Idan kaya ya gaji book book 4 - Chapter 22
Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 22: Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 22. wai ni kamar ni Maigogul kishiyarki ta zaunar dan ta bamu abinci take…
4,138 words
wai ni kamar ni Maigogul kishiyarki ta zaunar dan ta bamu abinci take neman dukan cikina. Kinji yadda take jero maganganu kamar wacce take karantawa a rubuce kuwa? Lolo nayi mamaki gaya. Tsam nayi inata nazari bata da gaskiya wallahi nina faɗa miki wannan maganar. Amman zan ɗauraki akan kirsa da kisisina da maɗe, da duk abinda kika sani na janye hankalin namiji. Kema ki haɗa da wanda kika sani. Babu cuta ba cutarwa Kin zauna da kishiyoyi fin tara ko goma ma kada ki sake kiji tsoro. Jibi a sanadin wannan auren yadda na zama Lolo har mace na samu ta aureni inci ƙwai, inci kaza, inci talo _talo in kwanta a ac ke ko wuta aka ɗauke za'ayi maza a kunna jen sai mu kwana cur dashi, ga ɗa ta riƙemun babu nuna ƙyama. Lolo ki buɗe kunnuwanki da kyau ki saka idanu sosai akan Hajiya, ki nutsu ki gama karanceta fes, duk abinda zata yi miki kada ma ki nuna kin gane balle ki ɓata ranki ko wani abun. Shi yaƙi ɗan zamba ne, da salon da take neman halakaki, dashi zaki yi amfani kema. Ki fita kirki da kyauta, ki nuna ma mijin ai ke kinfi sonta sama da yadda take sonki. Da kanta zata zame jikinta asalin kalarta ta bayyana ta bada kanta. Kada ki sake ta gane logonki domin ko mutuwa zaki yi ba zaki gane nata logon ba. Daidai da rana ɗaya kada ki sake ki kai ƙararta wajen miji. Kada ki sake dangin miji duk shaƙuwarki dasu su ɗebo magana su yi miki akanta ki tofa. Mijinki kuma zagewa zaki yi ki nuna duk duniya babu yashi a wajenki ki girmamashi fiye da yadda take mai. Ki fita iya kwalliya ko da zata fiki da kaya masu tsada da gwala_gwalai kema da sannu zaki tara naki kayan adon, dan naga gwala_gwalai sawar alfahari take musu. Ki fita iya rangwaɗa da sauke ido da sauke murya Ke ki mata fintinkau a ko ta ina, kuma ko da marinki zata yi kada kiyi faɗa da'ita nuna mata jikinki bashi da wannan ƙwarin na faɗa, da haka zata iya zagewa ta dakeki kinga ai asirinta ya tonu ko, dan dole aji ba'asi. Shi kanshi mijin ki dinga narkewa kina yin abu kamar baki da ƙashi, ki ƙirƙiri yanayin da zai zama naki ne ya riƙeshi har abada dashi zai dinga ganinki. Kamar misalin shagwaɓa Sanyin murya Saiɓi yayin wani abun Yawan son jiki Da shagwaɓar nuna kanki na ciwo, ko zazzaɓi kike ji dan Auna girman matsayinki a wajenshi da gwada yadda ya ɗauki lafiyarki da mahimmanci. Wataranma ki barshi har asibiti kuje su basa rasa cewa ga abinda ke damun mutum, ko na maleria su baki ki watsa. In zai fita ki haɗashi da abinda zai riƙeshi har yaje ya dawo da tunaninki. Lolo zan dinga zuwa akai a kai domin tabbatar da komai na tafiya daidai. Sannan ki dinga yin sallar dare. Hajiya Balaraba tace sirrin nasararta kenan kullum saita tasheni nima munyi tare kema ki riƙa yi ki dage kinga wannan Auren? Sai mutuwa in sha Allah. Kiyi iyakacin yinki wajen kafa kanki. Kada kiga muna faɗa da Rakiya ta cukumeni muyi dambe. Wallahi Lolo tasani sarai tana da matsayi na musamman ne a wajena. Wallahi Rakiya a zuchiyata bata da tamka. Tsiyarta ke haɗani da'ita kawai. Yanzu nan haka taita aiko mun da ruwan zagi da ashariya ni dai sai kashe wayata nayi. Kinsan da yau zamu tafi Dutse wallahi wani abunne ya taso ma ita Hajiya amman gobe tare dasu Labbai zamu tafi" Maigogul a wannan ranar saida ya buɗe mun kaina ya wanke mun tas na zama sabuwa fil har wani ajjiyar zuchiya na sauke wallahi tsabar farin ciki. Maigogul nagode sosai kuma naji daɗi. Amman ai inaga gara mu dinga yin waya ba sai kazo ba" "Nanne kuma baki ɗaya isaba" Ya hauni da tijara. Ba wai sabida komai bane sabida ita Hajiyarne tunda mu bamu san manufarta a kanmu ba. Kada yawan zuwanka ya haifar da matsala, sannan ko bai haifar da matsala ba zai zubar mun da mutunci. Gashi kaga na shiga babban falimi kada dangin mijina su dinga zargin ko kana zuwane dan wani abun su fassaraka ai bazanji daɗi ba. Ni nayi maka alƙawarin duk abinda Alhaji ya yanke mun na albashi zan dinga baka rabi duk wata amman su Rakiya zaka dinga yima cefane, in kuma suka ce baka yi. Kayi nayi zan koma turama, duk da itama na ware kuɗin da zan dinga bata duk wata tana hidimarta dashi wannan yawon kayi nayi nake so ta watsar ta zauna waje guda taci abinda take so" Shiru yayi can yace. "Amman zaki mishi magana ya bani jari mai tsoka? Shagon saida yadinan maza da shaddajo, da takalman maza nake da sha'awar buɗewa wallahi Lolo in dinga fita ina zamana Kano garine na kasuwanci sosai, Hajiya Balaraba ma mun tattauna harma ta ƙaramun ilimin za'a dinga ɗinka wasu kayan ya zamana akwai ɗinkakku da marasa ɗinkin. Itama zata bada gudunmawa mai tsoka, shima ki mishi magana ya taimaka duk a gagganɗa. Ita kayi nayin har nawa haka zaki dinga bata a watan to? " Murmushi nayi nace. Zan maka duk abinda kake so ko da kuwa zan siyar da gold ɗinane in danƙa maka kuɗin. Amman Maigogul da sharaɗin shagon zaka yi. Amman kasan kan harkar ne? " Dariya yayi yace. "Sabuwa kenan. Ai wannan ɗin tsohuwar sana'atane nayi yaron shago, kuma nasan harkar sosai a lokacin ogan ya buɗa mun harkar sabida ya yadda dani sosai bana cutarshi barni da son kuɗi amman bana ɗaukan na kowa. To shima fa ina zaman zamana yaran shagon sukaimun sharri wallahi inaji ina gani aka koreni a baƙar leda kayana suke haka ya jefomun su kala uku bana mancewa" Tausayi ya bani sosai nace. Amman Maigogul ba zaka nuna mana dangin Mahaifinka ba, ko da bakasan dangin mahaifiyarka ba, tunda kace tare da iyayenta suka fito cireni, kuma dukka Allah yayi musu rasuwa. To tunda dangin mahaifinka sunanan mu nemesu mana" "Hmmm yaro yarone akace ko da ɗan giwane. Lolo ai waɗannan mutanen barsu kawai. Kinsan Allah dani da Isuhu so sukai su kashemu ma sabida dukiya kawai. Lolo munsha azaba bata wasa ba, mahaifinmu yana da dukiya da tarin raƙuma da cilallai na gwal duk suka handame kuma suka sa muka bi duniya. Ni dasu har gaba da abada in sha Allah. Nace baki faɗa mun nawa zaki dinga ba kayi nayin ba, nima baki faɗa mun nawa zaki dinga bani ba Lolona" Muryar Labbai ne ya katse mana hirarmu. Amarya labbai ta sha lace tayi kyau abunta. "Ahh kuna ciki Maigogul kaine ka sake fari haka?" Tana dariyarnan tata. "To kinga yadda na koma duk na sake haske. Cicib ɗin na falo? " "E yana can suna gaisawa da Hajiya" Da gudu Maigogul ya kwasa ya fice. Tafawa muka yi da Labbai. "Sun haɗu zasu tusa mijinki a gaba kuwa su zubar da galan_galan a gabanshi kuwa. Lolo manya kin samu duniya fa sai sheƙin Amarci kike yi" Dariya nayi nace. Nice nake sheƙi ko kece kike sheƙi ku gashi har kun tawo honimod ɗinku ni gani a nan harfa Abuja kuka je biki" Dariya ta tuntsure dashi harda tsugunnawa. Menene ya baki kuma dariya? " "Wayyo Allah cikina" Ta sake kwashewa da dariya kafin tace. "Ke kinga Maman Shafa da Cicib yace mata zamu je Kano. Wallahi tuburewa tayi wai ita bata yadda ba, ita tunda nazo na janye mata miji. Dama zuwana matarnan ta sai siket na gwanjo in yamma tayi sai ta saka wallahi harda janbakinta majigi fa" Dariyace ta kuma cin ƙarfin Labbai wannan karon nima dole na dara wallahi. Duk da hankalina yana kan Alhaji dake falo duk da Hajiya na tsakaninsu dole wani abun ba zasu yi ba. Duk da in Maigogul da Cicib suka haɗu babu damane. Muna ta hira dai da dariya. Taso muje in gaisa da Cicib. " "Munafuka kiga mijinki dai zaki ce. Muje to, su Rakiya da Hauwa ma sunzo ganin waje ai. Da zagi in zaga da Rakiya suka rabu. Ke har riƙe Maman Shafa akeyi wai zata daki Rakiya fa. Wai ke kinga dirama kuwa" Muna dariya muka fito kafin mu shiga falo na saisaita kaina. Idanu muka haɗa da Alhaji Zaidu yana zaune a kusa da Cicib anata hira su Cicib shaddace dai ya saka amman babu hula gashi kanshi da suma sosai a cunkushe yayi na wata mace dan zaiyi kitso fes gashi baƙi kullum cikin yin dai yake. Ba kamar Maigogul da yake ado da furfurarshi ba. Idanu Alhaji Zaidu ya lumshe yana mun kyakkyawan murmushi. Gaisawa muka yi da Cicib wallahi kamar zai tsugunna mun sai kirana Hajiya yake yi sabida kwaɗayi. Gaishe da Alhaji Zaidu nayi da wata murya ta musamman harda ɗan tsugunnawa ta gefen ƙafarshi. Maigogul ya jijjiga kanshi yana mun murmushin hakan yayi. "Barka dai. Anty Labbai tazo shine na jiki shiru ko? " Murmushi nayi wanda wallahi babu mahalukin dana taɓa yima shi a rayuwa. Ajjiyar zuchiya ƙarama ya sauke. Kaci abinci ka ƙoshi ina fata ko? " Kai ya ɗaga mun sabida kamar bazai iya magana bane. Hajiya ce ta kira wayarshi, su Maigogul kuma suna ta hira dasu Hajiya har da Labbai Uzairu Zuchiyata kuwa baya nan. Wayar na zare a hannunshi na matsa gefe na ɗauka. "Yallaɓai har yanzu baku tawo ba? " Nice Hajiya. Wallahi kinga bamu tawo ba sai munyi sallah tukunna zamu tawo dake gida muka je Yayata ce tazo da mijinta. Amma dama yanzu nake shirin kiranki inji yanayin jikin naki, in kuma baki haƙuri akan wallahi ni na riƙeshi laifinane ai mun afuwa uwargida ran gida" Sai ta yi dariya har a muryarta cike da fara'a babu ko ɗigon damuwa. "Ahh Amarya kece ashe ai babu komai ni kaina na kira wayarki ma kafin in kirashi ɗagawane baki yi ba shi yasa na kirashi ma. Jikin da sauƙi duk da a kwance nake wallahi komai ciwo yake yi mun. Da ƙawata Hajiya Mansa tazo ne ma na ƙwarara jikin nawa" Murmushi nayi mata nace da'ita. Ayya Allah ya baki Lafiya Hajiya sai mun dawo" "To Amarya mai maganar sikari sai kun dawo Ubangiji Allah ya tsare muku hanya ku dawo cikin aminci" Datse wayar tayi, nayi murmushi kawai ina ɗan nazari dai haka. Dawowa falon nayi a lokacin Labbai da Cicib suna cin abinci Maigogul kuma yana jan Alhajina da hira, tunda dai na zauna Alhaji ya raba hankalinshi biyu. Hajiya Uzairu zuchiyata fita yayi ne? " Na tambaya ina fara'a. "Uzzi ya fita ƙila ko gidan abokinshi Sagagi. Da mota dai ya fita" Illahirin mamaki, lallai Uzairu zuchiyata ko kuma ince Uzzi ya cika tataccen baduniye. Ina ganin Labbai na dariya. Haka muka wuni a gidannan sai da mukai magriba muka ci abincin Maigogul kana mukai musu sallama Labbai tace gobe da safe zata shigo mun, nima nace dama akwai maganar da nake son mu tattauna da'ita mai mahimmanci sosai, sannan akwai saƙon Rakiya Muna cikin mota hannunmu sarƙe dana juna, yana tuƙi yana kallona jifa_jifa muna sakarma juna murmushin. Masta dan Allah mai Hajiya tafi sha'awar ci ko sha haka musamman in bata jin daɗi? " Ɗan juyowa yayi ya kalleni tare da mayar da hankalinshi titi. "Tafi son gashasshiyar hanta, ko yahuza suya, da nono mai sanyi" Yauwa masta to ka kaini Yahuzan mu sai mata kaza da nono sai in kai mata" Murmushi yayi yace. "Baki bani labarin me kuka tattauna da'ita bama data kiraki ba. Da muka fito masallaci na kira wayarta bata ɗaga ba ƙila tana sallah ne lokacin." Gulmarka muka dinga yi take faɗa mun kana son mu'amalar aure sosai wai saina dage" Kallona yayi muka tuntsire da dariyar soyayya da nishaɗi. "Wazirat al sa'ada kenan. Zaki sani inna kamaki ai. Ina sonki sosai na kuma ji daɗi da kika zaɓi aiki dani sabida a ko da yaushe inna buɗe idanuna zan ganki, kona gaji zaki ƙwararani" Wannan gaskiya ne masta, ai ita mace haka akeso ta kasance cikin al'amuran mijinta tayi kane_kane. Sannan aiki a ƙarƙashinka ai abune da zai taimaka mana ni dakai duka. Zan zama jaruma wajen ganin na taimakeka sosai zan zame maka garkuwa" "Da fatan jarumtarki ta ɗaki ba zata ragu ba sabida yawan aiki ba ko? Kinsan wannan jarumtar ni nafi buƙata ko? Sai nake ji a jikina tamkar kece uwar Ƴaƴana. Na Auri mata dayawa banji haka a kansu ba sai a kanki." Hannunshi na matsa. Wallahi sai yaci burki da ƙarfi, babu shiri ya sulale gefen titi. "Wazirat al sa'ada zaki samu mu yi haɗari ai" Kaina na karyar zuwa gefe guda cikin shagwaɓa nace. Tuba to nake yi" Na dawo kamar Mardiyya fa. Babu shiri ya matso da fuskarshi izuwa tawa muna shaƙar numfashin juna. "Wai kinsan menene Wazirat al sa'ada? " Saika faɗa masta" "Da ace kin ƙi aurena dana faɗa miki bana haihuwa bansan yaya zanyi ba Allah. Ganin farko dana miki a Airport kika kwanta mun" Bakinshi na kama na aikashi garin manya. Mantawa ma mukayi a titi muke ma sam a hankali na jingina da jikin kujera ina murmushi. Ina fatan Allah yasa Babynka yana kwance a cikina" "Allah ya amsa zamu je makka muyi ɗawafi mu roƙi Allah. Nasan da kika je kin roƙa mana, nima na roƙa mana, amman zamu sake zuwa in sha Allah in aiyuka sukai mana sauƙi" Da haka muka je Yahuza mukai siyayya kana muka dawo gida. Ni kaɗai na shigo Alhaji Zaidu ya wuce masallaci. A babban falon gidan na tadda Hajiya ita da Hauwa ga ɗinkuna an kawo mata tana duddubawa lasa_lasai kwantattu na alfarma. "Kun dawo kenan? " Tayi maganar tana ƙaremun kallo ga fara'a tana ta zubawa. Nima da fara'ar na ƙarasa na zauna. Wallahi kinga mun dawo. Ga tsaraba ma nasa Alhaji ya siyo miki" "Kinsa Alhaji ya siyo mun? To madallah nagode sosai. Yasu Hajiya Balaraba Alhaji Baba dai shi yazo" Ledar kazarta na miƙa mata nace. Tace a gaisheki. Alhaji Baba kuma ya faɗa mun kin tarbesu da kyau nagode sosai " Dariya tayi tana son magana sai wayarta ta shiga ruri. "Hajara anata hidimar suna ko gobe gashi ni inata fama da jiki, ban sani ba ko king zai kawo Amarya tazo sunan tunda ba budurwa bace bare ace sai ta jima a gida ba, yanzu ma suka dawo taje gida" Kallonta kawai nayi inaji kamar in dira a wuyanta wallahi. Da dariya da wasa tana yaɓo mun magana. Ina zaune ta gama wayarta. "Kinga sunane a Rano ko zaki iya zuwa ni naje wanda za'ayi nan da kwana uku? " Zani aini ba budurwa bace bare ince sai nayi wata. Allah ya nuna mana goben lafiya in maigidan ya amince sai inje nima ayi dani. Bari in shiga ciki in watsa ruwa" Na ɗauki lodojina nayi wucewata ɓarayina ina mamaki. Wanka na soma yi kafin nayi sallah. Riga da wando na saka amman rigar babbace, hakama wandon irin burguza burguzannanne masu ruwan jinin kare a Saudiyya na siyosu, ban saka hula ko ɗankwali a kaina ba sai kulaccham na gashi da nabi na shafe layi layin kitsona ƙanana dashi. Na cakuɗe da ƙamshin ingantattun kaya na wannan baiwar Allah Mrs BUKHARI. Tun safe da na saka turaren wuta wallahi in kika shigo ɓarayina zaki ɗauka yanzu ake ƙona turaren tsabar ƙamshinshi. Kicin na shiga na dafo shayi na cika flas. Na juye kazarmu a kwanon tangaran mai murfi na jera komai na fito. Hajiya tana falon ta kafa ta tsare sai waye_waye take yi, ga wasu mata a gabanta su biyu. Sannu nayi mata matan kuma muka gaisa nayi haurawata sama. Kafin in ƙarasa sama na jiyo sallamar Alhaji. Hakan yasa ina ajjiyewa burner kawai na jona turaren jiya na bari a jiki wanda na ƙona na sakko cike da yanga ina yarfe hannu. Gurum Hajiya taga Alhaji ya dena ba da amsa ya ƙurama ƙafar bene idanu, juyowa tayi daidai na kashe mishi ido ta gani. Ashe ka shigo kenan masta, to ina zuwa kaji? " "To shikenan sai kinzo kada ki jima" Juyawa nayi nayi imanin dashi da'ita duk ni suke kallo shi yasa na shiga jijjiga jikina ni za'a nuna ma bariki kuwa? Ɗan mayafin na ɗakko na rufe kaina na kulle ɓarayina na koma na zauna a kujerar da Hajiya take zaune mu duka muna fuskantarshi. "Ga ƴar aiki na sake miki tunda gobe zaki kama zuwa aiki ko? Yana da kyau dole fa kiyi ƴar aiki bafa zaki iya zuwa office ki dawo ki kula da miji ba. King ka faɗa mata gaskiya dai kaima da kake namiji yaya kake dawowa, sannan wataran sai ka kai sha ɗayan dare ma a office ana meetin da cike ciken takaddun lissafin kuɗi" Illahirin mamaki. Tabbas akwai abinda take nufi da masu aiki. Bata san naci dubu sai ceto bane bata san da wuta take wasa ba. In banda na tuba da nayi muku maganin matarnan. Amman zan yi maganinta da kissa wacce akace tafi asiri tasiri a wajen maza, tunda na lura maza su tamkar basu da wayo kan abinda suke so wani sa'in idanunsu a rufe yake. "To Hajiya ni tunda tace bata so ai bazan tursasa mata ba. Aiki kuma da kanta in taji wuyarshi da kanta zata nemi ƴar aikin ko Shalele? " Hakane Masta balle ni bana daga cikin matan da suke sallama ragamar aikin gidansu zuwa hannun ƴan aiki. Ni nafi sha'awar in yi komaina da kaina. Hajiya nagode sosai da kulawa, aikin guda nawane ɗan girkin abinda zanci, da ɗan wanke wanken tsirarin kwanuka ai bazai gagareni ba" Shiru tayi tana ta nazari sai can tace. "Shikenan Laure kuje wajen Hauwa ku kwana zuwa gobe da safe zan baku kuɗin mota" Godiya sukai mata suka fice. Hajiya ta miƙe. "Ni zan shiga ciki saida safenku ko King zazzaɓine sosai a jikina" Nan da nan ta narke ta shagwargwaɓe. Masta ka rakata ka tabbatar ta sha maganinta tayi bacci tukunna. Ina sama, Hajiya Ubangiji Allah ya baki lafiya sannu. " Ni dai harta ƙule ina mata sannu. Nayi hawana sama, ai kuwa turaren dana barshi a bona ya cika falon tab, kuma fa jiya shi na ƙona yauma haka gashi babu ko ɗigon ƙwauri kai madallah dake Mrs Bukhari gidan ƙamshi. Minti talatin saiga Alhaji ya shigo da sallama ina zaune a falo na kunna TV ina kallon wani Hausa film na Ali nuhu da Rahama hassan da nafisa Abdullahi. Zama yayi a kusa dani ya ɗaura kanshi bisa kafaɗata. "Wazirat al sa'ada inaga gobe dole in mayar da Hajiya asibiti. Gaskiya Jidda ma zan kaita kawai taje taga likitanta wanda Allah cikin ikonshi a hannunshi ta warke." Wayarshi ya ɗakko ya danna kiran wani waishi Jafar. "Jafar Jiddah nake so zuwa nan da jibi, Hajiyace ba lafiya" Jafar yace. "Zaka samu Alhaji in sha Allah" "To shikenan Jafar kayi abinda duk daya dace" Ajjiye wayar yayi na laɓe a ƙirjinshi ina jin ƙirjina na suya nace dashi. Amman dare dani za'aje ko Masta? Bazan iya zama ku kuna asibiti a wata ƙasar ba bazan iyaba wallahi. Kuma ya kamata ni zanyi jinyar Hajiya ai ba kaiba." Fuskata ya shafa yana murmushi yace. "Yadda kika tsara hakance zata faru kamar da ƙasa wazirat. Ai nima bazan so in tafi in barki ke kaɗai ba kaɗaicin zai miki yawa. Sai ki shirya daga nan sai muyi honimod ɗinmu uhm? " Dariya nayi na rungumeshi tsam na ɗago muna kallon juna, na gigitashi da salo na birkitashi, daga ƙarshe a kunne na raɗa mishi. Na barma Hajiya kwanana naci girma. Hajiya tana buƙatarka tana son jin ɗumin mijinta a kusa da'ita." Da sauri ya ɗago zaiyi magana na ɗaura yatsana a bakinshi dole yayi shiru. Sakeshi nayi na soma bashi abinci a baki ina yi mishi hira mai daɗi har ya ƙoshi. Jawoni yayi nima ya dinga bani namannan, na ƙoshi amman dan kada in gwasaleshi haka naita karɓa. Muna gamawa na miƙe na soma haɗa kwanukana. Na shiga ciki kenan ina haɗe zanin gadona da tarkacena. Sai ga Hauwa ta kirawo Alhaji da sauri wai kunji numfashin Hajiya sama_ sama yake fita. Wallahi na riga na ayyana hakan zai farune ganin yadda akayi sallamar, shi yasa tun kafin ace ni na sallama kwanana. Bawan Allah da gudu ya sauka yana harhaɗe bene. Ni kuma saida na kwashe komaina na mayar ɓarayina kana na nufi ɗakin Hajiya. "Amm Amarya nace shiga zaki yi ne ciki? " Tsohuwar kimuna kenan. Da fara'a nace. E zan duba yanayin jikin nata ne" "Ai dake ba'a shigar mata ɗaki ko zaki yi haƙuri zuwa da safe inta fito? " Bance mata komai ba na tura ƙofar da sallama na shiga. Hajiya rabin jikinta na kan cinyar Alhaji yana shafar bayanta. Ɗagowa tayi muka haɗa idanu ta mayar da kanta kawai. Sannu Hajiya jikinne ashe ya kuma motsawa Ubangiji Allah ya bada lafiya. Masta ka kwana anan basai Hajiya ta hau sama ba ba lallai ta iyaba sabida yanayin jikin naga babu daɗi. Nan da kwana biyu inta warware komai ya dawo daidai, ni kam na yafe ta nifi muƙatarka. Hajiya akwai abinda kike so a kawo mikine? " Kai kawai ta girgiza har hawaye idanta ke fitarwa. "Wazirat ki buɗe durowarcan ki ɗakko mata rigar baccinta dan Allah" Ya faɗa muryarshi da sanyi sosai har a yanayinshi ya nuna baiji daɗi cewa ya zauna har kwana biyu a wajen Hajiya ba. Ni ko ko'a jikina. Durowar daya nuna mun na buɗe rigunan baccine a rataye a hanga sunyi hamsin inma basu fi ba, suna ta ƙamshin turaren kabbasa amman ko kusa wallahi basu kama ƙafar kayan Mrs BUKHARI gidan ƙamshi ba. Ajjiyar zuchiya na sauke na zaro doguwar rigar bacci mai gajeren hannu na miƙa mishi. Bata ankaraba nasa hannu na zame mata gwal ɗin kunnenta dana wuyanta, zobunan duk nabi na ciccire mata. Ina akwatin sarƙoƙinta suke? " Ita da take nuna magana ma na mata nauyi sai cewa tayi. "Ki ajjiye a gaban miro kawai nagode" To shikenan Hajiya" Na zube mata a gaban miro na musu saida safe na fice. Ina shiga ciki na wanke bakina na saka rigar bacci na hau gado. Saƙon soyayya da nuna tsantsan kewa, da kuma kwatanta mishi juriyata na tura mishi na ajjiye wayar na saki ac na shige bargo. Hajiya duk yadda akayi bata sakeshi ba sai da asuba yazo zai tasheni, ya sameni ina yin sallah. "Masha Allah" Ya furta ya fita. Ina idar da sallah na shiga Kitchen duba farfesun dana ɗaura tun huɗun asuba na naman kai. Ai kuwa naje na sameshi kaɗan ya rage ya nuna, ruwa na ƙara na ɗaura ruwan shayi a butar shayi na wuta, saina shiga firar dankalin turawa. Saida na zuba a mai kafin na shiga nayo wankana fes na saka riga da siket na kanti, babu ko ɗankwali a kaina sai mayafi na yafa na shafe jikina da humra Mahalab, Ɗan kunne da sarƙar da Goggo Amfana ta bani ita na saka. Na jera musu kayan kari tas a tire nakai har falon Hajiya na ajjiye, na leƙa kicin na faɗa ma Hauwa ga abincin Hajiya can a falonta na ajjiye mata. "Shikenan kin hutasheni dama yanzu zan ɗaura" Ni dai murmushi kawai nayi mata na shige ɓarayina na kunna gawayi na turare ko'ina. Ina kan zagaye falon ƙasa da turarenne Adama ta kirani muka gaisa. "Lolo ni dai kwana nayi lissafi da tubka da warwara. Tunanin dana tsayar shine ki siyamun injin niƙa na ruwa, ko kuma in dinga shiga Kano ina saro ɗankunne, kayan kwalliya, da ƴan turarukan fesawa haka masu arhar kuɗi. To kindai ji abinda na tsayar Lolo sai ki duba kiga abinda zaki iya" Murna nayi sosai da tunanin Adama. Adama naji daɗi, kuma nafi tunanin ki dinga zuwa Kano kina sare_saren zaifi in abun yayi ƙarfi saimu buɗe shago, ko kuma ki dinga yin buhu buhun kaya. Yanzu dai gobe zamu tafi Jidda kafin in tafi zan ajjiye miki dubu ɗari a wajen Hajiya Balaraba sai ki shigo Kano kiyi sare_sarenki sai dai matsala ɗaya wa zai rakaki kasuwar ki yawata ki kukkurɗa?" "Lolo har dubu ɗari? Gaskiya nagode da wannan taimakon da kikaimun nagode sosai. Babu komai jibi zan shigo Jigawa gata sai in shiga Kano, inma bansamu wanda zaimun ido ba Lolo zan shiga a hakan a hankali zanyi idon" A gurguje mukai sallama ta tafi sallamar yara da ɗumamen safe. Allah sarki ƴan uwana Allah ya dubeku ya taɓa al'amuranku." Ina ajjiye kaskon Alhaji ya shigo hannunshi riƙe da carbi. Zuwa nayi muka rungume juna muna shaƙar ƙamshin juna. Yana ta kallon sarƙar dake wuyana Mrs BUKHARI ce Anan na kawo ƙarshen littafi na huɗu in sha Allah. Hutun kwana biyu zamu yi in sha Allah zan dawo muku da zafi muji ya zata kaya. Ku faɗi ra'ayoyinku dangane da zaman Lolo da Hajiya Son so💪🏼💪🏼💪🏼