Kenza eBookz

Idan kaya ya gaji book book 4 - Chapter 19

Idan kaya ya gaji book book 4 - Chapter 19

Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 19: Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 19. GIDAN MALAM:. Da yamma lis sai ga su Mardiyya sun dawo. Malam na zaune…

3,545 words

GIDAN MALAM:. Da yamma lis sai ga su Mardiyya sun dawo. Malam na zaune dasu Adda'u a ƙofar gida sai ga su. " Mardiyya kune a tafe har an gama bikin kenan. Ƙarama an dawo ko? " "Malam kenan kana waje ka tusa jikoki a gaba anata lele. Allah yayi dawowarmu. Sai da ma muka huta a can gidansu Sabuwan kafin muka tawo dake mota har tsakar gidansu ta shiga damu" "To madallah sannu da zumunci. Ita kuma Allah ya basu zaman lafiya. Mardiyya Saratu kuje ku huta" Malama Ƙarama tace. "Akwai cincin naka da Sabuwan ta bayar a kawo maka na ajjiye maka a turaka, da shadda" Murmusawa yayi yace. "To shikenan saina shigo ɗin. Ai da bakya gidan babu daɗi har duhu yayi mun, su Aminu ke ɗebe mun kewa" Murmushi tayi irin na matan da masu tsantsar ado da kunya wacce tazo har a al'adar malam bahaushe. Wanda a yanzu mata an zama fitsararru da sunan wayewa. Miƙewa suka yi yuu suka bisu dukka ciki. Murmushi Malam ya bita dashi kawai. Da daddare sai ko ga Babangida yazo wajen su Mardiyya. Malam ya bashi dama ya shige Suna zaune a ɗakinsu Mardiyya sun buɗe cincin dasu atampa da shadda ga kuɗi sunata zuba surutu ya shigo. Kayan yake ta kallo su kuma baki a haɗe suke mai sannu da zuwa har dai ya nemi waje ya zauna. Nan Malama ta shiga zubo mishi surutun biki da irin kyan gidan umminsu. Babangida sai haɗiɗiyar yawu yake yi. "Baba kaga duka wannan sabon Babanmu ne ya bamu. Kuma yasa munyi mishi karatu ni da Adda. Baba dan Allah zan... " A_a uwata kina tare dani ba zaki je ko'ina ba. Malam bazai bari ba in yaji ciwonshi zai tashi. Kina so ciwonshi ya tashi ne? " Tayi saurin girgiza kai. "To in bakya so kar kice komai. Nima bazan so ba" Aminu yace. "Amman Baba zaka dinga kaimu wajen Ummi? " Ai sai ya ɗaure fuska tamau. Me ya tuna kuma sai yayi murmushi yace da Mardiyya. "Kin bata saƙon nawa? " Mardiyya ta ɗago tace. "E Baba na bata. Amman dai a jaka ta saka" Shiru yayi yana nazari. "Bata buɗe ba kenan har kuka tawo kawai a jaka ta jefa? " "E Baba a jakar hannunta ta jefa, to kuma muna isa Kano wajen Dina muka wuce" Baki ya buɗe tare da jinjina kai yace. "Au har Dina ma akayi kenan? Ai shikenan Sabuwa" Cincin ta ƙulla mishi mai yawa ta ƙirgo kuɗi daga cikin kuɗin da Alhaji Zaidu ya basu ta haɗa da cincin ɗin. "Baba gashi. Dan Allah kada kaƙi karɓa ni ɗiyarka ni na baka" Cikin jin kunyar Mardiyya ya karɓa hannunshi na rawa yau shine riƙe da cincin ɗin bikin Sabuwa da wani ƙato? " Ai saiya miƙe ya fice kamar kububuwa. Ko da ya fito malam baya ƙofar gidan mashin ɗinshi ya hau ya fice da sauri. Har zai wuce tsohuwar majalisarsu sai dai ya dakata wallahi ko gidan baya son zuwa sam. A hankali ya isa tare da zama ya buɗe misu waɗannan kayan fulawa. Suna ci anata gulma da musu. Shi kuma bidiyon raya sunnah tsakanin Sabuwa da mijinta sai hasko mai yake yi harda yadda Sabuwa take karya wuya zuwa gefe saida ya hango. Da mugun zafi ya ɗaga shayin gahawa ya ɗaɗɗake zafin na ƙona maƙogoronshi da ƙirjinshi har zuwa cikinshi. Idanu ya lumshe kawai ya kwace sigari a hannun Gaddafi ya soma zuƙa. Har ya kusan shanyewa zuchiyarshi ta daka mishi tsawa tare da hasko mishi kuskuren daya tabka. Zuchiya tana magana da mamallakinta kamar yadda ƙawa ke magana da ƙawa. Wani sa'inma zuciya tana iya rabuwa ta zama kashi kashi tare da yin maganganu mabanbamta a lokaci guda. Miƙama Gaddafi sigarin yayi ya dafe kanshi kawai idanunshi a rufe. "Babangida kacigari duniya ta ɗau zafi mata sai caja mana kai suke yi. Dama ance wanda baiji bari ba zaiji hoho. Kaganni wallahi banƙi mu kwana a majalisarnan ba sabida tsabaragen yadda bana ƙaunar in shiga gida ko da kuwa da wasa ne. Duk ɗakin daka shiga kamar jira dama take yi. Sai kaji an soma kawo maka ƙara, ko ka shiga kaji suna zage_zage. Inma ka saki mace dole wata zaka ɗakko. Ni mata ma duka sun ficemun a kayi na" Musa yace. "Kunga ga Ladidi zata wuce uwar gantali yau tadawo ma da wuri" Idanu Babangida ya buɗe a hankali ya dubi Musa. Hankalinsu duka yana kan Ladidi har da masu lashe bakunansu. Idanu ya sake lumshewa yana jin zuchiyarshi na yi mishi tururi. Ada yafi kowa son Ladidi tazo wucewa ya more kallon sifikun zamanta. Shi dake ma ya fisu neman zunubin har fata yai tayi mijin Ladidi ya gaji da'ita ya sauta shi kuma ya aureta. Ladidi wata macece marar kamun kai da nutsuwa. Babu ranar duniya da Ladidi bata fita unguwa. Gata Allah ya hore mata zati. Sai take amfani da hakan ta hanyar saka kayan da zasu bayyana wannan zati. Bugu da ƙari tana tafe mazaunanta suna yawo a zani ko a siketi kamar an ƙulle ruwa a leda kuma da gangan take yi. To su kuma jama'ar majalisar su Babangida dake sheɗanune basu da wani abun nishaɗi daya wuce musu kallon sifikun Ladadi. Allah yasa mu dace ya tsare mana mutuncinmu. "Ku yanzu dan Allah wai ba zaku shiryu ba ko me kuke so ku zama ne? " "Ahh kaga ɗan malam kaƙi halin Malam tubabbe. Tunda kai ka tuba ka barmu muma zamu tuba watarana. " Wacce rana Sale? Ranar da lokaci ya ƙure mana ƴaƴanmu suka lalace, ko kuwa ranar da zamu yi nadama marar amfani, oh ko ranar da muka jimu a kabarinmu kenan shine ranar nadamar? Muji tsoron Allah mu tuba muita roƙon Allah yafiya Ai ko auri saki da kallon jikin matan mutane, da gulmar magidanta masu wucewa kaɗai aka barmu manyan zunubaine. Ba'a maganar shirka, ba'a maganar zinace_zinace cikinmu harda masu zina da matan mutane. Shin bama tsoron kamun Allahne. Ko ko dai bama tsoron ranar da nadamarmu ba zata amfanemu da komai ba? Ga wani hadisi zan bamu kyauta. An karɓo daga Abu Hamza, Anas ɗan Malik, yaron gidan Manzon Allah (S A W) yace, Manzon Allah ( S A W) yace. "Ɗayanku ba ya zama mai cikakken imani har sai ya so wa ɗan uwanshi abin da yake so ma kanshi." Bukhari (#13) da Muslim (#45) suka rawaito. Abu Hamza shi ne Anas ɗan Malik yaron gidan Annabi ( S A W) mai yi ma Annabi (S A W) hidima. Shi yake cewa. Na Abokanci Annabi ( S A W) tsawon shekaru tara ko goma, bai taɓa ce mini ba, dangane da wani abu da na yi ba daidai ba, don me ka yi kaza? Bai taɓa ce mini ba, dangane da wani sakaki da na yi, don me ba ka yi kaza ba? Shekaru goma yana matsayin yaron gida a wurin Annabi ( S A W) Mahaifiyarshi ita ce ummu Sulaim, matar Abu Ɗalha, wacce sadakin ɗaurin aurenta shi ne musuluntar Abu Ɗalha. A nan da Annabi (S A W) ya ce Ɗayanku ba ya zama mai cikakken imani, har sai ya so ma ɗan uwanshi abin da yake so ma kanshi. Wannan yana kore cikar imani ne, bawai yana kore asalin imani bane. Irin waɗannan hadisan suna da yawa. Wani wanda bai fahimcesu sosai ba, sai ya kafa hujja da su bisa cewa, mai aikata saɓo zai iya kafirta, kamar yadda khawarijawa suke yi. Sai su ɗauki irin waɗannan nassosi, sai su ce ai duk mai saɓo ya kafirta, kuma in ya kafirta zai dauwama a cikin wuta, don Annabi ( S A W) yace kore musu imani, ya ce mazinaci a lokacin da yake aikata zina ba shi da imani, ɓarawo a lokacin da yake yin sata bashi da imani, da sauran irin dangin saɓo da Annabi (S A W) zai faɗa, sai ya kore imanin ya ce babu shi. To manzon Allah ( S A W) ba yana kore cikar imani abin da yasa muka ce ba asalin imanin yake korewa ba. Shi ai masu saɓo Allah da kanshi ya kiraye su da sunan imani sannan ya ce su tuba. In basa saɓo a ce su tuba? In da kafirta suka yi a sa musu sunan muminai? Allah ne fa ya ce. ( Ya waɗanda kuka yi imani ku tuba zuwa ga Allah, tuba wadda take tabbacciya...) suratul Tahriim:8 Da ba musulmai ba ne a kira su da sunan imani? A nan hadisin da aka ambaci ɗan uwa., to ƴan uwantakar musulunci ake nufi, ba ƴan uwantakar jini ba, gari ba, bata ƙabila ba. Allah yana cewa. (Sani dai kaɗai, muminai ƴan uwa ne don haka ku sulhunta tsakanin ƴan uwanku kuma ku tsare dokokin Allah domin aji ƙanku) Suratul Hujuraat:10 Kenan Dukkan dangin Alherin da kake so wa kanka, haka ake so ka so ma kowanne ɗaya daga cikin ɗaiɗaikun Al'ummar musulmai, dukkan sharri da ba ka so wa kanka, to irinshi ake so ka guje ma dukkan ɗaiɗaikun al'ummar Musulmi. Ya ku abokaina ina mai kiranku zuwa hanyar tsira Muji tsoron Allah, mu guji duniya mu dena sakin matanmu, mu dena azabtar dasu, sannan mu dena shaye_shaye, mu dena bin bokaye, uwa uba mu dena zinace zinace. Ku sani da duk waɗannan abubbuwan da muka aikata in muka roƙi Allah zai yafe mana musamman in munyi kyakkyawan tuba, idan kuka shirya wannan majalisar gulman saida zama dandalin ɗaukar karatu zan dinga muku karatu kyauta, kuɗin da Mardiyya ta bashi ya damƙa a hannun Musa." Miƙewa yayi ya hau mashin ɗinshi ya barsu babu guiwa. Har ga Allah yana zuwa majalisar ne ba dan hira ko dan sha'awar zaman ba. Yana leƙowane sabida a cikin hikima ya dinga musu nasiha wala Allah wasu daga cikinsu su tuba kamar dai yadda shi da Mustapha suka tuba suka ture duk wani aikin ɓarna.

SABUWA MAI SABON AIKI😆 Da sauri na ɗauki wayar. Ina karawa a kunne yace. "Lolo ashe kishiyarki mutuniyar arziki babu lafiya kuma? " E maigogul a asibiti suka kwana? " "Ke kuma kika kwana a gida sabida iskanci lolo? To kiji in faɗa miki ki tabbatar yau kin kwana da'ita a asibitin. Ai da haka ne zaki ƙara dasa kanki a zuchiyar miji da danginshi. Lolo kifa buɗe idanunki ras dan abu ta kazanki, kinga ai yadda take dakewa take shiga lamuran mijin da daɗi babu daɗi duk abinda yake so yi take yi, ki nuna kin fita kirki da son kyautatama jama'a. Wallahi lolo a irin kirkin Kishiyarki sai kinyi da mugun gaske zaki ci nasarar zama tauraruwa a zuchiyar mijinki dama danginshi. Kada ki sake ki zama koma baya Lolona, da sai ki bisu duk ku ruguntsuma ku kwana a asibitin ai tunda shi shegen ciwon sai yanzu yaso tashi kema sai ki nuna ai Yayarki ce kun zama ɗaya ki ƙwace jinyar sai kiga anyi saurin sallamota, amman kin bar mata miji a asibiti ke kina gida ba sai ai wata guda ba'ayi sallamar ba ma dan abu ta kazanki. Maza dai ki zauna kita sanya a irin wannan babban gida. Lolona akwai aiki kashirɓan tattare dake, sai kuma kinyi tsayuwar daka zaki ci nasara, mijinki yana mugun sonki, ki taya shi ku tattala wannan son, kada ki bada ƙofa kiyi wani silais mistek Yanzu dai a gurguje ki samu kiyi mata lafiyayye girki sai kuje ki kai mata sai kiyi zamanki har sai an sallameta zaki sha mamakin yadda mutuncinki zai daɗu a idanunshi, dan ita ƙila tafi son mijin yaita kwana ai shi kaɗai acan. Babu irin maɗen da bamu sanshi ba, kin ganni da ido, ko da gira akayi wani abu wallahi nafa sani ku bar ganina haka tas nasan me nake yi Lolo, dole saina yi tsayuwar daka a kanki. Muma zamu zo da Hajiya, ki zage ki ƙure gayu ki saka gwal" Da sauri na miƙe nace. Ba sai kunzo ba Maigogul kuyi zamanku" Sai naji jikinshi yayi sanyi har da ajjiyar zuchiya. "Lolo kina jin kunyar nunani a matsayin uba kenan. Ko kuwa ƙyamata kika soma yi ne Lolo? To shikenan zan zauna bazan zo ba lolo" Ya salam sai hankalina naji ya tashi. Kafin in yi magana maigogul ya datse wayarshi Yana datsewa Wayar Adama ya shigo amman filashin ne. A gurguje nayo alwala nayi sallah. Maigogul na soma kira kamar ma bazai ɗauka ba sai ya dai ɗauka. Maigogul wallahi ba haka nake nufi ba. Ban gujeka a baya ba sai a yanzu? Lolo tana tare dakai duk rintsi" Sai yayi wannan dariyar dana tsana. "To shikenan Allah yayi albarka. Maza ki haɗa kayan kari maza jeki sai mun zo muma, duk abinda ta nuna tana so kiyi wuf ki tashi ki bata, ki fishi kulawa da'ita" To shikenan a gaida Hajiya Balaraba" "Hahahahh zata ji to" Ya kashe wayar. A gurguje nayi wanka na goge bakina, na saka riga da siket na atampa super, na saka ɗan kunne da sarƙata ta gwal da zobe. Maganganun Maigogul sai yawo suke mun a kaina inata nazarinsu da kyau ina rarrabesu ina ɗauka da ɗaɗɗaya. Dukkan abinda ya faɗa wallahi gaskiya ne. Murmusawa kawai nayi. Maigogul kenan. Ina kan ƙafar bene Alhaji Zaidu ya shigo. Ganin ina sakkowa yasa ya nemi waje ya zauna a falo kawai. Baya cikin nutsuwarshi ai dole ciwon mata ai akwai tashin hankali da ciwon miji. Allah ya taimaki mai taimakona barka da safiya ya Hajiya da jikin kuma? " Hannuna ya riƙo yaimun masauki a cinyarshi ya dubeni yace. "Kin tashi lafiya? Jikin Hajiya to da sauƙi za'ace tun jiyan da sukai mata allura har yanzu da na tawo bacci take yi" Kanshi ya cusa a ƙirjina yana shaƙan humrar manyan mata dana shafa mai wani irin sanyin ƙamshi mara ƙarfi dake nasan fita zanyi. Allah sarki nima sakkowa nayi zanyi abincin da za'a kai asibitin. To gas ɗin ashe ba'a ɗaura silinda ba, nace ko kicin ɗin Hajiyan zanje in yi girkin a can" Ɗagowa yayi muka haɗa idanu. Ya shafo cikina yana murmushi. "Haba Shalele uhm. Ai Hauwa mai aiki ta gama komai yanzu haka wanka zanyi kawai in kai musu abincin. Kema nace ta zubo miki ma. Yanzu dai bari in yi wanka maza maza suna jira in kai musu abinci" Miƙewa yayi hannunshi riƙe da nawa. "Ko zaki cuɗamun bayanane Shalelena?" Farfari nayi da idanu nace. Zan cuɗa maka bari in ɗakko ɗan mabuɗin sai muje. Asibitinma tare zamu je" Hannunshi na saki na nufi ciki na ɗakko mayafina, takalmi, da jakata sai kin turaka da kin ɓarayina. A jere muka fita shi ya kulle mun ɓarayin nawa muka fito muka ratsa asalin babban falo muka haye sama tin tin tin har zuwa turakarshi. Banɗakin na shiga komai tsab dashi gwanin sha'awa. Saita misha shawa nayi zafin daidai yadda za'a iya yafawa a jiki. Shigowa yayi daga shi sai tawul a ƙugu Kaina na sauke ƙasa shi kuma yayi murmushi tare da cire tawul ɗin. To a haka dai muka fito na taimaka mai na ciro mishi kayan sakawa na tayashi ya kintsa tsab sai tattaɓani yake yi yana jawoni idanunshi sun sauya kala sosai. Ni kuma sai noƙewa nake yi dan dana biye mishi da ya jani zuwa gado nice dai naƙi, da sauran lokaci nafi son in gama nazari tukunna. Tare muka sake sakkowa ya kwaɗama Hauwa kira sai gata da basket ɗin abinci ta tawo. Da fara'a ta gaisheni. Nasa hannu na karɓi basket ɗin muka tafi. A hanya yake ta yi mun hira. Adama kuma ta isheni da filashin har a wayar Rakiya aketa mun filashin. Wayar bata ruri na sakata a shiru. A jere muka taka tin tin har izuwa cikin ɗakin da Hajiya ke kwance Alhaji Zaidu na riƙe da basket ɗin abincin ni kuma ina riƙe da jakata muka tadda mata biyu a zaune a kujera. A tsanake na gaishesu tare da tambayar mai jikin. "Jiki da sauƙi Amarya har kin fito? Ai dama kin zauna abinki tunda Alhaji yana nan ga waje zo ki zauna. Alhaji Zaidu ka zauna kaima" Ah haba ai babu komai." Na nemi waje kusa da'ita na zauna. Shi kuma ya zauna a farar kujerar dake bakin gadon. "Hajiya Gado bata farka ba har yanzu allurar bata saketa ba? " Wacce tayi mun magana itace Hajiya Gadon. "Bata farka ba gaskiya. Ɗazu dai tayi sambatu gaskiya amman bata kuma ba dai" Itama a daddaƙilen take magana da wuya. Hmm wuya da kunne sun ɗauki wankan gwal Shiru yayi yana nazari can yace. "To me kuka tsinta a cikin maganganun nata, ko baku gane komai ba." "Hmm sunanka kaɗai muka ji gaskiya. Ko ke kin gane wani abun ummi? " Ta kusa da'ita ta taɓe baki tace. "A_a gaskiya." Tsam ya miƙe ya dubeni yace. "Ina zuwa zanga likita" Ya kama hanya ya fice. Haka na zauna. Ƴan uwanta sukaita shigowa anata kallona, ana yatsina, duk nabi na takura. Akwai aiki a gabana zanma Hajiya Balaraba magana a ɗinka mun kayayyaki ina cikin manyan mata sosai gaskiya. Duk da kayan dana saka nima babu raini tunda Super ce amman manya manyan kayayyakina ya kamata a ɗinkosu gaskiya. Naga wankan lace suke yi masu ɗan karen tsada da kyau, kai mai atampa sai kaga mai lace yafi kyau ko da atampar tafi lace ɗin kuwa tsada, dake shi lace yana mugun fito da mace sosai. Sai da su Maigogul suka zo na ɗanyi ajjiyar zuchiya. Mamakine ya kusan hallakani Uzairu zuchiyata da na gani riƙe da jakar Hajiya Balaraba harda kin mota yana kaɗawa. Man kainane naji yana tsiyayewa hiye. "Ya mai jikin bayin Allah. Ai nine mahaifin ita Sabuwa Amarya. Wannan wanta ne, wannan kuma iyalinace shine muka ce bari muzo mu dubata da jikin mutuniyar kirki" Ganin Hajiya Balarabane na tabbatar yasa suka saki fuskarsu sukaita fara'a Dan habaice _habaice suke tayi da labaran ƙanzon kurege da sukaita bayarwa a junansu da nufin hannunka mai sanda basusan a fice nake ba na sha da saninsu wallahi. "Hajiya Balaraba. Dama ashe kina da aure duniya bata sani ba? " Murmushi tayi ta nuna maigogul cikin alfahari tace. "Wallahi kinganshi nan Honey. Auren sirrine kinsan ba komai bane zaka yi shi a bayyane musamman mu ƴan siyasa. Kuma rayuwata daban da siyasata. Yanzu haka ma wani gidan rediyone ya gaiyaceni daga nan can zamu wuce" Yanzune na gane dalilin Hajiya Balaraba da yasa ta Auri maigogul. Macece wayayya sananniya. Dole zata so miji kyakkyawa wayayye ɗan kwalisa na fita taro mijin nuna ma Sa'a wanda babu raini zaka iya zagaye duniya dashi. Dan wallahi in kuka ga aikin gaban rigar maigogul zaku ɗauka wani sarautace a hannunshi. Hatta takalminshi mai kwale_kwalene fa irinna gidan sarauta. Na rasa a ina Maigogul kuma ya samo wannan shigar ta sarauta daga dai Auren Hajiya Balaraba shikenan ya canja. Ni dai sai Uzairu zuchiyata kawai nake kallo. Maigogul ne ya ciro kuɗi ya ajjiye musu Wallahi ko kaffara bazan yi ba bashi ya bada kuɗin ba Hajiya ce dai ta bashi ya ajjiye dan kankaruwar mutuncinta. Nan suka musu sallama na miƙe na rakasu. Maigogul yayi gaba yana amsa wayar Cicib Hajiya kuma tana ta gaisawa da mutane dake sananniyace. Wai Uzairu zuxhiyata dama da gaske kake yi wai nan zaka dawo ne? " "Ras lallai lolo baki da hankali. Dama ni nananne fa tabb in kin ganni a Dutse to na raka Dad ganin su Mum ne. Na gwammaci inyi zaman agolanci Ke kinga ɗakina kuwa hmm, gashi Hajiya Mum bata da matsala sam Yanzu ma daga nan gidansu Sagagi zani mu shiga gari da gayu. Rakiya sai wani kirana suke yi ni bana ma ɗauka kinsan halinta da baƙin kishi. Kayana nasa Adama ta tattaramun tsab jibi Dad zai shiga Dutse zai kaima su Rakiya Mum ta gansu sai in bisu in ɗebo kayana" Yama tunamun babu shiri na ɗaga wayata na kira lambar Adama. Rakiyace ta ɗauka. "Kema kin dena ɗaga waya kamar ubanki da Uzairu zuchiyata ko Lolo aita kira ba zaki ɗaga ba sabida munafucci. To wallahi ga saƙo kiyi gaggawar faɗama Maigogul ko ya dawo mun da ɗana ko kuma sama da ƙasa ta haɗe zanzo har Kano ayi wacce za'ayi" Ina jiyo Hauwa na sake zugata. "Baƙa baƙar munafuka mai kutunguilar tsiya ko ina ruwanki dani oho" Take faɗama Hauwa inaji faɗa ya kaure tsakaninsu A sanyaye na kashe wayata. Ai a kunnenka akayi komai sai ka koma gida kafin Rakiya tazo ta zubar da galangalan" Dariya yayi kawai. Lokacin mun ƙaraso wajen motar. Sai lokacin naga saƙon Alhaji Zaidu cewar ya fita sai zuwa yamma zai dawo ya ɗaukeni mu koma gida. Ya tafi Rano Goggo Amfana babu lafiya itama. Saƙon soyayya mai zafi da sauke nutsuwa na tura mishi nima. A nan mukai sallama dasu Maigogul Uzairu zuchiyata shi ke tuƙasu su suna baya abinsu Maigogul sai dariya. Ita kuma sai inga bata gajiya da kallonshi Allah mai iko Mrs BUKHARI [ Mrs Bukhari

Son so masoyana Sunayenku ba zasu lissafu bane wallahi shi yasa banma soma rubutawa ba. Amman ina sane daku masu dogon sharhi nagode sosai Allah ya bar ƙauna [10/6, 9:19 AM] BADA'AT IBRAHIM: MRS BUKHARI 20

INA MIƘA TA'AZIYYATA GA IYALAN HAUWA LAWAN MAITURARE. UBANGIJI ALLAH YA BAKU HAƘURIN RASHINTA HAƘIƘA DUNIYAR MARUBUTA DA MAKARANTA MUNYI RASHI BABBA. ALLAH YA KAI HASKE KABARINKI😭😭😭😭😭😭

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull