Idan kaya ya gaji book book 4 - Chapter 6
Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 6: Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 6. Sabuwa:. Ina yin Sallah Labbai ta shigo ta zauna naga ta sake gasa…
2,723 words
Sabuwa:. Ina yin Sallah Labbai ta shigo ta zauna naga ta sake gasa tagumi. Ina idarwa nace. Wai ni Labbai lafiya kuwa kina ta tagumi. Sannan me ya faru naga Rakiya da Maigogul sai riritani suke yi ne? " Ajjiyar zuchiya ta ja ta sauke kafin tace. "Lolo wai kinsan waye yace yana sona harna kasa bacci na kwana cikin tubkewa da warwarewa kuwa? " Kai kawai na girgiza mata ina saurarenta. "Cicib ne wai yake so zai aureni kuma da gaske yake yi, yace ma in dai na amince sai a haɗa bikin lokaci ɗaya dana Uzairu zuchiyata kinji abinda ya kaɗa mun kai" Dariyar dole ce ta suɓuce mun na dubeta na maya. Ke kuma to kina son nashi ne ɗan daudun? " "Lolo mu faɗa ma kanmu gaskiya. In naƙi Cicib wa zanso. In shi Ɗan Daudu ne ubanmu menene shi? Dashi da Maigogul babu wani bambamci Allah. Lolo wallahi nagaji da rashin aure na gaji. Nifa a wannan karon zanso ma Maigogul ya kafe ni a gidan Cicib inna shiga mutu ka raba. Wallahi lolo na gaji. Ke dai kakarki ta yanke saƙa" Kafin nace wani abun sai ga su Uzairu zuchiyata sun shigo dasu Gaza harda magazin. Uzairu zuchiyata sai rufe bakinshi yake yi tsabaragen dariya akan batun soyayyar Cicib da Labbai ne nasani. "Amarya kin sha ƙamshi matar manya kaga mai Sa'a" Kaine sai ya kuma ɗaurewa na dubi Uzairu zuchiyata nace. Ban fa gane me kuke nufi ba Uzairu zuchiyata ya bani da lafiya kuna kirana amarya. Wani abunne ya faru ne ku faɗa mun? " Maigogul ne ya shigo zuruf yace. "Zanyi miki bayani Lolo da kaina. Ta inda ake hawa tanan ake sauka. Ku bani waje ni da'ita" Ficewa suka yi suka barmu. Bayan shiru ya wanzu na lokuta sai Maigogul ya fayyacemun duk abinda ya faru. "To dan haka abinda nake nema dake Sabuwa ki rungumi mijinki sawu da ƙafa ki zauna har gaba da abada a ɗakinki kafeki ma ni zanyi gaskiya. Kinga yanzu haka gidanmu yace zai rushe yayi mana sabo. Lolo abun ƙarin farin ciki dani dake ya biya mana umara zan rakaki muje mu roƙi Allah akan lafiyarki, ki kuma roƙi Allah akan yasa mutuwace zata raba aurenan. Batun rushe gida da zuwa Umara ko Rakiya bata sani ba Aminina kaɗai na faɗama dalili shine a gidanshi zamu zauna kafin a gama ginin namu gidan. Yace kuma kada a takura miki a barki da kanki ki faɗi lokacin da zaki tare a ɗakinki a tsanake. Lolona nasan ai ba zaki bani kunya ba ko Lolo?" Idanuna na lumshe wasu hawayen farin ciki cakuɗe dana fargaba suka shiga gangaromun Har cikin raina naji sanyi sosai. Kuma ina jin tsoro shima fal raina. "Lolo kaddai bakya sonshi ne kike kuka? Ke da zaki yi farin ciki Allah ya zaɓeki ya baki miji irin Alhaji Zaid babban mutumne fa a ƙasarnan mai arziki kuma sananne. Nayi imani zai riƙeki da kyau. Duba yadda ya sauya miki rayuwa cikin ƙanƙanin lokaci. Ki dena kuka kada Allah yayi fishi ya karɓe ni'imar daya baki. Ga ƴan uwanki suna neman ko kamar tsohon faƙirin mijinki na dane basu samu ba. Ke Allah yayi gaba dake kuka kuma ai ya ƙare ki dubi abinda Allah yayi mana ta sanadiyyarki fa Lolo" Sai naga Maigogul na share hawayenshi da bayan hannunshi, take zuchiyata ta karye. Wato Allah ya jarabceni da son mahaifina sosai, duk yadda yakennan inason kayana a haka sosai. Hakane Maigogul nagode ma Allah sosai. Kuma nayi farin ciki gaya Ubangiji Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a garemu baki ɗaya Nayi farin ciki daya biya mana umara tare muje mu roƙi Allah tare. " Dariya muka yi. Zukatanmu cike da farin ciki marar misaltuwa ga hawaye tab guraben idanuwanmu Wannan ranar tana ɗaya daga cikin muhimman ranaku marasa goguwa a cikin zuchiyata. Lokaci ɗaya nauyin da kaina da zuchiyata yayi sai ya yaye baki ɗaya na shiga wani irin shauƙi kawai ni kaɗai inna tuno fuskar Alhaji Zaidu da kalamanshi sai in sauke ajjiyar zuchiya. Kunji fa wata ƙudurar Allah ina masu ganin bazan samu kamilin namiji ba sai ballazi irina? To shi Allah babu ruwanshi Soyayya kuma gaskiya ce. Tunda ana iya wanke karuwa tas a aura, ko a wanke kirista a aura balle ni tubabbiya mai cike da nadamar rayuwar dana gudanar a baya. Haka muka wuni a asibiti, rabi ina bacci rabi idanuna a buɗe. Labarin zuwana umara da ginin da Alhaji Zaidu zaiyi mana ya karaɗe gidanmu banda maƙota Maigogul yace kada labarin auren da labarin komai ya fita waje. Amman nasan Hauwa zaiyi wuya ta iya kame bakinta ta dai ce zata kame. Rakiya jin zamu je umara ta shiga fishi tana cewa ya dai tabbata Maigogul nake nuna ma tsantsar ƙauna shi yasa na zaɓi muje tare banda ita. Uzairu zuchiyata yai ta mata dariya kawai yana cewa. "Rakiya ai zaki Canada meye ma na ɗaga hankali tunda ya iya biya musu wallahi in kina da rabon zuwa zaki je ne, ko ni sai in biya miki gaba" "Ai shikenan Uzairu zuchiyata gata ga Maigogul na ɗauki idanu na zura musu zai bata kunyane in batai da gaske ba ma sai ya lalata mata auren zai huta. To kuma shi tarewar sai yaushe zaki tare tunda an riga da an ɗaura auren? " To inaso muyi magana ni dashi tukunna inji yadda yake so sai in gani Rakiya" Kai ta gyaɗa tace. "Ai shikenan. Wannan Alhaji ya taimakemu sosai gida shekara da shekaru babu sauyi kinga lokaci guda mun tattare komatsenmu za'a rushe gidan. Wai kinga yadda akaita fitowa a layi ana tambayarmu ko lafiya gidan muka siyarne. Hauwa ce ma take tankasu ni ko suna kan kwashe kayanma Maigogul yace in tawo wajenki." Uzairu zuchiyata yace. "Ni fa a wannan safgar ni aka taimaka Allah yasa yayi mana gidan sama wallahi da mun huta ma baki ɗaya" Murmushi kawai nayi. Sallamar su Mardiyya ce ta katsemun murmushina idanu biyu muka haɗa da Babangida da ya kafe ni da idanu. Da gudu malama tazo ta faɗa jikina. "Ummi yaya jikinki? " Da sauƙi malama ya kuke ya makaranta? " Gaisuwar da Babangida ke ma Rakiya yasa dole na ɗago uhm jama'a Babangida harda rusunawa fa in da ranka kasha kallo. Rakiya da Fara'a ta amsa tana riƙe da hannun Aɗɗa'u. Mardiyya ta ƙaraso ta ajjiye abincin duk yaran suka matso muka gaisa. "Sabuwa yaya jikin naki? " Na jiyo amon muryar Babangida. Ya cika turare ya wani ci uban ado kamar zashi gidan biki. Da sauƙi nagode" Na faɗa kadaran kadahan tare da kwanciya na lumshe idanuna. "Ummi ga abinci faten tsaki muka kawo miki in zuba miki? " A_a mardiyya nagode bakina babu daɗi ku ajjiye ƙila su Uzairu zuchiyata zasu sha. " "Ke kawo nan ki gani in zuba. Babangida Bismillah ka zauna ga waje" Cewar Uzairu zuchiyata dake dambe da kular fate. Bayan ya zaunane yake cewa. "Rakiya dama nayi niyyar zan samu maigogul in sanar mishi an kawo sadakin Mardiyya nera dubu ɗari da hamsin" Mardiyya tayi maza ta sauke kanta tana wasa da yatsunta, Uzairu zuchiyata ya duma mata dundun wasa su Aminu sunata mata dariya. Rakiya ta kuwa washe baki. "Kai masha Allah wannan labarin yayi daɗi Allah ya sanya alkhairi. Dashi Sauban ɗinne? " "Eh da shine Malam dai ya matsa bikin ma bazai daɗe ba kamar dai yadda ya faɗa." Yawun baƙin ciki na haɗiye wallahi Allah ɗaya kenan da badan Baba Malam ba banga uban da ya isa yasa ayi wannan haɗin ba. Babu komai zan ɗauki ido in zuba, sai dai fa bazan taɓa bari ɗiyata tayi boranci ba. A zuchiyata nake wannan maganar naƙi fur in buɗe idanuna dan bana ma son sake ganin Babangida har ƙarshen rayuwata ma. "Rakiya ta samu gurbin karatu ma Jami'a zata soma zuwa" Cewar Aminu Nan sukaita murnarsu. Uzairu zuchiyata yace. "Ai lokacin da muka shirin tafiya Canada ni da lolo mun kira ita mardiyya lokacin ma muna Airport akan suyi mana adda'a, naso ma in da kananan lokacin kaima muce kayi mana adda'a" Ya ƙarashe yana ƴar dariya. "Canada kuka je babu labari, ke mardiyya shine baki faɗa mun ba? " Babangida yayi maganar muryarshi har tana ɗan ɓari ko na meye oho, nasan Uzairu zuchiyata ya faɗa mishi ne danya kunnashi, ya kuma sani sarai ƴan gidanmu bama ƙarya gaskiya duk ɗacinta ita muke faɗa. Ni dai har suka tafi ina haɗiɗiye baƙin ciki. Suna fita na ɓude idanuna na dubi Uzairu zuchiyata sai fate yake ta sha baya ko magana ga faten yaji tantaƙwashi sai maiƙo yake yi harda yajin daddawa da man shanu a ciki. Idanu ya kashe mun, murmushi kawai nayi mishi" "Lolo girma ya hauki dole. Wannan yarinya biki ya gabato damma Allah ya taimakeki yanzu mai dashi kike aure zaki fitar da ɗiyarki kunya" Uhm ita ta kunya take. Ni kuma ta makomar auren kawai nake yi Sa'a bata da daɗi kamar kashi"
KANO:. Alhaji Zaidu yana tafe a mota yana waya da amininshi Alhaji Rabi'u suna batu akan auren nashi. "Amman tunda ka biya ma amaryar umara mai zai hana kawai ka bata kuɗin lefen su wuce ko Dubai ne su haɗo lefensu ko mai kake tunani in yaso sai ka haɗasu da mutuminka Rasheed. Ko Hajiya ce zata haɗa mata kamar dai ko yaushe? " Alhaji Zaidu yace. "To ka kawo shawara abinda za'ayi zamu tattauna da amaryar muji yaya take so. Hajiya ma sai in saka mata kuɗinta kawai a asusun bankinta kaga shikenan." "To tsare_tsaren yadda za'a gudanar da shagulgulan bikin fa? " Dariya Alhaji Zaidu yayi tare da cewa. "Mu ba yara ba ai ina ganin Dina kawai zamu haɗa ranar da Amarya ta tare aci asha a watse shikenan ai. Amman kada kayi hirarnan da Hajiya Mariya kasan dai mata sarai basu da sirri kuma wannan ba maganar wasa bace" Dariya suka saka tasu ta manya da haka sukai sallama da juna. Cikin hukuncin Ubangiji Alhaji Zaidu ya isa Kano cikin aminci. Yana isa ƙofar gidanshi ya matsa ƙararrawar motar maigadinshi ya leƙo yana ganin motarshi ya wangale mishi get ya shiga a hankali. A tsakar gidan ya ga motar Hajara Ƙanwarshi mai bi mishi. "Malam Bala yaya gida ya iyalan kuma? " Malam Bala maigadin gidan Alhaji Zaidu ne sun shafe fin shekaru ashirin yana musu gadi Tare yake zama da iyalinshi a wajen adana baƙi (BQ) "Iyali sun tafi ƙauye bikin ƴar ƙanwar ita Gaji akeyi shine ta tafi tun jiya. Yaya jikin Hajiya ashe bata ji daɗi ba? " "Wallahi kuwa Malam Bala. Allah ya dawo dasu lafiya ni bari in shiga ciki sai na fito Sallah" Malam Bala yayi mishi godiya ya koma ɗakin gadinshi. A tsanake cikin kamala ya shiga katafaren falon mai shaƙe dam da kayan ƙawa, ga wani irin turaren wuta na busa ƙamshi a falon Ac kuwa tsabar sanyi kamar hunturu. Babu kowa a falon sai tv a kunne da jakar Hajara a kan kujera da mayafinta. Falon Hajiya ya nufa kai tsaye, nanma basa ciki a ɗakin baccinta ya samesu Hajara na haɗa mata Shayi ga aminanta biyu suna kan gadon itama tana gadon ta jingina kanta da fuskar gadon Sallamarshi yasa ta lumshe idanunta ta buɗesu a hankali a kanshi. Murmushi ya sakar mata, itama murmushin tayi mishi. Ƙawayenta duk suka mayar da mayafansu jikinsu Hajara ta miƙa mata shayin. "Yaya Zaidu sannu da dawowa ashe zamu haɗu?" Hannu ya miƙa mata suka gaisa haka suka saba a gidansu. "Mutanen Rano me zan samu ne Hajara sai kyau kike sake yi Abdulmalik yana ƙoƙari da cinki sosai" Dariya suka yi harda ƙawayen Hajiya, ita ko Hajiya mijinta kawai take kallo damuwace linkib a fuskarta. Gaggaisawa akayi cikin girmamawa duk suka zame suka basu waje. Malum malum ɗin jikinshi ya ajjiye a kujera ya zauna a gefen gadon ya miƙo mata hannayenshi dukka biyun ta tawo, tana saka kanta a ƙirjinshi ta sau kuka. Ita mace fa bata tsufa da soyayya da shagwaɓa sai idan itace taso mayar da kanta baya Mrs bukhari
To ni kam na gudu🤺🤺🤺🤺 [10/4, 10:29 PM] +234 810 593 2041: MRS BUKHARI 7
Bayanta yake bubbugawa cikin sigar rarrashi. A kunnenta kuma yana raɗa mata. "Kiyi haƙuri ba gani a kusa dake ba. Ina tare dake har abada. Faɗamun Menene ya hautsina mun ke? " Ɗagota yayi yana share mata hawaye tare da bata duk hankalinshi dan jin menene kokenta. "Ba na sanar maka zamu je yima Hajiya Baturiya dannar ƙirji ba? " Kai ya gyaɗa mata halamun yaji. Taci gaba da cewa. "Munje anata sha'anin biki sai Matar Ibrahim suka iso mutan Abuja. Shine fa Hajiya Baturiya daga tambayar Matar Ibrahim Hafsa da muka je bikinta shine take cewa ai ta tafi london haihuwa su irin haihuwane kab danginsu in aka yima mace aure da ɗanta take shekara " Hawayene suka gangaro a kuncinta. Hannayenta ya riƙo yayi jigum yana nazari, ina kuma sai kuka marar sauti take yi zuchiyarta nayi mata baƙi" "Wato ita dai Yaya Dubu bata kama girmanta ita duk sha'anin da zata zo in dai zaku haɗu sai ta saka mun ke kuka? Ke kuma kin kasa cire maganar haihuwa a ranki kika sani ko ba alkhairi bane haihuwar a garemu ba shi yasa Allah bai bamu ba. Bayan ke ba wasu matan sun shigo basu haihun ba? ko dai kina nadamar kasancewa tare dani ne sabida nakasun rashin haihuwata, ko kina ganin akwai wani hakkinki dana tauye miki? " Da sauri ta ɗago ƙur taga shima ita yake kallo. "Har gaba da abada bazan taɓa ƙosawa dakai ba. Kada ka mance a shekaru biyar na aurenmu kayi mun tayin saki, a shekaru goma ma kayi mun tayi, muka shekara sha biyar shima kai mun tayi, mun shekara sha bakwai shima haka kamun tayin sakin yanzunma da muka riga muka manyanta tayi sakin zaka yi mun? . Zaid har abada ni ɗinnan taka ce rayuwata a gidanka zata ƙare kaine maƙabulina. Dangane da hakki wallahi ni gani nake yi babu yakai. Ka bani duk wata dama, ga soyayya, ga tarairaya danginka ma sai dai ince Alhamdullilah baka tauye mun komai ba" Rungumeta yayi tsam yana sauke numfashi sun jima sosai a cikin wani yanayi. Yaita rarrashin matarshi har saida ya kore mata damuwarta ta mance da komai. "Hajiya kin mance dasu Hajiya Kulu. Nima kin mance baki ce a bani abinci ba." "To ai Royal ganinka ya mantar dani komai. Kaje kayi wanka zan kawo maka abincin da kaina." Fita yayi yana murmushi tare da girgiza kanshi. Babban falon gidan ya tsara ya hau ƙafar bene da zata sadashi da sama. "Yaya inaso zamu yi magana fa? " Cewar Hajara. Bai juyo ba yace. "In Hajiya zata hauro sai ku hawo tare Hajara. Nasan ai jarinki ne zaki ce yayi ƙasa bazai wuce haka ba. Gaye yaushe zai bar Hajara ta tara dukiya, haka ma cin abinci ai bazai barki ki tara kuɗi ba. ( a daidai nan ina da tsokaci a page ɗin jiya akwai inda na rubuta Abdulmalik yana ƙoƙari da cinki, to dake maganace mai harshen damo wasu sun ɗauki ɗayan ɓangaren, wasu kuma sun ɗaukeshi a yadda na rubuta. Yana nufin yana ƙoƙari wajen ciyar da'ita Hajara mai cin abinci ce sosai dan Allah ayi mun afuwa Subhanallah haka nake nufi) Dariya tayi dan tasan a gidansu Yayanta yafi kowa saninta. Ai kuwa da Hajiya zata hauro tare suka hauro Hajara na riƙe da tiren abincin wan nata, a gabanshi ta dire yana zaune yana amsa waya. Saida ya kammala kana ya dubi Hajiya yace. "To Yaya jikin naki ince dai yayi sauƙi tunda gani ko? " "Da sauƙi kasu kusan hamsin ya tafi" Murmushi suka yi su biyun. Hajiya na shirin miƙewa dan ta basu waje yace. "Yi zamanki jarine ta karyo shine ta dawo. Gara dai ki zauna ko zaki ƙara mata haske kan yadda ake tattala uwar kuɗi a sake haɓakata da ribar da aka samu. Yarinyarnan na kasa gane kasuwancinta Abdulmalik yana ƙoƙari" Dariya suka yi dukkansu ya ɗauki kuɗi masu kauri ya bata, Hajiya ma ta ƙara mata da nata. Alhaji Zaidu mutumne mai ƙoƙari sosai, yana da son mutane da yawan alkheri in ana ganin kamar yawan Alkherinshi yayi yawa sai yace to wa yake dashi da zaici gado bare ace zai musu tanadi ai gara ya nemi lahirarshi.