Kenza eBookz

Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 - Chapter 4

Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 - Chapter 4

Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 Chapter 4: Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 Chapter 4. MRS BUKHARI 5

4,421 words

MRS BUKHARI 5

TASKAR BADI'T

WANNAN SHINE JADAWALIN SHIRYE SHIRYENMU DA WANNAN TASKAR TAKE GABATARWA YAYIN DA BA'A LITTAFI DOMIN ƘARUWARMU BAKI ƊAYA MU GUDU TARE MU TSIRA TARE.

MASU SON KASANCEWA TARE DA MRS BUKHARI GAREKU GA LINK NAN DUK MAISON KASANCEWA MEMBER SAI YA SHIGA A DAMA DASHI IN SHA ALLAH. ANA ƘARUWA MUNA FAƊAKARWA DOMIN AN HAƊA MALAMAI DATTIJAI WAƊANDA SUKA SAN DARAJAR MUTANE SUKA SAN ME SUKE YI. DUK DA ZAMU SABUNTA SHIRYE_SHIRYEN NAMU IN SHA ALLAH KU KASANCE TARE DANI A KULLUM

RANAR MONDAY 8:00 PM A GAMA 9:30PM

Shirin """"TARBIYYAR YARANMU"""

MASU GABATARWA ( MAMAN KHAIRY) (ANTY BADI'AT) (KHADIJA MAI DOKI) (ANTY ZEE) RANAR TALATA 8:00AP A GAMA 9:30PM

shirin """"AMFANIN TSABTA GA MACE"""

MASU GABATARWA (MRS BASH) (MRS BUKHARI) (MAMAN KHAIRY)

RANAR LARABA 4:00PM A GAMA 6:00PM

Shirin """TAURARUWAR MAKO"""" SHIRIN DA ZAI DINGA ZAƘULO MANA MATA DOMIN SU BAMU TARIHIN GWAGWARMAYARSU A GIDAN AURE.

MASU GABATARWA (HAJARA ALIYU) (OUM INTEESAR) (MAMAN SAFWAN)

RANAR ALHAMIS 8:00PM A GAMA 9:300

Shirin """MATSALOLIN MATA DA WARAKA"""" SHIRIN DA ZAI DINGA ƊAUKO MAUDU'I YANA TATTAUNAWA AKAI. MUSAMMAN MATSALOLIN DA SUKA ADDABI MATA. SANNAN ZA A DINGA KARANTA TAKADDUN MASU TURO MATSALA, DA BASU SHAWARI ME KYAU""""

MASU GABATARWA (Ummu Inteesar) (Mum khairy) (MRS BUKHARI)

RANAR JUMA'A 12: 00PM A GAMA 2:00PM

Shirin """"ADO DA KWALLIYA""" MASU GABATARWA (KKhadija maidoki) (Mrs BUKHARI)

RANAKUN ASABAR DA LAHADI KUMA RANAKUN HUTU IN SHA ALLAH. DOMIN KULAWA DA ME GUDA DA YARAN GIDA BAKI ƊAYA.

Kina tunanin tafi ƙarfin Allah ne in mu duk tafi ƙarfinmu? Ko tunaninki babu ranar da alkadarinta ita zai karye? Sumayya soma bani labarin zamanki da Hajiya munubiya dan Allah. Baku ji yadda zuchiyata take daka ba." "Hmmm Sabuwa kenan bana nufin Hajiya tafi ƙarfin Allah ya hukuntata wane mutum inji mutuwa. Ni zuwan Alhaji Zaidu wajena na farkone kaɗai bata sani ba. Zuwa na biyu tace mishi in yazo ya kirawoni a waya zamu gaisa. Da yazo kuwa yayi kiranta ya bani wayar muka gaisa cikin girma da arziki da mutunci sosai. Tun daga wannan lokacin muke waya da Hajiya sosai, in taƙaice miki harda mamanmu suna waya a gaisa. A dangi ana mamakin kirki da rashin kishi irin na Hajiya, da yawan dangi suna ganin nayi sa'ar da bako ke samu ba. Ƙalilan daga dangine suka kasa nutsuwa da kirkinta a cewarsu kirkin ya wuce misali, kuma ba'a san kishiya a haka ba a ko wanne ƙabila. A haka aka saka bikina da Alhaji Zaidu ta kirawoni tayi mun murna. Washegarin ranar da aka saka bikina muka wayi gari da mutuwar mahaifinmu ciwon ciki na faraɗ ɗaya ne yayi ajalinshi. Sabuwa da Hajiya munubiya akayi zaman bakwai, kuma a cikin kwana bakwai ɗinnan abinci take yowa mai yawa da kaji ta tawo dashi. Ranar sadakan uku da sadakan bakwai tayo abinci dasu masa na sadaka mai yawan gaske. Ta shiga dangina na nesa dana kusa duk aka santa suka gamsu babu ƙullin komai a zuchiyarta face alkhairi. Hmmm ashe ungulu da kan zabo ce bamu sani ba. Ita ta haɗamun lefe Alhaji ya bata kuɗin akwatuna biyar ta ƙara mun biyu suka zama bakwai. Da ita akayi shagalin biki muna manne da juna nazo na tare. Hmmmm daga lokacin ƙaddarata ta soma. Hajiya ta kawo mun mai aiki tace zata dinga biyanta duk wata na karɓa inata murna. Hajiya ta shigeni sosai bani da sirri har a kan gadona take zama tana yawan kawo mun magungunan mata masu kyau tace ta siyo mun ne. Hmmm in taƙaice miki sai da nazo nafi ba Hajiya mahimmanci fiye da shi maigidan dan cewa tayi in dena sakar mishi jiki a turaka tsofar dani zaiyi a banza, ita sai tayi wata guda ma ba sui mu'amalar Aure ba. Wallahi Sabuwa na biye mata kullum mu kenan a cikin rikici da Alhaji Zaidu, yadda kika san tayi mun allura haka taita juyani son ranta. Gashi duk abinda muka yi sai tace in bata labari haka zan zauna in labarta mata komai tsab. Watana uku a gidan ranar wata Juma'a na soma jinin Al'ada kamar wasa yau zan gama gobe ne, a_a jibi ne. Jini yaƙi tsayawa kuma zuba yake yi sosai in faɗa miki. Alhaji Zaidu da Hajiya sukaita sunturin kaini asibiti. Wallahi Sabuwa Hajiya da kanta ita da Mamanmu muke sunturin neman magani jini baya tsayawa. Takai ta kawo sai Hajiya ta kwantar ta tayar dani, jini fa ba wai irin na wasa ba. Yadda zaki san asirine da duk jinin da nake zubarwa a asibiti basu taɓa cewa jinina yayi ƙasa ba bare ya ƙare a saka mun wani. Tom Alhaji Zaidu baifa gazaba jarumine sosai ya nuna damuwarshi sosai akan ciwona. Saida na shekara tim kafin wata rana kwatsam jinin ya tsaya da kanshi a hankali jikina ya shiga yin sauƙi Hajiya da Alhaji sukaita Murna, lokacin har india aka kaini wani babban asibiti, har a injin sukutum ɗina aka sakani domin asan menene matsalar, hmm basa ganin komai. Ita da kanta ta buƙaci muje umara. Muka je muka dawo tasa Alhaji ya buɗe mun shago ita ta zaɓa mun in dinga siyar da kayan jirajirai kuma ita aka ba kwangilar gyaran shagon da zuba komai. Kasuwa ta soma tafiya kaɗan_ kaɗan A hankali naji Alhaji Zaidu na siremun inajin tsanarshi. Har Hajiya ta sani shima tun ina ɓoye mishi har ya sani. Mukaita rikici dashi dai daga ƙarshe na tubure saiya sakeni bazan iya zama da juyi ba, tun danginshi basu sani ba har suka sani. Suma fa saida na zagesu tas kuma nace sai an sakeni. Kinga da wannan ai ba zasu zargi Hajiya ba sun ɗauka kawai bani da kirkine dai. A lokacin ko bacci bana iyayi kaina kullum ciwo jikina ma haka, ga jini ya dawo mun ƙaƙas. Da na tusa kuka da tambotsai dole ya sakeni na koma gida. Ba sai ciwo ya taso mun ba sai an kwantar dani sai an tayar dani. Gidajen magungunan gargajiya kam mun zagaye Kano da kewayenta kab babu sauƙi. Tun muna yi har muka haƙura muka zuba ma sarautar Allah ido gashi sai ƙarewa nake yi. Na sha wuya sosai wallahi har gobe wani sa'in inna soma jini sai in yi wata guda inayi har yanzu ban warke duka ba abun yana jikina bai karye duka ba, ƙila dashi zan mutu ma. Kinji abinda ya faru ko? " Illahirin jikina babu inda baiyi sanyi ba, kuma babu inda baya rawa. Wannan tashin hankali da yawa yake. Lallai ina wasa da wuta ban sani ba. Lallai bazan iya da Hajiya ba. A irin gidanmu inna kwanta jinya wazai iya ɗawainiya dani haka kamar yadda iyayen Sumayya sukai tsayuwar daka a kanta. Ya Allah gani gareka ya Allah kaine gatana Ubangiji Allah na dogara dakai kaimun faɗan da kanka. Aisha tace. "Bambancin labarin Sumayya da nawa ɗayane zuwa biyu. Na farko ni ba jini aka saukarmun ba. Ɗankwalina tasa mai aikin data kawo mun ta ɗauka ta kai mata. Bazan mance ba tun ranar dana saka kayan ban sake samun zaman lafiya a gidan ba. Nice zabura firgici kaina kamar ya kunce. Hankalin dangina ya tashi ainun akaita sunturin asibiti sai likitoci suce lafiyata ƙalau ni kuma ni kaɗai nasan me nake ji. Ga Hajiya bata bada wata ƙofa da za'a zargeta ba sam tayi iya yinta a kaina. Bambanci na biyu ni shagon kayan Kitchen tasa aka buɗe mun ƙaninta na zama a shagon wani sa'in kuma ina ɗan leƙawa nima. Nima ta zugani sosai akan da ƙuruciyata zan zauna ba haihuwa shikenan na kashe rayuwata. Tun abun baya damuna na soma ɗaukar zugarta gashi dama gidan ya isheni ni bana samun nutsuwa da kwanciyar hankali har sai na fita a gidan Da zaran na dawo zanji ƙwaƙwalwata na tafasa wallahi ba zata taɓa denawa ba har saina kuma fita. Ya zamana kullum nike nan a cikin gantalin fita nake dana gaji nace ya sakeni bazan iya zama dashi ba. Haka ya sakeni, na koma gida. Ban dena jin faɗuwar gaba da razini ba har saida na kusan shekara guda ana ta jinyata. Na miki tsallake nima ita ta kawo mun Ƴar aiki ɓarayina da idanuna na kama mai aikin tana barbaɗa magani a abincin dana dafa ma Alhaji. Kunsan Allah hatta ƴar aikina saida ta kai ta kawo tsoronta nake ji. Tazo ta dena aikin ma sai dai ni inyi abuna da kaina, kuma bana iya mata faɗa har suturuna take sakawa ta sace mun kaya, ta sace mun kuɗaɗena. Gwal ɗin kayan Aurena kuwa ban tawo dashi ba dan anyi neman duniya ba'a ganshi ba." Aisha ta sharce hawayenta. Ni kaina fuskata sharab da hawaye. "Shawarar da zamu baki ki rabu da Alhaji Zaidu kawai. Ki bar Hajiya ita da Allahnta" Kaina take ya soma ciwo nama rasa abinda zance. Wayatace ta shiga ruri ina cirowa naga masta ke kirana. Sumayya da Aisha sai suka shige Kitchen suka bani waje. Muryata a dashe na amsa mishi sallamarshi jikina a mugun mace. "Wazirat lafiya menene waya taɓa mun ke to na jiki wani iri, kuma naga baki neme ni ba" Ajjiyar zuchiya na sauke nayi murmushi a ƙoƙarina na kawar da zargin nace. Ai na barka ne ka kirani da kanka kar inzo in kira Hajiya na gefenka shi yasa. Amman ka ganni cike da kewarka" Murmushi yayi yace. "To ko in kamo hanyar Abujan ne in sameki uhm?" A_a ni a su wa ai a cikin lokacin Hajiya kake. Mu yanzu ma da munyi sallah zamu kamo hanyar Dutse in sha Allah." Murmushi yayi mun. "Akwai abinda kike ɓoyemun Shalelena. Ki daure ki faɗamun abinda ke damunki. Kinsan yadda nake sonki nake kuma son ganinki a cikin farin ciki uhm" Ai kawai sai naji numfashina yana yin sama sama. Inason nayi magana sai nake jin kamar an zare mun harshena ya tsinke. Allah na soma ambato la'ilaha'illa'anta subuhanaka'inni'kuntuminal'zalumin shi na dinga faɗi a hankali ashe yana jina ni ban sani ba. Sai naji yayi ajjiyar zuchiya. "Menene yake damunki Shalele ki sanar dani dan Allah. Kaddai saƙon da aka turo mun da wata baƙuwar lamba kema an turo miki ne, ko kina da masaniya akan saƙonne, wata macece ta turo mun? Banso na ɗakko miki maganar a waya ba naso saimun dawo gida a tsanake sai muyi maganar uhm" Sai naji gabana ya kuma yankewa ya faɗi da ƙyar nace dashi. Wani Abunne ya faru? Ni bani da labarin komai wallahi. Kainane yake mun ciwo sai zazzaɓi da nake ji, wanne saƙon kake maganar an turo maka? " Ai take saiya ruɗe ya shiga aikin mun sannu sai cewa yayi mu nemi wani asibiti a Abuja muje a duba mishi lafiyata. Ni dai lallaɓashi nayi muka rabu akan zanje asibitin dan yaƙi fur. Yana kashe waya na kira Maigogul nace mishi na gama suzo Zone 2 mu tafi. Ina zaune kaina na mugun saramun. Sumayyace ta fito ɗauke da abinci. Murmishin dole nayi mata. A_a Sumayya sallah kawai zanyi zamu kama hanyar Dutsene daga can nake" "To shikenan muje ciki Aisha ma Sallar take yi." Tare muka shiga, da ƙyar fa nake jan ƙafar tawa ta sake nauyi. Nayi sallah muka ci gaba da hirarmu nima na labarta musu halin da nake ciki. "Hmmm ina baki shawarar ku rabu tun wuri. Sabuwa kada kiga munata ce miki ku rabu kiyi tunanin ko so muke mu kashe miki Aurenki. Kin ganmu duk da Aurenmu a kanmu. Wallahi Hajiya munubiya muguwace ta ƙin ƙarawa" A_a Aisha ai gaskiya kuke faɗamun kuma in sha Allah na tattare bayananku zanyi nazarin mafitar kaina. Ai ina ganin bama saina nemi ragowar tsofin matan Alhaji Zaidu ba bayanan bakin ku sun wadatar dani" Su Maigogul ne suka iso. Sumayya ta ɗakko zanin gado da yajin daddawa mai yawa ta bani. Nayi musu sallama muka fito Aisha ta saka mun kuɗi a jakata ina ƙi tana ƙi dole na haƙura na shiga mota muka kama hanya. Saida mukai nisa kana na labarta musu duk labarin dana jiyo. "Tabbas ba zaku rabuba kuma daga kanki alkadarinta saiya karye. Ni nasan magunguna bafa na shirka ba na tsari da kariya duk zan shiga jeji in tsinko miki. Lolo shawarar farko shine duk rintsi duk wuya duk bala'i kisan yaya Zaki hilaci Alhaji Zaidu ya sake miki gida. Kinga kayan sib ɗinki kwashesu za'ayi ai musu fitsari a wankesu fes da ruwan toka sai a kyautar ko ƴan uwanki ki rabemar tunda ko wani abun akayi a kanki akayi. Kinga gidanma kada ki sake ƙafarki ta taka, kawai kisan me zaki ce da mijinki. Ko ya saki a gida daban ko kiyi zamanki a gida muga abinda Allah zaiyi. Amman komawarki cikin gidan haɗarine ga rayuwarki Lolo. Inaji ina gani bazan barki ba. Amman fa wallahi in wani abu ya sameki narantse miki da Allah wannan matar saita raina kanta zata ga sharri zata ga bugayi ganin idanunta. Aljanu kuwa ba zasu barta ta huta ba saita haukace tuburan dan wallahi tsubbu zan koma. Kisan ya zaki faɗa ma mijinki mu zamu nuna bamu sanma komai ba. Ita Rakiya zan mata bayani yau a ɗaki inta bani haɗin kai amman. In kuma ta shiga shirme in watsar da'ita. Kuma Hajiya Balaraba ma zan sanar mata halin da ake ciki wala Allah tana da abun faɗe" Tun ina jin Maigogul har tunanukan kaina sukai zurfin da bana iya fahimtar me suke cewa ina dai jin muryoyinsu. Ga batun saƙo da Alhaji yace anyo mishi shima yana buga mun kaina, ga tunanin me zance da Alhaji dangane da raba gida ga fargaban ɗankwalina da yake hannun Hajiya tunda ina tsoron kada ta durƙusarmun da lafiyar jikina. Idanuna na lumshe hawaye sukaita wanke mun fuskata. Wayatace tayi ƙara halamun shigowar saƙo ina dubawa ilai Masta ne tare da kalaman ƙauna da zunzurutun kewata a gefenshi. Hawayen dake sakkomun ne suka sake tsananta. Amman saida na tura mishi martani na ajjiye dan gudun kada ya zargeni. Muna sharara gudu ni kuma zuchiyata nata tubkewa da warwarar mafita da yadda zan ɓulloma wannan lamarin har in shawo kan abun. Bamu muka shiga Dutse ba sai goman dare tun a hanya nake fama da matsanancin ciwon kai mai zafin gaske. Haka muka shiga cikin gidan kaina a dafe ko idanuna bana iya ɗagawa. Su mardiyyama suna cikin gidan ashe sun kawo mun rubutu kuma Baba malam yace su kwana. Gaza dasu Madamcy mai jego da Sama da rita duk suna zazzaune anata musu. Shigowarmu ce ta katse hirar da kuma yanayin da suka ganni ina tafe dafe da Uzairu zuchiyata suna tai mun sannu. "Lafiya Maigogul haɗari kuka samu ne ko wani abunne ya faru? " Cewar Rakiya kenan Saida na zauna msigogul ma ya zauna yace. "Kanta ke mata ciwo Rakiya babu komai" "Babu komanne aka haɗo uu mardiyya da jarkokin rubutu haka siddan? Sabida an ɗaukeni marar mahimmanci ko? Ko da yake baka da laifi Sabuwa itace mai haddasa wannan fitinar" "A_a Rakiya eh kiyi shiru dan Allah eh abi komai a hankali ga yara ga surukanki. Shi eh Maigogul yana da kyau eh ya sanar mana abinda ke faruwa kawai" "Zan faɗa muku duk ku kwantar da hankulanku, Lolo kije ki kwanta ki nutsu tukunna zamu yi magana gobe kafin ku tafi" Miƙewa nayi na shige ciki yarana suka biyoni tare da su Rahama. A hakan na ɗauro alwala nayi sallar isha magriba munyi a hanya. Mardiyyace ce ta matso ta kama mun kaina tayi mun adda'a wallahi kamar armara kafin ta sauke hannun naji sauƙi kamar ba ni ba. Ajjiyar zuchiya na sauke na dubi Aminu nace. Tun yaushe kuka zo Aminu? " "Tun wajen goman safe muka zo danma mun jira Malam ya ƙarashe rubutu shi da Aɗɗa'u shi yasa. Yace ɗan ƙaramin kofi zaki dinga cikawa ki sha ragowar kiyi bismillah ki shafe jikinki Ummi. Allah ya baki lafiya ummi kita Adda'a nima na tawo miki da littafin addu'o'i dana azkar na safe dana maraice. Azkar in kika riƙeshi duk wani waraka yana cikinshi babu abinda zai cutar dake, koma zai cutar dake bazai yi tasiri ba. Kuma ki dinga kwanciyarki da alwala ta hannun dama." Murmushi nayi musu su duka wani farin ciki ya lulluɓemun zuchiyata ko iya haka naci nasara a rayuwata ko yanzu na mutu na gode Allah. Rahama tace. "Muma duk ya bamu littafin wallahi tunda akwai na hausa a gefe zamu dinga yi in sha Allah. Har Labbai yaba tazo tayi jiran duniya baku dawo ba shine mijinta da yamma yazo ya tafi da'ita. Ta dai ce gobe da safe zata zo ku gaisa a gurguje. In kuma baku haɗu ba Allah ya tsare hanya, ga man ƙuli ta kawo miki" Allah sarki ɗan uwa abun wuya. Ai kuwa naji daɗin kyautar sosai. " Gaza ne ya shigo da jaririyarshi a hannunshi ya ajiye mun ita a cinyata. "Ki eh saka mata albarka Rakiya kayi nayi kenan eh mana rabin raina kenan fa" Murmushin ƙarfin hali nayi na dubi yarinyar nayi mishi barka ya karɓeta ya tafi. Sadiyace ta shigo mun da Abinci tare da malama muka ci, na samu na ɗan watsa ruwa na dawo na tarar sunata shinfiɗar bacci har malama da Aɗɗa'u sun yi bacci. "Aminu ɗauki Aɗɗa'u kuje ɗakinsu Magazin ku yi kwanciyarku sha ɗayan dare fa. Ke mardiyya da malama kuzo ku kwanta ta nan" Cewar Adama kenan. Suna kan gyaran shinfiɗar Maigogul ya turo Rakiya ta kirani. Miƙewa nayi na shiga ɗakin Rakiya na zauna a kafet Maigogul da Rakiya na bakin gado. Nan Maigogul ya labartama Rakiya kab abinda ke faruwa. Shiru tayi ta shiga tunani can sai tace. "To menene matakin da kuka yanke. Komawa gidan zata yi a haka taje taci gaba da haƙuri dai ko? Nifa Maigogul kada fa Sabuwa tace zata kaso aurenta Allah ya dubeta ya rufa mata asirinta. Ni wallahi taje kawai ta zauna a ɗakin mijinta ta dogara ga Allah. Ai asiri ƙaryane wanne irin bigene baku yi ba da kai ɗin da'itan? Yarinya ka rabu da'ita tayi zaman aure. In ta hasalashi ya saketa ina zata shiga ta sani ne, ko kuwa gidan uban yaranta mai mata huɗu zata koma a matsayin ƙwarƙwara? " Murmushi kawai nayi domin nasan za'a rina wallahi. Maigogul ya girgiza kanshi yace. "Ana ga yaƙi kina ga ƙura. Ni da kike ganina da lolo ta bar wannan auren na gwammaci komai nawa dana mallaka ya salwanta. Ai ta shiga gidan kenan. Amman Rakiya mafita za'a nema. Ya raba musu gida kawai shine. Kayayyakin sib ɗinta nace duk a rabe ma su Adama. Amman ita zata san yadda zata lallaɓa mijinta ya sake mata gidan tunda mu ba zamu nuna ko da wasa mun san halin da ake ciki ba Tunda ita kanta lolon bata yi magana dashi akan komai ba. Wannan mata tashi muguwar kiriminal ce wallahi. Amman fa ƙarshenta ne yazo haka nake ji Rakiya". "Nifa wannan lamarin bai kamata ace an ɗaukeshi da zafi ba. In mijinta yazo ta bishi su tafi kada ta sake ta nuna mishi komai. In kuwa tayi mai magana akan uwargidanshi kwaɓarta tayi ruwa, ko ya soma zargin bata son uwargidanshine kunga wa gari ya waya ya tsinci talatarshi a laraba? Kune tunda ko umara ai dakai akaje ba da Kayi nayi ba" "Ke ya isheki haka Rakiya ai ke sai dai a barki wallahi, da kamar ba za'a sanar miki ba ma. lolo tashi kiyi tafiyarki abunki" Miƙewa nayi na fata zuchiyata kamar zata fashe. Mun fi ɗayan dare muna ta tattaunawa dasu Rahama kafin dai suka kwanta. Ni kuma na ɗauro alwala na fito nai ta sallah ina kai kukana wajen rabbil izzati na bar komai a hannunshi yaimun mafita. Saina wayi gari babu nauyin zuchiya. Ina zaune a inda nai sallah ina karanta azkar a hankali dan wasu kalmomin wuyar faɗe suke yi mun. Wasu ma sai dai in wucesu bazan rufeku ba. Na jima sosai a kan sallayar na gama na yi adda'a sai da nayo wanka na shafe jikina da rubutu bayan na sha. Rahama fa Sadiya tun safe ban ganta ba" "Tana ɗakin madamcy tana ma Rakiya wanka Hauwa kuma na ma Madamcy" To mardiyya malama kuzo muje mu dubo masu jego. Hauwa ma bamu gaisa ba da su Raliya duka" Fitowa muka yi zamu sauka Rakiya ta fito daga waje. "Ina kuma zaku je kika taso yara a gaba lolo? " Ɗakin masu jego zamu je ne yanzu zan dawo" Baki ta taɓe ta kira Marsiyya wai zata aikesu ni dai na tafi ni kaɗai. A ɗakin na tarar da Hauwa da Rahama. Hauwa na gasa ma yarinya cibi. Rahama na ninkin kaya tana zubawa a wani babban kwali irin na firich ɗinnan shine sib ɗinsu. Itama jaririya naga kayanta iyakar cikin basket ɗin jinjirayene kawai. Sai katifa da layun Gaza zagaye da ɗakin fa. Wayyo sai na ƙudurce a raina zan saima madamcy sib da gado naga Rakiya ma tana dasu. "Lolo ashe kun dawo ni sai asuba naga Maigogul da yaron Hajiya Uzairu Zuchiyata. Ince dai lafiya ko naga yaushe _yaushe kika tare da har kinzo gida? Gashi naji ance su Mardiyya sun wuce da abu kamar magani nace ko an samu ƙaruwane? " Murmushi nayi kawai nace. Lafiya lau sabida dai na dawo daga wata ƙasarne sai maigidan yake ganin dacewar inzo in ganku. Yauma zai zo mu tafi" "Ayyo Allah sarki munga tsaraba harda ta kayan abinci wallahi mungode. Rannan ma ina zaune kayi nayi ta leƙo ta bani dubu talatin tace inji mijinki kai nagode sosai" Jaririyar ta miƙo mun na gaishe da madamsy da jiki. Muka gaisa da Rita wacce shigowarta kenan itama tazo taya aiki. Wajen Rakiya na koma mukai cinikin sib da gado wai sai dubu arba'in bafa wasu masu mugun kyau bane. Haka na bata kuɗin dani aka sakama Madamcy kayanta a sib Gaza da Magazin ne suka shigar da gado da sib ɗin. "Angode eh Lolo kinga dana samu kuɗi zan sai mata kafet dama na mata alƙawarin dashi zan zo mata in anyi eh albashin farko. Kinga shikenan ɗaki ya zama fes eh dashi. Rakiya da goshinta eh take tafe wallahi. Gata fara eh yarinyar sai dai ma rashin jin daɗina kamarta ɗaya da dattijo wallahi eh." Dariya muka yi kawai wajajen goman safe Alhaji ya iso Dutse sai mamaki nake yi dan a lokacin ni ina Kitchen ina mishi abinci ne bai kuma faɗamun ya taso ba. Da asuba dai ya tasheni a bacci, daya dawo masallaci ma ya kirani mun ɗan zanta duk da bana cikin hayyacina sam wallahi tunani ya cika mun kaina sosai. Sadiya ce ta karɓa mun girkin ni kuma na faɗa wanka a lokacin fa ina jin muryar Alhaji Maigogul ya tareshi. A gurguje nayo wankan na fito hoda da kwalli kawai na murza a fuskata nabi jikina da manyan humrorin Mrs BUKHARI wanda in kana amfani dasu wallahi kafi ƙarfin duk wani turare duk tsadarshi. Su mardiyya suna wajenshi ina jiyosu suna mishi karatu. Nayi shiru a tsaye na kasa fitowa ina tunanin ni kuwa yaya zanyi ace ban koma gida ɗaya da Hajiya ba, kuma bana gidanmu?. Maigogul ne ya shigo ya kira sunana a hankali. "Lolo jiya banyi bacci ba harda mugayen mafarkai doshin asuba da baccin na ɗan samu nayi. In kin rasa hanyar da zaki sanarma Alhaji Zaidu ya sake miki gida, ko kuma kin faɗa bai amince ba. Ba zaki bishi ba sai dai in tafi dake gidana" Rakiya da bamu san ta shigo ba tace. "Ai wallahi baka isaba saita koma ɗakinta. Duk yaran gasu a gabanmu yaushe tayi Auren? Adama ma da take malam madori ta zauna, labbai da take Auren Ɗan daudu ta zauna sai lolo ce ba zata zauna a gidan mijinta da kishiya ba? Wai me kuke nufi ne." Rahama ce ta shigo da sauri tace. "Rakiya ai zai iya jiyoki ba dan yara na mishi karatu ba. Mu a gidannan ba'a abun sirri. Ga Hauwa ta dage sai taji meke faruwa sai gulma da tambayoyi take yi ta mayar damu kamar bamu san abinda muke yi ba. Ke kuma kije ki sameshi koma menene abinda zai yiwu shi za'ayi ba zaki saka rayuwarki cikin haɗariba' Sum sum sum na fita ina jiyo rikici sosai daya ɓalle a tsakanin Rakiya da Maigogul. Ina shiga falon muka haɗa idanu da Masta. Zamanshi ya gyara da kyau ya zuba mun idanu har yana ƙanƙancesu. Ina isowa daf dashi naji yayi wata ajjiyar zuchiyar da daga ji ita tayi kanta da kanta. An gaisheku Aminu. To ku tafi kuje ku shirya ku tafi ko? " "Baba ne zai zo ya ɗaukemu inji Malam. Ummi kima Abba godiya kinga abinda ya bamu" Cewar mardiyya. Da take nuno mun leda shaƙe da su biskit da alawa ga kuɗi da kauri. To shikenan kuje ciki wajen Rahama" Da idanu muka bisu har suka ɓace kana muka kalli juna muka sakarma juna murmushi mai rai da motsi. "Wazirat daga zuwa gida sai kawai a juya mini baya uhm haka akeyi ne. Kinsan irin kewar dana shiga kuwa? Hatta Hajiya tayi kewar motsinki a gidan uhm Mrs BUKHARI Hmmmm to mu tara gobe [10/22, 10:33 AM] BADA'AT IBRAHIM: TASKAR BADI'T

WANNAN SHINE JADAWALIN SHIRYE SHIRYENMU DA WANNAN TASKAR TAKE GABATARWA YAYIN DA BA'A LITTAFI DOMIN ƘARUWARMU BAKI ƊAYA MU GUDU TARE MU TSIRA TARE.

MASU SON KASANCEWA TARE DA MRS BUKHARI GAREKU GA LINK NAN DUK MAISON KASANCEWA MEMBER SAI YA SHIGA A DAMA DASHI IN SHA ALLAH. ANA ƘARUWA MUNA FAƊAKARWA DOMIN AN HAƊA MALAMAI DATTIJAI WAƊANDA SUKA SAN DARAJAR MUTANE SUKA SAN ME SUKE YI. DUK DA ZAMU SABUNTA SHIRYE_SHIRYEN NAMU IN SHA ALLAH KU KASANCE TARE DANI A KULLUM

RANAR MONDAY 8:00 PM A GAMA 9:30PM

Shirin """"TARBIYYAR YARANMU"""

MASU GABATARWA ( MAMAN KHAIRY) (ANTY BADI'AT) (KHADIJA MAI DOKI) (ANTY ZEE) RANAR TALATA 8:00AP A GAMA 9:30PM

shirin """"AMFANIN TSABTA GA MACE"""

MASU GABATARWA (MRS BASH) (MRS BUKHARI) (MAMAN KHAIRY)

RANAR LARABA 4:00PM A GAMA 6:00PM

Shirin """TAURARUWAR MAKO"""" SHIRIN DA ZAI DINGA ZAƘULO MANA MATA DOMIN SU BAMU TARIHIN GWAGWARMAYARSU A GIDAN AURE.

MASU GABATARWA (HAJARA ALIYU) (OUM INTEESAR) (MAMAN SAFWAN)

RANAR ALHAMIS 8:00PM A GAMA 9:300

Shirin """MATSALOLIN MATA DA WARAKA"""" SHIRIN DA ZAI DINGA ƊAUKO MAUDU'I YANA TATTAUNAWA AKAI. MUSAMMAN MATSALOLIN DA SUKA ADDABI MATA. SANNAN ZA A DINGA KARANTA TAKADDUN MASU TURO MATSALA, DA BASU SHAWARI ME KYAU""""

MASU GABATARWA (Ummu Inteesar) (Mum khairy) (MRS BUKHARI)

RANAR JUMA'A 12: 00PM A GAMA 2:00PM

Shirin """"ADO DA KWALLIYA""" MASU GABATARWA (KKhadija maidoki) (Mrs BUKHARI)

RANAKUN ASABAR DA LAHADI KUMA RANAKUN HUTU IN SHA ALLAH. DOMIN KULAWA DA ME GUDA DA YARAN GIDA BAKI ƊAYA.

MRS BUHARI 6

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull