Idan kaya ya gaji book book 4 - Chapter 9
Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 9: Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 9. Cikin dare ba sai bacci yace baima sanni ba. Ina ganin su Adama a kwance…
3,811 words
Cikin dare ba sai bacci yace baima sanni ba. Ina ganin su Adama a kwance sunata baccinsu hankali kwance. Amman ni sai juyi kawai nake yi tunanuka biyu su suka ci ƙarfin zuchiyaya. Tunani na farko shine tunanin Alhaji Zaidu da nake jinshi tamkar a duniyar mafarki, ko kuma duniyar tatsuniyoyi, ko hikayoyi. Haƙiƙa na yaba, nayi ma Allah godiya daya dubeni ya jefo mun Alhaji Zaidu cikin rayuwata baban soyayya kenan. Allah shi ya tsara komai bamu da tsumi bare dabara shi yasa abubbuwan suke tafiya cike da almara. Cikin ƙanƙanin lokaci haɗuwar da bata fi sau uku zuwa huɗu ba. Mune muka mallaki gida, kuma wai yau ni Sabuwa Alhaji Zaidu ya biya ma Umara, lefena a Dubai zan haɗo shi. In banda Allah mai iko da saukar ƙudura wa zaimun wannan? Babu shi, a cikin jikina ina jin cewar da Auren Alhaji Zaidu zanyi amfani in gyara ma Maigogul Rayuwarshi, shine jigo nayi imanin idan ya shiryu abubbuwa da yawa na gidanmu zasu iya sauyawa. Muskutawa nayi na tashi zaune na jingina ina hararo al'amura ina fatan su kasance kamar yadda nake kallon hotunansu a idan zuchiyata. Ɗayan sashen na zuchiyata kuma tunanin a irin ƙurarren lokacin da Madubala yazo nake yi. Madubala ba irin namijin da za'ace an mance dashi bane sam wallahi domin masoyine mai sadaukarwa ga masoyiyarshi. Sai dai kash yaxo a ƙurarren lokacin mai ikon saukar da Ƙudura baiyi shi zan aura ba. Amman nayi farin cikin ganinshi cike da kamala tabbas. Rarrafawa nayi na fita na ɗauro alwala. Ɗakin namu ma a mugun cike yake bazan samu wajen Sallah ba. Gaza da Uzairu zuchiyata na kalla suna gefe a kwance a tabarma, su Ma'aru, dasu Sama duk sun kwakkwanta a tsakar gidan,murmushi nayi. Allah sarki ƴan uwa abun wuya. Duk lalacewar ɗayanmu baya sawa mu gujeshi tafiyarmu tare take in sha Allah. " Ɗankwalin materiyal ɗina na shinfiɗa na ta da kabbarar sallah. Raka'a biyu nayi na zauna na dinga godiya ga Allah bisa turo mun Alhaji Zaidu cikin rayuwata da yayi Domin Allah ni dai na roƙi Allah yasa ɗa ko Ƴarshi a jikina suke kunga laifina? Bani da laifi babu macen da bata son kuɗi, kuma babu macen da bata son mijin alfahari da nunawa, kuma babu macen da ba zata so ta auri Alhaji ta haihu dashi ba. Ina shafa adda'ata ana kiran assalatu. Idanu Gaza ya buɗe sakamakon Rahine data hau jikinshi tana shinshinar Uzairu zuchiyata. "Ni Uzairu zuchiyata na shiga uku dan masifa da bala'i mutum yana kwance ana shinshinarshi kamar mushe Gaza wai wannan karyar taka lafiya kuwa, nine bata gane ba dan ubanta ko menene? " Gaza ya harareshi kafin yayi magana yaran Rahine uku suma suka iso wajen suka kewaye Gaza. "Kai mata maza malalaci mai zama cikin mata hattara maza bisa kanka wallahi. Wuya a hannun maza dan abu ta kazanka" Wani ihu da Gaza ya danna da sauri Uzairu zuchiyata ya matsa. Ni da Gaza muka tuntsure da Dariya harda su Sama da Sama "Lolo kinga wannan abokin naki akwai tsoro eh mijin baturiya ba eh bari in yi eh alwala in tafi masallaci eh wallahi" Miƙewa yayi sukai alwala suka wuce masallaci tare suna tafe suna zolayar juna tsakanin Gaza da Uzairu zuchiyata, su Sama kam wucewarsu suka yi. Ina jin Gaza na cewa zai shaƙe Uzairu zuchiyata. Kai na girgiza ina kallonsu nan da wani shekaru a matsayin waɗanda bamu kaɗai ba al'umma ma zatai alfahari dasu in sha Allah. Da karfin guiwa da wani kwanciyar hankali da nutsuwa nayi sallah. Kana na tattashi Ƴan ɗakinmu suka firfito dasu Rita da Madamcy, Ƴan ɗakin Hauwa ma haka. Gaza na shigowa ya dama madara ya kira Magenshi daya saka mai Uzairu. "Zo Uzairu kasha madara maza" Dariya nayi nace. Wuu Gaza wannan muzuru zai yi mugun son mata, mata har gida zasu dinga biyoshi" Kowa sai da yayi dariya Uzairu zuchiyata shi da Labbai harda birgima dama sune sarakan dariyar mugunta a gidanmu. Shigowar Maigogul da Cicib faram_faram ita ta dakatar da hirar. Ɗaki Maigogul ya shige yana muzurai ko me ya faru oho dai. Sai da muka shiga muka tarar dashi jikinshi yayi zafi kau ya lulluɓa da bargo. Duk muka rufu a kanshi anata mishi sannu. Tutturesu nayi na zauna a kusa da kanshi ina shafa gashin kanshi ina mishi sannu. A hankali har bacci yayi gaba dashi, duk sai suka watse ni kuma madadin in fita saina zauna dirshan na ƙura mishi idanu yana ta bacci. Murmushi nayi mishi ina sake godema Allah daya ƙaddara muka fito da tsatsan maigogul. Hmm zaku yi mamaki jin hakan? Ai duk lalacewar iyaye ɗa dole ya sosu ko da gidan karuwai maigogul yake rayuwa inason kayana balle yana dawowa gida. Kuma wallahi yana da shiga rai dole a soshi ne ba zaku gane ba. "Ke dan ubanki wuce ki je ki samu su Labbai ki haɗa ma mijinki kayan karin kumallo. Ya zaki tusashi gaba haka. Kika san dame sukai gamo? Basu da aiki sai zuwa hotel rayuwar baƙin ciki an girma ba'a san an girma ba. " Jiki a mace na fice yadda Rakiya take a fusacennan nasan tsab saita mare ni ji take kamar du mu biyun ta dira a wuyanmu fa. Biredi da soyayyan ƙwai da shayi na tanadar ma Alhaji sai gurasa da su labbai sukai banɗashenta. Ƙarfe tara nayi wanka fes na share tsakar gidan tas. Har zuwa lokacin maigogul baccinshi yake yi. Dole da Alhaji yazo sai Ɗakin Hauwa muka shiga dashi bayan ya gaisa dasu Rakiya. Yana shan shayi yana ƙarema tsakiyar idanuna kallo. "Yaya darenki ya kasance Shalele? Naga bacci sosai a tattare dake me ya kawo bashin bacci uhm?" Kafin in yi magana sai ga maigogul kamar an jefo shi ni dai banji ko yayi sallama ba ya shigo. "Alhaji ashe ka shigo har ka soma karyawa. Ke Lolo abinda kika kawo mishi kenan meye wani shayi da ƙoyi me yasa ba'a tasheni ba? " "Ai babu komai Alhaji Baba. Ina kwana? " Da sauri Maigogul ya bashi hannu shima a kunyace ya miƙo suka gaisa. Maigogul yaita sokiburutsu da ɗakko labarai marasa kai da ma'ana. Shi kuwa yayi tsit sai ji yake yi. Yana so ya ɗauko zancan kawalcinshi. Ganin nayi kamar zanyi kuka sai yayi wannan dariyar ya miƙe. "Bari naje in jiraku a waje in ka kammala maje can gidan ko uhm Lolona ke kinci abincin ne? " Kai kawai na ɗaga mishi halamun eh sabida ya fice. Fita yayi yana ta dariya. "Ina jinki bani labarin daren to?' Yawun baƙin ciki na haɗiye na ƙirƙiro murmushin bogi na ɗaura kan fuskata. To bazai wuce mamakin yadda aurena dakai ya kasance ba gaskiya." "Me kika fi tunawa dangane dani? " Murmushinka, domin shine abu na farko daya soma shiga tsakaninmu" Kai ya jijjiga cikin gamsuwa yace dani. "Ni abinda yafi tsaya mun a raina shine ƙamshinki da taushi da ɗumin hannunki, da ƙyar nayi bacci. Shalelena na riga na kamu shin ba za'a sassauto da wannan tarewar ta kasance kuna dawowa ki tare ba? In fa ba haka ba zaki dinga sawo inta ziyartar Dutse ba tare dana shirya ba" Kaina na sauke ƙasa ina murmushi, shima murmushin yayimun, yasa yatsanshi ɗan manuniya ya ɗago haɓata dashi muka zuba ma juna idanu. Wallahi wani irin kallo mai taushi yake yi mun, ga wani mayunwacin saƙo da yake isarmun ta ƙwayar idanunshi. Lumshe idanu muka yi a tare, ya jawo numfashi daga huhunshi tare da fesar da iskar ta baki da hanci bai ɗaya. Cikin muryar raɗa yace. "Ki shirya sosai duk ranar dana miki riƙon alawar yara mai rabamu sai Allah" A hankali cikin irin salonshi nace. Babu ma bai rabamu alawarka saika shanyeta tas in sha Allah" Murmushi mai sauki yayi mun. Ya jingina da bangon ɗakin Hauwa yana ta kallona ƙasa_ƙasa. Ni kaina da ƙyar nake numfashi Allah Kunsan wallahi ji nake ban taɓa soyayyaba ma, kalaman, da yanayin da nake ji, da shi kanshi mijin da tazarar fa kamar sama da ƙasa ne tsakanin wannan Auren da auren Babangida, da samarin da nayi a baya. Wallahi sai nake jin duk ba'a iya soyayya ba ga gindin maganin na'iso dai yanzu. "Yaranki suna da labarin kinyi aure, ko basa zuwa inda kike ne?." Ya kawar mana da wannan yanayi da muke ciki dan gudun yin abun kunya. Kallonshi nayi da kyau nace mishi. Basu sani ba gaskiya ina jiran ƙarshen wata in sun zo in sanar musu ne" "To amman sun zo sun dubaki a asibiti ne? " Cikin kallon tuhuma nace mishi. Me ya kawo wannan tambayoyin? " Dariya yayi wacce na kasa gane wacce iriyace. Saida ya kurɓi shayi ya haɗiye kafin yayi mun kallon ƙasa_ƙasa yace. "Bani amsar tukunna" Ajjiyar zuchiya na sauke nace. Sun zo, harma suke faɗa mun ita babbar an amshi sadakinta zata auri yaron yan mahaifin nata" Ƙur yayi mun da idanunshi. "Babansu ne kenan ya kawosu ko dai su suka zo da kansu tunda ba yara bane? " Shi ya kawosu. Sabida basa zuwa ko'ina sai dashi in ba makaranta ba." Gyaɗa kanshi yayi tare da sauke ajjiyar zuchiya yace. "To yaushe zaki gabatar musu dani a matsayin Babansu, izuwa yanzu ya kamata su san da zamana ko dai baki shirya hakan ba? " Shiru nayi ina nazari dan ni har ga Allah na fi son sai lokacin tarewar tawa a fasa maganar kowa yaji. "Baki ce komai ba Shalelena uhm" Na jiyo muryarshi. Da naso sai lokacin tarewar tawa in tazo saji labarin sabida ba'a sanarma kowa ba tukunna" Murmushin dai ya kuma yi tare da cewa. "To shikenan Allah ya nuna mana lokacin, ya kamata suma ace dasu za'ayi miki Rakiya ai ko? " Kai kawai na ɗaga halamun E. Da haka mukaita taɓa hirar, a gaba ya tusani saida naci gurasarnan da kanshi ya haɗa mun shayi ya miƙomun tattali iya tattali fa. Haka Gaza ya leƙo wai in zuba mishi madara a shayi da kanshi ya karɓa ya zuba mishi. Ya bani kuɗi masu yawa yace in ajjiye a hannuna. Yana gamawa muka fito kusan mu goma ashe Maigogul ma da mota a hannunshi. Sai na ɗanji sanyi a raina. Su Rakiya dasu Layuza da Raliya da cicib amotar su Maigogul suka shiga. Ni kuma da Adama da Gaza da Uzairu zuchiyata muka shiga motar Alhaji Labbai dasu Sadiya suna gida da ragowar sauran dai. Duka gidajen biyun saida ya kaisu duk aka zagaya aka shiga lungu da saƙo na gidan dai aka gaggani. Maigogul ina ganinshi yana sharar hawaye Alhaji Zaidu na bashi kalma. Kiya teka ne ya bada takadda maigogul ya saka hannu, Gaza ma ya saka, sauran saka hannun in an gama za'a danƙa mana takaddun gidan a hannunmu, nan da kwana huɗu zamu ma iya tarewa kafinnan masu fenti sun gama fentin cikin gidan da wajen gidan duka ma. Daga nan ya mayar damu gida kuma. A mota mukai sallama bayan ya gama narkani da salon soyayyarshi, dani dashi da ƙyar muka rabu wallahi, ina nima fa bazan iya wannan wata ukun ba wallahi tab Ya kama hanyar Kano, su maigogul ma kama hanyar mayarma da masu mota suka yi shi da ango naku na Labbai:.
BABANGIDA:. A zaune Ƴar shuwa take tana ta zuba mita da ƙunƙunni Babangida ya shigo ya nemi waje ya zauna, ga miyar sutu a gabanta da nama da wani biredi mai laushi. "Aisha daga yau sai yau wallahi in na kuma jin labarin kin saka Ramatu aiki a gidannan ranki zaiyi mummunan ɓaci sosai ni dai na faɗa miki sabida ba aurenta kike yi ba, kuma kamar yadda kike da juna biyu itama juna biyun gareta. Sannan jiya naga nama cikin leda a ƙofar ɗakinki shima a cikin kuɗin ribarki ne koko yaya? " A zuchiyarta sai kutuntumo ashar take yi. A zahiri kuma ta haɗe ranta tamau tace. "Nasan bazai wuce Sumayya mai shegen munafurcinnan bace ta faɗa maka ba. Ni ba saka Ramatu aiki nake yi ba. Dafa kanta take zuwa karɓa tace zata yi mun. Zanƙi bata ne sabida Allah fa? " "Zaki ƙi bata mana itama ba sai ki barta taji da nata ba? " "Hmmm" Kawai tace shi kuma yayi shiru yana aiyana abubuwa da yawa a ranshi dangane da'ita. "To kayi haƙuri Jannaty. Nama kuma ragon da Mama ke kiwatawa ne ya kasa shine ta yanka ta aiko mun da rabi tace koma nawa ne in kawo" Ƙur yayi mata yace. "Dama tana kiwone ban sani ba? " "Tana yi sosai ma har kaji tana kiwonsu" "Uhm amman ba'a cikin gidanku ba ko, dan naga gidan babu sararin da za'ayi kiwo a ciki. Kuma in a ciki ne zan gani ko? " Ɗan zare idanu tayi, tayi shiru tana nazari. "A maƙota take yin kiwon nata sabida gidanmu babu waje akwai maƙotanmu suna kiwo shine ta roƙesu ta zuba nata" Haka dole ya yarda badan ya gamsu ba amman yaya zaiyi tunda baisan inda zaije yaji gaskiyar batun ba. "Mardiyya an kowa sadakinta ba da jimawa ba za'ayi bikin nata dan ko shekara ba zai yi ba" A razane ta dubeshi har tana ƙwarewa tace. "Da Sauban ɗin kuma za'a ɗaura wai? " Miƙewa yayi saida yakai bakin ƙofa yace. "E dashi za'ayi. Ai Baba Malam baya magana biyu kema shaidace. Ni na fita saina dawo" Dama jiranshi take yi. Yana saka ƙafa daya fice Ƴar shuwa ta saɓa mayafinta ita da Da Jami suka fice. Jami ta nufi hotel wajen baƙonta ƴar shuwa kuma ta nufi gidan Kulu suka rankaya wajen bokan data ce zata kaita. Bayan boka ya gama jin bayaninsu tsab ya buga ƙasa ya dubeta yayi dariya. "Ai Hajiya ga ɗaukakanan tana biye dake tamkar inuwarki. Zaki yi arziki ki buga rayuwar da kike mafarkin samunta. Amman akwai tashin hankali, ruɗu, da damuwa sosai, ga gargada a hanyar. Amman dai hanyar arzikice. Cikin murna ƴar shuwa tace. " To duk wani abu mara kyau a hanyar malam a kawar mum dashi. Akwai wani taro da zan halarta a Abuja ina ji a jikina daga nan ɗaukakata take da asali. Matsalata ɗaya mijina asiri baya kamashi har mata boka da siriki boka yayi amman haka suka buga suka barshi" Ta kwashe dai tabarin yadda take son ayi mata kab ta labartama wannan boka. "Uhmmm ita Sabuwan ai ga ubanta nan yanata muku turen aiki akan lallai sai Sabuwa ta dawo ɗakinta ko kuma ke su rabaki da mijin naki kowa ya rasa. Ita kuma mai aure Mardiyya ai babu haske a auren ƙunci, kuka, tozarci na hango a cikin zaman. Sai dai yaron zai iya zame mata gata sosai dan yana sonta kuma da ɗan abun hannunsh" "Tabbas yana da gidanshi ya gina, kuma da ƴar motarshi. Ni Malam ba nitsattsen miji nake son ta aura bairin Sauban ɗan malamai ba. So nake ta auri ɗan iska, ita kanta fa uwar ɗan bata so sabida yarinyar bata hanyar aure ma aka sameta ba. Malam za'a iya wargaza auren? " Ƙasa ya zazzana, ya share ya kuma zanawa yace. "Kai akwai rabo a tsakaninsu. Matsawar aka hana auren kota halin ƙaƙane sai wannan rabon sun samar dashi. Kinga tarihi zai maimaita kanshi kenan" Murmushi Ƴar shuwa tayi taji wani sanyi a ranta. "A hana auren, ita yarinyar taje ta kwaso abun kunyar haka nafi so. Ɗan iska ya aureta shine daidai da gidan uwarta." Dariya bokan yayi yace. "Wannan zamu iya. Amman shi ubanne dole sai mun duba wasu kwanaki da zamu yi amfani dasu dan ganin an mallakeshi. Amman fa shi ba zaki iya mallakarshi kita juyashi ba. Sai kina yi kina sabunta aiki akanshi kusan duk sati. A lokacin da yake halin rashin tsarkine kaɗai zamu iya aikin ya kwanta har gari ya waye da najasa a jikinshi to aikin zaici yaci gaba da aiki na ɗan lokaci kaɗan. " Murmushi tayi tabbas ashe akwai yiyuwar zuwanta Abuja taro dan ko Babangida yaƙi Allah sai ya kwana da najasa tayi wannan alƙawarin. Domin akan zuwa Abuja ta kwammaci ko saki ɗayane yayi mata dan wallahi sai taje kwana biyu dai sai taje anyi komai da'ita. Tana jin yadda suke maganar yanda taron zai kasance da irin manyan matan da zasu je taron har daga wasu ƙasashe ba'a maganar ƴan gari gari irinsu ma. An turo da ankon taron ma tuni Samirah ta siya mata ta ba telanta dake can Abujan ya ɗinka musu tare. Nan suka narka ma boka kuɗi ya haɗota da wasu turaruka da hayaƙin da zata je ɗakin Sabuwa tayi da wanda zata zuba musu a randar ruwan shansu. Ai kuwa a gurguje tana dawowa ta wuce ɓarayin su Sabuwa bayan ta gama waige waigenta taga babu mai ganinta ta shige ta aiwatar da duk abinda boka ya umarceta dayinshi. Ajjiyar zuchiyata ta sauke da taga ta fito daga lungun babu wanda ya ganta ma. Haka dai wunin ranar ya kasance. Da daddare sai ga Sauban yazo taɗi a ƙofar gida suka tsaya basu fi minti ashirin ba Babangida da kanshi ya leƙo yace dasu ya isa haka. A gabanshi mardiyya ta shige, shima Sauban ya shige motarshi yana ta washare bakinshi. Mardiyya dai ta soma zuwa jami'a cikin yaddar Ubangiji. Babangida lokaci ya ware sosai yaita mata nasihu masu ratsa zukata. Aminu kuma shima yayi sauka, Aɗɗa'u kanshi saura kaɗan ya kammala haddarshi. Aɗɗa'u da malama ne kaɗai a wannan lokacin suke zuwa boko su Yaya Aminu shima an girma. Malam ya ɗaukeshi ya sanyashi a gurbin saida littattafai na makaranta. Lamarin daya gigita yaran Malam kenan sabida duk waɗanda suke da wannan kujerar amintattun malam ne yardaddunshi na haƙiƙa. Abun mamaki sai ace Aminu aka ba, kuma Malam yana ta faɗi tashin ganin shekara mai zuwa shima an sama mishi gurbin karatu a Jami'a. Aminun dai shi ya karɓe Ajin maza magidanta da Babangida ke koyarwa a da. Wannan ranar da ƙyar Babangida ya iya dena kuka sabida tsantsar farin ciki. Ya yadda da gaske duk duniya babu mai ƙaunarshi sama da Baba Malam, dan a wannan lokacin Malama Babba ita kuka ta saka da Babangida yaje yana sanar da'ita halin da ake ciki. Madadin ta nuna jin daɗinta sai take cewa yaron wawo ya kamata a baiwa wannan kujera a ranar ne Babangida ya dubeta yace.. "Malama ba Sabuwa kaɗai kike ƙi ba har dani Ɗanki. In har zaki ƙi Aminu to nima kin ƙini. In na fahimci dalilinki na ƙin mardiyya to menene dalilinki na ƙin Aminu Malama? Shin mun kasa rungumar ƙaddara mu faɗama kanmu gaskiya? Ni ina ganin munfi Sabuwa da danginta laifi. Kuma sun fimu ƙoƙari. Ina jin ciwo in kina nuna ƙin su Aminu a idona" Miƙewa yayi zai fita ta kirayi sunanshi ya tsaya. "Ni kake cema bana sonka Sabida Sabuwa. Ni dana rabu da aurena sabida in kareka? Ni dana mallaka maka dukiyata kaƙi karɓa? Ni dana fifitaka fiye da sauran yaran? Yau ni Sabida Aminu kake faɗa mun bana sonka dan kawai kaga Allah ya jarabceni da sonka? " Babangida yaso ya fahimtar da Malama Babba sai ta nuna ita ina itace a bisa gaskiya. Haka dole ya rabu da'ita cikinsu zukatansu babu wanda yayi daɗi A haka Babangida ya koma gida ruhinshi na mishi ƙaiƙayi. Ƴar shuwa tana zaune zaman zirshan tana shan nono ta gama shirinta tsab gobe sai Abuja, duk da ta tambayi zata je biki Maiduguri bai bata amsa ba. Yau take son ta aiwatar da aikin da boka ya sanyata tayi ta daddage ta daka sakwara da miyar kifi ta baɗe tuwon da asiri harda ƙwayar bature ta saka bacci sabida so take tabbas ya kwana cikin rashin tsarki. Cikin sa'a kuwa ta samu yaci sakwarar da yawan gaske duk da a cikin damuwa yake mai yawan gaske. "Baban Faty muje ka watsa ruwa naga kamar bacci kake ji ko? " Ta faɗa cike da kissa. "Bacci na soma ji, bari in yo wankan sai in kwanta kaina ciwo yake yi mini sosai" Yana shiga banɗakin ta daka tsallen murna. "Dani kake zancan wallahi, da sannu ma zan samu mallaka sadidan." Ɗaki ta shige ta saka rigar bacci sabuwa dal ja mai raga. Ai kuwa Babangida na fitowa banɗaki ta hilaceshi tuni ya ba da kayinshi bori ya hau. Ta bashi wuya sosai ranar, shi kuma ya amfana da gyaran jikin da tayi ciki da waje sosai. Da haka bacci mai matuƙar nauyi na magani yai awon gaba dashi luuu. Asuba ta gari nima Badiat nayi nan
Mrs Bukhari
Wallahi masoyiya maidoki sabida ke da ummu inteesar yau nayi wannan Posting ɗin. Kaina ma ciwo yake yi [10/4, 10:29 PM] +234 810 593 2041: MRS BUKHARI 10
*(Inaso zanyi tsokaci kaɗan kuma daga haka in sha Allah bazan sake cewa komai a game da mutanen da suke ganin kamar ƙazantar gidansu Sabuwa tayi yawa bazai taɓa zama gaskiya ba ƙirƙirarren labarine kawai ƙarya nake yi, da masu cewa na ƙaƙƙara dan yayi armashi, da masu tuhumata, masu cewa hankali bazai ɗauka ba, da masu tambayoyi domin ganin sun ƙureni ko wani abun* *abu ɗaya nake so ku sani akwai gidaje birjik da yafi na gidansu lolo ƙazanta wallahil ƙudrat wasu ma a cikin unguwanninku suke, shin in ba ke ƙawar ƴar gidan bace, ko dangin gidan, ko ɗaya daga cikin ƴaƴan ire_iren gidan bace ke shin zaki iya sanin haƙiƙanin abinda yake tafiyane. Kuna tunanin da ba dan Sabuwace ta bani labarinnan ba kawai ƙila a unguwarmu suke nasan ƴan iska ne zan iya sanin ya suke rayuwar cikin gidansu da ɗakinsu ne da musabbin abinda ya sasu a wannan rayuwar?* *bazan sani ba face iyakar abinda na gani da idanuna kamar yadda kuma zaku iya gani, tsakaninki da Allah a labarinnan kika taɓa jin kab gida babu nagari, baki taɓaji a labarai uban da yayi ma ƴar cikinshi ciki ta haihu ba, baki taɓa jin labarin uban dake kwanciya da bazawarar ƴarshi ba, baki taɓa jin wa ya lalata ƙanwarshi ba, uwa ta nemi ƴar cikinta da maɗigo ke baki taɓa ji ba? Waɗannan labaran basu fi rayuwar gidansu lolo muni ba?* *Yana da kyau mu zauna muyi tsam mu nazarci wannan labarin da manufar rubutashi, darasin dake ciki ayi amfani dashi kusakuran da muka tsinta muyi ƙoƙarin kiyayewa gudun kada mu gurɓata tarbiyyar ƴaƴanmu* *nasan gidan da yafi nasu Sabuwa muni kab yaran gidan sun haifi yaran shege, uban ɗan iska uwar ƴar iska, Naga gidan da uwar ita ke tura samarin yaranta su siyo mata sigari suje su siyo suna kuka, bata dena shan sigari ba har saida ta bar duniyar baki ɗaya, ga ƙazanta iri da kala a duniya ana bugawa bakwa bibiyar abinda duniya take ciki ne? ya muke abu kamar ba a duniya muke rayuwa ba. Labarinnan na gaskene na rage abubuwa da yawa, in kunso ku yadda, in kunso ku ɗaukeshi a yadda tunaninku ya baku almuhim shine mu ɗauki darrusan dake ciki Allah yasa mu dace son so💪🏼)*
Sabuwa:.