Kenza eBookz

Idan kaya ya gaji book book 4 - Chapter 12

Idan kaya ya gaji book book 4 - Chapter 12

Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 12: Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 12. Gaga gaga haka al'amura sukaita tafiya. Kwanan su Rita biyu a asibiti…

3,567 words

Gaga gaga haka al'amura sukaita tafiya. Kwanan su Rita biyu a asibiti aka sallamosu. Daga danginsu aka turo wata tsohuwa tazo ta zauna da'ita. Sama baya iya tsinana komai sai ni na cire kuɗi na sai mata kayan abinci na sai mata kayan shayi. Ranar suna yaro yaci sunan Maigogul aka mishi inkiya da Abbati. Ragon suna mai ɗari mai ɗari biyu haka aka harhaɗa na cika aka siyo ƙaton rago Ga dangin Rita sai da suka ciko bus dan masifa wai sunzo suna. Sun dai kawo mana tsarabar dankali da risga, ni ban taɓa ganin risga ba sai wannan lokacin gashi da daɗi musamman in yaji ƙuli_ ƙuli. Allah ya tainakemu duk wannan sha'ani Maigogul baya gidan sun tafi biki Lagos shi da Cicib. Suna dai an ɗanyi hayaniya gaskiya har maƙota amman batai yawa ba ƙurar ta lafa akan hanjin rago akayi rikicin. Su mardiyya da yaran su Rahama, Adama duk sun zo suna, ganin Hakane Labbai itama tace dole yaranta suzo sunan. Ai kuwa taima Aisha kuɗin mota taje ta kawo yaran suka shiga cikin ƴan uwa sukaita nishaɗi. Matar isuhu da iyalinshi ma sunzo suna, harda Baba ma ƙanwar Rakiya tazo wannan suna, sabida dama Rakiya ta labarta mata mun sake gida gashi zamu je umara dalilin da yasa tayi amfani da hakan kenan tazo. Baku tambayi labarin Laraba ba. Hmmm Laraba dai tayi aure ta auri wani mahauci bata daɗe ba kishiyoyi suka sakata gaba auren ya mutu daga haka ta tattare kayanta ta koma ƙauye da zuwanta bata daɗe ba tayi wani auren abunta. Anyi suna da kwana biyu muka wuce Kano ni da Maigogul da Uzairu zuchiyata daya nace saiya mana Rakiya. Hotel Babba Alhaji Zaidu ya sauke mu sai nan nan yake yi da Maigogul, shi kuwa Maigogul tsabaragen farin ciki bakinshi yaƙi rufuwa. Da daddare ina kan sallaya dana tawo da'ita a jaka naji an ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin nawa. Ina buɗewa naga Alhaji Zaidu ɗauke da basket na abinci guda biyu. Murmushi yayi mun ya muƙo mun ɗaya. "Ga namu bari in kaima su Alhaji Baba nasu sai inzo. Anan wajenki fa yau zan kwana" Ai sai naji ƴar faɗuwar gaba domin har ga Allah nasan bazai kwana mu wanye lami lafiya ba, ni kuma nafi son in gyara jikina sosai tukunna. Komawa ciki nayi jikina a mugun sanyaye na zauna a ƙasan kafet ban jima da zama ba ya turo ƙofar ya shigo, ya saka key ya kulle gabana nata faɗuwa. Malum_malum ɗin jikinshi da ƴar cikin ya cire ya bar wandon shaddar da farar singileti. Zama yayi yana fuskantata yana murmushi. "Zuba mana abincin Shalele yau ni da kaina ma zan baki abincin domin kada ki gaji uhm" Jiki a kasale na zuba mana lafiyayyen tuwon shinkafa miyar taushe taji naman kan rago harda manshanu a miyar. Cokali ya saka ya gutsuro tuwon ya nufo bakina dashi. A hankali na buɗe bakin nawa ya saka mun. Taunawa nake yi a tsanake. Babu yabo babu fallasa miyar tafi kyau a ido fiye da a baki gaskiyar magana. Amman ba za'ace babu daɗi ba. Ya dinga ciyar dani ina amshewa saida na ƙoshi sannan ya miƙo mun cokalin yace. "A rama ma kura aniyarta., dan nima bai kamata in wahala ba ko uhm Shalelena? " Ina dariya na soma bashi abincin a baki. Cikin dabara nace. Wannan girkin Hajiyane? " Gyaɗa mun kai yayi saida ya cinye tuwon bakinshi kana yace. "Girkin Hajiyane Shalelena" Masha Allah abinci yayi daɗi. Ai na ɗauka matan manya basa girki sai dai ƴan aiki su dinga yi musu, har da gyaran ɗakin miji ma haka" "Kinyi gaskiya Hajiya bata girki sai dai tana da Ƴar aikinta wacce ta yadda da'ita itace mai yin girkin gidan baki ɗaya, kuma ko mata dana aura a baya duk itace dai take girkin ranar girkin mace itace zata faɗa mata abinda za'a girka har ta fita girki kinji yadda tsarin gidan yake." Kai na jinjina ina mamakin mata da samun waje. Abincin cikinku ku biyu da mijinki shine abinda sai ƴar aiki ta girka miki? Ina laifin tayi wasu aikace_aikacen ke kiyi girkin, kwanciyar aure shine kaɗai aikin da kika yadda naki ne ko? Hmmm Murmushi nayi nace Allah sarki. Abincin yayi daɗi sai dai Hajiya bata san mu ka kawo ma abincin ba ko tunda dai bata san da zamana ba" Ruwa ya tsiyaya ya sha kafin yace. "Bata san da zamanki ba tukunna lokaci zaiyi halinshi tunda kafin ki tare dole zata san da zamanki. Abinci kuma bata tuhumeni ina zan kai ba, nima kuma nasan ba zata tuhuman ba, na barota tana ta lissafin kuɗi. Kinsan menene Shalelena? " Girgiza kaina nayi. "Ina sonki sosai fiye da yadda kike tunani ki dage sosai ki roƙa mana Allah dangane da zaman aurenmu. Bacci mai munshari ba naki bane umara kika je ki roƙi Allah ya sanya albarka, kwanciyar hankali, da fahimtar juna a tsakaninmu. Jibi zan biyo bayanku, har Dubai ɗinma dani za'aje Hajiya itama zata je umara to tare zamu je, sai dai ba zamu dawo tare ba sai in ɗaukeku muje Dubai. Nayi hakanne dan in baki dama ki zaɓi duk abinda yayi miki. Familina babban familine ba'a rabasu da sha'ani biki ko suna gashi anayin taro sau biyu a shekara a Rano. Bana so kowa ya raina mun mata ko ya raina daga inda kika fito, kema bana so kice zaki raina kanki Shalele uhm. Sannan ki sai kaya masu tsada sosai matata bata ɗaura ƙaramin zani bata saka ƙaramin takalmi, kada ki damu da kuɗin akwai iya adadin kuɗin dana ware miki na lefenki duka nake son ki kashe kita mun kwalliya ni kuma ina morewa. Sannan zan ba Alhaji Baba kuɗin kayan ɗakinki ya sai miki komai in a Dubai ɗin kike so sai a siya a ɗauro a jirgin kaya, in kuma na nan gida Najeriya kike so shikenan. Bana so da wasa a raina mun ke. Yadda kowa zata nuna isarta kema ki nuna taki isar kema matace kamar kowa" To shikenan nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi Allah ya ƙara buɗi Ubangiji Allah ya barmu tare har abada. Allah yasa in zama uwar ƴaƴanka, batun kayan ɗaki bama saina siya a Dubai ba wallahi na gida Najeriya ma ya isa nagode sosai." Jawoni yayi na faɗo ƙirjinshi muka zuba ma juna idanu sai rarrabe idanunshi yake yi a kaina. "Shalele kina sani a cikin wani irin yanayi na musamman in ina tare dake sosai. Wannan tariyar na mata tanadi mai yawan gaske kema ki shirya kinji ko uhm?" A wannan daren mun daɗe sosai a cikin wani keɓaɓɓen yanayi, ni dai inata fargaban babban, shima sai bai nema ba, nutsuwa kawai ya samar ma kanshi yaimun raɗa a kunnena. "Wancan akan gadona zai kasance ba a ɗakin otel ba Shalelena. Ai wannan ranar ta musamman ce ba zanyi wasa da'ita haka ba. Nutsuwa na samar ma kaina ƙwalelen yayi mun yawa kyakkyawata uhm" Miƙewa yayi ya kintsa na rakashi ni da Uzairu zuchiyata har bakin mota muka saka mishi basket a mota. Washegari da misalin huɗun yamma jirginmu ya ɗaga zuwa ƙasa mai tsarki. Ina zaune a kusa da wata Hajiya a shekaru ba zata wuce Sa'a ba. Tun zamanmu dake kujerarmu tana kusa da tasu Maigogul sai naga tana ta satan kallonshi haka. Da dai abun ya isheta sai ta juyo tace. "Mahaifinki ne wancan bawan Allahn da naga yana ta tattalinki, ko kuwa dai mijinki ne? " Murmushi nayi nace. Mahaifinane" Sai ta murmusa itama gata ƴar gaye sosai sai ƙamshi take yi hannunta da ƙafarta sun sha ƙunshi yayi mata kyau sosai. Ga zobunan zinarai data jera a hannun hagunta har guda uku, su kansu awarwaron hannunta kamar na zinare ne gaskiya dan gyansu ya kai. Dana ɗago sai inga Maigogul dai take kallo abun almara. Bamu muka iso Saudiyya ba sai misalin ƙarfe ɗayan ɗare. Amman sabida kyau da hasken daya mamaye ko'ina da kai kawon jama'a yasa mutum zaiji kamar ba dare ba. Muna sauka jirgin ƴan wata ƙasar ya sauka shima. Munyi munti talatin a Airport kafin muka fito wannan Hajiyar tana biye dani, harma ta taimaka mun da riƙon jakata. Tunda muka sauka wallahi Allah naji na canja wani irin sanyi na shigata takota ina. Maigogul na kalla naga sai sharce hawaye yake yi kuka na tunkuɗo mishi. Nayi imanin kukan tsoron Allah ne. Ga mutane da yawa sunata hawaye ni kaina fuskata sharkab da hawaye. Gaskiya ana zuwa umara sosai babu laifi. Hotel ɗinmu muna daga ɗaki muna kallon harami. Allah mai iko kunga ƙudurar Allah ko? Maigogul na shiga ɗakinshi zazzaɓin tsoron Allah ya rabkeshi ƙaƙas.

Gidan Babangida:. Kwanan ƴar Shuwa biyu a Abuja cib. Saida aka kaita wajen shugabar ƙungiya suka amfana da juna. Harma aka saka sunanta a tafiya yawon buɗe idanu da za'ayi a cikin sabuwar shekarar da za'a shiga. Ta ƙudure a ranta wallahi ko da figi da yagi ne sai tayi wannan tafiyar ko me Babangida zaiyi sai dai yayi a yanzu ji take yi babu wanda ya isa rabata da su Sameerah. Tana zaune a motar Sameerah tayi shiru tana tunanin Babangida daya bi ya kanainaye zuchiyarta tana kokonton kamar cusa mata soyayyarshi akayi ta ƙarfi da yaji. Wayarta ce saƙo ya shigo ta yi saurin dubawa a tunaninta Babangida ne sai taga baƙuwar lamba. "Baby Aisha Zarah ce shugaba. Na kwaceki daga hannun Sameerah wannan kayanane kinyi mun sosai, taraiyarmu tayi mun daɗi. Ya zama sirri Baby zan baki duk abinda kike so, kiyi tunani ita kanta Samerah a ƙarƙashina take. Love you" Abinda saƙon ya ƙunsa kenan. Ƴar shuwa bata fice cikin mamakin hakan ba ta jiyo muryar Sameerah. "Baby wai tunanin me kike yi ne ko dodon naki bai ɗauki wayar bane har yanzu? " Ajjiyar zuchiya ta sauke tace. "Wallahi yaƙi ɗagawa sam. Yana da zafin kishine matsalarshi kenan. Baki ji yadda yake faɗa a waya ba jiya wallahi kamar zai zazzageni haka yake mun magana. Na mishi saƙo ma ina hanya wallahi yaƙi ɗaga dai wayar" Murmushi Sameerah tayi mata cikin salon mantar da'ita zancan Babangida tace. "Kada kiyi wasa da sharaɗin ƙungiya. Ke yanzu ba jigari_jigarin mace bace. Sannan ki riƙe mun alƙawarina kada ki samu wasu iyayen gidan a group, gaskiya ni ba'a haka dani ina da kishi zan iya komai akan Babyna wallahi bani da daɗi " Da haka dai sukaita hirarsu ƙarfe uku na yamma suka iso garin dutse a ƙofar layinsu Ƴar Shuwa Sameerah ta ajjiyeta. Ƴar Shuwa bata shiga gida ba saida ta tsaya a bakin layin nasu tayi cefanenta na kayan miya harda kaza ta siya a shago. Tana shiga matan gida sukaita mata sannu da zuwa sannu da zuwa ita kuma sai baki take washewa. "Sannu da dawowa Maman Faty kawo akwatin in shigar miki dashi" Cewar Rahama kenan. A taɓe tace" "Basshi kafin a kaini gaba ai kinga hankalinta yananan" Da Sumy take wacce take ƙofar ɗakinta ta baza lesuka da takalma na siyarwa mata nata zaɓa. Ɗakinta ta buɗe ta shiga tana ta haki. Saida ta huta tayi azahar da la'asar tayo wanka ta fito Kitchen ta ɗaura sanwa sai ga Jamee dasu Fati sun turo ƙofa sun shigo. "Kin dawo ashe? Yanzu muka dawo ai dasu Fati sun rakani wajen Kulu" "Nadawo in faɗa miki tafiya tayi kyau sosai na samo alkhairi akwai labari ke dai bari in nitsa tukunna zaki ji labari gobe. Ina zuwa bari in kawo miki taki tsarabar" Miƙewa Ƴar shuwa tayi ta shiga ciki ta zaro takalmin da aka raba musu a wajen taro ita nata yayi mata kaɗan ta miƙa ma Jami. "Gashi tsarabarki kenan" Karɓa tayi baki a yashe tai godiya nan ta lalace sukaita hirarsu ƴar Shuwa nata girkinta zuxhiyarta cike da tunanin Babangida a ɗakin wa yake ma ita wallahi bata sani ba. "Wai kuwa kinsan Ramatu babu komai yanzu a cikin ɗakinta sai katifa katifarma a wajen dillaliya ta siya? " Baki Ƴar shuwa ta buɗe nan Jami ta bata labarin dambarwar da akayi Ƴar shuwa taita farin ciki da jin daɗi. Ko da Babangida ya dawo yaga ƙofarta a buɗe bai nemeta ba itace ta wanke jikinta ta nufi ɗakin Ramatu ta sameshi ta gaisheahi yana zaune yana cin shinkafa da miya da dafeffen ƙwai. Ɗakin babu komai sai kafet dai a malale ko labule Babu zannuwan gado Ramatu ta saka ta kare tagoginta dama gulmar da Ƴar shuwa ta shigo yi kenan "Lafiya sai yanzu kika so dawowa? Daga yanzu sha'ani ya wuce na gari to banaso a sake kawoshi gabana ma yin hakan zaisa koma wacece ta fuskanci matsala. Ni dai na faɗa muku kenan wallahi bazan iya ba" "Ayi haƙuri Jannaty shi zumunci.... " "Kiyi mun shiru kinji ko? Ba faɗi in faɗa nake buƙata ba" Fuu ya shige uwar ɗaki ya barsu nan. Ƴar Shuwa bata miƙe ba suka jiyo Sallamar Sumy a bakin ƙofa. Tare suka shigo ita da Adeza Ƴar uwarta matar Mustapha ta ɗan ciki a jikinta. Sai lokacin Ƴar shuwa ta ƙarema Sumy kallo tsab itama ashe cikine a jikinta ƙarami sosai. "Ramatu Baban Amir yana ciki abokinshi na waje yana son magana dashi? " "E bari a kirawo shi" Miƙewar da zata yi sai Babangida ya fito yayi waje. "A kaine Mustapha da madam shine babu ko waya?" To bari a fito mana da tabarma, su matan a barsu a ciki. Ramatu kiba yara tabarma su kawo" Ramatu tayi sauri taba Yusuf tabarma ya fitarma da su Babangida, harda abinci da ruwan sha. Adeza ta zauna suna gaisawa da Ƴar shuwa, itama Sumy tana zaune duk a ƙasa tace. "Ashe kin dawo" "Uhm" Iyakar abinda tace kenan. Ramatu ta kawo abinci ta ajjiye ma Adeza, hirar dai jefi jefi akeyi sai kawai Sumy suka sake yare ita da Adeza sukaita yara yaren ibura. Ƴar shuwa ta taɓe bakinta ta hararesu kawai. Gashi babu damar ta fita ace ta wulaƙanta matar Mustapha.

Babangida:. Bayan sun zauna sun gaisa. "Ga abinci kaci Mustapha in zaka iya ci. Duk da a cikin damuwa na ganka" "Hmmm Babangida ga Adeeza nan na kawota gobe zata kama hanyar garinsu akwatinta yana mota ni da kake ganina na saketa saki ɗaya Wallahi bazan iyaba masifar yau daban ta gobe daban fa." "Ashsha Mustapha kayi kuskure kuma ni a so samuna dan Allah ka daure ka dawo da Adeeza ɗakinta ka ɗauki mataki. Kuma in matakin yaƙi ɗaukuwa ka ɗauka wannan sakamakone muke karɓa sabida mu kanmu babu irin tozarci da wulaƙanta mata da bamu yi ba. Ni Hameeda ce ta matsa kullum kuka da magiya akan in dawo da'ita kullum sai ta turo mun saƙo. tunda na rabu da'ita wallahi tace mutumin arziki bai sake zuwa wajenta ba da iskanci ake zuwa mata. Yana ɗaya daga cikin matsalolin da zawarawanmu na ƙasar hausa suke fuskanta. Allah kada kasa Ƴaƴanmu su ɗanɗana iriyar azaba da tozarcin da mu muka ma mata, Allah ka tsayar da sakamakon a iya kanmu Allah mun tuba. Mustapha kaji tsoron Allah girma fa ya kamamu ya kamata mu watsar da komai a tuba kuma. Club ɗinnan ka dena zuwa ka tuba ga Allah" Mustapha jikinshi yayi sanyi ya san Babangida ne kaɗai yake iya tsage mishi gaskiya duk ɗacinta sai kuma mahaifinshi. Ga babban yaronshi ya afka shaye_shaye neman matanma uwar tace yana taɓawa bai tashi ankara ba sai da komai ya lalace sakamakon riƙon sakainar kashi da yayi ma ahalin nashi kaico. "Ai na dena kulobin tuni Babangida dake ka jima baka ziyarci majalisarmu bane shi yasa. Na riga na tuba kuma nayi ma Allah alƙawarin bazan sake ba." Haka Mustapha ya tusa Adeeza a gaba suka koma gida. Washegari da daddare ƴar Shuwa na zaune sai ga kiran waya daga mahaifiyarta. "Ke Aisha wata Sabuwa wani babban al'amari ya faru fa. Bana sanar dake su Maigogul sun bar unguwarnan ba anata raɗe raɗin sun siyar da gidanne ba? " Ƴar Shuwa da gabanta ya tsinke tace. "E Mama yanzun wani abune ya faru kuma" "Hmmm gidan anata gyara ana mishi kwaskwarima in faɗa miki har da tsayin katanga ake ƙara musu. To yau sai ga Hauwa ta leƙo unguwar shine take faɗa mun mummunan labari wai Sabuwa ashe tayi aure? " Baki ƴar Shuwa ta washe wani farin ciki ya lulluɓeta. "Mama ai aurenta shine kwanciyar hankalina" "Inji uban wa kinsan yanzu Sabuwa da Maigogul suna umara, sannan daga can Dubai zasu wuce acan zasu haɗo lefe. Ga gidan sama ya siya musu shi mijin sun bar unguwar, nasu gidan ana gyarashi zasu zuba haya. A yadda Hauwa take labarta mun tace babban mutum ne wanda ya fito daga babban gida gidan malumta sanannu" Ai ba shiri ƴar Shuwa ta miƙe ta shige uwar ɗakinta ta shiga zirga zirga ita kaɗai sun jima sunata waya da Mama kafin daga bisani ta kashe wayar ta shiga kaikawo idanunta duk sun rufe tsabaragen baƙar hassada dake damunta. Kuka ta fashe dashi tayi tayi ta ƙoshi ta dawo ta zauna shirum. "Umara harda Maigogul sannan lefe a Dubai. Kenan Sabuwa kuma fina tayi? Ina inna yadda Allah ya tsine mun saina sakarma Sabuwa ɓera a yayi duk inda dangin mijinta suke saina nemo su na sanar musu wacece Sabuwa. Dan nasan zaiyi wuya susan wacece ita" Babangida ne ya kira sunanta da ƙarfi. Tana ɗagowa suka haɗa idanu. "Abincinki ya gama babbakewa kina ɗaki ke kaɗai kina surutan banza da wofi lafiyarki ƙalau kuwa? " Murmushin mugunta tayi tace. "Ashe Sabuwa tayi aure. Mijin ma ya biya musu umara ita da Maigogul yanzu haka suna can" Dummm _dummm zuchiyarshi ta buga ƙirjinshi ya wani yi jijjiga ta ciki. Take yawu ya sarƙeshi ya shiga tari kamar zai mutu. Da sauri ta kawo mishi ruwa ya zauna akan gadonta ya sha. Ita kuma ta tafi ta sauke girki ta dawo. "Ke a ina kika ji tayi auren harma tana umara? " Dariya tayi yadda taji muryarshi ta koma. "Labarin duniya baya ɓuya duk da ɓoye abun suke yi. Amman ya fito fili dan ance auren ma ya jima gaskiya. Ya sake musu gida tsohon gidansu kuma ya ɗaura Gaza akan aikin gidan. Ance ma daga Umarar dubai suka nufa acan zata haɗa lefe" Kai Babangida ya riƙe yanajin duniya na jijjigashi tana watangaririya da rayuwarshi abu kamar wasa wallahi da ƙyar Babangida ya fita ya koma ɗakin Ramatu. Bacci ya ƙaurace ma idanunshi duniyarshi ta tsaya cak. Wasane gaskene kafin gari ya waye Babangida baya ko iya ɗaga hannunshi, baya kuma gane waye a kanshi. Tun cikin dare yake ta sambatu yana barin wasiyya ya gama cire rai da rayuwarshi baki ɗaya. Ita kanta Ƴar shuwa ganin halin da Babangida yake ciki ba ƙaramin kiɗimata yayi ba. Tana kuka ta kira Malama Babba, ta kuma kira Mustapha a lokacin dukkansu kuka suke yi a tunaninsu raine ma yayi halinshi. Mardiyya tana ƙanƙame dashi tana kuka tana tottofa mishi adda'a Ƴar Shuwa tace. "Dallah sakeshi ki bari masu uban suyi kukan gaske dan ko mutuwa yayi baki da gadonshi dan ke ba Ƴar gidannan bace wawuya kawai" Tsaki taja tana huci. Da sauri su Aminu suka kalleta mardiyya kuwa kasa ɗagowa tayi kawai saita shiga faɗuwar gaba. "Wacce irin magana ce kenan wannan kike yi Maman Fati? " "Eh na faɗa ina nufin Babangida ba shine ubanta ba ƴar shege ce aka ƙaƙaba mishi ƴar wani ce can daban Sabuwa ta ƙaƙabama Babangida cikin sabida ya aureta. In anci gaba da ɓoye mata duk ranar da mutuwa tayi halinta ai dole a sanar da'ita ko" Kuka Mardiyya ta fashe tashi ta rirriƙe kanta tana jijjigawa. Allah sarki Aminune ya riƙeta yana jijjigata yana tofa mata adda'a. Da sauri ta miƙe ta fice a ɗakin ƴan uwanta suka bita daidai isowar Mustapha ya kinkimi Babangida shi da Ƙasimu sai Asibiti. Mardiyya kuma ta saka hijabinta da jakarta ta dubi ƙannenta tace. "Zanje in dawo Aminu ku zauna kuita ma Baba adda'a" Aminu yaso tambayarta inda zata sai ya fasa yace. "Adda nasan ba zaki guje mu ba ke mai ilimice. Kuma nayi imanin ubanmu ɗaya in aka duba kamanninki da Baba. Adda kada ki ɗaga ma kanki hankali ko da kin bincika hakan ta tabbata duba da a gidansu ummi babu abinda basa yi. Ki lizimci faɗin la'ilaha'illah'anta subuhanaka inni kuntu minal zalimin" Take taji ta samu nutsuwa a zuchiyarta. "Nagode ƴan uwana nagode sosai. Babu inda zan iya tafiya in barku. Ku dai ku zauna kuyi ma Baba adda'a" Tana faɗin haka ta saka kai ta fice kai tsaye taje wajen Baba malam a makaranta. Tana zuwa ta zauna kusa dashi ta saki marayan kuka na tashin hankali. Wannan dattijon da jin irin wannan kuka a ranshi yace. "Irin ranar da ake gudu tazo asirin Babangida ya tonu shikenan darajarshi ta zube" Mrs bukhari. Sai in Allah ya kaimu asabar kuma in muna cikin rayayyu Son so💪🏼 [10/4, 10:29 PM] +234 810 593 2041: MRS BUKHARI 13

ASSALAMU ALAIKUM MASOYANA NA FAƊIN DUK DUNIYA. GANI NA FITO JIKINA DA SAUƘI NA FITO DA ƘARFIN IKON ALLAH. HAƘIƘA BABU ABINDA ZANCE DAKU SAI ADDA'AR KHAIRORI NAGA MASOYA WALLAHI NAGA MASOYA HAR SAIDA TA KAI TA KAWO WAYATA MA NA KASHETA SABIDA TSABAR KIRAN WAYA. WAƊANDA KUKA KIRANI INA GODIYA. WAƊANDA SUKAI MUN ADDA'A TA PC INA GODIYA, DA DUBBAN MASOYANA NA CIKIN TASKATA DA AKAITA YI MUN ADDAU'O'I WALLAHI ALƘALAMI YAYI KAƊAN WAJEN RUBUTA IRIN FARIN CIKIN DANA SHIGA. NAGODE NAGODE UBANGIJI ALLAH YA AMINTAR DAMU BAKI ƊAYA SON SO💪🏼

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull