Kenza eBookz

Idan kaya ya gaji book book 4 - Chapter 8

Idan kaya ya gaji book book 4 - Chapter 8

Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 8: Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 8. A hankali Alhaji Zaidu ya sakko a cikin motarshi. Yana saye cikin farar…

3,966 words

A hankali Alhaji Zaidu ya sakko a cikin motarshi. Yana saye cikin farar shadda ɗinkin malum_ malum, zannar dake kanshi ta matuƙar dace da surfanin gaban malum_ malum ɗin. Tsintsiyar hannunshi saye da baƙin agogon fata wanda yayi lub akan gargasar dake lulluɓe da fatar hannun nashi. Baƙin haf koba ne a ƙafarshi kamala da natija su suka sake ƙawatashi. Yafi Babangida kyau da zati sosai, fari Babangida zai nuna mishi da tsayi sabida su su Babangida tsabar tsayi har dorone da mazan gidan nasu. Sallama yayi mana yana kallon ƙwayar idanuna illahirin kunya a wannan lokacin rasa yaya zanyi nayi. Wallahi Allah ba zaku gane bane, ban tsaya domin wani abun ba, kuma jin saukar tsumma kawai nayi a fuskata ba tare dana ankara ba. Wallahi Allah jikina har rawa yake yi a wannan lokacin, a tunaninku zanso wani abun ya ɓata ma Alhaji Zaidunku raine? . Da naga ya miƙa ma Madubala hannu sai nayi zuruf na shige gida gabana nata aikin faɗuwa. Shiru nayi a ɗaki idanuna a runtse inajin wani irin tashin hankali maras musaltuwa domin bansan wacce iyakar fassara zai yi mun ba. Muryar Alhaji Zaidu naji a tsakar gida suna gaisawa da Labbai tana mishi iso. Ita ta soma shigowa ya biyo bayanta da sauri nayi ƙasa da kaina kawai. Gefe ya samu ya zauna suka gaisa da Labbai muryarshi babu daɗi gaskiya. "Anty a nan gidan kuke zaune naga ai gidan kamar ba'a gama gininshi bama. Sannan ai gidan yayi muku kaɗan ma" "E gidan Abokin Maigogul ne. Shine yace muzo mu zauna tukunna" Shiru yayi can naji yana waya yace. "Alhaji Isa gani a dutse wanne gida zan samu da zaka bani ko na haya kona siyarwa mai kyau mai girma" Idanuna na lumshe hawaye suka wanke mun kwalliyata tas har ji nake numfashina na ɗaukewa. "To shikenan ka tura mun lambar kiya teka ɗin sai ya zazzagaya damu muga wajen nagode sai na jika" Wayar ya kashe yace da Labbai. "Ku shirya zamu je ku ga gida, inaga gara a sai gida kawai ku shiga sabida ita Shalele ta samu ta tare a ɗakinta zanfi samun nutsuwa da kwanciyar hankali. Alhaji Baba baya gidane? " "E ya fita, amman Babu damuwa akwai wanmu Garzali ko dashi sai mu je babu damuwa. Allah ya saka da alkhairi Ubangiji Allah ya zaunar daku lafiya" Murmushi kawai yayi ba tare daya amsa ba. Yace. "Amman babu damuwa kuna ganin ba sai an kira Alhaji Baba ba kuwa ko in kirashi ne?" Ni dai bama gane mai suke cewa nake yi ba. Naga dai Labbai ta fita ɗakin ya rage daga ni sai shi tsit babu kalma in ɗago na kasa. Amman inajin idanunshi na yawo a jikina hawaye sai ɗiga yake yi daga idanuna yana sauka kan cinyata. Labbai da Gaza ne suka katse mana shirun. "Cau cau Babban Yaya. Cau Sabuwa mai sabon aiki a lafiya dai ango eh mijin Amarya ba. Fari mai farin aniya, an buga dakai an barka, cau cau na gidana" Hannu Alhaji Zaidu ya miƙo ma Gaza. Carab Gaza ya riƙe suka gaisa. "Kafa yi haƙuri ranar kaga na tada tarzoma ko? A dai yi haƙuri damu wallahi abubbuwanne sai a hankali." Waje ya samu yana fuskantarshi. "Babu komai Yaya Garzali" "Kutumar dumadu yaya Garzali fa kace Alhaji? Ai kirani Gaza kawai uban Rahine" Dariya ya ɗanyi yace. "To Baban Rahine dama gidane nake son muje a gani, inaga yanzu ba saina shiga harkar gini ba. To akwai abokina harkarshi siyar da gidaje da fulotaine yace akwai gidaje biyu, ɗayan na sama ne, ɗayan na ƙasane shine nake son muje a duba in yayi sai a siya kawai. To Alhaji Baba gashi bayanan" "Allah dai ya Alhaji a lafiya dai gabanka da bayanka Allah ya kareka. Ni dama layincan ya isheni wallahi sosai fa. Batun Maigogul tureshi gefe nine Maigogul yau babban wa uba, muna da babban wa amman eh shi ba lafiyayye bane ma shi yasa kaji nace haka. Ga Labbai ga Lolo, ga ka, gani ai sai muje kawai" "Toh to shikenan babu damuwa sai mu je? " Da sauri nace. Baka ci abincin ba? " Ƙur yayi mun da idanunshi yana karantar yanayina ɓacin ran da yake ciki bai ɓoyu ba. Mikewa yayi yace. "Baban Rahine muje kaji daga can ma zan wuce ne. Akwai tsaraba da kayan abinci a mota bari in shigo dashi" "Ahh kafi haka ai. Sai dai muje ka buɗe in kwaso musu. Ni da zaku ɗaukeni gadi ma wallahi dana huta an tallafi rayuwata Allah nake gaya maka rayuwarnan yinta fa kawai muke yi wallahi wallahi babu daɗi gashi babu wanda zai ja mutum a jiki. Tsoron irinmu fa ake ji a cikin al'umma alhalin suna gani muka dawo haka" Dariya kawai yayi ya riƙe hannunshi suka fita. Suna fita nace. Labbai wai kinsan da wa Alhaji Zaidu yazo ya sameni a tsaye? " "A_a, atsaye kuma dama bashi ya aiko ai kiranki ba? " Bashi bane. Madubala fa na gani ina fita. Allah sarki madubala yazo a ƙurarren lokacin da bani da tsimi bare dabara. Amman da ace yazone kafin aurena da Alhaji da babu makawa..... " Yawu na haɗiye tare da ragowar maganar jin Gaza na rakaɗa mana kira. A sanyaye dukkanmu muka fito Wallahi Madubala na zaune a kan dakalin gefen gidan. Haka na wuce babu damar waige, Gaza da Labbai dai suna tsaye tare dashi. Bayan mota na buɗe na shiga. Ina ɗago kaina muka haɗa ta jikin mudubin motar lumshe idanun yayi yace. "Kinyi kyau sosai damma kin ɓata kwalliyar da hawaye Shalelen mijinta" Gaza ne ya buɗe gaba ya shiga, Labbai ta buɗe baya ta shiga yaja motar muka wuce. "To Baban Rahine sana'ar me kake yi da kake neman aikin gadi kai kuwa? Aikin gadi aina dattijaine ba irinku masu jini a jika ba majiya ƙarfi.? Gaza yace. "Wallahi ni dai in zan samu inaso. Me gida wallahi talaka na shan wahala fa kawai ku ba sani kuke yi bane kawai. Kaga ina da iyali ga juna biyu a jikinta, gasu Rahine da suke ƙarƙashin kulawata yanzu haka wani muzurun aka bani wancan daka gani ranar daka zo ya gudu ina tafe can wajen karɓoshi Labbai ta kirani shine na samu na duƙo fa. " Murmushi yayi yace. "Allah yasa mu dace. Zanga abinda dai ya dace ai sai a duba Gaza amman banda gadi akwai aiyuka da yawa da za'a iya nema maka. Amman kayi karatu?" "Wai karatu? Babu eh ɓoye_ɓoye ni da kake gani bana ƙarya wallahi ni ban taɓa yin makaranta ba arabi eh ko boko." "Babu damuwa zan nema maka aikin daya dace dakai banda gadi." "To godiya nake yi wallahi Babban Yaya eh ina sake godiya fa" Suna ta hirarsu mu dai munyi ƙus a bayan mota. "Shi wannan matashin dake ƙofar gida ɗan uwanku ne Baban Rahine? " Shiru Gaza yayi yana nazari can yace. "Maƙotanmu ne haka na can gidan da muka taso. Abokan ƙanne mazan gidanmu ne dai Haka. Labbai ai madubala eh kamar abokin wannan mata mazan ne ko Uzairu zuchiyata ko eh? Sannan yana shiga ko ina a gidanmu ma" Ajjiyar zuchiya ɓoyayya na sauke a hankali. Yana kallona ta madubin gaba, ko a fuska banga halamun ya yadda da maganar Gaza ba. Kai kawai ya gyaɗa bai kuma magana ba. Gidaje biyu ya kaimu a mabambantan unguwanni. Ɗaya gidan sama ne mai hawa biyu ɗakunan huɗu ne a ciki ko wanne da falo babba a tsakiya. Akwai banɗaki a falo, ɗakuna biyu suma suna da bayangidunsu, biyunne babu. Sai ɗakuna falle_falle a tsakar gida guda biyu da shago babba ɗaya a waje sai ɗakin maigadi. Gida na biyu kuma ƙaramine mai ɗauke da ciki da falo da bayan gida guda biyu, sai ɗaki ɗaya na maza shikenan sai tsakar gida babba da shuke shuke. Gaza Alhaji ya tambaya adadin yawanmu ya faɗa mishi. "Ok inaga gidan saman zaifi dai in yaso ƙila ɗakunan wajen kayi amfani dasu, ɗayan gidan ko haya kwa saka, sai ayi mishi kwaskwarima" Waya ya matsa yayi, ya dawo suka sake keɓewa da kiya tekan gidan sun jima suna maganganu kafin ya kwashemu ya mayar damu gida. Kuɗi ya zaro ya ba Labbai nata ya ba Gaza nashi. "Cau cau wallahi Allah. Maƙiyanka fadawanka, futu futu mugun icce baka ciba ka turniƙe da hayaƙi, kashin burburi ƙawanya_ƙawanya eh wallahi, sikari bakai farin banza ba. Fari mai farar aniya ango a wajen Sabuwa mai sabon aiki. Gaza nake uban Rahine mijin Madamcy wanda yaimun in yayimi ƙwanyar abu ta kazan. Wuya a gida wuya a lagos wuya a manunfashi, wuya a ogere wahihuhuhu🗡" Wucewa yayi yana tumɓele a hanya harya shige kana na sauke ajjiyar zuchiya. Shiru motar tayi na wasu lokuta can dai nace. Kayi haƙuri na fito a tunanina kaine sh.... " "Ya isa Shalele dawo gaba muyi magana to" A hankali na ɓelle murfin motar na dawo gaba na ɗan kalleshi kaɗan sai yayi murmushinsu na manya. "Shalele kenan. Waye shi Madubalan? Kuma gaskiya nake son sani kada kimun ƙarya dan hakan kasa in kasa yadda dake kwata_kwata. Ya da aure a kanki wani namijin zaki bari ya dinga share miki hawaye. Ni yaya zanji a zuchiyata kinyi tunanin hakan, ko kuma sabida auren kawai aka ɗaura kina gida shi yasa baki sallami zawarawanki ba? Da Alhaji Baba yana nan nasan bazai taɓa barinki ki fito ba. Ni da nake kano wanne tunanin kike son ki ɗaura mun dan Allah fa Shalele uhm?, kinsan yadda nake sonki kuwa? " Duka waɗannan maganganun a cikin tsari da kwarewa wajen iya daidaitacciyar hausa yake yinta. Babu hauragiya balle ingausa cikin maganarshi, kuma babu amon fishi mai zafi na rashin mallakar kai. Kayi haƙuri. Ina zaune yaro yace ana kirana a waje kaji dalilin fitowar tawa sai naga bakai bane?. Sannan shi ɗin tsohon saurayinane tun kafin in yi aure Wallahi rabona dashi yayi shekaru ashirin a ƙalla. " "To kukan yazo a ƙurarren lokaci kike yi yake rarrashinki, ko kuwa kukan tsohuwar soyayyarshi ce ta saka ki kukan uhm? " Wannan karon cikin sigar tuhuma yayi maganar da kaurin muryar kishi ba kamar ta ɗazu ba. Da sauri nayi maganar dan gudun kaucema zargi mai zurfi. A_a wallahi daga cikin wanda ka lissafo babu ɗaya daga ciki har ga Allah" "To me yasa kike kuka a gabanshi uhm faɗa mun ba'ayin kuka babu dalili. Ko ki faɗamun dalili ko in baki dalilin kukan naki ni" Jingina yayi a jikin kujerar motar ya cire hular kanshi tare da lumshe idanunshi. Sabida nace mai ina mahaifiyarshi ne yace mun ta rasu shine ya saka ni hawaye duba da irin sanayyar dake tsakani. " Wallahi ji kawai nayi na furta hakan. Ajjiyar zuchiya ya sauke tare da buɗe idanunshi ya saukesu a kaina. Da irin sigar daya kalleni wallahi babu mahalukin daya taɓa yi mun irin wannan kallon. "Shikenan na yadda dake kuma na huce Shalelena, kiyi haƙuri kina kuka na kasa rarrashinki. Yanzu dai zanje masallaci kinga magriba tayi anata kiraye_kirayen sallah" To amman in kayi sallar zaka ci abinci kafin ka wuce ko? " Tausasa muryarshi yayi yace. "Kina son inci ne Shalelena? Bayan kin dagulamun lissafina uhm? " A sanyayen nima nace. Inaso sosai ma, kuma inason inyi maka godiya mai tarin yawa duk da wallahi babu abinda ma zan iya ce maka" Hawayene suka zubo mun da gudu. Matsowa yayi har ina shaƙar nunfashinshi yasa babban ɗan yatsanshi yana ɗauke mun hawayen. "Bana son kuka. Kinga keba ishasshiyar Lafiya bace dake ba. Shalele ni abinda nake so a gareki soyayyace kawai kiyi ta mun adda'ar kafin Allah ya ɗauki rayuwata Allah yasa in ga jinina in dai kasancewarshi a doron duniya alkhairine ga rayuwata da kuma al, ummar duniya." Sai naji tausayinshi sosai ya rufarma zuchiyata. "Ga Alhaji Baba can bari in fito mu gaisa sai muje masallaci" Juyawa nayi na dubi ƙofar gida na hango Maigogul suna tafe da Rakiya kayi nayi ita kam buhun kayi nayinta ne a kanta. Kafin mu fito ta shige gida, maigogul kuwa wajenmu ya nufo. Uhm muna isowa ya rungume Alhaji Zaidu cikin annashuwa da nuna kulawa. Shi kuwa wallahi har ƙasa yaso zubewa ya gaishe da maigogul da sauri Maigogul ya riƙoshi. "Wane mutum Alhaji dan Allah kada ka sake illahirin kunya ai saita kamani " "Ai Alhaji Baba ya zamemun dole in durkusa maka tunda yanzu mahaifi kake a gareni nima." "To to nagode. Ke lolo shige gida ƴar albarka mu zamu je masallaci" Wucewa nayi na tsaya a ƙofar gida ina kallon su maigogul, ko wanne cikin shigar alfarma hannayensu sarƙe dana juna tamkar abokai. Murmushi nayi nace. Allah sarki maigogul ɗina Ubangiji ya hore mun ya kuma dafa mun a kanka in sake maka wannan sana'ar taka Allah ameen. Shigewa nayi ciki a gurguje nayi alwala nayi sallah. Gidan a cike kamar biki an dafa shinkafa miya suke yi ana zazzaune a tsakar gida anata hira da Dariya. Can muka jiyo muryar maigogul da Alhaji Zaidu dake gaishe dasu Rakiya. Suna ta zubo mishi godiyar tsaraba. Shi kaɗai ya shigo ciki ya zauna yana ƙarema ɗakin kallo ga duhu babu wuta sam bama a jawota ba sam. Ina kan zuba mishi abinci muka jiyo maigogul ya shigo har yana tuntuɓe Gaza ya sanar dashi komai sai godiya yake yi. Maigogul harda hawaye ganin hawaye na kwarara a guraben idanunshi sai nima na fashe da kukan murna. A haka Rakiya dasu Hauwa dasu Adama suka shigo akai mishi rubdugu na godiya da addu'O'in alkhairi suka fita. "Alhaji kaci abincin ka ƙoshi. Lolo ki ƙara mishi yaci da kyau nan gidane. Ni zan jiraka a waje eh" Ya ƙarashe maganar yana washe baki, a haka dai ya fita. "Shalele ki yi haƙuri kukan ya isa haka. Zuba mun abinci inci da kyau" Ƙara mishi nayi na zuba mishi salak ɗin a gefe. Lomar farko naga yana girgiza kanshi yana dubana. "Wannan abinci ba dai daɗi ba. Gaskiya kin ƙware sosai a girki sai kace wacce tayi karatun girki" Murmushi kawai nayi mishi. Ai kuwa yaci abinci sosai nan kuma na sake yi mishi godiya sosai. "Ba wannan ba yaushe ne tariyar taki Shalele yana da kyau in sani sabida in sanar ma mata da magabata. Ƙanin mahaifinane ma kaɗai yasan an ɗaura auren. Ko Hajiya bata sani ba. " Kaina na sunne nace. To da naso ace a haɗa bikin tarewar dana Uzairu zuchiyata, akwai Labbai yata itama duk lokacin ne aka tsayar na bikin nasu sai ayi taron tare. " "Wata nawa kenan? " Uku ne ba yawa." Murmushi yayi yace. "In dai hakan kike so hakan za ayi in sha Allah amman ban yadda ki sake fita ba sai da izinina. To ko zaki haɗo lefenki a Dubai ne daga Umara sai kawai ki haɗo ba sai na ba kowa wahala ba? " A_a babu damuwa bama saina haɗa ba. " "Uhm uhm ki dai ce to ɗin ke zaki fi iya soyo duk abinda kike da buƙata. In ma bakya buƙatar kayan ai ba zaki rasa abun siye a Dubai ɗin ba. Sai mu dawo batun biki akwai wani taron event (sha'ani) da kike ganin zakiyi ne? " A_a ni bani da ƙawaye sai ƴan gidanmu inaga babu wani sha'ani sai dai kuma ta ɓangarenka in akwai" "To mu zamu yi dinna ( bikin dare) ranar da aka kaiki sabida akwai abokan kasuwancina da zasu halarta in sha Allah. To matakin karatunki kuma fa uhm? " Kafin in bada amsa wayarshi ta soma ruri Matarshi ce ke kiranshi. Bai kai ga ɗagawa ba Maigogul ya shiga kwaɗa mun kira. Da sauri na miƙe ko shima yafi samun damar sakewa yayi wayarshi. Yana zaune akan turmi yana raba abincin gidan. "Ko zaici shinkafa da miya ne? Amman Hauwa ce tayi fa kinsan hannunta bai nuna ba har gobe? " A_a ya ƙoshi wancan ma bai gama cinyewa ba ya ƙoshi. " "To to kice mishi ya fito muje masallaci. " Juyawa nayi na koma ciki daidai ya gama wayar harma ya tashi tsaye. "Lokacin Sallah Alhaji Baba ya tunasar damu ko? To bari muje masallaci in muka dawo bama saina shigo ba zan mu ƙarashe maganar a mota in samu in wuce duk da bana ko son in yi nesa dake" Murmushi nayi mishi kawai. Wani kallo yayi mun masu fassarori. Saida suka fita ne na fito tsakar gida na samesu anata duba kayayyakin tsaraba da kayan abinci da Alhaji Zaidu ya jibge mana ga gurasa kanta hilimi guda rakiya ta juye a bokiti. Cikin su Adama na shige na saka hannu a kwanon Uzairu zuchiyata dake zaune yana ta latsa waya yana dariya. "Uhm lolo wallahi rigar aure Felisha ta tutturomun ala dole wai in zaɓa mata wacce zata sa. Shine tun ɗazu nake ta dubawa sai yanzu muka tsayar da matsaya. Uhm lolo Gaza yake shafa mana gidan sama zamu koma kai abunnan ni akaima an mugun fitar dani kunya. Ga shawara kinga mijinnan naki? Ƙanƙameshi zakiyi ram kada ki sake wata ɓaraka ta ɓullo ta ɓangarenki sannan kada ki bar Maigogul ya hau wani buzu gara ya soki naciral" Labbai tace. "Ai na faɗa ma Madubala kinyi aure yayi haƙuri. Ya ban tausayi sosai jikinshi har rawa yake yi. Na dai mai tayin ko Sadiya, ko Aisha yace a_a kuma yace yana miki fatan alkhairi sannan kiyi haƙuri baisan kinyi aure ba" Har cikin ƙoƙon raina na tausayama Madubala kuma na sake jaddadawa da ace yazo kafin a ɗaura aurena tabbas da shi zan aura babu kwana_ kwana amman ƙaddara ta riga fata. Sallar isha na gabatar ina zaune ina sabunta kwalliyata nice harda sake kaya zafi yasa saida na watsa ruwa a gurguje na saka riga da siket na materiyal mai taushi haka. Jane jikin materiyal ɗin sai afulawoyi masu ruwan zuma. Ina kan Shafa janbaki Maigogul ya shigo. "Maza lolo ba'a barin manyan mutane suna jira maza. Rakiya nan da sati guda zamu tattare yanamu_yanamu mu koma sabon gida. Gobe Gaza zai kaimu mu gano wajen muma" Rakiya tace. "Haihuwa mai rana. Yau dai sanadin lolo Allah yasa mun bar wancan ƙaddararren layin na magulmata. Ƙawayen Hauwa da suke munafurci tare kaga gulma ta ƙare. Da kuma yadda ake korema yarannan zawarawa da gulma da tsigudidi ba" Hauwa zata yi magana Maigogul ya ɗaga mata hannu. "A_a ya isa haka kada ku hautsina mana gida muna da baƙo dan Allah." Wucewa nayi sum _sum na fice Layuza na tadda a ƙofar gida wani mai mashin yazo wajenta. Muna haɗa idanu ta sakar mun tsaki ni kuma nayi mata murmushi tunda dama kowa abinda yake dashi shi zai bayar. Murfin motar na ɓalle na shiga da sallama. A hankali cikin ƙasa_ ƙasa da murya ya amsa mun yana jingine a kujerar motar sai lumshe idandunanshi yake yi. Hannunshi ya miƙo mun yana lumshe idanu. A hankali na ɗora hannuna cikin tafin hannunshi. Sai naga ya kulle idanunshi tare da matse hannayena ya ɗan jima a haka kafin ya buɗe idanun yana ɗan murza mun saman hannuna da babban ɗan yatsanshi. Gabaki ɗaya wani irin abune da ban taɓa jin irinshi ba naji yana tsirgamun. "Shalele anya zan iya jimurin jiran wata ukunnan kuwa. Kinga wannan kwalliyar taki da shi kanshi taushin yadin yanda ya sukurkutamun tunani kuwa? Kinyi kyau sosai Amaryar Zaid" Mirmushi nayi ɗan taƙaitacce ba mai yawa ba sabida yadda yake wasa da babban yatsanshi a saman fatar hannuna abun na shiga. Matso da fuskarshi yayi daf da tawa muka shaƙi numfashin juna. "Kin tabbatar zaki iya wata ukun da kika ɗiba mana kuwa, bakya gudun mu sha wahala uhm? " Ya ƙarashe maganar yana so ala tilas sai mun haɗa idanu. A hankali na ɗago nayi mishi fari da ido irin nawa na da can da nake yima samarin bariki in sukurkuta dukkannin kuzarinsu. Ai babu shirin ya kwantar da kanshi lub a saman ƙirjina yana ja da sauke numfashi a hankali. Shiru ya biyo baya na wasu lokuta masu tsayin da ba zamu iya tantancewa ba. Da ƙyar ya ɗago daga jikina muka duba agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunshi tare. "Kwanan dutse ya ganni Shalele. Zaki bini hotel ne ko zaki shiga gida? " Shiru nayi ina nazari bana son binshi domin akwai buƙatar in nutsu in gyara jikina irin gyaran da ban taɓa yin irinshi ba. A hankali cikin kasalalliyar muryar dana tabbatar zan jefashi cikin shauƙin tunanina a ɗakin hotel a yayin daya kasance shi kaɗai nace. Gida zan shiga, ai bazan iya binka ba waneni? Na karashe ina kaɗa idanu. Hancina ya lakace cikin murya mai haɗe da numfashi nannauya yace. "Shikenan Shalele zan tafi tun kafin in kasa tuƙa kaina zuwa makwancina. Gobe da safe zan shigo in karya in yaso sai in ɗauki Alhaji Baba ma muje wancan gidan duk su gani kafin in wuce ko? Sannan ki sanar dashi zancan zuwa Dubai ɗin kafin in shigo gobe" To in sha Allah" Daga haka mukai sallama harna fito shima naga ya fito a cikin motar ya buɗe bayan motar akwatin ajjiye kaya na mota ya zaro wata ƙatuwar leda da wata ƙaramar jakar kwali. "Muje in kai ki har zaure kafin in tafi" A jere muka iso har ƙofar gida kana ya miƙo mun ledojin hannunshi. "Wannan babbar ta Alhaji Baba ce. Ita wannan jakar taki ce. Sai da safe" Juyawa yayi da sauri ya faɗa mota ya tayar da'ita. Murmushi nayi inajina tamkar sabuwar mutum ce ni, tabb soyayya duniyace. Da farin ciki na shiga gidan. Yanda na barsu a haka na taddasu maigogul na kan turmi yana basu labari anata dariya. Kallona yayi yamun murmushi ya yafitoni da hannu na nufeshi ina jin daɗi sosai. "Ya tafi Lolona Amman dai ba Kano ya kama hanya ya tafi ba ko? " E yace sai gobe da safe in yazo yaci abinci sai ya kaiku kuga gidan kafin ya wuce. Wannan ledar yace in baka" Dariya yayi ya cabke ledar ya buɗa wasu irin shaddajine waganbari asalin manyan guda biyu da takalmi da agogon fata komai na cikin ledar mai bala'in tsada ne sosai. "Hiye Lolo duk wannan kaɓakin arzikin duk nawa ne. Lallai Lolo yanzu ne kika yi aure. Ke dake da Uzairu zuchiyata yanzu ne zaku nuna mini kun haifu yanzune asalin kuttun farin jini da Sa'a ya fashe a gidannan" Da Rakiya da Hauwa tare sukai dogon tsaki. "Aikin banza" Cewar Rakiya dake dokin ƙofa tana cin gurasa da shayi. Ni da maigogul muka kwashe da Dariya a tare. "Lolo ai kin gani tun daga gida kin soma fuskantar ƙabulabe ko? " Na gani Maigogul dama yace in sanar maka daga Umara zamu wuce Dubai mu siyo kayan akwatina" Rakiya tace. "Agen duk Maigogul ɗin? Lallai kin cika tabbatacciya Lolo yayi kyau Allah ya taimaka" Rakiya bafa ni nace ba shi yace haka" "Ba shakka sabida kin nuna fifikon Maigogul sama da nawa ba. Ba gashi ko tsaraba shi kaɗai ya yoma ba ni ina zaune gaho" Zan yi magana Adama tace. "Haba Rakiya banda muhalli daya siya mana har wani abun muke nema kuma. Sannan mutuminnan fa ko maigogul yayi ma ai ke mai jin daɗi ce" "Batta Adama ta yi yadda take so. Lolo dai ɗiyata ce, kuma kinsan da wuya ina tare da'ita bare da daɗi. Kina zaune duk shekara zata kaini aikin hajji ba dai dani kike zancan ba? Ke lolo wuce ki shiga ciki abunki, ni ɗinkima zan kai a darennan dama bikine damu. Ku kulle gidan dan bazan kwana a gidan ba" Da wannan ledar ya fice fuu. Rakiya tafi awa biyu cur tana zage_zage saida na dunƙula mata kuɗi da takalmi wanda Alhaji Zaidu ya siyo mun sannan tayi shiru harda washe bakinta sai lokacin na yi ajjiyar zuchiya tare da girgiza kaina kawai. Mrs Bukhari

Son so💪🏼 [10/4, 10:29 PM] +234 810 593 2041: MRS BUKHARI 9

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull