Idan kaya ya gaji book book 4 - Chapter 16
Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 16: Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 16. " Abu ta kazan uba, kace me? Aure naji kana faɗe Maigogul kake ko uban…
3,512 words
" Abu ta kazan uba, kace me? Aure naji kana faɗe Maigogul kake ko uban wa? A ina zata tare wai? Narantse da Allah baka isaba ni Rakiya zakaima haka ko sabida kawai ka samu bakin ajjihun mijin Ƴata shine da kishiya zaka saka mana. Hauwa fito kinji alo tsiya alo danja. Au Lolo kitimurmurar da kuke ƙullawa ke da ubanki kenan? Mitsiyaciya dama babu ƙauna a tsakaninmu inda ƙauna ya za'a haɗa baki da ɗiyar cikinka ai maka kishiya" Cicib yace. "Ayi haƙuri Rakiya bakin alƙalami ya bude"... " Rufa mun baki baƙi baƙin munafuki mai kutungullar tsiya ɗan daudun banza, ka auri ɗiyata kazo kana wani cewa ayi haƙuri. Kema ki rasa wanda zaki Aura a duniya sai wannan wanda dake dashi banga ta inda kuke da bambamci ba" Maigogul ya kalli Cicib yace. "Kaje daga sama Labbai zata zo bari in gama dasu kasan Rakiya kishinta ya ƙazanta. Zamanin Hauwa ma haka ta cukumeni muka faɗi ƙasa mukaita burgima muna dukan juna wallahi har kusa da lambatu." Wucewa Labbai tayi gaba Cicib ya bi bayanta suka haura sama. Rakiya ta cukume Maigogul gam tai ta jagalanci tana jjigashi tana zage_zage mu kuma mukai ca a kanta muna kiciniyar kwace Maigogul. Abun mamaki sai haƙuri yake bata lallai abubbuwa da yawa sun canja da dane a wannan gida da dambe har maƙota. "Lallai Maigogul ka cika makiri wallahi. Muna zaune cikin baƙin wahala babu ci babu sha babu sutura yanzu daga sake mana gida ka kwashi kuɗin kayan ɗakin lolon kenan shine kayo aure ko. To a ina kake so ta zauna a sama tare da Rakiya ko? " "Allah suturu buƙwui sai dai ta zauna a ƙasa tare dake wallahi ni da gidan ƴata. Ni ya sakeni ma in huta ko zan samu sabon miji mai ciyarwa gara mu rabu narantse da Allah insan bani da miji makiri" Maigogul tun yana lallaɓa Rakiya da Hauwa har sai da suka tunzurashi suka shiga kokawa da Rakiya ya samu ya kwaci kanshi ya haɗata da Hauwa ya gwarasu da juna. Ya cire malum_malum ɗinshi zai doka da ƙasa Uzairu zuchiyata dake tsugunne riƙe da ciki yayi saurin karɓe rigar. Rakiya ta dira a wuyan Maigogul da kokawa harda cizo fa wallahi, ga kuka tana yi kashirɓan. Hauwa kuwa Raliya ce tazo ta riƙeta gam. Sai da Maigogul ya kusan raɗa Rakiya da ƙasa Rahama tayi saurin fisge Rakiya gefe. Sama da ƙasa Allah bai bani ikon cewa uffan ba. "Lafiyanku ƙalau kuwa sabida raini daga cewa na sake aure shikenan sai wannan cin mutuncin a gaban yarana da girmana akwai uban daya isa ya hanani aurene ke da ke duk wacce take jin ba zata iya zama dani ba ƙofar gidana a buɗe yake. Wannan wanne irin masifa da bala'ine yake damun Rakiya nene? Rakiya matar dana Aura a Kano ma take tana da gidanta ba ɗaya ba ba biyu ba, kuma tana da motocinta ba wai irinku bace wagairahun wannan Hajiyace mai ji da kanta ƴar gidan mutunci. Ku bini a hankali wallahi in ba haka ba tsab zan fatattakeku danni ba ajinku bane yanzu" Fuu ya shige ɗakin Hauwa yana huci. Rakiya bafa ta haƙura ba binshi tayi suka ci da gabzawa dambe tsakanin Maigogul da Rakiya wallahi har waje Rakiya ta dinga janshi suka fita. Gaza ne ya raba wannan dambarwar ya jawo Rakiya da Hauwa, ni kuma na riƙo Maigogul ni da Cicib Rakiya ta yaga mishi riga daga sama har ƙasa. "Haba Rakiya dan kawai Dattijo eh yayi aure shine wannan eh kuikuyamai ɗin da eh kike yi har waje eh shikenan a gidannan mu babu mu babu yin eh abu cikin sirri ne. Eh naji ana cewa namiji mijin mata huɗu ne eh dan yayi aure eh Rakiya yanzu Maigogul kike kishi eh haka har kina kuka rabin raina, ni banga abunda yake tsinana muku ba da eh kuke wani sonshi Allah. Hauwa eh duka kuyi haƙuri dan Allah eh ku barshi haka ni kunga eh Kano zan koma kamfanin motocin Alhaji eh Zaidu zan dai dinga zuwa. Eh abinda kuke so ai zanyi eh muku in sha Allah. Shi kuma eh kuyi mishi Adda'a tunda yace Hajiyace ƙila shima yayi kuɗi eh ko Allah zaisa ya kula daku kuskuren da aka aikata eh a gyara dan kurakuren maigogul da yawa, duk ba shi eh ya mayar damu ƴan iska ba, jibi rayuwata fa yadda ta koma wai kuna tunanin daɗi nake ji ne eh? Haba uwargida an buga dake an barki, waye yace dake bake ba dan abu ta kazan ubanshi muma eh muce dashi bashi ba. Kece Uwargida a gidan Maigogul masoyiyarshi ta farko kuma uwar Ƴayanshi manya eh kece fa rabin ran Gazanshi uban Rahine da Uzairu da Maigogul ƙarami, da Rakiya ƙarama eh Allah eh a huce a huce a huce eh a lafiya Rakiya kayi nayi, wuya a hannunki, wuya da zafi a zuchiyarki, eh Dattijo ya kuikuya miki a huje a huje uwargida ran gida Allah. Uzairu zuchiyata yana tsugunne yana dariya Gazan shima kanshi Dariyar yake yi wallahi. Ni dai lallaɓa Maigogul nayi yace mun zai haura sama yayi kwanciyarshi, Cicib ma dole haka dai ya tafi babu arziki. Har tsakar dare wallahi Rakiya basu dena artabu da Maigogul ba sai da yayi mata hauka hauka ya cire rigarshi ya maka da ƙasa ya rungumeta sukaita gabzawa da taga wuta ne ta rabu dashi sannan muma muka sarara. Adama tace. "Allah mai iko Allah yaso ki Rakiya bata san ke kika haɗa wannan auren ba yau da sai buzunki wallahi zargi dai take yi, duk da in hankalinta ya dawo jikinta wallahi ki kuka da kanki, ke yau ni naga masifa ido da ido Lolo." Labbai tana dariyarta ta mugunta tace. "Rakiya kishi saita dinga nuna bata damu da Maigogul ba amman in abun kishi ya motsa nanne zaku gane kishinta" Rahama tace. "Dan Allah mu bar batun Rakiya da Maigogul ni wallahi murna na taya shi fatanmu Allah ya basu zaman lafiya shikenan fa. An tsufa gidannan jiya iyau. Yanzu Labbai menene abun yi yaushene tarewar musan wanne shirye _shiryen zamu yi ko ba gaskiya ba. Ƙarashen ginin gidan Cicib ɗin da Alhaji Zaidu ya ɗaura Gaza an gama ne? " "Yau aka gama fenti ma, yace mun gobe iyalinshi zasu tare. Ni da so samu ne in tare nan da kwana uku sabida lolo ta samu damar Rakani nima in Allah ya soni sai kuga ya barni na rakata. Ai shima nasan yana can ana dambarwar tsiya dashi ya faɗa ma matarshi wa zai aura kafin a ɗaura auren yace mun ya barota tana ta ɗure_ ɗuren ashariya ni dai ku taya ni da adda'a Allah ya bamu zaman lafiya kuma Allah ya dafa mun Cicib ya dena kawalci kamar yadda Maigogul yace ya dena. Nasan in ya dena zai dena wannan karairayar a hankali ma. " Na yi dariya nace. Amaryar Cicib zafa asha Amarci nan da kwana ukun ai sai a tare. Ya batun kayan wajen Rakiyan nawa tace ta bar miki dan kayan sunyi sabunta kuma sunyi kyau ko Adama? " "Sunyi gaskiya dubu ɗari biyu fa Rakiya tace ko sisi ba zata kankareba wallahi wai itama ɗari da saba'in ta siyo nayi _nayi ta bar mata da saba'in ɗin kinsan kayi nayi da kuɗi. To tukwane ma fa naga yau ta ɗan ƙaƙƙaro harda su kulolin cin abinci da su plate ko Labbai? " "E Cicib ne ya bani dubu sittin shine na harhaɗa na siyo tunda babu a wajen Rakiya" Ranar bamui bacci ba gaskiya haka mukaita hira muna musu harda shewa kamar ba dare ba. Sai da mukai sallar asuba kana muka kwanta bacci. Cikin kwanaki biyunnan Maigogul da Rakiya sai rikici dan ma baya saurarenta haka zata tsaya a kanshi tai ta yaɓo mishi maganganu wasu yayi murmushi wasu yayi dariya dai. Mu kuma motar kaya muka kira aka lode kayan Labbai muka wuce harda Hauwa da Baba Laraba mahaifiyar Tsahare itama Tsaharen jiya tazo tare da su Rakiya ƙarama duk muka ɗunguma har da su Madamcy dasu Rita zuwa gidan Labbai. To nanma har muka kammala jere wallahi Maman Shafa bata dena zage_zagen wai anyi auren cin Amana ga gidannan Labbai tazo taci uwar da zata ci. Sai da ma suka hau sama dasu Adama suka duro. Ɗaki ɗaya Labbai ta samu amman babbane gaskiya sosai. Gadonta ƙaramine bai kai shida da shida ba (6by6) ƙaramine gaskiya amman mai kyaune sosai, sai doguwar kujera da ƙananu biyu, sai sib ɗinta mai ƙofa takwas bango ɗaya ta cinye tas kuma duk da haka mutum huɗu zasu iya jeruwa suyi sallah a filin tsakar ɗakin. Mu dai ko ruwa bamu sha ba nice ma na fita na siyo mana Awara muka ci muka kora da ruwa. Bamu muka bar gidan ba sai bayan magriba muka shiga gida duk a gajiye sosai. Washegari da magriba muka kai Labbai ɗakinta taci kwalliya da kayan dana siyo musu daga Dubai dan jiya ɗinkinnu ya iso daga kano. Maman Shafa dai babu yabo babu fallasa haka muka kai mata Labbai ɗakinta. "Ba shakka aure ba ɗaya ba ba biyu ba ai dole ki shigo ido a buɗe maciya amana" Labbai tayi murmushi kawai. Maman Shafa ta zagemu tatas. "Maman Shafa bawai tsoronki muke ji ba da kika ga munyi miki shiru ba. Aure kike yi itama aure tazo yi. Kinsan dai in tijarane baki kai Labbai ba, in kin so ku zauna lafiya in baki so ba ku kashe kanku. Baba ku taso muje saida nace muku kada a wani kawota ɗakin Maman Shafa amman baku ji ba" Cewar Adama kenan da take ta ruwan zazzaga. Baba Laraba tace. "Allah ya kyauta Ku taso muje dare nayi. " Miƙewa muka yi muka shiga da Amarya a ƙofar gida muka tadda Maigogul da Cicib Maigogul na miƙa mishi ledar kazar amarci. Tare muka juya da Maigogul zuwa gida. Haka dai al'amuran biki aka shiga nawa. Ana jibi tarewata Alhaji Zaidu yake sanar dani zamu yi baƙi Hajiya tayi mun akwati tace zasu zo a kawo akwatin da taso azo da'ita amman dai ta wakilta su Hajara da wasu daga cikin ƙawayenta zasu zo. Dawowata daga wajen Baba malam kenan ma, na sake zuwa na sameshi a makaranta ya dafa kaina yaita mun adda'a wannan Dattijon arziki har kuɗi masu kauri ya bani kuma yayi mun alƙawarin zai saka Wawo ya kawo shi, kuma zai turo Malama ƙarama da'ita za'a kaini har ɗakina. Tunda na kashe wayar sai naji jikina yayi sanyi, su Sadiya kuwa tuni aka aikesu kasuwa siyo kaji, muka tanadi kuɗin tukuici dan Alhaji zaidu dubu ɗari biyu ya turo yace a basu duka. Kaji bakwai aka soya musu jar suya Maigogul ya gwafe yayi musu, anayi Rakiya na habaice habaicenta, sai cincin mudu biyu da Adama tayi, sai ƴar Jallop kaɗan da Maigogul yayi musu, harda wata shinkafa mai ƙwallo da Maigogul naga yayi ya kuma tsoma a ruwan ƙwai ya soya kamar yam bolls amman na shinkafa yayi musu dan fita kunya. Maigogul sai shige da fice yake yi yana tambayar baƙin suna ina yaci ado yayi kyau dashi. Ai kuwa suna shigowa Dutse Hajara ƙanwarshi wacce suke ɗaki ɗaya sai ta kirani. Maigogul ne ya rubuta mata adireshin unguwa da lambar gidan ya tura mata. Ni kuwa naci kwalliya na saka wani babban lace, na ɗauki ƙaramin ɗankunne da sarƙar gwal wannan nawan na saka Sadiya tayi mun kwalliya sukaimun ɗauri. Ana kiraye kirayen Sallar la'asar suka shigo mota biyu suka ciko cike da mata ƙosassu jiƙaƙƙu kuma ni dai daga taga dana hangosu da irin gwalagwalan dake wuyansu da kunnensu duk saina tsure. A haka su Adama suka sakko aka hauro dasu sama da akwatunansu har uku shaƙe wallahi da kaya har akwati guda tayi mun na kayayyakin bacci masu kyau, ga akwatin dogayen riguna, sai akwatin zannuwa da lesuka, ƙaramin akwatin kuwa sarƙoƙine fashion harda na azurfa babba sosai. An bubbuɗe kaya anata san barka tare da godiya, Maigogul dai ya shigo sun gaisa ya gabatar da kanshi kana yayi shigewarshi ciki Allah ya soni. "Babu komai ai Hajiya tafi haka kuma mutum ce guda har da ɓari" Wata zabiya ina jinta tace tana son ganin Amarya. Adama tayi carab tace. "Gashi bata nan bata daɗe da fita ba anata hidimar biki" Ajjiyar zuchiya na sauke. Yanzu na gane dalilin Alhaji Zaidu da yake cewa in sai kaya mai tsada sosai, sannan ya zaɓamun kayan da zan saka in akazo ɗaukana. Wannan kajin da su ruwa a mota aka saka musu Adama ta basu tukincin dubu ɗari biyu har saida motarsu ta bar cikin layin kana na sauke ajjiyar zuchiya tsorone ya kamani ni dai Ina jiyo su Adama anata hayya_ hayya. Nima fitowa, Maigogul sai ɗaga zannuwa yake yi. Zama nayi ina daga zaune suna ta kallon kaya ana mamakin Hajiya wacce iriyar macece. "Lallai lolo kinfa shiga babban famili mai girma. Ke kinga yadda wasu mata su uku suke ƙarema gidannan kallo suna yamutsa fuska kuwa? Gashi sun sha gwala_gwalai, sun raina gidanne, to waɗannan da gidanmu na dane anya zasu iya shigowa ma kuwa? " Cewar Rahama. Ni dai jikina a mace mus yake sai naji duk na raina kaina sosai wallahi. Wayata ce ta sake kuka. Da sauri na shige ɗaki a ciki na samu Uzairu zuchiyata yana ta ninke kayanshi da yayi wanki, shima sai shirye_ shirye yake yi bikinshi da Felisha yanata ƙaratowa. Bayan na ɗaga wayar da sallama ya amsa mun sai yace. "Ashe su Hajara har sun kamo hanya? " E wallahi sun tafi ai" "Tace mun baku haɗu ba kin fita ni kuma nasan kinanan menene matsalar Shalelena tsoro kike jine ko menene uhm? " Ɗan murmushi nayi kawai nace. Ba tsoro nake ji ba. Nadai fi so sai ranar da na tare a cikin gidanka tukunna zasu ganni ai yafi ko? " "Uhm hakane hakanma babu laifi Shalelena. Yauwa Ƙawayen Hajiya su nawa ne akazo dasu? " Sai da yayi murmushi yace. "Su uku ne ragowar duk danginane kinsan fa nace miki muna da yawan gaske. Biki suna ba'a rabo dashi yanzu haka ƙanwata Fatima ta haihu yau kinga ƙila dake za'aje suna ma" A raina na aiyana ƙawayen Hajiya sune mata ukun da Adama suka ga suna ƙarema gidanmu kallo suna taɓe baki. Shima dake hidimace a gabanshi sosai gaskiya bamu yi wata hira mai yawa ba. Washegari da Adama, da Labbai Amarya da ango ya kawota sassafe, sai Hauwa, da aminiyar Hauwan, da Uzairu zuchiyata da Magazin, da Rita da Baba Laraba suka nufi Kano kai tsaye gidan Hajiya Balaraba suka wuce sabida Maigogul yace ita yaba kuɗin kayan ɗakin nawa yace ayimun abinda ya dace. Sabida tana da kamfani da take da ƙwararrun kafintoci da kayan aiki show room gareta ƙato wanda take siyar da duk wani abinda ya danganci gida ƙatuwar plaza ce har kayan Kitchen duk tana saidawa, katifa, fulo, kafet, su tv da komai daya shafi ƙyale_ƙyalen gida tana yi. Sanna tana yin intiriyo dakwareshon Dan ta kirani take tambayata ko akwai kalan da nake sone nace na bata wuƙa da dama.. Daga nan dake shatar bus su Adama suka yi sun tafi da ragowar komatsaina. Rahama kuma da su Madamcy su sai gobe zasu bi tawagar kai Amarya kuma. Ni dai sai naji komai da kowa sun fice mun akaina. Yadda kuka san in gudu wallahi. Gashi gobe akwai Dina da za'ayi anan duk ɓoye ɓoyen da nake yi na rashin son a ganni ya kau dole kowa yaganni.
KANO:. Su Adama sun isa Sabon gidan Hajiya Balaraba. Anan suka ga aikin girma da karamci sunci kaji sun goge wuya dashi. Bayan sun huta da yamma kuma suka nufi gidan amarya motar kaya tuni tayi gaba su daga baya suka isa. Motocinsu a harabar gidan suka ajjiyesu dake tsakar gidan akwai yalwa sosai dan motoci suma kusan biyar suka samu a tsakar gidan banda motar kaya da su Uzairu zuchiyata suke ta saukewa da Magazin. Sun tarar da taron mata masu yawa a tsakar gidan anata musu sannunsu da zuwa Musamman da akaga Hajiya Balaraba a cikinsu harda aminiyarta itama kuma sananniyace a idanun al'ummar jihar Kano dan har yau har gobe ana damawa dasu ta fannin siyasa da wayar da kan mata musamman na karkara. Hajiya Laure ce ta jagorancesu zuwa ciki dattijuwar arziki wacce Alhaji Zaidu yake bi ita a Ghana take aure bikinne ya kawota. Falon Hajiya suka soma shiga danƙam yake da ƴan uwan Hajiyan har babu masaka tsinke da gani itama daga babban famili ta fito. Sai a falo na biyu su Adama suka taddasu ita da ƙawayenta amintattunta. "Ah Hajiya Balaraba kune a gidan maraba sannunku" Cewar Uwargidan Alhaji Zaidu dan tare suka yi makarantar kwana da Hajiya shirine dai basa yi har suka gama makarantar ko ga miciji basa yi. "Wallahi kuwa nice. Mune muka kawo kayan Amaryarki" Sai da suka yi turus tukunna amman dake macece mai wayau sai ta saki fara'a tare da cewa. "Allah sarki ashe kinsan bazawarar da Alhaji ya auro Hajiya Balaraba. To bari a baku kin ɓarayin nata. " "To shikenan. Yarinya kam ai Ƴata ce mahaifinta nake Aure. Kinga wannan ma Kishiyarmu ce duk iyayenta ne mu waɗannan fararen kuma yayyinta ne" Ta nuna Hauwa wacce ta sha leshi da ɗan sarƙa da ɗankunnenta na azurfa wanda Layuza ce ta ara mata. Leshin jikinta kuma Loloce tayi musu anko da Rakiya. Akan ankonnan ma Rakiya ansha artabu da'ita ta dai yi rantsuwar itafa ba zata saka ba. Hajiya da kanta ta tashi cikin tafiyar ƙasaita ansha kayan ado taje ta buɗe musu ɓarayin Amarya ta damƙa kin a hannun Hajiya Balaraba. Nan suka shiga aikinsu ma'aikatan kamfani kusan su sukai aikin rabinshi da kwatanshi su suka san a inda zasu ajjiye komai cikin tsari Su Adama a gyaran Kitchen da wanke banɗaku aka barsu. Su Uzairu zuchiyata ma bafa a barsu a baya ba sam. Ɓarayin na lolo yadda yake da farko dogon hanya zaki shiga itace a farko Corridor kenan. Daga nan zaka murɗa ƙofar da zata sadaka da babban falo a cikin falon akwai Kitchen da wajen cin abinci daining kenan, sai ɗakin baƙi da banɗaki a ciki sannan akwai ƙafar bene da in aka hau akwai ƙaramin corido a inda ɗakunan suke ciki guda biyu ɗaya daga ciki shine akaima lolo jeren kayan gadonta, ɗayan kuma kafet aka malala mata sai wata doguwar kujera guda ɗaya da aka saka mai suffar L da teburinta. Gaskiya gidan lolo yayi kyau matuƙa gaya. Kafet da labule da ta siyo a Saudiyya a uwarɗakinta aka saka mata. Yadda aka tsara ɓarayin da yadda Hajiya Balaraba ta zaɓa mata kayan kece raini babu raini tattare da ɓarayin duk kuma wanda ya shigo haƙiƙa yasan iyayen Lolo sunyi mata bajinta. Ga gara mai yawan gaske da aka haɗota dashi. Dukka fa wannan ƙoƙarin Alhaji Zaidu ne dan Maigogul sau uku yana kiranshi yana sanar mishi kuɗin kayan ɗaki bazai isaba. Shima ya fita da fitarshi ya ɗinka kayayyaki na alfarma waɗanda zaici Amarcinshi dashi ya kuma ɗinka kayan da zai sa ayi dinar Lolo. Ya dai yi ƙoƙari ya sai kayan abinci basabamba ya raba ma Hauwa da Rakiya abinda bai taɓa yi ba a rayuwarshi ya siyo ya jibge. Ko a da can kafin su tara iyali da yake ƙoƙarin ganin ya taimaka awo dai suke yi. Gwangwani uku huɗu na shinkafa da wake daga baya ma ya zirarama idanunshi kwalli. Hajiya Ta saka an kawo abincin masu jere shinkafa da miya da kaji manya manyan yanka aka kawo musu sai salak da lemukan kwali da ruwan gora, su cincin sinasir alkubus nakiya duk an kawo musu fanteka fanteka na nuna isa da son bajinta da burgewa. Godiya su Adama suka yi nan Labbai ta shiga rabon abinci dama a gajiye suke tulus suka ci suka ƙoshi da ɗaya da ɗaya dangin ango sukaita shigowa suna santin wajen da gaisuwar baƙi. Basu suka baro gidan ba sai wajajen goman dare a hakanma sun tawo da kayan abinci rigi_rigi wanda aka kuma lodo musu na dare. Har dai suka tafi basu haɗu da Hajiya ba sakamakon gidan ya kuma ɗinkewa da Jama'a. Suna komawa gida sai bacci an gaji washegari gari kuma itace ranar tarewa. Hajiya Balaraba sunyi waya da Maigogul yake sanar mata Alhaji Zaidu yace Rano za'a wuce da Lolo kai tsaye. Akwai iyaye acan da za'a kaita ayi mata nasiha lafin a wuto kano. Sunyi dashi akan su Manyan zasu wuce Ranon in yaso ko su Adama sai su wuce gidan Amarya su jira zuwansu.
Mrs Bukhari ce [10/4, 10:29 PM] +234 810 593 2041: https://chat.whatsapp.com/I7uDGV8V2DQDVS5RHRi0St
https://wa.me/message/QBXV2PDE2Y3CI1
Kina neman inda zaki samu ingantattun kayan gwanjo wato thrifts ma yaran ki kwantar da hankalin ki yar uwa oumokasha thrifts store ta kawo muku kala kala kaya na fita kunya akan farashi mai sauki tun daka kan overalls jumpsuits bodysuit bibs jeans tops blouses da sauran kaya na kece raini from 0 to 15 years Muna garin abuja koh kaduna Muna tura kaya ko wani gari da yarda Allah quality da sauki shine taken mu
MRS BUKHARI 17