Kenza eBookz

Idan kaya ya gaji book book 4 - Chapter 3

Idan kaya ya gaji book book 4 - Chapter 3

Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 3: Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 3. Ƴar Shuwa ce yau da girki gobe kuma zata wuce Bamaina wajen Sameerah ta…

3,786 words

Ƴar Shuwa ce yau da girki gobe kuma zata wuce Bamaina wajen Sameerah ta gama shirinta tsab ta zuba kayanta a akwati, ƙannenta da suka zo ta basu su Fati sun tafi dasu gida. Tuwon shinkafa miyar kuɓewa ɗanya tayi harda nama gundun_ gundun. Yanzu ai ƴar Shuwa daɗi take ci sosai musamman ranar da Babangida baya ɗakinta tunda in yaga abun yayi yawa yana yawan tuhumarta ta fahimci yana zarginta sosai. Sai tayi mishi ƙaryar kasuwanci take yi ƙannenta ke saida mata acan layinsu. Ya dai jine amman bai yadda ba. Tana kan kwashe tuwo Babangida ya shigo jikinshi saye da biri da wando na aikin Baban bola da yake yi ya shige ciki. "Sannu da shigowa Jannaty" "Yauwa sannunki da aiki anata aiki kenan" Ya shige kai tsaye banɗaki ya shiga zai watsa ruwa yaga Ƴar Shuwa ta siyo wasu sabulan wanka manya na ruwa masu tsada ko a ido, ga wasu kayan ƙamshi da sabulan ƙamshi duk a banɗakin. Har buta da randar banɗakin ta sauya da sababbi. Cike da damuwa da fargaba ya gama wankan a gurguje ya fito ya wuce masallaci tare da su Aɗɗa'u Sai da akayi isha ya soma yima magidanta karatu a masallacin tunaninshi yana kan to ina Ƴar Shuwa take samo kuɗi take wannan siyayyar. Haka dai ya lallaɓa takwas da minti hamsin ya tashesu ya shiga gida. Saida ya tambayi mardiyya babu abinda suke buƙata suka tabbatar mishi babu kafin yayi musu sallama tare da umartarsu suyi adda'ar bacci kafin su kwanta. Sauran matan nashi saida ya bisu ya duba lafiyarsu data yara ya tambayesu ko akwai abinda suke buƙata kafin ya yada zangonshi a ɗakin da yake. Sababbin kuloli ɗebi da kanka yaga an zuba mishi abinci harda zoɓo mai sanyi. Zama yayi yana ƙarema ƴar shuwa kallo tayi ƙunshi da lalle na tafiya yana lure da'ita har gyaran jiki yaga tana yi kallonta kawai yake yi. "Jannati ga ruwa ka wanke hannunka kaci tuwo. Ko a baki za'a baka ne? " Murmushi yayi yace. "A_a zanci da kaina nagode" Wanke hannunshi yayi a robar ruwan wanke hannun ta zuba mishi tuwon ta turo gabanshi. Cinyar kaza da ɓangaren ƙirji ta saka mishi ga bushssshen kifi yana gani ido da ido harma da ɗanyen kifi dukka. "Duk a kuɗin dana baki kiyi cefanene kika sai kaza da kifi? Nifa na kasa gane irin kuɗin da kike kashewa da irin canja abubbuwa da kike yi ke ki faɗamun a inda kike samun kuɗi abun ya wuce kuɗin kasuwanci har nawa kike juyawa cinikin nawa kike yi haka a rana nifa ba mahaukaci bane, ba kuma Babangidan da kika sani da bane mai adankiya da iyalanshi" Yayi kicin _kicin da ranshi har da ture abincin a gabanshi. Ƴar Shuwa ma takai iyakar maƙurar ƙuluwa sabida dai bata son suyi rikicinne kada ya shafi tafiyarta shi yasa ta sassauto. "Haba Jannati to shikenan ina kasuwanci sai in kasa cin abinda nake so a lokacin da nake so? Wai ni kam zargina kake yine ko me kake nufi? " "Zargi sosai ma zargi irin da namijin da yasan kanshi yake yi dan gudun kada iyalanshi su faɗa halaka. Hakkinane duk abinda zaki yi ki sanar dani inyi nazari akai, bawai inzo inga kifi inga nama ba, alhalin ni nasan ban bayar ba. Kasuwancin da Ke fakewa dashi ban ganshi ba bare in auna jarin inga yayi daidai da ribar da aketa wadaƙa da'ita. Ban yadda dake ba kwata _kwata dan nasanki akan kuɗi kada fa ki manta nasanki ƙwar nasan yaya muka yi mukai aure. Me kike saidawa sannan inason a nuna mun abinda kike siyarwan" "To inna dawo zansa Mama ta aiko kayan ka gansu ko zaka samu nutsuwa" Ƙur yayi da idanunshi yana ƙare mata kallo. Can ya nisa a ƙoƙarinshi na kawar da kai yace. "To bari in kira Mama inji daga gareta sai in samu nutsuwa. Sabida hakkinane insan inda kike samun kuɗi ta hanyar halas ne ko akasin haka wanda bana fata. " Idanu ƴar Shuwa ta zaro waje hankalinta yayi mummunan tashi, yana kallonta yana karantar yanayinta har Mama ta ɗauki wayar tare da Sallama. "Babangida ince dai lafiya kira da daddare haka? ". "Mama lafiya ƙalau dama na kirane muyi magana dangane da kasuwancin Aisha. " Mama buɗar bakinta tace. "To ina jinka wani abunne ya faru Babangida, ko dai jari zaka bata? " Ajjiyae zuchiya ya sauke duk da bawai ta gamsuwa bace. Yana kallo itama ta sauke ajjiyar zuchiya. "A_a dama so nake in tambaya me take saidawane sannan jarin waya bata kuma nawa ne? " "Haba Babangida wannan ai tsakaninka da matarka ne ya ina uwa zaka zo ka titsiyeni kana tuhumata ko zargi kake yi shin ƴan uwanta ba zasu iya bata jari ta juya ba kenan kome kake nufi? Kuma kuɗinnan ma aro aka bata ribar kawai take cirewa uwar kuɗin ba tata bace ƙanina taima ƙorafin rashin sana'a tunda kai ka samu karayar arziki shine ya tallafa mata take saida dogayen riguna da takalma" Murmushi yayi kawai in duk jikinshi kunnene bazai yadda da abinda Mama tace ba amman yaya zaiyi tunda bashi da hujja? "To shikenan dangane da batun biki kuma ayi haƙuri na janye ba zata samu zuwa ba gaskiya. Wata rana taje ko in wani bikin ya tashi. " A zabure ƴar Shuwa ta kalleshi harda dafe ƙirjinta. A sanyaye Mama tace. "Shikenan tayi zamanta ai ba wani abun bane biki kam muna dasu da yawa kamar yadda kace wani jiƙon taje ni kaina bana jin daɗin ƙafata ba lallai inje ba sai da safenku to" Yana sauke wayar tace. "Ban fa gane me kake nufi ba. Ya zaka ce ka barni in gama shiryawa tsab kuma saida tafiya ta rage gobe kawai zaka ce ka fasa. Ohh shi yasa ka janyo magana kake tuhumar mahaifiyata akan kasuwancina? Wallahi bafa zai yiwu ba. Nifa nagaji da wannan mulkin da kake yi mun name akan kuma wanne dalilin? Kai ba sisi ba sai bin diddigi ka zaci kowa Sabuwa ne " Miƙewa yayi ya nufi hanyar waje ya barta tana ɓaɓatu har ya fita ya dawo tana gurfane a wajen tana ƙananun mita ta tusa tuwo gaba tana ci. Abinci ta gani a hannunshi ko daga wanne ɗakin ya karɓo oho lamarin daya dagula lissafinta kenan ta sake buɗe magana ganin baya magana yasa ta zage take ta maganganu. Ɗagowa yayi kawai ya sauke mata idanunshi da suka rine wallahi babu shiri ta risina. Ita har a ranta aiyanawa take yi Babangida asiri yayi mata son da take yi mishi bana lafiya bane kuma duk yadda akayi kafeta yayi. Bata san kamun Allah bane kawai yasa ta jarabtu da Babangida ba. "Ni kika tusa gaba da wannan gajiya da hayaniyar koyarwan da take kaina. Sabida kinga kura tayi lafiya ko? Hmm Aisha ki bini a hankali kinga waɗannan fitintinun bazan iya ɗaukarsu ba sabida haka ki kama kanki. A matsayina na mijinki hakkinane inji inda kika samo kuɗin da kike juyawa asalima dole saida izinina zaki soma kasuwancin. Batun zuwa biki kuma ni ba irin mazajen da suke barin matansu sasakai bane a titi kin gane ko? " "Amman naga Sabuwa har zangon katab ka barta taje biki kwananta nawa acan sai nine zaka ce haka." Miƙewa yayi ya nufi hanyar shiga ciki. "In banda abunki wani in yayi rawa aka bashi kuɗi wani in yayi duka zai sha. Kuma kinsan amincina da ita Sabuwanne?" Ya ƙarashe shiga ciki yana dariya shi kaɗai. Kai ƴar Shuwa ta jinjina tayi shiru ta zuba ma waje ɗaya idanu. "Wallahi ko dan in raba Sabuwa da Babangida dole ma in san duk yadda zan shigo in samu kuɗi. Wallahi ko tsirara zan dinga yawo Sabuwa bata isa ta dawo gidannan ba sannan dole saina juya Babangida ko a buzu yake kwana" Murmushi tayi a zahiri baɗininta kuma ita kaɗai tasan baƙin cikin da take ƙunsa. Abincinta taci ta ƙoshi yadda ya kamata tayi kwanciyarta a ƙasan kafet tana tunanin yadda zata yi da Sameerah. Tana cikin rabe ɗayan biyu wayarta ta shiga ruri daga uwarɗaki zumbur sai gata kan ƙafafunta, da sauri harda gudu_ gudu ta ƙarasa ɗakin taci Sa'a Babangida yana zaune akan kafet ya tanƙwashe ƙafafunshi yanata zuba karatun Qur'ani wani abu sha'awa da Babangida duk sati yake sauka tundai bayan rabuwarshi da Sabuwa. Ranar Juma'an dai zai yi sadaka, kuma ranar yake kai yara wajen Sabuwa, Ranar yake zuwa wajen Baba Malam ya dubashi. Yanajin zafi da ƙaiƙayi mai yawa a zuchiyarshi game da fishin Baba Malam da rabuwa da Sabuwa ji yake yi duk ranar da yaji labarin wani ya auran mishi Sabuwanshi tamkar katsewa rayuwarshi zata yi zai iya haɗiyar zuchiya ya mutu kowa ya huta. Da sauri dai gunɗu ta ɗauki wayarta ta fita duk da ma dai wayar ta katse tana ƙoƙarin bin bayan kiran kiran wayar ya sake shigowa ta ɗaga tana leƙen ƙofar korido. "Babyna zuchiyata a cike take tab da murnar da nake jin tamkar ko bacci daya fi kowa iya sata yau bai isa ya saceni ba yau ɗinnan. Gobe ƙarfe nawa zaki taso da so samune asubar fari sabida ki iso mu karya tare ko Baby.? " Ajjiyar zuchiya tayi tace. "To wallahi ya hanani zuwa kinsan Allah kafiyane dashi da tauri kamar kafuran farko. Hatta kuɗi da yaga ina kashewa saida ya kalubalanceni akai" Jim Samira tayi ta ɗauke wuta sosai tama rasa to ita mai zata ce sai ta soma sheshsheƙar kukan baƙun ciki kawai. Ƙasa _ƙasa ƴar Shuwa ta soma rarrashinta daga ƙarshe dai saida tace mata zata zo goben saidai ba zata kwana ba, shine Samirah ta yi murmushi. Itama murmushin tayi mata. "Shikenan zanje in kwanta mutuminki yau fishi yake yi sosai kinsanshi da zafin zuchiya" Wayar ta kashe ta shiga ciki Babangida yana inda ta barshi saidai yanzu ya ɗaga hannu sama yana kwararoma yaranshi adda'ar shiriya. Shafa adda'ar yayi ya tattare daddumar ya ajiyeta a saman durowar roba ta kayan yara, Qur'anin kuma ya ajjiyeshi a muhallinshi. Kwanciya yayi kusa da Ƴar Shuwa ya jawota cike da son samun nutsuwa. Amman saita ture mishi hannunshi. "Lafiya yau kuma ni ɗin ake gudu. Ko dan na hana tafiya bikine? Ki sani mutuncinki nake karewa a matsayina na mijinki, kuma nasan a cikin irin rayuwar da wa'iyazubillah muka haɗu kada kiga laifina. Daga gobe ma duk matar da nake ɗakinta zamu ware minti arba'in koma awa guda. Minti talatin in koya mata karatun Qur'ani ragowar minti talatin kuma muyi tafsirin inda na karantar da ko wacce. Tunda inanan ba sai kun shiga makaranta ba kuyi zamanku a gida a killace hakkine ratayayye a kaina in baku ilimi" Ƴar Shuwa dariya take tayi a zuchiyarta. A fuskarta kuwa ta turɓune harda juya baya. Murmushi yayi mata ya tada kanshi bisa matashin filo rufe idanunshi tare da ninƙaya a cikin tunani da begen Sabuwa. Allah yayi dare gari ya waye. Bayan Ƴar shuwa ta sallami Babangida da shayi da mummuƙi da wainar ƙwai ya gama ci zai tafi aiki sai Ƴar shuwa ta tareshi. "Inaso zanje unguwane dan Allah an gayyaceni sunan wata ƙawata" Agogon hannunshi ya kalla itama ya kalleta baiji ya yadda ba amman yana ƙoƙarin ganin ya kawar da wannan rashin yaddar sai yace. "Adawo lafiya kina da kuɗin mota ne? " "E akwai kuɗi a hannuna nagode". Sallama yayi mata ya nufi wajen su Mardiyya tare suka fita. Da wani bawan Allah matashi suka ci karo sai yaga mardiyya na kallonshi kallo irin na sani. Babangida bai fita daga mamaki ba yaji wannan matashi yace.. " Baba barka da fitowa an tashi lafiya? ". Matashin ha'a harda tsugunnawa. Da fara'a kacigari ya amsa mishi ya bashi umarnin tashi tsaye. " Mardiiya ki jirani a wajen babur ɗina Aminu ku kuma sai kun dawo ku riƙe hannun Usama da kyau" Saida suka bar wajen Babangida ya ce. "Samari meke tafe da kaine? " Cikin kunya yace. "Am dama Baba ita mardiyya ce nake yawan haɗuwa da'ita a hanyar dawowanta makaranta nima a lokacin na taso aikina. To sau dai ɗaya na tareta saita nuna mun rashin dacewar hakan. To itace tamun kwatancen gidannan tace inzo in nemi izini a wajenka. To ashe ma Malam kaine ai ina daga cikin ɗalibanka na asuba da kake koyarwa a masallaci." Dam Babangida gabanshi ya faɗi aure da siyasa sune abunda suka fi tono asalin mutum da asalin ɓoyayyen halinshi yana tsoron ranar da allura zata tono garma amman to yaya zaiyi tunda bazaice mardiyya ba zata yi zance ba. Kuma na daga cikin hikimar Malam na zaɓarma Sauban mardiyya. "To naji jawabanka ka ɗan bani lokaci gobe da daddare kazo akwai wani abun da nake son tabbatarwa tukunna kafin kaji daga gareni ko. Yaya sunan naka". " Sunana Sale ɗan gidan malam Baita" "A ina kake aiki menene matakin karatunka? " Kai Sale ya sosa yace. "To ma'aikacin gwammati ne dai saidai ina taɓa kasuwancin shadda da takalmin maza. Matakin karatuna kuma mastas gareni ta fannin addini kuma inada izifi talatin" Murmushi Babangida yayi yace. "Masha Allah nazari ko hadda? " "Hadda in sha Allah Baba" "Nagode da girmamawa Sale lokacin dana baka in yayi sai ka dawo zaka ji amsa daga gareni" Da haka sukai sallama Babangida ya ɗauki Mardiyya yaje ya sauketa a makaranta harta juya ya kira sunanta ta dawo cike da kunya Yana mamakin yarinya irin kunyarta da hankalinta tamkar ba uwar da uban bane iyayenta. "Shi Salen kina ganin yayi miki a matsayin miji izifi talatin gareshi hadda, kuma babu laifi babbane ta fannin boko gwamnati yake ma hidima" Dariya tayi ta shige makaranta da sauri wasu hawayen nadamar lalata tarihin mardiyyane ya zubo mishi dole ƙanwar naƙi ya share ya ƙarasa ƙofar gidansu. Malam yana kan kujera Dattijon ya rame sosai Babangida ya cire takalminshi a gefe ya durƙusa gaban Baba malam Kallonshi Baba Malam yayi yanata nazari Cikin ladabi da biyayya ya gaisheshi babu yabo babu fallasa ya amsa mishi sai sukai shiru zukata nata saƙe_ saƙe. "Dama akwai wani yarone da ya nuna yana son mardiyya yazo neman izinin soma zuwa zance a wajena shine nace dashi ya dakata har sai nazo wajenka" Kai Baba Malam ya girgiza yace. "Ai ƴarka ce mardiyya in kana ganin Sauban dana zaɓa mata bai dace ba sai ka bata wanda ya dace. Ni nama ɗauka Mustapha abokinka da bashi da tamka zaka baiwa aurenta, ko ka haɗata da Jamilun wajenshi ai" Da sauri Babangida yace. "Kaimun afuwa wallahi banƙi ba. Yaya Sa'a ce tayi rantsu.... " "Kai Babangida tashi kayi naka wajen kada in saka ƙafa in shureka nan ba gidan rawa bane bare kace zaka taka iyakar ganin masu kallo." Kuka ya fashe dashi mai tsuma zuchiyar duk mai saurare haƙiƙa Baba Malam ya iya gasa mutum da man jikinshi har sai ya ƙone ƙurmus. Baba Malam yayi shiru yana sauraren amon kukan Babangida wanda hakan ya tuno mishi kukan da yayi a lokacin yana da shekaru goma a duniya wawo ne ya dokeshi. A guje yazo ya faɗa jikin Malam a makaranta bai dena wannan kukan ba har saida Malam ya bashi alawa da nera biyar. " Natuba afuwarka nake nema nayi nadamar duk abinda na aikata ya Abati ka yafe mun ko rayuwata zata yi haske in fita daga cikin jalala" Yana gama faɗin haka ya miƙe ya tsallaka ya hau mashin ɗinshi a sanyaye ya tuƙa ya fice a layin ko gidan kawu Manga da Malama baije ba. Ajjiyar zuchiya Baba Malam ya sauke kawai. "Duniya makaranya" Iyakar abinda ya furta kenan. Kana ya watsa magungunanshi a baki ya bisu da ruwa.

Ta ɓangaren ƴar Shuwa kuwa takwas ma a tasha tayi mata. Ƙarfe tara da ɗoriya motarsu ta kama hanyar Bamaina babban birnin jihar jigawa kenan. A tasha ana saukesu ta hango Sameerah a wata iriyar jibgegiyar mota fara sol. A hankali ta ƙarasa ta buɗe murfin motar ta shiga. Kallon _kallo na ƴan sakannine ya wanzu tsakaninsu cikin shauƙin son kasancewa da juna. Murmushi Samira tayi. "Daga ƙarshe dai Baby kinzo hannuna. Yau zaki sha lele" Dariya suka yi samirah ta harba motarnan kan titi tana tafe sululululu har suka sulale suka nufi wani ƙaton gidan sama mai baƙin get maigadi dajin dirin motar ma ya wangale musu suka shiga. Danƙari sunan kare a lahira wannan gida da girma yake Ƴar Shuwa sai ƙarema gidan kallo take yi. Hannunta Samirah ta riƙe suka ratsa tsakar gidan har izuwa babban falon gidan ƙafar bene suka haye wadda take cikin falon har izuwa falon sama. A wata ƙofa suka tsaya ta saka key ta buɗe suka shiga. Sanyi da ƙamshin turaren wutan sandal ne ya doki hancin ƴar Shuwa ga wani sanyin ac daya mamaye ko ina. "Muje daga ƙurya Baby. ". Wata ƙofar ta sake turawa suka shiga ɗakin baccin Samira anan ashe duniyar take. Tabb akace wani kayan sai amale a wannan ɗakin gado na sameerah an haɗa duniya sosai kamar ba za'a mutu ba. Zama ƴar Shuwa tayi a kujera tana sauke ajjiyar zuchiya ƙamshi na tashi tako ta ina. "Ina zuwa bari in saka a hauro mana da karin kumallo. Amman kafinnan ga banɗaki na tara miki ruwan zafi ki shiga kiyo wanka ina zuwa" Idanu ta kashe ma Ƴar Shuwa. To a gurguje dai abinda zai faru ya riga daya faru tsakankanin Ƴar Shuwa da Samirah kuma dake harkace ta shaiɗan, da wani sirri da ita Yar Shuwa bata san dashi ba. Nan take taji duk duniya babu wanda zai iya cewa ta bar Samirah ta barta. Tana jin zata iya yin fito na fito da koma waye. Komai ya lafa ne a bisa sharaɗin babu rabuwa, kuma dole zata zama ɗaya daga cikin ƙungiyar wasu gaggan matane mazauna Abuja ƴan maɗigo, babu ita babu sake mu'amala da wata macce in ba na ƙawance ba, babu ita babu sakarma miji jiki ko da yaushe da sauransu da sauransu dai. Sannan za'ayi mata rijista shedar zama memba ta wannan ƙungiya ta matan Abuja. Tuni Ƴar Shuwa ta amince mata da ƙudurinta. Har bayan la'asar suna gado suna lelen juna Ƴar shuwa bata ankara lokaci ya ja ba saida taga biyar har ta gota, dake akwai komai naci a saman kuma akwai hasken lantarki sosai. Ko sallah a wannan ranar Ƴar Shuwa bata yi ba. A gaggauce ta saka kayanta ta zari jakarta. "Ya kamata in tafi lokaci ya ja sosai" "To shikenan Baby bari ina zuwa" Wadrob ta buɗe ta zaro ghana most go ta buɗeta ta shiga sakama Ƴar shuwa atampopi lasa lasai da mayafai sababbi kuma ɗinkakku. Maya mayai da turaruka da kayan kwalliya duk saida ta haɗa mata kana ta ɗakko kuɗi ta bata ta kira ƴar aiki ta saukar mata dashi. Mota ta buɗe suka shiga a tunaninta tasha zata kaita sai kawai taga sun ɗauki hanyar Dutse. "Kinga mijinnan naki zai kawo mana cikas gaskiya sabida wannan harkar tamu akwai buƙatan yawan haɗuwa sannan yanzu haka akwai taro da zamu yi a Abuja dole fa ki halarta sabida kin zama memba ya zame miki dole. Kinga akwai buƙatar kisan yadda zaki yi da mijinki. Sannan muna tafiye_tafiye ƙasashe_ƙasashe, ke tafiyar kwana ɗaya ma ba'a barki ba bare kuma barin ƙasar? " Sun daɗe suna tattaunawa cikin hukuncin Ubangiji suna tafe ruwa ya ɓalle tafiya kunsan dole ba zatai sauri ba dan ruwa ake zugawa mamako sai wajajen takwas na dare motar Samira ta ajjiye Ƴar Shuwa a bakin titin layinsu anata yayyafima har wannan lokacin. Sallama suka yi akan sai sunyi waya ƴar Shuwa na tafe anata kiraye _kirayen sallar Isha. Ajjiyar zuchiya ta sauke data saka ƙafarta a ɗakinta. Kayan data shigo dasu ta nemi waje ta adana kuɗaɗenma tai musu muguwar ajjiya. Sai lokacin ta yi sallar azahar, la'asar, magriba isha. Tana wanka ta jiyo muryar Babangida yana kiranta a zafafe. Ras gabanta ya yanke ya faɗi. Babu shiri ta warwatsa ruwa ta fito ɗaure da tawul a ƙugunta. Mrs Bukhari ce.

Son so masoyana💪🏼 [10/4, 10:29 PM] +234 810 593 2041: IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA HUƊU SHAFI NA HUƊU

😆😆😆

Sabuwa:.

Ƙirjina ta daka da ƙarfin gaske ta cukumeni. Wallahi tsabaragen tashin hankali narantse muku da Allah idanuna saida suka dena ganin hasken duniya na wucin gadi. Na shiga wani irin ruɗu sosai "Ke cikata dan abu ta kazan ubanki. Lolo wace ƴar akuyarce Eh zata zo har gida ta cukumeki ke kuma dan abu ta kazanki kina tsaye kamar gunki ba kya fyaɗa shegiya da ƙasa" Fisgeta Gaza yayi a jikina Rahine suka tayarma haushi suna neman kama siket ɗin matar Khalid. Da sauri Alhaji Zaidu ya ƙaraso ganin Gaza na neman zaro wuƙa. "A_a abokina a huce kada kayi haka a matsayinka na babba. Baiwar Allah baki kyauta ba ke kuma. Shalele koma jikin motata ki jirani" Babu laka guiwata kamar an daddatsa da jan ƙafa na ƙarasa jikin motar tashi na jinjina jikina na wani irin mazari. "Wallahi saita raina kanta ƴan sanda ne zasu yi mun iyaka da'ita in baki rabu da mijina ba wallahi saina yi ajalinki. Wallahi na fiki iskanci" Da ihu da tafi take wannan maganar abinda ya soma jawo hankalin su Rakiya kenan. Sai ga Maigogul da Rakiya sun fito. Dariya Gaza yayi tare jijjiga kai ya fisge hannunshi da Alhaji Zaidu ya riƙe ya zaro wuƙa yaima wuƙar tsirara. "Kutumar dumama yihuhu saini Gaza uban maza wuya a gida wuya a mararraba wuya a tafa wuya a dawo. Harmu za'a faɗama iskanci mu da gidan ɗan kande gidane a wajenmu. Kaga Malam kamar yadda ake yanka rago zan yanka matarnan. Ni da maza ma in suka ganni aron na kare suke yi bare mata. Ita kanta lolon zata iya farɗeta balle ni Gaza kaji fa cika bakin da take yi" Wannan ihu da kirarin da Gaza yake yi ya jawo hankalin munafukan unguwarmu har su Adama suma suka fiffito. Alhaji Zaidu ya riƙe hannu Gaza kam suka shiga kici_ kici. Maigogul kuwa hannu ya dunƙule ya zuba ma Matar Khalid dundu ba baya. Yana ta ɗuma zagi. Ban ankaraba naga Labbai a ruwan cikin Matar Khalid ta kaita har ƙasa, Adama mai fama da hannu ma harda ita. Gaza na tsaye Alhaji Zaidu na tausarshi bamu yi aune ba Magazin ya yanki matar Khalid a gefen kunne. Maigogul da Rakiya ne suka cabke mishi ƙugu. "Rahine ku ƙaddamar mata" Gaza ya ba karnukanshi umarni wallahi da ƙyar Labbai ta rabata dasu Rahine ta faɗa mota da mugun gudu ai da baya ta bar unguwar dan masifa har titi su Rahine suka rakata. Da gudu na gangara kamar mahaukaciya na shige gidanmu a tsakar ɗakinmu na faɗi na sake sakin rushin kuka mai ciwo take na soma ganin duhu duhu babu zato babu tsammani numfashi ya katse.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull