Idan kaya ya gaji book book 4 - Chapter 7
Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 7: Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 7. SABUWA:. Ina bacci bayan na idar da sallar isha wayata ta shiga tsuwa.…
3,263 words
SABUWA:. Ina bacci bayan na idar da sallar isha wayata ta shiga tsuwa. Rakiya ce ta tasheni ta mika mun wayar Alhaji Zaidu ke kirana. Gabana saida naji ya ɗan faɗi a sanyaye na kara wayar a kunnena. "Barka da dare Shalele amaryar Zaidul'abidin, da fatan jikinki da sauƙi ko? " Idanuna na lumshe ina jina wani iri dani wani bawai nake ji wallahi. Lafiya lau kaje gida lafiya? " Ajjiyar zuchiya ya sauke kafin yace dani. "Lafiya lau na je gida. Sai dai babu nutsuwa sam tare dani. Na tafi na barki a cikin halin jinya, duk da gobe nake son zan dawo har sai an sallameki tukunna" Idanu na zare nace. Haba dai ai ba sai ka dawo ba. Kayi zamanka nagode sosai " Shiru ne ya ratsa wayar ni dai bansan ta ina zan soma mishi godiya bane shi yasa nayi shiru. Shi kuma ashe hawa da saukar numfashina yake saurare sai can yace. "Kinyi shiru na zaci zaki tambayeni me yasa na aureki ba tare dana nemi izininki ba. Duk da dai kinsan abinda ke raina a game dake" Daddagewa nayi nace. Ni kuma nayi shiru ne ina jiran ka tambayeni gaskiyar abinda wannan matar tazo tana faɗi, da kuma tambaya akan ahalina" "A_a wannan ai sabgar kishinku ne na mata Shalele ina ni ina shiga wannan maganar. Batun tuntuɓar ahali kuma ai mun riga mun haye wannan siraɗin uhm? Da fatan dai kin amince dani a matsayin miji ko? " Munfashi na ja na sauke kana nace. To ai babu macen da ba zata amince dakai ba. Babu abinda zance dakai sai dai ince Allah ya bamu zaman lafiya ɗorarre sannan Allah yasa in haifa maka masu kama dakai" Murmushi yayi yace. "Ameen matata naji daɗin wannan shinfiɗar taki. Sai dai kuma kash ni nafi son in samu masu kama dake, ko masu kama da Alhaji Baba dan ya fiku kyau nesa ba kusa ba" Murmushi kawai nayi ina tuno fuskar Maigogul. Shiru ya kuma ratsa wayar nina katse shirun ta hanyar cewa. Naji labarin ka biya mana umara, kuma kasa su tashi zaka rushe mana gidan ayi sabon gini. Sannan nagode da ɗawainiyarka Ubangiji Allah ne kaɗai zai iya biy.... Kukane yaci ƙarfina na kasa ƙarashe maganar. Rakiya ta zubo mun harara. "A_a Shalelena banda kuka wannan ai yima kaine iyayenki ai nawa ne. Ni ba dan sabida ke nayi ba sabida Allah nayi. Ke da baki da lafiya kina kuka" Shiru nayi kawai. "Shikenan yanzu ki kwanta kiyi baccinki zan shigo gobe da yamma in duba jikin naki, ki kula mun da kanki ko? Illahirin kunya da mamaki tasa harna kashe wayar ko tari na kasa yi. Ina sauke wayar Maigogul da Cicib da Labbai suna shigowa ga kulolin abinci a hannun Labbai. "Lolona ke da wa kike waya? " Maigogul ya ƙaraso ya zauna a bakin gadon. Alhaji Zaidu ne ya kirani. Shine nake mishi godiyar abinda yayi." "Allah sarki Lolona na fiki farin cikin samun wannan hamshaƙin mijin. Amman fa tsugunne bata ƙareba kinsan ba lallai abokiyar zamanki ta soki ba. Dole zan warware buzu in ɗanyi abinda zan iya tawa gudunmawar kenan. Ko ba haka ba Rakiya? " "Sosai kuwa kayi daidai hakan yayi irin waɗannan masu arzikin matansu kishi dasu babu kyau ai" Cicib ne ya ƙaraso bakin gadon da nake har da dafa mun kai. "Ƴannan ya jikin naki, ya muka ji da abun arziki kuma? " Lafiya lau jikin da sauƙi" "Kai ba dole jiki yayi sauƙi ba. Matar mai kuɗi ce, ga zuwa umara na jiranta. Allah kaɗai yasan ƙasashe nawa zata taka haihuwa tayi mun rana ni maigogul" Tsaki Rakiya tayi, Labbai tayi jigum, inta kalli maigogul sai ta kalli masoyin nata Cicib. Maigogul da kanshi ya zubo mun faten tsaki yaji kifi da tantaƙwashi. "Gashi ki sha ni da kaina nayi miki maza matar manya ki sha" Karɓa nayi ina sha yana bani labarai na takaici dana dariya dukka dai yaita hilatata na ko sha faten dayawa. "To Rakiya mu kam ki taso muje mu saukeki Labbai zata zauna da lolo sunce ma zuwa gobe zasu sallameta da yau ma suka ce to tunda dai har tara tayi sai kuma gobe" Sallama Rakiya tayi mun ta kwashe kwanuka ta tafi dasu. Labbai ta hayo gadon tace. "Mun dai sasanta kanmu da Cicib ke wai kinji kalmomin soyayya lolo illahirin kunya ai lulluɓeni tayi. Gashi yanzu gidanshi muka koma da zama. Da yamma ma ni da Shafan shi mukai wanke wanke. To Allah yasa hakan shine alkhairin. In da rabo watarana zai daina daudun zan yi ƙoƙari ko Allah zaisa in zama sila. Lolo ki taya ni murna da adda'a" Wallahi ba ƙaramin mugun tausayin Labbai naji ba. Har ga Allah nasan bata da zaɓine yasa ta amince zata auri Cicib domin samun mafaka da zama a shinfiɗar aure. Amman meye abun burgewa tattare da Cicib illahirin jikinshi babu inda baya lanƙwasawa in yana tafiya. Maganarshi kuwa ko tsohuwar karuwa albarka. Amman shima bashi da laifi ta fuskar zati fuskarshi ma ta mata ce, kuma yana da haske saidai yana ƙarawa da man shafe_shafe dai Ajjiyar zuchiya na sauke nace. Allah ya sanya alkhairi Labbai. Yanzu acan zamu zauna kafin dai a gama ginin gidan ko? " "Eh a canne. Maigogul fa kuɗin haya mijinki ya bashi kinsanshi da maganar kuɗi ai. Ga Sama da Rita suma sun zo suna can gidan wai notis ashe aka basu wata shida to yau ita matar ta tafi aiki, shima ya fita mai gidan yazo ya kulle gidan shine suka rankayo amman matar tasa ana nema musu wani gidan hayar ko a layin su Cicib ɗinne. " Iko sai Allah wannan mata ta Sama tana ƙoƙari so hana ganin laifi kenan. Yanzu bil haƙƙi tana son Sama ko Labbai? " Dariya muka saka harda tafawa tabb Raujin amon shigowar saƙone ya katse mana hirar tamu. Ina buɗewa ga abinda Alhaji Zaidu ya rubutu. "Watarana uwar haka a cikin wani dare makamancin haka kina ƙirjina ina shafar kanki. Ni Zaid zan nuna miki gata zan tarairayeki sai na mayar dake fil. Kiyi bacci mai cike da mafarkan rayuwar aurenmu Sai da safe jinin jikina. Mijinki Zaidul'abidin." Tunda na lumshe idanuna sai kawai na kasa buɗewa na shiga wani shauƙi mai girma Jijiyoyin jikina sai amsar saƙon Alhaji Zaidu take yi. Man kaina sai tsiyaya yake yi Sai kuma naji na faɗa fargaban shin danginshi zasu karɓeni da mutunci kuwa, matarshi fa wanne irin zama zamu yi? Da wannan tunanin na jiyo wayar Labbai na rauji Darling Cicib ne ya kirata sun kuwa daɗe ainun suna wayar har saida tace mishi bacci take ji. Washegari ƙarfe taran safe aka sallamemu maigogul da mota yazo ya ɗebemu zuwa can gidan. Ni dai ina saka ƙafata a gidan illahirin mamaki ya kamani. Dukka ƴan gidanmu da iyalan cicib suna tsakar gida kowa fa da abinda yake yi. Masu karyawa nayi, masu kwalliya nayi, masu wanki nayi. Gaza dai yana gefe shi da Madamcy suna zuba ma su Rahine abinci. Uzairu zuchiyata yana kwance a ɗaki duk jikinshi na cikin ɗakin kanshi ne kawai a tsakar gidan yana waya dan masifa ko jin abinda yake faɗa ba'ayi. Rakiya ta yi gurum da kofin shayi a gabanta ga mummuƙi a hannunta amman fa bata sha. Hauwa dasu Layuza suna zaune suna cin ɗumamen tuwo ga balango mai yawa an watsa akan tuwon. Jin shigowarmu yasa hankalinsu ya dawo garemu Cicib yana tsaye yana shanya a igiya murmushi yake ta sakar ma labbai da ƙyar na haɗiye dariyar tawa kusa da kan Uzairu zuchiyata na rarrafa na zauna. Shima Uzairu zuchiyata sai murƙususun dariya yake yi danma waya yake yi Nan aka shiga yi mun yaya jiki. Layuza ma a taɓe ta tambayi jikina. Raliya tace. "Lolo ashe kuma an ɗaura miki aure, ai ni bansan ma auren ya mutu ba sai da nazo tukunna nake jin wasu labarai a wajen Hauwa ashe har kotu aka shiga" Wallahi kuwa Raliya ke dai ki bari kawai. Yaushe kika zo ina kuma yaran? " Maigogul daya nemi waje ya zauna yace. "Suna ciki yara har bakwai ta tarkato suka tawo a cikin irin wannan ƙadamin. Raliya sai tafi shekara biyar bakwai bata ko leƙo ba. Ko haihuwa tayi sai dai wataran inji a wajen Hauwa. Ita kanta Hauwan fa bata san ta haɓaka yara haka ba. " Hauwa tace. "To wai me akeyi ne da sai dole tazo. Na gabanka ma baka gama dasu ba me kake tsinana musu. Raliya dai kaga yadda dai ta koma kamar ita ta haifeni bani na haifeta ba tsabar muni da lalacewa ta riga da ta dafe ma" Rakiya tace. "Amman ai ko bazai tsinana mata komai ba yana da kyau tazo ta duba ubanta ko? Duk dai lalacewarshi ai ubanta ne. Sai fa Raliya ta shekara biyar kyawawa bata tako tazo ba. In ta tashi zuwa sai dai a ganta raɓe _raɓe da goyo da ciki babu uban abinda take kawowa. " Gaza yayi dariya yace. "Ni da ƙyar ma na ganeta naga ta dawo baƙa. Ko ni nan da nake busa hayaƙi ai ban kaita eh duhu ba. Ma'aru ɗebo mun ruwa in ba Rahine kaji" Ma'aru ya tashi yana dariya ya ɗebo ruwan ya kaima Gaza. "Lolo amshi abinci ko zaki iya ci tuwone harda yajin daddawa" Cewar matar Cixib godiya nayi mata na karɓa. Adama ta haɗa mana shayi a ƙaton kofin silba ni da Labbai muna ci ana hira. "Dama sakina hallirun yayi harma na gama iddata shine dalilin dawowar tawa" Rakiya har da ƙwarewa. Hauwa kuwa salati ta saka. "Ahab ni wallahi nasan za'a rina ai ruwa baya tsami banza. Wato Raliya sakin ki akayi sai kika tuno ai kawalin ubanki yananan babu shakka. To kai Maigogul kaji" Muƙewa yayi ya shiga tukuntuma ashariya. "Shine kika tawo mun da bataliyar yaranki dukka? Lallai baki da hankali taraliya. Hiye daga ke har Hallirun baku da madafa. Shi ya sako ki, ke kin tarkato yara kin tawo dasu. Kinsan Allah sai sun koma. " Sama yace. "Eh gaskiya su koma taya ma za'ayi wannan aikin. Yara bakwai ai da yawa. Lokacin da kike gidan auren nunawa kika yi bakya buƙatar uban kowa yazo miki sabida ke ƴar iska ce ƴar tsakuwa samu ki ƙi dangi. Yanzu data kwaɓe miki shine zaki kwaso yara haka." Raliya tace. "Nifa zan riƙesu haya ce zan kama in zauna dasu kamar dai yadda su Adama suka yi. Nasani nima bazan samu muhalli ba bare su" "Ke ƙarya kike yi. Yarannan fa a raba Halliru ya ɗebi nashi su ragowar ki tarkata ki kaima takarin ubansu inma takarancin zai tafi dasu laba'as amman yau ba gobe ba zaki mayar dasu". Rakiya tayi shewa tare da jan tsaki tayi shigewarta ciki. Nima ɗakin na shiga na kwanta a katifa idanuna a lumshe ina shirin soma bacci wayata ta soma ruri. Da mugun sauri Maigogul ya shigo ai kuwa ya runtumo akan Uzairu zuchiyata daya tattare ƙofa. Da sauri ni da Rakiya muka miƙe. Hannun maigogul na riƙe ya samu ya ɗaga Uzairu zuchiyata da yake ta faman wash ƙafafuwanshi Ga kuma dariya kamar zata halakashi har hawaye yake yi tsabar dariya. Dariya maigogul da Rakiya suma suke yi. "In banda iya shege ya zai zo dokin ƙofa ya kwanta. In yana waya da baturiyarshi baya ji baya gani. Lolo wayarki ce take ruri ko hala Alhaji Zaidu ne. Dan ɗazu ma munyi waya nake sanar mishi an sallamoki. Harma na shigar mishi da wata ƴar buƙata. " Dam gabana ya yanke ya faɗi. A dibibice nace. Amman maigogul gaskiya bai dace ace ka shigar mishi da wata magana ba. Umara ya biya mana ga gyaran gida zai mana dan Allah Maigogul kayi...." Kasa ƙarashewa nayi bana so ko da wasa in faɗa mishi magana mai zafi. Amman ina tsoron kada Alhaji Zaidu yaga kamar bamu da kai" "A_a Lolona ba wani abun mai girma na tambaya ba. Dama abincine nace ko zai siyo kayan abinci ya jibge mana sabida ni ina jinyarki bazan iya fita ba. Wallahi yace ma ya riga da ya siya suna bayan motarshi tun kafinma inyi maganar. " Salati Rakiya ta saka. Niko saida hawaye suka zubo mun ƙirjina sai dokawa yake yi. Shikenan duk abun kunyar da akayi a gabanshi bai isaba Maigogul shikenan ya samu nayi zaici gaba da ɓarar mun da mutuncina. "Amman Maigogul baka kyauta ba gaskiya wannan wacce iriyar rayuwace. Yanzu duk ɗawainiyar da wannan bawan Allahn yayi bai isheka ba. Jibi shayi mai madara yau waye bai sha ba a cikin gidannan. Harfa biredi yau da kuɗin jikinka ka siyo kowa yaci duk da dai Allah kaɗai yasan nawa ka tatsa. " Kuka kawai na fashe dashi da naga suna rikici. Wayarma ya sake kira na kasa ɗauka Maigogul ne yazo yana share mun hawayen da rigarshi. "Yi shiru lolo bazan sake ba. Duk ma abinda nake so sai nazo na tambayeki tukunna. Dama shine yace duk abinda ake buƙata in sanar mishi. Ɗauki wayarki kinji ta Maigogul shalelena" Uzairu zuchiyata mai zaiyi ne in ba dariya ba. Hannun Rakiya Maigogul ya fisga suka fice. Ni kuma na ɗaga wayar da kira na uku ya kusan tsinkewa. Ajjiyar zuchiya naji ya sauke da ƙarfi. Ni kuma illahirin kunya tasa na kasa magana Tagumi Uzairu zuchiyata yayi yana kallona. "Shalelena ina kika shiga ko jikinne hankalina ya tashi sosai. Duk da ɗazunnan muka yi waya da Alhaji Baba yake sanar dani an sallamoku?" Uhm an sallamomu ina tsakar gida ne lokacin daka kirani. " "To ina kwana tunda ni ba zaki gaisheni ba" Kunya ta sake kamani ba shiri na gaisheshi. "Gani a hanya zanje office daga office kai tsaye Dutse na nufo ko akwai abinda kike bukata na ci ko sha in tawo miki dashi? " A_a bana buƙatar komai. Ubangiji Allah ya tsare maka hanya" Wallahi jina nake kamar duk a mafarkine komai yake faruwa ba gaskiya bane. " Da haka mukai sallama na yafito Labbai da Sadiya suka shigo nake labarta musu zuwan Alhaji Zaidu. "To me kike ganin za'a dafa mishi Lolo tunda kinga dole zaki shigo dashi ya huta yaci abinci ko? Ga gid danƙam da al'umma kamar bakin masallaci " Kafin in yi magana Maigogul ya shigo yaji akan duk abinda muke tattaunawa cewa yayi. "Kada ki damu Lolo ni zan miki girkin da zaki tarbeshi dashi. Zan ɗauke ki muje mu yo cefanen komai tunda akwai mota a hannuna kada ki damu" Murmushi kawai nayi. Wallahi inason Maigogul sosai. Hakan kuwa akayi bayan nayi wanka, shima. Ya kintsa Maigogul ya ɗaukeni a gaban mota muka je muka yo cefanenmu yana ta bani labarai muna ta dariya. Kaza muka siyo da mai, kayan miya, ruwan gora, da 5alive, sai taliya leda uku, da su karas, kabeji, latas, da koren tattasai, da jan tattasai, sai madarar gari. Kula na cire kuɗi na siyo mai uku masu kyau farare, na sai kafet na tsakiyar ɗaki sabo fil muka dawo gida ana kiraye_kirayen Sallar azahar. Maigogul na dawowa masallaci ya kuma yo wanka ya zura sabuwar baƙar jallabiya dan s kwalima ya yage ta. Ai kuwa ya aika aka siyo mishi kalanzir ya gwafe ya shiga aikin girki. Ni dai ina kwance a tabarma a waje ina kallon yaran Raliya yadda suke ma gadamurƙi cin hauka ko shaƙesu bayayi ne oho. Raliya kuwa illahirin kunya ta kamata da taga su nake kallo. Wayata ce ta shiga ruri Alhaji Zaidu ke kirana. Ɗagawa nayi da sallama ya amsa mun. "To yanzu zan kamo hanya shalele na tsaya ne ma a danja zan siyo miki gurasar kano mai sikari kike so ko mai gishiri, ko kuwa duka biyun? " Murmushi nayi mishi tare da cewa. Duka biyun. Mai sikarin akwai daɗin ci da shayi sosai " Dariya yayi mun kawai yace. "To shikenan saina iso ko. Ki turo mun adireshin gidan yanzu a waya inna zo ƙofar gidan zan kiraki sai ki yi mun iso. Ki saka mun kaya mai jan kala a jikinshi" Murmusawa muka yi tare dashi. Da haka mukai sallama na ajjiye wayar tawa. Labbai ce ta fito daga cikin ɗakin Rakiya. "Lolo na gyara ɗakin dai an shinfiɗa ƙatuwar taburmai biyu ya rufe ƙasar ɗakin. Kafet ɗin sai na saka shi daga ta bango haka zaifi. Nace tashi in miki tsifa kitson ya tsufa in yaso ko rubon kya saka ki kama gashin. Tashi lolo saifa kin dage sosai zaki samu zuchiyar mijinki a hannunki" Maigogul na kalla dan in tabbatar baya jinmu. Ina baya ji ya duƙufa sai kaji yake soyawa ga gidan Hauwa bata nan Rakiya bata nan. Sauran ƴan matan kowa bayanan. Sama da matarshi wai sunje ganin ɗaki ance an samu a ƙasan layinnan. Kafin dai la'asar Maigogul ya gama komai ya barma Adama ta zuba a kula ta jejjera a ɗaki ragowar kuma ya zubo ma Labbai da Adama dake bacci, ya yafutama su Shafa, Raliya dai da yace bazai bata ba da ƙyar na roƙeshi ya zuba musu yaranta suka daka ma abincin wawa. Ni da Maigogul kuwa a tukunyar muka ci abinci kamar dahuwar kamfani dan daɗi soyayyar taliyar inna zuba a baki kamar kada in dena taunawa maggi yabi taliyar yayi lub dashi. Muna gama ci shi yayi sabon wanka ya sake kaya ya fice. Adama kuma ta gyara wajen. Bayan na idar da Sallah ina gaban mudubi ina shafa kwalli, na saka jar atampata mai tsada sosai, na ɗakko jan ɗankunne da sarƙa sababbi na maƙala. Ɗaurin ture kaga tsiya nayi har ribon ɗina dana tubke gashina ana hangowa, tsayin jelar gashin iya kafaɗata sai dai gashin bashi da cika laƙwam haka yake, gashi duk ma ya zube sabida rashin kwanciyar hankali na kaɗar da gashi sosai. Ina fesa turare yaro ya shigo wai Sabuwa tazo. Ni dai jikina a sanyaye ina haɗa hanya na fita. Nayi mamakin da Alhaji Zaidu bai kira wayata ba ya turo yaro. Ina fita gabana ya yanke ya faɗi. Hmm wai kunsan wa na gani kuwa? Nasan kun ƙosa ko to Madubala na gani cikin shiga irin ta mutunci da kamala gabaki ɗaya kamanninshi sun sauya fiye da tunaninku. Madubala kaine? " Na furta muryata na rawa. Takowa yayi yazo inda nake yake ta murmusawa sai kallon soyayya mai cike da kewa yake yi mun. "Da ace zaki iya taɓa ƙirjina da kinji yadda zuchiyata take watsa jini da sauri _sauri bisa rashin ƙa'ida. Sabuwa ga madubalanki mai so da ƙaunar ganinki a cikin farin ciki. Wanda zai iya bada ranshi fansa a gareki. Nazo in auri abuna duk da lokacin dana fito akace mun tuni kinyi aure lokacin yaranki uku ma. Zafin hakan yasa na koma inda na fito ban sake tako ƙafata na shigo Dutse ba. Naji labarin mutuwar aurenki, naji labarin aminiyarki dake auren mijinki na da. Sabuwa a cikin idanun Ƴar Shuwa babu komai sai ƙiyayyarki gayatan. Banzo gareki bane har saida na tabbatar kin gama iddarki. Gani nazo miki a matsayin nutsattsen mutum mahaddacin Qur'ani mai halastacciyar sana'a Sabuwata" Tunda ya matso kusa dani daf ya soma maganarshi nake hawaye nice harda shessheƙa. Ɗago kan da zanyi muka haɗa idanu da Alhaji Zaidu tsayuwar motarshi kenan idanunshi a kanmu ƙur. Gabanane ya tattake ya faɗi Banyi aune ba naji tsumma a fuskata Madubala na share mun hawayena. Mrs bukhari.
Gobe Alhamis ba Posting haka ma Juma'a, asabar ma dan girman Allah kada kuyi ƙorafi babu Posting sai ranar lahadi. Wallahi abubbuwane a gabana inata haɗa kayan turarukan wuta na masu adashene asabar nake son in sallami kowa to aimun wannan alfarmar nagode💪🏼 [10/4, 10:29 PM] +234 810 593 2041: MRS BUKHARI 8