Idan kaya ya gaji book book 4 - Chapter 17
Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 17: Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 17. Lolo Ni dai da zazzaɓin tsoro da fargaba na kwana ga gidanmu ya cika ya…
4,081 words
Lolo Ni dai da zazzaɓin tsoro da fargaba na kwana ga gidanmu ya cika ya batse da ƴan unguwarmu na da harda Maman Ƴar Shuwa tazo tana ɗakin Hauwa duk da ta tarar abokiyar gulmar tata batanan amman hakan baisanya ta tafi ba. Sauƙinta ɗaya mutane sunyi yawa kuma ranar ta farin cikice tabbas da yawan waɗanda suka zo bikin duk gulmace kawai ta kawosu sai kuma abokan kasuwancin Kayi nayi suma sunzo sun mata kara sosai a wannan karon. Wajajen azahar sai ga Malama Ƙarama da su mardiyya suma sunzo. Mardiyya da malama harda kayansu kala bibbiyu a leda suka zo. Aminu da Aɗɗa'u kuma sunce a wajen su Rakiya zasu zauna har su Adda su dawo. Har ɗakin Rakiya nabi malama ƙarama na tsugunna aka gaisa. Ta miƙo mun kuɗi masu yawa tace malam ne yace a kawo mini agen Wannan kuma nata ne kulace mai kulu mai kyau sosai. Godiya nayi mata sosai na fito Nan Mardiyya ta miƙamun ambulon a manne fari wai gashi inji Babansu. Karɓa kawai nayi na cusa a jakata tare da kuɗin da Baba malam ya bani. Da misalin ƙarfe uku dangin ango da dandazon masu ɗaukar amarya suka zo a cikin zuƙa zuƙan motoci. Ni dai jikina har rawa yake yi Malama Ƙarama ta danƙani a hannun wata Dattijuwa. Fuskata a rufe kamar sabon aure jikina kuwa sai rawa yake yi zazzaɓine sosai wallahi a jikina. Da bismillah na fito daga samanmu ina riƙe gam da hannun Maigogul muna ta ratse mata aka sakani a cikin mota ni da Rahama da Madamcy. Maigogul nake ta kallo shima idonshi a kaina ga Rakiya a gefenshi. Maigogul kace tare zamu tafi dan Allah ni ka shigo mu tafi tare" Sai na saki kuka. Rakiya tace. "Dake ku abun kunya gaba kuke bashi ba baya ba ai dole kice yazo mitsiyaciya. Maza dai yaje ya kaso miki auren kinga ai sai ku tare a gidan Amaryar tashi tare tunda Uzairu zuchiyatama yace can zai koma. Wawuyar banza in banda hauka ina aka taɓa hakan? Ai ko kawoki cikin mota da yayi yana ratso mata kaɗai abun kunyane." Nan Rakiya ta shiga kumfar baki. Maigogul yayi ƙur yana kallona idanshi fal da hawaye, kawai saiya faɗa gaban mota yana goge idanshi. Rakiya ta zagayo tace. "Ai ko dai wallahi anji kunya raka Amarya da ubanta ko da yake ga can abokin sheɗanancin naka Cicib ma ganin shigarka mota shima ya shige daga can sai ka zauna a wajen Amaryarka mu kuma sai mun ganka sallamemme" Allah ya so mu direban motar tamu baya ciki da a gabanshi za'ayi wannan aikin. Sai daga baya ya shigo. Duk da Maigogul bai sake kallon Rakiya ba. Rahama ta fita su dasu Sadiya suka shiga tantance waɗanda za'aje dasu. Motoci biyar kawai aka cika ragowar a haka suka koma cikin gomboi muka tafi. Mai mota ya sake mana waƙar ranar murna gimbiya tahau dokin girma muiyo murna zamu tafi mu kaita ɗakin aure. Wannan waƙar ko yau aka fileyin ɗinta ina tuno wannan ranar a ƙwaƙwalwata. Sai hawaye nake zubarwa duk na ɓata fuskata da hawaye. Gashi nayi kyau kayan da Alhaji Zaidu ya zaɓamun su na saka da setin gwal ɗina na akwati, takalmi da jakan ma abun kallone. "Lolo jikinki yayi zafi sosai. Ya kamata ci cire wannan tsoron dan Allah ki bari ayi a gama komai lafiya. Ke dai kiyi ta adda'a kawai. Naga Malama Ƙarama itama ta shiga mota ashe da'ita za'aje. Ragowar kayayyakin da kika samu an ɗura a buhu mun tawo dasu. Akwatunanki kuma naga mota daban akayi musu Sadiya ce ta shiga gaban motar su gidanki zasu wuce kai tsaye." Kai kawai na gyaɗa mata ina jin wayata na rauji amman wallahi na kasa cirowa a jakata sai Rahama ce ta zaro mun tare da ɗagawa ta bani. Ga wayar a kunnena ina jiyo sautin amon muryarshi Wallahi na kasa magana ni kaɗai nasan halin da nake ciki wallahi na tsorata da yawa kuma gani nake aurenma kamar zaman bazai yiwu ba. Rahama ce ta zare wayar a kunnena ni kuwa na saki kuka kawai. Maigogul yau baya magana sai girgiza kai yake yi sabida shima kamar fa kukan yake yi. "Alhaji Zaidu Rahamace Lolo dai ta kasa magana sai dai ƙila zuwa anjima" Ta cikin wayar yace. "Yaya Rahama dama ke kuna Dutse tare kenan, Su Yaya Labbaine suke Kano kenan? " "E sune muna mota zuwa Rano da Amarya. " To shikenan Ubangiji Allah ya tsare muku hanya. A kula mun da'ita sosai a tabbatar taci abinci in kuka isa Rano. Na danƙa miki ragamar kulamun da Shalelena Yaya Rahama" Dariya tayi tace. "In sha Allahu kuwa. To shikenan sai mun iso Kano nagode" Ta kashe wayar ta danƙamun kenan saƙo ya shigo kamar haka" "Shalelen mijinta nasan dai wannan kukan na farin cikine bana baƙin ciki ko nadamar aurena bane. Kukane na farin ciki da murnar shiga wata sabuwar duniyar soyayya. Shalelena gidana cike yake tab da soyayya na tanadar miki abubuwa da dama na soyayya wanda ba sai gobe ba ayau zaki soma gani. Mijinki mai ɗokinki a ko da yaushe Zaidul abeedin Murmushi nayi tare da sauke ajjiyar zuchiya sassanya sai naji na samu ƙwarin guiwa sosai Allah cikin ikonshi da amincewarshi sai gamu a Rano da yamma lis mune tafe_ tafe har ƙofar katafaren famili house ɗinsu Alhaji Zaidu wanda yake ɗauke da gini irinna sarauta da ganin ginin kasan irin gidajen gaggan masu kuɗin da ɗinnanne. A hankali na fito daga mota Malama Ƙarama da Rahama suna riƙe dani, Madamcy na riƙe da jakata haɗe da wayata. Maigogul yana cikin mota su basu sakkoba ma. Ina cikin mayafi ina ƙirga zauruka saida muka shiga zauruka goma sha biyu kafin muka shigo ainihin gidan. An yi ma gidan ginin zamani sosai ta ciki. Haƙiƙa daga waje in kaga gidan ba zaka taɓa tsammanin haka zaka shigo ka tadda cikin ba. Masha Allah Al'umma dai kuwa akwaita cikin wannan gida. Muna shigowa aka soma yiriririr. Nan wata farar Dattijuwa tace. "A wuce dasu shiyyar Goggo Amfana maza Mariya. " Kafin mu kai ga bin Mariya su Hajiya Balaraba dasu Hauwa suka iso suma sai muka ɗunguma du tare zuwa ɓarayin Goggo da akace. Tsofaffine a falon kusan su bakwai wannan na wane waccan a tsufa. Haka na gurfana gabansu kaina a ƙasa bana ko iya ɗagoshi sai dai kama muryoyi kawai nake yi. Gaisuwace ta wakana kusan na minti biyar abunka da gidan Malunta wannan Tsohuwa mai suna Goggo amfana ita ta buɗe taro da adda'a adda'a ta larabci zuryan tare da yin sallama duk muka amsa kafin ta soma da cewa. "To Sabuwa muna farin ciki sosai da shigowarki cikin wannan zuriya tamu mai ɗumbun tarihi da daraja. Mu nan da kike ganinmu daga iyayenki sai kishiyoyinki anan wanda da sannu zaki gane matsayin kowa tunda ana yin taro sau biyu a shekara. Sannan ko biki ko suna ƙwai da ƙwarƙwata ake taruwa ayi, in abun kukane haka za'a haɗu a jajanta ma juna. To kin shigo gidan yawa dole kiyi haƙuri da abubbuwa da zaki ji zaki kuma gani ko ba gaskiya ba? Kisa a ranki zaman mijinki kike yi ba zaman burge kowa ba. Amman ki rungumi dangin mijinki ki ba kowa matsayi daidai dashi. Wanda yace yanayi maraba, wanda yace bayayi umma ta gaida Aisha. Ba za'ace duk wannan taron kowa ya soki ba, kuma ke kanki ba zaki iya son kowa ba. Uwargidanki ba mace bace mai matsala ba mun shaida tunda ta zauna zaman mutunci ba da kishiya ɗaya ba bada kishiya biyu ba mun shaida wannan. Ki yi ƙoƙari kibi layinta a zauna lafiya. Mijinku kune masu kwantar mishi da hankali a duk lokacin da wata damuwa ta dameshi, to hakan baya samuwa sai kun haɗe kawunanku" Haka sukaita yi wannan ta zuƙa ta cika taba wannan ta guntsa sukaita mun nasihohi masu ratsa jiki. A maganganunsu wallahi na tsinci abubbuwa da yawa kuma na yaba ma waɗannan tsofaffin gaya. Cikinsu ko wacce kuɗi ta bani sai Goggo Amfana data ɗakko ɗan kunne da sarƙa na azurfa dahuwar da masu kauri sosai. "Wannan ki riƙeshi da kyau. Tarihine mai tsawo inata ɓoyonshi Allah yasa rabonki ne haka kurum naji ina sonki fiye da ragowar matan da Zaidu ya aura. Ƙila rabonshi na jikinki ne" Nan akaita Allah yasa Allah yasa. Nan kuma suka ƙare da koke koke dai da tuno mahaifan Zaidu da suka rasu. Daga Ɓarayin Goggo Amfana an kaini shiyya shiyya takwas da nata tara kenan. Ba fa ƙarewa suka yi ba dattijan gidanne suka shigo suna faɗan a sake mu hakanan dare yayi mu kama hanya. Wallahi duk shiyyar da muka shiga kuzo kuga abun alkhairi zumunci garesu sosai. Daga masu kuɗi sai masu bani turaren wuta, sai masu bani turmin zani, masu bani takalmi nayi harda wacce ta bani ƙatoton zanin gado ɗan madina fari sol babban gaske. Sai da mukai Isha muka ci tuwo kana aka sallamemu. Ni dai naji an sakani a mota Adama da Sadiya suka biyoni. Sai taran dare muka iso gidan Alhaji Zaidu, Anan Maigogul mukai sallama na rungumeshi inata kuka yana rarrashina, Hajiya Balarabace ta janyeni. Na gaji iyakar ƙarshe bana sha'awar komai sai in yi wanka in haɗiyi maganin zazzaɓi in kwanta kawai. Nasan hakan bazai samu ba tunda akwai dina Amman ina ana shigo dani Hajiya Balaraba da Hauwa, da Malama Ƙarama da Baba Laraba suka nufi ɓarayin uwargida dani. Shaƙe da mutane ɓarayin sai tashin hayaniya kawai kake ji. Waje aka bamu muka zauna nima ina daga kan kujera a cikin mayafina. "Wacece Uwargidan a cikinku ne bayin Allah. Gara muyi a gurguje mu samu muje mu kwanta mun shawo hanya" Cewar Hauwa dan da muka shigo madadin su mayar da hankalinsu garemu sai suka ci gaba da hayaniyarsu. Wata matace ta shigo ƙamshin turarenta ya daki hancina ga ƙaran takalminta mai tsini. "Ah marabanku Amaryata ta iso ashe. Ai Hajiya Balaraba da kun wuce da'ita ɓarayinta ta watsa ruwa taci abinci ga Dina da aka shirya Alhaji yace daga Rano kuke ma ƴan zuwa dina duk suna can nima ku nake jira" "Ai babu komai dama gaisawa muka kawota kuyi a baki girmanki ko? " "Ahh babu komai wannan al'adar bana fiye sonta Amaryata a barta ta huta ta samu ta shirya awa ɗaya gareta kawai" Matsowa tayi kusa dani ta shiga mayafin da nake ciki a hankali na ɗago muka haɗa idanu tubarkallah masha Allah itama tana da kyanta daidai misali wallahi yabon gwani ya zama dole. A yadda nayi tunaninta ba'a haka na ganta ba. Na zaci ƙatotuwace ashe bata da irin wannan ƙibar ta Hajiyoyi ta dai kai Rahama jiki kamar dai ni da rabi da kwatana bata ƙarasa biyuna ba. Nayi zaton farace sai naga baƙace irin baƙinnan na baƙaƙen fata mazauna Amurka ( blacks American) Amman gaskiya ba yabon kaiba na fita kyau sosai. Tayi ado da gwala gwalai, ta zuba kayan kuɗi sosai a jikinta. Tayi tsam da muka haɗa idanu amman bansan menene daliliba dan ta kalleni ta maya harda mamaki akan fuskarta. Sai kuma ta saki guda tare da dunƙulamun kuɗi rafa uku tace. "Amarya ta ƙara a kuɗin liƙi Allah ya bamu zaman lafiya yasa kin shigo kenan sai dai ki birneshi ko ya birneki ya kaɗe fitina a tsakanin mu. Hajiya Balaraba a kaita ɓarayinta. Za'a biyoku da abinci yanzu. Alhaji ma ya shigo yafi a ƙirga yana dakon zuwanku baku zo ba" A daddaƙile take magana irin na madiga ɗinnan kun gane mata masu cikar iko. Ni dai godiya muka yi muka wuce ɓarayina. Saida aka zaunar dani a bakin gado na sauke ajjiyar zuchiya tare da buɗe fuskata na sarara. "Sabuwa lallai Allah yana sonki irin wannan gida ko a mafarki ban taɓa tunanin Aure zai iya kawo ɗaya daga cikinmu ba wallahi, sai gashi ke Allah ya zaɓa ya kawoki. Gashi kishiyarki gaskiya halamunta ya nuna bata da wani matsala kema mun sanki sarai zamanku zaiyi kyau. Kije ki watsa ruwa kizo ga doguwar rigar bacci ki saka Kafin a kawo miki kayanki" Kuɗin da Hajiya ta bani na miƙama Labbai. Ki adanamun da wannan sarƙar da kudaɗennan dana samu. " Ina faɗin haka na faɗa banɗaki dana saki ruwan zafi daidai_ daidai a jikina na duɓe idanuna a cikin ruwan naga kyan banɗakin sai kawai naji ina zubar hawaye. Cikin ƙudurar Allah harna gama wankan hawaye bai rabu da idanuna ba. Ina fitowa na samu su Adama na cin abinci a tire ga kaji guda guda ko yankawa ba'ai ba kai da ƙafa da kayan ciki kawai aka cire. Duk sun sake kaya sun saka ankon farin lace dake fararene sai suka fito kamar matan wasu hamshaƙan Labbai har haƙorin makka na bogi naga ta saka, ga wata sarƙa barawon zinari da duk suka saka. Doguwar rigar baccin da Adama ta ciremun na akwati na zura kafin kayan nawa na dina su iso Alhajine ya kai ɗinkin. Nayi zaman dirshan na shafe jikina da Kulaccham ta jiki na wajen MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI kulaccham ce wacce take gyara jiki tasa laushi da sheƙin fata, bugu da ƙari ƙamshi ya zauna daram a fata, gata ɗauke da sirri mai girma. Ina gama shafe jikina da man na bi jikina da humrori masu dogon tarihi na shafe jikina. "Lolo waɗannan kayan ƙamshin na gaske ne nima zaki sanmun inje in ci amarci dashi wallahi naga Amaryar Maigogul tayo miki kayansu show glass guda muka je Ɗorayi gidan wata Farar Hajiya mai fara'a da sanin darajar mutane Hajiya Zainab sunanta Zee musa collection. Naga tana siyar da kaya ita kanta Hajiya zainab ɗin da dama, su kayan jinjiraye, atampopi, kayan Kitchen ke komai ma siyarwa take yi gaskiya." Murmushi nayi nace. Hajiya Labbai Amaryar cicib ohh duniya juyi juyi wai yau ke Cicib ya aura. Dan Allah daren farko yaya kuka yi ne? " Adama harda ƙwarewa tsabar na bata dariya. Ita kanta Labbai ɗin har ƙasa ta kwanta dan mugunta. "Kinsan Allah banma taɓa samun wani ɗa namiji a kab mazajen dana aura a baya irinshi ba. Gaskiya uwargida take ta zage_zage. Daudunma yace mun zai dena tunda bana so. Yace tunda Maigogul ya dawo daga Umara yake ta faɗa mishi ya sauke Daudu su fuskanci gaskiya da gaskiya. Kunga kuwa ai akwai damshin nasara ko? Ku dai ta taya ni da adda'a kawai amman fa naga waje wallahi, in dai mu'amalar Aurene to an rufe ƙofa kawai yasan takan mace." Ai kuwa sai ga wayarshi ta shigo. Ai saina shiga salati ita kuwa a guje tayi waje Adama tace. "Ba gara Labbai ba. Nifa inna tuno zan koma malam Madori sai inji gabana ya faɗi. Sabuwa Alhaji wani irin ƙazamin mutumne sannan ranar kwanana baya ɗaga ƙafa sannan salamatu kwanta kawai ya iya. Ga baƙar wahalar gidan abun duk ya fice mun a raina. Amman haka damun koma Dutse nima zan tarkata in koma" Tausayin ƴan uwana ya kamani sosai. Sallama muka jiyo a bakin ƙofa nayi saurin saka mayafina a ka na rufe fuskata. Ashe Hajiya ce tana sanye cikin wani leshi mai manyan huda ja mai bala'in kyau kai da gani kasan da tsada. Takalmin ƙafarta baƙine mai tsinin gaske sai adon gwalagwalai da tayi su zobuna kawai saida tasa takwas wallahi kuma duk zinarine kwalliya irin dai ta alfahari. Ta sha baƙin goggoro tayi kyau. "Amarya mai maganar siga. Da fatan kinci abinci dai ko? " A_a fitowata daga wanka kenan yanzu zanci" "Allah sarki. To dama Alhaji ne yake son ganinki yana waje yana jiran in kawoki. Kinsan fa bai fiye jin kunya akan abinda yake so ba" Ta ƙarashe da dariya. Mamakinta nake ji shin bata kishine irin na mata ita? Allah mai iko. Ledar kayan dina ta miƙo mun Adama ta karɓa. "Bari in jiraki a falo in kin kammala sai mu tafi ko? To nagode sosai" Doguwar rigar wani irin leshi ne ko net ne ni wallahi nama kasa tantancewa tsabar kyau mai ruwan tokane kalanshi turarre, sai baƙin takalmi da goggoro baƙi a naɗenshi yake sakawa kawai zanyi. A cikin takalmin muka ga wata sarƙa babba da ɗankunne harda warwaro da zobe. Kuma wallahi gwalne ɗanye ma kuwa. Cire ta wuyana nayi na adana na saka wannan warwaron wacce na cire da zoben sai ban cire ba na ƙara na sabuwar sarƙar a hannun dama nasa zoben daidai hannuna kuwa warwaronne ma sukaimun yawa amman Adama tace in saka a haka. A gurguje Sadiya tazo taimun kwalliya na fito shar dani goggoronne dai yaƙi shiga kaina sam yayi mun kaɗan. Sadiya yi mun ɗauri mai kyau kawai da ɗankwalin kayana kinga har goma saura fa" Ai kuwa ɗauri ta buga mun gashina ya fito ya kwanta a tsintsiyar wuyana nayi kyau na musamman. Fitowa muka yi tare Hajiya dake zaune a falo ta ƙuramun idanu har muka sakko. "Goggoronne bakya so baki saka ba? " E ban fiye son goggoro bane shi yasa nace aimun ɗauri kawai da ɗankwalina." Baki ta ɗan taɓe ina lure da'ita. Wucewa muka yi ina jiyo muryoyin su Baba Laraba dasu Hauwa a ɗakin dake ƙasa sunata hirarsu. Muna fitowa muka samu Alhaji Zaidu a tsaye ya sha malum malum ta waganbari mai ruwan toka anyi mishi baƙin surfani a rigar irinna sarakai, ga hularshi Zanna Bukar asalin babbar kunsun akwai Zanna Habu akwai Zanna Bukar 😆 Ƙafarshi saye da baƙin takalmi mai rufaffen gaba. Murmushi mai taushin gaske ya sakarmun tare da cewa. "Wata barakallahu ahsanin khalikin." Iyakar abinda yace dani kenan. Hajiya tayi dariya tace. "Alhaji Manya to muje ko, kuyi gaba zan ɗakko jakata" "A_a mu na dai jiranki kije ki ɗakko mu tafi uwargidan Alhaji Zaidu" Dariyar manyan basawa tayi dan saida ta kaurara muryarta. Tana wucewa Alhaji Zaidu ya jawoni ya shiga shinshinar ƙamshina. Cikin wata muryar magagin ƙauna yace. "Zaki soma shiga turaka Shalelena yau. Zan jiraki komai dare haƙurin nawa ya ƙare wannan ƙamshi ya susutani" Jin takun Hajiyane yasa na zame jikina da ƙyar. "Amman kamar zazzaɓine naji a jikinki ai ko. Subhanallahi da kin sanar dani ai bama zamu je Dinar ba. No muje in baki magani kisha ki kwanta kawai" Hajiya ce tace. "Haba Baban Soyayya a daure dai. Anyo gayya gari _gari abokanka da matansu duk suna can suna jira kuma ace amarya da kanta bata samu Halartar wannan taron ba. Muje akwai maganin warware gajiya a jakata sai in bata tasha a mota gabaki ɗaya Dinar ta awa biyu ce. Kuɗin da aka kashe ai bana wasa bane ko? " Murmushi nayi nace. Zan iya ma Hajiya dana sha magani in sha Allah zan warware" "Yauwa ƙanwata muje kinji" Hannuna dana Alhaji ta kama har zuwa mota. Mu uku muna baya mun sakashi tsakiya sai direba ni dai har muka isa bance komai ba da'ita suke hirarsu ta biki da ɗan abubuwan da suka faffuru dai a taron har muka iso. Kaga masu yi dan Allah ashe tarone mai suna taron manya aka shirya. Mutane kuwa sun samu zuwa sosai babu yara babu mata masu goyo babu masu ciki. Anyi biki sosai. Maigogul shi da Hajiya Balaraba sun iso har inda muke zaune mu uku maigogul ya ɗaga mun ajina dan wallahi kwalliyar da ya ɗauka zaku rantse yana da sarauta a hannunshi dan rawani ya naɗa mai kunne biyu irin na zazzagawa ga wata farar malum malum tasha ɗinkin Sarakai aiki daga sama har ƙasa ga haƙoran makka, ya kuma saka farar alkyabba irinta sarakai fa narantse muku da Allah ga takalmin nashi irin alkyabbar na sarakai mai kwale_kwale da wasu gasuwa a jiki. Hajiya Balaraba kuwa ba'a magana ta caɓa adon manyan mata. Idanu muka haɗa da Maigogul mukaima juna murmushi har yana shafa mun kaina kunsan dama a fice yake dai" Cicib ma yau malum malum yasha yayi kyau fuskarnan kamar an gasa agada tsabar shafe_shafe . An gabatar mun da matan abokai kala da iri. Anci abinci an raba jakunkuna shaƙe da kaya a ciki ƙarfe biyun dare taron duk ya watse Muna shiga mota kafin Hajiya ta shigo tana magana da ƙawayenta ya dubeni tare da taɓa jikin nawa zafi ma ya sake yi. "Alhaji kuje kawai zanbi motar su Hajiya Mansa Amarya naga ɗazu ta kasa sakewa. Kuma kaima nasan kana da buƙatar keɓewa da'ita akwai maganganu bakin ka" Hajiya ce take magana da fara'arta. "Ke dai zaki bisu ku tattauna dai Hajiya ƴan gulme_gulmenku na ƙawaye. To shikenan sai mun haɗu a gida" Tangaran ɗin motar ya ja sama ya umarci direba daya ja mu tafi. Ni kuma ya jawoni jikinshi na laɓe lub sai shafan bayana yake yi na gaji irin gajiya marar musaltuwa har bacci ma ya soma surata saida aka iso gida ya ɗagoni ya ƙara mannani a jikinshi dake direban ya fice. "Idan kinje ɗaki ki watsa ruwa kizo sama zan baki magani saiki yi kwanciyarki a jikina uhm?" Ya ƙarashe idanshi a cikin nawa. Amman ya kamata inzo gida cike da mutane ka bari a watse zuwa gobe. Sannan bansan ma ɗakin ba" Hannu biyu yasa ya tallafo fuskata. "Hakan nake so ne Shalelena ko bazan samu bane, ashe baki ga haƙurin duk da nayi a baya ba? Babu abinda zanyi miki bacci kawai zamu yi. Zan nuna miki ƙafar benen da zaki hau kina hawa falona zaki tarar sai ɗaki ɗaya a cikin shine turakar tawa uhm in jiraki ko Shalelena uhm? " Ya ƙarashe maganar a shagwaɓe sosai. To zan zo. Amman ina dugun kada Hajiya ta ganni ne wallahi kunya nake ji" "Hajiya da ko shago taje ta gaji bata zuwa ɗakina balle ita da take da baƙi sosai ba zaki ganta ba ni dai ina jiranki" Fitowa muka yi Adama ta ja hannuna muka shiga ciki. Tun ina wanka Alhaji yake ta kiran wayata lokacin kusan ukun dare. Ina fitowa na dubi Adama na faɗa mata abinda Alhaji yake so. "To sai me mijinkine fa. Kawai ki saka kayan baccinki ki zura hijabi kije maza da asussuba saiki sulale ki dawo" Wayarshi ce ta kuma shigowa a sanyaye na ɗauka.. "Shalelena kin barni inata juyi ni kaɗai tunaninki na neman numfashina. Kizo dan Allah shalelena ɗuminki kawai nake buƙata uhm" To ganinan daga wanka na fito yanzu na fito" "To shikenan ina jiranki ƙofar a buɗe take" A gurguje na shirya na muttsuke jikina da humrar matan aure Adama ta yagemun jar jigar Bacci mai gajeren wando na saka na zurma hijabi har ƙasa na sakko kowa yayi bacci. "
ALHAJI ZAIDU:. Yana kwance da kayan bacci yana ta juyo mararshi har murɗawa take yi. Sai yaji an turo ƙofar an shigo. Cikin ƙanƙance ido ya juyo sai yaga Hajiya tsaye da rigar bacci doguwa har ƙasa mai hula. "Hajiya kece a darennan ashe baki yi bacci ba?" Ya tambayeta cike da mamakin ganinta, da kuma rashin jin daɗin zuwan nata. Tunda dai da dane ba zata taɓa zuwa ba cewa zata yi ta gaji, balle gida cike da mutane gashi ƙawayenta duk a gidan zasu kwana suma. Takowa tayi tazo ta haye gadon. "Banyi bacci ba nace bari inzo in taya ka kwana ko baka maraba dani ne? " Murmushi yayi ya shafi fuskarta yace waneni kema neman magana kawai kike yi haba Matata. Nayi dai mamakin zuwanne tunda nasan a gajiye kike gaya. Shi yasa ma...." Kafin yayi wata magana Hajiya ta haɗe bakinsu waje guda.
Sabuwa:. Da sauri na haye saman harda sauke ajjiyar zuchiya dana ga babu wanda ya ganni. Falon na ratsa har izuwa ƙofar turakar. A hankali cike da kunya na tura ƙofar. Ganin Hajiya Alhaji ya murginata ya haye bisanta nayi saurin ja baya. Ina dafe da ƙirjina Kafin su juyo na rufo ƙofar a guje na sakko na koma shiyyata da gudu Allah yasa basu ganni ba. Ina haki na shige ɗakina babu kowa a ciki ai saina sauke ajjiyar zuchiya kawai. Hijabina na cire kawai na shige bargo tare da lumshe idanuna. Buɗewa nayi ina hango yadda Alhaji ya murgina Hajiya ya hayeta.
Mrs BUKHARI [10/4, 10:29 PM] +234 810 593 2041: https://chat.whatsapp.com/I7uDGV8V2DQDVS5RHRi0St
https://wa.me/message/QBXV2PDE2Y3CI1
Kina neman inda zaki samu ingantattun kayan gwanjo wato thrifts ma yaran ki kwantar da hankalin ki yar uwa oumokasha thrifts store ta kawo muku kala kala kaya na fita kunya akan farashi mai sauki tun daka kan overalls jumpsuits bodysuit bibs jeans tops blouses da sauran kaya na kece raini from 0 to 15 years Muna garin abuja koh kaduna Muna tura kaya ko wani gari da yarda Allah quality da sauki shine taken mu
MRS BUKHARI 18