Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 - Chapter 2
Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 Chapter 2: Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 Chapter 2. Da sauri na yar da akwati na nufeta ina mata sannu. Fatana…
4,368 words
Da sauri na yar da akwati na nufeta ina mata sannu. Fatana kar ta suma ace an fasa tafiyar domin ita kanta ƙurudinta kenan. Ina ganin makirci. Wallahi saita soma sambatu wai ita mutuwa zata yi tana ganin mala'ikun mutuwa bama sai anyi tafiyar ba. Ta tashi hankalin Alhaji Zaidu, nima dai hankaalina ya tashi sabida kamar yanzu kam ciwon nata ya tashi da ƙarfin tsiya, ni har wata rama ta faraɗ ɗaya naga tayi fa Allah. Haka na taimaka mishi muka sakata bayan mota ƙaninshi ya tuƙamu zuwa filin jirgi tana ta ambaton Allah ko idanu bata buɗewa. Shi kuwa Goga sai tofeta yake yi da adda'a a haka har ƙarfe tara daidai aka sakamu a bus zuwa gaban jirgi, daga nan muka haye jirgi. Awanmu goma a jirgi dake jirgin yayi tsaye tsaye sosai duk mun galabaita ƙarfe bakwai na dare muka sauka a Jidda. Daga nan muka shiga mota kai tsaye zuwa asibiti. Dakta Sameer Abbas asibitin kuɗi naga an rubuta. Hmm asibitin ya haɗu sosai. Ni dai ina biye dasu, muna gani aka shiga da ita wani ɗaki na musamman. Ni dashi muka bi bayan Dakta zuwa ofishinshi ni dai inata kalle_ kalle gaskiya. Ina ji sunata larabci ba ƙaƙƙautawa Daktan ma har nunoni yayi ni dai naji Alhaji yace mishi wai ko Zaujati kamar dai haka ɗaliban larabci su gyara mun in na rubuta ba daidai ba. Tare da Daktan suka fita basu suka dawo ba sai goman dare, ya dai leƙo ya miƙo mun laban a ƙaramar gora na sha, shi kuwa ko ruwa bai kurɓa ba abun tausayi. Suna shigowa ya dubeni yayi murmushi. Nima murmushin na mayar mishi yace. "Shalelena mu tafi masauki sai kuma gobe da daddare ma zamu dawo asibitin dan anyi mata allurai sai gobe da daddare zata farka ko jibi ma da safe. " Hannu ya miƙo mun na riƙe hannun nashi na miƙe yace da Dakta. " Doktor ma'assalama" Sukai musabaha muka fito daga asibitin muka ɗauki Tasi. Muna bayan motar ina laɓe a jikinshi jakata na cinyarshi tsautsayi yasa nace ya miƙo mun agogona. Yana zura hannu ya zaro ambulan ɗin da Babangida ya aiko da mardiyya ta kawo mun. Take wani ruwa ya hauro mun kaina sai naji hannuna yayi sanyi har yana damshi dan masifa. Agogon ya miƙo mun nasa hannu na karɓa shi kuma ya kalleni yayi murmushi kana ya buɗe wannan ambulon sai ga kuɗi da takadda. Kuɗin basu da kauri, takaddar ya ɗauka ya kalleni. "Saƙon waye baki buɗe ba Shalelena uhm? " Bai yi tambayar dan yana jiran amsa ba takaddar ya warware rubutun ciki baifi layi huɗu ba ga abinda makirin ya rubuta. _Cus bazan ce ina taya murna ba dan wallahi zuchiyata ji nake tamkar zata faɗo. Ashe da gaske akwai wata ranar da zaki rayu a ƙarƙashin inuwar wani ƙaton bani Babangida kacigari ba? Duk da nayi farin ciki da baki Auri wancan ɗan akuyan Khalid ba. Daga ƙarshe ina neman yafiyarki Har abada ke ta Babangida ce_ Take naji wani zazzaɓi. "Cus, har abada ke tashi ce, cus, cus?" Naji yana maimaitawa muryarshi da rauni linkib. Takaddar ya nannaɗe ya haɗa da kuɗin ya mayar cikin jakar. Har muka iso zangon baƙi bai kuma magana ba, amman yana murmushi in muka haɗa idanu. Da muka sauka muka shiga zangon baƙin. Muna shiga ɗakin da muka kama ya ɗakko takaddar Babangida ya saka a shara. Waya naji yanayi yana larabci. Yana ajjiye wayar ya sauke ajjiyar zuchiya ya faɗa banɗaki naji ya saki ruwa. Nima saina bishi idanunshi a rufe yaji hannuna a fuskarshi ruwa yaci gaba da zubo mana mai zafi daidai da yanayin lokacin. Kallona yayi idanunshi sai naga sun rine yace. "Kinsan kalan kishina kuwa Shalelena? " Kafin inyi magana ya jawo hannuna ya ɗauramun saitin zuchiyarshi da take ta bugawa. Ƙanƙameshi nayi nace. Sabida rashin mahimmancinshi yasa na mance da takaddar ma. Da ace naso zan karanta ma in yaga ba tare da kai ka gani ba" Fuskata ya tallafo muna kallon juna. "Shalele kada ya sake aiko takadda kisa hannunki ki karɓa bazan lamunta ba. Sannan abinda yafi komai ɓata mun rai shine Cus da naji ya ambaceki, Cus fa yace miki amman ke kinsan menene ma'anar cus da irin macen da ake cema cus kuwa? Matar tawa zai kira da cus. Da kuma cewa da yayi wai har abada... " Bakinshi na toshe da abinda yafi so dole yayi shiru ya shiga sauke ajjiyar zuchiya. Saida na wanke mishi zuchiyarshi tas kana muka yi wanka tare da alwala muka fito. Magriba da isha nayi, shi kuma isha kawai yayi yana sallamewa aka kawo abinci shinkafa kaza harda wani nono a kofi amman naga albasa da koren ganye a ciki dai. Ashe dashi ake haɗawa aci, na gani lokacin da muka je Umara amman ni yar da nonon nake yi sai yau Alhaji Zaidu ya zuba mana kuma wallahi da daɗi. "Shalele me kike ganin ya dace ayi ma Mama da Mama Hauwa, da Alhaji Baba? " Haba dai masta, baza mu ɗaura maka wata ɗawainiya ba, ai gida da ka siya mana ma wallahi ya'isa babu abinda zamu ce. Ga aiki ka ba Gaza shima ai zai taimaka musu" Hararata yayi na soyayya, nayi dariya bance komai ba, shima baice ba har muka gama cin abincin na kora da laban shi kuma shayin da suka kawo yake ta sha. Kayan bacci na ciro mana, a lokacin ya fita yace yana zuwa. Farar rigar bacci na saka ta tashin kai. Na cakuɗe jikina da kullacham na matan aure da humrar matan aure, jigidar matan Auren dake ƙuguna na shafe da Humra danna lura yana mugun son jigidar tana ɗaukar hankalinshi, kuma yana yawan shiɗar ƙamshin. ( kema ki mallaki taki Hajiya wannnan jigidar akwai sirri a cikinta mai girma, in kina so kimun magana Hajiya) Na sake goge bakina da brush tas na jefa minti a bakina na haye gado ina ajjiyar zuchiya. Turo ƙofar yayi ya shigo Ya ilahi abunda ya faru a wannan daren ko na musamman ne sosai mun murje junanmu sosai Alhaji tamkar mayunwacin Zaki haka ya koma mun. Mun kasance cikin wani irin farin ciki na musamman. Bayan komai ya lafa mun tsarkake jikinmu mun dawo gado ne nace mai. Wai me likita yace maka dangane da jikin Hajiya ne?" Fuskata ya shafa yaimun raɗar wasu kalmomin da na kusan narkewa. Shi kuma sai dariya yake mun. Da haka muka shashantar da batun Hajiya muka shiga fallasa asirin zukatanmu kowa na faɗa ma ɗan uwanshi yadda yaji lokacin da akayi kaza da kaza_kaza......., haka mukaita birgima a gado na lura alhaji nason wannan birgimar sosai, kuma shima wani nau'in salon soyayyane mai tsaiwa a zuchiya Allah Daga haka mukai bacci fes zuchiyoyinmu muka wayi gari, shi ya tafi masallaci kafin ya dawo na shalla wankan ƙananun kaya masu ɗaukar hankali. Ai kuwa saida muka yi kafi karin kumallo kafin muka koma bacci bamu muka farka ba sai wajajen goman safe, shima ni na soma farkawa na tashi na sauka a hankali gudun kada in tasheshi yana da bashin bacci sosai bawan Allah. Har nayo wanka, na sake saka wani riga sa siket ɗin na kanti bai farka ba. Ga yinwa sai ɗibana take yi, na ciro gumbata ta dabino da riɗi na dinga ci, ni dai saida naci kusan rabin bokiti lita ɗaya wallahi kafin na ɗanji dama dama na kora da laban ragowar ta jiya. Sai sha ɗayan rana Alhaji ya tashi. Yana buɗe idanu yayi tozali dani. Murmushi na sakar mishi kawai, waya ya soma yi da masu kawo abinci kafin ya faɗa banɗaki. Kafin ya fito na gyare gadon na ciro mishi kayanshi. Ni na taimaka mishi wajen shafa mai da saka kayan. "Kinyi kyau sosai. Kayan sun karɓeki in dan tanine atampa sai dai a saka in za'a fita. Amman in ganki cikin irin wannan shigar nafi jin daɗi musamman in ganki babu ɗankwali. Kina sake burgeni kan wanda kike mun uhm wazirat ɗina mai sambatu uhm" Dariya nayi mishi shima dariyar yake ta mun yana ta tsokanata. A haka muka karya cikin farin ciki sosai. Bayan la'asar yace in shirya mu ɗan fita yana da abokinshi ɗan Kano mazaunin nan jidda muje mu yawata inga gari. Ai kuwa ba shiri na shirya cikin abaya fara sol ni da kaina nasan abayar tayi mun. "To abayarma inaso gaskiya dan itama tana miki kyau uhm inaga zamu ƙara kafin mu tafi ko? " Murmushi nayi mishi na riƙe mishi hannu muka fita. Sai da muka fita, muka shiga tasi muka isa unguwarsu ya kira abokin nashi da lambarshi ta saudiyya sai yake sanar mishi basa nan suna madina ya raka madam ɗinshi. "To Shalelena mu shiga gari ga prince majid park a bayanmu da ƙafa ma zamu gangara muje kisha kallo uhm" Ai kuwa nasha kallo sosai gashi park ɗin babu hayaniya duk da lokacin mutane suka soma zuwa dama ance su Labaraba da daddare suka fiye fitowa da safe rana matansu na killace a gida. Mun sha soyayya harda guje_guje wallahi kamar kada mu bar wajen. Amman dole anayin Magriba muka hau abun hawa zuwa asibiti wajen Hajiya. Mun dai shiga mun dubata tana kwance ana ƙara mata ruwa tana ta bacci. Naga lokacin da muke park ma ya kira asibitin yana tambaya. Daga gidansu Hajiyan ma sun kira dan jin lafiyarta. A ɗakin ya barni yaje yayo sallah ya dawo kana muka bar asibitin akan gobe sassafe zamu dawo dan zata iya farkawa ko yaushe goben. A taƙaice mu kam sai wajajen sha biyun dare muka shiga gida. A wannan darenma kwanan nutsuwa gami da farin ciki muka yi. Sassafe muka nufi asabiti ana muƙu_ muƙun sanyi. Ai kuwa Allah cikin ikonshi da amincewarshi sai muka samu Hajiya ta farka. Amman wallahi da gaske bata da lafiya yanzu kam na tabbatar, duk da likitocinma sun tabbatar. Sai dai hawan jinin da take ciki yafi yawa sama da cutar damuwan cewar likitanta. Na lura bata ko so da ƙaunar ganina. Ko da na gaisheta hannu kawai ta ɗaga mun taƙi magana dani sai mijinta da take ta manne mishi. Baifa samu sukuni ba har saida akai mata allurai bayan taci abinci wajajen ƙarfe goman safe kuma ance sai zuwa gobe zata farka. Sanda abokinshi da iyalinshi suka zo ma mu muna shirin tafiyane sai kawai muka tafi tare dasu gidan nasu, ga matar Abokin mai fara'a da son mutane tana da wayewa sosai a yadda na fahimceta. Dan ko da muka isa gidansu tana ta haba haba dani har cikin ɗakin baccinta ta shigar dani. Muka zauna ga yaranta mata guda biyu ƙanana sai shige da fice suke yi. "Amarya ikon Allah ai mu bamu da labarin Alhaji Zaidu ya sake Aure. Mu munyi tunanin ya haƙura ma da Auren tunda matarshi ba barin yaran su zauna take yi ba" Saita ƙarashe tana murmushi mai ɗauke da fassarar da ita ta barma kanta sani. Cikin mamaki nace. Banganeba ita take koran matan Maman Yasmin? Ai naga Hajiya bata da matsala. Har akwati tayi mun fa, kuma tunda aka auroni take haba_haba dani" Murmushi tayi tace. "Hmm Amarya kenan. Kin ganni nan? Ƙanwata uwa ɗaya uba ɗaya ta Auri Mijinku ni na haɗa Auren. Kinsan Allah ita ke koran matan cikin ruwan sanyi. Da wannan kirkin da kikai mata ishara dashi. Kada in cika ki da surutu bari in kawo mana abin motsa baki" Tana shirin sakkowa daga gado nayi maza na riƙeta. Dan Allah Maman Yasmin ki sakani a hanya. Wallahi bana fatan abinda zai rabani da mijina wallahi Allah" Murmushi tayi tace. "Wasa kike da wuta Sabuwa baki sani ba. Hajiya Munubiya Haɗari gareta fa sosai. Ta wuce duk yadda za'a baki labarinta. Amman zan taimakeki zan haɗaki da ita ƙanwar tawa tana nan a Abuja tana Auren wani babban mai muƙami gwamnati ne a hannunsu ma. Zata fini sanin abinda zata ce miki. Kiyi ƙoƙari ki tabbatar da kun koma kin Haɗu da Aisha kun tattauna. Nima zan tsokata miki abinda ba za'a rasaba. Ke dai ina zuwa" Fita tayi ta barni illahirin mamaki ya hanani sukuni wallahi Allah. Nasan Hajiya makircinta mai girma ne, amman ban taɓa tunanin ita ke koran matan da Alhaji ya Auro ba. Lallai akwai aiki a gabana domin daga kaina in sha Allah alkadarinta saiya karye. Saina nemi kab matan da Alhaji ya zauna zaman Aure dasu na haɗa ilimin zama da Hajiya ni na ba kaina wannan aikin. Ni dai ina zaune a inda ta barni ta dawo da tiren kayan ƙwalam da maƙulashe ta dure mana. Muna ci amman munyi shiru dukkanmu da abinda muke saƙawa a zuchiyarmu. Ni na soma katse shirun ta hanyar cewa. Amman Maman Yasmin Alhaji baisan wacece Hajiya Munubiya ba. Kuma bashi da ilimin sanin ita ke koran mishi mata ko? " Dariya tayi naga idanta cike da ƙwalla sai tsoro ya kamani. "Sabuwa Alhaji ya yadda da Hajiya Munubiya fiye da yadda ya yadda da kanshi. Bana tunanin zai yadda da wata mace irin dai yaddar da yayi mata. Bashi da masaniya akan hali da makircin matarshi. Haka zalika danginshi basu da masaniya akan halinta. Baki sani ba. Macace fa mai haɗarin gaske. Sannan tasan kanta tasan takunta. Aisha ta wahala har bayan rabuwarta da Alhaji Zaidu tayi jinya sosai. Shi dake ya ɗauki yadda ya bata bawan Allah baisan komai ba, gashi da kirki da son taimako wallahi haka danginshi gasu dai da yawa amman suna da haɗin kai son juna da sanin ya kamata. Ai shawarar da zan baki ki yagi dukiya sosai ki zauna da shirinki nayi miki imani da Allah Hajiya Munubiya ba zata bari Alhaji Zaidu ya rayu da wata macen ba sai ita kaɗai." Murmusgi nayi mata cikin ƙarfafa guiwa da miƙa lamurana ga Allah nace mata. Rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya ta mai kaya. Maman Yasmin Hajiya Munubiya ƙila alkadarinta ne zai karye shi yasa Allah ya haɗa Aurena da Alhaji Zaidu. Ƙila suma sauran matan wayo take musu tayi amfani da wayewarta da yawan shekarunta ta ɓarar dasu ko? Ni bazawarace daidai gwargwado ina da ɗan ilimin rayuwa na zauna da kishiyoyi sun kai goma, kuma ko wacce da irin nata makircin take zuwa. Duk da sunci nasara a kaina amman na koyi darasi sun koya mun ilimi, shi wani wuyar rayuwar matattakalar ilimin mutum ne ba tare daya sani ba, gwagwarmaya na taimakon mutum a tafiyarshi musamman in da Allah ya dogara." Murmushi tayi mun tace. "Ya kamata mu shiga Kitchen mu san abinda zamu sarrafa musu suci rana tayi. " Tare muka shiga Kitchen har muka gama girki hira muke yi kuma hirar ta shafi hirar mata da hirar rayuwa bai ɗaya. Sai azahar muka kammala komai. A lokacin su Alhaji sun mana sallama sun tafi masallaci. Ni na jera kayan abincin a ƙasa, ita kuma ta kunna turaren wutanta mai daɗi shima ɗan Saudiyya wanda duk yawanci in mahajjata sunje irinshi suke siyowa yana da farin jini sosai wani mai jan murfi da kwalbarshi irin na basilin ɗin maigurguwa. Saida muka kintsa ko ina kana muka tafi yin Sallah kuma. Mun yi sallah muna zaune muna ci gaba da labari muka jiyo sallamarsu sai muma muka fita. Maman yasmin taci abinci da mijinta a faranti ɗaya. Muma tare muka ci muna hirarmu ƙasa_ ƙasa. Sai kalaman soyayya yake faɗamun. Wallahi ni dashi sai naji ina tausaya mana. Ko yaya zanyi in Hajiya Munubiya ta rabani da farin cikina? Shi ɗinma yaya zaiyi to dan tabbas na yadda yana mun wani irin so marar misaltuwa. "Amman zan dai kaika Hotel ne ka ɗakko kayanku ko? Ai anan ya kamata ku sauka ga waje ko? " Cewar Mijin Maman Yasmin. Dariya Alhaji yayi yace. "Ina za dai mu dinga wuni muku in kuka buƙata amman na riga na biya kuɗin ɗaki na kwana goma kaga ai ba'ayi asararshi ba ko? Maman Yasmin ya Aisha take a gidan mijinta? " "Aisha tana lafiya tama kusan haihuwa ta biyu. Basu daɗe da barin Jidda ba ita da mijin" Dariya yayi yace. "Aisha kenan. Yanzu ta girma kenan. Allah yaima zuriya albarka. Ga Amarya Maman Yasmin ai zaku yi ƙawance ko? Kin ganta bata da ƙawa, sai nine na haɗata ƙawance da Zarah da Anty Khadija" Murmushi Maman Yasmin tayi tace. "To gani nima na zama ƙawarta in sha Allah, zamu dinga waya. Kafin ki bar Jidda ma zamu zagaya ni da ita akwai gidajen Hausawa mazauna nan Jidda duk zamu zaga" Kallona yayi ƙasa _ƙasa yace. "To ke kinji baki ci ta zama ba" Murmushi kawai nayi. Bamu muka bar gidansu Maman Yasmin ba sai wajajen goman dare. Koda mukai wanka muka raya daren, ai saina tashi wajajen ƙarfe ukun dare na tadda Alhaji akan sallaya yanata tulawa. Alwala na ɗauro na fito. "Al sa'ada sallah zaki yi? " Sallah zanyi masta in mana adda'a Allah ya bamu rabo mai albarka da amfani " Murmushi yayi ya shafi fuskata. "Ni ya kamata inja sallar nan" Ai kuwa shi yaja mukai ra'aka goma sai mukai wutiri. Dana saka goshina a ƙasa nake kai ƙaran Hajiya wajen Allah. Bayan mun idar ma na jima inata adda'a. Kafin na haye gado masta ya biyoni. "Ya kamata mu nemi Jidda yanzu ai ko" Ƙoƙarin guduwa nayi ya danneni da ƙirjinshi, dole na bayar da kai, amarci sosai mukaita yi Alhaji ya samu dama sai murzata yake yi kamar tunkuza. Washegari muka sake komawa asibiti jikin dai da sauƙi. Alhaji na roƙa muka je umara. Naita ɗawafi inata roƙon Allah ya bani nasara adda'a yi nake yi babu ƙaƙƙautawa, na tsorata na tsinke, na razana da lamarin Hajiya. Hajiya kuwa ko munje asibiti sai tai ta nuna ta damu dani taita jana da hira tana mun godiya. Harda Haƙuri take bani akan ciwo ya hanani Amarci. Cikin kwana biyar ta warke ras taita roƙon sai dai a koma najeriya ita tagaji mu koma kawai. Ni kuma naita ƙarfafa Alhaji akan a barta ta gama, warkewa tas ni wallahi har bana son mu koma gida, sai in dinga jin wani irin muguwar faɗuwan gaba da zaran ma ance za'a koma gida. Mrs BUKHARI Ayi haƙuri sai jibi Juma'a kuma kunsan jikinne babu daɗi dauriyace kawai nagode.
Son so💪🏼💪🏼 [10/16, 11:26 AM] BADA'AT IBRAHIM: MRS BUKHARI 3
BABANGIDA:.
Ta ɓangaran gidan Babangida abubbuwane suke ta cukumurɗewa babu dai sauƙi sai wanda ba'a rasaba. Ita dai Hamida ta kama sana'a ka'in da na'in duk wani gulma da cece kuce in anayi babu ita a ciki. To inama taga lokaci ita da kullum a cikin dafa zoɓo da tace kunun aya dana zaƙi take, da kwaɓa fulawa. Babangida kuma harkar baban bola ta buɗe mishi sosai harma Allah ya haɗashi da uban gida ɗan China wanda ya jawoshi sosai jikinshi ƙarfi da yaji saida ya mayar dashi kamfaninshi na siyen ƙarafuna. Kuma yana da biranch a Lagos inta kama harda Babangida ake shiga Lagos ɗin domin ya tabbatar kayan sun isa lafiya an Auna an samu komai daidai kamar yadda aka ɗauro. Inda yake siyen kayan Baban bola kuma saiya jawo Aminu harma da Aɗɗa'u ya saka a kan harkar tare da babban yaron da suke aiki tare. Da ƙyar Baba malam ya amince da hakan har saida manya suka tawo daga Ringim suka shiga al'amarin kana Baba malam ya amince ma Aminun tare da sharaɗin Aminu daya soma Jami'a zai bar aikin. Domin gudun kada abin yayi mishi yawa ga koyarwa' ga jagorancin littattafai a makaranta, ga karatu ga sana'ar baban bola. Ta ɓangaren Ƴar Shuwa ta fake sosai akan kasuwanci ta samu dama ire iren damammakin da matan da suke bin mazan banza da Aurensu suke samu. Su fake da sana'a domin su kawar da hankula a kansu. Ta kuwa ci galaba akan Babangida musamman yanzu da bai fiye zama ba sai take cin karenta babu babbaka. Har Bamaina take zuwa ta wuni cur a wajen Sameerah. Zarah kuwa itama tana zuwa daga Abuja ta kama hotel Ƴar Shuwa taita sunturin zuwa ba tare da sanin Babangida ba. Abokan zamanta suna ganinta amman babu wacce ta damu da'ita kowacce harkar gabanta take yi. Suna dai ganin yadda Ƴar shuwa ke tsoma biyar ta wanke goma, ga yawan cin daɗi da bala'in tara mata a ɗaki a wuni ana shewa da sunan sana'a sai in itace da girki sai dab Magrib zata soma kacaniyar gyaran waje da ɗaura girki, dake bata rabo da miyar sutu shaƙe da namomi da kifi kala kala aciki, miyar tuwonma bata fiye rasawaba dan ta sai shinƙimemen frich itama ta zuba su cola cola da su 7up harda su mondin dew na Iyabo Allah sarki iyabo ta Hamma tsuntsun soyayya aminiya a wajen uwani ta Balbalin. Tana ta tara kayan jirajirai masu tsada, ko gwanjon data siya masu tsadane taba ƙawarta ta wanke mata ta goge mata a gidanta. Kayan fitar suna kuwa babu wanda bata ɗinka ta adana a cikin adaka ba. Ɗan kuɗin da Babangida yake basu na kayan haihuwa tana dai karɓane tayi godiya ba dan zasu amfaneta ba. Ta tara kuɗin masu kauri a account ɗinta sanadin Zarah dan Zarah kuɗinta take kashewa sosai akan Ƴar Shuwa. Kamar dai kullum tana zaune a Kitchen ɗinta tana kwashe tuwon shinkafa da miyar agushi data yi taji bushasshen kifi da kayan cikin Saniya. Ga lemunta na gwaiba tayi ta zuba komai a kula taje ta jera a daining ɗaki sai ƙamshi yake yi, su Fati kuma suna zaune ta sakar musu kallon katun suna tayi babu ƙaƙƙautawa. Kulle ƙofarta tayi kirib dan yana daga cikin sabon salon data ɓullo dashi na kulle ƙofa ko da yaushe a cewarta bata son ƙura. Tana zaune akan sallaya idar da sallar nata kenan saita gasa tagumi ta rasa ta ina zata bi diddigin sanin halin da Sabuwa take ciki su gashi yaran basa gidan, ita ba zuwa gidan Baba Malam take yi ba bare ta doki cikin yaran taji wani ƙarin haske. Wata zuchiyar tace. "To amman ai gidan iyayen mijin sanannen gidane me zai hana kije Ranon kai tsaye kawai? Wata zuchiyar tace. " Lambar kishiyarta ko lambar mijinta zaki nema kota halin ƙaƙane" Murmushi tayi tare da gyaɗa kai daidai Babangida ya turo ƙofa da sallama ya shigo yana sauke ajjiyar zuchiya. Da gani a gajiye yake tulus. Da sauri ta miƙe ta karɓi ledar tsarabar dake hannunshi, yara kuma suka shiga yi mishi sannu da dawowa. Saida ya zauna kana yace. "Ki ɗakko faranti ki kididdiba tsarabar ki kaima kowacce ta ɗauki nata dana yara. Akwai kaza biyu ce bansan ya zakiyi rabon ba. " Baki ta taɓe kaɗan tayi murmushi. "To Jannaty angode" Miƙewa tayi ta fita, shi kuma ya bita da idanu yana tuno yaushe rabon da su raya sunna, indai a ɗakinta yake sai dai ya ɗau haƙuri. Da yayi ƙorafi zata ce yanayin wannan cikin data samu ne yasa sunnah ta fice a kanta. Ya zaiyi dole ya yadda da'ita akan hakanne. Dawowa tayi ta yayyaga kajin ta kasafta ta cire musu nasu ita dashi da yara, lemo da ayaban ma duk ta raba ta fice ta soma da ɗakin Hala sai wani taɓe_ taɓen baki na iskanci take tata yi. Har dai tazo ɗakin Sumy ita kam Sumy Amir ne ya leƙo ya karɓa ya shige. Hamida kuwa tana tsaye a gaban firiza tana ba yaro zoɓo yazo siye Ƴar shuwa ta miƙo mata wannan tsaraba. "Angode Allah dai ya ƙara buɗi" Tana dawowa ta tarar Babangida ya haye Daining yana cin abinci. Itama can ta nufa. "Yau kaji yinwa kenan Jannaty? " "Ki bari kawai aikinmu baya bamu damar zama wani sa'in mantawa da kanka kake yi in ba sallah data zama dole ba. To ya gidan ya jiki jikin? " Dariya tayi, shima ya ɗanyi murmushi yace. "Gobe za'a koma asibitin ko? " "Uhm gobe ne, kuma dama inaso zan leƙa gida na kwana biyu ban leƙa ba Mama bata jin daɗi jikinta ɗazu ta kirani take sanar mini" "Assha Ubangiji Allah ya bata lafiya. Zan ɗan baki wani abun ki kai mata. Gobe zan wuce Lagos in Allah ya kaimu a ƙalla zan kwana biyar zuwa shida acan. Sannan akwai yiyuwar wata na gaba zamu China da ogana akwai aiki daya taso a kamfanin ƙarafanshi na can" Haka dai sukaita hira, har lokacin bacci yayi suka kwanta kai da ƙafa dan tunda Ƴar shuwa ta shiga wannan ƙungiya take kwana kai da ƙafa da Babangida a gado. Shi kuma sai yayi amfani da wannan damar a ɗakinta yafi raya dare wajen bautama Ubangiji ta hanyar tsaiwar dare, karatun Qur'ani. Kullum Babangida a cikin yima yara matanshi Adda'a yake akan Allah ya karesu da karewarshi Allah kada yasa abinda yayi ma yaran wasu ayi mishi shima. Washegari ya nufi Lagos ƴar shuwa kuma ta nufi asibiti daga nan ta tafi gidansu acan ta wuni. Mama tayi mata alƙawarin da kanta zata je ta samu aminiyar Hauwa tayi mata kwatancen gidan Sabuwa, za kuma ta karɓo mata number mijin Sabuwan a soma ta waya in bai yiwu ba kuma sai tayi takakkiya. Ai kuwa da farin ciki da annashuwa ta koma gida tana jiran Mama ta kawo mata kyakkyawan labari. (Wato ɗan tsokacin da zanyi anan shine mata mu kula mu kula sosai da irin ƙawayen da zamu riƙe a matsayin abokai. Duk da nasan wata ƙawar baka sanin muguwace ta ƙunshe muguntarta a zuchiyarta a zahiri kuma tana maka dariya in abun murna ya sameka ta nuna ta fiki ma murna, haka zalika inna baƙin cikinne shima ta nuna ta fiki damuwa dashi. Mafita ɗaya shine mu dage muita adda'a muna faɗama Allah cewar ya Allah ga ƙawayena a cikinsu in akwai wacce babu alkhairi a tarayyarmu Allah ka rabamu cikin sauƙi. Nima in akwai wacce shiga rayuwarta da zanyi bazai zame mata alkhairi ba Allah kada ka bani ikon shiga. Allah ka kareni da dukkan abun ƙi, ka azurtani da dukkan alkhairai. Wannan ya wadatar dake na riƙe wannan adda'ar ina ganin haskenta. Wallahi ko ƙawace nayi Sabuwa saina nemi zaɓin Allah a kanta in da Alkhairi sai zuchiyata ta nutsu da'ita in kuwa babu alkhairi sai kuga nama kasa sakin jiki da'ita, ni dama Mijina da yarana sune duniyata gaskiya) Gaga_gaga al'amuran gidan Babangida suka ci gaba da tafiya.