Kenza eBookz

Idan kaya ya gaji book book 4 - Chapter 15

Idan kaya ya gaji book book 4 - Chapter 15

Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 15: Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 15. Mun shiga kano cikin amince da yaddar Allah. Abinda ya bamu mamaki…

3,416 words

Mun shiga kano cikin amince da yaddar Allah. Abinda ya bamu mamaki unguwa kawai Hajiya Balaraba ta faɗa ma Magogul ya ɗauki hanya kawai mukaita tafiya sai murmusawa yake yi Allah kaɗai yasan abinda yake saƙawa a ranshi. Kenan Maigogul yasan Kano sosai fa kenan? Ko da yake garuruwan daya zaga ai suna da yawa Wallahi ni kaina ina taya shi murna sosai ina fatan su Daidaita a tsakaninsu. Duk da Hajiya Balaraba ta tabbatarmun tana son Maigogul a haka zata wanke kayanta ta Aura. Idanuna na lumshe harma na hango al'amuran gidanmu da izinin Allah sun sassauta Maigogul in ya samu mafaka a wajen Hajiya Balaraba ni kuma sai inji da sauran irinsu Gaza, mata matan ma in sha Allah ba barinsu zanyi a baya ba, ni basai Alhaji yayi mun komai ba in ya taimakeni akan ƴan uwana ma wallahi shikenan nagode Allah Rayuwarsu tafi mun tawa rayuwar mahimmanci inaso inga gidanmu ya zama kamar sauran ragowar gidaje. Duk da nasan ba'a ɓari a kwashe a ƙallah dai al'amura zasu ɗan daidaita, in Allah ya dafa ma sai komai ya zama tarihi. A ƙofar wani katafaren gida muka tsaya Maigogul na duba lambar gidan "Yauwa ga gidannan Lolo kira mana ita kice gamu mun iso" Ya ƙarashe yana dariya haɗe da gyara tsayuwar hularshi. Dash bot ya buɗe ya ɗakko kwalbar turare na musamman ya feffesa a jikinshi, ya zazzagi farar hoda fashion mai farin gida da jan murfi kun ganeta ai? , ya murza a hannunshi ya shafe fuskarshi da'ita, ya dankwali yawu ya kwantar da gashin girarshi ya sake fitowa yayi fes duk ɗan maiƙon fuskarahi ya biyu wallahi. "Dad kenan babu wasa. Yanzu itace da wannan gidan? To aini in su Felisha sun zo najeriya sai dai in kawo su nan wallahi unguwar kawai abun kallone. Gaskiya Dad kana da Sa'a, nifa kai zan biyo wallahi zanyi agolanci fes" Dariya kawai yayi mishi baice uffan ba. Kiran Hajiya Balaraba nayi na faɗa mata gamu mun iso tace zata turo maigadi zai buɗe mana get. Ba'a jima ba maigadin ya leƙo ya kallemu ya juya da sauri ya buɗe mana get muka shiga. Abinda ya sake ƙawata gidan a idan mai kallo bai wuci yadda aka ƙayata gidan da shuke_ shuken fulawowi ba, ga wasu zomaye sunata cin fulawowi a tsakar gidan har ɗawusi ne a gidan da irin agwagin turawannan gigs farare ɗima ɗima. "Tabbb kuɗi suna inda suke lolo kunga waje? " Cewar Maigogul daya fito yana jingine a jikin mota yana ƙarema gidan da motoci kallo. Ni kaina ko kusa banyi zato Hajiya Balaraba takai haka kuɗi ba, na dai yi tunanin rufin asiri gareta Wata matashiyace ta iso inda muke bayan ta gaishemu tace mu biyota. A baya mukaita binta har zuwa babban falon gidan da yasha fararen kujerun leda komai tsab dashi ga turaren wuta an kunna a burner sai tashin ƙamshi mai sanyi da sauke ni'ima yake yi. Ni dai turaren yayi mini sosai wallahi bamma taɓa jin turare mai inganci irinshi ba. ( ga dama a gareki in dai da gaske kina son kayan ƙamshi ga link nan ki faɗa group ɗin adashe ba zaki yi dana sani ba, kuma akwai kyauta ta musamman da zan ba kowa bayan an gama adashen dan Allah in kinsan ba adashe zaki yi ba kada ki shiga naroƙeki da girman Allah 2k ne zubi duk sati, amman zaki iya haɗawa ki zuba 8k a wata) "Ku zauna Hajiyan tana shiryawane" "To to ai babu komai yarinya" Cewar Maigogul da yake ta dariya hankalinshi kwance. Wannan dai matashiyarce tare da wata Baba dattijuwa suka shigo aka jera mana dambun nama, cincin, samosa, da alkaki, soyayyun kaji jar suya, da lemukan kwali kala kala banda kayan marmari yankakku da aka cakuɗasu aka wadatasu da ruwan madara. "Sannunku Alhaji ya hanya, kun sha hanya gaskiya" "Hanya Alhamdullilliahi ke yarta ce nace? " "A_a mai aikinta ce ni fin shekara ashirin nike aiki a nan gidan marigayi ne ya ɗakkoni daga ƙauye" "Allah sarki ashe ƴar aiki ce. To mun gode sosai ko"? Duk fa Maigogul ke wannan maganar. Suna fita ya soma zuzzuba mana wannan kayan marmari a kofin tangaran. " Ku matso mu soma ci ƙila tana can tana kwalliya ni kuwa banma karya ba. " Naman kaza ya saka a bakinshi ya soma ci. Ni dai wannan kayan marmarin nake sha, Uzairu zuchiyata kuma dambun nama ya jawo yanata damƙa yana cusawa a bakinshi anga na banza😆. Ta wata ƙofa muka jiyo ƙwasƙwas ɗin takalmi babu shiri Maigogul ya shiga gyare_gyare ni da Uzairu zuchiyata sai kallon abun mamaki muke yi. Da sallama ta fito tana sanye da baƙar abaya mai kyau da tsada kuma gata fara sol itama kyakkyawa dan ba'a kirata mummuna ba, gata da kyan jiki babu laifi gaskiya. Da murmushi ta ƙaraso ta nemi kujerar dake fuskantarmu ta zauna sai ƙamshin humrar Mrs BUKHARI take yi mai wani irin sanyin ƙamshi. "Hajiya Sabuwa ashe dake za'azo barkanku da zuwa. Wannan ma ɗan uwanki ne ko? Kamanninshi da Alhaji Maigogul ya fito sosai" "Eh wallahi ni wanta ne Hajiya. Mun same ku lafiya? " Nan muka shiga gaisawa. "Hajiya mun same ku lafiya ya zafin kano? " Cewar Maigogul wanda yayi magana da wata iriyar murya ta dattijan asali wanda mu dai a iyakar saninmu bamu sanshi da wannan muryar ba." Illahirin mamaki "Lafiya lau barka da zuwa Kano ya gajiyan aikin Umara? " Dariya kawai yayi baice komai ba. Niko illahirin kunya saita saki Maigogul ta kamani ganin yadda yake ƙarema Hajiya kallo yana buɗe ido yana mayar dasu ciki. Hum zan yi sallah Hajiya naji kamar kiran Sallah akeyi ko? " "Eh lokaci yayi akwai masallaci a gidannan su Alhaji Maigogul sai suje ke kuma bari Saude tazo saita kai ki ɗakina kiyi sallah. Saude, saude" "Na'am Hajiya" Saude ta amsa da sauri sai gata ta iso. "Ki kai wannan Ƴar tawa ɗakin baccina tayi Sallah. Shi Alhaji in ya dawo ki wuce dashi babban falo, wannan yaron nawa kuma ki buɗe mishi ɗakin Gaddafi a kai mishi abincinshi can" Ni dai Saude nabi zuwa ɗakin Hajiya. Masha Allah" Na furta a fili bayan fitan Saude ɗakinne ya bani sha'awa sosai komai a killace gashi babu wani tarkace komai na ajjiye a muhallinshi. Banɗaki na faɗa shima sai ƙamshin turare yake yi, kai gaskiya Hajiya na ta'amali da turarukan wuta masu ƙamshi da riƙe waje, ko wacce kusurwa ta gidan nata ƙamshi take yi. ( ga dai dama na muku adashen gata kuma zaku samu damar cin kyautar da zanyi ma duk masu adashen ko da kunfi mutum ɗari. Hajiya in fa ba adashen zaki yi ba kada ki shiga dan Allah) Alwala na ɗauro na tada sallah dan Saude ta shimfiɗa mun dadduma a gabas. Ita kanta daddumar da nai sujjada ƙamshin turaren wuta take yi wallahi mai wani irin ƙamshin daɗi. Ina sallamewa wayata ta shiga ruri. Murmushi nayi dana ga Alhaji zaidu ke kirana. Dama ko bai kira ba na ƙudurce a raina ina idar da Sallah zan kirashi in sanar mishi gani a Kano nasan zaiyi farin ciki sosai. Amincin Allah ya tabbata a gareka kykkyawa. Ga kano naga yau ana ƙwalla rana ga zafi ko? " Murmusawa yayi yace. "Tabbas kin canka Shalelena. Kiyi haƙuri kin jini shuru ko? Aiyukane suka taso mun zuwa jibi ma ƙasar zan bari gobe zaki ganni" Sha kuruminka gani a kanon ni nazo ganin abun ƙaunata kana ina inzo in sameka har inda kake? " Sai da yayi dariya kana yace. "Yanzu haka dai ina kamfanina na motoci dake mun shigo da motoci ana ta lissafe_ lissafe. Da gaske kin shigo Kano kuma me kika zo yi Uhm?" Na shigo kano Maigogul muka rako ni da Uzairu zuchiyata kazo ka ɗaukeni inason ganin kamfanin motocinka ka zazzagaya dani inga ko'ina" "To shikenan Shalelena ki turo adireshin unguwar da lambar gidan yanzu zan bar duk abinda nake yi inzo in ɗakko matata ta kaina." Sallama muka yi na ajjiye wayar sai ga Hajiya da Saude sun shigo. Abinci Saude ta ajjiyemun ta fita ita kuma Hajiya bakin madubinta ta nufa ta gyara hodar fuskarta ta ɗakko wata humra a kwalba mai kyau ta shafe jikinta dashi ƙamshin wannan humara ta karaɗe ko'ina a ɗakin. Kwalbarma ta musamman ce wallahi a ido kawai kaga humrar kasan duka ɗauka ne Kai Hajiya Balaraba a saudiyya, ko sudan kike siyan kayan ƙamshine naji ƙamshin humrarnan da turarukan wutan na musamman ne" Dariya tayi ta zauna akan gado tace. "Ai kuwa anan gida Najeriya nake siye a hannun Mrs Bukhari ƴar mutan Kanuri wannan marubuciyar littattafan hausan wacce sanadin littafinta na Shanono na santa. Bari kiga akwatin turarukan wutan dana siya a hannunta, amman anan kano hannun Anty Zee Agent ɗinta na karɓo dake ɗorayi da zama dake ita a Lagos take Aure amman har Saudiyya tana tura kayanta, nijar, kamaru, Ghana duk tana tura kaya kuma cikin aminci" Ai kuwa kwalin da turarukan suke ciki kaɗai abun kallone, bare kwalaben uwa uba ƙamshin turaren nata. Gashi turarenta saita zuba a leda ta silin ɗinshi sannan zata zura a cikin kwalba kamar dai kayan kamfani. Ga wasu irin humrori da turarukan wuta. Hajiya Balaraba tai ta sammun ina shafe jikina dashi, har humrar gashi da kulaccham ta gashi saida ta bani na shafa. Naita santi wallahi. "To abunda za'ayi tunda nan da sati biyu zaki tare nayi miki alƙawarin show Glass guda zan saka ta haɗa miki daga nan sai ɗakin mijinki in sha Allah. Wannan ɗinma ki tafi dasu ki soma amfani dasu kafin ki tare duk suturunki ki turaresu da turaren turara kaya dana fesawa yayin turarawa, wannan kinga na tsugunnone, wannan turaren turara jikine kullum ki dinga yi. Kinga wannan ƴar kwalbar ita kuma humrar mata aurece da kike ganinta. Ƙawata ta jima tana bani labarin humrarnan da tasirin da take ma maza. ( masu son siyan ɗaiɗai su tumtuɓeni akwai kayana a Kano hannun Anty Zee dake Ɗorayi. Sannan akwai a hannun maman Inteesar kaduna) "Kinga na bar Alhaji Maigogul yana cin abinci kema bari in barki haka. To shikenan Hajiya nagode sosai nima Alhaji nake jira zai zo mu ɗan fita kafin ku gama" "To shikenan muma in ya gama zamu je wajen yayana dashi su gana mu ba yara bane Hajiya Sabuwa in za'ayi ayi kawai nan da sati ɗaya ma sai a ɗaura auren ai" Fita tayi tana cike da farin ciki marar musaltuwa. Buɗe kular abincin nayi naga jallof ɗin soyayyar shinkafa wacce ta wadata da kayan lambu ga hanta baja baja ɗayar kular kuma kazace soyayya ta cikin jajjagen attaruhu da albasa ga wani lafiyayyen kunun aya. Zubawa nayi naci nayi ƙat na kora da kunun Ayannan. Sai ga Alhaji ya kirani yana ƙofar gidan Miƙewa nayi na fita na tadda Saude a falo tana turaren wuta. Saude dan Allah wajen ɗan uwana zaki kaini zamu fita" "To Hajiya muje in kaiki" Kaini tayi ɓarayin yaron Hajiya Uzairu zuchiyata harda cire riga yana ta ɗura abinci babu wasa. Yayi ɗaiɗai a kafet. Taso muje ka rakamu zaga Kano ni da Alhaji Zaidu ko in barka kana kallo? " "Wallahi Lolo prison break nake kallo an tsaya a daidai inda na tsaya na kalli season 1 a gidan abokina. Amman muje dai zamu dawo ai in sha Allah sai an auremu a gidannan zadai a yita da Rakiya dan bata da daɗi sai dai fa mu duka muna bayan Maigogul wallahi nan gidan yafi dacewa dashi ita kanta tafi dacewa dashi su Rakiya yadda kika san su suka haifeshi fa. Dariya muka yi ya wanko hannunshi ya shirya muka fita. Alhaji Zaidu saina ganshi a wata ƙaramar mota mai kyau ja sai sheƙi take yi. Gaban motar na buɗe na shiga, Uzairu zuchiyata ya shiga baya. "Ashe gidan Hajiya Balaraba kuka zo ai dama kince itace ba sai kin sha wahalar turo adireshi ba tunda sananniyar Ƴar siyasace sun sha gwagwarmayar siyasa ita da marigayin mijinta shi ai ya riƙe kujerar ɗan majalisa ma. Suna da kirki da son talakawa sosai gata da yawan sadaka da yawan ziyartar asibiti da gidajen marayu da gidan gyaran hali" Murmushi nayi tare da farin cikin jin Hajiya Balaraba mutuniyar kirki ce wala Allah Allah ya turo mana itane ta zama sababin shiriyar Maigogul, in Maigogul ya shiru magana ta ƙare ni zanji da sauran. Gaisawa muka yi baki ɗaya Alhaji Zaidu sai juyowa yake yi yana kallona ni dai ganin shirun yayi yawa sai nace. Wannan ƙaramar motar tayi kyau sosai " "Kema mai sha'awar ƙananun motocinne? Motar Hajiya ce yau da tawa ta fita shine nima na ɗakko tata na fito." Kai kawai na jinjina Alhaji muna tafe yana nuna mana wajaje yana faɗa mana sunayen wajajen har muka iso kamfanin motocinshi. Ashe katafaren wajene mai ɗauke da motoci masu yawa, ga sababbi tiya leda ga kuma kwatano tokumbo kenan, harda bus_bus dasu j5. Haka yaita zagayawa damu yana nunnuna mana wajaje. "Kinga inda nake son in ɗakko Gaza in bashi kulawa da wani ɓangaren. Dan kinga kamar can ɓangaren ƙanin Hajiya ke riƙe dashi, to shi Gaza in so samu ne ma sai a dinga fita dashi kwatano suna shigo da motocin da sahalewar hukumar fasa ƙwauri tunda naga jarumine kuma kinga tafiyar ta jajirtattuce" Murnace ta lulluɓeni har akan fuskata na kasa ɓoyewa. Haka ya shiga damu ofishinshi ƙato na alfarma muka zauna a kujera. Shayi yasa sakatarenshi ya haɗo mana ya kawo. "Kunga yanayin wajen ko tare zamu dinga zaman ofishinne kina taimaka mun da lissafe_lissafe ko kema kinfi sha'awar buɗe shago kina fita ƙasashe saro kaya kamar dai Hajiya? Nayi nayi da'ita mu dinga aiki tare in bata wani ɓangaren ta riƙe taƙi tafi son tabi tawagar ƙawayenta zuwa ƙasashe sare_saren kaya. Ko harkar fuloti nace mata mu dinga yi tare duk da sana'ace da maza suka fi yawa a cikinta in da matanma basu da yawa. Hajiya sai tai ta mun dariya sabida bata so. Alhaji Gali abokina tare suke ko wanne irin kasuwanci da matarshi kullum suna tare. To ni sai abun yake burgeni naita kwaɗaitama Hajiya wallahi taƙi" Murmushi nayi sai nake jin kamar ya haska mun wata hanya ne. Aiki tare dashi bazai hanani buɗe shago ba ai sai nake ganin ai gara in zauna muyi aiki tare domin in samu gogewa tunda ni ba karatu nayi ba, kuma ba sabawa nayi da shiga cikin mutane inyi gwagwarmaya ba, bani da wayewar juya kuɗi, da wayewar mu'amala, aiki dashi zai fi mun sauƙi sosai zai buɗe mun ƙwaƙwalwata kafin in samu ilimin" Ai ni kuwa tare da kai zanyi aiki duk inda ka kutsa nima zan kutsa" Dariya yayi ya juya a kujera yace. "Allah yasa zaki iya tafiye_tafiyen da yawa Shalele uhm. Yanzu kinga wannan tafiyar China zamu je babu shiri ko zaki zo muje tare ne?" A_a gara kaje kai kaɗai ni kuma inci gaba da shirye_shiryen tarewa. Amman daga wannan tafiyar babu inda zaka dinga zuwa sai tare dani" Dariya yayi yace. "Uzairu zuchiyata ka zama shaida tunda tace zata yi aiki dani to dole ta bini ko ina sai ki zama mai bada shawarana ko uhm? " Ya ƙarashe yana kallona ta gogul ɗin dake maƙale a idanunshi. Uzairu zuchiyata yace. "Ai zata ma yi ba sai kace dole ba. Wannan kasuwanci aina gata ne. Fita ƙasashe ai wayewace da buɗewar kai Alhaji" Kunji fa mutuminku Mun jima sosai a ofishinnan har suka je sallar la'asar suka dawo nima a nan nayi sallata zuchiyata fes da farin ciki. Sai wajajen ƙarfe biyar Maigogul ya doshi kiranmu. Kwatance Alhaji Zaidu yayi mishi na kamfanin sai gasu shi da Hajiya itama a tata motar da dukkan halamu daga nan sai Dutse. An zazzagaya da Maigogul ko ina dako ina a kamfanin ya gani. "Alhaji nima na faɗa maka da nayi saida motoci har kwatano nake zuwa, yanzunma wani sa'in nakan taɓa harkar dake kasan harkar kawalci baya barin mutum da lokacinshi amman yanzu dana dena anya ba nan zan dawo da aiki ba kuwa" Kunya kamar ƙasa ta buɗe in shige tsabar kunya. Hajiya Balaraba tana daga gefe tana ta waye_ waye. "Ai yanzu girma ya kamaka Alhaji Baba sai dai wani aikin ba wannan ba. Zamu tattauna da Shalele muga me ya kamata a maka amman banda harkar tafiye tafiye ai bazan so kasha wahala ba. Ai sai yayi dariya yace. " Har kwatano da ina kawalci ni da babu.... " "Haba Dad dan Allah tunda ka dena wannan kawalcin bai kamata ka dinga maganar ba. Alhaji Zaidu sirikinka ne fa" Cewar Uzairu zuchiyata wanda ranshi ya riga daya gama ɓaci niko idanuna sun kaɗa sunyi jawur dasu. "To to hakane kuyi haƙuri ba zan sake ba. Alhaji aita haƙuri dani zan gyara" Sai tausayinshi ya ɗarsu a zuchiyata sosai Alhaji Zaidu kuwa ya iya tafiyar da Maigogul sosai da sosai. Anan Hajiya Balaraba ta saka mun akwatin turaren Mrs bukhari a mota tayi mana sallama ta tafi sabida ana jiranta Uzairu zuchiyata da Maigogul suna cikin mota ni kuma na tafi ɗakko jakata a office. Ina shiga na saki kuka mai tsuma zuchiyar mai saurare. Juyowa nayi sai kawai na jini ƙam a ƙirjin Alhaji Zaidu yana ta shafar bayana da sigar rartashi. " Sai ƙamshi kike fitarwa mai daɗi Shalelena har kanki ƙamshi yake yi uhm. Shalele bana son kuka. Sannan kada a sake tsinka Alhaji Baba in yana magana baki ji tausayin daya bani ba. Ni ɗanshi ne ba laifi bane dan yayi magana ko wacce irine dani. Haba shalele uhm menene to na kukan share hawayen kada ki sake kuka kina dani, Alhaji Baba nawa ne fa." Ɗagoni yayi ya shiga share mun hawayen da yatsunshi yana ta murmushi. Nima murmushin nayi na dubeshi da kyau nace.. Dama kasan sana'ar Maigogul ne? " Kai ya gyaɗa mun yace.. "Na sani ya faɗa mun da bakinshi tun kafin muyi aure dake, kuma nima na bincika Shalelena" Amman a hakan kaji kana so in zama matarka shin baka ji.... " Bakinmu ya manne waje guda dole nayi shiru na lumshe idanuna wasu hawaye masu ɗumi suka gangaro mun. Mun jima a wani yanayi kafin ya zare bakinshi ya tallafo fuskata da hannunshi biyu yana kallon tsakiyar idanuna yace. "Ki dena dawo da hannun agogo baya Shalelena Shi abu inya wuce ba'ason dawo dashi baya musamman abinda ba kyau bane dashi, abunda bashi da kyau rurrufewa akeyi fa. Abu mai kyauma ba ko wanne ake buɗewa ba. Ni dai ina sonki a duk yadda gidanku yake uhm. Yau ƙamshinki yayi mun daɗi fiye dana ko yaushe tun a mota ƙamshi yake ta sauke mun kasala, shi yasa kika ga duk na susuce uhm" Bakinshi ya kuma mayarwa cikin nawa. Mun jima a tsaye a haka da ƙyar muka rabu amman saida ya sakani na mance duk wani ɓacin rai ya sake jaddadamun yana fa ƙaunata fiye da tunani. Fitowa yayi suka yi sallama da Maigogul muka ɗauki hanya sai wajen goman dare muka shiga gida. Haka abubbuwa sukaita shurawa kamar da wasa ranar Juma'a aka ɗaura Auren Maigogul da Hajiya Balaraba sadaki dubu ɗari amman ba wannan gidan da muka je zasu zauna ba tace tana da sabon gida data gina wannan gidan da muka je gidane da suka rayu da mijinta da ƴaƴanta maza uku. Sai da daddare Maigogul da Cicib suka shigo ashe a ranar aka ɗaura Aurenshi da Labbai shima kawai aka wuce wajen. Muna tsakar gida suka shiga rabon goro Maigogul wai ku kunga gaye kuwa fararen kaya ƙal ya saka komai fari har zabban azurfan hannunshi masu fararen duwatsu ya saka yadda kuka san gwamna, takalmin ƙafarshi kuwa mai kwale_kwale irin na ƴan gidan sarauta mai karen muski ne a ƙafarshi gaskiya yayi kyau sosai wallahi. Uzairu zuchiyata sai ƙunshe dariyarshi yake yi a bayan Labbai, ku kuwa gabana sai dokawa yake yi. Nasan Rakiya babu kyau babu daɗi wallahi. "Wai wannan rabon goron na menene Maigogul kuma na ganku kamar daga biki kuke ko?" Cewar Rakiya kenan da take ɓallar goro. "Goron ɗaurin Auren Labbaine da kuma goron ɗaurin Aurena. Allah ya nufa yau an ɗaura Aurena da Hajiya Balaraba in Allah ya kaimu sati mai zuwa zata tare, ko nine zan tare ma gashinan dai" "Me kace wai? Abu ta kazannan..... 😆 Kuna ganin za'a wanye lafiya da Rakiya kuma? Mu haɗu ranar monday muji yadda zata kaya Mrs Bukhari

Masu adashe ina jiranku [10/4, 10:29 PM] +234 810 593 2041: ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/FyrOjhxZpaIDkhKKwuhZOO?mode=ems_wa_t

MRS BUKHARI 16

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull