Kenza eBookz

Idan kaya ya gaji book book 4 - Chapter 18

Idan kaya ya gaji book book 4 - Chapter 18

Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 18: Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 18. Babangida:. Wasane gaskene Babangida dai yaƙi dawo da Ƴar shuwa, kuma…

4,355 words

Babangida:. Wasane gaskene Babangida dai yaƙi dawo da Ƴar shuwa, kuma bai tuntuɓi Malam akan dawowar tata ba shi baya ma son ganinta yana fatan Malam ya bashi umarnin ya saketa ne ya huta. Duk da yasan malan bazai taɓa aikata hakan ba. Ya warware sosai sai ciwo da ƙullin son Sabuwa da yake sarƙe da numfashin shi wanda yake tunanin shi zaiyi ajalinshi baya taɓa ji a zuchiyarshi akwai wata rana da zai daina jin son Sabuwa ba. Ya yadda sonta a jininshi yake. Ko tunanin Aurenta ya bijiro mishi sai yaita istigifari kawai amman babu ranar da aka taɓayi ta shuɗe ba tare da Sabuwa ta faɗo mishi ba. Abubuwa da yawa dai sun faffaru a taƙaice. Ranar daya je gida ɓarayin Malam duba su Mardiyya anan yake ji a bakin Malama wai zasu tafi Kano tarewar Sabuwa. Ji yayi jiri na shirin kayar dashi wallahi da yana da iko da ya hanasu zuwa amman ina yanzu su yaran Baba Malam ne. Ambulon ya samo yayi rubutu tare da cusa gudunmawarshi yaba Mardiyya yace ta kai. A wajen Malama Babba yake jin labarin ashe da Bashiru ne zai Auri Sabuwa kuma harma ya amince. A ranar dasu Mardiyya suka tafi Kano yake jin wannan labarin. Iyakar labarin kawai saida ya sakarma da Babangida zazzaɓi mai zafi, ya kuma ƙullaci Bashiru sosai. Yazo zai wuce a mashin zuwa gida ya tadda Baba Malam da Kawu Manga a ƙofar gida saiya faka mashin ɗin ya ƙarasa inda suke ya tsugunna ya gaishesu suka amsa.. "Dama ina son ko ban ganka ba in sa ayi mun kiranka. Kaje ka dawo da matarka Aisha sannan in ta dawo kace tazo. Kai kaje ka ɗakkota kuzo tare ma" A sanyaye Babangida yace. "Yanzu kake so Malam a ɗakko maka ita yanzu inje? " Dariyar dattijantaka Malam yayi yace. "Babangida kacigari kenan kamar gaske" Kai Babangida ya kuma sunkuyarwa illahirin kunya ta lulluɓeshi. "Kamar da gaske. Eh yanzu kaje ka ɗakkota kuzo. Jiya uwar tazo ta sameni ta shiga ma wajen gyatunarku. " "Shikenan Baba Malam sai mun zo. Har kullum ina dai sake jaddada neman afuwarka" Miƙewa yayi ya nufi gidansu Ƴar Shuwa kai tsaye. Gidansu Sabuwa ya kalla yayi murmushi abubbuwa da yawa sukaita dawo mishi harma yanajin inama jiya ta zama yau da yanzu Sabuwa tashice ba ta wani ba. Yaro ya tura aka kirawo Ƴar Shuwa. Tana fitowa da taga shine saita yashe baki duk da bata daɗe da cin kuka ba mama nata basu labarin irin dangin mijin Sabuwa da irin motocin da suka ɗauki Sabuwan a ciki da irin gwal ɗin data saka, harda Auren Hajiya da Maigogul yayi. Tayi kuka har saida hawayenta suka ƙare tas dan baƙar hassada. Ganin Babangida sai ya sake baƙanta mata rai fiye da da. "Ki shiga ki kwaso kayanki mu tafi" Sai tayi turus tana son tace ya saketa kamar yadda suka tsara da Mama. "Baki ji bane nace ki shiga ki kwaso yanaki_yanaki mu wuce ko? " "Sai yaune kaga damar zuwa kenan. To ni gaskiya bazan koma gidanka ba ka bani takaddata" "Takaddarki kike so? " Ya tambayeta cikin kakkaurar murya tare da ƙanƙance idanu. Tana kallonshi da suka haɗa idanu sai taji ina ko dukanta yake yi dole ta bishi. "Sai ka jirani ai. Ko gobe mama zata kaini" Shiru yayi hannunshi zube a ajjihun kaftaninshi. Baice mata komai ba ta juya ta shige gida sai gata da kayanta. Mashin ta ɗale sai gaban Baba Malam suka gurfana. "Aisha ko? Kin kyauta da kika fallasa asirin mijinki kinyi daidai. Dama Maras kunya sai maras kunya ƴar uwar fitsararshi. Ke yanzu ko wani zai tona asirin Mardiyya har dake kina Aminiyar Sabuwa? To bari kiji in kafa miki wata doka bana son in sake ganinki a cikin gidana ko wanne sha'ani kuwa za'ayi ke ko mutuwa akayi bana buƙatarki. Sannan idan na kuma jin abu makamancin wannan ya faru zaku sha mamaki daga ke har mijin naki. Mardiyya kininace ai ko iyakar kamannin da tayi dani dama ubanta kaɗai ya isa ya cire zargi da kokonto. Inma ba Ƴarshi bace mun karɓeta hannu bibbiyu balle a duk inda kininmu yake baya ɓata. Ya zame miki dole ki nemi gafarar Mardiyya a bisa tozarcin da kika yi mata. Mardiyya da kike ganinta jinin jikinace rayuwata wallahi zan iya fito na fito da Babangida ma akanta. Ku tashi ku bani waje" Zata yi magana yayi saurin ɗaga mata hannu ranshi a ɓace kamar me. Miƙewa yayi ya tafi ya barsu a wajen. Wani farin ciki ya lulleɓe Babangida jin maganganun Malam akan Mardiyya. Yau yaga soyayya tsantsarta. "Ai saiki tashi mu tafi ko?" Shima yayi maganar a hasale. Haka Ƴar Shuwa ta dawo ɗakinta ta sake buɗe sabon shafin iskanci da yawon bin gidan bokaye da maƙota sai ta kai har magriba a moƙota ko da itace da girki. Ta duƙufa wajen bama Malamai kuɗi akan ɓalɓanta Auren dai Mardiyya da Sauban. Sannan bafa ta mance da Sabuwa ba. Ta ƙudurce a ranta saita tarwatsa Sabuwa da ƴaƴanta ko da fa Tsirara zata yi yawo Wannan kenan:.

Sabuwa:. Idanuna na kulle kawai ina sauke numfashin a hankali_a hankali. Na kai kamar awa biyu a kwance kafin nayi bacci. Tunane_tunanena sun tafi akan kuskuren amince ma Alhaji Zaidu zan biyoshi tura da nayi. Yanzu shikenan matarshi tayi tunanin ko a matse nake gani bazawara. Babban haushin daya turniƙeni shine dole tasan tabbas nice kaɗai zan iya haurawa har zuwa ɗakin baccin Alhaji Zaidu. Ko da suna da yara bana tunanin ko da suna iya shiga turakar mahaifinsu zasu iya shiga a cikin irin darennan ba. Kaina ya ɗaure na jima ina tubkewa da warware menene manufar Hajiya akan abinda ta aikata. Kenan duk wannan kyautatawar da manufa take yi kenan ko? hmmmm Da waɗannan tunane tunanen nayi baccina kuma dasu na tashi. "Sabuwa yaushe kika shigo na jima a falo ina jiran shigowarki in shigo ɗaki sai naga har bacci ma kika yi? " Cewar Labbai dake tsaye a kaina. Wallahi ai ba kwana nayi a can ba banfi minti talatin ba na dawo gida cike da mutane" "Gaskiya kam. A gurguje kiyo wanka haɗe da alwala ai gara ki shirya da wuri gida cike da dangin miji dana kishiya, ki yi wanka ki saka kaya ki fito tas. Wanka nayi na ɓare sabon asuwaki na wanke bakina tas kana na ɗauro alwala na gabatar da sallah. Su Adama sunata gyare_gyare ni kuma na cancaɗa kwalliyata da wata jar atampa Aura mai fulawar goldin kala a jiki. Sadiya na nemo tazo ta buga mun ɗauri. "Yafa kamata ace i yanzu kin ƙware dai a ɗauri dan a gidannanne ake kishi da buga gasar kwalliya dan a burge miji." "Ai fa ta iya iskancine dai inta ganki sai tace sai ku zaku yi mata. Amman ai a shirye take ta bar ganin kishiyarta na haba_haba da'ita harda yi mata akwati. Ko da yake tafi kowa sanin waye kishiya tunda da guda nawa ta zauna wallahi ki buɗe idanunki dan ni ban faɗa da kirkin kishiyarki ba, kibi komai a tsanake kada kiyi gaggawa." Ni dai sai kallonsu kawai nake yi. Malama da Mardiyya ne suka shigo suka gaishemu nan suka zauna naita jansu da hira muna ta yi. Daga ƙarshe muka baro ɗakin Labbai na gyarawa na shiga ɗakin da su Hauwa da Malama Ƙarama suke muka gaisa. Muna kan gaisuwar muka jiyo shigowar mata kusan su biyar cikinsu Harda Hajiya a ciki. Ragowar biyun dai duk yadda akayi dangin mijine dan kamanninsu kusan ɗaya gaskiya. "Kaga Amaryar Alhaji Zaidu ashe har kin tashi kin buga kwalliya haka? " Murmushi nayi nace. Wallahi kuwa Hajiya. Ina kwana ya taro? " "Lafiya lau. Taro yau kowa zai tafi a barmu da gyaran gida kuma" Murmushi kawai nayi muka gaggaisa da fara'a da ragowar matan, ni dai sai kallona suke yi yadda kuka san sun samu sinima, musamman Hajiya sai kallon ƙurulla take yi mun. "To inaga muje ki ɗan gaggaisa da jama'a wasu da sun karya zasu tafi ko?" Kunga a daddaƙile take magana tana kaurara wuya na isa. Haka fa take yi. To bara in ɗakko mayafina" Sama na koma na sanyo mayafina da takalmi mai tsini na riƙo Labbai muka tafi tare dai duk aka gaggaisa anata yi mana adda'ar zaman lafiya haka. Daga ƙarshe muka dawo ni da Labbai. Su Adama na falo suna aikin ware cincin dasu alkaki wanda za'a ba dangin ango da dangin Uwargida, shima angon a ware nashi. Ni dai sama na koma ina haurowa aka kawo abincin karyawa. Farfesun jelar saniya da biredi da shayi ya ɗau madara da milo aka kawo wadatacce. Ina tsakiyar gado ina ci Alhaji Zaidu ya kira wayata. Murmushi kawai nayi, sai zuchiyata ta ɗakko hoton faifayin bidiyon jiya ta hasko mun. Sai naji na sosu. Wato kishi bala'i ne wallahi Allah. Ɗaga wayar nayi kamar ba'ai komai ba a ƙoƙarina na ganin na daure na kuma danne domin hakanne zai bani damar karantar Hajiya da manufarta. "Shalelena kin tashi lafiya ya sabon waje kuma uhm? " Lafiya lau mijin Shalele da fatan kaima ka tashi lafiya ko? " "Ki shirya zan shigo mu gaisa" Ido na zare tare da cewa. Haba dai a cike ɓarayin nawa yake ai ka dai barshi anjima kaɗan zasu tattara su tafi" "Shalelena kenan to in ke bakya son ganina zan zo mu gana da yarana kafin su tafi kuma in sallamesu uhm" Wayarshi ya kashe na lumshe idanuna abincin da ban iya cinyewa ba kenan na ajjiye a gefen gado na sauka na kuskuro bakina na dawo na haye gado. Daga ƙasa na jiyo anata gaishe_gaishe ya shigo kenan. Can na jiyo takun haurowarshi. A hankali ya murɗa ƙofar ya shigo bakinshi ɗauke da sallama yasha shadda mai ruwan sararin samaniya. A hankali ya tako har inda nake ya zauna a gefen gado yana fuskantata. Hannuna ya kamo dukka biyun ya tasoni tsaye tare da yi mun masauki kan cinyarshi guda ɗaya. Hannunshi ɗaya riƙe da ƙuguna ɗayan hannun riƙe da hannuna yanata kallon tafin hannuna da yasha ƙunshi Bai ɗago ya kalleni ba, kuma ko da na gaisheshi bai amsaba. "Shalelena kunyarki ma nake ji. Jiya na kwana da ƙishin ruwanki sosai. Kiyi haƙuri na gayyaceki uwargida ta nuna ikonta akan turaka. Aimun afuwa nasa kinga abinda nasan dole zuchiyarki saita sosu aimun Afuwa dan Allah. Kinsan tazo ai bazan koreta ba, kuma bazan hanata kaina ba uhm? Sabida duk macen da akai mata kishiya uhm dole a lallaɓata ke kanki ba zaki so in koreta ba. Aimun afuwa Shalelena na kwana wallahi cikin damuwa da tunanin halin da zaki shiga. Ina roƙonki kada kiyi wani tunani marar kyau ko a kaina, ko a kan ita Hajiya" Wallahi a lokacin naji na ƙara sonshi ya ƙara yin lub a cikin zuchiyata sosai. Wai yau ni miji ke ba haƙuri akan abinda ma ba laifi yayi mun ba? Allah Alhamdullillah. A hankali cikin raɗa a kunne nace dashi. Babu komai mijin Shalele baka buƙa... " Ji nayi yayi saurin ƙanƙameni yana. Sauke numfashi a hankali. Mun daɗe sosai a hakan daga bisani yace. "Nagode da fahimta uhm. Yau ai zaki ci gidanku" Ya faɗa tare da lakace mun hancina mu kai murmushi tare. "Kirawo yara mu gaisa inaso zanje in gaishe da su Alhaji Baba da abokanshi da Kawu Isuhu ƙaninshi" A hankali jiki a mace na fito na kira su mardiyya muka dawo tare, ni na zauna a kujera su kuma suka gurfana a gabanshi cike da ladabi da biyayya suka gaisheshi inaji yana musu tambayoyi dangane da karatu. "Duk inda na jawo miki zaki iya ƙarashewa kamar dai na musabaƙa kin tabbatar zaki iya? " Sai da Mardiyya tayi murmushi irinna ubanta sak tace. "In sha Allah Abba zan iya" Ai kuwa haka sukaita yi tana cabkewa. Suka dawo ɓangaren hadisi yace ta bashi ƙanana goma. "Abba zan baka ashirin" Murmushi yayi ɗakin tsit sai tashin amon karatun Mardiyya haka takawo hadisai ashirin babu gargada. Malama tace itama fa saita kawo uku. Itama ya bata dama ta kawo nata. Yayi murna da farin ciki gaya kuɗi ya basu masu kauri kana yace zai turo Hajiya da kaya ta basu harda su Aminu ma a kai musu nasu. Sallama yayi mana, su Adama da duk ƴan rakiya ya bibbisu da kuɗaɗe. Ana cikin haka sai ga Maigogul tare da tawagar abokanshi su kusan bakwai da Uzairu zuchiyata na takwas ɗinsu. Illahirin kunya saita kamani. Shi kuwa Alhaji Zaidu cikin haba_haba ya tarbesu harda zubewa a ƙasa domin kwasar gaisuwa. Maigogul ya riƙo hannunshi ya ɗagashi. "Ba girmanka bane Alhaji. A dai miƙa hannu a gaggaisa. Ai da kaina dai nace bari muzo. Abokaina sun matsa sabida kasan sana'ar bata fiye son ana nisa ba in ba dai kasuwancin ne ya kawo tafiyar ba" "Allah Sarki. Nima dama yanzu nake shirin inje ɗin in sameku. Ayi haƙuri na ɓata lokaci" Cicib yace. "Babu komai Alhaji wallahi, ai mu bamu da sanya gamu mun tattako mu kam" Ni dai dasu Adama muna tsaye. Su kuma Maigogul sun zazzauna haka duk muka gaggaisa. Maigogul ya kalleni yace. "Lolona to yaya. Kinga dai wannan alƙaryar duka taki ce ke kaɗai Allahu Akbar. Allah dai yayi albarka ya baku zaman lafiya. Allah yasa a aikin hajji zamu yi babbar sallah tare dani dake da sirikina" Sai ya sake washe baki. Abokanshi suka bishi da Ameen harda Uzairu zuchiyata. "Adama a kawo ruwa da ɗan abun motsa baki mana kunzo duk kun tsattsaya a kanmu" Juyawa Adama da Labbai suka yi. Shi kuma Alhaji Zaidu da jin haka yace yana zuwa. Ai kuwa yana fita na kirawo Maigogul gefe. Yaci ado ya sake saka alkyabba baƙa amman bayyi rawani ba. Ko ina ya samu wannan salon oho gashi shigar ta amsheshi. Kaifa kace ka dena Maigogul sai kaita maganar kawalci bayan kamun alƙawarin ka dena. Sannan dan Allah maigogul me yasa zaku zo yanzu fa yake shirin zuwa wajenku. Kazo kace a kawo abinci, ga aikin Hajji ka roƙa. Maigogul ina tsoron kada ya gaji da halinmu fa ya koroni ko kuma ya juya mun baya"... Bub ya buge bakina irin na inyi shiru ba mai cutarwa ba. "To kiyi haƙuri kinga wallahi ni nayi tunanin daɗi zaki ji ganin ubanki da abokanshi. To lolo ki dai yi haƙuri ko? Sai in kiyaye gaba. Ki dena wannan koke_koken ai gidannan kinsan Allah kin shigo kenan lolo babu rabuwa sai dai.... Dawowar Alhaji da Hajiya, da ƙannenshi biyu tafe da manyan kuloline yasa maigogul ya koma ya zauna ni kuma ina gefe, Hauwa ma fitowarta kenan da tana ciki. Gaggaisawa akayi Hajiya harda tsugunnawa. "Ah dan mahammada rasulillahi tashi dan Allah Hajiya. Ba sai kin tsugunna ba. " Cewar Maigogul fuskarshi ɗauke da dariya. Miƙewa tayi tana murmushi. Miƙo mun ledojin hannunta tayi na amsa tace nasu Mardiyyane suka dai yima su Maigogul sallama suka fita. Alhaji yaso ya tafi Maigogul yace sai dai yazo yaci abinci. Zanyi magana Alhaji Zaidu ya dubeni ya lumshe idanunshi halamun in bari. Dole na koma sama. "Lolo ba zaki zo muci tare ba? " Ni na ƙoshi" Na faɗa ba tare dana juyo ba Tsabar haushi. A ɗakina na tadda su Adama harda Hauwa dasu Baba Laraba suna maganar. Ni ko dan baƙin ciki kuka na fashe dashi. "Kima dena ɓata hawayenki in dai ubanki ne baki ga komai ba. Bare yanzu shima aure yake yi a Kano yadda aka auroki haka aka auroshi. Billahillazi bai yi komai ba saiya turguɗe miki auren tukunna hankalinshi zai kwanta. Ya kwaso ƴan iskan abokai sun baza riguna zasu zo suyi bara ƴar nasu ta samu gidan hutu. " "Hauwa ya isa haka mana kina ɗaga murya. Mu dai dake komai namu babu sirri. In sha Allah ba zamu ga haka ba" Cewar Rahama da ranta ya gama kaiwa ƙarshe da ɓaci. Baba laraba tace. "Allah ya kyauta. Mu kam yanzu zamu soma shirin tafiya. Tun asussubar fari kayi nayi take ta kirana ko lafiya oho. Lolo mun kaima kishiyarki cincin ɗinta dangin mijinki ma akwai babbarsu a mata na danƙa mata da, uwargida na bata na ango nace ta ajjiye mishi. Ni da Adama dake mu muka kai ta bamu turamen zani biyu da dubu ashirin ashirin. Allah ya baku zaman lafiya amman kishiyarki dai mutum ce gaskiya hannunta a sake yake." Ni dai sai binsu da ido kawai nake yi. Nan suka ci gaba da shirye_shiryensu. Uzairu zuchiyane ya hauro ya kirawomu wai su Maigogul zasu tafi. Kuɗi na ɗebo na fita. A hannun maigogul na ba da rabi. Ragowar na damƙa ma Cicib shi da su kawu Isuhu. "To shikenan Lolo Hajiya ma ta aiko mun da shadda harda kuɗin ɗinki kin ganta." Ko magana banyi mishi ba" "Zan rakasu su zasu wuce Dutse yau. Ala bashi gobe sai in kawo ita Iyali tazo ta kuma ganin waje." "A_a Maigogul ai zata zo ma da kanta zasu yi waya tafa san gidan ita ta kawo mu muma" Cewar Rahama. Yana dariya yace. "Hakane hum Hakane to babu damuwa mun tafi Lolo. Ke kuma Hauwa sai kuma na dawo Dutse wajenku" Murmushi Alhaji Zaidu yayi kawai. Ni kuwa kamar me haka nake ji. Sai da aka rabu dasu lafiya kana na samu nutsuwa. Su Adama sha ɗaya suka tarkace yanasu _yanasu suka kama hanya. Saida suka gyara mun waje tsab. Ina hawa ɓarayina na sake buga wanka na sakko falo. Dangin miji suka ce Salamu Alaikum Ai nan muka wuni akayi kaca kaca da gidan baki ɗaya akaci abinci duk aka tattaka shinkafa a kafet aka zubar da ruwa abubuwan kamar ma da gayya suke yinshi. Sukaita hirar zumunci ni dai suna sakani ciki sai dai nai murmushi haka, suna da fara'a sosai sai haba_haba suke yi dani. Ga ilimi a cikin maganganunsu magana ɗaya biyu ta ukun larabci zaku ji anyi. Basu suka watse ba sai magriba da suka ci abincin dare. Nan ni kuma na shiga gyare_gyaren ɓarayina gashi babu mataimaki. Ga kwanukan abinci da suka ci komai a wajen suka bar mun fa. Ina gama kintsa wajen na banka turarukan wuta a gidan na Mrs BUKHARI gidan ƙamshi cikin ƙanƙanin lokaci gida ya kaure da ƙamshi mai sanya nutsuwa turarukanta suna da ƙarfi da mugun kama waje sosai gaskiya. Na zaɓi rigar baccin da zanyi amfani da'ita na ɗaura akan kabbasa na zuba turaren kaya bayan na feshe jikin kayan baccin da kabbasiyya turaren fesawa kafin turara kaya, na bisu da turaren maiƙo shima da ake ɗiɗɗigawa a jikin kaya kafin a ɗaura akan turaren kayan. Na jawo ƙofar na sakko saida na game wanke_wankennan tas bani na gama ba sai wajejen taran dare. A gurguje nayo wanka na saka doguwar rigar yadi mai laushi nabi ko wacce kusurwa a jikina da humrar Mrs BUKHARI. Na shafe marata da humrar matan aure. Jigidata wacce take a tsume cikin turare na ciro na ɗaura itama daga wajen Mrs BUKHARI ɗinne wannan mata ƙarshece ni wallahi burgeni take yi sosai gata da lafazi. Na sauko na zauna ina ƙarema falona kallo ina jin wani farin ciki na ziyartata marar misaltuwa. Sai kawai naji an buɗe ƙofa kuma da ɗan mabuɗi tabbas nasan Alhaji ne. Ai kuwa ilai shine saye da jallabiya mai ruwan toka kanshi da hula. Amman sai naga babu nutsuwa tattare dashi. "Shalelena aimun Afuwa Hajiyace babu lafiya kuma ciwo sosai shine zan kaita asibiti nace bari in sanar dake" Subhanallah meya sameta Alhaji? " "To shine sai munje tukunna. Ba jimawa zamu yi ba in sha Allah. Ga ɗan mabuɗin turakata ki haura kije ki jirani acan" Amsa nayi a sanyaye. Allah ya bata lafiya sai kun dawo. Dan Allah kayi mata sannu." Fuskata ya shafa kawai ya fita. Ta taga na leƙa naga shigarshi cikin mota da ma fitarsu daga gidan. Ajjiyar zuchiya na sauke kawai. Kitchen na shiga ashe ba'a ɗaura silindar gas ba. Sai buta na jona na dafa shayi naci cincin da nakiya na ƙoshi. Banje turakarba sai kawai na saka kayan baccina na kashe komai na haye gado. Sai naji ina kewar gida. Wallahi da kawai na tuno da rigimar gidanmu da sababbin rigingimun Rakiya data buɗe sai nayi dariya. Adama na tsinci kaina da kira. Ai kuwa ashe ita firgitata nayi. "Lolo ince dai lafiya ko? " Dariya nayi nace Ah lafiya lau. Hajiyace ba lafiya Alhaji yaje kaita asibiti shine nace bari in kiraki inji kun koma gida lafiya? " "Hmm lafiya lau Lolo. Nima jibi sai Malam madori kuma Rahama da Baba Laraba zasu kaini." To Allah ya kaimu. Zamu yi magana zuwa gobe da safe zan kiraki mu gaggaisa duka harda su Rakiya" Sai ta kece da dariya tace. "Rakiya daru. Ai ɗazu ta kira Maigogul a waya matarshi ta ɗauka Rakiya ta dinga narko ashar baki ji ba. Har kuka fa saida tayi wallahi, sabida Hajiya data ɗauka sai tace wai Honey bacci yake yi sai dai Rakiya ta kuma kira. Kai kishi masifane musamman irin nasu Rakiya" Nan suka shiga bani labari da Rahama. Daga ƙarshe dai mukai sallama na ajjiye wayata. Saida na duba agogo sai naga sha biyun darene ashe. Lallai munsha hira da ƴan gida. Gashi har lokacin Alhaji Zaidu bai kirani ba. Inason kira ina fargaban kada suga kamar na matsune in soma kwana turaka wallahi shine dalilina da yasa ban kira ba. Ina wannan tunanin sai ga kiranshi kuwa ɗan halak. Ɗagawa nayi da sallama ya amsa mun muryarshi a tausashe. "Kinganmu a asibiti jikin Hajiya yayi tsanani ciwonta ne kamar ya tashi sai dai ki taya ta da adda'a, ciwon inya tashi muna shan wuya Shalelena Sannan bazan dawo ba Shalelena bazai yiwu in baro yayarki a gadon asibiti in dawo gida ba uhm. Amman ina mai baki haƙuri zuwa gobe dai da safe zan shigo gidan kinji? " A sanyaye nace. Bai kamata ba kam lafiya ai itace komai. Wallahi babu komai Allah ya bata lafiya" Ajjiyar zuchiya ya sauke yace. "Wallahi inason wannan sanyin naki yana sake narkani cikin soyayyarki. Gaki da sauƙin kai uhm. Ki kwanta kiyi baccinki da safe angonki zai zo inda kike in sha Allah. Ki kwana kina mafarkin Zaid ɗinki. Ina sonki Amaryar Zaidul'abideen muah." Murmushin jin daɗi nayi mishi mukai sallama na kwanta. Murmushi kawai nayi wanda ni kaɗai nasan dalilin murmushin Dama ga gajiyar biki gata aikin gyaran gida ai sai bacci. Wani sassanyan lafiyayyen bacci nayi zuchiyata sawai da'ita gwanin daɗi wallahi. Bani na farka ba fa sai shidan safe na makara. Shima kiran Maigogul ne ya tasheni" Kunga Maigogul zai soma ko?

Me kuke tunani game da Hajiya ne, ga ciwo ya tashi har an bata gado Ku faɗi ra'ayoyinku Mrs BUKHARI [10/4, 10:29 PM] +234 810 593 2041: https://chat.whatsapp.com/I7uDGV8V2DQDVS5RHRi0St

https://wa.me/message/QBXV2PDE2Y3CI1

Kina neman inda zaki samu ingantattun kayan gwanjo wato thrifts ma yaran ki kwantar da hankalin ki yar uwa oumokasha thrifts store ta kawo muku kala kala kaya na fita kunya akan farashi mai sauki tun daka kan overalls jumpsuits bodysuit bibs jeans tops blouses da sauran kaya na kece raini from 0 to 15 years Muna garin abuja koh kaduna Muna tura kaya ko wani gari da yarda Allah quality da sauki shine taken mu

MRS BUKHARI 19

GIDAN B HOUSE:.

"Nace lafiya ya ina miki karatu bakya mayar da hankalinki ne. Zaki ajjiye wayar ko saina farfasa wayar? Haba ki bani hadda aya biyu kin kasa ina ƙara miki kin kasa mayar da hankalinki. Bari kiji Aisha ba wai tubana zaisa matana su samu lasisin rainani bane wallahi babu wacce ta'isa. Na lura abun naku ya wuce gona da iri fa, wannan wanne irin buyagine hiye" Cike da faɗa yake magana dan tura ta kaishi bango akan sha'anin gidanshi ko wacce ranar girkinta da gwaramar da zai shiga ya tarar Hameeda ce kaɗai yaga kamar a kintse ta dawo zawarcine ko menene dai ta ladabtu ba irin Hameedar daya sani da bace. "Kayi haƙuri Jannaty kaga kayane nake son sara na sai da gold ɗina shine matar take tutturomun da'ita muke magana amman kayi haƙuri." "Matsalolinki da yawa. Ga yawon maƙota kinga wallahi bazan ɗauki duk wannan abun ba. Sannan bazan hanaki kasuwanci ba tabbas da gwal ɗinki na auroki amman ki sani bafa zaki fake da kasuwanci ki ɓige da yawo ko nemo rikicin kuɗin mutane ba. Sannan gargaɗi nagaba shine. Wallahi Allah ɗayane duk ranar dana sake shigowa ɗakinki na tarar da matan maƙota a kan gadona ke a cikin ɗakin baccinnan to komai zai iya faruwa su kansu matan inaga saina kulle ɗakin nayi musu duka. Sabida na lura so kike ki turani baki san waye Babangida kacigari bane labarina kike ji" Yana gama faɗar haka ya miƙe ya fita waje kawai ya samu dakali ya zauna badan komai ba sai dan ya huce ko zai samu sauƙin zuchiya. Sai da zuchiyarshi ta sauka ya shiga ɗakin tana ganinshi ta sauke waya a kunnenta. Gadan_ gadan ya nufo ta tare da fisge wayar yadda ta nuna halamun rashin gaskiya data ganshi sai yake zargin ko da namiji take waya. Zarah yaga an rubuta duk da haka sai yake ganin ai gidogace irin nashi na da. Sau nawa_ nawa yake sama macce sunan maza. Danna kiran Zarah yayi tare da saka wayar a buɗe tana ta ruri kamar zata tsinke sai Zarah ta ɗaga da murya tattausa tace. "Ba mai gidan bane ya dawo ba? Kije ki bashi hadda kada ki kuma laifi" Ajjiyar zuchiya Babangida ya sauke tare da datse wayarshi. Yana jin kamar yayi ma mai muryar farin sani. "Wato wannan abinda ya faru har kin kira ƙawarki kina fesa mata ko? Ya ilahi ina zan saka raina?" Wayarta ya tsilla kan kujera yayi shigewarshi ciki ya kwanta yanata saƙe_saƙe ita kuma madigar a kan kujera ta mimmiƙe abunta taƙi shiga ɗakin tunda tasan tana shiga zai hayeta. Washegari ko data gaisheshi ƙin amsawa yayi, ta bashi abinci yaƙi ci. Da zai fita ya ajjiye mata kuɗin cefane yayi tafiyarshi ya barta a tsaye tana hararar bayanshi. Da Sumy suka haɗa idanu itama da hararar ta bita harma da daɗi da tsaki. "Aikin banza da wofi. Tayi komawarta ɗaki rai a jagule tanata tunanin Sabuwa da Sabuwar rayuwar data shiga.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull