Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 - Chapter 5
Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 Chapter 5: Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 Chapter 5. Murmushi nayi mishi na ƙarfin hali. Domin kiran sunan…
3,249 words
Murmushi nayi mishi na ƙarfin hali. Domin kiran sunan Hajiya ke da wuya sai naji kaina ya sara mini Wallahi. Amman a haka na dake nice harda hararar soyayya nace dashi. Kaji ka, kai da kake da Hajiya yaushe zaka zauna cikin kewa. Aina tabbatar zata kula dakai fiye da yadda zanyi" Murmushi yayi mun yana ƙarema tsakiyar idanuna kallo. Shigowar Sadiya da kayan abinci ne ya katse mishi kallon. Maigogul ne ya shigo fuu yayi ɗakinshi Rakiya kuwa ta bishi nasan rikicin za'a ci gaba dayi kai Allah dai ya sauwaƙe. Abincin zaka ci yanzu in zuba maka ne koko ba yanzu ba? " "Ai gara inci sabida ban ko karya ba na kamo hanya ina Allah_Allah inzo in sameki. Kinsan fa jiya naji muryarki cike da damuwa uhm. Kuma nima akwai abinda ya faru da nace miki zan sanar miki amman sai mun tafi Kano." Abincin na soma zuba mishi farfesun kazane wanda na ɗan ɗaure romon da sitati na masara., na ƙawatashi da jan waken gongoni. Sai farar shinkafa, sai shayi mai kayan ƙamshi. Ƙasa ya dawo daf dani ya zauna na tura mishi abincin gabanshi. Na ɗauki kofi ina zuba mishi ruwan shayi kenan Sai muka jiyo sallamar Babangida Kaci gari gabanshi gaɗi ya shigo shi taƙamarshi nan ai gidansu ne. To ai kunga dole a falo zai zauna ko?. Muma gamu a falon Rahama ta leƙo tace ya shiga falo" Babu guiwa ya tako yana shirin zama a kujera naji ɗumin abinci a laɓɓana Alhaji Zaidu ya ɗebo ya ɗaura a bakina. Buɗe baki nayi ya zuba mun yana murmushi. Nima murmushin nake yi. Fitowar Maigogul ne yasa su mardiyya suma suka fito. Babangida baice mana ba bamu ce mishi ba. Alhaji Zaidu sai magana ƙus_ ƙus yake yi mun inajin kaifin idanun Babangida na yawo a jikina. "Alhaji ga Baban yaran Lolo ku gaisa. Kai Babangida ga mijin Lolo ku gaisa" Murya a shaƙe yace. "Assalamu Alaikum" Alhaji Zaidu ya amsa mishi tare da duban Maigogul yace. "Ai Alhaji Baba bamu sanma ya shigo ba dake bamu ji sallamarshi ba sam. Ya gida Baban Mardiyya" Alhaji Zaidu ya miƙa ma Babangida daya miƙe tsaye hannu. Dole ya miƙo nashi suka yi musabaha yace. "Mun gode da gudunmawar Aure daga bayar. Tare da Wazirat al sa'ada muka buɗe ma ambulon ɗin Allah ya saka da alkhairi" "Wazirat al Sa'ada? " Babangida ya maimaita a hankali nayi imanin bai san munji ba sai kawai yayi hanyar waje. "Ummi mu zamu tafi yaushe zaki dawo ummi?" To zan zo bikin Uzairu zuchiyata zamu haɗu ku gaishe da Baba malam ku yi mishi godiya" "Ke Mardiyya zaku fito ne ko saina shigo na jawo ku ne, menene haka kun barni a tsaye ina jiranku, wannan me kenan? In binta zaku yi gaku ga ta ai" Da sauri suka fice Maigogul yace. "Babangida jarabar duniya. Hmm a haka ma kura tayi lafiya da dane da wallahi sai dai kaga ya rungumeka kun kaure da dambe Babangida bashi da daɗi sam bashi da kirki, yadda kasan a ƙofar tasha Aka haifeshi, da zasu haɗu da Gaza ma sai sun taɓa damben. Allah dai ya raba lolo da ƙaƙai ko a kotunma da yaya aka.... " Sai kuma ya haɗiye zancan shi sakamakon hayaniyar da muka jiyo a waje. Babu shiri duk muka ɗunguma waje. Dambe ne ya kaure tsakanin Babangida da Gaza sai doki in doka suke yi, ga bakin Babangida yana jini, bakin Gaza kuma ya sha naushi ya aune. Fisgewa Gaza yayi ya nufi ɗakinshi da gudu. "Maza ku fice a guje yanzu nasan adda yaje ɗakkowa kuje dan Allah bama son fitina. Kai kullum kazo sai anyi rikici dakai" Cewar Maigogul Babangida ya kama hannu Malama ya dubeni yace. "Ga abinda kika ja ai Sabuwa kina gani ai a gaban yaranki duk sanda zanzo sai an samu matsala, sabida ku gidanku babu tarbiyya" Hannun yaran yaja suka fice fuu ni ko bakina na taɓe. A guje Gaza ya fito da adda Alhaji Zaidu da Maigogul ne suka cabkeshi yanata zage zagen rashin daraja. Maigogul na rungume da ƙugun Gaza carab sai fisgewa yake yi. "Da kun barni dashi wallahi da saina tsinke mishi ƙafa. Ya zai shigo har gidanmu ya dinga mun eh kallon banza. Allah da kun barni dashi eh. Allah ya sake zuwa kuma muka haɗu saiya rasa eh ƙafafunshi, me ma yake eh zuwa yayi ne, dole ne eh zai ya shigo mana eh gida. Menene bai ma eh iyayenmu na rashin mutunci ba eh" "Haba Baban Rahine. Alƙawari fa kayi mun ka dena shaye_shaye da daba shine zaka ɗakko adda haka. Ai ko babu komai an haɗa zuriya dashi sai yaci albarkacin yaran. Dan Allah kada ka sake" "Cau cau wallahi. A lafiya dai eh futu futu mugun icce. Sai ni wallahi makara motar ƙarshe, tsatsa mai kashe ƙarfe nake, sabon kabari mai sa a tuno Allah. Waihihuhuuuuu" Duk saida muka dara haka Gaza ya mayar da Addarnan mu kuma muka haura sama. Sabon abinci na zuba ma Alhaji Zaidu shi kuma sai kallona yake yi. Yana cin abincin muna ɗan hirarmu sama _sama harya kammala. "To wazirat ya kamata kuma mu kama hanya ina da aiki sosai dana baro." Yauwa nace ba. A cikin gidajen da kake ginawa na siyarwa kana da wani ginanne a ƙasa ne? " Zama ya gyara yace. "Babbar magana. Uhm akwai gidaje uku a mabambanta unguwanni. Amman wanda yake ɗorayi shi har kaya an zuba a ciki. Kinsan misali in mutum na so yafi daraja da kaya a ciki kamar tsarin da Ƴan Abuja suke yine muma nan Kano mun soma. Sai dai kiga magidanci ya lale kuɗinshi ya sai waje shi da iyalinshi sai dai kawai su ɗebo suturunsu kawai ba ruwansu da komai. Wasu kuma haya ake bayar dasu da kayan. Kamar gidaje da nake ginawa a Abuja yawanci haya nafi sakawa." "To na ɗorayin inaso in mun shiga Kano kafin mu shiga gida mu soma zuwa inason zan ganine" Kallona yayi na tuhuma yana murmushi yace. "Ko siya zaki yi ne uhm Wazirat? To shikenan zamu je ki gani ƙaramin gidane ba wani babba ba, sai dai yanayin tsarin gininshi yana da kyau" Miƙewa nayi nace. To bari in fito sauran zancan ma ƙarashe a hanya. Ai kuwa na shiga ciki na haɗa ragowar kayana duk da zuchiyata tab fargabar me kaje kazo amman dole ita rayuwa sai an gwada ake dacewa ko akasin hakan. Rakiya na miƙa ma kuɗi Rahama da su Sadiya duk na basu na dubesu nace. Duk yadda ake ciki zaku ji in sha Allah adai taya ni da Adda'a. Rahama muje ki rakani ƙasa" Tare ma muka sakko dukkanmu Maigogul da Alhaji Zaidu suna jingine a jikin mota Gaza na riƙe da get ya wangale mana. Kayana ya karɓa ya saka mun, nayo ma Hauwa, da Madamcy sallama Rita ta tafi aiki ita. Mota na shiga muka nufi get. "Sabuwa kima Sikari godiya wallahi ya biya eh kuɗin ragon Rabin raina harda eh kuɗin abincin suna wallahi" Allah ya saka da Alkhairi, Gaza sai ka dawo mu kam mun tafi" Na faɗa ina dariya. "Alhaji batun Rahine a duba wallahi ni dana dawo sai naga duk ta rame har shi muzuru Uzairu duk ya rame har ciwo ya jiyo a ƙafa a ƙila sata ya haura yayi duba mana" "To Baban Rahine ka tawo da Rahine harda Uzairun shi Uzairu ka bamu dan magen yayi mun kyau. Rahine kuma saita zauna a kamfani amman fa anan zata dinga kwana" Ihu ya saka ya shiga kirari, "Batun albashinta fa Rahinen aiki zata yi tuƙuru" muna dariya muka fice muka ɗauki hanya muna dai hira sama_ sama ba kamar yadda muka sababa. Can da tafiya tayi tafiya sai mukai shiru kawai kowanne cikinmu da abunda yake saƙawa. Ni tunanina ya kasu kashi kusan ukune. Na farko batun Hajiya munubiya Na biyu batun sake gida. Na ukun shine magana da yake ta cewa zamu yi dashi dan gane da saƙon da aka turo mishi. Idanuna na lumshe tare da gyara zamana. Bana son ma yayi mun wata tambayar sam sai kawai muka tafi a zuwan bacci ne ya kwasheni wallahi har muka shiga Kano idanuna biyu a baɗini a zahiri kuma bacci nake yi. Nifa ban buɗe idanuna ba har saida muka shiga ɗorayi ƙofar sabon gida. Sai naji ya tsaya ya fita a motar. Sai lokacin na buɗe idanuna da sukaimun nauyi na dubi bayanshi da gidan da fasalin unguwar. Unguwace cike da mutane ni da na ɗauka unguwace da zanga gidaje ɗaiɗaiku ajjiyar zuchiya na sauke. Shi da kanshi ya buɗe get ɗin gidan. Tabbas ƙaramin gidane kamar yadda ya faɗi. Dawowa cikin motar yayi ya sameni idanuna a buɗe. "Wazirat kin tashi ne? Ai bamma yi niyyar tashinki ba naso ne in shigar da motar ciki sai in kashe in zauna inta kallonki" Murmushi nayi na farin ciki sai nayi ƙwal_ƙwal kamar zanyi kuka. Saurin riƙe mun hannu yayi cikin ƙasa da murya sosai yace. "Menene wazirat ɗina ki daure ki faɗa mun dan Allah tun jiya zuchiyata take cikin damuwa" Ya yanayin girman matsayina a wajenka yake Omri? " Murmushi yayi mun mai rai da motsi. "Omri? Wannan sunan yayi mun kuma kin burgeni sosai shi Masta a barshi sai muna shinfiɗa uhm. Menene matsalarki al sa'ada? " Alƙawari zaka yi mun in mun shiga ciki duk alfarmar dana nema a wajenka kai mun. Kai mun alƙawari anan tun kafin mu shiga. Sannan abun baifi ƙarfinka ko ta ko ina ba. Omri bazan taɓa neman alfarmar da nasan baka da'ita ba" Na ƙarashe maganar da rawar murya wasu siraran hawaye suka zubo mun." Babban yatsanshi yasa ya sharce mun hawayen nawa. "Dena kukan zanyi miki duk abinda kike so in sha Allah. " Motar ya ja muka shiga gidan. Gidan yana da kyau ni ƙanƙantarshi ce ta sake burgeni ma sosai. Yana riƙe da hannuna har muka shiga falon zagaye da kujeru irin masu L ɗinnan marasa hannu na fata masu mugun tsada da gani Zaunar dani yayi a kujera. "A_a ka kaini ciki in kwanta bana jin daɗin jikinane" Baice komai ba ya shiga dani cikin komai yana ajjiye cikin tsari da kyau gwanin sha'awa katifar dai babu zanin gado a haka na jawo fulo na kwanta. Zama yayi a gabana yana shafan kaina. "Ke nake saurare Wazirat Omri ɗinki yana jinki" Hannunshi na riƙe gam nace. Munyi Aurenmu cikin soyayya tare da fatan sai dai mutuwa ta rabamu ko? " Kanshi ya gyaɗa halamar Eh. To ina fatan ni dakai mutuwa ce kaɗai ka iya mana shamaki ba dai mutum ba. Kaga shigowarnan da nayi gidannan? To na dawo nan da zama bazan koma can gidan Hajiya ba, Allah ya hore maka ba dole sai mun zauna waje ɗaya ba. Kuma raba gida na rage zafin kishi da jin zafin juna sosai. Mu ba yara ba bare muce zumuncinsu muke kallo. In kuma kace dole sai na koma can to daga nan Dutse zan koma" Na ƙarashe ina hawaye. Duk wannan maganar zuchiyata fa sai daka take yi mun Bansan me zan samu a matsayin amsa ba. Ya dai yi shiru yana ta saurarena da dukkan zuchiyarshi. "Wazirat nasan kina da dalili mai ƙarfi kuma zanso jin dalilinki kada kiyi tunanin ɓoye mun komai ko kiyi tunanin rage mun komai nake son sani" Shiru nayi ina tunanin to ni mai zance mishi ne. Kafin in gama tunanin ya miƙo mun wayarshi yace. "Kinsan wannan lambar kuma kinsan wacece tayo saƙon? " Amsa nayi jikina na ɓari na soma karantawa cikin zuchiyata ga abinda rubutun yake cewa. "Sabuwa bata aureka domin soyayya ba. Sai domun kuɗinka da niyyar tarwatsa maka gidanka. Sannan ƴar iska ce kayi bincike mai zurfi a kanta ɗiyarta mardiyya bata hanyar aure aka sameta ba bata san ma waye ubanta ba shine ta liƙa ma tsohon mijinta cikin. Sannan ita da ubanta suna bokanci kayi bincike da kyau, mijinta da kwarto ya kamata sanadiyyar rabuwarsu kenan. Na barka lafiya." Ai take hajijiya ta soma ɗibana daga wannan zaunen da nake, amman fa babu ko ɗigon hawaye a idanuna zuchiyar sai naji ta bushe. Lallai Ƴar shuwa ashe abinda na tare mata a rayuwa har ya kai haka, ai ni na ɗauka iya Babangida ya isheta rayuwa ashe Aurene bata son taga nayi shi kwata kwata. "Halamu ya nuna kinsan mai rubutun ko" E na santa farin sani ma kuwa. Abinda ta faɗa gaskiya ne face Mardiyya da tace ba yarinyar Babangida bace ƴarshi ce." Na faɗa cikin rashin tsoro kawai ma duk abinda zai faru gara ya faru bana ƙarya kawai gara in sanar mishi gaskiya. "Wacece ita, a ina kuma take? " Kishiyata ce ta da matar Babansu Mardiyya aminiyata wacce muka yi rayuwa a gidanmu tare, aminiyar da ko mutum na kashe ita zata taya ni mu birne" Zama ya gyara yana kallona cikin mamaki. "Ban gane ba, aminiyar taki ce ta Auri mijinki kuma duk da kun rabu take binki da bita da ƙulli? Ina bazan bar wannan maganar ba wazirat dole hukuma ta shiga cikin lamarin. Kuma dole mijinta yasan abinda ta aikata." Kunji a daidai gaɓar dana samu zarafin fashewa da matsanancin kuka mai tayar da hankalin duk wani masoyina. Riƙeni yayi a jikinshi tsam yana rarrashina. Ka barni inyi kuka. Shikenan babu dama ka tuba mutane su karɓeka a matsayin wankakke kenan. Bafa mu muka zaɓi rayuwarmu ba, kuma bamu isa mun kauce ma ƙaddararmu ba. Ya Ƴar shuwa take son rayuwata ta ƙare ne ni Sabuwa da abinda zata saka mini kenan" "Ya'isa wazirat. Ba ta turo bane dan ta ɓata mun ke ba? To wallahi kimarki da darajarki saita sake ɗaguwa a wajena kinsan menene dalili Shalelena?" Girgiza kaina dake manne a ƙirjinshi nayi. "Yauwa Sabida da kika ga saƙon baki yi yinƙurin kare kanki ta hanyar layancemun ba. Sai kika karɓi abinda ta rubuta kikace hakane face batun mardiyya data yi miki sharri akai. Al sa'ada bata san in duk kowa zai ƙi ki ni a lokacin ma zan soma sonki. A binciken da nayi a kanki tabbas banji batun Mardiyya ba. Amman a layinku akwai wani malam Habu ko ina ya samu lambata ban sani ba ya dai kirani yake faɗamun maganganu masu nauyin maimaitawa to a ciki harda batun bokancin duk ya sanar mun. Bincikena kuma ya tabbatarmun da hakanne. Ni ba jahili bane da zan ƙyamaceki dan kinyi wata rayuwa a baya. Sannan in har Allah da kaima laifi ka roƙeshi ya yafe maka me yasa zaka daka ta mutane wanda ba'a iya musu sam? Babban abinda kowa yake fata shine ƙarshenshi yayi kyau ba farkonshi yayi kyau daga ƙarshe abun ya lalace ba. Dukkanmu masu laifine, kuma kullum a cikin saɓa ma Allah muke. Babu mamaki kin fini matsayi da zamowa marar yawan zunubi a wajen Allah sabida kin tuba akan dukkan abinda kika aikata a baya ke wankakkiyace. Wazirat kada ki sake kuka Ƴar shuwa ko? Sai mu tsaya a gaban kotu ta nuna miki mahaifin ita mardiyyan ba shikenan ba tunda ita jahilace. A yau kaɗai dana sanshi ban isa in kalli mardiyya ince bashi ne Abbanta ba. Sabida haka kina dani babu ke babu wulaƙanta in sha Allah. Har gida zamu je muyi sallama in gana dashi in kuma gabatar mishi da wannan saƙon" Ruƙunƙumeshi nayi ina jin wani irin daɗi cakuɗe da matsananciyar kunyar da ban taɓa jin irinta ba a duniya. Ɗago fuskata yayi yana son mu haɗa idanu ni kuma na kasa kaina ya ɗago da ƙarfi sai nayi dariya. Shima dariyar yayi. "Faɗamun me yasa kika kawo mu nan gidan? Kinsan kuma kasancewarmu a hakan sai yayi mun daɗi fiye da tunaninki" Uhm ai har abada a hakan zamu kasance. Sai dai ina fatan ragowar ɗakunan su cika da yaranmu na faɗa maka na dawo nan da zama" Sumbatata yayi a goshi yace. "Me kike nufi ne uhm? " Itace alfarmar da nake nema a wajenka ka barni nayi zamana a wannan gidan naka ni kaɗai dan Allah kada ka tambayeni dalilin ina mugun ganin darajarka da girmanka kuma wallahi mu bama ƙarya" Shiru yayi yana kallona cike da illahirin mamaki maɗaukaki. Nima shiru nayi ina sauraren menene amsarshi.
Babangida:.
"Aikin banza aikin wofi wazirat al sa'ada ni zaka cema Sabuwa haka a wajena? " Sai yayi tsaki ya shiga gyaɗa kanshi yama mance yara na bayan mota sai da yaji amon muryar Malama tana cewa a bata biskit ita ba alawa take so ba. Idanu ya lumshe yana hango sanda aka ba Sabuwa abinci a baki, da wani irin kallon so da Alhaji Zaidu yake binta dashi. "Ku ajjiye kayannan nace dan ubanku. Meye bana siya muku da zaku zo kuna raba kaya a mota" Da tsawa yake maganar. Idanu ya runtse da ƙarfi. Ai kuwa ya bige wata yarinya mai tallar dafaffiyar gyaɗa. Ranga_ ranga aka ɗauki mai gyaɗarnan sai asibiti Allah ma ya so shi ƙujewane kawai sai bakinta data fasa. Gyara mata wajen kawai akayi aka bata magunguna Babangida ya mayar da'ita gaban iyayenta yayi musu bayani tare da basu kuɗi babu laifi kana yaje ya ajjiye su Mardiyya ya wuce wajen aiki zuchiyarshi nata tafasa yana ta maimaita wazirat al'asada a zuchiyarshi. Yana cikin tunaninnan ne akayi kiranshi Sumy tayi ɓari suna asibiti jini ya ɓalle mata. Babu shiri daya tashi a wajen aiki asibitin ya nufi Sumy na bacci lokacin Matar Mustapha Adeeza itace ke zaune da'ita sai Hameeda da ta kawo musu abinci da ruwan zafi zuwan nata kenan shima ya shigo. "Adeeza ya jikin nata? " "Jiki da sauƙi an auna arziki Dr yace ba sai an ƙara mata jini ba, amman naji suna batun wankin ciki ka sameshi a ofishinshi dai. Haka Babangida ya samu likita a ofishinshi suka yi maganar da zasu yi. Amman ina hankalinshi da nutsuwarshi baya jikinshi wannan suna da abinci da aka ba Sabuwa a gabanshi shine babban abinda ke hautsinashi, da kamala da cikar mutuntata da dattijantakar Alhaji Zaidu. Kuma gadon da Sumy take kwance a gadon Sabuwa ta kwanta sanda akayi mata wankin ciki Sai lamura suka sake hautsinewa a ƙwaƙwalwarshi ainun. Har ya isa ɗakin Hala yana cike da baƙin ciki da takaici. Ga hayaniya da shewar mata daga ɗakin Ƴar shuwa yana jiyowa. Lokuta da dama sai yaji kamar ya rabu da Ƴar shuwa shine sassaucin da zai samu a rayuwarshi. Fuu ya fice sai gashi a tsakiyan mata a uwar ɗakinshi. "Ko wacce Ƴar iska ta fice a ɗakinnan. Marasa tarbiyya kawai" Ai ba shiri suka shiga tururuwar fita. Ya ƙurama ƴar shuwa idanu yace. "Kinji kunya wallahi tur da mata masu taurin kai irinki." Ya saka kai ya fice. A wannan dare dai Babangida kusan rabawa yayi yana karanta wasiƙar jaki. Da ƙyar ya yakice tunanin Wazirat ya miƙe ya shiga jera sallolinshi kamar yadda ya saba. Yanayi yana jin wani irin yanayi mai turiri Mrs BUKHARI To sai kuma gobe [10/23, 10:23 AM] BADA'AT IBRAHIM: Kunyi ready ku koyi skill ɗin da ke kawo kuɗi! Idan kuna son ku iya yin voice over kamar masu tallace-tallace, ko ku iya video editing kamar professionals - to wannan class ɗin naku ne! 💪🏽
📚 Za ku koyi: 🎧 Voice Over (recording, editing, delivery) 🎬 Video Editing (cuts, transitions, subtitles & more!) 💻 Practical + Real Project Training
📍 Location: [TELEGRAM ]
Payment: 9163354359 Sa'adatu Adamu Opay
Send receipt via 📞 Contact: [07044292865] 🗓️ Registration ongoing - Limited space available!
💥 Kada ka tsaya jiran lokaci - ka shiga yanzu
MRS BUKHARI 7
SABUWA:.