Kenza eBookz

Idan kaya ya gaji book book 4 - Chapter 13

Idan kaya ya gaji book book 4 - Chapter 13

Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 13: Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 13. Jawota yayi kusa dashi kamar zata shige jikinshi. Ya ɗaura mata kanta a…

3,954 words

Jawota yayi kusa dashi kamar zata shige jikinshi. Ya ɗaura mata kanta a kafaɗarshi yana shafan kanta. "Haba malama Mardiyya ke da kike mahaddaciya kuma malama mai koyar da tarbiyya har akwai abinda zai damekine. Ke da zaki yi aurenki a dangin mahaifinki kuma wanda zaki aura yana sonki. ke da Allah ya ɗaga darajarki da hasken Qur'ani da hasken makaranta har kina ganin akwai abinda zaisa tauraronki yi dishe ne. Ke da na fifitaki sama da sauran jikokina, ke da nake wasa dake sama da kowa, ke dana saka Jami'a, jami'ar da ko ƴaƴan cikin maza da mata ban yadda sunyi ba meye zai dameki? Ke da kike kama da kakanki, kike kama da mahaifinki. Duniyar da za'a mutu mai gata da marar gata, mai uwa da uba, da marar uwa da uba, wanda aka haifa a sunnah, da wanda aka haifa a waje?. Mardiyya share hawayenki kiji wani abu, ki koyi ƙarfafa kanki da kanki, share maza" Tana ajjiyar zuchiya ta ɗago zata soma share hawayen ya saka leɓen malum_malum ɗinshi ya share mata hawayen tas. "Koke fa. Faɗamun menene ya sakaki irin wannan kukan? " Murya a sanyaye tace. "Maman Faty ce tace wai Babanmu bashi ya haifeni ba, kuma bata hanyar aure aka sameni ba" Idanu Baba Malam ya lumshe yana murmushi kawai gami da girgiza kai" "Haka kurum ta faɗa miki hakan ko akwai sila? " Labarta mishi yadda akayi tayi kab. "To naji menene babban abinda ya sakaki kuka. Kasancewarki ba Ƴar Babangida ba, ko kasancewarki yarinyar da aka haifa bata hanyar aure ba? " Kallonshi tayi kamar tana nazari kana tace. "Kasancewata ba Ƴarshi ba" Sai yayi dariya yace. "Abu mai sauƙi. Babangida dai shine mahaifinki duniya da lahira Mardiyya. Wanda ma yace bashi ya haifeki ba wawane. Sabuwa tabbas mahaifiyarki ce. Kawai basu sameki ta hanyar aure bane. Wannan kuma ƙaddarace data sameki amman fa kinfi waɗanda aka haifa ta hanyar aure ta wasu fuskokin sau dubun dubata. Shekararki sha bakwai amman gashi kin zama Malama. Ko kusa kada kiji zafin Babangida ko Sabuwa sabida ƙaddarace ta afka musu. Kuma a duk inda kike kiyi alfahari dasu sannan kada kiji ko ɗar wajen nunasu a matsayin iyaye. Allah daya tashi warware al'amarin sai aka haifoki kamarmu ɗaya dake, sakamakon kamar da mahaifinki yake yi dani, hatta muryarmu tafiyarmu babu bambanci da mahaifinki. Da kika tashi ɗebo kamar har sai tayi miki yawa. Wannan kaɗai abun misaline. Batun Auren mahaifiyarku hakane tayi aure tabbas" Kawu Manga ne ya shigo afujajan. "Yaya yaronnan Babangida wai yana asibiti kuma a mawuyacin hali mai tsanani." "To Manga Allah ya bashi lafiya kaje zamu zo ni da Mardiyya yanzu" Ajjiyar zuchiya kawu Manga yayi yace. "Shikenan Yaya sai kunzo" Ya saka kai ya fita. Kallon Mardiyya Baba Malam yayi tayi mai murmushi, shima murmushin yayi mata. "Sabida ke zanje asibitinnan. Ba dan ke ba har a sallamoshi bazanje ba." Wayarshi ya ɗaga ya kira wawo baiyi minti ashirin ba sai gashi Shi ya kaisu Asibiti acan suka tarar da matanshi, malama Babba, kawu Manga, da Kudidi. Malama Babba ta dubi Baba malam kanta a ƙasa tace. "Barka da zuwa Malam ashe zaka zo? " Murmushi yayi yace. "Zan zo Saratu. Yaya jikin nashi? " "To Malam tunda suka shiga basu fito ba balle muji halin da yake ciki" "Kinsan dalilin rashin lafiyar kuma? " Kai ta sauke ƙasa kawai tana ɗigar hawaye mai ciwo. Ga soyayyar malam na nuƙurƙusarta. "Hmm Allah ya kyauta" Idanunshi ya ƙurama Amir ya ɗago da sauri ya kalli Kawu Manga. "Manga yaushe Babangida ya haifi yaronnan ban sanshi ba?" "A_a Yaya yaron Amaryarshi ne da tazo dashi fa Amiru, yaron kam yayi kama da Babangida haka Allah yake ikonshi" Murmusawa Baba Malam yayi yace. "Mango hoo. Lallai wato ka ɗaure ma ƙarya ƙunƙuru. Ke Aisha ko? Saƙonki ya iso yarinya kin fallasa ta yadda aka sameta hankalinki ya kwanta. Amman daga nan asibitin ki tafi gidanku kinji abunda nace miki ko? Sannan wannan yarinyar da kike ji da gani jinin jikinace rayuwatace in baku sani ba ku sani." Hankalin ƴar Shuwa ba ƙaramin tashi yayi ba. Ai sai kuka da roƙon a rufa mata asirinta. Baba malam baima sake magana ba. "Ke Aisha kije kawai za'a nemeki daga baya. Amman baki kyauta ba kuma shi kanshi Babangida bazai taɓa jin daɗin wannan labarin ba. Amman angode Allah yarinyar tayi tawakkali sosai amfanin ilimin kenan" A sanyaye Ƴar shuwa ta juya tana tafe tana sharce hawaye hankalinta a mugun tashe shikenan asirinta ya tonu. Baba Malam yace Ramatu ta ɗan basu waje zaiyi magana. Baba Malam yana daga zaune a benci hannunshi riƙe dana Mardiyya. Ya dubi Sumy dake zaune a gefen Malama ga Amir a gefenta yace. "Shekararku nawa da yin aure da Babangida a ɓoye ba tare da an sani ba?" Shiru babu amsa kanta dai a ƙasa. "To naji in wannan kin kasa amsawa. Shi wannan yaron ta hanyar aure aka sameshi kamar su Aminuna. Ko shima kamar yadda aka samu Mardiyyana aka sameshi? Kafin ki bani amsa ɗago ki kalleni" Kai wawo ya girgiza kawai. A hankali Sumy ta ɗago ta kalleshi kwarjininshi ya daketa ainun. Sai kawai taji faɗar gaskiya a wannan gaɓar yafi mata alkhairi tunda ba ita kaɗai ke da shegen ba. Tana hawaye ta faɗa musu gaskiya da gaskiyar irin zaman da suka yi da Babangida a baya" Take numfarfashin Malama Babba da Baba malam, wannan karon har da Kawu manga suka soma hawa da sauka. Wawo da kudidi aka bari da sallallami. Nuna Malama Babba Baba Malam yayi yace. "Kinji da kunnenki halin ɗanki ko, in kin zargi Sabuwa sabida ɗiyar kawalice, ai yanzu kya zargemu tunda shi iyayenshi malamaine ko? Kuma nayi imani in kowa bai gane wannan ɗan na Babangida bane ke kin gane gudun tonuwar asirinshi a karo na barkate bazai barki kiyi magana ba. Babangida kenan sheɗancinshi tsoro yake bani wallahi. Wawo mayar dani gida kaji" Tashin hankali a wannan ranar dai an shigeshi sosai. Harda Kawu Manga aka raka Baba Malam gida mardiyya ma binsu tayi tana kusa dashi har turakarshi. "Manga kuje Gombe ku zauna da iyayen Hamida in dai batai aure ba ayi mata tayin dawowa ɗakinta inta amince shikenan kada ku baro Gombe har sai an ɗaura auren, in so samu ne ku tawo da Hameedan. Mardiyya kuma Wawo ka ɗauketa ka kaita gida ta kwaso duk kayansu ita da ƙannenta su dawo nan gidan da zama. Ke Ƙarama da ke Alawiyya ku gyara ma yarannan ɗakin ajjiya dake haguna, mazan kuma a gyara musu ɗakin dake kallo ɗakina" Ƙarama tace. "Kayayyakin ciki ina za'a kaisu Malam sannan za'a buƙaci fenti, sannan akwai buƙatar aima ɗakin karatu kafin a shiga shekara da shekaru ba'a taɓa zama a ciki ba. " "Kuyi magana da magajin Malam zai haɗo almajirai su yi sauka a ɗakunan. Kuɗin fentin zai bayar ya duba Safiyanu yayi fentin. Ko bayan raina Amiru inya tasa ku tabbatar an haɗashi aure da ƴar dake goye a bayan alawiyya in kuka ƙetare wannan umarnin ban yafe ba. Sannan a kira mun Sauban yazo ya sameni" Kawu manga yace. "Gobe sassafe zamu ɗauki hanya sha Allah. Za'ayi duk abinda kace ayi alƙawarinnan ya ƙullu Ƙarama ba daga nan ba ka fini sani. Wawo maza ɗauki Mardiyya kuje ni zan Zauna da Yaya" Ai kuwa haka su Mardiyya suka koma gidan Babansu. Ɗakin Malama Babba aka buɗe musu sabida ko sharar ɗakunan nasu ba'aiba bare ayi fenti. Babu wata damuwa a tattare da'ita sai ma labarin auren Umminsu data labartama su Aminu da umara da suka tafi, sukaita murna suna sanya ma umminsu albarka tare da mata adda'ar samun farin cikin aure. Ƴar shuwa tana ji tana gani dole ta tattare ƴan kayanta kala biyu. A madadin ta nufi gida saita nufi wajen Sameerah suka wuni suna sheƙe ayarsu ba ita ta dawo daga Bamaina ba sai daf magriba. A lokacin Mama tana zaune a gaban murhu. "Lafiya Shuwa da magriba haka, kuma na ganki da yara da jaka? " Zama tayi jagwab a kusa da Mama tare da labarta mata halin da ake ciki harda guntun hawayenta duk da irin farin ciki da nutsuwar data kwaso a wajen Sameerah dan ita nuna mata take yi ta rabu da Babangida ta huta kawai. Duk irin mijin da take so yanzu ne zata sameshi ta sake haskawa a duniya. Amman me sai take jin kamar ba zata taɓa iya rayuwa babu Babangida ba. Ta wani ɓangaren in ta tuno lolo na can umara harda ubanta sai ta soma canki cankar zaman gidan Babangida ko akasin hakan. Amman Allah cikin ikonshi saita canki zaman gidan Babangidan. "Aikin banza da wofi ni wallahi bai burgeni ba da baisa an sakeki ba wannan ƙaddararren auren. Kiyi zamanki yara dai tunda kinzo dasu ai shikenan. Shi yanzu akan Sabuwa har a kwantar dashi a asibiti? A wannan karon kam kafin ki koma zaki tafi da shirinki wallahi kinji na rantse biu zan kaiki Maiduguri garin bare bari sai kin mallakeshi kin takashi yadda kike so sannan kema zaki tafi ki barshi. Ki duba Sabuwa ci gaban data samu bakiji labarai a bakin Hauwa bane. Danma bana cin ribar zance ban gama ji duka ba na katseta. Amman har gida zancan zai sake biyo ni yanzu ma zan shiga gidan aminiyar Hauwan nasan zan jiyo mana komai Ku kula da girkinnan" Miƙewa Mama tayi tare da jan mayafi a igiya tayi waje. Ajjiyar zuchiya ƴar shuwa ta sauke tana gaban girkin tana ta mamaki. Mama bata dawo ba sai bayan magriba harda tsarabar dambu ta shigo. "Ke lallai Lolo ta samu duniya sosai ta kuma yi sa'a data shiga babban fimilin malamai haka. Hmm su Tabawa anata shiri suna dawowa daga umara za'ayi tarewar Tabawa tace zata gano mun komai da komai tunda kinsan sune kan gaba a bikin dan ko da matar Sama ta haihu da'ita akai suna lokacin su Sabuwa basu tafi ba. Taje mun banga gidan da aka sai musu ba babba gashi sun zuba sababbin kayan ɗaki ko'ina haske" Murmushin baƙin ciki ƴar Shuwa tayi kawai A wannan ranar ko gyangyaɗi batai ba sam yadda taga rana haka darenma ya kasance mata. Wannan kenan

Sabuwa: Malamanmu suke kula da lamuranmu malamai mata, maza ƴan uwansu maza ke kula da lamuran nasu. Cikin hukuncin Ubangiji muka shiga aikin ibada a aikace da izinin Allah a bisa jagorancin malamanmu, duk suna nuna mana a aikace ire irena suna da yawa waɗanda basu san komai ba. Ashe aikin ba aikin ragwaye bane jama' Bari in kawo muku yadda muka gudanar da umarar mu.

Yadda ake yin Umara. Umara ibadace mai matuƙar daraja a musulunci Wacce ake yinta a masallacin Harami a makka. Anayin umara a ko wanne lokaci ba kamar aikin Hajji da yake kasancewa daga shekara sai shekara ba. Ga yadda ake yin ibadar umara daki_daki.

1 shirin umara da shiga ihram:. Kafina fara umara, dole ne mutum ya shiga cikin yanayin ihram, wanda shi ne shirin ibadar umara.

Shiryawa kafin shiga ihram:. A wanke jiki sosai da wanka ( ghusl) domin tsarkakewa. A yanke farce, a cire gashi mara buƙata a jiki, a sanya turare ga maza kafin su shiga ihram A sanya tufafin ihram Maza su sanya zanin ihram biyu. Zani da riga maras ɗinki. Ba tare da huluna ko takalmi mai rufe yatsu ba. Mata su saka kayansu da suka saba sawa amman bana ado ba, ba zasu saka safar hannu ko niƙabi ba. Niyya da shiga ihram:. Ayi niyyar umara a zuchiya A faɗi labbayka umrah" Wanda ke nufin na amsa kiran Allah domin yin Umarah" Daga wannan lokacin, abubuwa kamar cire gashi, yin jima'i, sanya turare, da yanka dabba suna haramtuwa har sai an gama umarah Yin talbiyya: A fara karanta talbiyya ga muryar da tafi dacewa musamman ga maza. Aci gaba da yin talbiyya har sai an shiga makka Labbayka Allahumma labbayk, labbayka laa shareeka laka labbayk, innal hamda wan ni'imata laka wal mulk laa shaeka lak.

Shigowa masallacin Harami: A shiga da ƙafar dama tare da karanta: Allahummaftah li abwaba rahmatik ( ya Allah ka buɗe min ƙofofin rahamarka) Idan mutum ya ga ka'aba ya fuskanceta yayi addu'a domin wannan lokacin yana da matuƙar daraja.

Tawaf zagayawa kusa da ka'aba: Tawaf yana nufin zagayawa ka'aba sau bakwai 7 A fara daga hajar aswad Aci gaba da yin talbiyya har sai an shiga makka Labbayka Allahumma labbayk, labbayka laa shareeka laka labbayk, innal hamda wan ni'imata laka wal mulk laa shaeka lak.

Shigowa masallacin Harami: A shiga da ƙafar dama tare da karanta: Allahummaftah li abwaba rahmatik ( ya Allah ka buɗe min ƙofofin rahamarka) Idan mutum ya ga ka'aba ya fuskanceta yayi addu'a domin wannan lokacin yana da matuƙar daraja.

Tawaf zagayawa kusa da ka'aba: Tawaf yana nufin zagayawa ka'aba sau bakwai 7 A fara daga hajar aswad Idan za a iya taɓa shi da hanny da sumbatar shi, yayi kyau, idan ba zai yiwu ba a ɗaga hannu a faɗi Bismillah, Allahu akbar" Aci gaba da zagayawa bakwai a kusa da ka'aba. A karanta addu'o'i daban_daban yayin tawaf, ba lallai a karanta wani abu na musamman ba. Idan an kai rukun al yamani ( ƙarƙashin ka'aba ɗaya kafin hajar aswad) a taɓa shi idan zai yiwu ba tare da yin sumbata ba. A tsakanin Rukun al yamani da hajar Aswad ana karanta. Aci gaba da yin talbiyya har sai an shiga makka Labbayka Allahumma labbayk, labbayka laa shareeka laka labbayk, innal hamda wan ni'imata laka wal mulk laa shaeka lak.

Shigowa masallacin Harami: A shiga da ƙafar dama tare da karanta: Allahummaftah li abwaba rahmatik ( ya Allah ka buɗe min ƙofofin rahamarka) Idan mutum ya ga ka'aba ya fuskanceta yayi addu'a domin wannan lokacin yana da matuƙar daraja.

Tawaf zagayawa kusa da ka'aba: Tawaf yana nufin zagayawa ka'aba sau bakwai 7 A fara daga hajar aswad Idan za a iya taɓa shi da hanny da sumbatar shi, yayi kyau, idan ba zai yiwu ba a ɗaga hannu a faɗi Bismillah, Allahu akbar" Aci gaba da zagayawa bakwai a kusa da ka'aba. A karanta addu'o'i daban_daban yayin tawaf, ba lallai a karanta wani abu na musamman ba. Idan an kai rukun al yamani ( ƙarƙashin ka'aba ɗaya kafin hajar aswad) a taɓa shi idan zai yiwu ba tare da yin sumbata ba. A tsakanin Rukun al yamani da hajar Aswad ana karanta. Rabbana atina fid_duniya hasana wafil akirati hasana waƙina adhabannar Bayan an gama zagaye na bakwai tawaf ya cika

Yin sallah bayan tawaf: Bayan tawaf ayi sallah raka'a biyu a maƙam Ibrahim ko a wani guri na masallacin harami A raka'a ta farka a karanta tariha da suratul kafiru A ta biyi fatiha da suratul iklas

Yin sa, i : tafiya Tsakanin safa da marwa Tafiya zuwa safa Bayan sallar tawaf a tafi zuwa dutsen safa. A karanta Innas-safa-wal-warwata min sha'a'iril-lah.. A hau dutsen safa a fuskanci ka'aba a ɗaga hannu ayi addu'a ds kuma tasbihi.

Yin sa'i: tafiya tsakanin safa da marwa Daga safa zuwa marwa yana nufin zagaye ɗaya Daga marwa zuwa safa yana nufin zagaye biyu A haka akeyin zagaye har sai an cika bakwai Wato a ƙare a marwa Maza zasu yi gudu a yankin al mas'a'a ( wani wuri a ake ƙaiyade tsakanin sama da narwa) Ayi addu'o'i da tasbihi a ko wanne wuri Aske gashi ko ragewa Bayan an gama sa'i ana yin aski ko rage gashi Maza yafi kyau su aske gashin gaba ɗaya ko su rage daga dukkan ɓangarorin kai. Mata su yanke ɗan gashi kaɗan kimanin yatsan hannu ɗaya daga ko wanne ɓangare na kai Da zarar an gama aski ko rage gashi ana fita daga ihram, kuma Umara ta cika. Duk abubuwan da aka haramta a ihram sun halatta Bayan kammala umara Ana iya yin Sallah a masallacin harami Ayi addu'a da shukar Allah domin cikar ibada. Idan mutum yana son yin umara fiye da ɗaya sai ya fita zuwa masjid Aisha domin shiga sabuwar ihram. Zuwanmu da kwana biyu Alhaji Zaid shima ya iso. Ni da Maigogul gabaki ɗaya wani irin farin ciki ne shimfiɗe a fuskokinmu. Duk wata adda'a nayi ta alkhairan duniya dana lahira na roƙama kaina, ƴan uwana ƴaƴana aurena mijina, iyayena musamman Maigogul. Alhamdulillahi irin kukan da naga Maigogul yayi ta yi nayi imanin na nadamane da dana sanin rayuwa inaji yana faɗama Allah da muryar kuka. "Allah ni da kawalci har abada" Gashi wannan Hajiyan sai haba haba take yi damu. Ita ta rakani na saka haƙori na gwal Alhaji Zaidu ya dubeni bayan mun fito suna tsaye da Maigogul nayi dariya haƙorin ya bayyana Sai naga Maigogul yana share hawaye shima ya ƙara haƙorin makka a bakinshi. Kunsan mutumin naku babu dama ne. Idanu Alhaji Zaid ya kashe mun kawai Hajiya Balaraba kuwa hankalinta na kan Maigogul. To daga haka kuma muka dai siya tsarabar gida, Maigogul ya sai kaya da turaruka masu yawa. Nima na yima kaina ƙaramin akwati, zannuwan gadona a can na siya Alhaji Zaidu yace za'a saka kayan a jirgin kaya, nice harda siyan labule da irin kafet na larabawa mai kwalliya mai kyau. Zannuwan gado masu bargo manya nasai biyar harda maigida sakko mu gaisa, saina ƙara da ƙananu guda biyar Haka aka auna kayanmu zuwa Najeriya mu kuma muka nufi Dubai A bakin hotel ɗinmu muna tsaye da Hajiya Balaraba tace. "To Lolo ga katina dan Allah in kun dawo Najeriya ki kirani inaso muyi magana. Sannan inason zanyi magana da Alhaji Baba in babu damuwa" Murmushi nayi mata na juya muka kalli bayan Maigogul a tare nace. Babu damuwa Hajiya Balaraba nagode sosai Allah ya bar zumunci" Harna juya tace. "Af lolo ji mana" Juyowa nayi na dubeta. "Amm nace ba Maigogul matarshi ɗayane? Kiyi haƙuri kada kiji zafina Sabuwa wallahi ba laifina bane Allah ne ya jarabceni na sani, ina son abu mai kyau" Da murmushi da farin ciki a fuskata nace da'ita. Matanshi biyu kuma muna da yawa yaranshi. Amman Hajiya Balaraba ai namiji mijin mace huɗu ne. Ni kaina na muku sha'awar juna sosai. Kuma Maigogul mutum ne mai sauƙin kai sosai kuma shima zai soki na tabbatar. Ina ganin tunda kinji kina ra'ayinshi ku sasanta kanku kawai. In kika bani dama ma sai in shige miki gaba ki samu abinda zuchiyarki take so" Murmushi tayi ta ɗanji kunya har a fuskarta. "Bakya tsoron Hajiyarku taji labarin ke kika haɗa tayi fishi dake. Kinsan mata da ƙiyayyar kishiya?" Kunji wai Rakiya ce Hajiyarmu tayi tunanin Maigogul ai wani ƙusane, bare tana ta faɗin Alhaji Baba yasan abubbuwa masu tsada. Babu komai ai bama zasu ji ba. Muna da kyakkyawar alaƙa da Maigogul zamu kashe mu burne tare in dai kina ciki" Da haka mukai sallama akan saita jini in sha Allah. Gaga_gaga haka muka shiga Dubai cikin hukuncin Ubangiji bisa jagorancin Alhaji Zaidu mukai duk siyayyar data dace na akwati nice harda setin sarƙa da ɗankunne na zinare. Na sai kayan cin biki, na sai abubbuwa da dama. Maigogul ma yasai turaruka, da gogul, da takalma da agogoguna. Ɗakin hotel uku Alhaji Zaidu ya kama mana sai lelena yake yi. Da daddare yana shigowa ɗakina muyi hirarmu ta masoya, muji ɗumin junanmu. Maigogul kuma yana fita harabar hotel ɗin ya zauna a rumfa yana shan jus yana kallon kyau da tsarin hotel ɗin. Bayan mun kammala siyayyarmu muka tarkato muka dawo gida Najeriya muka kwana a kano washegari Alhaji Zaidu ya ɗauki mota ya mayar damu gida da tarin tulin kayanmu rigi_rigi Ganinmu ya hautsina gida da murna Gaza da Uzairu zuchiyata harda Murna, su Labbai sai tattaɓani suke yi suna farin ciki. Muma farin ciki fal ranmu wallahi. Da ƙyar na yakice na samu Alhaji Zaidu a falo na zuba mishi abinci yana ci yace. "Shakelena nan da sati biyu kuma sai mu shiga maganar tarewa kawai. Kinga banyi maganar kayan gado ba a Dubai ko? Sabida bazan iya jure har kayan su iso bane muna da kayayyakin waje a Kano zaki iya samun duk abinda kike so Uhm Shalelena?" Murmushi nayi mishi ya mayar mun har yana kashe ido ɗaya. "To kuɗin kayan gadon in tura a asusun bankin Alhaji Baba ko in tura a naki uhm? " Sai da naji faɗuwar gaba. Amman haka na daure nace. Sai yadda kace kaina bisa wuya ranka shi daɗe da girman kujerarka" "To shikenan zan tura miki a asusun bankin ki tunda sai kun shigo kano zaku siya. Sai kuɗin ɗinki da ragowar hidima ko? Kuɗin hidimar abincin biki da abincin tarban dangina masu zuwa ɗaukar Amarya zan tura a asusun Alhaji Baba. Shalelena ai musu tarbar da ba zasu mance ba. Wannan jan leshin da sarƙarki ita zaki saka in sun zo ɗaukarki ki fito kamar sarauniyar data lashe gasar kyau ta duniya nasan Hajiya da'ita za'azo. Tunda haka take maramun baya a duk aurena na baya. To bani labarin tanadin da kikai ma darenmu na farko uhm Shalelena sabida nima insan irin shirin da zanyi ma Shalelena uhm kinga inata tattalashi ai nayi ƙoƙari bana wasa ba. Inasone ya kasance na musamman mai tsayuwa a zuchiya da rai" Kallonshi nayi irin kallon da nasan lallai zan burkitashi a shagwaɓe nace. Harshe da haƙori ba zasu iya fasalta maka tanadin da nayi maka ba. Kai dai ka shirya ka zauna da shirinka kawai" Murmushi kawai yayi mun irinna cikar Dattijantaka Bai jima ba ya kama hanyar Kano Washegari ya sako mun manyan kuɗaɗe sosai na kayan ɗakina da na ɗinki da ragowar hidindimun biki dai. Nan muka shiga buɗe tsaraba ana rabawa su Adama kuma suna kan akwatunan lefe da su zannuwan gado dana siyo gida dai ya kaure da kacaniyar biki. Mun tura da ɗinki kano wajen wani tela da Sadiya ta haɗamu dashi. Na ba Labbai zanin gado babba mai bargo da ƙarami. Su Adama dama na siyo musu kayan fitar biki duk tare aka kai mana ɗinkin na biya. Alhaji Maigogul ma an cika mishi banki da kuɗi sai washe baki yake yi sunata hidimar zuwa Kasuwa da shi da Cicib A ranar da muka dawo na kira Hajiya Balaraba na feɗe mata biri har wutsiya a game da halin Maigogul da sana'arshi da halin da gidanmu ke ciki. Duk da kanta ya buga amma ta amince da aurenshi sabida ta riga da ta kamu har wuya na gani. Gefe na jashi na labarta mishi halin da ake ciki sabida murna rungumeni yayi tsam yana ta saka mun albarka na ɗauki lambar Hajiya Balaraba na danƙa mishi sauran aikin nasan nashi ne. "Lolo yanzu wannan matar dai ni take so? Allahu Akbar ashe kallon da take ta yi mun kenan? Lolo gaskiya kina sona, wallahi nima ina sonki fiye da kowa cikin Ƴaƴana" Ai kuwa kwananmu huɗu da dawowa da safe sai ga Maigogul ya leƙo ɗakinmu ya kirawoni na fito muka shiga ɗakin su Uzairu zuchiyata shima yana ciki "Lolo Hajiya Balaraba ta nemi son ganina domun mu tattauna batun aurenmu tunda mu ba yara bane mun riga da mun daidaita kanmu shine nace ko zaku rakani ke da Uzairu zuchiyata tunda ke kika haɗa abun ta inda aka hau tanan ake sauka. Ku shirya muje yau mu samu mu dawo danma Cicib baya nanne dama da shi zai rakani" Fita a ɗakin yayi zuwa shiryawa, Uzairu zuchiyata ya dubeni baki har kunne niko na labarta mishi ai sai ya miƙe da daka tsalle harda ihunshi. "Lolo shima Dad wuf za'ayi dashi kenan hiye Kece ma kika haɗa ki kuka da kanki in Rakiya taji wannan labarin ke da ita yaƙare wallahi yadda take kishin Dad abun azimun. Gashi tunda kuka dawo an samu canji sosai agun Maigogul kiga jiya tujarar da Rakiya ta sakar mishi amman bai kula ba Mrs BUKHARI

Son so💪🏼 [10/4, 10:29 PM] +234 810 593 2041: MRS BUKHARI 14

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull