Kenza eBookz

Idan kaya ya gaji book book 4 - Chapter 11

Idan kaya ya gaji book book 4 - Chapter 11

Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 11: Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 11. SABUWA:. Haka muka wayi gari a sabon gida cikin amince da jin daɗi.…

3,673 words

SABUWA:. Haka muka wayi gari a sabon gida cikin amince da jin daɗi. Mutuniyarku Labbai tana kichin tana ta tuyar ƙwai. Su Adama sabo da zaman tsakar gida yasa sun sakko ƙasa sun shinfiɗa tabarma a ƙofar ɗakin Gaza. Su Uzairu zuchiyata anata brush a wajen famfo, magazine kuma yana zaune yana shafa kan Uzairu dake shan madara ( magen Gaza fa) Muƙarraban ɗakin Hauwa ma suna waje wasu da wanki suka tashi, Hauwa kuma sai gyare_gyare take yi. Masa kuma yana zaune yana taya Aliya tsifa. Raliya kuma gawayi take kunnawa a kurfoti, su Qamriyya kuma anata shafa hoda. A hankali na sakko. "Lolo barka da sakkowa fa. Kai gaskiya mun gode miki wannan gida munyi kwanan farin ciki sosai" Cewar Raliya kenan. Layuza taja tsaki ta kawar da kanta. Murmushi nayi na dubi Raliya wacce duk ta fice daga hayyacinta ta zama ƴar ƙauye futuk ƙafarta duk kaushi kaushin ya ɗebi annakiyar dauɗa yayi baƙi abinka da farar fata sai ya fito sosai. Raliya ya gida ya sabon waje? " "Ga sabon waje nan wallahi ni dai jiya da ƙyar nayi bacci balle na saba da ɗakin jinka" Dariya gabaki ɗaya aka kwashe dashi Uzairu zuchiyata harda tuntsurawa tsabaragen dariya. Wannan dariyar yasa Gaza ya fito hannunshi da kofin shayi cike ga mummuƙi a ɗayan hannun. "A lafiya dai Matar manya. Eh wallahi Sabuwa mai sabon aiki Babbar yarinya da tauraruwarta ke haskawa. Da gama takaba da aure, miji duka ɗauka eh wallahi babu wani shege" Zama yayi su Rahine suka baibayeshi ya shiga basu shayinnan da mummuƙi. Ana cikin haka Labbai ta leƙo ta sama tayi kiran su Aisha suka sakko mana da abun karyawa. Duk muka yi da'ira. Wai Sama da Rita basa gidanne? " Adama tace" "Ita dai tayi mana sallama zata aiki. Shi kuma yana ciki yana baccin asara na rashin zuchiya" Ɓurum sai gashi ya fito. "Ke Adama waya faɗa miki baccin asara nake yi? Wallahi ƙwaya nasha taimun karo ga gajiyar tuƙin wurbaro. Ni kudu ma zan tafi kirsimeti ya kusa muje muci kasuwar balam_balo ko na samu na ragon suna" Amman Sama ai gara ka zauna ta haihu kananan cikin ai yazo watan haihuwarshi tace ma ya wuce watanshi na goma sha ɗaya kenan fa kamata yayi ka kaita asibiti. Wanne kuma kudu zaka nausa yanxu ga cikinta da girman gaske tun yana wata biyar da ƙyar take turawa fa." Yana zare idanu yana cusa ƙwai a baka yace. "Bafa ki sani bane tajajje asibiti wallahi cewa akayi nan da sati in bata haihu ba aiki za'ayi mata. Shi yasa nake son lallaɓawa in gudu in yaso in ƙurar ta lafa nadawo" Gaza yace. "Gaskiya baka da hankali an samu matsala eh matar taka zaka kuikuyama wannan akuyancin eh? Wallahi babu inda zaka je dole ta haihu a gabanka in kuma so kake ɗanka ya zama arne ai shikenan. Ke madamcy! Madamcy!! Fito muci ƙwai matar manya ta ɗauki nauyinmu" Madamcy ta fito itama aka dama da'ita Sama yayi shiru yanata tunani ko tunanin me yake yi Allah masani. Bayan mun karya duk muka watse muka shiga gyaran gida da kaye kaye. Ina shanya masa yazo yace. "Sabuwa dan Allah ɗakin mai gadincan dake bakin ƙofa in da hali a bani zanyo aure muyi zamanmu dan Allah Sabuwa. Wallahi rayuwarce sai a hankali da kuka rabu da ganina kinsan Allah gadi nake yi a wani kamfani haka siddan akayi sata a kamfanin aka ƙala mun banji ba ban gani ba. Ke kinsan bana sata sai dai barni da iskancina kin gane? To Sabuwa naji labarin mijinki yana da kuɗi dan Allah ki nema mana aiki a wajenshi ko rayuwar zatai mana sauƙi" Shiru nayi ina saurarenshi sai warin sigari yake yi bakinshi duk yayi duhu har dasashinshi ga tomtom yana ta tsotsa a mugun cake yake ya tsaya a ƙafarshi ya kasa. To masa'u ɗaki dai zaka iya zama in Allah ya yadda wancan ɗinma za'a gyara in yaso ku dukka sai ku koma can maza mazan in kunyi auren. Amman masa'u da gaske auren zakayi dan Allah wacece zata aureka? " Ai daga faɗin haka kuma sai ya hau zage_zage yana ɗaga mun murya. Sai da Gaza ya daka mishi tsawa tukunna, kuma yasa Rahine ta shiga haushi na rashin mutunci. Masa'u ma Hauwa sai ta lallaɓashi ya bar gidan baki ɗaya dama haka ta saba ta tsani taganmu da ƴan ɗakinta a waje guda. Wunin ranar maƙotane sukaita shigowa bisa al'ada kamar yadda aka saba in kun taso daga wata unguwar maƙota zasuita shigo muku sannu da zuwa, kuma in an kwana biyu zaku bisu da haka zumunci yake ƙarko tsakankanin maƙota. Hmm nasan dai a gidanmu babu wani zumunci da maƙota muma bamu nema ba aini Ƴar shuwa ta shani harna warke. Haka dai muka wuni cikin nishaɗi, wayata motsi kaɗan sai inji kira ko saƙon karta kwana daga Alhaji Zaidu. Wallahi ashe da gaskene dattijai duniyar iya soyayya da narkar da mace ne ashe? Cikin ƙanƙanin lokaci Alhaji Zaidu ya dawo dani mutum mace mai ƴanci da sanin ya kamata. Sai da daddare muna ɗakinmu Labbai na guga, Adama na shafa magani a ƙunanta su Sadiya kuma tun yamma basa gidan. Uzairu zuchiyata ya samu lungun katifa ya kwanta anata abu ɗaya. Sai muka jiyo Maigogul ya shigo hannunshi riƙe da leda sai ƙamshi yake yi. "Lolona ungo wannan nakine kici ki more dan Allah" Tasowa nayi na amshi ledar najita da zafi ga maiƙo. "Rakiya tana ciki kenan an samu waje babu mamaki yanzu haka tayi baccinta ma. Labbai anata shirye_shirye dai da Cicib ɗin ba wata matsala dai ko? " "Babu komai lokaci kawai ake jira Maigogul. Amman wallahi ni bani da kayan ɗaki duk sun galgance nama rasa yadda zan sanar mishi gashi yace akwati yake haɗawa" Dariya dukka muka sa Uzairu zuchiyata harda birgima dan masifa. "Shi yace miki yana haɗa akwati, dama kayan da naga yana tsittsinta naki ne? Nako ga yanata ƙoƙari. Toh kinsan dai bani da kuɗi bani da dalilin kuɗi aure na barkate ma sai kin damu kanki? Bafa zai rasa katifa ba ko ita ba sai kuyi rayuwarku akai ba? Ragowar kunji_kunji ai sai ƴan uwanki su yi karo karo su yi miki" Rakiya ce ta shigo. "Me aketa taunawa ne Maigogul? " Labarta mata yayi. Baki ta taɓe tace. "Aikin ɓur tunda yaji ya gani ke meye naki to? Tunda dai abokin ubanki ne sai ki faɗa mishi baki da kayan ɗaki ko zai tagaza miki" A_a Rakiya in sha Allah za'ayi mata daga gida zamu san yadda zamu yi ba zata kunyata ba" "To ai ke kinji matar mai kuɗi ta saka baki magana ai ta ƙare. Adama ke kuma ai ya kamata ki koma ɗakinki tunda hannun yayi sauƙi dai bawai kizo ki jibge a gida ba abun ya kuma isa haka." Adama tace. "Idan hanun ya kuma sha zan koma. Wallahi Rakiya girkin gidanne da wahala nafi son hannun ya warke tukunna" A haka dai suka tafi suka barmu, muna jiyosu suna faɗa. Ledar da Maigogul ya bani na buɗe gasassun banƙararrun zabine guda biyu anyi musu jar suya. Yaga nayi na cire ma Rakiya na kai mata. Muna cin namu na dubi Adama nace. Yanzu Adama komawa Malam madori ashe zaki yi, mutumin da ko sau ɗaya baizo inda kike ba, kuma bai taɓa kiranki ba zaman gidan nashi kike so? " Kafin tace wani abun sai muka jiyo Muryar Rahama a falo Rakiya nata faɗa. Tatsuniyar gixo ai bata wuce ƙoƙi sakine ma mun sani. Shigowa tayi ta zauna muka cinye zabonnan tas muka shiga hira, da ɗaya da ɗaya su Sadiya duk suka dawo muka cika ɗakin dam wasu dole a ƙasan kafet suke kwanciya. Haka muka dai wayi gari da nakudar Rita kuma Tun asuba take abu ɗaya Hauwa na kanta abun dai yaƙi ci yaƙi cinyewa wajen sha ɗaya su Rahama suka kwasheta da Hauwa zuwa asibiti mu kuma aka barmu da girki da dafa ruwan zafi. Ina zaune a kujera ina tuƙa tuwo kiran mardiyya ya shigo akan gasu a bakin titin unguwar sun kasa gane kwatancen. Miƙewa nayi na warware gyalen dake kaina. Labbai kwashe tuwonnan zanje titi in tawo dasu Mardiyya " Ina faɗin haka na fita, na fita kenan kiran wayar Alhaji Zaidu na shigowa. Da sauri na ɗaga nasan ƙorafi shine abu na farko da zaiyi mun ilai kuwa ina ɗagawa yace. "Ni fishi nake yi har sha ɗaya da rabi baki ga wayata ba, baki ga saƙona ba kuma ke baki kirani ba. Anya Shalelena kin damu da wannan angon naki kuwa uhm? " Murmushi nayi lafiyayye kana nace. Shalele kuwa itace ta damu dakai, kai ɗin da soyayyarka da begenka ke hanani saƙat. Wallahi mun tashi ne da naƙudar matar Babban wanmu obarol ( maman twins ana magana 🤣) Sama yanzu haka sun tafi asibiti mu aka bari da girkin abincinsu. To ina cikin kwashe tuwo yaranka suka kirani wai gasu a bakin titin layinmu inje in ɗakkosu" Tsit yayi kamar ruwa ya cinyeshi, sai naji ya sauke ajjiyar zuchiya mai nauyi kana yace. "Tare da Babansu kenan fa? " Murmushi nayi nace. Kishi kenan har a muryarka. Kasha kuruminka Babansu baya gabana wallahi ko maza ƙarewa suka yi a haka zanyi zamana" Dariya yayi, nima saida na dara. "To shikenan bari in kashe wayar bai dace kina matar aure kina tafe kina waya ba. Tuwon kuma a ragemun ina tashi daga meeting Dutse na nufo zanzo ganin ƴar matata mai mun ƙwalele uhm" Ba shiri na kashe wayata. "Sabuwa kece anan me kike yi a layinnan? " Na jiyo muryar da ko magagi nake yi bazan taɓa mance mamallakinta ba. Khalid ne na gani a gabana sai murmushi yake yi. Haɗe raina nayi gabana na dukan tara_ tara, sai na ƙara sauri shine harda gudu ya kuma shan gabana. "Naroƙeki dan Allah ki tsaya ki saurareni Sabuwa zuchiyata wallahi tana azubtuwa da soyayyarki. Kuma naji abinda Matata tazo tayi a gidanku, wallahi yanzu haka na saketa duk sabida ke, Sabuwa ina sonki" Ka soni ko kada ka soni ina da aure yanzu dan haka kada ma ka sake tunanin tare ni a hanya" Wuce wa nayi na barshi nan. Da sauri ya kuma shan gabana, yana ƙoƙarin zai kawo hannunshi jikina, nayi saurin yin baya bakina a buɗe. Kafin in yi magana sai muka jiyo Babangida yana magana da kaushi, ga hannun Khalid carab a hannunshi, duk wasu jijiyoyin kishinshi sun tattashi. "To tunda taƙi tsaiwa ai sai ka barta ko Khalid? ɗan anace ɗaye manna kenan ana ɗayeka kana mannewa. Ke kuma kinyi kyan kai ashe nasihar da nayi miki ta shigeki" Murmushi Khalid yayi ni kuwa na haɗe raina na ja hannun Aɗɗa'una na barsu a wajen ina jiyo Babangida yana cewa. "Ai na rantse da Allah tunda na rasata kaima saika rasata. Ko sama da ƙasa zata haɗe Sabuwa ta Haramta a gareka" Sai dukan ƙirjin Khalid Babangida yake yi yana ɗaga murya tare da hayaniya. Yaya suka ƙare ohon musu sai da muka zo ƙofar gidanmu na jiyo takunshi a bayanmu. Muna shiga shima sai kawai ya kunno kanshi a daidai wannan lokacin ita kuma Aliya suna rikici da Raliya akan yara biyu data ƙi mayar ma da ubansu su ubansu daban sune manya. Shine fa suke ta gorantama junansu. Labbai kuwa tana zaune tana kallonsu jigum. "Ahh kaga mardiyya Amarya, Malama kune ashe sannunku" Cewar Labbai. Babangida kuwa sai ƙarema tsakar gidan kallo yake yi. Naga mamaki da wani irin damuwa da macewar jiki ƙaƙas tattare da Babangida. A sanyaye ya gaishe da Labbai hadda tambayar Rakiya fa" "Rakiya tana sama. Mu jenku daga ciki mana kuga waje" Miƙewa Labbai tayi, tana gaba Babangida na binta a baya, mu muna bayanshi Malama da Aɗɗa'u sai labari suke bani har muka isa sama. Rakiya da Uzairu zuchiyata suna falo suna ninkin kaya. "Ahh mardiyya Amarya yau kune a gidan? Babangida ga waje zauna mana" Hannuna Malama ta sake ta nufi wajen Rakiya. "Rakiya ina Maigogul yake? " "Ja'ira aurenne ya tashi kenan. To in dai Maigogul ne baki more miji ba wallahi" Ni dai shigewata nayi ciki na faɗa gado ina mayar da numfashi. Can mardiyya ta shigo. "Ummi wai kizo inji Baba yana so zaku yi magana ne muma ba daɗewa zamu yi ba" Miƙewa nayi na fita, su kuma Labbai ta jasu zuwa ɗakinmu Rakiya da Uzairu zuchiyata suka bar falon. Ina zaune wajen ya ɗauki shiru abun har ya soma isata da tsiwa na ɗago zanyi magana sai naga ashe ni yake ta kallo. Murmushi yayi yace. "Lolo kenan kin yi kyau sosai, da tsiwar zaki yi mun kenan ko chus. Ashe gida kuka sake" Ya tambayeni tare da kakkafeni da idanunshi dan son ji daga gareni. Kace kana son magana dani, kayi da hanzari sabida zanyi baƙo yana da kyau inje in shirya" Muƙut ya haɗiye yawu tare da yin ƙasa da kanshi ya shaƙa iyakar shaƙa. "Dama gafararki nake nema domin Allah da albarkacin Ƴaƴanmu a yafe mun duk abubuwan da nake da laifi a ciki. Naki kusakuran na yafe miki su. Kema da fatan zaki yafe mun nawa. Sannan dan Allah zan roƙeki ki dinga kama mutuncinki ko dan yaranki irinsu Khalid ba abun su dinga biyoki bane. Sannan a ƙalla in kika ganni ko dan yara da tsawon shekarun Aurenmu kya saki fuskarki Gariza ce insaniyya. " Miƙewa nayi nace.. Allah ya yafe mu baki ɗaya ni zan shiga ciki zanyi baƙo" Cikin fishi yace. "Ko yaran su fito mu tafi kada su takura miki tunda duniya kika saka a gaba. Ƙila ma Bazawarin naki ne ya sai muku gidan" Da dai yafi wani lokacin sa dawo tunda sunga waje sai su zo ai. Sannan ai ba sai ka dinga biyo su ba zasu iya zuwa tunda ba yara bane" Wucewata ciki nayi na barshi yana girgiza kai. Mardiyya ya kira yake sanar mata nan da awa guda su sameshi a ƙofar gida su tafi. Dawowa tayi mukaita hirarmu ina jin nishaɗi, har Sauban ta bani da waya muka gaisa. Na sake musu nasiha akan duk rintsi su riƙe zumunci. Aɗɗa'u kuma na kuma yi mishi nasiha akan halinshi sosai. Mardiyya ta miƙo ledar bakko ɗin da suka shigo dashi shaƙe da kayan abinci ta labartanmu dalilin siyo kayan. Ƙauna da tausayin Aɗɗa'u suka kuma shigata naita mishi faɗa. Tun kafin awa guda Babangida ya gallabesu da kira dole suka fita suka tafi. Ni kuma shirye shiryen tarban Alhaji Zaidu na shiga. Nayi kwalliya na cancaɗa kyau jan lashi na saka mai adon fari da baƙi a jiki. Ina zaune ina fesa turaruka naji wayata tana ruri shi yake kirana. Da hanzari na ɗaga tare da karawa a kunnena kana nace. Amincin Allah ya tabbata a gareka ya hanya kaddai har ka iso ne? " "Ameen tare da ke Shalelen Alhaji Baba kuma Shalelen mijinta. Ai tafiyar dole sai zuwa gobe zaki ganni abubbuwa ne suka riƙeni" Sai naji har cikin raina banji daɗi ba harma rashin jin daɗin ya fito a muryata. To babu damuwa amman na riga na saka raina da ganinka" Murmushin jin daɗi yayi mun. "To me zaki bani Shalele in nazo ɗin? Naga kamar nauyina kike ji sosai uhm" Tabbas ina jin nauyinka amman hakan bawai yana nufin ban damu dakai bane ba. Kawai dai" "Kawai dai me saifa kin faɗa" So yake ya saka mun magana a bakina. Idanu na lumshe kana nace. Kawai kunyarka da kwarjininka ke cikani. Amman inaso in ganka kusa dani ina shaƙar ƙamshinka mai taushinnan" Sai da ya sauke ajjiyar zuchiya mai haɗe da murmushi sannan yace. "Toh gani a ƙofar gida ki fito kiyi mun iso gimbiyar mata uhm" Dariya nayi da sauri kuwa zurub na miƙe na sakko. Ƴan gidan suna tsakar gida, Labbai da Adama sun bi su Rahama Asibiti da abinci da ruwan zafi. Madamcy na ƙofar nata ɗakin tana girkinta. "Irin wannan ƙamshi harnan ga kwalliya da gaye da aka zuba ango ne amman yazo ko? " Kai Madamcy shine yazo ai dole shi za'aima wannan kwalliyar sabida cancantarshi" Tsaki Layuza ta saki tace. "Aikin banza sai fi'ili da rawar kai aketa mana sabida an auri mai kuɗi. Ba giringirinba tayi mai" Yarane na maƙwabta suka soma shigo da doya ina ji Madamcy na cewa su haura sama. Ni dai fitowa nayi waje Alhaji yana cikin mota bai fito ba. Ta ɓangaren direba naje, ina zuwa na ɓalle murfin motar muka haɗa idanu dashi yana mun lallausan murmushinshi mai narka mun zuchiyata. Wannan farin dai da idanu dana saba yima mazan bariki in tafi da imaninsu wallahi shi kawai naji nayi ma Alhaji. Ai kuwa take saƙo ya isa inda ni ban aikeshi ba. Muryarshi a dashe yace. "Shalele anya tariyarnan zan iya barinta har wata kusan biyu da rabi kuwa ina kallonki? Shiga mota ki rakani uhm Shalelena" Ina murmushi na zagayo na shiga motar na jiyo na dubeshi na sake yi mishi fari da idanu wannan karon harda guntuwar shagwaɓar da nayi tunanin tuni tayi esfiya ashe da ranta. Wallahi sai kawai naga ya dafe kanshi ya lumshe idanunshi yana sauke numfashi a hankali. Ai saina ƙara ƙaimi da shagwaɓata wallahi kamar ba Sabuwar da kuka sani ba. Nan take na gane logonshi shi namijine mai son shwagwaɓaɓiyar mace. Nayi mu'amala da maza da yawa, ko wanne namiji da irin abinda yafi so a wajen mace to shi dai Alhaji Zaidu na bugo jirginshi. "Shalele so kike yi daga nan in gudu dake Kano sai dai mu kira a waya muce an tare ne?" Me yasa to za'ayi hakan?" Hannunshi ya ɗaura a saman hannuna dake kan cinyata, dukkanmu muka lumshe idanu a tare. A hankali muka buɗe idanun a tare muka zuba ma juna idanu ba tare da munce uffan ba. Sai ƙarema ƙirjina kallo yakeyi kamar zai cinyeni da gayya dama na ɗan zame mayafin mamana ya ɗan burtso har wushiryar data rabasu ana gani. Hannu ɗaga yana nufin shafan wuyana na lumshe idanuna Ƙwanƙwasa kwalbar motar da akayine yasa muka dawo hayyacinmu. Maigogul na gani a tsaye yana ta washe baki. Da sauri Alhaji Zaidu ya saisaita kanshu ya fita cike da girmamawa yake gaisheshi. A sanyaye na fito ina mai roƙon Allah kada yasa Maigogul ya saki layi. "Sabuwa haka akeyi maimakon ku shige daga ciki kin tsayar da babban mutum a tsaye haka? Alhaji muje dan Allah tawo" Hannunshi Maigogul ya ja suka shige ciki nabi bayansu har zuwa falon sama. Rakiya tana gaban tulin tsarabar da Alhaji Zaidu ya kawo. Maigogul yana ganin rigirigi ai sai ya sake sakin dariya ya shiga godiya. Hannun Rakiya ya ja bayan Alhaji Zaidu ya gaisheta suka shige ciki, kafinma su shiga saida ya juyo. "Lolo kin dai tanadar mishi abincin da zaici ya isheshi ko? " E Maigogul na tanadar mishi. "To to shikenan" Bayan sun tafi saina dawo da hankalina kan Alhaji Zaidu. Barka da zuwa ina yini, ya hanyar, ya ka baro yayar tawa? " "Lafiya lau jinin jikina. Yayarki ma tana lafiya, ya masu haihuwa ta sauka kuwa? " Ban kirasu ba, su Adama dai sun tafi asibitin duk yadda ake ciki zamu ji. Bari in kawo maka ruwa" "A_a kiyi zamanki dai inta kallonki ai yafi mun abinci. Duk da dai shi kanshi abincin inason ci tunda daga hannunki ya fito. " Murmushi nayi na gyara zama da kyau mukaita kallon juna muna jin nishaɗi sosai, cikin raɗa yace. "Allah yasa Alhaji Baba baiga abinda naso nayi ba Shalelena". Murmushi nayi kawai muka ci gaba da kallon kallo Kiran sallah la'asar ne ya katse mana kallon soyayar da muke ma juna haɗe da fitowar Maigogul yana saɓa malum malum. "Yau ga tsiya da wasali ƙasa lolo banga abinci ba banga abun sha ba, lafiya kuwa kike? " "Lafiya lau Alhaji Baba dama sabida naga lokacin sallah ya ƙaratone shi yasa nace ta barshi inna dawo naci" "To to shikenan muje, ke kuma ki jera komai kafin mu dawo" Suna fita na jejjera komai na yanka kankana da ayaba na ajjiye mishi daga cikin tsarabar da ya kawo. Ina idar da Sallah sai gasu Rahama da Labbai sun shigo suna haki. "Lolo Rita dai ta haihu, to babu fa kuɗi a hannunmu ƴan kuɗaɗen da suke hannun Rita dashi aka biya abubuwan daya dace. Yanzu haka kuɗi ake buƙata dan wallahi babu yadda take bata gane ma wake kanta yarone namiji baki ganshi ba ƙato fari sol dashi sak ubanshi fa. Sama kuma Adama ta kirashi, nima na kirashi sama da ƙasa yaƙi ɗaga wayarshi almurin. Shine muka dawo mai taro mai sisi sai mu harhaɗa, ni dai wallahi bani da dako ficika" Saini na bada dubu ashirin Labbai ta bayar da dubu biyar. Rahama ita kaɗai ta koma su Labbai kuma sukai zamansu. Rakiya ce ta leƙo. "Lolo ki fito gashi yadawo, Maigogul ya kama zuba sai yi yake yi. Kiyi mana wallahi" Da gudu na miƙe ina fitowa Maigogul ya miƙe. "To Alhaji tunda ga lolo ni bari in shiga daga ciki kuma dama wai kada a barka kai kaɗaine" Ina zuba mishi abinci su Adama suka leƙo aga gaggaisa kana suka koma ciki. Yaci tuwon sosai yana ta yi mun santi, ni kuma ina zolayarshi. Sai da yakai shidan yamma, lokacin har Hauwa ta dawo asibiti ta hauro sun gaisa ma. Da zai tafi yai ma kowa rabon kuɗi ya bani wata leda da yace in ba Gaza da kuɗi dubu ashirin yace a ajjiye mishi. Ni dai da ƙyar muka rabu shi kanshi da ƙyar ya yakice muka rabu, dan a bayan mota muka zauna Allah munfi minti ashirin ya sani kawai a jikinshi ya ɗaura haɓarshi a kaina. Muka yi lum ni har wani zazzaɓi_zazzaɓi nake ji wallahi. Da ƙyar muka rabu da juna cike da wani irin shauƙi da zabarin son keɓewa. Kuma da mukaita waya har saida ya shiga garin kano, duk da tana katsewa in anzo inda ba sabis Mrs BUKHARI Mu tara gobe in Allah ya kaimu sai da safenmu [10/4, 10:29 PM] +234 810 593 2041: MRS BUKHARI 12

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull