Kenza eBookz

Idan kaya ya gaji book book 4 - Chapter 4

Idan kaya ya gaji book book 4 - Chapter 4

Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 4: Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 4. "Ohh ni Maigogul Alhaji Zaidu kaine ashe kazo kazo ka tarar da rikici. Ke…

4,336 words

"Ohh ni Maigogul Alhaji Zaidu kaine ashe kazo kazo ka tarar da rikici. Ke Rakiya ku shige ciki maza. Gaza mayar mai da wuƙa gara da Allah yasa Alhaji Zaidu ya hanaka da yanzu wata maganar akeyi ba wannan ba. Kaida yaushe _yaushe ka fito daga yari kaima magazin ya kuma isa haka tunda dai ta tafi " Wuƙarshi ya mayar cikin gidanta ya dubi Maigogul yace. "Allah taci sa'a ba a cake nake ba kuma ai baka ga yau ƴan mutunci nake ji ba. Amman Allah eh da yanzu jini na kwarara anan mu za aima iskanci. Lolo fa tazo ta shaƙe tana eh magana akan ƙazamin mijinta wallahi taci sa'a macece da ace mijin nata ne da yanzu yana mace anan wajen." Alhaji Zaidu wani jiri ne yaji yana ɗibarshi tsabar kiɗima da mamaki. Rakiya tace. "Aikin banza ƙila matar Khalid ɗin lolo ce tazo za tai mana rashin hankali bata san gidan... " Adama ta janye Rakiya suka shige ciki. Layuza ta taɓe bakinta tace. "Su lolo anji kunya matar farka har gida" Da sauri Alhaji Zaidu ya dubeta cikin razana. Maigogul ne yayi mata daƙuwa ya cire takalmin ƙafarshi zai jefeta dashi tayi ciki a guje. "Labbai shige maza ki kirawo Lolo tazo" A sanyaye labbai ta amsa ta gangara. Maigogul yace. "Alhaji ina zuwa bara in shiga ciki in saka a shinfiɗa tabarma" Yayi yinƙurin zai haneshi Maigogul ya shige a guje yana saɓa malum_malum. Da idanu cike da maɗaukakin mamakin daya gigita tunaninshi ya buka kanshi yabi maigogul da idanu. Maigogul kafin ya ƙarasa shiga ya hau kwaɗama Rakiya kira a gigice ya shiga gidan. "Rakiya shinfiɗa mana tabarma a ƙofar ɗaki Alhaji Zaidu zai shigo saurayin Lolo" Baki Rakiya ta washe "Au yanzu dama wannan mutumin mai haiba wajen lolo yazo? Uhm hiye babu shakka kaga yarinyar da aka haifa tsiya na bacci. Ai sai dai a shimfiɗa mishi a ciki. Akwai ƴan hana ruwa gudu duk gasu suje ma su soma farautarshi" Hauwa tayi shewa tace.. "Rakiya kenan ke dai baki da aiki sai takale_ takale magana na zame miki ƙarfen ƙafa wallahi a gidannan kina da aure har kina kallon wani namijin kina ganin haibarshi" "La'ilahaillahhau yanzu Rakiya biye mata zaki yi baƙo na waje? To shikenan kuci gaba" Rakiya tayi dariya tace. "Kaina bisa wuya Darling maigogul" Dariya dukka suka kwashe dashi Maigogul yana dariya ya nunata da manuniya yace. "Makirar mace kai Rakiya sai dai a barki" Da sauri ya fice Adama ta shiga suka kakkawar da kaya aka shinfiɗa tabarma harda feffesa turaren Maigogul a ɗakin. Maigogul ya fita ya tadda Alhaji Zaidu ƙiƙam a wajen daya barshi ya shiga dogon tunani da nazari mai zurfin daya wuce gaban misalin da alƙalami zai iya rubutawa" "Mu shiga daga ciki. Unguwar cike take tab da munafukai kaga ai sai zuruftu suke yi" Ajjiyar zuchiya yayi kawai yayi ƙundunbala yabi Maigogul izuwa ciki. Yayi mamakin ganin gidan da irin kwaraɓewarshi yanzu dama su Sabuwa da Uzairu zuchiyata duk wannan gayun nasu gidansu kenan. Bai gama rabe ɗayan biyu ba suka ƙarasa ƙofar ɗakin Rakiya yana saka ƙafarshi ɗaya Labbai ta shigo a guje tana faɗin "Shikenan Lolo ta mutu shikenan Adama kuzo ku taimaka mun" A guje Maigogul ya nufi hanyar fita yama mance Alhaji Zaidu na bakin ƙofar sai ji yayi ya rungumeshi. Da sauri suka fito a gidan dukka gidan harda su Hauwa da Layuza. Alhaji Zaidu shine har tsakar ɗakin su Lolo tana kwance shame_ shame bata san wainar da ake toyawa ba. "Alhaji Baba a ɗakkota mu kaita asibiti" Maigogul da Labbai ne suka sureta aka fito da'ita. Shi Alhaji ya rigasu fita ya je ya ɗakko mota aka shinfiɗata a bayan mota. Maigogul yayi carab ya shige gaban mota. "Labbai shiga muje maza ku Rakiya ku tafi gida babu komai Uzairu zuchiyata ma ya shige muje" Labbai da Uzairu zuchiyata suka shige baya fuuu suka fice a layin a guje. Gaza na ƙarasowa inda su Rakiya suke Rakiya na kuka tace. "Gaza Lolo dai ta bar duniyar shikenan hankalin kowa ya kwanta" "Ahh ban gane ba wani abunne ya eh faru bayan na tafi ne. Ke madamcy shafa mun mana" Madamcy ta faɗa mishi yadda duk akayi. "Rakiya Hauwa muje gida kunga eh jama'a sun soma taruwa zo muje" Hannun Rakiya ya riƙe suka shiga gida. "Bari a kira Labbai duk ma inda aka kaisu saita faɗa mana Rakiya sai in kai ki. Shi Uzairu zuchiyata dan abu ta kazanshi ai da shi ya zauna ke kika je. Rakiya Uzairu zuchiyata anya ba mata maza bane kuwa? Naga abun nashi yayi yawa" Rakiya ta sake fashewa da kuka. Dariya Gaza yayi. "Tabbb Rakiya eh ashe wai kina sonmu? Ni wallahi na ɗauka ke da tsoho bakwa ko son ganinmu maganar fa gaskiya ku kuka lalata komai. Ni wallahi eh har cewa nayi zan tambayeki anya kuma kinji zafin naƙuda da zaki haifemu kuwa? " Adama tace. "Gaza gidanku meye haka? " Dariya ya tuntsire dashi yayi ihu. "Adama Adama matar dakacin ƙauye ƙonanniyar amarya. Ke wai kinga idon kishiyarki lokacin da nake kuikuya mata kuwa" Hauwa tace. "Ohh ni Hauwa Allah wadaran naka ya lalace gida sai kace gidan magajiyar karuwai" Gaza ya harareta ya doka tsaki. Wayarshi ya ciro ya kira Labbai akan in suka isa asibitin ta sanar mishi sunan asibitin. Zama yayi a turmi yana shafa Rahine ga ƙaton cikinta haihuwa ko yau ko gobe. Rakiya kuma tayi shiru tana ta tunani. Adama ma a zaune take ga ƙuna a hannu. Suna isa asibitin Labbai ta labarta musu asibitin. "Rakiya shirya ki ɗan canja kaya muje. Adama ara mata takalmin ƙafarki muje" Adama ta cire takalminta tasa silifas ɗin fata na Uzairu zuchiyata. "Amman Gaza wannan rigar farautan ni kam daka cireta dan Allah kasa wasu kayan. " "Tabb wallahi bazan cire ba ina laifin kice in ajjiye makaman jikina dai tunda asibiti zanje" Yana muzurai ya ciccire komai madamcy ta karɓa. Rakiya na fitowa Sama ya shigo gidan babu ko sallama duƙun duƙun dashi. "Gaza muje maza kaji" Cewar Rakiya kenan. "Rakiya sai kun dawo to. Amman zuwa anjima in gado aka bata zan daure in yo girki in kawo, in kuma su Aisha sun dawo sai su kawo" "A_a ke da eh kike fama da ƙuna tunda dai lolo ce eh ki ba Madamcy kayan girkin tayi. Inma gadonne ni zanzo in karɓa musu abincin. Rakiya mu sakata" Ficewarsu suka yi Adama da Sama suka bi bayansu da kallo.

Asibiti:. Asibitin kuɗi mai tsada Alhaji Zaidu ya tambayi Maigogul sabida so yake a ba Sabuwa kulawa ta musamman. Suna shiga aka amsheta cikin gaggawa Alhaji Zaidu da Uzairu zuchiyata suka nufi bakin taga inda za'a yanka muku kati. Maigogul da Labbai kuma suna ƙofar ɗakin da aka shiga da lolo Labbai tayi tagumi kawai Maigogul kuma ƙoƙarin kiran Cicib yake yi a waya ya sanar mishi halin da Lolo take ciki. "Helo Cicib ka gammu a asibitin kuɗinnan da Alhaji Baraya ya taɓa kwanciya ɗiyarka lolo babu lafiya" Cicib daga cikin wayar yace. "Ma'aikin Allah na madina ni Cicib to banci ta zama ba kaga yanzu na ajjiye haƙarƙarina a gado zan kwanta kenan. Ɗiyarka Shafa auren nata ya mutu tana tsakar gida da uwar tata suna mayar da zance kasansu da rakin tsiya ganinan kaji" Da haka sukai sallama Maigogul ya ajjiye wayar. Uzairu zuchiyata da Alhaji Zaidu tare sukaita kai kawo har ɗaki yasa aka sake ma lolo aka maidata nata ita kaɗai. Dr ne ya nemi ganinsu tare suka shiga da Maigogul suka zauna. "Jininta ne ya hau sosai gaskiya nayi mamaki da ɓarin jikinta bai shanye ba tunda kunce kamar faɗuwa tayi. Tana cikin damuwa mai tsananin gaske. Baba dama kunsan tana ɗauke da waɗannan manyan cutukan masu ruguza mutum hawan jini da cutar damuwa?" Alhaji Zaidu ya ja numfashi yana jin tausayin rayuwar Sabuwa na tsirga mishi tako ta ina. "Dafta mun dai san tana fama da hawan jinin tun tana gidan uban ƴaƴanta dan ta taɓa yin wani ciwo da har saida muka zaci duniyar zata bari. To shi cutar damuwanne da kace ni wallahi bansan damuwa cuta bace wallahi ssbida ka ganni bana shiga damuwa kwata_kwata haka Allah ya yoni. Dr yayi rubuce_rubuce kafin yace. "Bata da aure kenan yanzu Baba? " Maigogul harda share ƙwallar makirci. "Bata da aure yanzu. Burinta bai wuce ta samu miji nagari ta aura ko Allah zaisa ta samu nutsuwa ba. Dafta rayuwarce sai adda'a yayyenta duk zawarawane haka ƙannenta ma. To ita mai saka damuwowin kowa a ranta ne, ga rashin miji na damunta sosai" Da rishin kuka Maigogul ya gama maganar. Alhaji Zaidu yace. "Alhaji Baba ka dena kukan in dai miji Sabuwa take nema tasamu a shirye nake da in aureta" Ai sai sabon kuka Dafta da Alhaji Zaidu suka taru sukaita rarrashin Maigogul. Shi kuma sai godiya yake yi ma Alhaji Zaidu. "Babu ai komai Alhaji Baba. Dr yanzu amman ya yanayin jikin nata yake? " "To jikinta yayi tsanani akwai buƙatar a kula da'ita sosai. Sannan tana buƙatar terafis gaskiya a cikin depretion take sosai. In sha Allah zamu kula da'ita yadda ya dace sannan dan Allah banda zuruftun mutane, ko kuma mata su taru aita magana a kanta hutu take buƙata in sha Allah jinin zai sauka. " Dr ya jima sosai yana musu bayani daga ƙarshe sukai mishi godiya Maigogul ya riƙo hannun Alhaji Zaidu suka fito. Suna shawo kwana Cicib na shawowa shima yana tafe salab_salab kamar ƙwai ya fashe mishi a ciki yau dai jallabiyar ce kaɗai a jikinshi babu ɗankwali a kanshi. "Yauwa Alhaji kaga wannan shine Cicib aminina kenan bashi da tamka. Cicib wannan sirikinka ne wanda zai auri Lolo" Gaisuwa ce ta wanzu a tsakaninsu na minti biyu. Kafin Alhaji Zaidu yace yana zuwa zaiyi waya da ƙanin mahaifinshi. Gefe ya matsa can da nisa. Maigogul ma ya ja cicib suna tafe yana labarta mishi abinda duk ya faru. "Na taɓaka da Alheri kishiya ta taɓa kishiya da bakin wuta. Wallahi kada muyi sake wannan babban tajirin ya kuɓuce mana. Wannan yarinyar in ka shiga ka fita ta shiga wannan haula sai fa munfi uban kowa morewa. Maigogul kayan tsubbunka suna adane ko? To ga a inda zaiyi aiki nan. Kawai kaje ka soma aiki." "Kai dai bari Lolo ta shiga gidan Alhaji Zaidu ƙila harkar kawalcimma dainata zamu yi ya sama mana abun yi mai kyau" Dariya suka saka Cicib ya ja shi suka koma ƙofar ɗakin da su Labbai suke. Gaza da Labbai da Uzairu zuchiyata suna zaune suna tattaunawa Rakiya na ciki su Cicib suka ƙaraso. Yana hango Labbai ya soma washe bakinshi. "Maigogul anya ba Labbai zaka bani ba kuwa in aura? " A kunne yayi ma aminin nashi raɗa. Shima maigogul raɗar yayi mishi. "Gaka gata in kun daidaita ni menene nawa cicib. Kai da kasan kana sonta shine kayi ƙumun baki? " Leƙowar Rakiya yasa suka juyo. "Maigogul a kira likita sai sambatu lolo take ta faman yi fa" Uzairu zuchiyata ne yaje ya kirawo ma'aikatan jinya suka shiga ɗakin Rakiya kuma suka ce ta jira a waje. Duk suna zazzaune anyi cirko cirko. Alhaji Zaidu ne ya ƙaraso bai zauna ba yace. "Alhaji Baba inaso mu gana dan Allah" Da sauri Maigogul ya jawo hannun Cicib suka nemi keɓaɓɓen waje suka keɓe. "Alhaji Baba muddin babu damuwa ni kuma zan auri Sabuwa a yau ba ma sai gobe ba. Zanso ta buɗe idanunta ta ganni a matsayin mijinta wala Allah hakan ya rage mata nauyin raɗaɗin da zuchiyarta take ɗamfare da'ita. Sai dai yana da kyau ayi bincike a kaina tukunna. Ni ba sai nayi binciken komai ba. Akwai Aminin ƙanin mahaifina a cikik jigawa in kun bada damar a ɗaura auren yau sai yanzu inyi waya su tawo ayi komai. A hankali lokacin data shirya saita tare" Tabb faɗin farin jiki da irin murnar da Maigogul da amininshi suka yi wallahi yafi ƙarfin gaban a kwatanta ma mai karatu. Take suka amince da ɗaurin auren ayau ɗinnan. "To shikenan zan kira yanzu in sanar musu su kamo hanya kawai" Hannu yasa a ajjihu ya ciro kuɗi mai kauri ya ba Maigogul yace ko zasu yi wani abun dashi. Ya matsa gefe yaita waye_ waye. Maigogul ya kirayi ƙaninshi Isuhu ya shaida mishi halin da ake ciki. Sai dai anyi rashin sa'a baya gari ya dai ce daga baya iyali sa zo gida. "Cicib to kaifa zaka karɓi auren lolo a ƙofar gidanka ma za'a ɗaura auren munafukan layinmu babu abinda zssu sani sai in zata tare ananne zasu ga biki" Cicib ya kwashe da dariya yace. "Ai babu damuwa dama Sabuwa ai tamu ce. Kai yau muna cikin alkhairi dumu _dumu Maigogul komarmu ta kama babban kifi. Mu tafi a sanar dasu Rakiya halin da ake ciki sabida ai ya kamata ace anyi girki sabida baƙi shi tuwon girma miyarshi nama" Rankayawa suka yi ƙofar ɗakin da lolo take su Rakiya duk suna zaune Maigogul ya labarta musu abun alkhairin da suke ciki. Murna a wajen waɗannan mutane bata faɗuwa. Nan da nan aka tashi Labbai da Uzairu zuchiyata zuwa kasuwa domin siyo abinda ya dace. Nan da nan su labbai suka shiga waya dasu Adama da Rahama kafin kace me sai suka haɗu a gidan Cicib suka haɗu da iyalanshi suka shiga girkin abincin baƙi anayi ana shewa da farin ciki. Baƙin dai sai daf magriba suka samu isowa, A masallacin unguwarsu Cicib sukai sallah bayan an idar da sallah liman ya sanar da batun ɗaurin auren. Cikin ƙanƙanin lokaci aka ɗaura auren Lolo da Alhaji Zaidu bisa sadaki ɗari biyu da hamsin Tarewa ba yanzu ba sai an shirya. Baƙi dai anyi juyin duniya akan su shiga cikin gida su ci abinci sunƙi fur dole sai Rahama da Uzairu zuchiyata ne suka saka musu abincin a mota suka tafi dashi. Alhaji Zaidu kuma ya ja su Maigogul ya mayar dasu asibiti, kafin su ƙarasa asibitin saida ya biya ta shagon siyayya aka siya musu kayan tea manyan gwangwanaye. Ya ajjiyesu a asibiti har ɗakin da Lolo take kwance ya shiga. Rakiya na zaune tana cin abinci suka shigo. "Sannunku da shigowa kaddai an ɗaura Maigogul? " "Wallahi an ɗaura bamu da ranar da tafi wannan a wajenmu. Tashi maza ya zauna" Rakiya ta yunƙura zata tashi yace. "A_a Mama ki zauna ni yanzu zan tafi masaukina dama dai su Alhaji Baba na kawo. Allah ya bata lafiya" Yana faɗin haka ya saka kai ya fita. Su Rakiya dai zukatansu shaƙe da farin ciki da annashuwa. Sabida ma fitina maigogul cewa yayi a asibitin zai kwana hakan kuwa akayi. Yana kan kujera yana shan tea mai kauri bayan ya raka abokinshi ya tafi yace da Rakiya. "Cicib ma ya nuna mun yana sha'awar auren Labbai ni dai nace suje su sasanta" Dariya Rakiya tasa harda hawaye tace. "Ya ko ji kunya wallahi. Amman in taga ta karɓeshi mu bamu da matsala sai duk a haɗa da bikin Uzairu zuchiyata a game kawai. Haka suka ci gaba da tattaunawa. Cike da farin ciki lolo bata san wacce wainar ake toyawa ba. Kunji wata ƙudurar Allah ko? Allah shi ke yin komai a sanda yaso

(Aimun afuwa daya yanzu posting ya dawo 8 na dare in sha Allah nadena na safe) Mrs BUKHARI

Masoyiya maidoki Allah ya baki lafiya yasa kaffarane. Dan Allah ku taya ta adda'a Allah ya bata lafiya mai ɗorewa. Aminiyatace masoyiyata ta haƙiƙa wacce bata da tamka kamar cicib da Maigogul. Kamar iyabo da Tabalbalin😆 [10/4, 10:29 PM] +234 810 593 2041: IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA HUƊU SHAFI NA BIYAR

GIDAN BABANGIDA:.

A hanzarce ta ƙaraso gabanta na wani irin bugawa. "Gani ashe kadawo? " "Na dawo ai tun yamma. Amman meye ya tsayar dake a waje har kika kai dare alhalin dokar gidannam kinsan magriba Ba zata ma ko wacce mace a waje ba. Meye ya tsayar dake sannan me ya samu wayarki da bakya ɗagamun? " Kanta ta sosa. "Rashin abun hawane yasa ban dawo da wuri ba, ruwa kuma kaga yazo ya kece" Murmushin takaici yayi kawai ya fice. Ajjiyar zuchiya ta sauke mai nauyi. Haƙiƙa ba da ban ta jarabtu da son Babangida ba da a daidai wannan gaɓar zata ajjiye auren. Amman ina tana fatan har a gidan aljanna ta tashi a ƙarƙashinshi balle tana jin yanzu itace uwargida a gidan na Babangida, kawai dai saita tashi tsaye ne sosai a kanshi wannan kullen ne kaɗai ba zata iya lamunta ba sam. Tana zaune a bakin gado tana shafa mai suna waya da Samira har ta gama shafa man taje Kitchen ta kunna gas suna wayar, har ruwan shayin data ɗaura ya tafasa wayar suke yi da ƙyar sukai sallama ta ajjiye wayar ta zaro kayan ciye_ciyenta taci ta sha shayi tabi lafiyar gado. Washegari da misalin goman Safe ƙannenta suka kawo mata su Faty a lokacin tana kan haɗama Ramatu kayan wanke wanke. "Ga kwanukannan in kin gama ki ɗan kife mun a kwando, wannan wajen ki ɗan share mun shima, da dai abinda kika ga ya dace. Ku kuma mujenku" Tsaki tayi ta shige ciki, Ramatu ta ɗauki bawon wanke_wanken tana mamakin dalilin da yasa bata iya musu da Ƴar Shuwa duk da tana jin zafin abinda take yi mata a ƙasan zuchiyarta amman bata iya faɗa mata. "Anty Mama ce dama tace in akwai kuɗi a hannunki ki bata ko dubu biyar ce bata jin daɗine take son zuwa asibiti" Ƴar Shuwa ta taɓe baki tace. "Ku kenan tambayar kuɗi dai. Ita Mama madadin ta jiƙa ararraɓi tasha. To na dai ji in zaku tafi zan baku. Yauwa Binta cefanen miya zaku yi mun tunda gaku kunzo saima ku taya ni muyi miyar tare." Kuɗi ta zaro ta basu suka nufi cefane ita kuma ta nufi tsakar gida tana son shiga ɗakin Jami ƙawarta ta ƙut da ƙut. Fitowa tayi tana tafe ɗaiɗaya ji take yi tafi uban kowa. Ashe tsautsayin za'ayine ya fitar da'ita tana fitowa ta tarar a tsakar gidan anata caccakarta akan aikinta da Ramatu take yi mata a ko da yaushe ga ƙaramin ciki du su biyun suke laulayin a tare. Sumy da bata san Ƴar shuwa ta fito ba tace "Uhm asiri tayi mata fa. Wallahi ina ganinta har a ƙofar ɗakina ta barbaɗamun. Yarinya bata sanni bane wallahi shi yasa take wasa da wuta. " "Ai dole kice asiri nayi mata sabida yarenku basu yadda da Allah ɗaya ba. Munafuka nan kin fito ne kuka dasa gulmata ko? " Sumy ta dubeta tana wanke tukunya ta miƙe da tukunyarta a hannu Ƴar shuwa batai aune ba Sumy ta gabɗa mata tukunyarnan take goshin ya fashe. Dambe ne na Allah tsine uwar mai ƙarya ya kaure tsakankaninsu Sumy ta fita ƙarfi da girma da ƙyar aka raba wannan faɗan Jami ta tura Ƴar shuwa ɗakinta dake sun fi kusa. Babangida da yayi mantuwar fefofin gwaji ( test) na ɗalibai ya dawo ɗauka ya tarar gidan a cike ana dambarwar tsiya ga Ƴar shuwa jini ya wanke mata fuska amman dan masifa a guje ta fito ta sake dirarma Sumy. Sum_ sum_ sum ya wuce ciki yana jin tamkar ya haɗiye zuchiyarshi ya mutu duk a huta. Ihu ne yaji ya kaure a tsakar gidan ana ambaton. "Jini ya ɗebeta ta suma" Ledar naman daya ɗauka yana kallo ya saki ya fita. Ranga_ ranga Babangida ya ɗauki Ƴar shuwa zuwa asibiti yana jin kamar zai yi hauka. Kiran makaranta yayi yake sanar musu halin da yake ciki ba lallai ya dawo makaranta ba ƙila sai zuwa gobe dai. Dan hatta shima da za'a aunashi gado tsab za'a bashi ƙila harda ƙarin ruwa koma jini gabaki ɗaya baya jin daɗin duniyar baki ɗaya. Dr daya fito daga ɗakin da Ƴar shuwa take ne ya katse mishi zaren tunanin shi ta hanyar cewa. "Ka Sameni a office ya Sheik. " A baya ya bishi tin_ tin_ tin har zuwa office ya nemi waje ya zauna. "Babu wata matsala mai girma gaskiya zama ku iya tafiya gida yau da zaran ta tashi a baccin da take yi. Abinda ke cikinta kuma yana lafiya babu wata matsala. Godiya kawai yaima Dr Ya je ya biya kuɗin magunguna da komai da komai ya tusata gaba kawai yana kallonta da goshi kumbure yana ta ƙissima abubuwa da dama a ranshi. Daya tuno da chus sai yayi murmushi ya zaro wayarshi ya shiga ma'ajiyar hotunanta dan ya kalla yaji sanyi hotunan Sabuwa sune abincin zuchiyarshi dama idanunshi.

ALHAJI ZAIDU:. Yana kwance a ɗakin hotel fitowarshi wanka kenan shine ya samu ya kwanta dan bala'in zazzaɓi yake ji tun lokacin da matar Khalid ta cakumi Sabuwa ta soma feso maganganu marasa daraja da duk ma dai abinda ya faffaru masu tarin muni a gabanshi. Idanunshi ya lumshe yana hango fuskar Sabuwa da kuma irin sanyin halinta da irin muguwar kunyar da aka sakata a ciki, da irin yadda yaga ta muzanta. Amman babban abinda shine yafi komai jan hankalinshi cutar damuwar dake damunta Matarshi tayi cutar damuwa wanda sun sha wahala bata wasa ba. Da farko ma an ɗauka jinnu ne la'akari da irin abubbuwan da take yi. Irin su ihu, fisgewa a guje, keɓewa a ɗaki, rashin son ganin haske, da kuka, da rashin bacci. (To a daidai wannan gaɓar ga tsokacina ƴan uwa. Akwai mata da yawa da suke fama da cutar damuwa ake ta ɗirka musu magungunan hausa, wata ma aita mata ruƙiya ana labtarta a tunanin makusantanta cutar jinnu ke damunta. An ɗauketa an aita wajen masu bada magani na bogi daya kalleta sai yace aljanu sunfi ɗari bisanta alhalin ƙaryane cutar damuwa ke damunta. Shawarata anan dan Allah duk macen data shiga ɗaya daga cikin waɗannan halamomin dana lissafo asibiti shine inda ya dace a soma kaita aba masana dama su gabatar da aikinsu. Ubangiji Allah kasa mu dace ameen? ) Sai daga baya da cutar tayi tsananin da ta soma raunata kanta ne aka kwasheta zuwa Asibiti. Da farko Alhaji Zaidu asibiti yaso a kaita danginta da danginshi suka haɗu suka danneshi cewar cutar bata asibiti bace saida ruwa ya ƙarema ɗan kada kana aka dangana wajen likitoci suka tabbatar musu cutar damuwace. Ta ɗauki damuwar duniya akan rashin haihuwa ta ɗaurama kanta, duk inda taji mai magani saita je ta karɓo musu sunzo sunyi ta ɗibga da dai taga abun yaci turane girma nata tunkarota har ta kusa isa ƙadamin mainofos aimun afuwa ban iya turanci ba ( khadija maidoki😆 zo ki gyara musu) shine wannan cutar ta damuwa taci gabala a kanta. Amman yanzu ta warke sai dai fa abun yana zuwa mata tamkar zuwan iska Ajjiyar zuchiya ya sauke yana tunanin irin gidan da ƙaddara ta zana mishi ya auri ƴar gidan. A zahiri tausayinsu shine abu na biyu daya jashi wajen auren Sabuwa. Na farkon shine ya jarabtu da matsananciyar ƙaunarta wanda abun har mamaki yake bashi irin yadda lokaci guda zuchiyarshi ta jarabtu. Fatanshi Allah yasa ya zamema wannan zuriyar wani matattakalar da zasu gyara ɗabi'unsu yayi imani a ɗan zamanshi da Sabuwa da Uzairu zuchiyata yasan sun bambamta da ragowar ƴan gidansu ƙaddararsuce a haka basu da tsimi bare dabarar sauya ma kansu ƙaddara. Kuma ya lura harda laifi al'ummar da suke rayuwa a cikinta. Ajjiyar zuchuya ya kuma saukewa tare da fesar da iska.. Tunaninshi ya sauka izuwa kan uwargidanshi kuma baisan yadda zata ɗauki lamarin ba, da sauƙi ko akasinshi oho. A baya dai bata fiye ɗaga hankalinta ba, amman a yanzu da yake ganin kamar ƙara ninka mata sonshi akeyi sai yake ganin kamar ba zata ji daɗi ba. Kiran wayarta ce ta katse wannan tarawa da ɗebewar. Yana kara wayar a kunne sai yaji ta sauke ajjiyar zuchiya. Tausayinta ya tsirga mishi sosai. "Alhaji dare yana ta yi, ni banji kace mun ka taso ba bare kace mun ko gaka a kano da dai makamancin hakan? " Ajjiyar zuchiya ya sauke kana ya saki murya ya ware.. "Ai dawowar dai bari muga mai gobe zata haifar. Ni kin ganni a ɗakin hotel ina kwance. Kiyi haƙuri ban kiraki ba har kece kika rigani kira. Kainane ya ɗauki zafi sosai abubbuwane sukaimun yawa man kaina duk ya kwaranye" Dariya tayi tace.. "To ko dai zance kaje ne Alhaji kafa faɗamun gaskiya Alhaji. Naji kace dubiya zaka je ta wuni guda sai kuma ka ɓige da bari aga abinda gobe zata haifar bafa tabbas a goben kenan? " Dariya yayi sosai. "Hajiya kenan ke baki da dama. Zanyi ƙoƙarin ganin ko jibi ne na dawo, inma na gama abinda nake yi gobe zaki ganni kwatsam" "A_a banda kwatsam ka mance gobe Amaryar Yaya isiyaku zata tare zamu je ma Hajiya Baturiya dannar ƙirji? " Murmushi yayi yace. "Zaku je dai gutsiri tsoma irin naku na mata da in bakui ba bakwa jin daɗi. Dan Amaryar Isiyaku zata tare har sai kunje ma Baturiya dannan ƙirji Baturiyan da yara biyu ta kai gidan miji." Dariya suka yi yana dafe da kanshi da yake mishi ciwo. "To ni kam Hajiya saina dawo asha dannar ƙirji lafiya. Ko akwai wani abun da kike da buƙatane? " "Eh to babu zance akwai kuɗi a hannuna, masu hayar shaguna ma sun soma biyan kuɗaɗensu" Murmushi yayi yace. "Kice a Hajiyarki kike, to a siya mun wani abun a cikin kuɗin. " Dariya tayi tace. "Da dai zaka ƙaro aurene da akwati zan haɗa ma amarya in fansheka." Dariya yayi kawai sukai sallama ya kashe wayarshi ya fahimci zarginshi take yi da zuwa zance, shi yasa take ta soko zancan cikin raha. Dole sai da dabara zai sanar mata batun auren ta sigar da hankalinta bazai tashi ba. Tunane_tunanene cikin kanshi wanda da ƙyar suka barshi ya runtsa. Mamaki yake yi wai daga ziyara sai ɗaurin aure matar ma na cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai. "Allah ya baki lafiya Shalelena Allah shine shaida wallahi ina sonki. Tarihinki bazai hana in soki ba" Tuno fuskar maigogul da Cicib yasa saida ya saki murmushi ba tare da ya shiryama hakan ba. "

ASIBITI:.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull