Idan kaya ya gaji book book 4 - Chapter 10
Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 10: Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 10. Kwana huɗu da tafiyar Alhaji Zaidu muka tare a sabon gidanmu, ɗakin…
4,245 words
Kwana huɗu da tafiyar Alhaji Zaidu muka tare a sabon gidanmu, ɗakin Rakiya ne a sama ɗakin Hauwa kuma yana ƙasa. Setin kujeru da gado na saima Rakiya dama na sai kafet ranar da Alhaji Zaid zai zo. Hauwa ma naga ta jera kayan ɗakin layuza. Gaza yana ɗakin dake tsakar gida, ɗayan ɗakin kuma Gaza da kanshi yace Sama su dawo shi da Rita, dama suna ta fama da neman gidan haya ba'a samu ba har zuwa lokacin. Ɗaki ɗaya a falon Rakiya muka ɗauka, su Uzairu zuchiyata suma suka ɗauki Ɗaya, mazagin ma ya dawo yana gida duk ya rame ya fice fit a hayyacinshi. Ɗayan ɗakin ɗakin gadon Rakiya ne, ɗaki ɗayan Maigogul naga a ciki ya jibge bataliyar kayanshi, ko daya fita sai gashi da sib harda katifa sumbuƙa da labulenshi to a cikin kuɗi yake dumu_ dumu, tunda har nera dubu biyar yaba Rakiya wai ayi cefane ayi abincin tarewa. Ai wannan rana munyi mamaki fiye da tunani wallahi. Haka da daddare muka zauna a babban falonmu ga wutar lantarki tanwar kota ina. Ga abinci tire uku manya munyi da'ira. Gida ya cika kowa yananan ko wacce tana ɗakin mahaifiyarta kab matan cikin gidanmu zawarawane banda Adama da take ba a sake ba ba'a ɗaure ba sai Rahama. Wannan mummunan tarihi yana sosamun zuchiyata sosai. Mardiyyace ta kirani da daddare take sanar dani zasu zo sati mai zuwa, sannan ga fa muƙami da Baba Malam ya baiwa Aminu. Ai tsulum na koma ɗakinmu na kwanta a katifa ina musu adda'a da nasiha ina hawaye. Suna gama wayar dani dana duba lokaci naga ƙarfe takwas ne saina kira Baba Malam. Da kamalarshi ta asali ya ɗaga muka gaggaisa na yi mishi godiya bisa muƙamin daya ba Aminu, harma da makarantar mardiyya daya sama mata. "Sabuwa babu komai ai. Ni fatana yaranki su kasance daban a cikin zuriyarmu dama taku zuriyar, zan basu dukkan kariyar data dace kema sai kici gaba dayi musu nasiha. Dama ko baki kirani ba ina da niyyar zan ɗakko Bashiru muzo Sabuwa. Sabida na yadda da nagartarshi in dai zaki iya daurewa ki amince mishi ku sasanta kanku ki aureshi. Ƴan ɗakin ƙarama suna da dattaku shi Bashiru na tattauna dashi harma ya amince mun Ƙarama ma ta saka albarka" Wasu hawayenne suka sake wanke mini fuskata tas nama rasa abinda zance ban taɓa ganin mai irin kirkin Baba Malam ba, kazalika ban taɓa ganin adali irinshi ba. "Sabuwa kina tare dani? " E Baba Malam ina tare dakai. Dama nima naso inzo makaranta in sanar dakai an ɗaura mun Aure da wani bawan Allah amman ban tare ba tukunna" Kunyace ta kamani dan tabbas ban kyauta ba da ban sanar dashi da wuri ba har ga Allah. "Sabuwa shine Maigogul bai sanar dani ba in ke kina jin nauyi na" Dake ba'ayi taro ba, ni ina gadon Asibiti ma bani da lafiya aka ɗaura auren. Tarewar kuma zanyi nanda kwanaki tamanin da biyar" Ko a murya ya nuna zunzurutun farin cikinshi sosai. Sannan yace in sha Allah inna tare a ɗakin mijina zai zo har gidan." "Sannan kizo ki sameni a makaranta kafin lokacin tarewar, zan kuma turo Ramadan da ɗan abinda ya samu in bikin yazo. Yaran amman basu Sani ba ko? Da malama mutuniyata zata faɗa mun" A sanyaye nace. Basu sani ba dama nace sai in zan tare ɗin tukunna" "E yayi kyau, kuma zansa a turosu ayi duk wani sha'ani dasu, kuma atafi dasu har can Kano ɗin. " Godiya nayi ta yi mishi da haka mukai sallama. Ina jiyo Uzairu zuchiyata shi da Labbai sunata zuba dariya. Murmushi nayi dana fito naga kowa a cikin farin ciki. Damuwowin dake danƙare a ƙirazanmu ma da sannu Allah zai wanke mana tas in sha Allah saina kawo haske da canji a cikin wannan zuriya mai cike da haɗin kai. Hannu na saka muka ci gaba da cin abincin. "Ya haka eh Uzairu zuchiyata kana cin na gabana fa" Cewar Gaza daya ke zazzare ma Uzairu zuchiyata idanu. Rakiya da take ci a tiren su Adama tace. "Haka kuka iya babu fus sai son cin abinci. Ga gida cike da yara amman yaran iska marasa amfani" Illahirin ɗakin duk sai ya ɗauki shiru na kusan minti biyar babu wanda ya iya cewa uffan. Maganar Rakiya ta daki zukatan ƴan ɗakin kowanne cikinmu tunaninshi da ban. "Da kun sauke nauyin da Allah ya ɗaura muku. Kun tsaya kai da fata kun mana tarbiyya eh ko da baku saka mu a makaranta ba eh wallahi da yanzu eh muke riƙe da gidannan. Rakiya munfa san eh abinda muke yi kada ki zata mu ƴan iska ne eh. Wallahi duk ku kuka ruguzamu eh kuka tarwatsamu. Eh jiya fa eh Adama na haɗu da Sani abokina wanda muka taso tare. Yaranshi bakwai ya sakosu a mota ga matarshi kyakkyawa a gaban mota zasu je eh wai shan askirim fa eh. Ya sha malum_malum yadda eh kuka san Maigogul. To dan Allah eh karatu yayi? Baima taɓa zaman aji ba eh kamar ni eh sana'ar kafinta yake yi amman ya samu rufin asiri. Mu tun muna shekara bakwai_takwas aka sallamama eh duniya mu, me ake tunani akanmu to? Eh ai ba mu muka haifi kanmu ba ba kuma haka aka tsara muzo muyi ba eh wallahi nifa ba tsoronku eh nake yi ba. Wannan eh wacce ma eh irin magana ce rabin raina? " Miƙewa yayi tsaye. "Ke Madamcy tashi mu tafi" Gaza na kalla yana ta huci yana kumbura hanci. Rakiya kuwa sai zage_zage take yi. Sai muka ga shigowar Maigogul. "Toh yaya tun daga get muke jiyo hayaniyarku lafiya kuwa? " Maigogul muka kalla ga wasu ƴan iskan kilakai har su huɗu ya kawo su zasu kwana ba yaga yalwar waje ba. "Su kuma waɗannan kilakan daga ina dan abu ta kazan ubansu? ". Cewar Gaza dake tsaye dama. Magazin ya miƙe ya zaro wuƙa a ƙugu. " Baƙinane da kuke tambaya yau kuka saba ganinsu. Ke magajiya ga can ɗakina ku shiga kuyi kwanciyarku" "Su shiga ina wai? Ashe lahira zatai baƙo wallahi in basu fice ba dani da magazin zamu saka kansu gabas. Kaga yadda na yanka tumakan malam Habu? Wallahi haka zan yankasu fursunace dai nan kuwa gidane eh wallahi eh wuya a tafa wuya a legas, wuya a akumadu, wuya a ogere, ku dan abu ta kazan.. Ku bar gidannan" Wuƙa ya zaro ya doki wuƙar hannun Magazin Matannan suka ba da ƙara a guje suka ruga har ɗayar na yar da jakarta. Basu ƙyalesu ba sai da suka kaisu har titi Maigogul kuwa har suka dawo yana tsaye da jakar da baƙin suka yar yana zage_zage. "To mata dai babu wacce zamu sake bari ta eh kwana anan ka kama musu eh lojin tunda wannan ƙaddararriyar sana'ar kaƙi barinta eh ko dan yaranka mata. Ni ina barin gidannan zanyi kafin eh zuchiyata ta faɗi ta fashe ko kuma wataran in danne eh kanka da fulo ace na kashe ubana. Eh wallahi tsab zan iya danna ma fulo ka mutu kowa ya huta" Haba Gaza Maigogul ɗin kake faɗa ma haka? Hakan bafa daidai bane" Na faɗa murya a sanyaye. Ajjiyar zuchiya maigogul ya sauke ya yafutoni nazo na tsaya a kusa dashi baice mun komai ba. Gaza yaita ɗiban albarka kafin ya finciki matarshi suka sauka ƙasa. Sama ma sauƙa ƙasa suka yi da matarshi. Uzairu zuchiyata dasu Adama sai cin abincinsu suke yi. "Lolo bari inje in samesu sai gobe zan dawo kinji?" Dan Allah maigogul kada ka kwana acan ka dawo komai dare" Rakiya tace. "Uwar kilbibin tsiya da kanzagi wata uwar zai miki inya dawo ɗin ko kuwa soyayyar taku ce ta motsa shi da baya iya kashe miki ko sisin kwabonshi amman kin fifitashi sama dani uwarki" Rakiya kema bakya kashe mana ko sisi, saima tsine mana da kike yi akan abu kaɗan. Dan Allah ku dinga sararama kanku. Sabuwar unguwa muka dawo mu daure dan Allah kada mu raba abun faɗen da zai sa mu koma mujiyoyi aci gaba da kore ma matan gidan Zawarawa. Maigogul kaje abunka sunata jiranka" "Allah yayi miki albarka lolo. Ke Rakiya baƙin cikinki shi zai halakaki in kikai wasa wallahi bazan taɓa yadda lolo ta biya miki Umara ba bare aikin Hajji. Nasan duk sabida wannan duk kike wannan abun. Ke kiyi Hauwa tayi sabida baku da hankali ki bini a hankali wallahi in ba haka ba babu ke babu zuwa Umara a gaba, sai insa a biya ma Hauwa inga iyakarki. Wallahi ba dan lolo ba yau da saina miki duka a cikin gidannan meye wannan hassada haka" Fuu ya fice bagazan_bagazan da jakar mata. Saida ya kai dokin ƙofar da zata sadashi da ƙafar bene yace. "Abb Labbai Cicib na tsakar gida yana jiranki yazo zance" Tana lashe hannu tace. "To Maigogul kace mishi ina zuwa" Ficewa yayi yana ta mita. Rakiyan ma ba daina mitar tayi ba, mu kuwa ɗakinsu Uzairu zuchiyata muka shige muka ci gaba da hirarmu, Uzairu zuchiyata yana kwance a kujerar falo yana wayar tashi ta masifa daya saba. Nima Alhaji Zaidu ne ya kirani na fito zan koma ɗakinmu shine na ganshi yana ta dariya yana zubo kalami sai juyi yake yi cike da shauƙin soyayya. Masauki nayi ma kaina a katifarmu na ɗaga wayar da sallama" "Kema amincin Allah ya tabbata a gareki. Allah ya amintar dake Shalelena. Yau baki kirani kince zaki kwanta ba kamar dai yadda kika saba, ko kuwa santin sabon gidanne ya hana a tuno dani uhm Shalelena? Ni ko ina nan tunaninki ya addabeni uhm " Ya ƙarashe maganar yana murmusawa. A_a yau banzo kwanciyar da wuri bane sabida mun sha aiki sosai wallahi. Ni dai inata jaddada godiyata a gareka Ubangiji Allah ya biyaka da aljannah maɗaukakiya" "Shalele ke bakya gajiya da godiya ne? Nifa ba sabida ke nayi wannan abun ba sila ce kawai ke. To ya shirye_shiryen tarewa me da me kike shiryawa? Dan nifa so nake a yi tariyarnan kowa ma ya huta uhm Shalelena " Dariya nayi mishi kawai shirin kam ai inata yi. Magungunan mata cikin bakko Maigogul ya kawo nagartattu tafiyayyu daga Maiduguri. Daya dure a gabana saiya haɗa ni da matar a wayarshi taimun bayanin magungunan dallah _dallah. Illahirin mamaki ranar saida ya kashe kowa. Ga magungunan gaskiya suna da kyau harda sabulun amare ina wanka dashi jikina yayi santsi sosai. Murmushi naji ya kuma yi ƙasa_ ƙasa yace. "Sirrine abun bazan ji ba kenan ko Shalelen mijinta da Alhaji Baba ƙanwar maza kuma. Ina Gaza mutunina? " Dariya nayi nace. Gaza bai daɗe da sauka ba shi da matarshi tare duk muka ci abinci. " "Alhaji Baba dai ɗazu muka yi waya dashi yace mun suna wani mitin ne zai kirani. Daya gama muka yi waya mun jima sosai muna magana" Ai illahirin jikina sai yayi sanyi nayi shiru kamar ruwa ya cinye ni sai dafe ƙirjina da yake ta dokawa nayi. "Shalelena" Ya kira sunan a mugun tausashe. Na'am" Na amsa a kasalance. "Wai meye sunan da kika saka mun na soyayya ya kamata in sani ko? " Murmushin dole nayi nace. Yana sebe a cikin wayata sai dai kuwa in kazo ka duba da kanka" Mun daɗe muna waya da dai naga dare yayi nace. Wai kai kaɗai kake kwana a ɗakinka ne? " Dariya yayi sosai kafin ya bani amsata. "Lokaci zuwa lokaci Hajiya takance tana buƙatar ta kwana a ɗakinta. Musamman in ta gaji sosai dake tana da shagonta da wani sa'in take zama a ciki duk da bata fiye zaman ba. Amman in tana buƙatar za'a jera kayayyaki a shago a gabanta ake komai. To yau ɗinma hakance ta faru a shago ta wuni cur ta gaji. Kema jira nake ki shigo sai mu tattauna batun kasuwanci dake sai ki zauna kiyi tunanin wacce sana'ar kike so, in kuma babu sai in tattauna da da Hajiya muga me zai yiwu sai ayi ko? " Jinjina kaina nayi na riƙe haɓata, sai nayi mishi murmushi ba tare da nace uffan ba. Haka dai mukaita hirarmu cike da soyayya da tattalin juna, nima tuni na kwale nake nuna mishi iyawata har su Adama suka daddawo Labbai ma ta shigo da shofin cikin leda fara. Jin hayaniyarsu ne yasa mukai sallama ba dan zukatanmu sun so ba. Ina sauke wayata sai ga Uzairu zuchiyata da Magazin sun shigo sunyi tsaye. "Labbai wai duk wannan kajin Cicib ɗinne ya kawo har da jus ni Uzairu zuchiyata tsohon ɗan daudu da soyayya" Labbai tace. "Ni kaina abun wani iri yake yi mun wai kunga soyayyar da yake nuna mun kuwa? Ga tesa_tesan soyayya iri da kala" Ranar gaskiya munyi dariya sosai Uzairu zuchiyata haka yaita riƙe ciki yana burgima yana wayyo Allahna tsabar mugunta. Haka dai aka rarraba kaji da jus ɗinnan a tire kowa ya kwashi rabonshi, Rakiya ma aka miƙa mata nata. Yau munyi wani irin kwanan farin ciki wanda baki bazai iya faɗeba balle alƙalami ya rubuta muku ku fahimta.
Babangida:. Bashi ya farka a bacci ba sai takwas na safe lokacin Ƴar shuwa tana Kitchen tana tuyar ƙwai suna waya da Sameerah taji yana kwaɗa mata kira. Da sauri ta kashe wayar ta shiga ciki. Yana tsaye dafe da kanshi baccinma ba sakinshi yayi ba. "Garin yaya kika barni naita bacci baki tasheni ba kina kallon lokaci kuwa takwas fa? " "Baban Fati kenan ai nayi maka tashin duniya tashinne bakai ba kuma naji jikinka da zafi. " "Amman ko ruwa ba kya shafamun ba zaki barni inta bacci" Tsaki yayi ya wuce banɗaki ya ɗauro alwala yazo ya gabatar da sallah bai tashi akan daddumar ba da duk baccin da yake ji yana zaune yana azkar ta shigo mishi da tiren abincin karyawarshi ta dure gabanshi kana ta zauna. "Ni na gama shiryawa kai nake jira dama in tafi banso na kai takwas a gida ba" Ɗagowa yayi ya zuba mata idanunshi bai tanka ba sabida tsabaragen bacci bakinshi har rawa yake yi. "Kina da kuɗin mota ne dama sannan kwana nawa zaki yi? " Ajjiyar zuchiya ta sauke har wani dariyace ta suɓuce mata kafin tace. "Ina da na mota sai dai na shan ruwa a hanya ko? Sannan kwana biyu zanyi babu yawa ko in ƙara ne sabida kaine dama nace biyun Maiduguri da nisa" "Yaran fa dasu zaki tafi ne? " "A_a yara kam zan barsu a hannun Jami tunda bazan daɗe ba. " Kai kawai ya jijjiga ya tashi da ƙyar ya haye gado. Ita kuma ta turo akwatinta suka fito ita da yaran Taci wani lashi mai matuƙar tsada, takalmi da jakanta ma masu tsadane suna daga cikin kayan da Sameerah ta bata ɗinkakku. A bakin titi taga motar Samira, shigewa tayi nan suka niƙi hanya zuwa yamma sai gasu a garin Abuja. Zangon baƙi (Hotel) Sameerah ta kama musu, a dogon falon da ake zuwa a biya kuɗi Sameerah ta haɗu da wata Hajiya tana tare da yarinya ƙarama da bata wuce shekaru ashirin ba. Ashe ita wannan Hajiya sune manyan memba na wannan ƙungiya ta mata masu maɗigo. Sameera da girmamawa sosai ta gaisheta. Ganin hakanne yasa Ƴar shuwa itama tayi saurin rusunawa ta gaisheta. Ai kuwa da fara'a ta amsa har tana taɓa mata kafaɗarta tana mata wani irin kallo. "Hajiya Sameerah yarinya kika sake ne da wurwuri haka? " Samerah tace. "Wallahi kuwa Hajiya kamawa tayi. Ita waccan yarinyar ƙasar suka bari da iyayenta kinji dalili. Amman har yanzu muna magana da'ita ta waya" Hajiyannan tace. "Nima kinga sabuwar Babyna rijista za'ayi mata bata daɗe da shigowa hannuna ba. Ni kinsan ina da yara da yawa sai dai wallahi ba ƙaramin caza mun kaina suke yi ba gasu da cin kuɗi. Mujenku to kowa ya sha hanya an gaji. " Shigewa suka yi ko wacce ta shige ɗakin data kama. A daren wannan ranar Ƴar shuwa ta bambance tsakanin zare da abawa. Da bakinta tayi ma Sameerah alƙawarin a wata sau ɗaya zata iya mallakama Babangida jikinta. Sabida taga yadda Sameerah duk ta gigice mata sai sambatu take yi mata jiki yasha gyara sosai gashi ko ina a jikinta ƙamshi yake fesarwa har kuka Sameerah ta dinga mata da wasu irin tambotsan sambatu na tashin kai irin nasu ƴan madigo ( wa'iyazubilla). Washegari da misalin ƙarfe tara su Yar Shuwa suka gama shiryawa tsab cikin ankonsu na lace mai matuƙar tsada, gwal Sameerah ta ciro ta saka ma Yar Shuwa a wuyanta da kunnenta. "Kinga wannan sarƙar zinare ce na mallaka miki itace tukuicin daren jiya. Amman abinda nake so dake kiyi biyayya ga ƙungiya banda kuma fitar da sirrin ƙungiya waje yin hakan babban kuskurene. Kuma ƙungiyarmu in aka shiga ba'a fita duk tsanani. Akwai waɗanda sukai yinƙurin fita kinsan meya faru da biyar daga cikinsu? " Tana maganar tana shafa wuyan Ƴar Shuwa data ɗauki wanka kwalliya tabi fatarta ta kwanta kyawunta ya sake bayyana. Kai ta girgiza domin san jin abinda ya same su. Duk da taji faɗuwar gaba taji nadama na neman sakko mata. Tana bala'in son kuɗi tana son zama babbar mace, amman tana tsoron abinda kaje kazo wanda bazaiyi mata kyau ba. Tana mutuwar son aurenta bugu da ƙari "Uku daga cikinsu haukacewa suka yi. Biyu kuma har lahira suka mutu? " Idanu Ƴar shuwa ta zare tace. "Hauka da mutuwa duka sabida sunce zasu tafi?" "Ai ba wai tafiyar bace. Tsoron tunuwar asirinmu muke ji a ƙasa najeriya muke, kuma da kika ganmu ko wacce mijinta sanannene, da damansu ƴan siyasane wasu daka cikinsu kujera ce a hannunsu, matanma da yawansu siyasar suke yi. To kinga tonon asirinmu nasu ne. Sannan saida suka mallaki gidaje, motoci, da zunzurutun kuɗaɗe sannan zasu ce zasu fita a cikinmu? Kinga taso muje sauran bayanin zaki jisu a wajen taro" Ƴar Shuwa bata gama tsurewa ba saida ta ganta a cikin manyan hamshaƙan mata waɗanda suka ɗauki duniya da dukiya ba'a bakin komai ba, wasu da yawa tasansu a jaridu, da kafafen yaɗa labarai, wasu kuma tasan sunan bata taɓa tunanin zata iya matsowa inda ma suke ba Hmmm a wannan rana ta zama memba ta wannan ƙungiya harda shaida aka bata, tare da saka hannu a wasu wuraren yarjejeniya. Kuma su sababbin zuwa suka ji manufofin ƙungiya da aiyukan ƙUngiyar. Ba tare da tunanin komai ba Yar Shuwa ta raftaɓa hannunta akan yarjejeniya. A tunaninta kuɗi sune komai a rayuwa.. Anci an sha anyi duk abinda ya kamata matane masu tarin yawa. Ita shugabar kungiyar ba zata wuce shekaru arba'in ba, ta samu duniya gata kyakkyawa tamkar ita tayi kanta. Duk da matan ƙungiyar wasu irin zaɓaɓɓun matane waɗanda Allah ya hore musu kyau zati ga kuma kuɗi dake maida mummuna ya zama kyakkyawa, ina kuma ga kyawawan ga kuma kuɗi. Atampopi supa_supa da takalma aka raba a wajen taron, taro fa sai dare ya ƙare babu sallah babu salati. Abubuwa da dama na ƙazanta sun faffaru ba abu bane na daɗin rubutu ba. Kuma ba abu bane da zanta bayyanawa wa'iyazubillah Allah ya kiyashemu taɓewa kawai.
Babangida:. Bashi ya farka ba sai azahar shima kiraye_karayen sallah ne ya tasheshi. Wanka yayi a gurguje ya wuce masallaci. Daga nan bai dawo gidan ba sai dare. A ɗakinsu Mardiyya ya yada zango ya tarar sun tusa Aɗɗa'u a gaba suna mishi faɗa yana ta kuka. Shigowarshi ce yasa sukai shiru, amman shi bai daina kukan fitar rai ba. "Mardiyya menene ya faru? " "Baba sata yayo a maƙota kuɗi masu yawan gaske fin dubu saba'in. Yama ci da yawa daga cikin kuɗin sai yaune Malama take faɗa mana" Idanu Babangida ya lumshe maganganun Baba na shago ya shiga kaɗa mishi ƙararrawa a kunnuwanshi akan su guji ranar da nasu ƴaƴan zasu dinga sasu magana, ko su hanasu bacci ma kamar yadda sukai musu. A hankali ya zauna kusa da Aminu yana ƙarema yaran nashi kallo sune yara mafi soyuwa a rayuwarshi, sai dai kashi ga Adda'u ya ɗebo halin sata. Yana roƙon Allah ya yaye mishi, kuma kada Allah yasa yaranshi su ɗebo halinshi ko na mahaifiyarsu. "Bazan sake ba Baba" Ya faɗa yana kuka. Mardiyya ta shiga ɗaki ta fito da kuɗi dubu casa'in da shida ta danƙama Babangida ya saka hannu ya amsa. "Ina ka ɗakkosu a mayar musu dashi. Sannan Adda'u me kake so wanda bana muku, me zakayi da kuɗin daka sato, shin a ajinku ba'a faɗa muku sata bata da kyau bane? " "Bazan sake ba nayi alƙawari. Dama inaso in siya ma Ummi kayan abincine naga gobe zamu je wajenta" Babangida baisan sanda hawayenshi suka sulalo ba, da sauri ya goge hawayen da dabara ba tare da yaran sun sani ba. "Duk abinda kake son siya ma umminka ka tambayeni sai in baka ka siya mata. Allah yayi maka albarka tare da ƴan uwanka baki ɗaya. Ina ka sato kuɗinnan to? " "A ɗakin maman Hamusu mai kifi" Baki Babangida ya buɗe tare da cewa. "To nawa ne duka kuɗin daka ɗakko ɗin? " "Dubu ɗari ne" "To shikenan Aɗɗa'u dan Allah ka kiyaye. Ke mardiyya zaki iya mayar mata da kuɗinta ba tare data san an sata ba? " Kafin mardiyya tayi magana yace zai iya shi a bashi suje da Mardiyyan. Ai kuwa kuɗi Babangida ya zaro ya cikace kuɗin ya basu dubu biyu yace su siyo kifi. Da haka wannan asirin ya rufu. Yai musu sallama akan goben su shirya sai ya kaisu wajen Ummin nasu. "Baba sun sake gida muma bamu san gidan ba. Dama ummi tace sai Baba Gaza yazo zai mana kwatancen layin" Cewar malama take gaban Babangida ya tattake ya faɗi haka kurum yaji hankalinshi ya tashi da ƙyar ya iya magana. "To shikenan in ya kwatanta sai in kaiku zanje in kwanta. " Ɗakin Ramatu ya shiga ya tarar da'ita a gaban kulolin abinci tana ta tubkewa da warwarewa bata sanma Babangida yazo inda take ba. Yayi sallamar yayi ya maya yaji babu amsa a tunaninshi ko tana can ɗakin maƙota tunda haka ta saba sai yaga ashe tana ɗakin. Sai da yayi magana a kanta ta ɗago da sauri suka haɗa idanu. "Lafiya kuwa Ramatu wannan wanne tunanine haka? " Ajjiyar zuchiya ta sauke. "Sannu da zuwa. Hmmmm" Zama yayi suka gaisa ta zuba mishi shinkafa da miya da soyayyan sukunbiya, da jus ɗin kankana. "Menene yake damunki Ramatu? ' Ya tambayeta cike da tuhuma. " Wallahi bashikan da suke kaina suna da yawa. Ga Safiya zata yi aure dubu hamsin hamsin aka yanke mana mu mata nasan dana tambayeka zaka ce baka dashi. Bashikan da ake bina kuwa wallahi sunyi dubu ɗari biyar koma fi" Idanu ya zare, sai da ya kurɓi ruwan kankana ya dawo daidai. "Dubu ɗari biyar ni kuwa ina na ganta, ai ko dubu hamsin ɗin bani da'ita gaskiya. Abinda zaki kula shine bafa ke kaɗai bace ku uku ne. Shin inna baki dubu hamsin suma ina da hamsin hamsin da zan basu ne? Bani dashi ki ba Mama haƙuri kawai. Ƴan bashi kuma ke kika san yanda zaki yi dasu Ramatu ke da na baki jari masu yawa tun kafin ki tare. Yanzu haka ai na raba muku jari ke mai kike saidawa? " "Bana siyar da komai tanadin haihuwa nayi da kuɗin kanaso in haihu ƙawayena suzo suna mun dariya ne? " Mamakine ya ƙume shi magana wannan ya kasa sai ya mayar da hankalinshi kan abincinshi kawai. Amman fa da tunanin sake gidan da akace su Sabuwa sunyi ya kwana. Ya kira wayar ƴar Shuwa kusan sau takwas duk a kashe ake ce mishi. Kai kawai ya girgiza. Da wannan aka wayi gari. Sassafe sai ga matar da take bin Ramatu kuɗaɗe tazo tana neman yi mata tereren bankaɗa a cikin gidan haya mai shaƙe dam da mata, ga kishiyoyi. Mrs Bukhari Ubangiji Allah ya tashe mu lafiya ameen🤲🏻 [10/4, 10:29 PM] +234 810 593 2041: MRS BUKHARI 11
Ita akan dole sai an biyata kuɗinta take ko kuma ta ɗebi kayan kuɗinta. A lokacin Babangida ya fito wanka kenan. Sauri sauri ya shirya ya fito ya tadda wannan mata tana rantsuwa. Ganinshi baisa ta risina ba sam. "Baiwar Allah kiyi haƙuri ko biya biyar ne in sha Allah sai in miki. In kuma zaki bani wata shida akwai adashe da zan ɗauka sai in baki baki ɗaya nawa ne kuɗin naki?" "Wai kuɗina zasu yi ɗari bakwai. Kuma wallahi ko biya biyu zaka yi mun bana so kuɗina sunyi shekara narantse da Allah ko kuɗina ko in yashe ɗakinnan tas wallahi kasan Allah ƴar hau ce ni ta gaske" Ai saita tuɓe ɗankwali ta ja ɗamara mamanta suna sama suna ƙasa tsabaragen jijjigar da take yi" Shima Babangida a ranshi ya aiyana "Kura tayi lafiya lallai harmu za'a faɗa ma hau, mu da hau ɗin inta gammu gudu take yi" A zahiri kuma yace. "To Allah ya kyauta. Tunda abun haka ya zama ke Ramatu sai ki barta ta kwashe kayan ayi mata ciko in kuma sun kai kuɗinta shikenan." "Haka zaka ce Abban mardiyya ta kwashe kayana in zauna dame ko gida kake son inje, ya ina da kishiyoyi zaka bari ayi mun haka? " "To bani da yadda zanyi ban baki damar zuwa ko'inaba kuma na baki umarnin ta kwashe kayan in dai hakan take ganin zaiyi mata ba zata zubar mun da mutunci ba. Ga kuɗin cefanenki ni na fita" Saka kai yayi ya fice zuchiyarshi na tafasa. Matan gidan ashe duk sun fito suna tsaye cirko cirko. Ɗakin su Mardiyya ya shiga ya kirawosu suka kama hanyar titi dan taran abun hawa.