Idan kaya ya gaji book book 4 - Chapter 5
Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 5: Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 5. Washegari bayan maigogul ya dawo daga masallaci yana zaune a kan kujera…
4,237 words
Washegari bayan maigogul ya dawo daga masallaci yana zaune a kan kujera yana haɗama Rakiya shayi nashi yana gefe ya gama haɗawa. "Wai ni maigogul kace wai Cicib Labbai yake so matarshi ta rage wannan kishin nata ne? Afa duba jibi Adama a gida a ƙone kada fa a kuma matar da ta rabkama kishiya muciya. Yanzu da ba dan kun shiga kun fita ba Allah kaɗai yasan shekaru nawa zata yi a gidan yari" Shayi mai kauri ya miƙa mata ya yaga mata biredi mai kwakwa mai musulmin daɗi. Saida ya ci biredi ya kurɓi shayi kafin yace. "Rakiya hoo to ita labbai kanwar lasace, ko kuwa tayar baya ce irin wacce aka rabka mata muciyar? In sun daidaita da Labbai ba shikenan ba dafa su zamu yi mu sha romon? In ta yi mata itama ta yi mata, su kashe junansu ba shikenan bane? Ai gara taje ta zauna koma yayane. Ke dai ki godema Allah yara uku a tsukuku guda ace suyi aure ai ba'a taɓa haka a wannan gidan ba. Kina ganin yaran Hauwa babu ma mai shinshinarsu. Layuza ce ma naga yaron wajen malam Habu tsohon mijin Labbai yana ɗan leƙowa wajenta. To malam Habu in sama da ƙasa zata haɗe kinsan bazai yadda ba. Gaba yake yi mun tunda dai abinda Gaza yayi ya yanke mai tumakai. Ni ina mamakin inga ana riƙo, ko fishi sai inta mamaki. Rakiya ashe wai damuwa ciwo ce? Allah sarkin girma inji kishiyar mai mazaunai. Harararshi Rakiya tayi tace. "Haka fa" Dariya yayi yace. "Kada ki kawo rikici cikin hirarmu wannan Alhaji da Allah ya kashe ya mallakama lolo Rakiya ai damu da talauci kakarmu ta yanke saƙa. Yana daga cikin sanannun mutane a Kano, gaskiya yana da kuɗi mazajen kuɗi fa ba irin na wancan mitsiyacin Babangida ba mai gorin tsiya akan abinci. Familinsu sanannune kuma ƙosassu da ilimin addini." Rakiya ta washe bakinta tace. "Wa ka gane mun gidan da lolo zata tare. Kai nayi farin ciki maƙiyanta sun faɗi tim ƙasa babu nauyi. Wannan abu yayi mun. " Hauwa ce ta shigo ita da Layuza da Aliya Sai ƙarema ɗakin da ledojin gaban maigogul kallo suke yi. Rakiya kuwa kanta ta juya ko kallo basu isheta ba. Hauwa tace. "Naji wani yashasshen labari a bakin su Labbai wai an ɗaura auren Lolo a gidan cicib dama Lolon tana da wanda suka daidaitane mu bamu da labari? " Rakiya tayi dariya tace. "Yafi ƙarfin yashasshen zance. Kin ganta nan matar hamshaƙin mai kuɗi ce. Ƙarewarta ma a jirgi suka haɗu" Dariya da Rakiya da Maigogul suka fashe dashi wallahi harda tafawa Wanda yayi daidai da buɗe idon lolo"
SABUWA:. A hankali na buɗe idanuna ina ta jiyo maganganu a kaina da irin muryoyin dana kasa tantancewa. Dishi _dishi na soma ganinsu. Idanuna suka washe tanwar a kan fuskar maigogul sai murmushi yake yi mun. Idanuna na runtse maganganun da matar Khalid ta yaɓa mun suka shiga dawo mun Da sauri na sake buɗe idanuna domin in tantance a inda nake, ga kaina sai sarawa yake yi. "Sannu Lolo maigogul kaje ka kirawo ma'aikatan jinya. Sannu lolo" Cewar Rakiya kenan. Kai kawai na ɗaga yanzune na gane akan gadon asibiti nake Rakiya na riƙe da hannayena har maigogul ya shigo shi da ma'aikacin jinya. Ya fi minti uku yana mun tambayoyin yadda nake ji a jikina kafin ya dubi Maigogul yace. "Tana buƙatar hutu sosai. Sannan mutane sunyi yawa a ɗakin ku bata sarari dan Allah kada a cika yawan magana a kanta kuma. Yanzu abinda ya dace ta samu taci abinci zuwa anjima za'ayi mata allura Allah ya ƙara afuwa" Ya saka kanshi ya fice. " Matar manya sannu. Rakiya tasheta a hankali kinji? " Maigogul yayi sauri ya tsugunna ya haɗo mun shayi mai kauri ya saka mun cokali. "Lolo zaki iya riƙe kofin ko in baki a baki dan Allah? ". Hauwa da suka tashi zasu fita ta rabka salati maigogul ya juya a fusace. " Wallahi kaji kunya kai kam maigogul tur da wannan mummunan ta'adar taka. Kuzo muje kada baƙin ciki ya kashe mu" Fuu Hauwa ta fita su Layuza suka mara mata baya. Kofin na karɓa a hannunshi. Ina ta kallonsu Rakiya yadda suke ta tarairayata. A hankali na soma shan shayin ina lumshe idanuna, bayan Maigogul ya tagazamun na tashi zaune na jingina da ƙarfen gadon. A zuchiyata nace. Bariki ba riba jibi abinda matar Khalid tayi mun a gaban Alhaji Zaidu. Hmm nasan har gaba da abada bazai sake waiwaye na ba. Yo ni ko ya waiwayeni bani da idanun kallonshi. Ina cikin zancan zuchi naji Maigogul ya saka mun biredi a baki. Kafin in tauna sai ga Gaza da Madamcy da kayan abinci. "Ah lolo eh ashe kin farka? A lafiya dai Sabuwa mai sabon aiki. Eh ya jikin naki to? Su labbai duk tare muka tawo dasu eh suna waje wajensu eh Hauwa" Jikin da sauƙi Gaza nagode. Madamcy nagode" Na faɗa a sanyaye dan kaina mugun sarawa yake yi Ina ƙarashe shan shayin na kwanta dan kaina saramun yake yi har ina ji kamar zai ɓalle. Ma'aikaciyar jinya Gaza ya kirawo tazo ta yi mun allura. Tun ina iya ganin shigowar ƴan ɗakinmu da fitarsu har idanuna suka rufe Bani na sake farkawa ba sai washegari da safe uwar lokacin da akaimun allurar jiya. Alhaji Zaidu na gani a zaune shi kaɗai a ɗakin ya nannaɗe hannayenshi a ƙirjinshi yana ta aikin kallona. Idanuna na sake rufewa na buɗe a karo na biyun ma dai na ganshi dan nayi tunanin ko kawalwainiyane. "Sannu Shalele kin farka?" Ya tambayeni cike da kulawa. Idanuna na lumshe hawaye suka soma zubo mun. Illahirin kunya tasa na kasa buɗe idanuna nice harda kuka mai gunji" "Ko menene ya sanya ki kuka ki tureshi gefe dan Allah. Ko dan Alhaji Baba da ya damu da lamarinki ki yi haƙuri. Sannan fa ki sani bake kika zana ƙaddararki ba Shalelena. Kuma Allah na iya kawo miki agaji ta ko wanne irin yanayin da zato bai zata ba. In nine bakya son gani zan fita yanzu" Sama da ƙasa Allah bai bani ikon na buɗe idanuna ba har saida na soma juyo takun takalminshi ƙwas_ ƙwas kafin na buɗe idanuna na dubi bayanshi wasu hawaye masu ɗumi suka sake zubo mun. Wallahi banji zan iya haɗa idanu dashi bane ku fahimceni ku tuno irin cin mutuncin da cin zarafin da akayi mun a gabanshi. "Ahh Alhaji Zaidu zaka tafi ne? " Cewar Maigogul da suka ci karo. "E Alhaji Baba zan koma Kano maiɗakina itama munyi waya da'ita bata ji daɗi ba shine zan koma. Amman kafinnan inaso muyi magana" Baki maigogul ya washe yace. "To to Bismillah muje. Lolo ina zuwa Labbai zata shigo ta zauna dake" Fita suka yi Labbai ta shigo ta zauna tayi tagumi. Labbai wani abunne ya kuma faruwa ko. Naga Alhaji Zaidu bai tafi ba har yanzu" Hannun da tayi tagumin ta sauke tace. "Bari a kira ma'aikatan jinya su duba ki. Amman kafinnan ko akwai abinda kike da buƙata? " E inaso inyi fitsari, kuma bakina ma babu daɗi" "Taso in rakaki ai tun jiya naga Maigogul ya tawo miki da kaya harda man goge baki da asuwaki. " Labbai ce ta taimaka mun nayi wanka da ruwa mai madaidaicin zafi sabida masu hawan jini ba'aso suna ta'amali da ruwan zafi sosai musamman a lokacin da ciwon nasu ya tashi. Da nayo wanka na ɗauro alwala, na sauya kaya sai naji har wata iska mai daɗi nake shaƙa. Ina zaune a kan gado ina cin fatan dankalin turawa Dr ya shigo. "Sabuwa yaya ƙarfin jikin naki? " Kallon labbai yayi yace. "Ina fatan babu gishiri da yawaitan ɗanɗano a cikin abincin ko? Kamar dai yadda akayi muku bayanin yanayin abincin da zata dinga ci" Labbai tace. "Babu gishiri, ɗanɗanonma baya baya aka saka mata Dr" "To shikenan in babu matsala inaso ki bani waje zamu yi magana da Sabuwa" Miƙewa Labbai tayi ta fice. Kujera Dr ya jawo ya zauna yana fuskantata. "Sabuwa" Ya kirayi sunana murya da sauƙi. Sama da ƙasa Allah bai bani ikon amsawa ba kaina na ƙasa kawai. Shima dai bai kira da tunanin in amsa ba. "Shawara zan baki kyauta Sabuwa sabida yanayin jikinki da kuma yadda aka kawo mana ke ranga ranga. Ita rayuwa Sabuwa ɗan adam a duk yadda ya ɗauketa yawanci haka take zuwa mishi. Na sani akwai waɗanda al'amura suke zuwa musu akasin abinda suke tunani. Mutum ya zama jarumi ma wani abune. Ita damuwa abokiyar gaba ce. Daga lokacin da kaga abokin gabanka ai ƙoƙarinka ka sauke fara'a koda ta bogi ce a fuskarka dan gudun kada yaga ka gaza. Haka in ka samu ni'ima so kake maƙiyinka ya gani domin ya ji duniyarshi tayi mishi zafi. Wannan ƙaramin misali kenan akan damuwa da jarumta. A lokacin da wani tashin hankali ya tunkaroka Allah zaka ambata shine garkuwa madogara. Wannan Allahn shi zai baki kariya kiji ki kan ƙafafunki wata jarumta na bayyana tattare dake. Damuwa dama kin gama da'ita. Shikenan zaki tsinci kanki cikin irin mutanen da babu abunda yake girgizasu a duniya. Ai in dai muna rayuwa mu ayyana komai ka iya faruwa in muka yadda da haka kamar yadda muka yadda mutuwa da hisabi gaskiya ne sai kiga mun zauna lafiya." Shiru yayi yana nazartata. A hankali nake jin wata nutsuwa na sakkomun abun har mamaki ma ya bani. Numfasawa yayi yace. "A yanayin da jikinki yake ciki akwai haɗari a faɗuwarki. Ita ƙafa da kike gani ana tattakawa kaje inda kake so a lokacin da kake so. Baka gane asalin amfaninta da gudummawar da take badawa sai ranar da ka tsinci kanka a kwance baka da ƙafafun dogarawa. Bazance ƙafa itace komai ba tunda akwai idanu da ƙwaƙwalwa mahimmancinsu suna da yawa. Sabuwa ki daure duk wani tashin hankali ke da kanki zaki guje shi. In a cikinshi kike rayuwa kiyi yinƙurin ƙaurace mishi. In hakan bazai samu ba kuma kiyi ƙoƙarin zama dashi a haka ba tare da ya cutar dake ba. Sunana Dr Rabo nine terafi ɗinki ina fatan zaki kasance cikin farin ciki" Miƙewa yayi ya fice ajjiyar zuchiya nannauya na sauke na tada kabbarar sallah ina daga zaunen na shiga rama salloli.
ALHAJI ZAID
Fita suka yi har harabar asibitin suka samu ƙeɓaɓɓen waje suka tsaya. "Alhaji Baba dama dangane da tarewar Shalele ne nake son ince kada a takura mata a barta da kanta ta fitar da lokacin da take ganin ya dace. To magana ta biyu dama inaso. A nemi wani ƙaramin gidan haya a kamashi baki ɗaya inaso gidan zan mishi gyara ne kafin lokacin biki in sha Allah ko kuma ince zan rusheshi, kuɗin hayar zan biya in sha Allah" "Alhaji kace zaka mana gini? Alhaji mungode mungode sosai. " Tsugunnawa maigogul yake shirin yi bakinshi tamkar ya yage tsabar farin ciki. Da sauri Alhaji Zaidu ya taroshi. "Kai haba Alhaji Baba ai ku iyayene duk abinda akayi muku ladane ka cancanta ne. Sannan kana da paspo ne Alhaji Baba? " Idanu Maigogul ya zare cikin zakwaɗi yace. "Ina da paspo na Alhaji" "To shikenan Abinda za'ayi zaku tafi umara da kai da ita Shalelen ka rakata taje tayi addu'o'iinta ko zuchiyarta zata yi mata sanyi, in kuka dawo ta nutsa.... " Rungumeshi Maigogul yayi ƙam tamkar zai ɓallashi dan jin daɗi da murna ta ƙin ƙarawa ya dinga sumbatar hannayenshi Godiya Maigogul ya dinga zubawa harda shessheƙar kukan farin ciki da murna. "Wai Alhaji me zance maka ne, haƙiƙa ka ɗaureni da jijiyoyin jikina abinda zance maka kamar yadda ka faranta mun kaima Allah yayi maka haka. Ubangiji Allah ya raya maka Haula" Maigogul har bakin mota ya rakashi kuɗin hayar ya dunƙulo ya bashi, da wasu kuɗaɗen daban na hidimar asibiti. Har saida maigogul yaga ɓacewar motar Alhaji Zaidu kana ya sauke hannunshi daga adabon da yake yi mishi. Wayarshi ya ciro yana zumuɗi ya kira cicib a waya. "Ƙawata ya akayi ne? Ka ganni gida zamu sake notis na rashin daraja aka bamu. Gidana da nake ginawa kasan na rufe ɗakuna huɗu falle falle babu dai daɓe a ɗakunan, nagaji da turajar masu gidan haya da irin tozarcin da suke yi mini can gidan zamu koma yanzu haka mota ɗebe mana kayanmu take yi" "Cicib kaya ya tsinke a gaɓa. Bani ragowar ɗakunan mu shiga kaji akwai labari in muka haɗu gidan nawa ma rushemun za'ayi kaga in Allah ya taimakeka kaima a jikin mijin lolon zaka samu kuɗin ƙarashe wannan ƙaddararren ginin naka da yaƙi ci bare ya cinye. Har umara yace zamu tafi ni da Lolo" Ihu cicib yayi harda buga cinya yace. «ƙawata a ina zamu haɗu to. Kun kwashe kayan naku ne? " Dariya suka saka Maigogul yace.. "Yanzu zanje gidan mu tattare komai zamu haɗu kawai a can gidan naka ƙawata nima in ɗana abun naku na ƴan Daudu. Tabb haihuwa ashe dai zataimun rana tabbb. Mrs Bukhari ce
Sai mun haɗu gobe [10/4, 10:29 PM] +234 810 593 2041: Shafi na shida
Babangida:.
Yana tubkewa da warwarewa sai jiyo muryar Ƴar Shuwa yayi tana faɗin. "Ko sama da ƙasa zata haɗe bazan taɓa yadda Sumayya taga logona ba wallahi" Idanu Babangida ya zuba mata ya kasa cewa uffan. Duk wata daƙiƙa yana mai nadamar aurenta da yayi ta shigo cikin rayuwarshi. Ko da yake hausawa na cewa mugu baya cika mugu in bai ma kanshi da kanshi mugunta ba. Wallahi a wannan lokacin baya jin ko ɗigon sha'awarta ko sonta yana dai kawai dannewane yana mu'amulantarta ba tare daya nuna mata ba. Wallahi yasan da ba dan aurota da yayi ba da Sabuwa zata yafe mishi ƙila da yanzu tana ɗakinta a zaune" "Jannaty inata magana tuntuni fa" Ya jiyo muryar Ƴar Shuwa. Jannaty inta ambaci wannan sunan sai yaji tamkar ta watsa mishi ruwan narkakkiyar dalma. A ƙoƙarinshi na son kawar da damuwar ya juyo yace. "Maikika ce Sabuwata? " A zabure ta miƙe zaune kanta ya sara mata sosai amman tsabar masifa na cinta ko zafin ciwom kan bata ji ba sai zafin kiranta da suna Sabuwa da yayi. Ganin yanayinta yasa ya tuno da suɓutar bakin da yayi na kiranta da suna Sabuwa" "Ka kira sunanta a mafarki, ka kira sunanta in muna mu'amalar aure, kana ka kira sunanta a matsayina. In na bacci kace mun baka da ikon mallakar kanka, shima yayin mu'amala kace baka sanin kana faɗa to wannan fa? " Ta ƙarashe maganar cikin shessheƙar kuka. A ɗakin Sumy a daren da washegari zai baro ɗakinta saida haka ta faru a tsakaninsu. Ranar kwanciyar auren da ba'a gama ba kenan ta hankaɗeshi saida ya faɗo. Yau gashi ya maimaita inama Sabuwa ta yadda su gina Sabuwar rayuwa mai ingancin da sai duniya ta buga ma ma'aurata misali dasu, sai sun zamema dangi da jama'ar gari ababen koyi sai dai kash ko da ta amince shari'a ta riga ta raba wannan aure har sai Sabuwa tayi wani auren ta fito. Inya tuno Sabuwa watarana dole ta zama matar wani saiyaji kamar ya lumama cikinshi wuƙa yanaji a jikinshi zai iya rasa ranshi in Sabuwa ta auri wani. "Ki taso mu tafi gida" Yana gama faɗin haka ya saka kanshi ya fita ba tare da ya juyo ba. Allah ya sani yana jin zafin ƴar Shuwa kuma yasan zaici gaba da jin zafinta abadan muddin zai buɗe idanunshi ya rufe ya ganta. Ga haihuwa matanshi biyu duk ciki garesu ai dole ya ɗauki matakin tsare iyali sabida halin rayuwar. Har suka isa gida basu yi magana da juna ba sam ko wanne da abinda yake saƙawa. Suna shiga gidan aka shiga jajanta musu, shi dai yana kaita ɗaki ya fice a gidan ya nufi unguwarsu kawai. Ƴar shuwa tana zaune suna waya da Sameerah tana sanar mata halin da ta shiga, ga taron Abuja sai ƙaratowa yake yi tarone na manyan mata tunda wasu daga ciki mazauna ƙasashen ƙetare ne amman wannan taron basa wuce shi sam tunda shekara_ shekara akeyi, kuma su tasu harkar a ƙungiyance suke yinshi akwai abubbuwa da yawa da Sameerah ta rufe ma Ƴar Shuwa sosai. Shigowar Jamila da Kulu ne yasa ta datse wayar. Suna zama wayar Jamila ta soma ruri. Matsawa tayi ta dinga noƙe muryarta tana kashe idanu dai Ƴar Shuwa tayi kasaƙe tana kallonta har saida ta gama. "Jamila sabuwar soyayya ce ta tsikareki Baban Musba ɗin ake kashe ma murya haka? " Dariya Jamila tayi suka haɗa idanu da kulu suka tuntsire da dariya. "Ha'a lafiya kuwa? " Jamila tace. "Wanne Baban Musba ana zaune ƙalau. Ni da Alhajina nake waya ya shigo gari shine nake lallaɓashi sai gobe da sassafe zan iya zuwa mishi dama gobe Baban Musba zaiyi lodi zuwa Inugu. " Baki Ƴar Shuwa ta riƙe. "Jamila wai dama ashe ƴar hannu ce kema matarnan shine duk wasu abubbuwa na ƙawa sai ki fito dashi tsakar gida kice mijinki ne yayo miki tsarabarsu? " "Uhm kinsan Allah ni nake yima kaina komai. Ba mazajen yanzu basa iya sauke nauyin iyalansu ba? Kuma ko sun ganki da kuɗi suka tambaya ɗaya biyu da kince sana'a kike yi sai kiji baki gum ba?. Nifa mitsiyacin mijina inya tashi dawowa ko lemon totuwa baya riƙowa. Idan ya tafi sai yafi wata guda bai waiwayoni ba. Nera dubu ashirince yake bani ni da yara uku. A ciki zanyi awo, a ciki zansai kalanzir, aciki zansa mai da maggi, kayan miya, kifi ko nama, a ciki zan sai ruwa, wani sa'in har kuɗin wuta. Shin zama zanyi talauci ya kasheni, ko kuma in zama bazawara ana zinɗena a unguwa?" Kulu tace. "Uhm dani da'ita duk fa hakan take. Kuma ke kanki da halama kin shiga sahu dan munga sai gyare_gyaren ɗakinki kike yi kinyi ma abokan zamanki zarrah" Ƴar Shuwa tace. "Ai saina ma haihu zanyi sunan da sai kishiyoyina sun gane ruwa ba sa'an kwando bane wallahi. Kuma inanan kafin suna saina sake komai na ɗakinnan nawa ya koma sabo fil. Ashe dai sirrin kenan Kulu ke da Jamila kullum shar daku? Jamila tace. " Wai kinsan wa ya ɗaurema Kulu ƙunƙuru kuwa? Baban Shafa maƙocin ɗakin Ramatu kishiyarki fa" Idanu Ƴar Shuwa ta zare tace. "Baban Shafa na gidannan wai? Tabbb ashe da Maman Shafa zata sani da sama da ƙasa ta haɗe tabb. Ni bama wannan ba wanne malaminne yake baku Sa'a ne. Nifa wallahi mijinmu mugun taurin kai gareshi asiri baya kamashi sam. Gashi da mita da saka idanu. Sannan ga matsalar da nake fuskanta kan tsohuwar matarshi kunsan ko mu'amala muke dashi sai kuji yana ambaton sunanta. Ga matsalar Sumayya wannan abinda tayi mun wallahi bazai tafi a banza ba sai nayi maganin ƴar banza" Kulu tace. "Ke na taɓaki da alkhairi. Muna da boka a hannu duka ɗauka abu ma in bazai yiwu ba shi baya cin kuɗinki zai tsage miki gaskiya. " "Yaushe zaku kaini dan Allah? " Jamila tace. "To ni gobe ina da fita kin dai sani. Amman ga Kulu ko gobe ai sai kuje. Amman fa ki tanadi kuɗaɗe dan wallahi aikinshi kinsan muguwar tsada? To akwaita ƴan siyasa sun lalatashi da manyan kuɗi. " "Kuɗin bazai zama matsala ba inaso a rufe ma Baban Fati baki ne. Sumayya kuma sai ta zama bola a gidannan in sha Allah" Sun jima sosai suna tattaunawa sune har la'asar sakaliya kafin suka tafi dama haka suka saba zama su shantake ko wanne ɗaki suka shiga. Daga wannan ranar aminci da yadda da juna ya samu gurbi a zukatan waɗannan shaiɗanun mata ukun.
Babangida:. Gidan malama Babba yaje yayi kwanciyarshi zazzaɓine kau a jikinshi a duk lokacin da tunanin sabuwa da son kasancewa da'ita ya motsa mishi ciwo sai ya kaishi ƙasa. Wajen malama Babba yake gudowa yazo yayi kwanciyarshi. Yanzu ta ɓalla mishi fanado ya haɗiya. Yana kwance a doguwar kujera Sa'a ta shigo tana ta kururuwa da kwaroroto. Kudidi na biye da'ita. "Wai Sa'a lafiyanki kuwa?" Faɗin malama babba" "Ina lafiya Baba malam ne ya kira Baban yara suka tsaida lokacin auren waccen shegiyar yarinyar wai nan da shekara guda. Kuma kiji malam ya nema mata gurbin karatu a jamila ɓangaren islamik sitadis. Abinda mu bai yadda munyi ba bai jawo yaranmu ya basu koyarwa ba duk sai mardiyya ita kaɗai ya ɗaukaki yaran abun har yayi yawa. Gurbin karatu a jami'a fa" Babangida ya miƙe zaune yace. "Sa'a kada ki sake ki sake kira mun yarinya da shegiya dan nine ubanta shege kuma wanda baida ubane ita kuma mardiyya nine ubanta. Idan rayuwata da duk abinda na mallaka zai salwanta zan bata kariya ina bayanta yana da kyau ki riƙe mutuncinki sabida na lura baki san abinda ake kira kawaici ba sam." Ba Sa'a ba har malama Babba sai da suka shiga ɗimuwa ɗakin yayi tsit anata kallon Babangida. Da sauri Sa'a ta miƙe tana shirin marinshi yayi carab ya riƙe hannunta ya matse jikinshi har rawa yake yi ya ƙura mata idanunshi da suka rine. "Ni kake riƙema hannu Babangida shaye _shaye ka koma kome? " Murmushi yayi daya tuno sanda yake jifan Sabuwa da irin kalmar sak. "Ba shaye _shaye nake yi ba amman ki sani akan mardiyya zan iya rungumarki mu yi mutuwar kasko a kiyaye taɓamun ita. Sannan tunda dai Baban yara ya amince da auren ai shikenan. Har cikin raina bazan so ɗiyata tayi auren ƙasƙanci ba domin zumunci zai iyayin lalacewar da zato bai zata ba. Sa'a bana jin zan iya kawaici ki ci mun zarafin ɗiya, kuma wallahi ba zata zama borar miji da dangin miji ba. Sannan wallahi in labarin asalinta ya fito ta bakin ki har abada ni dake" Shirin fita yake yi. Malama tace. "Dawo Baba me yayi zafi. Dawo ka zauna nace. Ke Sa'a menene haka muna zaman zamanmu kinzo kin hautsina mu akan abinda kika san tun yarannan suna ƙanana aka haɗa, yaronnan ba daɗi yake ji ba yanzu na bashi magani ya haɗiya fa. Baban yara zaiƙi bin umarnin Malam ne a matsayinshi na almajirinshi? Kai kuma Baba kayi haƙuri duk a taru a rufa ma kai asiri tunda malam ya matsa kasanshi da kafiya." Zama suka yi Sa'a tana faɗin har gaba da abada ba zata so Sabuwa da zuriyarta ba. Kuka ta fashe dashi tana faɗin.. " "Ni wallahi an cutar damu me yasa Sauban aka zaɓa ma Mardiyya ba'a bata wani ba. Baga yara maza a ɗakin kudidi da ɗakunan su Wawo da su Bashir ba me yasa sai Sauban? " Kudidi tace. "Allah mai iko. Ni wallahi zanje in tari Baba malam da batun a haɗata da Surajo na wajena dama ya kusan kammala jami'arshi ta madina in ya amince wallahi ko gobe a ɗaura. Sa'a mardiyya fa bata da laifi cikin wannan lamarin. Inma akwai fa to wannan shashashan shine mai laifin." Babangida yace. "Ba Surajon da zata aura. Wallahi Sauban ɗin muke so sai dai ita Sa'an ta mutu" Kawu Manga ne ya shigo ya zauna tare da cewa. "Zancan Surajo baima taso ba Kudidi Allah yayi miki albarka zamu ce kawai. Kai kuma ga Sadakin ɗiyarka Malam ya biya nera dubu ɗari da hamsin za'ayi bikin da wuri in sha Allah gudun matsala da ance nan da shekara to labarin ya canja. Ke kuma Sa'a zaki gane Malam kika taɓo wallahi, yana can yana fishi dake sosai tashi ki fice a gidannan mutuniyar kawai" Sa'a fita tayi tana kuka. Babangida ya karɓi kuɗin ba dan yana so ba sai dan rashin zaɓi kawai Malama Babba tace. "Ai shikenan wato shi Malam tsaurinnan nashi yayi yawa ace bazai iyaye su zaɓa ma ɗansu matar aure ba wai dole ni sai Malam ya kasheni da baƙin ciki ne? " Kallonta Babangida yayi tana shirin zubar da hawaye. Idanun da suka haɗa taga idanunshi jawur yasa ta fasa kukan ta kuma ji kunyarshi ainun. Kanshi kawai ya sauke yana jin shima kamar ya zubar da hawayen. Sun jima sosai suna tattaunawa Babangida dai sai da yayi sallar isha ya hau mashin ɗinshi ya tafi gida. Kai tsaye ɗakin su Mardiyya ya shiga ya taddasu suna ta karatun Qur'ani mai girma. Shiga yayi sukaita rare ƙira'a cikin suratul ali imran Idanunshi suna rufe sun taru da hawaye suke wannan karatun sun daɗe sosai suna yi kafin daga bisani suka gama. Suna shirin yin adda'a wayar Mardiyya ta yi ruri Labbai ke kiranta. Da zumuɗi ta ɗaga wayar ta saka a hannu huta ( hands free) "Ke mardiyya gobe ki tambayi Baban naku kuzo ku duba umminku a asibiti bata da lafiya kinji ko?" Babangida yayi shiru kanshi a ƙasa. "Umma Labbai meke damunta dan Allah, ya jikin nata? " Yaran duk suka dawo wajen Mardiyya. "Hawan jininta ne ya tashi Mardiyya" Ai da sauri Babangida ya amshi wayar sai jin muryarshi Labbai tayi. "Labbai me ya sameta har hawan jininta ya tashi. Ya jikin nata dan Allah, ko in kawo su yanzu? " "Jikin da sauƙi ba sai kunzo yanzu ba. Gobe in Allah ya nuna mana kwa tawo ɗin nagode sai da safenku" A hankali ya sauke wayar zuchiyarshi yaji ta sake karyewa sosai. Inama Sabuwa zata iya sake ara mishi dama su sake zaman aure. Da taga gata ma'ishi gatan da sai ta zama abar kwatance abar sha'awa a dangi. "Mardiiyya ku shirya gobe sai muje mu dubota irin wajajen sha ɗayannan ina da ɗalibai masu jarabawa inna sallamesu sai in zo in kai ku. Zan baki kuɗi gobe kiyi cefane ni da kaina sai in girka mata abinda ta fi so."