Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 - Chapter 1
Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 Chapter 1: Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 Chapter 1. [10/14, 8:39 PM] Diejahmaidoki: IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO…
3,814 words
[10/14, 8:39 PM] Diejahmaidoki: IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA BIYAR SHAFIN FARKO
BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI.
NAGODE SOSAI DA ADDU'O'INKU HAƘIƘA HAKANNE YA ƘARA ƘWARARANI. SAI DAI ALFARMA ƊAYA NAKE NEMA A GAREKU ALFARMAR ITACE BA KULLUM ZAKU DINGA SAMU BA SABIDA YANAYIN JIKINA. AMMAN FA DA ZARAN NA WARWARE IN SHA ALLAH BABU WASA SAU BIYAR ƊINNAN A SATI ZAKU SAMESHI NAGODE NAGODE SON SO💪🏼
"Wazirat al sa'ada barka da safiya ya darenki ya kasance uhm" A kunne yake mun maganar ya riƙeni ƙam kamar za'a ƙwaceni a hannunshi. A kunnen nima nace. Na kwana cike da kewa da begen abun ƙaunata. Amman yaya zanyi nasan komai mai wucewane kamar ma ba'aiba." Murmushi yayi mun a kunne tare da sumbatar kunnen. Ya jani muka zauna a kujera ina kan cinyarshi muna hirarmu ina tambayarshi jikin Hajiya cike da nuna damuwata da ciwon nata wanda hakan na lura yana ƙara mishi sona da nutsuwa dani. Amman fa idanunshi akan wuyana. Hannu ya saka ya ɗago azurfar wuyana ya ƙurama kwaɗon sarƙar idanu. "Wazirat a ina kika samu wannan sarƙa amman bai ba dai siyanta kika yi ba ko?" Yayi maganar cikin sauke numfashi mai nauyin gaske. Ba siya nayi ba. Kyautarta aka bani a matsayin gudunmawar Aure" Shiru yayi ya saki sarƙar ya kama ɗan kunnen ya dubi tsakiyar idanuna yace. "Waye ya baki uhm?" Goggo Amfana" Kafin in rufe baki ya ƙanƙameni tsam a ƙirjinshi yana sauke ajjiyar zuchiya. Ni da tsoro ma naji sabida halin rayuwa da halin jama'a nayi tunanin wata maƙarƙashiyarce sabuwa kuma. Mun jima a haka kafin ya ɓanɓare jikinshi a nawa ya dubeni cike da farin ciki. Yaimun raɗa. "Akwai hikmar da yasa Uwata ta baki wannan sarƙar haƙiƙa kin bambamta kuma kin sake samun wani irin matsayi na sake ɗaura sonki a wani bigiren da babu wata mace data taɓa hawa kai" Murmushi nayi na ɗan ja gemunshi tare da sumbatarshi. "In zaki haɗa kayanmu ki haɗa mana waje guda, sai ki zaɓa mun wanda kika fi so. Ƙanwar Hajiya Naja'atu zata zo anjima ta haɗa mata nata, bata sanma dake za'ai tafiyar ba jikin nata babu daɗi Hajiya maganar rashin haihuwa ta ɗauka ta ɗaura a ranta wazirat ko jiya da sambatun batun haihuwa a bakinta muka kusan kwana, sai wajajen ukun dare bacci ya ɗauketa tasha magungunanta ma ta samu bacci wallahi taƙi kinsan ciwon damuwa akwai wanda yake taɓa ƙwaƙwalwa to nata ya kai wannan matakinne." Ajjiyar zuchiya na sauke. Da gaske tausayi Hajiya ta bani dole ko maƙiyinkane ka tausaya mishi in baya haihuwa kuma yaƙi karɓan ƙaddararshi. Ciwon damuwa kuwa ko Ƴar Shuwa da mijinta dana fi tsana fiye da komai a rayuwata wallahi bazan so musu wannan ciwo mai wuya ba. Allah sarki. In akwai rabo Allah ya bata. Allah kuma ya bata lafiya. Haƙiƙa duk da nawa ciwon bai kai nata ba, nima na ɗanɗani azaba sosai kuma ciwone mara sauƙi gaskiya. Ka rabu da Hajiya tayi fama da kanta basai ka faɗa mata tare zamu je ba dan Allah. Kayan kuma zan haɗa mana ko zuwa yamma ne, ko dare ma. Kuma inaso in zaka fita in bika in gaisheta na kai muku abincin karyawama yana falo" Farin cikine ya lulluɓeshi sosai yaita bina da adda'a. A hakanma ban barshi ba saida na sako mishi farfesun kaɗan yaci tukunna kafin muka jera har zuwa ɗakin Hajiya. Wallahi ni dai naji muryarta kafin mu shiga ras babu halamun ciwo. Amman shi ba lallai yaji ba da danginshi yake waya batun suna yake sanar musu zai kawoni amman ba daɗewa zanyi ba tare zamu juyo. Yana gaba ina binshi a baya muka samu ƙanwarta da Akwati turola tana haɗa ma Hajiya kayanta. Ɗakin Hajiya gaskiya yafi nawa kyau kayan ɗakinta ƴan wajene masu tsada sosai, ɗakin ni kaina ya bani sha'awa sosai, kuma komai tsabtsab duk da dai mai aiki ke hidimar. "Alhaji ka shigo, kaida Amaryane? Ai Hauwa take cewa ashe tayo abinci ta kawo. Yanzu nake son in taimaka mata ta kintsa sai in kaita taci" Zama yayi a gadon. Ni kuma a kujera na zauna muka soma gaisawa da Naja'atu fara'a kamar zata halakata. Hajiya kuwa dana gaisheta hannu ta miƙo mun, na lura bata son magana duk cikin ciwonne. Hannuna na miƙa mata ta ɗaga mun halamun godiya. Shi kuma duk saiya sake shiga damuwa yana ta shafan hannunta. "Wannan ciwo Allah dai ya kawo ƙarshenshi ya bata lafiya mai ɗorewa. Dake naga kusan shekara nawa bai tashi ba, mu mun ɗauka ma ta warke sumul wallahi Depretion ciwone mai wuya da tsanani. Ubangiji Allah dai ya dawo daku lafiya. Amarya sai ayi haƙuri a ɗauki ragamar kulawa da gida har zuwa lokacin da Allah zai dawo dasu" Murmushi kawai nayi inata adda'ar Allah yasa kada Alhaji yayi katoɓarar faɗama Naja'atu tare zamu tafi. Itama da biyu tayi maganar. Inma Hajiya na ciwo wallahi ciwon kishine duk da tana ƙoƙarin dannewa amman dai shi ɗinne wallahi. To bari in shiga ciki zuwa anjima zan sake leƙowa" Na faɗa tare da nufar hanyar waje. "Rigunan bacci nawa zan saka miki Yaya? " Naja'atu ta faɗa harda ƙara murya." Wucewata nayi ɗakina na baje ɗaiɗai a ƙasa ina shan farfesuna ina nazari, dana tuno Alhaji Zaidu sai inji sabon farin ciki, haka inna kalli sarƙar wuyana sai inji na ƙara godiya ga Goggo Amfana. Wajajen taran safe sai naji ana buga ƙofa nasan bazai wuce Labbai ba. Ina buɗewa kuwa na ganta tare da Uzairu zuchiyata. Baki na washe cike da farin ciki da murna muka shiga har falo. "Lolo kenan kinsan Allah? Ke mai sa'ace a rayuwa. Yanzu wannan gidan gidan mijinkune duk girman cikinnan naki ne. Wallahi Lolo kada ki yarda kiyi irin zaman gidan Babangida, anan kam kema ki baza komarki kici karanki babu babbaka" Uzairu zuchiyata ke magana ga farfesun da nake ci a hannunshi yana yi yana shan romo. Nan ya shiga loma. Zama labbai tayi ni kuma na shiga ciki na haɗo musu kaɓakin arziki rigi_rigi muka sake bajewa. Ga Labbai ga milo da madara anyi haɗin murtuk anata sha😆. "Lolo kina cin duniya da tsinke. Lolo banga kishiyarki ba? " Tana kwance magashiyyan gobe ma zamu tafi Jidda zata ga likitanta. Amman bata san dani za'aje ba" "Toh ikon Allah mata ana munafurci Allah ya kyauta. Ke dai ki kwantar da hankalinki ki kula da aurenki. Kina gani dai mu gamu bamu samu ko kamar Babangida ba, bare wannan babban gida na hamshaƙai. Gashi ɗakinki da jikinki duk ya ɗauki ƙamshi. Gaskiya duk zaki sanmun waɗannan turarukan alfarman na Mrs Bukhari gidan ƙamshi ina." Baki Uzairu zuchiyata ya washe. "Tabb lolo irin abinda nake da sha'awa kika samu. Inason inga ina zagaya duniya da kika ganni. Ni dai Lolo ki fitar dani kunya biki nata matsowa su Felisha suna ta shirye_shiryen tawowa. Nayi tunanin sauke su a gidan Mum to Felisha tace Hotel zasu kama, a zo ayi bikin da za'ayi mu wuce Canada canma ayi bikin shikenan na zama mijin Baturiya. Girki kuma ina koya a wajen Maigogul dan ya karɓe ragamar girkin gidan shi yake yin komai. Amman wallahi Mum na mutuwar sonshi yana kasheta da gayu. Duk bala'in son taga ta ƙure gaye wallahi ta kasa kamo Dad yanzune ma fa yake adonshi na asali. Gashi tana shiga dashi taron kunya sosai harda gwamnoni Maigogul na ta'amali. Duk da dai suna haɗuwa dasu a sha'anin biki" Labbai tace. "Koni bikin da muka shiga Abuja gwamnoni uku nagani harda Atiku Abubakar na gani. Sun saba da manya gaskiya." Muna ta hirarmu muna shewa Alhaji Zaidu ya shigo yana murmushi da yaga su Labbai. Gaza na biye dashi da jakar baya da kayan farauta a jikinshi. Gaza har ka iso kenan ikon Allah" Dariya yayi ya nemi waje ya zauna, ya kalli waje ya kuma buɗar bakinshi yace. "Kutumar dumadu Lolo wai eh duk wannan gidanki ne, ji madara ga kayan more eh rayuwa? Allah sarkin eh girma. Eh kai mata maza nan aka tawo kenan. Babban Yaya kaga wannan aminin Lolo kenan sai su kashe su eh haƙa su birne abinsu. Ni nasan eh sabida ita ma ya eh dawo Kano. Ya bar Rakiya a eh damuwa sai ni nake ta kulin ɗinta eh wallahi" Alhaji Zaidu ya zauna kusa da Gaza yana murmushi yana kallona. Ni kuma duk kunya ta kamani. Me yasa Gaza zai wani ɗakko kayan farauta ya saka dan Allah. "Wazirat ki ba Gaza abinci yaci zanje in kintsa zamu fita tare zan kaiki gidan suna ki dai leƙa kada ace babu wanda yazo daga gidana. Anty Labbai ashe kune a gidan' Nan aka shiga gaisawa ya fita yana dariyar Gaza. Ni kuma nayi maza_ maza na tafi shiryawa na bar labbai na zuba ma Gaza abinci. Farin lace sol mai masifar kyau na saka ɗinkin riga da siket anyi mishi surfani har a siket ɗin. Mayafina goldin na ɗakko mai tsada na wannan zamanin. Na ciro takalmi da jaka da suka dace da mayafin. Na ɗakko gwal ɗina ƙaramar na maƙala zubuna biyu na jera a hannayena ga agogo ga awarwaro. Ina fesa turare marar ƙarfi Labbai ta shigo. Yauwa Labbai kina ganin sana'ar me ya kamata ace kin soma tunda Maman Shafa na tata sana'ar kema saiki soma taki ai ko? " "Wallahi Lolo ni kaina inata tunanin yafa kamata sana'ar ko babu yawa a jaraba. To ni wallahi ko man ƙuli sai in dinga saidawa tunda na iya matsar man a jikin tunkuza." Kuma zaki iya tunda naga kina da jarumta. Nawa ne zai isheki jarin to? " Baki ta washe tana ta murna dubu saba'in na ƙirga na bata nata. Na ƙirgi dubu ɗari nace taba Hajiya Balaraba Adama zata zo sai ta bata. Na ware wasu kuɗi nace taba Rakiya da Hauwa Atampa na cira a cikin akwatin da Hajiya taimun na zura a leda zan tafi ma da mai jego, na ciro kala biyu da takalmi harda sarƙa nace a kaima Rakiya sarƙar kuma ko Rahama a bata tayi zawarci dashi. Da muka sakko na ɗiba mata su madara milo harda siga, dasu shinkafa kamar dai yadda aka saba e. Turarukan wutanma na ɗiba mata na bata lace mai kyau a cikin akwatin da Hajiya taimun. Alhaji bai jima ba ya kirani yace mu fito. Nako ci sa'a Hajiya bata babban falo. Su Gaza sukai gaba da Alhaji Zaidu, Uzairu zuchiyata Labbai taba ledar kayanta ya fice mata dashi. Ni kuma na raka Labbai falon Hajiya tana falo ita da Naja'atu Labbai ta gaisheta da jiki. Ni kuma nayi mata sallamar zan leƙa gidan suna daga nan kuma zan soma shiga ofice yau." "To shikenan sai kin dawo. Itama yar taki zata dawo ne? " A_a yau zasu wuce ita da mijinta" Naja hannun Labbai muka fita. Sai muka ji Hajiya tace. "Subhanallahi wankin kula yana shirin kaini dare, ya zama dole in ma tubkarnan hanci. Ofice?" Idanu muka haɗa da Labbai inyi magana na lasa jikina ya mutu yayi mus wallahi. Labbai ce ta ja hannuna muka fita. Ni dai har muka kama hanyar Rano jikina a mace. Gaza sai hira yake ma Alhaji suna ta cin dariya. Ni ko saida Labbai ta zungureni ma na gane me ake ciki. Dake Gaza ne a gaban mota ni ina baya a tsakiya hankalin Alhaji Zaidu a kaina duk ɗagowar da zanyi sai mun haɗa idanu dashi. Har muka iso Rano gidan suna kenan. Dani da Labbai dashine muka fito zuwa cikin gidan, su Gaza kuma muka barsu a mota. Ai kuwa gidan shaƙe dam da jama'ar suna anata ɗaura tukwane, wata tukunyarma cike da jallof har an sauketa ga kaji anata suya. "Ga Amarya ga Yaya. Sannunku da zuwa Amaryarmu ashe zaki zo?" Cewar Zarah data rungumeni tana dariya. "Zara'una kenan. Duk kunanan. Anty Tani kema kinzo ashe? " Ya ƙarasa ya tsugunna a wajen wasu mata su uku manya dan sun girmeshi. Binshi nayi nima na zube, Labbai kuma tana ta gaisawa da ragowar dangin Alhaji. "Zaidu ashe saida ka ɗakkota kuka tawo? Ai data yi zamanta haihuwa da bata ƙarewa a wannan haula kamar suna gasarta. Yanzu jibi kusan mutum goma ke da ciki ma fa. To ku shiga Fatiman na ciki" "Ai Anty Tani ba zama dama zata yi ba. Na dai kawota ne tayi barka taga Ƴan uwa tunda Ita Hajiya ba zata samu zuwa ba. Gobe ma Jidda zamu wuce" Ta kusa da Anty Tani tace. "Wannan ciwo Alla ya yaye mata shi. To yanzu menene ya tayar da ciwon ne? Dan ba'ace kishiya ba ko, naga ai jarumace wallahi kuma mata nawa aka kawo mata a baya ma" Nan dai akaita maida yadda za'ayi kafin Zarah da Anty Tani sukai mana jagora zuwa ciki. Shi a falo cikin tarin ƴan gidansu ya zauna mu kuma muka shiga wajen maijego muka dubata da jinjira. Naga bata fara'a kuma batai murna da ganina ba tunda yaune haɗuwarmu ta farko ita ba biki tazo ba. Ashe ita ƴar ɗakin Hajiyace irin ta ƙuryannan sai da Zara'u ta faɗa mun na fahimceta dan wallahi Alhamdulillahi kowa yanata haba_ haba dani Anty Tani ta miƙa mun yarinyar tace in kaima Alhaji Zaid. Na shiga falon na sameshi dasu Zarah suna tattaunawa akan kasuwanci. Na miƙa mishi yarinyar ya haɗata da hannuna ya riƙe ya kalleni tare da lumshe idanunshi. Na fahimci duk ya damu da yadda yaga yanayina wani iri, ku kuma duk wata fara'a da nake yi ta dole ce. Hankalina yana kan furucin Hajiya wallahi. Bansan me zai biyo baya ba, bani da ilimi amman da Allah na dogara. Murmushi nayi mishi na zare hannuna na nemi waje na zauna. Cikin minti ashirin muka gama komai muka fito daga gidan kai tsaye Family house muka shiga shima mun kai minti ashirin, kuɗi ya bani masu kauri duk tsofaffinnan na bisu na danƙa musu. Ya haɗani da Anty Khadija yace mata. "Anty khadija ga Shalelena na haɗaku tunda ke ba team ɗin Hajiya kike ba. Ko dai bakya so Anty Khadija? " Dariya tayi tace. "Alhaji Zaidu kenan ai baka sani ba Goggo Amfana da kanta ta ce ta haɗani da Sabuwa ƙawance. Ina da lambarta zan sata a group ɗin family na mata zallah. Sabuwa akwai groups ɗina biyu zan sakaki zaki ƙaru sosai. Ina zuwa ko?" Ta tashi ta shiga ciki sai gata da magungunan mata cikin leda. Nan Alhaji Zaidu ya fice taimun bayaninsu tas kana tace a group ɗinta tana koyar da yadda mace zata zama sarauniya duk wannan magungunan tana koyarwa bama ita kaɗai ba harda ƙwararrun mata daga Sudan, da Chard, da kamaru. Nayi mata godiya muka fito ni da Labbai a ƙofar gida muka samu su Gaza muka rankaya sai kamfani. Nan Alhaji Zaidu yaita zagawa da Gaza da Uzairu zuchiyata. Ni da Labbai kuma muna ofishinshi ina ɗiɗɗiban mata maganin matannan. Tsumin sai ruwan gora muka shanye na haɗe mata su waje guda dan tsumi kala uku ta saka mun. "Gaskiya Lolo ki gode ma Allah. Wannan karon dangin miji na sonki sosai. Wannan Anty Khadijan tayi mun wallahi da ganin yanayinta kinsan tasan kanta. Yanzu lolo anan zaku dinga aiki? Allah mai iko wannan wai ofishinki ne" Dariya muka yi. Basu gama zagayensu ba su Maigogul suka iso da Hajiya balataba da Cicib suna son zasu kama hanyar Dutse. Yau dai Hajiya zata je taga su Rakiya kuma ko ya zata kaya sai Allah. "Gaza ashe kazo ikon Allah Alhaji me zamu ce maka ai sai godiya." Cewar Cicib kenan. "Babu komai Alhaji, Baban Rahine ai abokinane" "Ni duk kewar Rahine ke damuna Alhaji. Na barota tana ta fisge_ fisge eh ni wato da zaka eh barni sai in ɗakko Rahine mu zauna abinmu wallahi Allah zata yi amfani sosai zata dinga gadi" Dariya kawai Alhaji Yayi ya riƙe kafaɗar Gaza kawai. Maigogul yace. "Shashancin banza. Kai da aka kawo aiki ina kai ina batun Rahine ai gara ka zauna kayi aikinka. " "Hattara eh wallahi Dattijo tunda nazo wajennan kaga na eh kulaka ne? Ai tunda ka taɓo rabin raina ka taɓo gidan rina eh wallahi" "Kul Baban Rahine ba'a faɗama iyaye irin wannan maganar tausasa harshe akeyi akansu. Alhaji Baba kayi haƙuri" Dariya Maigogul yayi yace. "Ai babu komai gyatumarshi yake tayawa kishi fa shi yasa. Munafurcinsu ɗaya shi yasa ai daya shigo bai neme ni ba ma, bare ya so ganin ƙaramar uwar tashi" Ni dai ina tsaye ina fama da kunya. Gaza ya dubi Hajiya Balaraba yace. "Ina eh wuni nace" Ita kuwa da fara'arta ta amsa ato ai ba'a rufeta ba. Labbai ce tace. "Mu kam zamu tafi Allah ya ƙaddara saduwarmu, Alhaji Zaidu ka sake gaishe da Hajiya da jikin "To shikenan zata ji" Kuɗaɗe Alhaji ya laluba ya damƙama Cicib ya danƙama Maigogul, Uzairu zuchiyata ma an bashi. Ya bani na miƙa ma Labbai kuma naji da kauri na labbai zaiyi dubu hamsin gaskiya ko talatin haka. Tare da Maigogul da Uzairu zuchiyata da Hajiya suka tafi a mota ɗaya ya rage sai mu uku. "Yauwa Babban Yaya. Naga kamar akwai ɗakin kwana a kamfaninnan kuma naga shanya ma halamun ana kwana ko? Madadin inje in zauna eh a gidan Ƙanwata a bani waje anan eh kawai ni zanfi sakewa eh gaskiya" "Na fahimta Baban Rahine. Akwai Shu'aibu ɗaya daga cikin amintattun yaranane dashi ma nake son ku dinga sintirin zuwa kwatano, da sauran ƙasashe siyo mota. Haya na kama mishi kuma ɗaki biyu da falone dan ciki da falo muka so, ba'a samu bane sabida yaso ya dawo da iyalinshi birni sunƙi dole ya barsu a Rano. Sai ku zauna ɗaki ɗaya. Ina zuwa bari in kirashi kuje ka kama aikinka. " Kiran Shu'aibu yayi sai gashi da sauri. "Shu'aibu ga Baban Rahine wan Matatane zaku zauna tare a ɗakinka, shine wanda zaku dinga zuwa siyo motoci dashi. Sai ka nuna mishi duk abinda ya dace, ka sai mishi katifa da duk abinda yake da buƙatar sawa a ɗakin" "To shikenan maigida an Gama. Baban Rahine maraba da zuwa, zamu iya tafiya" Gaza yayi dariya yace. "Lolo a taya ni godiya, godiya dubu nace eh Alhaji sai da kai eh wallahi. Zako kaga amana wallahi" Sa kai yayi ya wuce yana ɗaga hannaye sama. Hannuna Alhaji Zaid yaja muka shige ofishinshi. A cinyarshi yaimun masauki hannayenshi biyu riƙe dam da ƙuguna." "Waye ya taɓa mun ke uhm. Hankalina kacokam yana kanki, Menene uhm faɗamun" Ƙuguna ya matsa na lumshe idanuna. Babu komai kawai dai yanayin jikinane ba daɗi" Duk sai ya rikice yana cewa muje asibiti. Saida na saisaita shi ta hanyar yimai abinda na lura yafi so sumba kenan. Tuni muka shige sama jannati mukaita shillo, da ƙyar jirginmu ya sakko. Idanu a lumshe sunyi jawur cikin muryar kasala da zabari yace. "Gashi kin kyautar dani a wajen Hajiya uhm. Kamar ni kaɗai nake kewarki uhm wazirat. Ko hotel to zamu tafine in muka kammala mitin ɗin uhm? Ina da mitin sannan zan gabatar da Baban Rahine za'a rubuta sunanshi zan taimaka mishi ya cike wasu takaddun, kema zan gabatar miki dasu" Narkewa nayi a jikinshi kamar yarinya. Yadda kake so ai haka zanyi. Ka mance kaine malallakin Sabuwa sukutum ne?, gangar jikina cike da kewarka abin ƙaunata" Murmushi yayi mun, ya sake dulmiyawa inda yafi so mun jima a cikin wannan inuwa mai sanyi da daɗi. Sai da lokacin miting yayi ya miƙe ya saisaita kanshi muka fito kai tsaye zuwa ɗakin da aka ware domin mitin ɗin. Kowa ya hallara ashe harda Gaza yana zaune da wannan ƙaddararrun kayan da bashi da wasu masu kyau da suka fisu. Zama nayi a kujerar da take kusa dana Alhaji Zaidu aka soma gabatar da mitin sai da muka yi minti talatin kana aka sallami kowa. Yace da Gaza yazo ya sameshi a ofice. Yazo suka yi cike_ciken takaddu daga haka suka tafi zuwa sallah. Alwala na ɗaura nima nayi sallah, yana dawowa ya ɗaukeni a gaban mota sai wani lafiyayye Zangon baƙi na masu dashi. Kuɗin ɗaki ya biya muka wuce. Muna shiga ya matseni tsam a bango. Lallai a wannan zangon baƙi munyi abu gaskiya shima yanayine mai tsayuwa a zuchiya. Raɗa yaimun a kunne harna soma bacci. "Allah yasa ajjiyata ta shiga Al sa'ada. Kin shirya cin amarci a Jidda dai ko? Kifa shirya in sha Allah acan zamu samo ɗiya mai suna Jidda in sha Allah" Kuma laɓewa nayi a jikinshi, ina na kasa magana sai bacci. Bamu muka tashi ba sai la'asar a gurguje yayo wanka ya wuce masallaci. A taƙaice sai taran dare muka baro zangon baƙinnan zuwa gida. Zukatanmu cike fes da farin ciki da wani irin shauƙi da nutsuwa ta musamman, wallahi Allah wannan abun na sake haifar da shaƙuwa da nutsuwar zuchiya dana ruhi. Ko da muka je gida. Ƙannen Hajiya suna gidan ita kuma tana kwance tana mun kallon biri inai mata kallon ayaba. Dubata nayi da jiki harda tsarabata nayi wucewata ciki. Nan na kira su Rakiya. Ko data ɗaga ina jiyo hayaniyar Maigogul. "Ai wallahi sai dai ka kama mata zangon baƙi taje ta kwana goben ta wuce. Ko kuma ni in bar mata gidan" Cewar Rakiya. Idanu na lumshe. Haba Rakiya me yasa zaki... "Abu ta kazan... Ke lolo cikinki nake dashi ki yi mun shiru kada in haifeki mitsiyaciya. Ai da saka hannunki akan Auren ke da Uzairu zuchiyata dake ku tambaɗaɗɗune. Menene kike kirana to? " Ajjiyar zuchiya na sauke nace. Allah ya baki haƙuri dama Jidda zamu tafi gobe shine nace barin in sanar miki. Sannan na ba labbai saƙo zata kawo miki. Rakiya ki dinga haƙuri dan Allah faɗanki yayi yawa." Guɗa ta saka tace. "Ƴata ta zama sarauniya hiye Lolo kika ce Jidda fa ta ƙasa mai tsarki? Ma'aikin Allah na madina ni Rakiya. To shikenan Lolo kince Labbai zata kawo mun saƙo saƙon menene? " Murmushi nayi mata nace. Kuɗine da atampa, sai ɗankunne nace aba Hauwa" Tsokanarta nake yi "Ina baƙa baƙar munafuka kenan babu abinda zata samu na rantse miki da Allah. Cikin Ƴaƴanta ubanwa ya taɓa bani wani abun. Layuza ma na kulle a ofishin Ƴan doka uban me tayi sai Allah. Sunata nuƙu_ nuƙu kinsan Hauwa da gulma" Rakiya tafi minti goma tana magana da ƙyar ta barni mukai sallama ina ji tana hawan Maigogul. Ni dai a daren saida na gama shirya mana komai kana nayi bacci. Da sassafe kuma shayi kawai nasha na gyare ɓarayina na fito fes cikin baƙar abaya da jaka da takalmina sai akwatin kayanmu. A falo muka haɗu da Hajiya tana tsaye harda jingina da bangi. Ganina da akwati a shirye tsab ya tsitaye mata man kai tas. Alhaji Zaidu ne ya sakko cikin shigar jallabiya baƙa mai wando yayi kyau sosai fuskarshi cike da annuri. Sai ji mukai tim Hajiya ta faɗi ƙasa tana numfashi ɗaiɗai. Kuyi haƙuri mu dasa aya anan nagode Mrs BUKHARI [10/15, 12:53 PM] BADA'AT IBRAHIM: MRS BUKHARI 2