Idan kaya ya gaji book book 4 - Chapter 21
Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 21: Idan kaya ya gaji book book 4 Chapter 21. Ni da kaina ka ɗaukeni ne ka sakani a wata iriyar rayuwa, wata iriyar…
3,557 words
Ni da kaina ka ɗaukeni ne ka sakani a wata iriyar rayuwa, wata iriyar duniya mai tsabta wacce babu hargowa da hauragiya. Ka shayar dani wata iriyar zumar da ban taɓa lasarta ba. Fatana Allah yasa zamanmu dakai ya ɗore a haka. Kuma ina roƙon Allah kada ya nuna mun ranar da zan ginsheka, sannan ina fatan Allah yasa kayi ajjiya a jikina masta" Murmushi yayi ya saka hannayenshi bibbiyu ya tallafo fuskata sosai ya matso dani muna musayar numfashi. "Ji Wazirat al sa'ada. Bazan taɓa dena jin ƙishin ruwanki ba balle har ki hau kaina. Baki san girman matsayinki da girman yadda kike a rayuwata bane. Uhm masta naji kince mun. Me yasa naci wannan suna?" Yayi maganar cikin sigar ƙauna. Dalilin da yasa naci wazirat al sa'ada. Duk da bansan fassararba sunan na musamman ne kamar yadda ya fito a wajen miji jarumi na musamman " Na ƙarashe ina rufe fuska yana sauke mun hannuna. "Na baki aiki kije ki tambayo fassarar sunan dana baki, gobe kizo mun dashi uhm sai in miki kyauta." Kofin shayin ya bani a baki. Na cika bakina na juye a bakinshi kamar zamu koma ruwa dai, dan al'amura sun kankama sosai da sosai sai na zulle na koma gado ya biyoni madadin mu kwanta saiya jingina da fuskar gadon ni kuma nayi ruf da ciki ina fuskantarshi kaina a cinyarshi yana shafar kaina yake cewa. "Babansu mardiyya yayi wauta sosai daya yadda ya rabu dake gaskiya" Da sauri na ɗago muka haɗa idanu ya jinjina mun kai tabbacin abinda ya faɗa daga zuchiyarshi yake. Me yasa kace haka? Kasan ita mace tamkar riga ce, wani da yaji rigar ta tsufa zai yar sabida ƙila yana da wadatar wasu" Bakina ya shafa yace. "Wani kuma in ya ɗauka a wajenshi wannan rigar bata da tamka. Nifa tsabar farin ciki uhm Wazirat al sa'ada ko baccin bana ji, banƙi inta kallonki ba har garin Allah ya waye. Sauƙina ma tare zamu yi aiki bani da wata fargaban barinki uhm? " Haka mukaita hirarmu, muna burgima a gado sai jin kiran sallar farko muka yi. A hankali ya zare jikinshi a nawa ya sakko lokacin jikina yayi nauyi harna ɗan soma bacci. wanka ya kuma yi ya wanke bakinshi tas ya fito. Cikin farar jallabiya ya fito fes dashi da wasu littattafai na addini a hannunshi. Gaban gadon yazo ya tsugunna yaimun sumba mai kyau a goshina. "Ki tashi kiyi wanka sai kiyi sallah. Ni zan tafi masallaci sai takwas nake shigowa. Inama magidanta karatu bayan ko wacce asuba in dai ina gari. Kema da mun gama amarcinmu zamu soma karatu. Nine malamin naki da izinin Allah abinda duk ya dace ki sani zan karantar dake wazirat al sa'ada. Saina dawo ki kwanta ki huta sosai kada ki wahalar da kanki Hauwa zata yi kayan kari damu zan faɗa mata" Yana shirin tashi nasa hannu na riƙe mishi hannu sai ya bani dukkan hankalinshi. "Menene uhm? " Ai tunda ka Aureni duk ranar da kake cikin fadata Hauwa tayi kaɗan ta ciyar dakai wallahi da girkinta mara kan gado. Haba Masta yanzu sai in barka kaci abincin mai aiki alhalin gani? Allah ya kiyaye" Ƙur ya zuba mun idanu yayi murmushi kawai ya miƙe a tsanake ya fice, nima cike da farin ciki nayi wanka nazo na gabatar da sallah Na jima ina godema Allah tare da roƙonshi ya kaɗe fitina a zaman alkhairi yaci gaba da wanzuwa. Ban fita a ɗakin ba saida na gama gyara komai tsab na banke ɗakin da turaren wutan turara turaka dana tawo dashi kaɗan dama sabida da safe in saka. Falo na dawo na shiga gyarawa babu datti ko ƙura amman dai haka nabi na kakkaɓe kujerun na goge abinda zan goge, na share na sharewa saina koma ɓarayina ina jiyo ɓuruntun Hauwa a kicin. Nima Kitchen ɗin na faɗa a gurguje farfesun kifi tarwaɗa da aka kawo jiya mai yawan gaske na ɗaura na tsayar da sanwa tare da saka duk ɗanɗanon daya dace da kayan ƙamshi. Saina ɗaura ruwan shayi mai citta da kanunfari a butar shayi, doya na gutsura na soya dayawa dan inaso in zuba ma Hajiya farfesun ma da'ita na ɗaura. Doguwar riga abaya na saka mai ruwan jinin kare. Zatina ya fito sosai, na lakato kulaccam na shafe kaina da'ita, na ɗakko humra ta matan sudan na wajen Mrs BUKHARI Anty Badiat kenan guda da ɓari na shafe illahirin jikina dashi. Na saka ɗankunne da sarƙa na gwal na fito na ɗauki abincin Hajiya zan kai mata na samu Hauwa a falo muka gaisa kana na wuce falon Hajiya. Tana zaune da rigar bacci tana waya. Bakinta ta ɗan saki data ganni. "Zan kiraka Jamilu Allah ya raya in jikina yayi ƙwari zan zo barka. Muma sunane damu har biyu a familin Alhaji" Ta ƙarƙare wayar tana mun murmushi harda miƙo mun hannu. Abincin na ajjiye a gabanta na miƙa mata hannu muka gaisa. "Lafiya lau. Kina ta aiki haka ya Amarya tana Amarci tana shiga kicin ai Alhaji da yace Hauwa tayi abinci daku ko? Kuma mai aikin ki ma anjima zata dawo gaskiya dole ne ki ɗauki mai aiki, bazai ma yiwu bane dan sai inyi fishi dake." Murmushi nayi to ita menene nata da dole sai mai aikin data kawo tayi mun aiki? Sannan in mai aikin nake so ai gara in tuntuɓi su masoyiya Maidoki nasan zasu bani mai aiki ta jeki ki dawo ina ni ina sakankancewa da kishiya? Ba kishiya ba ko ƙawa na sakankance mata wane mutum, zan mance akuyancin da Ƴar shuwa ta guikuya mun ne har abada. "Wannan gwal ɗin naki yayi kyau ɗan mitsitsi dashi kamar na yara amman kuma yayi miki kyau." Nagode sosai ni zan koma Hajiya" Nan na tafi na barta inaji tana kiran Hauwa. Magana wai ta faɗa mun dan ita tana saka ƙatuwar daham ni kuma na saka ƙarama shine take cewa kamar ta yara. Abincinmu na jera a falon sama ina zama Alhaji na haurowa da sallamarshi. Da hanzari na dosheshi da nufin karɓan littattafan. Sai ya haɗa dani da littattafan ya matse gam muka zube a kujera sakamakon wasa da yake yi da harshenshi a bakina. Zarewa yayi yana shinshinan wuyana. "Waɗannan turaruka ba dai sauke nutsuwa da saka farin ciki ba wazirat al sa'ada uhm kinyi kyau sosai. Amman baki wahalar da kanki ba wajen girki mai wahala ba ko? Da safe bana cin abinci mai nauyi" Kai dai tawo masta in baka a baki kaci ka ƙoshi gwarzona" Dariya yake yi harya zauna. "Wazirat wannan masta ɗin wai mastan menene uhm nifa ban gane ba? " Idanu na kashe mishi daidai shigowar Hajiya Hauwa na biye da'ita da kulolin abincin dana kai mata. Kuma tabbas taga abinda nayi Dure tiran tayi ta gaishe da Alhaji ta fita. Hajiya wai tazo ne muci abincin tare ƙila taci da yawa. Kunji fa, akwai gagarumin aiki a gabana wallahi. Haka muka ci abincin muna hirarmu da dariya. "Alhaji mai aikinnan fa ta dawo ka saka baki a ɗauketa Amarya dole tana buƙatar mai aiki" "A_a Hajiya gaki gata. Amman tunda tace bata so anya ba za'a haƙura ba? In kuma dan ta samu aiki kike yi shikenan ta dinga wanki a injin in yaso shi tasi'u an rage mishi guga kawai zai dinga yi ko? " Ya ƙarashe tare da shan shayi yana kallona cike da shauƙi. "Amman Alhaji ni aikin ɓangaren Amarya na ɗakkota a bata. Itama shi tafi so. Sannan ita Sabuwa kace zata soma aiki wa zai dinga mata aikace_aikace kuma ka duba mana" Ta haƙiƙance fa abun dariya abun mamaki wallahi, sai tababa akeyi da'ita. Sama da ƙasa Allah bai bani ikon cewa komai ba. "Hakane maganarki. Aiki kam gobe ma zamu soma fita a ƙarƙashina zata yi aiki a ƙarƙashin ofishina. Sai tari ya turniƙe Hajiya ta zuƙi shayi ba da kyau ba. Ta jima tana tari harda hawaye mukaita mata sannu. " A ofishinka zata yi aikin cikin maza? Ai ni na ɗauka shago za'a buɗe mata a danƙara mata kaya ta dinga fita, kamar dai yadda muka yi da sauran matanka na baya. Ni ina jiran ka bani kwangilar cika mata shago da kaya. Mastas gareta hala ko P H D? " Ta ƙarashe tana mun dariya. Nima dariyar nayi. "Ke ba kin ƙi yadda ki zama mataimakiyata ba, da abubbuwan zasu yi mun sauƙi sosai. Ita kuma bata saba da kasuwanci ba shi yasa ta zaɓi ta zauna a ƙarƙashina kawai. Sai ki koya mata mota ai Hajiya sabida zuwa ofis ko ranar da bananan, duk da dai tafiyar dole tare za'a dinga yi, sai kuma halin ciwo ko wani uzirin babba da zaisa in tafi ni kaɗai" "To Alhaji yadda kace haka za'ayi. Amarya Allah yasa a soma a sa'a. Zaki sha aiki in dai Alhaji ne babu wasa mitins ma kaɗai ai ya isheki. Kinga dole kina son mai aiki. Ni bazan iya wannan aikin cuɗanya da mazan ba gaskiya, kuma aikin da wuya ba zaki zaɓi shago a cika miki da kaya ba ko ɗan uwanki ya zauna miki a shagon ba kinga shima kin taimakeshi, in yazo sai mu dinga fita sarin kayan tare? " Nagode sosai Hajiya. Amman batun ƴar aikinnan zanyi tunani akai in sha Allah mu gani, duk da babu abinda zai canja ra'ayina akan ɗaukar mai aiki. Batun shago kuma gaskiya bana ko sha'awa na dai fi son in yi aiki da Masta zaifi mun." Haka dai muka gama karyawa na tattare komai na mayar ɓarayina na wanke komai na kife a kwando kana na koma sama. Har lokacin Hajiya na sama wallahi kwanciya ma tayi magashiyan ta shiga wash_wash ba lafiya. Magungunanta yaje ya ɗakko ya ɓalla mata ya bata tasha. Bata wuce minti ashirin ba tayi bacci ya lulluɓeta da bargo Ni kuma ya riƙo hannayena muka shige ciki tare da zubewa a kan gado, mukaita hirarmu cikin soyayya muna murgima da murƙushe juna, wajajen goma dai ya tashi ya shirya yace yana da meeting amman a gida zaiyi azahar. Ko da muka fito Hajiya ta ɗan farka, yace ta taso ya kaita ɗaki zai fita. Sai cewa tayi ba zata iya gangarawa ba sabida jiri ya barta zuwa anjima Hauwa zata taimaka mata. Har bakin motarshi na rakashi na shige gaban motar na narke mishi. Yanzu a cikin lokacin amarcin nawa za'aje mitin kuma kace fa har azahar." Shafan fuskata yayi yace. "To shikenan shiga ki shiryo muje tare ba dai shikenan bane uhm. Nima dole ce zata sa in fita in barki wazirat al sa'ada nafi sha'awar in kwanta lub a jikinki kinga jiya bamu samu bacci bama, ya kamata in muka dawo mu kwanta mu huta kafin dare" Babu damuwa jeka abunka sai ka dawo, kafin ka dawo na gama girkima. Ka kula mun da kanka na baka amana" Na rungumeshi nan ma na sukurkutashi wallahi ƙin yadda yayi ma in sauka a motar ja kawai yayi muka fice. Hannunshi ɗaya akan sitiyari ɗayan kuma mun sarƙe yatsun juna. "To ya zanyi dake wazirat dole in tafi dake in ba haka ba bazan iya mitin ɗin ba ma. " Haka muka tafi muna cike da wani irin farinciki da zumuɗin juna. A ofishinshi ya ajjiyeni amman ba kamfanin mota muka je ba, wani wajene dai ni bazan iya tantance ne menene ba. A ofishinshi nayi zamana shi kuma daya gama cikani da soyayya saiya tafi mitin ya barni. Labbai na kira dan muna hanya inata ganin flashin ɗinta. "Lolo Amarya kuna ta shan amarci ko to ya kuke ya Alhaji da Hajiya?" Murmushi nayi kamar tana gabana nace. Lafiya lau Labbai ya sabuwar rayuwa, ina Maman Shafa? " Saida ta gama dariyarta ta mugunta tace. "Da labari kin gammu ni da Baby muna hanya zamu shigo Kano. Amman fa gidan Amininshi zamu sauka" Ai sai dariya ta kamani nima na ɗana irin nasu nice harda riƙe cikina. Itama dariyarta take yi rai ɗaya wallahi. To Allah ya kawo ku lafiya kin ganni ma bana gida na rako Alhaji mitin zan roƙeshi daga nan mu biyo gidan dama wallahi nayi niyyar daga nan inje inga Maigogul da Uzairu zuchiyata" Da haka mukai sallama na kashe wayata kenan kiran Maigogul na shigowa. Da murmushi na ɗauka. "Lolona gamu a bakin ƙofar ɓarayinki kizo ki buɗe mana ƙofa muna ta bugawa bamu ji motsin kowa ba" Numfashi na ja nace. Bananan Maigogul mun fita da Alhaji. Dama kuma daga nan wajen wajenku zamu tawo. Maigogul nace maka kada kazo fa amman... " "Gidanku nace yau ga mutuniyar banza. Ke wallahi baki isa hanani zuwa in duba lafiyarki ba Lolo. Zamu dai koma tunda bakya nan. Lolo akwai kuɗi a bankin ki ki aramun dubu hamsin dan Allah? Zan dawo miki dashi" Akwai zan turo maka Maigogul dan Allah ku tafi kada ma matar gidan ta ganku" "Nan fa ɗaya lolo wannan mutuniyar arzikin? Ai kinganta ma ta sakko daga sama bari mu gaisa sai mu tafi sai kunzo" Inaji Hajiya tana cewa su shiga falo Hauwa ta basu abinci. Idanu na runtse dan nasan ƙarshenta taita dukan cikin Maigogul tunda dai naga kamar tana da ɗabi'ar son jin ƙwaƙwaf sosai. Uzairu zuchiyata na kira. Uzairu zuchiyata dan Allah ka kula kada Maigogul ya fasa mun taya. Ka ankare ka kyau" "To" Kawai yace mun ina jiyo Hajiya na tambayar Hajiya Balaraba. Murmushi kawai nayi nace Hajiya kenan Allah ya kyauta mata masu duniya. Ni dai fa hankalina bai kwanta ba saida Uzairu zuchiyata yayo mun tes yace sun bar gidan. Hajiya ta basu jallof da kaza ta ɗakko dubu arba'in ta basu su ƙara mai kana na sauke ajjiyar zuchiya. Banɗakin ofishin na shiga na ɗauro alwala na hau kan daddumar dake shinfiɗe tana kallon alƙibla nayi sallah. Ina kan sallayar Alhaji ya leƙo a gurguje. "Yauwa Wazirat al sa'ada bari nima inje masallaci sai mu tafi ko? " Kai na ɗaga mishi kawai. Ni dai inata tubkewa da warwarewa har ya dawo. Fitowa muka yi kai tsaye muka wuce gidan Hajiya Balaraba. Muna hanya ne na tambayeshi. Masta kunyi waya da Hajiya ta samu sakkowa daga sama kuwa, ya kuma jikin nata kunyi waya kuwa? " Murmushi yayi ya matsemun hannuna da yake ta murzawa tun tasowarmu. "Kina ji da Antinnan taki. Hajiya munyi waya jikin dai tace babu laifi Hajiya Mansa ƙawarta tazo shine ta ɗan warware" Kai na gyaɗa nace. Allah sarki wannan Hajiya Mansan tana ji da Hajiya sosai " "Ahh tsakaninsu sai dai a barsu aminiyarta ce sosai. Amintakar tasu ma muma saida ta shafemu tsabar yadda shi yake yawan kawota gida, da yadda nima nake yawan zuwa kaita ko ɗakkota. Kuma kasuwanci iri ɗaya suke yi. Wazirat al sa'ada Baban Rahine gobe zai zo fa, zai sauka a can gida sabida zamu je dashi kamfani in zazzagaya dashi ko'ina ko? " Allah ya nuna mana ameen hakan yayi nagode sosai Masta" "Masta ko? Zaki ga masta bari dare yayi zaki yi bayani da manyan baƙi uhm" Dariya muka yi dukkanmu. Maigadin gidansu Uzairu zuchiyata ne ya wangale mana get muka shiga muka ajjiye motarmu a rumfar motoci. "Ki yi zamanki al sa'ada zan buɗe miki da kaina" Fita yayi ya zaga ya buɗe mun motar. Yana murmushi ya miƙo mun hannayenshi, nima ina murmushin na ɗaura hannuna a hannun nashi na fito. A jere muke tafiya har zuwa ƙofar shiga falon. Mun ɗan jima muna bugawa har zan kira Maigogul sai ga ɗan masu gida ya buɗe mana yana saye da gajeren wando da amles ɗaya daga cikin kayan da muka je Canada. "Ahh ashe manyan baƙine damu. Na zaci su Labbai ne har suka iso ai. Alhaji bismillah, ke kuma ki koma Lolo" Dariya muka yi dukka Uzairu zuchiyata ya bamu hanya muka shiga tare da ya da zango a falo. Gaisawa Uzairu zuchiyata suka yi da Alhaji Zaidu. Ya dubeni yace. "Ke bakya gaisuwa ko lolo zanyi maganinki. Ka ganta Alhaji gani take yi ma ta girmeni sabida kawai ina abokinta" "To ai Yaya Uzairu ai ƙawarka ce shi yasa, bana shiga tsakaninku hakane Wazirat al sa'ada uhm? " Ya ƙarashe yana kallona cike da kulawa. Uzairu zuchiyata ina ganinshi yana haɗiye dariyarshi. Fitowar Maigogul saye da jallabiyya baƙa da carbi a hannu ne yasa Alhaji ya dena kallona. Ƙamshinshi ya karaɗe falon har haske da wani kyau naga Maigogul ya ƙara yi wallahi to ya samu nutsuwa. "Alhaji ashe kun ƙaraso. Haba nace ma ita Hajiya kamar ana buga ƙofa ashe dai kune" Tsugunnawa Alhaji Zaidu zaiyi Maigogul ya riƙeshi. "Dan mahammada rasurulillahi ka dena ba girmanka bane kai Uzee maza je kasa a kawo ruwa da abinci. Bari in kirawo Hajiya" Saida ya zaunar da Alhaji Zaidu a kujera kana ya tafi bagazan _bagazan jallabiyyar tana ƙara. Mai aiki ce ta kawo mana abun sha, Uzairu zuchiyata kuma ya kunna mana TV sai ga Hajiya ta fito tare da Maigogul tana a cikin ado abunta sai fara'a take yi. "Alhaji Zaidu kai da Amaryane a gidan? To sannunku da zuwa" "Mun same ku lafiya Hajiya? " Ya faɗa kai a ƙasa. "Lafiya lau ya Hajiya da jikin nata ince dai ta warke ko? " Jikin da sauƙi Hajiya ina wuni? " Na faɗa ina dariya. Itama da dariyar muka gaisa. "To taso mu shiga ciki kinji ga la'asar ma tayi suma nasan masallaci zasu shiga. " Jakata na ɗauka nabi bayanta muka shiga ɗakinta. Ina zaune akan kujera Maigogul ya shigo ita kuma Hajiya tana gaban firich. "Lolona bari in yi alwala muje masallaci mu dawo sai inzo muyi magana kafin su Labbai su ƙaraso ai zaku jira zuwansu ko? " E zamu jira Maigogul ka faɗa mishi" "To to shikenan zamu yi maganar" Banɗaki ya shige. "Ƴata ga wannan sha rabi" Ta miƙo mun wani abu kamar tsumi a gora na buɗe na sha rabin da tace mun in sha. Wani ta kuma bani a kofi na shanye. Maigogul ya fito ya tsaya a gaban madubi yana ta fesa turare. "Hajiya zamu je masallaci, babu wani abun ko? " "Babu Honey adawo lafiya Allah ya tsare ya kare" "To ameen Hajiyata" Ya ƙarashe da dariya ya fita. Nima dariyar nayi Hajiya Balaraba tace. "Dariya iyayen naki suka baki Lolo? Bari in dama miki wannan gumbar ta musamman je ki ɗauro alwala kafin in gama" Miƙewa nayi na ɗauro alwala na fito ta bani gumba damammiya taji nono wadatacce na shanye tas na tada Sallah ita kuma ta fita. Ko wacce kusurwa ƙamshin turaren Anty Badiat yake yi turaruka masu inganci da kama waje babu algus kenan, sai dai kace yai tsada ba dai kace bashi da kyau ba. Gaskiya kana kunna turarenta wlh kasan ba da ka take aikinta ba, cikin ilimin abun take yi. Humrar matan aurenta da Kulaccham ɗinta ta matan Aure mai suna Laiya wato dare gaskiya duniya ce. Ina zaune akan sallaya na kira Adama da ƙyar na sameta. "Hmmm Lolo gani a gaban tukunya ina aikin tuwon dare na bataliyar gidan Alhaji. Nadawo kishiyarmu tayi yaji wai ita ba zata zauna da yayar ɗan daba ba. Ragowar matan kuma sun dasa kishi sabida sunga yadda na sake kyau da kuma kayayyakin alatu dana tawo dashi. Ke ni dai ganinan dai" Ajjiyar zuchiya na sauke nace. Amman Adama me kike ganin zaki dinga siyarwa da sai in baki jari ki ɗan dinga jujjuyawa, nima in da kasuwancin naki zaiyi ƙarfi sai in saka kuɗina ko ɗan kunnena in siyar ki dinga juya mun. Duk da gobe zan soma zuwa ofis kuma ina da albashina" Adama tace. "To Lolo da kuwa naji daɗi zanyi tunanin da ɗan bincike inga mai ya dace in yi. Zan kiraki gobe da safe, kafinnan na ɗan nutsa." Da haka mukai sallama hayaniyar yaran gidanma ta hana in jita da kyau yadda ya kamata. Mai aikice tayi sallama ta shigo da kula biyu a tire da robar zuba abinci da cokali harda abun sha ta ajjiye ta fita. Abinci na zuba tuwone na shinkafa miyar nama dagargajajje ina saka abincin a baki na saki dariya wannan ɗanɗanon girkin Maigogul ne tabbas. Wato shi yake girki soyayya daɗi su Kayi nayi ana can uhummmm Ina cikin ci Hajiya ta dawo. Abinci yayi daɗi ai Maigogul ya iya abinci sosai. Dariya tayi tace. "Hiye ashe har kin gane abincin Babanki ne wannan? Uzee ma yana ci ya gane, dama yace har a can Dutse yana musu girki in ta ciciyoshi. (Miyar namannan duniyace wallahi daɗinta baya musaltuwa itace asalin miyar da malam Bahaushe ke cema tuwon girma miyar nama😆) Muna haka Maigogul ya shigo ya nemi waje ya zauna. "To ni kam bari in baku waje ku ɗan zanta" Cewar Hajiya data miƙe ta fita. Maigogul ya ƙanƙance idanunshi ya kalleni fes. "Lolo kinga kishiyarki ba ƙaramar muguwar tantiriyar kiriminal bace. Amman in tasan wata bata san wata ba wallahi tayi da ɗan halak. Yawon duniyana gogewar dana samu da buɗewar ido, da ilimin rayuwa, da gogewa wajen karantar mata akanki zaiyi aiki. Taci sa'a na koma ga Allah da a dare ɗaya zan ɓarar da ita ko wanne irin boka take bi. Ke ko oremi take mata aiki shugaban bokaye mace a ƙabilar yarbawa to wallahi da inna dinga turen aljanu gidannan saita fita ta baki waje ni bana wasa bane amman sa'arta ɗaya dai wallahi al'mura Mrs Bukhari [10/8, 9:15 AM] BADA'AT IBRAHIM: MRS BUKHARI 22