina na taɓe na shige ciki Uzairu zuchiyata ya biyo bayana. Su Rakiya saida Maigogul ya shigo kana ya tsawatar musu. "Aikinku kenan ɗaga murya sai kace gidannane kaɗai gida. Kundai ji kunya wallahi. Ke Adama Labbai ku shige mu je ciki mu tarbi su lolo yaushe ma zaku daka ta Hauwa da ƴaƴanta" Suka shigo suka bar Hauwa da kumfar baki. "Lolo kije kuyi sallama da Billy zai tafi maza jeki ɗiyar kirki" Mayafina na zura na fito. Hararata Layuza tayi da muka haɗa idanu. Ni kuwa nayi mata dariyar mugunta na kaɗa kai na fita. A zaure naci karo da magazin. "Ahh Hayya hayya babbar yarinya kaga Sabuwa mai sabon aiki. Baki kwantan aiki ai wallahi ina gwanin wani ga tawa. Ai na dawo Fada yake faɗa mana ashe Uzairu zuchiyata ya samu wata baturiya zata aureshi shine kuka tafi tare. Ya ina batun tsaraba Lolo? " Dariya muka yi duka nace. Magazin duniya tsaraba maza shiga kada a kasafta baka" Ina faɗin haka na fita, shi kuma ya shiga gidan da mugun gudu yana ihu. Ƙarasawa nayi jikin motar Alhaji Bilya na jingina kawai na zuba mishi fararen idanuna. Hannayenshi harɗe bisa ƙirjinshi yanata kallona. "Wato Sabuwa kina da kyau mai tasiri sosai hasken idanunki kaɗai ya isa in shagaltu da kallonki" Zai sake yanko magana na datseshi ta hanyar cewa. Yanzu dai kaga na gaji hutu nake buƙata sosai. Kuma ƴan uwana ma suna buƙatar lokacina ka saka rana sai ka dawo ko? " Murmushi yayi ya gyaɗa kanshi. "To to naji. Nan da yaushe kike ganin zan dawo mu tattauna ni dake mu tsayar da matsaya guda ɗaya sabida ni bana son auren ya wani ɗauki lokaci gaskiya. " To inaga nan da kwana huɗu ko biyar kana iya zuwa kafinnan na huta sai kaji ra'ayina ko? Nagode ni zan shiga ciki" Hannu ya saka a ajjihu ya ɗebo kuɗi ya bani nasa hannu na amsa nayi godiya. Daidai yana bani kuɗin Layuza ta fito turus tayi da ganin ƙatuwar motar da muke jungine a jiki. To Alhaji nagode ka gaida iyalan, sai munyi waya" Na ƙarashe ina fara'a ƙaƙas. Saida naga yaja motarshi ya gangara sannan na nufi gida Layuza na tsaye ta babbake a ƙofar gidan. Malama zan wuce ko? " "Aikin banza dan wannan tsohon yazo wajenki shine har kike fiffiƙa? Sabida shi kenan kika kaso auren dan kizo kici gaba da iskanci a gaban Rakiya uwark... " Buf Gaza ya buge mata bakinta ta baya ya hankaɗota tazo ta rungumeni. "Ke Rakiya rabin raina wai kike zagi dan abu ta kazanki yarinya sai baƙin ciki da hassada ashe baki dena hassada da Lolo ba? Eh wallahi lolo tafi ƙarfinki kina gidannan zaki ga irin mijin da eh zai aureta. Dena kallona dan abu ta kazan ehhh. " Ba shiri tayi ƙasa da kanta Gaza kuma yace. "Ke lolo shige gida ni fita zanyi zanje wani aiki ne saina dawo ma haɗe ko a mutu ko ayi rai. Ko a kasheni a kawo muku gawata, ko in kashe, in tsere, ko a killaceni a gidan yari eh wallahi Allah" Ya gangara da Rahine a kafaɗarshi jikinshi da kayan farauta. Murmushi nayi ma Layuza da naga jini a bakinta ya wanke mata haƙora. Ina shiga ɗakinmu na tarar Maigogul yayi zaman daɓaro da akwatuna a gabanshi anata ganin kaya. Uzairu zuchiyata yana ta wawware ma kowa tsarabarshi. Nan su Aisha ma suka shigo muka ba kowa tsarabarshi kayana kuma duk na tattare. Maigogul ya cika cake a baki ga lemun kwali yana korawa yace. "To batun auren kuma Uzairu zuchiyata ni shi yafi damuna yaushe kuka tsayar ne kaga in baiyi tsayi ba ai sai a haɗa dana lolo tunda Alhaji Bilya shi yace baya son ya ɗauki lokaci. Uzairu zuchiyata yace. " To ita tace tana son nashi ne a dai bi a hankali gaskiya. Ni aurena da Felisha nan da wata uku ne. Ni abinda yafi damuna iyayenta sun nuna dole anan Najeriya suke son a ɗaura auren suna son ganin iyayena da dangina kafin mu ɗunguma muje ayi bikin coci. To ni Dad maigogul a wannan gidan zan kawosu? " Dariya duk muka kwashe dashi Maigogul harda dukan cinyar magazin. Saida ya kuskure baki da jus kafin yace. "Wannan fa mai sauƙine wallahi a rashin hankali irinna turawa sai kaga in suka ga gidannan ya burgesu babu mamaki suita ɗaukar su Rakiya hoto dasu da gidan sabida sha'awa Ni inaga fenti kawai za'aima gidan ai. Wannan katangar a ƙara mata tsayi a saka ƙofa wai ba shikenan bane, sai filastar tsakar gida ai an gama" Ai kuwa ina wuta Rakiya ta saka maigogul da ƙyar rikici ya lafa. Adama tace. "Gaskiya ne ba sai kayi wata ƙaryar ba sufa turawa babu ruwansu rayuwa mai sauƙi suke yi." Hararar Adama yayi yace. "Tabb nifa gaskiya sai dai mu koma wani gidan koma gidan hayane na wani lokacin sai dai mu kama" "To Allah ya kaimu ai sai a kama ƙaton gida ayi bikin ba shikenan ba. Ni zanma iya samo mana ƙaton gida ayi komai a gama mu da muke da Alhazai ko wani ges house ɗin zan iya samo maka. Ince dai dani za'a tafi bikin cocin ko? " Maigogul ya tambaya yana zare idanunshi. "Yauwa yanzu naji sanyi wayyo Daɗi. Dakai da Rakiya da lolo, sai Adama ko Labbai, ko kuma Gaza ko Magazin dai a cikinsu za'a ɗauki ɗaya sukenan iyakar ƴan rakiyar dai da muka tsara da'ita Felishar su su Salaha ko suna in ta haihu sa zo tunda bazai yiwu mu tafi dukka ba" Mun sha hira sosai ranar hirar yaushe gamo. Bayan la'asar muka fito muka ɗaura abinci taliya da kifi sutu sutu Hauwa sai kallonmu take yi. Tsarabar biskit da lemun kwali na bata tai ta murna tana godiya dai. Bamu muka samu kanmu ba sai bayan isha sannan muka runtuma zuwa ɗakinmu kuma fitowata wanka kenan wayata naji tana ruri ina ɗagawa naga Alhaji Zaidu ne. Idanuna na lumshe na ɗan murmusa kafin na ɗauki wayar muka gaisa a tsanake, muka tambayi juna gajiyar hanya. Baka gida a irin wannan lokacin, ko kaima mai zaman majalisar maza ne? " Dariya na bashi sosai sai da yayi ta isheshi kafin yace. "Me zaman majalisar kike nema, ko kuwa shi kike gudu? " Kunji tambayar hankali da hikima a wajen manya ko? Murmushi nayi nace. To sai naji a wanne bigire kike kafin inyi aman abunda ke raina" "To naji wayon. Ai Antinki ba zata taɓa barina inyi zaman majalisa ba sam. Ni da ko aiki zan fita sai munyi tababa da'ita kafin ma ta amince wata rana ma sai dai muje tare mu dawo tare. Kin ganni dai yanzu nake shirin komawa cikin gida maƙocinmu ne yayi sallama dani." Allah sarki ai ta kyauta kuma haka akeson mace. To nagode da kulawa yana da kyau ka shiga gida" "Kafin dai muyi sallama zan sanar miki gobe inaso zan shigo dutse da fatan zan samu tarba? " Idanu na zare nace. Me zaka zo yi a Dutse? " Sai da yayi murmushi tare da ambaton Shalele kafin yace. " "Ni kaina bana ce ba. Ni ba yaro ba, kuma ba sabon shigan soyayya ba. Sai dai taki ta kasance ta musamman. Zuchiyatace take fusgata lallai tana son jin cikakkiyar amsar wanne muhalli muka samu. Wata zuchiyar kuma tace dani garin kallon ruwa Zaidu kada kwaɗo yayi maka ƙafa" Idanu na lumshe a hankali na furta. Allah ya kawoka lafiya, ya tsare hanya" Da wannan mukai sallama. Na labartama su Labbai waye Alhaji Zaidu. Amman na lulluɓe sirrinshi na rashin haihuwa. Sai dai sun san bashi da yara dai Sun haɗu sun taya ni murna sun kuma bani shawarar gara in ɗaukeshi in yi fatali da Alhaji Bily indi maigogul. "Amman ki killace kayanki gaskiya ki bashi daman zuwa sau ɗaya rak. Ragowar komai a gama a waya kinsan Allah yazo ya kuma kema kinsan sauran. Tunda ku ba yara bane dama za'a haɗa dana Uzairu zuchiyata ai da yafi. Ohh ranar za'a ga abu. Allah yasa kafin lokacin hannuna ya warke" Labbai tace. "Uhm wallahi gaskiya aka faɗa miki kiyi auren sirri kawai. Ohh ke dai lolo sa'a tafiya kuke yi kunnen doki, daga gama idda sai samun mazajen aure harma saida kika zaɓa. To ni zanma Maigogul magana ya haɗani da shi Bily ɗin nima in ci albarkacinki gaskiya" Adama tace. "A jarraba gaskiya Labbai. Inma yace a_a gasu Salaha, su Aisha ya zaɓa ya dirje. Ke lolo ke zaki yi mana wannan. Ko ni yace yana so wallahi da gudu zanje in amso takaddata tunda dama auren tangal tangal yake yi" Dariya nayi nace. Gaskiya wannan kishiya ba za'a zaman lafiya da'ita ba. Amman ƙila tunda Gaza ya taɓata ta sama miki lafiya. Ke dai ki lallaɓa ki koma zaifi miki" Baki ta taɓe tace. "Gashi anata bashi shawarar ya tsaya takara ba. Kai amman fa bambamcinshi da Alhaji tili na kofur zubaina Ghana wallahi kaɗanne ke lolo kinga yinwa. Amman inna tuno ko gidanmu ma kai kake nema ka ciyar da kanka sai inji dama dama can ɗin dai. Allah cuta Allah magani dai abun wallahi." Mun kai kusan biyun dare muna hira mune harda shewa. Labbai kuwa dariya harda tsugunnawa dan mugunta. Allah sarki ƴan uwa akwai daɗi musamman mata, in kuma akaci sa'a kawunanku basu rabeba babu baƙin ciki a zuchiyar kowa. Da tunane _tunane na kwana a raina. Washegari na tashi da shirin tarban baƙo. Ƙarfe tara ya baro kano dake a ranar yake son komawa. Ba shirin na shiga shirin tarbarshi zuchiyata na bugawa da ƙarfi da ƙarfi. Labbai na ɗauka muka je ƴar kasuwa cefane muka dawo nandanan muka fito da risho ƙofar ɗaki na soma aikin abinci. "To wai Lolo amman shigowa zaiyi yaci abincin anan gidan dai ba'a waje zai tsaya ba ko? Nifa ina jiye miki ƴan unguwarnan su ganshi ne. Kinsan Allah ko uwar Ƴar Shuwa taganshi sai tayi duk yadda tayi taje ta tareshi har titi ta tona miki asiri. Ni dai shawara kawai kai tsaye ma da kin leƙa kice mishi ku shigo. " Ina kwashe kazar dana soya na tsoma cikin jajjagen attaruhu nace. "Kinsan gidannan gidan matan aurene gasu da munafurci na masifa taya zan ɗakko namiji in shigo dashi dama kallon karuwaima suke mun. Kuma na faɗa miki sunyi hira ta awa guda da Maigogul me kike tsammanin ya saura a cikin sirrinmu ma? " Adama da fitowarta daga ciki kenan zata tafi wanka tayi ƙasa da murya tace. "Uhm abinda labbai ta faɗa miki shi za'ayi" Dole na amince da haka Labbai ce ta ƙarashe mun girkin ni kuma nayo wanka na shirya cikin wata jar atampa mai agon baƙi da fari abinka da farar fata sai atampar ta haskani sosai. Kirana yayi ya sanar mun gashi a cikin layin dana kwatanta mishi in fito. Turare na fesa. Ci gaban zai zo fejinne ya yanke........ ✍🏻 [10/4, 10:29 PM] +234 810 593 2041: ƘARASHEN PAGE 2 NE KADA KU RUƊE Turare na ɗauka na feffesa na zari mayafina na nufi zaure. Adama da labbai suna gefen ɗakin a tabarma suna hirarsu. Ina fita na hangoshi daidai ƙofar gidansu maigogul. Saida naji faɗuwar gaba cike da taraddadi na soma haurawa. Yana da wata iriyar nutsuwane da kamala kamar Baba Malam yanayinshi yake yi mun. Wata farar mota ce ta wuce ni ta paka a bayan motar Alhaji Zaidu. Wata farar kyakkyawar macece ta fito cikin shigar kamala. Wuceta nazo zanyi ina kallon Alhaji Zaidu dake jingine a jikin motarshi yana kallona fuskarshi cike da annuri kuma da gani a shagale yake wajen kallon nawa. A cikin ƙwayar idanunshi nake iya karanta saƙon da zuchiyarshi ke ɗauke da'ita "Amm baiwar Allah dan Allah ina tambayane gidansu Maigogul Kawali" Dum naji ƙirjina ya buga da sauri na kalleta mukai kallon kallo da'ita. Gashi batai kama da mutuniyar banza ba a ido balle inyi tunanin ko irin jama'arshi ce. Sannan nasan ya dena harkar tsubbu balle ince ko magani tazo ya bata tunda daga irin motarta kasan mai arzikice zaiyi wuya tayi hulɗa dasu Maigogul. "Ai kece ma wacce nake nema bake bace Sabuwa tsohuwar budurwar mijina Khalid ba. Kwartuwa mai bin mazan mutane ayi zina da'ita akan gadon sunnah. Ko da yake ubanki ai kawaline dole ma ku zama haka dan abu ta kazan ubanki" Illahirin kunya ne ya kamani wallahi zuchiyata har tsalle take yi mun tsabar tashin hankalin dana shiga. Kaina naga tayo a hassale daidai fitowar Gaza su Rahine da yaranta na biye dashi harda wani muzuru baƙi mai ɗaure da ƙatuwar baƙar laya a wuya Mrs Bukhari.
Na ƙoƙarta nayi muku Typing da yawa. Amman maganar gaskiya sai zuwa Monday dai zaku jini in sha Allah A fito ayita sharhi kawai Son so [10/4, 10:29 PM] +234 810 593 2041: IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA HUƊU SHAFI NA UKU
GIDAN B HOUSE:.