Kenza eBookz

Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 - Chapter 6

Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 - Chapter 6

Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 Chapter 6: Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 Chapter 6. "Nasan kina da dalili zai iya zama mai ƙarfi uhm? To…

3,255 words

"Nasan kina da dalili zai iya zama mai ƙarfi uhm? To hakkinki ne ki yadda ku zauna gida ɗaya da kishiya. Kuma hakkinki ne kice ba zaki zauna gida ɗaya da'ita ba wazirat kina da wannan damar. Mata da yawa basu sani bane. Sai dai in miji bashi da halin rabawarne yake da damar da zai bada haƙuri har ku amince. Da yawa_ yawan malamai sun tafi akan cewar in kasan baka da ikon raba musu gidanma to kada ma kayi ƙarin auren. Wasu kuma suka tafi akan in da amincewarku ne babu matsala. Wasu malaman ma basa taɓo wannan ɓangaren gudun faruwar matsala da bore daga wajen nisa'u. Ta ɓangarena na amince miki zaki zauna ke kaɗai. Amman wannan gidan ai yayi miki kaɗan wazirat akwai waɗanda suka fi wannan ɗin girma da kyau da komai. Tun farko naso dama a wannan karon in raba muku gida, to sai Hajiya ta roƙi alfarmar tana fatan tare zaku zauna sai kawai nace da'ita eh Amman hatta Goggo amfana taso a raba muku gida haƙuri na bata dake tana da sauƙi saita yadda. Amman faɗamun kina kewata kuwa? " Ai kafin ya rufe baki nayi ma bakinshi riƙon alewar yara muka tafi sama jannati Bamu muka dawo ba saida muka more rayuwarmu muka wartsake ta hanyar yin wanka. Sai da muka fito na sauya kaya ya riƙoni ta baya yace. "Zamu dinga guje_guje kamar yadda ma'aikin Allah Arrasul S A W yake yi tare da Nana Aisha uwar muminai ya tsere mata ta tsere mishi uhm. Wanne alƙawarin farin ciki akayi mun? In ba haka ba in fasa" Juyowa nayi na saƙalo wuyanshi nace. Ai zamu gudanar da duk wata soyayya daka sani. Kai dai kaje masallaci anata kiraye kirayen Sallah." Sumbatata yayi ya fice da sauri. To dama munyi azahar a hanya Nima sallar la'asar ɗin na kabbara har ya shigo ina kan sallaya da azkar ɗina ina karantawa da ƙyar. Tsugunnawa yayi a gabana ina karantawa a tsanake yana yi mun gyara. Zamanshi yayi daf dani ya karɓe littafin ya ajjiye. "Ki dinga faɗa in na faɗa zai fi miki sauƙi" Ai kuwa nai ta bin bakinshi har muka gama" "Naji daɗi sosai dana ga kina azkar. Waye ya baki littafin" Yaronka Aminu ne yai mun kyautarshi" "Allah sarki. Yau zamu soma karatunmu in sha Allah kuma ba zamu dena ba, sai dai zai kasance duk ranar kwananki ne uhm? Kaina na jingina a kafaɗarshi nace. A ofice ba za'a dinga ƙara mun ba, ko da lokacin hutune da cin abinci. Inaso inji ina ƙira'a irin taka data yara" Murmushi yayi mun ya miƙe tsaye. "Tashi muje ki rakani Rano Baba Abdullahi babu lafiya ƙanin mahaifinane a hannunshi nake" Miƙewa nayi na kuma shiryawa muka fito tare muna tafe muna nishaɗi da farin ciki. Duk yadda na ɗauka zan sha wuya wajen ganar da Alhaji sai abun yazo da sauƙi dake yana da sani kuma yana amfani da sanin nashi baya tauye hakkin kowa. Ba irin su o_o ba. Muna tafe muna hira har muka iso Rano. "Ki shiga zan gaisa da Mutane. Kinga ga motar Hajiya ma ashe bata tafi ba" Sakkowa nayi a hankali na ratsa almajiran dake karatu a ƙofar gidan kaina a ƙasa naita shigewa zaurukan gidan har na ɓullo tsakar gida da sallamata. Matan gida duk suka tarbeni cikin fara'a. Anty khadija kamilar mace taimun jagora zuwa ɓarayin Kawu Abdullahi wanda yake damƙam da Ƴaƴa da jikoki, da surukai. Ina shiga muka haɗa idanu da Mandiya ta hakimce a ƙasa ga gwalagwalai ta zubasu. A kusa da'ita ta nuna mun inzo in zauna baki a washe. Da bismillah na zauna nan aka shiga gaisuwa tare da tambayar mai jiki. Anty Tani tace. "Kinga gashi can a gado mai rumfa bacci yake yi anyi mishi allura. Jikin sai godiyar Allah kinsan yanayin tsufa ciwon sai haƙuri. Ya kika baro gida duk kowa lafiya ko?" Suna lafiya Anty Tani. Allah yaba Kawu lafiya" "Madam ashe kin dawo, shine Hauwa bata kirani ba, hala baku shiga gidan bane ko? " Ta tambaya tana dafe da kafaɗata. Uhm nadawo Hajiya. Bamu je gida ba nan muka yo shi yasa bata kiraki ba. " "Ayya to maraba da dawowa bakya gidan duk sai kaɗaici koma yayane ana jin motsinki yafi wallahi" Hajiya Amina tace. "Ke dai Hajiya munubiya akwai kyautatama kishiya. Allah ya dubeki in kina da rabo ya dubi zuchiyarki mai kyau da sadaukarwar da kikai ma Zaidu ya baki ɗa ko ƴa" Duk ɗakin aka amsa da. "Ameen" Ciki har da ni. Kiraye kirayen sallar magriba yasa aka watse a ɓarayin izuwa ɓarayin su Goggo Amfana. Ina bakin famfo ina alwala Alhaji Zaidu ya fito daga falon Goggo Amfana. "Kuna nan ashe? To ni na tafi masallaci" Shigewarshi yayi da sauri. A kusa da Goggo Amfana nayi sallah su Hajiya suna bayanmu ita da ƴar ɗakinta mai jegon da naje suna. Muna idarwa Goggo tace. "Ashe kece kusa dani Sabuwa. Allah sarki ya kika baro iyayen to? " Lafiyansu Ƙalau Goggo ya jikin Kawu? " "Kaiya jikin tsufa ciwonshi sai dai ya sassauta kawai. Yanzu Zaidu yake mun wani bayani mai saka farin ciki bamu gama maganar ba lokacin sallah yayi amman yanzu zaki ganshi ya dawo" Hajiya da jin haka tayi sauri ta matso suka gaisa da Goggo da fara'arta. Itama Goggon da fara'a ta amsa. "Munubiya sai haƙuri ita rayuwa haka ta gada. Jarabawar wani sai kiga daban da jarabawar wani. A babin mutuntaka a matsayinki na babba uwargida obarol dama yana da kyau ace kin kasance gidanki daban yake ba wai a haɗaki da abokiyar zama ba" Carab ta tari numfashinta da cewa. "Ai babu komai Goggo ni ra'ayina nafi son mu zauna gida ɗaya domin mu taimaki juna kuma shima a sauwaƙe mishi wahalar. Ni nake zaɓan a kawosu sabida wanzuwar shaƙuwa a tsakani" Shiru Goggo tayi can tace. "To hakane abun? To Allah yasa mu dace. Ke Sabuwa ki shiga wajen Khadija ƙawarki kuci abinci. Ke kuma sai kije wajen Huwaila ina jiran wannan yaro Zaidu yazo muna tattaunawa ne" Miƙewa nayi nace A tashi lafiya Goggo" Na saka kai na fito a wajen na bar Hajiya a zaune. Na zauna a ɗakin Anty Khadija ta kawo mun dambu da lemun zaƙi kenan Goggo Amfana ta aiko Zarah tayi kirana. Da sallama na shiga falon bata ciki. Daga uwarɗakinta na jiyo tace. "Ƴarnan shigo gani nan a ciki nazo shan maganine" Na buɗe labulen ɗakin na shiga na zauna a gabanta hannunta ta saka a kaina tace. "Naji daɗi da farin ciki da kika zaɓi zaki zauna a gida daban ba a gidan da Zaidu ya saba Auren matanshi ya ajjiye ba. Akwai abinda nake tunani sosai akan yawan rabuwa da mata suke yi dashi sabida rashin haihuwa kawai. A nagarta irin ta Zaidu da son kyautatama duk wanda ya raɓeshi kaɗai yaci ace mace ta zauna dashi ko da baya haihuwar. To sai kiga abu yaƙi. Ya tabbatar mun yana sonki sosai nace ya baki farin ciki. Kuma wannan gida da kika zaɓa yayi kaɗan ya zagaya dake zuwa gobe ki duba a cikin gidajenshi wannene yayi miki sai ki tare acan. Kinyi dabara sosai. Akwai wani abu da kika fuskantane a zamanki da ita Hajiyan? Nasan dai tana takurama matan Zaidu sosai ala dole sai sun shaƙu da'ita a lokuta da yawa sai naita tunanin ko babu zuchiya a ƙirjinta ne. Munyi wani irin zama na girmama juna ni da yaya amman kowa na da iyakarshi. Bata matsawa ta shige mun yadda zan takura ko ace komai nawa ta sani. Haka nima bana yi mata hakan. Amman kullum muna tare hatta kaya kala ɗaya muke sakawa. Kinga wannan azurfa dana baki? Azurfarta ce tafi shekara ashirin a wuyanta da kunnenta duk wanda ya santa ya san wannan azurfa shi yasa zaki ganta da nauyi. Mu mutan da muna ɗaura azurfa a matsayin tsarine babba, shi yasa hatta jirajirai muke ɗaura musu a wuya ko a ƙugu maganice kuma tana maganin kambun baka sosai. Sai da ilimi ya yawaita ne komai ya canja. Da zaki mayar da azurfarnan wuyanki ta zamana ko da yaushe kina tare da'ita da yadda sonki zai ƙaru a zuchiyar mijinki zaki yi mamaki, wannan azurfa zata zame miki garkuwa. Duk wani abu da zai taɓaki da sunan cutarwa zai ji zafin kamar ita akayi ma." Sallamarshi ce ta katse mana hirarmu. Suka shigo shi da ƙaninshi mijin Anty Khadija wallahi kamar ƴan biyu tsayi kawai Alhaji yafi mijin Anty khadija da kaɗan. "Ashe tana nan. Hajiya ta karaɗe gidannan tana nemanta fa. Goggo wannan yarinyar me tayi miki ne?" "Soyayya min indillahi nake yi mata sosai. Shi yasa na haɗata da Khadijanka nasan zasu ƙaru da juna sosai." Da kunya na gaishe da mijin Anty khadija shi kuma ya mutuntani a matsayin matar wanshi. Goggo bari inje wajen Anty khadija" "To shikenan Allah yayi albarka. Neman me munubiya take yi mata ita da bata barin mutum ya sha ruwa? " Na saka kai na fice ba tare da sanin amsar me suka bata ba. Tsohuwarnan tana zargin Hajiya bata da tudun dafawane babu hujja shi yasa. Nayi imani ba za'a rasa waɗanda suma suke zargin nata ba. Ɗakin Anty Khadija na shiga, ina shiga na soma cin dambu kenan Hajiya ta leƙo firit babu sallama. Sai ta washe baki. "Wai ina kika shiga na neme ki na rasa a gidannan? " Wallahi ina wajen Goggo muna ta hirarmu sai yanzu na dawo" Anty Khadija tace. "To ki shigo mana Hajiya sabida sauro" "A_a ba shigowa zanyi ba ina ɗakin Huwaila in kin gama ki same ni acan" Ta saki labule ta wuce da idanu Anty khadija ta bita sai cewa tayi "Allah ya kyauta." Ni dai naci dambu nayi ƙat na kora da kunun zaƙi. Anty khadija ga nera ta dubu hamsin a bani magunguna naji daɗin waɗanda kika bani sosai. " "Ai zaki ji daɗinsu. Akwai babban basket na amarya shi ya kamata ki siya dubu saba'inne amman ki ɗauka a hamsin ɗin. To shikenan nagode sosai naga wasu tsumi ma da kika koya a group inaso inna samu lokacine sai in shiga kasuwa in harhaɗo kayan nazo in daddafa in adana." "Bakya ra'ayin mai aiki kema kamar ni kenan? Kinga surukan gidannan duk suna da masu aikinsu sai ni kaɗai. Kayan haɗin magungunan ma ina siyarwa harda zuma da mazar ƙwailan ma. Hajiya fa bata taɓa siyan magani a wajena ba. Su da su Huwaila daga Senegal ake kawo musu magungunan matansu, suna kashe kuɗi sosai kuma basu fi nawa kyau ba." Dariya muka yi nace. To a bani komai Anty Khadija gobe sai in daddafa abini. Wallahi ƴar aikince bana ra'ayi duniyarce abun tsoro wallahi sannan naga dan dai aikina ni ni kaɗai ace saina ɗauki mai aiki" "Nima abinda nake gani kenan gaskiya. Shi yin aikace_aikacen gida yana ƙara lafiya sabida tamkar atisaye ne kake fa. Sunfi so su jibge waje ɗaya suci sui ta ƙiba" Mun jima muna hirarmu ni nama mance da wata Hajiya itama bata sake bibiyata ba, a ɗakin nayi sallar isha munata hirarmu har dai Alhaji ya leƙo yace in fito. Haka na fito muka wuce wajen Goggo nayi mata saida safe nace sai nazo mata wuni. "Ai akwai meeting sati mai zuwa na bikin su Isma'il kusan su bakwai za'a Aurar gya zo ranar ko? " To shikenan Goggo nagode sosai Allah ya ƙara lafiya." Tare da Hajiya duk muka fito ta nufi motarta muma muka nufi tamu motar. Mu muka soma yin gaba tana biye damu a baya. "Wazirat can gida zamu soma zuwa zan ɗebo kayan sawata sannan zamu yi magana da Hajiya tunda bata san ma mai ake ciki ba. Goggo Amfana tace sai dai in kai ki cikin gidajena ki zaɓi wanda ranki yake so wannan na ɗorayin yayi kaɗan. Tayi na'am sosai da hakan ai ke baki da matsala. Sannan yaushe kike tunanin mu nemi Baban Mardiyya akan batun matarshi ni ba'a waya nake so muyi magana ba ido da ido nake so muyi. Kinsan ɗazu na tura mata amsa ta godiya data faɗamun wacece ke. Hmm Wazirat sai ta sake jero wasu miyagun maganganun masu yawa a kanki. Lallai wannan mata bata ƙaunarki sam gaskiya." Bata ƙaunata na yadda. Sanda muke zaune a ƙarƙashin miji ɗaya tayi sharafi sosai Omri, amman ni wallahi bata gabana sam. Ci gabane sam bata so nayi tafi sha'awar ta ganni ina bara tana jefamun kuɗi a kwano. Duk sanda ka shirya sai mu je mu. Amman zan fiso muje gaban mahaifinshi mu yi mishi bayani in yaso sai shi ya kirawo mana su. " Wasu hawayen baƙin ciki suka taru a guraben idanuna. Bamu muka isa Kano ba sai wajajen goman dare. Mun fito daga mota Hajiya tace. "Baki fito da akwatin kayanki ba. Ko Hauwa za'a kira ta shiga dashi ciki? " Bani nayi magana ba shi ya bata amsa da cewa. "Ke dai rabu da batun akwati Hajiya ku zo mu shiga ciki" Yayi gaba muka bishi a baya. Sai adda'a nake yi babu ƙaƙƙautawa kuma inajin tsigar kaina tana wani irin buɗewa. Wallahi ina tsallake ƙofar falon gidan sai naji kamar na taka wani abu mai tudu haka. Dana duba banga komai ba ko tsinke babu a wajen. Adda'a na tsananta yi na sake ɗaura ɗayar ƙafar tawa na shiga Hajiya ina kallonta tana murmushin muguntar ita ƙila ta gama dani. Tabbas asiri na taka babu ko kaffara. Zama na nayi a babban falon gidan sai tayi sauri ta juyo ta dubeni. "Ba zaki shiga daga ciki bane, ni bacci nake ji sosai bare in zauna muyi hirar zumunci" "Hajiya shige magana zamu yi. Wazirat ki hau sama ki haɗamun abunda ya dace ina zuwa" To shikenan Omri sai ka fito. Hajiya sai da safe." Na haye ƙafar bene su kuma suka shige ciki. Kayanshi na haɗa mishi a akwati ƙarami. Inason ɗiban zannuwan gado a ɓarayina Allah ya sani tsoro nake ji bansan me akayi mun a ɗaki ba. Gashi can babu zanin gado ko ɗaya, zannuwan gadon Alhaji kuma ban yadda dasu ba dukka. Ni dai ina zaune sha ɗaya, sha ɗaya da rabi sha ɗaya da arba'in na jiyo takun Alhaji Zaidu. Ajjiyar zuchiya na sauke dana ga ya shigo da fara'a. "Muje wazirat na tsaya rarrashin yayarkine kinsan tafi son a zauna gida ɗaya kar kiga na daɗe muje ko Shalelen mijinta" Miƙewa nayi shi ke jan akwatin har muka sakko ƙasa Hajiya na tsaye yau babu wannan fara'ar ta gulma. Idanunta ma naga sun gumbura kuma sunyi ja kamar kuka tayi fa. "To Sabuwa Allah ya tsare ko sai nazo ganin waje" To shikenan Hajiya da Alkhairi in nayi miki ba daidai ba ki yafe ni dan Allah" Sai tayi wani murmushi mai fassarori tace. "Allah ya yafemu baki ɗaya. Sai yaushe za'a kwashe kayanki to? " To bazai wuce jibi ba in sha Allah zamu zo mu kwashe" "To yanzu ba zaki shiga ɗakin ba kenan ko suturu ki ɗiba dasu zanin gado da abubuwan da ba'a rasaba?" Murmushi nayi mata nace. Bana buƙatar komai Hajiya nagode sosai " Ina faɗan haka na saka kai na fita shi kuma na barshi a tsaye. Bai jima ba ya biyoni muka dawo ɗorayi a falo muka kwana sakamakon rashin zanin gado. Ranar mun gudanar da wani irin soyayya mai taushi da laushi sosai wannan dare yana daga cikin dararen da ba zamu mance shi ba. Sai dai fa sai nake jin abu kamar yana shiga jikina wallahi haka nake ji. Dana shiga banɗaki sai nake ganin kamar inuwar mutum a kaina. Idanuna na runtse gabana nata faɗuwa fat fat fat a haka na gama wankan na fito. Adda'a kuwa yi nake ban fasa ba. Ƙanƙame Alhaji Zaidu nayi ƙam na cusa kaina a ƙirjinshi. Wallahi Allah bacci ko ɗis banyi ba yaƙi zuwa. A hankali na zame jikina na miƙe na sha rubutuna na shafe jikina dashi na zauna inata adda'a sai can bacci yayi gaba dani na kwanta a jikin Alhaji da yake baccinshi hankali kwance. Washegari muka wayi garinmu cikin farin ciki sai na jini garau dani. Kafin ya dawo daga masallaci nayi wankana na shafe jikina da humrori ina zaune a falo ina jiran shigowarshi. Ai kuwa yana yin sallama naje na ɗafe shi muka yi murmushi. "Jiya ƙarfi da yaji kin samu kwanciyar ƙasa uhm?" Tuba nake yi kaina bisa wuyana. Yau zan tanadar mana duk abinda ya dace in sha Allah" Hancina ya lakace yace. "To naji. Yanzu abinda yafi dacewa shine bari in shirya sai mu fita. In zagaya dake gidajannan ki gansu sai mu nemi gidan cin abinci muci. Daga nan kuma mu nufi Kano dan wannan lamarin bazan yi wasa dashi ba da zafi zafi ake dukan ƙarfe" Zanyi magana ya ɗaura mun yatsanshi a leɓena dole nayi shiru. Taimaka mishi nayi ya shirya muka rufe gidan muka fice ya zazzagaya dani gidajen na zaɓi ɗaya, daga nan muka shiga gidan cin abinci muka ci dankali da ƙwai da shayi kana muka ɗauki hanyar Kano. Ina ji yana waya da Hajiya yana sanar mata tafiyace ta kamashi amman yau zai dawo inya dawo zai biyo ta gidanta. Goma a cikin Dutse tayi mana sai gamu a gaban Baba Malam. Yayi farin cikin ganin Alhaji Zaidu sosai. Ashe ma Baba Malam yasan mahaifinshi tare suka yi karatu a tsangaya ɗaya. Bayan an gama gaisawa muka gabatar mishi da abinda ya kawo mu. Hankalin Baba Malam sai ya tashi ainun duk sai ya shiga damuwa. "Kayi haƙuri Zaidu dan Allah. Yanzu zansa ayi mun kiran shi Babangidan da matar tashi suzo su same mu. Duk matakin da zaka ɗauka sai ka ɗauka akai ina zuwa" Yana gama faɗar haka ya miƙe ya fita waje. Su Mardiyya ne suka fito zasu tafi makarantar boko. Suna ganinmu suka shiga murna tare da zubewa a gabanmu suka kwashi gaisuwa. "Za'a tafi karatu ba? To Ubangiji Allah ya taimaka. Bari a ƙara muku kuɗin tara" Ya zaro dubu ɗaɗɗaya ya miƙa musu suka amsa suna godiya da adda'a mai kyau. Binsu nayi waje na jaddada musu su yi mun adda'a kada su gajiya ina cikin matsala. Sun tafi kenan wayata ta shiga ruri Adama ce. Adama barka da safiya" "Barka dai lolo kinga gani nan na shigo shine muke hirarki wallahi kinji dalilin kiran. Na shigo gobe zan shigo Kano sari in sha Allah zan shigo miki" Yauwa Adama dan Allah ku tawo da Rahama da Sadiya na canja gida kayana dake can ɗayan gidan zaku kwaso mun sai mu jera a sabon gidan. Ki biya musu kuɗin mota zan baki in kuka zo" "Au har an sake miki gidan? To madallah munyi farin ciki. Nazo gidan ai nake jin me ake ciki. Babu komai ta Allah ba tata ba wallahi dukkan sharrinta kanta zai koma ke dai ki iya takunki kawai. Sai goben dai in mun shigo ɗin tare da Maigogul ma zamu tawo" Murmushi nayi nace to shikenan sai kun shigo ki gaida su Rakiya" Da haka mukai sallama na koma zauren na tadda Malam ya dawo Na zauna ban jima ba sai ga Babangida da Ƴar Shuwa sun shigo zauren. Ganinmu yasa duk sun sha jinin jikinsu musamman ita Ƴar Shuwa da tasan abinda ta shuka ba abu bane mai kyau sai tayi turus" "Ai sai ku nemi waje ku zauna ko? " Cewar Baba malam da muryar rashin wargi. Babu shiri suka zauna ni da Ƴar Shuwa sai kallon_kallo. Alhaji da Babangida ma sai kallon_ kallo Mrs Bukhari [10/24, 6:45 PM] BADA'AT IBRAHIM: MRS BUKHARI 8

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull