Kenza eBookz

Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 - Chapter 3

Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 - Chapter 3

Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 Chapter 3: Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 Chapter 3. SABUWA:. Kamar kullum muna asibiti tun safe da Hajiya ta…

5,630 words

SABUWA:. Kamar kullum muna asibiti tun safe da Hajiya ta warke gaskiya kuma likitocin sun tabbatar mana da hakan. Ta matsa mu koma gida, duk da shima aiki na najeriya yana jiranshi sai waye waye yake yi da mutane. Wayar Alhaji na karɓa na fita, dama nakanyi hakan ba dan komai ba sai don in basu waje su tattauna zantukansu na mata da miji. Lambar wayar Labbai na soma kira ai kuwa tana ɗagawa na jiyo muryar Maman Shafa da Cicib anata gabzawa. Cicib sai tattafa hannaye yake yi yana zage zage. "Hmm Kina dai ji ko Sabuwa? Ni sai nake ganin Aure kamar bai karɓemu bane. Tun jiya ake ruwan bala'i a cikin gidannan Maman Shafa mitsiyaciya ta hana kowa saƙat. Jiyan saida na kwaɓe muka daku har Shafa saida naima shegen duka wallahi kafin fa suka shiga taitayinsu." To wai duk wannan akan menene Labbai? " "Akan taga ina yin mangyaɗa ana siye, ina yin ƙuli ƙuli, masu kilishi ma Cicib na kai musu tunkuza suna siye shine take tunanin shi ya bani jarin kinji fa musabbabin wannan rigimar da aketa faman yi taƙi ci taƙi cinyewa" Ajjiyar zuchiya na sauke nace. Allah shi kyauta ke dai ki kula da sana'arki kawai. Ya Adama ta saro kayan kuwa? " Na tambayeta dan mu kawar da wancan zancan. "Ta saro kaya harta koma. Wallahi ko da muka yi waya jiya tace anata siye, kuma Hajiya Balaraba ta ƙara mata jari kuma ita ta haɗata da mai aikinta ta rakata kasuwa" Wani farin cikine ya lulluɓeni har ajjiyar zuchiya saida na sauke tsabar jin daɗi nace da'ita. Saura su Aisha da su Rahama so nake suyi Aure tukunna. Yanzu dai in sha Allah gida zan dinga wadatawa da komai tunda Alhaji Zaidu yace zai dinga siya musu hatsi ni sai in dinga basu na cefane kinga yawo in sha Allah ya ƙare in duka sukai Aure sai in basu jari ko wacce ta kafa kanta itama shikenan" Mun jima muna hira kafin na kira gidan nanma aka saka a bayyane mukaita gaisawa harda su Hauwa dasu Raliya da magazin da Sama duk saida muka gaisa. Sama ya roƙeni jari zai zuba furobishon a shagon waje na ƙofar gida na mishi alƙawarin zuwa ƙarshen wata. Su Magazin kuma nace su ɗan ƙara haƙuri shi Magazin zan tuntuɓa ko Alhaji Zaidu ko Hajiya Balaraba in za'a sama mishi aiki dan su ka basu kuɗi kayi aikin banza ba jarin da zasu wani ja ƙarshe ma su cinye a shaye_ shaye. Ina gama waya dasu na kira Maigogul nanma mun jima muna waya ina kashewa na kira wayar Mardiyya duk muka gaggaisa da yaran sai naji sanyi a zuchiyata. Na jima a zaune inata waya kafin daga bisani na koma ciki a nanne Alhaji yake sanar mun zamu koma gida Najeriya nan da jibi. Mun shiga dashi kasuwa mun yo tsaraba sosai gaskiya. Mun je gidansu Maman Yasmin mun musu sallama ta ɗauki lambar ƙanwarta da adireshinta ta bani a takadda, nima na ɗauki lambata na bata a takadda. Ranar talata jirginmu ya dira a kano da daddare misalin ƙarfe bakwai na safe. A mugun gajiye na shige ɓarayina, ga gidan cike da ƴan uwan Hajiya harda ƙawayenta, ni kuma babu nawa ko ɗaya. Ko dana gaishesu sai wani mele bakinsu suke yi ni kuwa nayi shigewata ciki. Sai naga halamun kamar an shigar mun ɗaki tabbas ni dai nasan ba'a buɗe ba bar sib ɗina ba. Tsayawa nayi a gaban sib ɗin sai naga kamar dai ba'a ɗauki komai ba amman ya zamemun dole gobe gobe in duba in tabbatar komai nawa yana nan. Banɗaki na faɗa na saki ruwan ɗumi a jikina idanuna a lumshe inata tunane tunane. Bayan na fito na nemi yadi mai sauƙi na saka na shiga Kitchen na haɗa tea na ɗebi cincin na dawo falo. Zan zauna kenan naji ana buga ɓarayina nasan ba Alhaji bane. Turyan turyan naje na buɗe. Ƙawayen Hajiyane bisa jagorancin Naja'atu ai kun tuno ta mai saka rigar bacci. Da fara'a na tarbesu na juya suka shigo duk suka zazzauna muka sake sabuwar gaisuwa. "Sannu da ƙoƙari Hajiya Munubiyace dama tasa muzo muyi miki godiya bisa jinyarta da kika jajirce kika yi, angode sosai Allah ya bar zumunci ya kuma haɗe kawunanku" Cewar Hajiya Mansa kenan Amiyar ita Hajiya. Ayya ai babu komai abunda yayi Hajiya tabbas shi yayi ni mun riga mun zama ɗaya" Nan dai sukai mun sallama suka fita. Ni wallahi dana gama shan shayi na nayi isha sai nabi lafiyar gado. Wajajen goman dare naji shigowar Alhaji Zaidu. A bakin gado ya zauna yana mun murmushi. "Lallai Wazirat ke baccinki kika yi ma kin mance kece da kwana ne? Kin barni a sama inata juyi?" Murmushi nayi nace. Ai na zaci Hajiya ke da kai tunda ni kaga tare mukaita kwana acan ko?" Fuskata ya shafa yace. "To ita kam Hajiya ta haɗiɗiyi magunguna tayi baccinta tace a soma rabon kwana daga kanki kiyi kwana biyu itama tayi kwana biyu" Jawoshi nayi ya faɗo jikina dan yadda nake jin gajiya bana jin zan iya haurawa sama. Ai kuwa a ɗakina ya kwana, mun sha soyayya sosai na lura Alhaji bashi da wasa ta fannin mu'amala bil haƙƙi yake yi mun. In nayi ƙorafi sai yace bana isarshi ne ai shi yasa. Washegari dai da asuba daya fice na tashi nayi mana abun kari mai sauƙi dankalin turawa da ƙwai na soya sai shayi mai kayan ƙamshi kawai. A samanshi na jera mishi komai na kunna buna na zuba turaren wuta, na jirashi ya shigo muka karya a gurguje yace. "Muna da aiki a ofice da yawa fa. Amman yau ki zauna ƴan Rano sun yi mun waya zasu zo uhm" To shikenan nagode, dan Allah da daddare inka dawo... " Bakina ya rufe da nashi mun ɗau lokaci a haka kafin ya sakeni. "Ba sai kin faɗa ba zamu je wajen Alhaji Baba. gobe in Allah ya kaimu sai muje Dutse mu kaima su Mama tsarabarsu" Ai saina ƙanƙameshi gam. Sai kuwa daya samu nutsuwa dani kafin yayi wanka ya caɓa ado ya fita. Ni kuma na koma ɓarayina na shiga binciken sib ɗina saida na fito da komai na sake jerawa. Ɗankwalin jar atampatane ban gani ba sama da ƙasa. Kuma ko ana jibi zamu tafi tabbas naga ɗankwalin. Ai take hankalina ya tashi ainun. Na gama mayar da komai kenan na jiyo dirin motar Ƴan Rano ko dana leƙa Bus guda suka ciko yaran mata da dattijai. Kaya na sake daga cikin kayan da na tafi dasu dan wallahi kayan sib ɗin duka sai naji ni bamma yadda dasu ba. Fita nayi na samesu a ɓarayin Hajiya anata gaisawa. "Amarya sannu zo ga waje ƴar albarka" Cewar Yaya Tani kenan. Gefenta data nuna mun naje na zauna aka gaggaisa suna ta jinjinamun bisa ƙoƙarina. Hajiya na ƙara basu labarin ƙoƙarin da nayi. Kamar minti talatin da zuwansu na dubi Zarah nace. Zarah muje mu ɗaura sanwa ko? " Yaya Tani tace. "Hauwa aikin me take yi da ke sai kin ɗaura girki. Baki da Ƴar aikine ke a ɓangaren naki? " Murmushi kawai nayi Hajiya tayi carab tace. "Kema kya faɗa har sau biyu na nemo mata masu aiki wallahi wai ita bata so dole na haƙura Alhaji kuma yace tunda bata so a barta" Shiru Yaya Tani tayi can tace. "Ai ba'a haka ita ya kamata ace ta nemo ƴar aikinta da kanta ai bawai kishiya ce zata nemo mata ba. Ko ni nan bazan yadda da hakan ba, ko ɗiyata bazan yadda ayi mata haka ba. Sabuwa ya kamata ko matar Babanki kima magana ta nema miki mai aiki ta ɗan dinga rage miki aiki. Amman abinda zamu ci Hauwa zata sarrafa mana tunda zuwan na Hajiyane kuma a ɓarayinta muka yada zango kada ki damu" Hajiya dariyar yaƙe kawai take yi. Tare da maganganun data tabbatar ta kare kanta sabida gudun zargi. Na fahimci kamar Yaya Tani bata shiri da Hajiyane, ko kuma macace mai faɗa da bata son wargi. Duk da haka saida na ɗaura farfesun kaza guda uku suke nan a firjin cikin awa guda ta dahu dake kajin gidan gonane na juyo musu a ƙatuwar kula na kawo musu. Ai kuwa sunji daɗi sosai. Wuni sukayi ko da zasu tafi na ɗebo sabulai da man Shafawa nace akaima Goggo amfana, ina da ragowar farfesun naman kai na cika kula dashi nace akai mata. Bamu sake haɗuwa da Hajiya ba har saida Alhaji ya dawo, yaci Abinci ya shirya da zamu je duba su Maigogul ne muka je falonta na duba jikin nata tana zaune tana shan fura. "Bari ina zuwa ko? " Ta miƙe ta shiga ciki, sai gata da leda fara ta miƙo mun wai in ba Uzairu zuchiyata. Godiya nayi mata, na fita na ɗan basu waje ko zasu yi magana. Ya kai kamar minti goma haka ya fito ya sameni muka wuce, muna tafe muna hira har muka isa gidan. A falo muka tarar dasu suna cin abinci Uzairu zuchiyata dai baya ciki. Maigogul da sauri ya miƙe ya nufo mu sai murmushi nake yi mishi. "Lolona ashe kuna hanya, dafa nace gobe in zan wuce Dutse zan biyo ta gidan naku mu gaisa ashe kuna hanya Alhaji Zaidu? " Hannu ya miƙa mishi suka gaisa da girmamawa sosai. Sannan muka zube a ƙasan kafet ga tsaraba niƙi niƙi. Mun jima sosai a gidan kafin daga bisani mukai musu sallama suka rakomu har bakin mota. Muma gobe zamu shiga Dutsen in sha Allah" Baki Maigogul ya washe yace. "Allahu Akbar to ai shikenan tazo gidan sauƙi saimu tafi a jere, goben zan biyo ta gidan naku sai mu wuce daga nan" Ni dai banso yace haka ba, amman tunda Alhaji ya amsa yana iya dole na haƙura a hakan. Ko da muka dawo Hajiya ta rufe ɓarayinta sama muka haye muka raya darenmu da farin ciki. Washegari ina gaban akwatina ina haɗa kayan tsaraba Alhaji ya shigo saye da farar shadda yayi kyau sosai. Ya nemi waje ya zauna a bakin gado. Yace dani. "Wani abune ya taso mun wallahi wasu fulotaine gwamnati zata yanka a Kaduna sai yanzu ake sanar mun. Yana da kyau in kasance a wajen sabida zamu samu alkhairi sosai Wazirat ga maganar tafiyarmu Dutse kuma" Zama nayi kusa dashi nace. To ai babu komai inka amince mun ba sai in bi Maigogul mu tafi tare ba in yaso in zai dawo ma dawo tare, in kuma kwana biyu zaiyi kai sai kazo ka ɗaukeni mu dawo ko? " Ajjiyar zuchiya ya sauke yace. "To shikenan hakan ma yayi wazirat. Akwai kayan abinci da tun jiya da daddare nasa aka loda a bayan motar da zamu tafi dashi sai a kwashe ga keyn motar da baƙar zan tafi in kin kwashe ki ba Hajiya keyn." Kuɗi ya zaro a ajjihu masu kauri kashi kashi ya kasafta har Madamcy saida yace ga nata da Rita. Yace kuma zai tura mun wasu a account in ba su Mardiyya" Allah ya saka da alkhairi nagode sosai. Dan Allah inaso zanje gidan kakannin su Mardiyya in dubo su, sabida zan gaishe da Baba Malam kakansu in ka amince amman" Shiru yayi yana kallona can dai ya miƙe tsaye. "To shikenan. Ina fatan ba a gidan Babansu yake ba ko? " A_a ba'a nan yake ba" "To kije ba damuwa, jibi zan zo sai mu dawo in sha Allah. Tunda Kaduna ayau zanje a yau zan dawo inna gama ma Hajiya kwananta sai inzo ko? " Murmushi muka yi ma juna, muka sakko tare na jirashi yaje yayi sallama da Hajiya. Sai ta biyoshi ni a wajen nayi mishi adawo lafiya nayi komawata ciki naci gaba da shiri. Ya tafi bai jima ba sai ga Uzairu zuchiyata da maigogul ina jiyosu suna gaisawa da Hajiya nazo na buɗe musu muka shiga. Ko zama basu yi ba aka shiga buga ƙofa haka na koma naje na buɗe Hauwa ce da kular abinci. Godiya nayi mata na karɓa na shigo. Maigogul ya riƙe bakinshi yana kallon ikon Allah, nima abun mamaki ya bani lamarin Hajiya yana firgitamun lissafina. Ga batun ɗankwalinnan dana rasa wallahi hankalina yayi mugun tashi, gashi zan kuma tafiya in bar gidan bansan meye zai sake biyo baya ba. Allah kaɗai yasan ma mai akayi mun a ɗakin gashi bansan ta inda zan ɓulloma Alhaji da maganar ba. Amman maigogul zan soma faɗama ko zai mun mafita. Ku bani shawara dan Allah wallahi ina cikin tsaka mai wuyar fita. Mrs BUKHARI [10/20, 8:03 AM] BADA'AT IBRAHIM: MRS BUKHARI

4

Wai me zan gani lolo, abinci ta aiko mana dashi almurar? Ohh so take ta asircemu kenan, ko tana nufin mu mayinwatane dan kawai munzo bakya nan ta bamu abinci mun miki kara munci? Ai kuwa wannan abinci saidai ki zabtara ki zuba a leda in zamu fita mu fita dashi ma zubar a hanya, ba zata siyemu da abinci ba, munfi ƙarfinta wallahi tana wasa da nine bata san kura bace tayi lafiya ba" Uzairu zuchiyata dariya harda riƙe ciki. "To ai gaskiya ne Uzze wallahi jikina yana bani tana da muguwar nufaƙa a zuchiyarta sosai. Ki dai bi a hankali wallahi. Lolo nace kin yo ma su kayi nayi ƴar tsaraba kuwa? " E nayo Maigogul zan tafi musu dashi. Alhaji wani abunne ya taso mishi ya tafi Kaduna ku zanbi muje" "Eh ya kirani ya tura mun kuɗin man fetur wallahi. Yanzu abinda za'ayi mu dai mun karya Hajiya ta haɗo mu da soyayyar kaza da fura suna mota shiryo kawai mu kama hanya. " Sama na haura na fito da kayana na kulle uwar ɗakin saida na kalli komai tsab domin in tabbatar da a yaya na bar ɗakina kana na gangaro. Leda na samu na juye rabin farfesun da doya a ciki na ƙulle a leda muka fito. Kulolin na niƙa ma Hauwa harda godiya naima Hajiya data kafa ta tsare a babban falo tana jiran fitowarmu. Maigogul ma harda godiyarshi. Hajiya har gaban mota ta rakomu ta tafi taƙi tafiya dole haka na buɗe bayan motar Alhaji Uzairu zuchiyata ya ɗebe kayan abincin ya dawo dashi bayan motar Maigogul duk Hajiya na tsaye. Keyn motar na miƙa mata mukai mata sallama. Har motarmu ta fice a gidan Hajiya na tsaye a wajen. Muna tafe Maigogul da Uzairu zuchiyata suna ta hirarsu suna dariya ni kuma nayi shiru inata tunanin rayuwata da irin kishiyar da kuma Allah ya jarabceni da'ita. "Lolo na lura tunda muka kamo hanya kike karanta wasiƙar jaki. Shin menene matsalarki? Kada kiyi sake ki rasa Aurenki Hajiya tayi miki wani abunne kome? " Ajjiyar zuchiya na sauke na zayyanama Maigogul komai da komai da yadda muka yi da Maman Yasmin, da ɗankwalina dana rasa dan wallahi abun ya dameni sosai hankalina baya jikina akan wannan ɗankwali. Hawaye na share na sauke kaina ƙasa inajin wani irin ɗaci. "Tabb kikace me lolo. Itace ke koran matanshi fa kikace. Ita Aishan da aka baki lambarta kin nemeta ne? " Maigogul sai zazzare idanu yake yi. A_a ban kirata ba tukunna. Bansan me zance mai bane ya barni inje Abuja ba shiyasa" Ai sai Maigogul ya faka mota a kan titi tunda a lokacin muna daf da shiga dutse ne. "Lolo kwana nawa ya baki kiyi a Dutse? " Kwana biyu yace jibi zai zo mu tafi tare" "To ya zama dole muje in kai ki Abuja. Ni da kaina zan kirashi in roƙeshi zaku rakani ke da Uzairu zuchiyata muje mu dawo a goben inta kama ma sai mu tafi tun biyar na asuba mayi sallar asuba a hanya sabida mu samu mu dawo a goben, nine kaɗai zan iya tsaya miki a duk abinda ya shige miki wallahi wallahi ta Allah bata Hajiya ba. Ke kayan tsubbuna fa ba zubarwa nayi ba. Kuma ina da tulin tarin abokai masu tsubbu wasu da rauhanai ma suke aiki fa afa bini a hankali. Lolo kada kiyi sake da adda'a kuma kita tsayuwar dare. Ke da izinin Allah asirinta saiya tonu. Ki mayar da hankalinki kan aikinki kuma ki dena shiga ɓarayinta in ta fito ki leƙo ku gaisa, ke inma zaki shiga ki tabbatar tare dashi zaku je kudun kada ta sheƙa miki wani abun. Sannan batun ɗankwalin data turo aka ɗauka bazai wuce ƴar aikinta ta saka wannan aikin ba. In kika dage da adda'a shikenan. Zan rakaki wajen Baba Malam muyi mishi bayani ko da taimakon da zai bamu ta Allah ba tata ba. Lallai Lolo dole kiyi shiru ki kasa magana, domin zama da makiran mata abune da bashi da sauƙi. Kada ki sake ki faɗama kayi nayi halin da kike ciki dan terere zata yi miki kinsanta ba'a abun arziki da'ita sam." Ajjiyar zuchiya na sauke. Ni kaina dama nayi niyyar in tunkari Baba Malam da lamarin nasan zai taimaka mun sosai. Motarmu muka ja muka shiga garin Dutse. Sai gamu a layinmu a ƙofar gida. Magazin na zaune a benci a ƙofar gidan yana ta busa hayaƙi ya hangomu ba shiri ya wangale get Maigogul ya shiga da motar har cikin gida. Su Rahama duk suna tsakar gida, da ƴan ɗakin Hauwa. Ganinane yasa su Rahama duk suka miƙe suka tawo bakin motar. "Ahh mutanen Jidda kece a tafe tare dasu Maigogul mu muna shirin zuwa miki ashe ke zaki zo mana" Cewar Rahama data buɗe mun murfin motar na fito. Layuza ta dubeni sama da ƙasa sai ciwon hassadarta ya motsa. Wallahi kinganni na biyosu in zo in ganku. Ina Rakiya fa? " "Kayi nayi ai tun sassafe ta fice da buhu kema fa kin sani. Madamcy kuma sun tafi Asibiti da Sadiya da Hauwa Haihuwarce" Maigogul ya fito yace. "Wato kayi nayi koda nace mata zanzo yau shine ta tafi kayi nayinta ko? Ai shikenan Lolo muje sama ki huta kinji" Shigewarshi yayi yana saɓa malum _malum, ko da Layuza tace mishi sannu da zuwa hannu kawai ya ɗaga mata baiko kalleta ba. Muka bi bayanshi yuu. Magazin kuma aka barshu da tiri tirin fito da kayan abinci tare da haurowa dasu sama. "Lolo ashe kun dawo daga jiddan ya jikin kishiyar taki kuwa?" Cewar Raliya" Wallahi mun dawo Raliya jikinta da sauƙi sosai " Sama muka haura da kayayyakin tsarabobin dana yo musu. A falo muka zube nan muka shiga ɓarin zancen yaushe gamo anata dariya da musu. "Ke Lolo Sadiya ta faɗa miki kuwa madubala yazo gidannan har kusan sau uku ma? " Ras naji gabana ya faɗi na dubi Magazin daya dure buhun shinkafa nace. Magazin takashin labari bani to in sha" "Wallahi kawai ranar farko ne yazo da ledarshi shake fal da kayan shayi ya kawo ma Rakiya fa. Shine tace mai ko zai Auri Aisha ko Sadiya tunda ke kinyi Aure. To shine bayan yayi zuwa na biyun Rakiya ta sake taranshi da maganar dai. To zuwa na uku wajenta yazo sukaita hira a ƙofar gida in faɗa miki, amman fa yace tayi haƙuri bazai iya Aurenta ba kinji yadda akayi fa." Murmushi nayi kawai na girgiza kai. A raina nace. Allah sarki madubala Ubangiji Allah ya ɓullo maka da wacce zaka so ta fiye da yadda muka kasance a baya. Muna cikin hirarmu Hauwa tayi kiran waya Madamcy ta haifi ɗiya mace suna asibiti babu yadda take hawan jini ya rabketa. Gaza dai ya turo dubu goma gashi sun ƙare tas. Rahama ce ta miƙe tace. "Ku harhaɗo maza inje asibitin Uzairu zuchiyata ɗan Hajiya ko kai zaka ɗauki nauyin komai? " Ta faɗa da zolaya. "Rai dai Rahama ke dai bari in auri Felisha zaku sha mamaki nifa kuɗaɗe zanta turowa ina siyan gidaje wallahi sabida ko ta sakeni na fita da fitata dan ba mutunci bane dasu akwai wani abokina da yake Auren Baturiya wallahi da muke hira yake faɗa mun kullum a cikin faɗa suke da kai ƙararshi kotu, muna kan wayarma ta fisge saida taji muryata shine ta sauke ajjiyar zuchiya" Dariya muka tuntsire dashi dukkanmu Bana Uzairu zuchiyata yayi abun kai har nera dubu biyar ya bayar ni kuma na bada dubu ashirin Rahama ta saka kai ta tafi. Saida nayi sallah kana na rarrabe tsarabar dana kawo lokacin Maigogul ya fito yana falon yana waya da Hajiyarshi sai kashe murya yake yi yadda kuka san tsohuwar karuwa. Har su Layuza saida na musu tsarabarsu nasa Aisha ta kai musu, sai ga Raliya ta hauro godiya. Ni dai ina yin sallar la'asar na sake kaya na fito shar dani tare da tsarabar su Mardiyya da Baba Malam. Har zuwa wannan lokacin Rakiya bata dawo ba su Aisha suna Kitchen zasu ɗaura abinci. Dubu biyar na basu nace a siyo kaza ƙatuwa a fasheta a cikin jallof ɗin. Maigogul ya tusani gaba sai gamu a ƙofar gidansu Babangida almajirai cike anata karatu Baba Malam na zaune akan kujerarshi ya hangomu mun nufoshi. "Sabuwa Maigogul kune a tafe? Lallai yau ina da manyan baƙi. Kai magajin malam shiga zaure na uku ka shinfiɗa mana keso maza" Ai kuwa sai Malam ya miƙe yayi gaba muka bishi har zaure na uku. Ins hango zuwanmu gidan na farko lokacin ina ɗauke da cikin mardiyya a wannan zauren muka zauna. Rayuwa kayan Allah komai mai wucewane ada inna doso zaurukan gidannan sai inji tashin hankali dan nasan dole in shiga in tarar da ɗiban albarka da rashin mutunci iri _iri daga Malama Babba. Amman yau gani a gaban Baba Malam hankali kwance. Bayan mun gaisa sai nayi shiru shi kuma Maigogul sai ya zayyanama malam Halin da nake ciki. Ya ɗaura da cewa. "Ni da naso in mata kiranyen aljanu ma. To amma wallahi na tuba kawalcinma bana yi sam sa'ar da taci kenan wallahi Malam, itama Sabuwan nasan ba zata bani haɗin kai ba shi yasa ma. "Ashsha banji daɗi ba. Haƙiƙa zama da irin sheɗanun matannan akwai haɗari sosai. Amman babu komai zan mata rubutu gobe Babangida da yaran sai su kawo mata, ki dinga sha kina shafe jikinki in sha Allahu babu abinda zata miki yayi tasiri. Sannan ni da su Aminu zamu yi sauka mu miki adda'a sosai. Ai maganar turen aljanu shirkace Maogogul na kuma ji daɗi sosai da kace ka tuba. Abinda ya kamata shine mai zai hana da kai da iyalai ku shiga makarantar magidanta ku yi karatu abubuwan zasu kuma sauƙi sosai " Maigogil yace. "Dake ina da iyali kasan acan Kano Dutse shigowa nake yi duk sati in koma. Su dai sai su shiga makarantar. Baba Malam izifi talatin cib akwaishi a kaina kuma na iya baƙi aikine dai dashi ba'ayi kuma babu sanin fassara bare mutum yasan ma'anar" Ya ƙarashe yana wannan dariyar ta baƙin ciki. "To ai ta kwana a gidan sauƙi in sau ɗaya zaka zauna a aji, ko majalisin karatu zaka ƙaru sosai. A Kano ga manyan malamai suna karatuttuka da littattafai in kana so sai in haɗaka da gadon ƙaya ko Dr Sani rijiyar lemo ka dinga zuwa majilisi kana sauraren karatu. Kuma in ka shigo Dutsen ma zaka iya shigowa tamu makarantar a hakan ka dinga ɗaukar darasi da tuban zaifi tafiya da kyau yadda za'a bautama Allah bil haƙƙi." "To shikenan zan dinga zuwa makarantar in na shigo. Suma su kayi nayi zan musu tayi in suna so ai sai su dinga zuwa wallahi mun gode Baba malam sosai" "Maigogul ina abokinka Cicib? " Dariya suka yi du su biyun ni kuma nayi murmushi. "Ki soma shiga ciki Sabuwa ku gaisa da Ƙarama sai ki fito mu shiga makaranta kiga yaran naki" To shikenan. Ga tsaraba na kawo maka" Na ajjiye ledar na shiga cikin gidan da tsarabar yara dana Malama Ƙarama. Tayi mamakin ganina sosai kuma da fara'a sosai muka gaisa na bata tata tsarabar na fito. Bisa jagorancin Baba Malam muka shiga makarantar anata ɗaukan darasi A ƙofar ajin su Mardiyya muka tsaya, tana tsaye tana koyarwa abun sha'awa tana hangomu ta fito da sauri ta rugunƙume maigogul sunata dariya. "Ƴar nema" Cewar Maigogul, murmushi Malam yayi yana kallon mardiyya. Malama da Aɗɗa'u suna aji suka hangomu ai da gudu suka iso inda muke. Duk muka ɗunguma zuwa ofishin Aminu Yana zaune yana ba wata matar Aure littafin arba'una hadith muka shigo Baki ya rufe ga murmushi ga hawaye a fuskarshi. "Ja'iri ƙaraso mana" Cewar Maigogul yana wannan dai dariya da kuka santa ƙarasowa yayi ya riƙe hannuna. "Ummi kece kika zo mana. Yaushe kika dawo?" Shafar kanshi nayi. Nice Aminu ya karatu? " Murmushi yayi ya dubi ƙannenshi suma suna cike da farin ciki. "Adda dama kinsan Ummi zata zo shine baki faɗa mana ba? " Mardiyya tace da Aminu. "Bata faɗamun ba nima ganinta kawai nayi" Ofishin Baba Malam muka shiga acan mukayi hirarmu na basu tsarabarsu na ƙirgo kuɗi na basu nace su sai wani Abun. "Ummi bikin Adda amman dake za'ayi komai ko dan Allah? " Dani za'ayi Aɗɗa'u zan zo tun saura kwana biyu soma bikin in sha Allah" Ai sai farin ciki ya lulluɓesu. Baba malam yana kan teburinshi yana rubutamun addu'o'i a jikin takadda da zamu tafi ya miƙo mun. Nan mukai sallama dasu muka tafi akan gobe yara zasu kawo mun rubutun. Muna hanya Alhaji ya korawoni mun jima sosai muna waya. Mun isa gida mun tarar kayi nayi ta dawo suna ta cin abinci dake magriba har tayi lokacin Saida nayi sallah nazo muka gaisa da kayi nayi. Su madamcy kuwa har lokacin suna asibiti Gaza ma yazo yana can asibitin tare dasu. Da daddare ma mun kai kusan minti talatin muna waya da Alhaji kafin ya kashe wayarshi yace ga Hajiya nan ta hauro sama. Kuma Maigogul ya sanar dashi gobe zan karashi Abuja wajen Iyalan Amininshi ya amince mun inje. Ajjiyar zuchiya na sauke Ai kuwa washegari asussuba ni da maigogul da Uzairu zuchiyata muka fito da zummar nufar Abuja. "Wai maigogul me akeyi to a Abujan da zaka kwashi yara ku tafi. Ke Lolo wai meke faruwane nace miki? Ka mayar da ƴaƴan cikin ka abokan yawonka ko ina dan masifa kuna tare wannan dai abu da zafi yake" Babu komai Rakiya ai yau zamu dawo" Tsaki tayi tace. "Allah ya tsare in kun so ma daga can ku wuce Kano ai Allah yana ganin irin zaluncin da maigogul yake yi mana. Ku kuma bamu bane a gabanku barinma Uzairu zuchiyata sallamammen banza. " Maigogul zaiyi magana nace. Dan Allah maigogul kayi shiru. Rakiya dan Allah ki dinga sanyaya ranki. Wallahi ba wani abun muke ƙullawa ba kawai gidan wata zamuje su rakiya kawai zasu yi mun" "Au ta huɗu kuka samo mishi? Ai kuwa na rantse miki da Allah in ya ƙaro wani Auren duniya zan shige uban kowa ya huta." Wallahi dukkanmu saida muka dara "Rakiya kenan makirar mace. Allah ya shiryeki mu sai mun dawo. Kuma yau zamu dawo sai ki shirya tarbata ai kamar yadda Hajiya Balataba take mun ta soya kaji da basmati tana jirana. Ke kuwa koda na faɗa miki ina hanya bai hanaki zaran buhu ba." Motarshi ya ja Sama ya buɗe mana get muka fice. Sai a hanya muka dakata mukai sallah muka naushi hanya awanmu bakwai tafiya yankin Azaba. "Bani takaddar adireshin in gani, dan babu inda ban sani ba a garin Abuja. " Jakata na zaro na ciro takaddar na nuna mishi ya riƙe baki. "Wuu anguwar manyan kenan. To ki kirata kafin muje a sakar mana kare" Uzairu zuchiyata da yake ta waya ai sai dariya. "Wallahi akwai gidan da muka taɓa kai wasu mata anan Abuja ashe karene mai gadin gidan. Muna tura get karennan ya taso mana gudun kilomita nawa kunsan muka yi? Cicib dai har takalmi da Ɗankwalinshi sai da ya yar. Munci wuya" Munyi dariya kamar zamu mutu Uzairu zuchiyata faɗi yake. "Wayyo cikina zan mutu. Ƙyal ƙyal ƙyal ƙyal" Mun jima muna dariya wallahi, baza ku gane ba ina mugun son ahalina koba komai za'ayi dariya ayi raha. Kiran Aisha nayi ringin biyu kuwa ta ɗauka da sallamarta. Gabatar mata da kaina nayi sannan nayi mata bayanin gani a Abuja ma inaso inzo gidanta. Ai kuwa ko a muryarta ta nuna jin daɗinta sosai ta sake yi mun kwatance duk da nace mata Maman yasmin ta bani adireshinta. Cikin minti arba'in sai gamu a ƙofar gidanta. Waya nayi mata tasa maigadi ya buɗe mana get muka shiga ciki. Tana tsaye da ƙaton cikinta a gaba fara kyakkyawar mace mai gashi sosai. Da fara'arta ta ƙaraso. "Ahh har da su Baba kuke. Sannunku da zuwa. Baba mu shiga ciki maraba" Tare duk muka ɗunguma zuwa falon gidan wanda yaci kuɗi daidai gwargwado. Zama muka yi aka sake dasa sabuwar gaisuwa kafin kuma falon yayi shiru. Mai aikice ta shigo da kular abinci da komai a ƙaton faranti ta ajjiye a gabanmu tare da gaishemu cike da ladabi duk da dattijuwace. Miƙewa tayi da ƙyar tace. "Bari in baku waje kuci abinci ko" Ta saka kai ta bi wata ƙofar. Abincin na zuba mana jalof ɗin kuskus ne da soyayyen kaza na cikin jajjagen yaji sai lemukan sha. Maigogul na soma zuba ma, ni da Uzairu zuchiyata kuma na zuba mana tare ni dai duk hankalina ma baya jikina wallahi komai ma dauriya da ƙarfin hali nake yi. Abincin kanshi loma uku kawai nayi na ajjiye lokalin nayi shiru ina sauraren yadda gabana ke ta aikin dokawa. "Lolo mu kam zamu je mu dawo kafin ki gama abinda ya kawoki zan leƙa abokaina. Duk abinda ya kamata kuma ya dace ki sani kada ki mance ki nutsu ki tambayeta da kyau. Taso muje Uzzy" Sallama sukaimun suka wuce. Suna fita Aisha ta shigo da fara'arta. "Su Baba sun tafi ne? " E kusan hakan zance yace inna gama in kirashi sai mu tafi dake yau zamu koma Dutse" "Ayya. To mu shiga kiyi sallah tukunna dan labarin gaskiya da tsayi in dai labarin Hajiya Munubiyane" Binta nayi har zuwa ɗakin baccinta mai kyau komai na cikin ɗakin ruwan hoda da ruwan maimo. Banɗaki ta nuna mun na shiga na ɗauro alwala na fito ta nuna mun gabas nayi sallah. Na jima sosai akan sallaya inata adda'a na shafa kana na fuskanci Aisha. Na idar ke kawai nake saurare Aisha akwai magana a bakinki sosai Maman Yasmin ta faɗa mun" "Ƙwarai akwai magana a bakina Sabuwa. Kin ganni nan? Bala'i ido da ido babu wanda ban gani ba. Dan ko da Alhaji ya sakeni nafi shekara guda ina jinya in faɗa miki zan iya kaiwa shekara biyu ma Amman me kike son sani akan Munubiya? " Jikina ya sake mutuwa mus ajjiyar zuchiya na ja na sauke da tauri. Inason sanin wacce hanyar tabi ta koreki a gidan Alhaji Zaidu. Sannan da wanne salon tayi amfani har taci galaba a kanki? " Dariya tayi mun ta muskuta ta gyara zamanta. "Bani kaɗai ba ko Sumayya haka tayi mata ta koreta." Idanu na zare nace. Ke ya soma Aura kafin Sumayya ko ita ya soma Aura? " "Ita ya soma Aura. Itama yanzu haka tana Abujannan tana Aure a zone 2 muna zumunci dan ko da nayi haihuwar fari da'ita akayi komai" Dafa cinyarta nayi nace. Aisha ko zaki taimakeni muje gidan Sumayya mu haɗu mu tattauna baki ɗaya in babu damuwa? " Miƙewa tayi ta buɗe cib ɗinta ta ɗakko mayafinta da jakarta. "Muje babu wata matsala. Domin Sumayya matsalar data shiga ai tafi tawa yawa." Miƙewa nayi babu guiwa wallahi illahirin jikina sai naji rawa yake yi. Illar rashin bincike a Aure kenan haƙiƙa ƙila da anyi bincike da za'a iya gano halin Hajiya munubiya duk da hatsabibiyace sosai. Amman ni kaina baƙin tarihin rayuwar ahalina yasa bamu damu da yin binciken Alhaji Zaidu ba. Domun yayi ƙoƙari namijin ƙoƙari da ya gama jin tarihina kuma ya aureni a hakan ba tare da nuna mun ƙyama ba sai tsagwaron so. Dafani Aisha tayi na dawo hayyacina. "Muje ko? " Mai gidanki baki kirashi ba ko babu matsala? " "Ya yarje mun inje duk inda zani, ba matsala" Fitowa muka yi ni dai jan ƙafata kawai nake yi sai naji ƙafata ta hannun hagu kamar ta samu matsala tayi nauyi sosai janta nake yi bana iya ɗagawa. Ƴar aikinta ta sanarma mun fita ta kula da yarinya tana ɗakinta tana bacci. A hankali ta dinga tuƙin ga ciki him a gaba. Muna hanya ta kira Sumayya ta tambayeta ko tana gida. "Ina gida Sista Aisha zaki zo ne? " "Eh muna hanya tare da baƙuwa sai munzo to" Wayar ta kashe ta dubeni tace. "Mun taki Sa'a tana gida" Yaƙe kawai nayi mata. Muna tafe har muka iso get ɗin gidan Sumayya gidajene na sama sama guda shida a tsaye sai babban get kewaye da katanta. Ga motoci birjik a cikin haraba. Muma ajjiye tamu muka yi muka nufi gidan Sumayya Allah yasa a ƙasa take ba a sama ba. Kwankwaasa ƙofar Aisha tayi mai aiki tazo ta buɗe mana muka shiga. Gaskiya ana faluka a gidajen masu dashi dake ni ban saba da ganin irin haka ba nadai saba da falukan faƙarahu alal lalurati ƴaƴan malam Shehu irinmu" Ruwa aka kawo mana sai ga Sumayya ta ɓullo ta wajen Daining da dukkan Halamu Kitchen ne a wajen. "Aisha sannunku da zuwa. Baƙuwa maraba lalenku" Gaggaisawa muka yi Aisha ta gabatar mata dani da abinda kuma ke tafe dani. Kallona ta shiga yi tana jijjiga kanta ta jima a haka hawaye suka zubo mata a kumatunta. Kalmarta ta farko itace. "Sabuwa in kina son lafiyarki da rayuwarki ki rabu da Alhaji Zaidu cikin ruwan sanyi wallahi. In kika ƙi ƙila ƴan uwanki ne zasu fitar dake cikin halin jinya. Dan na rantse miki da Allah Hajiya munubiya ba rabaku kawai zata yi ba saita tabbatar ta nakassa rayuwarki" Kunji ƙudurar Allah ko? Ga ƙafata sai sake nauyi ma take yi Mrs BUKHARI Mu tara gobe in Allah ya kaimu [10/21, 9:08 AM] BADA'AT IBRAHIM: https://chat.whatsapp.com/IUKFTeul76p2VaAvQ5nk0U?mode=wwc

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull