Idan kaya ya gaji book book 4 - Chapter 14
Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 14: Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 14. Kiga jiya tijarar da Rakiya ta sakar mishi amman babu abunda yace mata…
3,819 words
Kiga jiya tijarar da Rakiya ta sakar mishi amman babu abunda yace mata har saida ta ƙureshi ne ya cire rigarshi ya doka da ƙasa to da dai taga ranshi yayi mummunan ɓaci shine tayi shiru. Da dane ai wallahi da sai sun daku ya wuni yana tijara. Lolo gaskiya dai mu zuwa Canada ya zame mana dalilin alkhairi tunda dai a ta dalilin canadan kuka haɗu da Alhaji Zaid harya aureki, ta dalilin dai kuka je Umara har Maigogul akayi gamo dashi. Kinsan Allah dama shi ba nanan bane sam yaushe su Rakiya suka yi macin dashi ƙaddarace da talauci kawai ta haɗe su waje guda ai ya fisu kilas" Uzairu zuchiyata kai dai wallahi ka iya bakin ka narantse maka da Allah. Bari inje in shirya mu tafi." Nan da nan muka shirya gashi yau su Mardiyya suka ce mun zasu zo karɓar tsarabarsu sai kiransu nayi nace su bari tukunna gobe inna dawo zanje wajen Baba malam zan tafi musu da tsarabar sai mu haɗu acan tunda ta labarta mun halin da Babansu yake ciki sanadin jin labarin Aurena. Amman yarinyarnan sabida tarbiyyya da tsananin kunya bata faɗa mun ta samu sanin asalinta ba, ta dai cemun sun koma ƙarƙashin kulawar Baba Malam. Allah sarki wallahi shi yasa ban mance dashi ba nayo mishi tsaraba mai kyau sosai gobe na ƙuɗurce a raina zanje dama. Cikin minti talatin muka fito Wallahi Maigogul zaku ɗauka gwamnane tsabar kyau da caɓa kayan ado. Turarukanshi kuwa ƙamshinsu saida suka danne namu tas babu yadda muka iya. "Wai nace Maigogul inata magana tun a ɗaki kayi banza dani. Nifa naga kwana biyunnan ka sauya koma ince tunda ka dawo umara gabaki ɗaya ka zama wani iri ko fita ka dena yi Allah yasa lafiya ya zakaita zama a gida haka? " Murmushi yayi yana gyara agogon hannunshi yace. "Rakiya kayi nayi kenan. Kamar kinfi sha'awar ganin ina biye miki muna buyagi ko? To ni Allah ya shiryeni ya tarfama garina nono. Lolo yarinyarnan ta zaunar dani munyi magana sosai wallahi Rakiya na fahimci kusakuraina Allah yasa ki fahimci naki shashashar mace wacce bata san komai ba sai jaraba, in baki yi wasa ba sai kinci yari nake faɗa miki. Ku muje abinku mu mun tafi Kano sai Allah ya dawo damu." Sauka muka yi muka bar Rakiya a tsaye illahirin mamaki ya kamata sama da ƙasa ta rasa me zata ce sai ido kawai da aka batta dashi. A wata ƙatuwar jeep muka nufi hanyar Kano muna tafe Maigogul na ba Uzairu zuchiyata labarin umara da irin taimakon da Hajiya Balaraba tayi mana. "Wallahi ashe ita kuma ni take so nifa banyi mamaki ba. Sabida mata da yawa suna tallatamun kansu in auresu basa dai gabanane na gidanma yaya na'iya dasu. Akwai wacce ma tace zata sha guba in fa ban aureta ba wallahi. Nace ai kuwa sai dai tasha fitinar Rakiya da ace ni ɗin ba jan wuya bane ai da yanzu ta kaini ƙasa nake faɗa muku. Gaskiya kusan ko da yaushe muka je biki ko dai wani taron manya ina samun mata kusan uku da zasu nuna ra'ayina. Ina da jama'a sosai kuma ina da farin jini sosai da sosai. Kai da Lolo ai farin jinina kuka ɗebo, duk da ita kanta Kayi nayi tayi Sharafi sosai" Dariya muka yi duka Uzairu Zuchiyata yace. "To ai Dad wallahi kayi ne dole mata suce suna sonka kamar Hauwa ma ita tace tana sonka ko? " Wannan dariyar yayi yace. "Har da gyatumar taka ma ita ta ƙyalla ta ganni tace tana so da dai naga itama ba baya ba wajen kyau saina yadda na aureta gata da gashi" Haka Uzairu zuchiyata yaita takalo Maigogul shi kuma bil haƙƙi yaita bashi labarai da wanda ya dace da wanda ma bai dacen ba duk shi kaɗai Ni dai dariya kawai aka barni dayi.
Babangida:.
Kwananshi biyu a asibiti baima san inda kanshi yake ba, sau ɗaya ya farka ya sake komawa bacci. Ta ɓangaren su kawu Manga sunje gombe kuma Allah cikin ikonshi sun tadda Hameeda tananan batai aure ba, ko da mahaifinta ya kirata ya sanar mata da abinda ke tafe dasu Kawu Manga sai taji ta amince dama tana son mijinta kuma a hakanma tana yawan tura mishi saƙon gaisuwa da tambayar yara, tun yana ce mata yara suna lafiya sai taga to bari ta shigar da kanta a karo na biyu ko zata dace tunda har zuwa lokacin babu wani tsayayye ga takurawar iyaye da sosaitin da muke ciki daya addabeta. Dama ire iren tsangwamarnan ke sawa bazawara ta koma gidanta ko babu daɗi, ko kuma duk wanda yazo ta amince mishi ko ya cancanta ko bai cancanta ba. Hameeda ta amince Kawu Manga da kanshi ya bata sadakinta dubu hamsin a ranar aka mayar da auren. Su su kawu Manga suka tawo da Hameeda da ƙanwar mahaifiyarta. Washegari motar kaya ta biyosu sukai jerensu tas a ɗakin Sabuwa, sannan kuma suka shiga sunturin asibiti su ukun. Ƴar Shuwa dai tana gidansu shiru shiru babu wanda yazo itama bata je ba tana tsoron Baba Malam dan tasan bashi da daɗi. A hankali Babangida ya buɗe idanunshi a rana ta uku kenan. Hameeda tana zaune tayi tagumi tana ta saƙe _saƙe a ranta, Ramatu kuma shigowar tata kenan suka ga ya farka, Ramatu ce ta juya ta kira likita yazo. "Ku ɗan bamu waje dan Allah" Ya faɗa a ɗaure tare da juyowa kan Babangida. Babangida kuwa ƙirjinshi da kanshi ne suka mai wani irin nauyi sosai ya kaɗu hankalinshi ya tashi matuƙa da jin labarin aure Sabuwa, to amman yaya zaiyi bashi da tsumi bashi da dabara. Soyayya kuma gaskiyace zaici gaba da roƙon Allah ya yakice mishi soyayyarta a zuchiyarshi da jininshi ko zai huta. Nan likita ya gama yi mishi aune aune da gwaje gwajen da zaiyi mai da tambayoyi biyu dai. Babangida kuwa Allah kawai yake ambato yana neman ya cire mishi tunanin matar wani a zuchiyarshi. "Astagafurullah Astagafurullah Astagafurul" Abinda yaita nanatawa kenan har su Hameeda suka shigo. Shayi Hameeda ta haɗa mishi mai kauri ta bashi daidai sha. Yana son tambayarta amman bata tata yake yi ba ta kanshi yake yi tukunna. Yasa hannu ya karɓa yana sha a hankali sakamakon ɗaci da bakinshi yake yi mishi. Malama Babba da Mustapha da Adeeza ne suka shigo Ramatu tayi maza ta miƙe taba Malama waje. "Babana ka tashi? " "Natashi Malama Baba Malam yazo kuwa? " A sanyaye yake magana kamar baida laka. Mustapha ne yace. "Kwananka uku a kwance, kwanaki biyu duk yazo yaune kawai baizo ba. Babangida ni abinda nake so dakai tunda komai ya ƙare a tsakaninka da Sabuwa ya kamata shiga damuwa a kanta ya isa haka kuma. Kaga dole dama ba zata dauwama a zaune babu aure ba in ba dai jarabawa ta samu ba wanda kuma bama mata fatan hakan. Ba daidai bane ka zube dan kawai kaji Sabuwa tayi aure ba. Ya kake tunanin iyali zasu ji? " Idanu ya lumshe kawai baice komai ba malama tace. "Sannu Babana yaya kake jin jikin naka yanzu? " "Ina jin jiri sosai amman gida nake son in koma a sallameni babu komai. Kuma abinda ya farunma ba da gangan bane ƙaddarallah. " "Hakane Babana babu komai Mustapha a tambayi likita ko za'a iya bashi sallama ai sai mu tafi gidana yaje can ya ƙarashe jinyar" Fita Mustapha yayi yana fita su Mardiyya da Baba Malam suna shigowa. Da sauri Malama Babba ta miƙe cike da girmamawa take tayi mishi sannu. Babangida ya kallesu yana jin wani irin zafi a zuchiyarshi daya kasance silar raba auren lalle. "Kai ya jikin naka? " "Da sauƙi Baba Malam " "To madallah. Sannunku ku kuma da ƙoƙarin jinya Allah ya ba da lada ko? " Su Hameeda suka amsa da Ameen. Su mardiyyane suka ƙarasa suka duba Baban nasu da jiki mardiyya sai kallonshi take yi, shima idanshi a kanta. Cikin dai ƙanƙanin lokaci aka sallami Babangida tare da kafa mishi dokiki da bashi magungunanshi. Dake likitan ma na gidane yace zaici gaba da kulawa da Babangida a gida har zuwa ya warke Malam ne ya hana Babangida bin Malama yace yaje iyalanshi suyi mishi jinya. "Yaro anƙi a barshi ya girma yanzu wannan gona_gonan shine sai an tafi dashi jinya? Kai Babba son Babangida zai halakaki" Ganin su Mardiyya sun bisu Baba malam ne yake tambayar Mustapha dake tuƙasu zuwa gida su suna gaba su Malama su huɗu a baya. "Ai sun koma gidanku. Hameeda kuma ta yi jere a ɗakin Sabuwa zaka ji bayanin koma menene ka bari jikinka ya warware ukunna" "Allah sarki." Kwanan Babangida biyu a ɗakin Hameeda ita ya tambaya ta bashi labarin iyakar abinda ta sani na game da komen aurensu. Ragowar zancan Malama ce tayi mishi. Idanu ya runtse kawai ya shiga hawaye mai zafin gaske. "Shikenan hankalin Aisha ya kwanta ta fallasa asirin gidana. Allah sarki Mardiyya baiwar Allah yarinya mai haƙuri. Malama ba dan ina tsoron fishin Baba Malam ba dana sallami Aisha wallahi. Na tsaneta fiye da tunani, kuma abadan bazan sake ganin girmanta ba, wanne irin zama zanyi da'ita? Har zata ce Mardiyya ba jinina bace to jinin uban waye ita" "A_a Baba kada ka sallameta ka dakata kaji me malam zaice kawai. Amman Baba ai ka bani mamaki kasa na washi yarinyar mutane kai ashe daduro ka ajjiye harda rabon ɗa wannan sheɗanci naka da yawa yake Babangida. Idan kasan akwai wani abu da kake ɓoyewa gara ka bayyanashi tun wuri zuchiyata ta samu ta buga lokaci guda kawai ka huta. Batun mardiyya ba ƴarka bace baima taso ba yarinya kamarka ɗaya da'ita har shi Amir ɗin Babu kokonto ɗankane na jini. Baba kayi iyakar yinka kaje ka roƙi gafarar mahaifinka ya yafe maka. Haƙiƙa ka sake saka Malam a cikin wani hali ina tsoro kada kayi sanadin mutuwar malam Babangida " Hawayenta ta share shima ya share nashi yace. "Zan roƙi gafararshi kuma dan Allah ki rakani muje tare har kema ki roƙi gafararshi ko Allah zaisa ya mayar dake" "To Allah yasa Baba ai zanso sosai sai dai in bai samu bane shine zan haƙura" Sun daɗe suna rarrashin juna zuwa can su Kudidi dasu Wawo da yaran ɗakin malama Ƙarama harma da'ita suka zo duba jikin nashi sun daɗe sosai dai anata tattauna abubbuwa marasa daɗi Babba taƙi sakewa tunda ƙarama ta shigo Awa ɗaya tayi ta tafi tace iyakar ƙa'idar da malam ya bata kenan Bashiru ya tafi mayar da'ita Su Babba kuwa saida sukai la'asar suka fita Babangida na zaune a saman kujerar Hameeda ƙwaƙwalwarshi na hasko mishi hoton Sabuwa a umara tare da sabon mijinta. Istirifari ya shiga karantowa a haka Hameeda ta shigo Usama na biye da'ita ta ajjiye mishi farfesun kaza. Hameeda ta canja sosai tayi mugun laushi ga wani rama da duhu da tayi. Zamanta ke da wuya sai ga Mardiyya da Sauban sunyo sallama sun shigo hannun Sauban shaƙe da kayan shayi da su lemo da ayaba. Durƙusawa Mardiyya tayi tace. "Baba ina wuni ya ƙarfin jikin?" Illahirin kunya ai saita kama Babangida harma yake jin tsoro_tsoron Mardiyya gami da jin kamar ƙasa ta tsage ya faɗa. "Baban Usama Mardiyya na gaisheka hala baka ji ba ko. Mardiyya ina su Aminu da Malama" Ta ƙarashe da tambayarta ƴan uwan nata. "Suna nan lafiya lau suma zasu zo anjima" Babangida da ƙyar ya ɗago ya amsa gaisuwar Mardiyya a ɗarare yana ta kallonta a ido a ido. Sauban ma ya matso yayi gaisuwa tare da tambayar jikin nashi. Miƙewa Mardiyya tayi ta ja Usama suka fita ɗakin yayi shiru na lokaci mai tsayin gaske duk su ukun da abinda suke saƙawa a zuchiyoyinsu. Can dai Babangida yayi namijin ƙoƙarin duban Sauban yace. "Yanzu ka riga kaji dalilin Sa'a na ƙin aurenka da Mardiyya ko tunda naji ance Baba Malam ya nemi ku gana. Sauban har yanzu kana kan bakanka na wannan auren, kuma ka tabbatar zaka riƙeta da mutunci domin wallahi bazan iya ɗauka inga Mardiyya a wani hali ba sanadin kuskuren da mu muka aikata shi" Sauban cikin matsananciyar kunya mai girma muryarshi har rawa take yi sabida kunya yace. "Ta ɓangarena wallahi Baba ko da da gaske ba kai bane Mahaifin mardiyya ba. Babu gudu babu ja da baya. Sabida mardiyya ta samu tarbiyyar da mu bamu samu irinta ba Baba bugu da ƙari gata malama mahaddaciya wannan kaɗai ya mayar da'ita mai nagartar da ba ko wanne Ɗa ba" Ajjiyar zuchiya Babangida ya sauke yace. "Madallah dakai Sauban. Allah ya dafa muku ku haifi haula mai albarka. Mardiyyata wallahi ki sani duk duniya baki da uba masoyi kamata a kanki raina fansane. Abinda zance dake shine kiyi haƙuri haƙiƙa naso zaunar dake in faɗa miki asalinki domun gudun ir.... "Baba dan Allah ka dena bani haƙurinnan. Dani daku bamu isa mun canja abinda Allah ya ƙadarta mana ba. Ina alfahari daku musamman ummi domin duk wannan tarbiyyar ita ta bamu kuma tayi tsaye a kanmu dan gani mun bambamta. Baba wallahi duk inda muka shiga mukai mu'amala da mutane sai ance madallah da uwar data jajirce wajen bamu tarbiyya. Baba ka dena damuwa dan Allah" Shiru Babangida yayi yana jujjuya maganganun mardiyya. Illahirin kunya cakuɗe da nadamar rashin tsayuwa kan iyalinshi ya shigeshi sai girgiza kai kawai yake yi har suka tafi bai iya sake furta wani abun game da wannan maganar ba. Face adda'a da yai ta yi musu. Da haka suka tafi. Gaga gaga haka Babangida yaita jinyar jikinshi da zuchiyarshi, a hakan aketa rabon kwana duk da sanin sun san bazai iya komai ba. Ƴar shuwa kuma tana can gida. Ranar da Babangida jikin yayi mishi dama_dama sai ya ɗauki mashin kai tsaye sai wajen Malama Babba. Daga wajenta suka nufi gidan Kawu Manga shi yayi musu jagora zuwa makaranta ofishin malam yana zaune akan kafet dake malale da ofishin suna cin abinci tare da mardiyya suna dariya kamar labari ma yake bata. Yana ganin Babangida ya miƙe tsaye sai Kawu manga ne yace. "Yaya dan Allah ka sauraremu. Mardiyya zo ki bamu waje" Da sauri ta bar cikin ofishin. Aka kaɗa aka raya Baba Malam ya zauna wallahi fur yaƙi zama Malama da Babangida sai roƙon gafararshi suke yi shi kuwa Dattijon bayanshi a juye yana sharce hawaye lallai akwai baƙin ciki danƙare a ƙirjinshi. "Haƙiƙa Allah ne ya jarabceni da kai Babangida. Kuma na karɓi ƙaddarata hannu bibbiyu. Ita kanta uwarka Allahne ya jarabceni da'ita domin bataimun halakciba sam. Ashe kai sheɗan ke buga maka ganga kana ta didimarka kana cin amanar iyayenka, Ubangijinka, malumta. Kuma uwarka da tasan halin da kake ciki bata iya sanar mun ba bata iya kwaɓa maka ba kullum cikin kareka take yi. Kai kuma a lokacin kana ji da ƙuruciya da dukiya sai kaita sheƙe ayarka. Ka ajjiye dadiro kuka haihu da'ita kake ɗaukar nauyin ɗawainiyarta, kake rabon kwana da'ita. Ina ƙuruciyar ina dukiyar yanzu, ina abokan naka masu ruɗarka. Duk girma ya soma kamasu ko, yaransu sun soma girbe musu abunda suka shuka ko? Hmmmm Juyowa Malam yayi ya saka kai ya fice abunshi. Malama Babba tayi zaman dirshan tana ta kuka, Babangida kuwa kukan zuchi yake yi idanunshi sun soye baya jin akwai ragowar hawaye kuma. "Inaga mu sake saka lokaci dan Allah" Cewar Kawu Manga da yake shirin tafiya ya barsu nan. "Manga" Malama babba ta ambaci sunanshi dalilin daya tilasta mishi juyowa fuska a murtuke. "Kaima kana fishi da ɗan naka ko, ya kaika maƙura ko? " "Ai dole duk haƙurina saida yaronnan ya kaini bango. Na ɗaga mishi ƙafane sabida dalilin ya rigaya da ya tuba kuma yayi ƙoƙarin rufe sirrin gudun tonuwar asirinshi. Babba hannunka baya ruɓewa ka yanke ka jefar. Allah ya bamu alkhairi" Ya saka kai ya fice. Suma a sanyaye suka fice Babangida a gidan Malama ya kwanta aka lulluɓeshi zazzaɓi ƙaƙas saida ya haɗiyi fanado yayi bacci shine ya samu dama dama ya rarrafa ya tafi gida kuma. Haka al'amura suka ci gaba da gudana.
ƳAR SHUWA:. Ta ɓangaren Ƴar shuwa duk da tana cikin damuwa da son komawa ɗakinta bai hanata zuwa Bamaina wajen Sameerah sun sheƙe ayarsu ba. Kana taje Abuja wajen Zarah kwana ma tayi sukutum ta dawo da kayan alatu da kuɗaɗen da yasa ta raina Sameerah domin taga masu yi da gaske kuma taga riritawa da tarairayar da tafi ta wajen Sameerah yanzu ne ma ta soma gane daɗin abun wa'iyazubillah Astagafurullah. ( kuyi haƙuri ina tsallake abubbuwa da yawa in nazo wajen Ƴar Shuwa da su Sameerah gudun matsala) Amman data dawo gida tazo ta haɗu da ƙannenta sai taji tana kewar ɗakinta ganin damuwar da Ƴar shuwa ta shiga yayi yawa yasa ta ɗauketa suka tafi maiduguri basu tsaya ko ina ba sai Biu anan suka zubar da maƙudan kuɗaɗe domin a shawo kan Babangida yazo da kanshi ya dawo da matarshi. Kafin su Dawo Malam yasa an zo an tafi dasu Faty an kaisu wajen Ramatu Magunguna da hayaƙe hayaƙen iska aka basu suka kwana uku suka dawo tayi duk abin da boka ya umarceta ranar da su Sabuwa suka dawo daga Umara ranar ta gama magungunan ta ɗaga waya ta kira Babangida amman fa magani kamar baici ba dan bai ɗauki wayar ba a lokacin, kuma bai biyo kiran ba har washegari. Da kuka ƴar shuwa kawai ta tashi mama tayi mata alƙawarin zata je har gida ta samu Babangida taji abinda yake nufi da'ita. Ai kuwa bayan kwana biyu da hakan da daddare irin takwas da rabi a ƙofar gidan Babangida tayi musu Mama ce ta shiga, ita kuma ƴar Shuwa ta shiga gidan Kulu. "hummm Maman Fati kece da daddare haka? Kinga Jami ma tana ciki ki shiga mana" Shiga ciki Ƴar Shuwa tayi ta nemi kusa da Jamee ta zauna. "Wayarki bata shiga Maman Fati ga gulma amman babu damar ayita." "Jami ai gani nazo zaman gidan ya isheni sosai gaskiya kai gida babu daɗi" Kulu ce ta shigo da dariya ga abinci a tire ta ciko musu kifi zuƙu zuƙu. "To ku sakko muna ci ana gulmar. Amman Maman Fati dawowa dai kika yi ko? " Sai da Ƴar shuwa ta zauna ta saka kifi a bakinta kafin ta labarta musu tare da Mama suke. Jami tace. "Tabb to wallahi an yanka ta tashi ke kin tafi kin bar baya da ƙura kinga dai na farko su Mardiyya sun koma gidan surukanku. Na biyu shine mijinku ya dawo da Mamansu Usama" Ai ba shiri man kan Ƴar Shuwa ya shiga tsiyaya hankalinta ko dubune saida duk suka tashi tsaye. "Hameeda ta dawo kuka ce daga tafiyata? Habawa shi yasa Babangida yaƙi zuwa biko sai mu muka biyo shi mana. Ni tsorona ma kada ya bani takaddata dan bai ɗauki saki a bakin komai ba. Ni na shiga ukuna" Ai sai ta soma hawayen baƙin ciki tare da nadamar fasa wannan ƙwai da tayi. Harfa gidan Sa'a taje amman Sa'a tace bata da wani abunda zata iyayi akai tayi haƙuri har sai Malam ya waiwayeta dan shi kaɗai ke da ikon cewa ta koma ɗakinta tunda shi yace ta tafin. Yanzu ga mummunan labarin dawowar Hameeda ta samu gashi su Mardiyya sun mata nisa yanzu ba zata iya sanin halin da suke ciki ba bare ta saka idanu akan asirin da tayi yaci ko baici ba duk da tana fatan taji ana labarin mardiyya ta samu ciki tana wannan fatan. "Ohh ni Ƴar shuwa ya kamar ruwa nason ya ƙarema ɗan kada ne? " Kulu tace. "In ɗan kada yaso ba. Kizo muje wajen Malam ai yayi miki aiki kin gani ba sai ki koma ba. Ko kuma shi uban mijin kuje kui tayi mishi magiya ko za'a dace" Ajjiyar zuchiya ƴar Shuwa ta sauke bata ce uffan ba suka jiyo sallamar Mama. Tashi ƴar Shuwa tayi suka fito suka samu Mama. "Sai mu koma gida. Babangida dai yayi fur yace ba zaki dawo ba sai dai muje wajen ubanshi tunda umarninshi ne. Yana ɗakin Hameeda ashe mitsiyaciyar matsawarki har ya bata damar dawowa ta ci ado sai ƙamshi suke yi ta tusa kaza a gaba tana sharɓar romon" Jami tace. "Ai sana'a take yi tunda ta dawo kuma ana siye kunsan kayan ruwa da albarka zoɓo dasu kunun zaƙi take saidawa, naga yauma ta kwaɓa cincin da mutufib ( meat pie) wallahi ciniki take yi sosai." Ƴar shuwa tace da firiza ta tawo kenan? " "Ƙaton gaske ma kuwa bawo biyu take yi na zobo bawo ɗaya na kunu wuni ake zuwa siye." Ranar dai ƴar Shuwa da baƙin da takaici gami da taraddadi suka tafi gida. Gashi Mama ta rantse ita ba zata je wajen Baba malam ba ita fatanta da burinta Ƴar Shuwa ta kashe auren kawai. Gyaran ɗakin shirgin gidan Ƴar Shuwa ta soma yi kwanciyar matsi ya isheta bare tana jinta a cikin kuɗi Zarah ta buɗe mata bakin ajjihu. Fenti tasa akayi a duka gidan aka felasce tsakar gidan, ƴar Shuwa ta siyo manyan katifu biyu ɗaya ta ba Mama ɗayar ta saka a ɗakin data gyara suka koma ita da ƙannenta. Amman fa hankalinta yaƙi kwanciya gashi gulma har gida kwatsam suna zaune suna cin abinci sai ga Hauwa ta shigo tana murmushi. "Hauwa kece a tafe? " "Wash Allah jikin tsufa nice wallahi kin ganni rabon minti nazo yi nan da sati biyu Sabuwa zata tare. Sun dawo ita da uban wai kinga kayan akwatin yarinyarnan harda setin gwal fa banda kayayyaki masu tsadar da tunda uwata ta haifeni ban taɓa ganin irinsu ba. Ɗinkin bikinma Kano ta tura ayo mata tela namiji fa. Mijin kuwa ya sake bakin ajjihu ya ɗauke nauyin komai ke hatta abincin Ƴan biki, da kayan ɗakin Sabuwa ya fa ɗauke komai." Nan take ƴar Shuwa ta sake ruɗewa ta birkice sosai dan ɗaki ta koma ta takure waje guda ta dinga aikin kuka kashirɓan. Hauwa dai ta gama gulmarta ta fice zuwa rabon minti har Mama ta ba cingam kuma tayi mata alƙawarin zata zo inma ta kama har kano sai aje dasu in ta samu dama, in bata samu bama tana da c i d Wannan kenan
Mrs Bukhari Mu kwana lafiya [10/4, 10:29 PM] +234 810 593 2041: https://chat.whatsapp.com/JhqzMy5IC6V7wZpDxerUWh?mode=ems_copy_t
*INA WAƊANDA SUKE TA JIRAN A GAMA ADASHE IN KAFA WANI DOMIN SUMA SU MALLAKI NASU* *NESA TAZO KUSA HAJIYA KAYAN MRS BUKHARI GIDAN ƘANSHI INGANTATTUNE KI SHIGA KI MALLAKI NAKI CIKIN SAUƘI* *2K DUK SATI KI KWASHI KAYAN DUBU HAMSIN HAJIYA KI MORI ƘAMSHI MAƘOTANKI MA SU MORE* *IN KINSAN BA ADASHE ZAKI YI BA KADA KI SHIGA*
*ZAN KOYA MUKU YADDA ZAKU YI KABBASA YA KAMA KAYANKU SOSAI*
*ZAN KOYA MUKU YADDA AKE ƘONA ITACEN TURARE YA KAMA GIDA YAFI SATI YANA ƘAMSHI*
*SANNAN AKWAI KYAUTA TA MUSAMMAN A KO WANNE BOX HAJIYATA GARAƁASAR TAYI MA MUKU YAWA.* *DUK WACCE TASAN DA GASKE ZATA YI GA LINK TA SHIGA, IN KINSAN BA YI ZAKIYI BA NA ROƘEKI DA GIRMAN ALLAH KADA KI SHIGA*
MRS BUKHARI 15
SABUWA:.
KANO.