Kenza eBookz

Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 - Chapter 7

Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 - Chapter 7

Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 Chapter 7: Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 Chapter 7. "Kai Babangida tashi ka yo kiran Ƙarama tazo. Sabida tasan…

4,419 words

"Kai Babangida tashi ka yo kiran Ƙarama tazo. Sabida tasan cewar nayi ma matarka iyaka da yaran Sabuwa. To dake kai take Aure kaima dana haifa baka darajani ba bare matarka. Kaima dana haifa baka girmama maganganuna ba bare matarka" Alhaji Zaidu yace. "Ayi Haƙuri malam kasan ɗan yau ka haifi mutum baka haifi halinshi ba." Babangida ya kalli Alhaji Zaidu ƙasa ƙasa bashi dai da yadda zaiyi tunda a gaban Baba malam muke. Kirawo Malama Ƙarama yayi suka tawo tare, aka gaisa kafin Baba Malam yace. "Malam Zaidu ba shi Babangida ya karanta saƙon iyalinshi mu saurara dukkanmu" Ƙur Baba Malam yayi yana nazartan Ƴar shuwa da duk ta ruɗe take ta zufa. Babangida yasa hannu ya amshi wayar ya soma karantawa da murya mai kauri da farko, daga kusa da ƙarshe sai muryarshi tayi sanyi, ta ƙarshe kuma sai muryarshi ta shiga rawa har tana karkatsewa" Salati Malama Ƙarama ta soma yi tana tattafa hannunta. Hannunta ɗaya fisa haɓarta tace. "Allah mai iko da abun ikonshi. Ke yanzu Maman Fatima abinda kika zaɓama kanki kenan, ke ko wannan bita da ƙulli har ina? " Babangida yana zaune jikinshi na rawa. Ranar da muka zo gidannan da Maigogul da Ci cib ne kaɗai naga Babangida a cikin irin wannan kaɗuwar sai kuma yau da Jannaty ta taro mach. Idanunshi sukai jawur sai kallon tsana yake yi ma Ƴar Shuwa" "Abinda zan soma dashi babba guda ɗayane kafin sauran bayanan su biyo baya. Aisha kece kika rubuta wannan saƙon lambar data tura saƙon lambarki ce? " Shiru babu amsa sai rawar murya. "Ba dake ake magana ba ko saina tattakaki a nan wajen tukunna....? " Babangida yayi magana da murya mai amon maɗaukakin ɓacin rai da tsawa_ tsawa." "Kash_ sha kada ka sake magana sai anzo gaɓar da zaka amsa naka tambayoyin. Ke Aisha kada ki bari in maimaita tambayata bana wasa da yarana ma bare surukata" "Nina rubuta? " Ta faɗa tana matsar hawaye tasan Baba malam ba mutum bane mai wasa shi yasa ta amsa. Kuma dolenta ta amsa dan ruwa ya ƙarema ɗan kadane. "To shi mijin da ba naki ba a ina kika samu lambarshi, da har kika zauna kika jero mishi wannan maganganun dan ki tozarta Sabuwa? " Ƙur yayi mata Kunji tuhumar data tashi kaina. Wato Baba malam dattijone sosai wallahi madallah da uba nagartacce kuma tsayayye, mai kaifin basira. Anan tsiyar take gashi dole ta faɗa tunda tana son aurenta. "Mamanmu ce ta karɓo mun a wajen Hauwa kishiyar Babarsu Sabuwa" Dam naji gabana ya faɗi Hauwa kenan ita da Rakiya kowanne ya kafe akan halayyarshi dai sun ƙi sauka. Tun muna yara Hauwa ke haddasa husuma a gidannan. Damma bamu taɓa daka ta tata ba sai Layuza da take biye mata. "To shikenan ta zo da sauƙi ai ke kinsan mahaifin mardiyyan ko? Sai ki faɗama kotu in akaje kotu zata bincikoshi saita bashi ɗiyarshi inace shi kaɗai kike so ko? Sai mijin Sabuwa yace ya rabu da'ita ko ba shikenan burinki ba dai? Kin rabata da gidanta bai isheki ba. Sabida a sanadin shashancin shi mijinki daya Auroki yake ganin hukunci zaima Sabuwa sai kika zame mishi hukuncin shi akab_ karan kankin kanshi. Shi mugu baya cika mugu sai yayi ma kanshi mugunta. Kai kuma ai kaga irin abinda ka jama haularka ko. Tun farko da baka tsangwamar yaranka ita wannan bata isa kawo wannan maganar ba ko da kuwa hakanne. Baka tsara gidanka ta yadda matanka zasu ji shakkar ka ba, duba da yadda aka haɗu aka gina zaman babu mutunci sam a sabgar ga rashin gaskiya zuchiyoyi fal abubuwa marasa daɗi. Kuma har gobe ina faɗan Kafi Sabuwa laifi a matsayinka na ɗan malamai ita Ƴar kawali a wancan lokacin. Sannan tambayar da nake maka. Kai ɗin a haka matanka suke sakaka ka buɗe musu ƙofa suyi duk yadda zasu yi, haka sharia ta tsara, ko shariar gidanka ce ta tsara haka?" Murya a dashe sosai yace. "Wallahi Malam sha'anin Aisha lamarin taurin kanta yana da yawa. Kuma ban barta sasakai ba, ina yawan binciken wayoyinsu musamman itan. Babu abinda na taɓa gani sai dai akan ƙawaye yadda take mutuntasu yawanci abinda ke bamu saɓani kenan. Amman in sha Allah zan sake lura. Su Mardiyya kuma.... " Hannu Baba Malam ya ɗaga da sigar dakatarwa, dole ƙanwar naƙi kuwa ya haɗiye maganar daya jawo. "To ga Zaidu ya Aure Sabuwa dai, tare da sani haƙiƙanin rayuwarta ya kuma karɓeta tare da danginta kab. Maigogul daka raina shi a idanunshi Dattijone mai cikar kamala da natija. Zaidu bazan taɓa cewa kada ku maka su kotu ba. Amman in kun fahimci juna ta kawo uban yarinyar anan ma shikenan. Ke da aminiyarki ace kina bibiyar rayuwarta da irin wannan sharrin, kina mata hassada Allah na ɗaga darajarta. Yaranta sun kasance fitila mai hasken haska ahalin da zaku tara. Ina fatan addinin Musulunci yayi fahari dasu musamman ita mardiyya da kike tunanin bata da gata. Ana Aurenta da Sauban zata koma tsangayar madina da karatunta ta tafi tare da mijinta zan ɗauki nauyin komanta har digirgir sai ta haɗo kafinma ki sake ganinta. Kuma da ba dan babu kyau umarni da saki ba da yanzu zan umarci Babangida ya sauwaƙa miki. Amman bazan yi haka ba sabida nima na haifa kuma burina su mutu a ɗakunan mazajensu. Amman akan Sabuwa tunda na iya Rabuwa da Babba to Babangida zai iya rabuwa dake, kije ki saurari hukuncin da zai biyo bayan wannan abun da kika aikata dan ba ƙyaleki zan yi ba" Ajjiyar zuchiya na sauke tare da share hawayen farin ciki. Zuchiyar da bata ƙullaci kowa ba Allah shi ke taimakonta. Ƴar shuwa ta muzanta gaya ta kuma tsorata sosai Haka taita kuka tana riƙe zanina akan mu yafe mata yarinya tabbas ta Babangida ce sharrinta ne kawai. Babangida kuwa tunda ya sauke kanshi bai sake samun zarafin ɗagowa ba. "Shikenan albarkacin Baba Malam mun janye sai dai dole zamu je ofishin ƴan Sanda ayi a rubuce duk abinda ya sake biyowa baya makamancin wannan to tabbas sai anyi sharia har zuwa kotun Allah ya isa. Sannan Baba Malam dan Allah ka yafe mata ka barta a ɗakinta kada yaronnan ya sallameta gara su zauna su gyara junansu" Mugun kallo Babangida yayo ma Omri wallahi sai da na kusan dariya ma. Alhaji ya jima yana roƙon Malam kun san shi da kafiya da ƙyar ya janye hukuncin da yace zai yi matan. Dole Ƴar shuwa ta amince muka je tare harda Baba Malam aka saka hannu aka kashe kes ɗin ruf. Dama tun muna hanya ya riga yayi waya da abokinshi babba a Ƴan doka. Daga nan ofishin ƴan doka muka kama hanyarmu sai Dutse, a hanya dai mukai azahar la'asar a garin kano tayi mana. Bamu shigo gida ba saida muka biya muka ci abinci ya kaini sito ɗin Hajiya Balaraba na siyo zanin gado da senta kafet na uwar ɗaki, dana falo kana ya zo ya saukeni a gida ya wuce wajen Hajiya. Gidan Ɗorayi na koma sai gobe zan koma wancan gidan. Na dai bashi sallahun ya tawo mun da gas kuka na da silinda haka. In ya dawo mayo cefanen kayan abinci dan wallahi kayan abincin ɓarayina sun haramta a gareni da ragowar kab abinda ke cikin ɓarayin nawa su Adama zasu tafi da kaya rigi _rigi kuwa. Nasan dai zaiyi wuya ama gas kuka asiri da tukunya baya ga su ban yadda da komai ba. Ga babbar sarƙar gwal ɗina tana gidan Allah ya soni azurfar wajen Goggo tana cikin han bagi na ɗayan gwal ɗin na wuyana. Maigogul na kira a waya ban rufe mishi komai ba kamar yadda kuka sani. "Kinyi kyan kai. Nima dani za'aje ɗiban wannan kaya Sabuwa tun a cikin gidan za'a watsa musu fitsari kafin a taɓa. Na haɗo miki itatuwa da zaki daddafa ki dinga shansu tsarine da izinin Allah babu fa shirka ko kaɗan a lamarin. Kinsan dai ba'a faɗama Bararo magani ba ko? Shi kanshi gas kuka ki tottofeshi da adda'a kafin kiyi amfani dashi. Babu komai. Ita kuwa Hauwa akan wannan Abun kinji na rantse saina saketa ta ɗanɗani zafin zawarci, ina na dena barinsu Kayi nayi kaɗaima ta isheta Allah. Ita kuwa Shuwa taje dan kanta ruwa cikin cokalima ya ishi mai hankali. Abinda nake sonki dashi shine kinga tunda kin matsa gefe to sai fa dagewarki tafi ta baya Lolo. Sabida kafin mijinki ya dawo gidanki tsab za'a iya wanko mishi kai yama fitittike yace bai sanki ba, koma yace ya sakeki bafa komai bane. Bacci bai gammu ba Lolo dole mu dage muita faɗama Allah muci gaba da tuba a bisa laifukanmu na baya. Hajiya Balaraba gobe da safe zata tawo ita da ma'aikata ai miki sabon jere ni zan biya kuɗin Lolo in sha Allah." Mun daɗe muna waya kafin mukai sallama. Sai na shiga aikace_aikacen gida kuma. Alhaji Zaidu bashi ya shigo ba sai bayan isha ya tawo mana da gashasshiyar kaza, sai kayan shayi da biredi da ruwan gora da lemun gora. Kazar muka ci muka baje mukaita hirarmu, kana muka soma karatu da koyon baƙi sabida yace so yake in fahimci karatu ta yadda bazan sha wuya ba. Hanya mafi daɗi itace in iya baƙi. Bayan mun gama karatu kuma muka shiga raya dare muka wayi gari cikin farin ciki. Kuma banji wannan irin abunda na ji jiya ba da daddare na sha rubutuna na shafe jikina dashi, kuma sai dana tsarkake jikina na kwanta ina daga kwance inata ambaton Allah har bacci yayi gaba dani. Wannan kenan. Gaga_gaga da safe muka wuce sabon gidana gas kukan ma ko sakko dashi ba'ayi ba. Ruwan shayi na dafa mana a butar shayi na wuta dake Kitchen ɗin. Na ɓare sababbin kofuna a leda na ɗaurayesu da tafashasshen ruwa muka sha shayi da biredi sai ragowar kazar da muka bari. Muna gamawa muka tattara komai muka wuce. Mun yi waya da Hajiya Balaraba ma suna hanyar zuwa can sabon gidana dake unguwar Tarauni. Kusan minti sha biyar ne a tsakaninmu mun iso suka iso. "Wazirat to ni zan wuce office kawai Hajiya tace zan kawota amman sai da daddare. To zan zo in kawota in sha Allah. Me da me kuke buƙata na cefane tunda su Yaya Adama suna hanya? " To shikenan Allah ya kaimu, ashe fa yau a wajen Hajiya kake. Allah sarki ni, yau daga ni sai fulo kenan" Murmushi yayi mun ya kalleni sosai. "Shalele rigima kenan. To su kayan da su Yaya Adama zasu ɗebo yaya za'ayi dasu ne uhm? Naga ga sababbin kaya kince Alhaji Baba ya baki uhm" Hakane. To su Adama ne zasu raba a tsakankaninsu gaskiya kaji yadda za'ayi dasu. Kayan abinci kuma kayan miya nake buƙata da su nama dai haka sai ruwa da lemo" Bana so ince harda su shinkafa da mai ne ya soma zargin wani abun in kirama kaina ruwa inya fita na saka a siyo tunda akwai kuɗi a wajena. "To shikenan Abinda za'ayi zansa yara su kawo muku Shalele ni na tafi sai mun yi waya" Da haka mukai sallama ya ja motarshi ya tafi. Gas kuka kuwa kamar yadda Maigogul yace sai da na tottofeshi fes kafin na wankeshi tas da ruwa a tsakar gidan. Hajiya Balaraba kuma tana ciki tare da ma'aikata tana basu oda. Ma'aikatan nata na tura kasuwa suka siyo mun kayan hatsi komai da komai. Da yaran Alhaji suka kawo cefane sai na tashi girki. Gaga_gaga cikin awa ɗaya da rabi aka gama komai falo ya ɗauki fasali har turarukan B4B gidan ƙamshi ta kuma kawo mini box guda kuma tace dani show glass yana tafe. "Naji labarin komai. Kinga munubiya tun muna makaranta macace mai son mulki da son kanta sosai, gata da mugunta hatta a kalaman bakinta babu alkhairi sam. Wannan dalilin yasa bana cikin sabgarta kwata kwata ai na faɗa miki. Adda'a zaki riƙe babu mamaki wa'adinta ne yayi. In kuma da rabo sai kiga kin haihu dashi ke ɗin. Allah Ameen da munyi farin ciki Hajiya Sabuwa" Gaga_gaga da misalin ƙarfe biyar na yamma sai ga motar kaya tare da motar su Maigogul. Mu muka buɗe musu get aka zube kaya kwatsar a tsakar gida harda suturun dake sib dana akwatinan da Hajiya tayi mun dan ba kayan ciki kaɗai ba har akwatin banso wallahi. Sai dai fa sarƙar gwal tayi layar zana basu ganta ba sam. Magazin da Ma'aru ma sun biyosu, a mata Kuma Adama, Labbai, Rahama, Uzairu muzuru da Gaza yace ayo gaba dashi harda sarƙa aka saka mishi a wuya sabuwa. Ƴan uwa masu daɗi sai naji sun zabtare mun rabin damuwata. "Wannan kayan gado dai zasu koma show Room in da ciko sai in yi ma Hajiya. Ragowar karikicen Kitchen da suturu, da kayan abinci, da waɗannan kayan fulawa na biki kuma rabon su Adama ne sai su wauwanke su shanya duk su bushe dan fitsarine linkib a jikin suturun. Kuma harda laya gata a ƙarƙashin gadon lolon muka tarar harda sunan lolo da sunan Alhaji Zaidu a cikin baka kun ganta" Maigogul ya ciro baƙar leda a aljihunshi ya warware mana muka ga layarnan jikina yayi sanyi ƙalau wallahi." Sai da suka gama wauware kaya suka kasafta tsab suka wanke hannuwansu muka shiga ciki muka baje aka soma liyafar cin abinci sai santin gidan suke yi dan gaskiya gidan yayi ga falon yayi biyun wanda na baro haka ma ɗakunan tabka tabka komai a yalwace. Ɗakina kaɗai aka saka kayan gado ragowar ɗakuna ukkun a haka aka barsu sai kafet malala a ciki kawai dama a ciki muka taddasu. Bayan magriba sai ga Alhaji Zaidu shi kaɗanshi da leda mai zane shaƙe da banƙararrun kaji da jus_jus ya shigo, amman shi shi ɗaya yazo shi banda Hajiya ko me ya faru oho dai. Haka ya shiga cikin dangina yana ta murnar ganinsu tare da martabasu a yadda sukensu. Ya ɗan jima kafin yayi mana sallama akan sai gobe da safe zai zo. Na bar maganar gwal ne akwai gaɓar da zanyi mishi maganar in ya dawo gidana kafinnan ya nitsa. Ni da Maigogul mukai mishi rakiya zuwa gaban motarshi. "Dama akwai wasu saƙe saƙi dana sassaƙo muku a jeji da hannuna na haihuwane. Lolo sai ta dafa muku ku dinga sha musamman kai ka zage ka kakkaɓa muna sa ran in sha Allah za'a dace. Kasan da nayi harkar bada magungunan kurga, da amagyagya na yara, to bada taimakonma na taɓa wallahi denawa dai nayi" Ya ƙarashe yana dariya. "Mungode sosai Alhaji Baba. Matsalar ma daga garenine ina kyautata zato zan kuwa zage in sha in sha Allah. Kuma wallahi naji daɗi sosai a baya ma duk na sha daga baya ne na watsar." "Hahahahhh babu komai. Sai dai gaskiya kullum ake so a sha shi babu fashi duk da kullum zaku haɗu babu matsala tunda wajen aikinku guda ko. Ai haiƙan zakai ta sha za'a dace da izinin Allah. Itama fa mai ɗakina Hauwa wallahi na saketa sabida ba ma Babar Ƴar shuwa lambarka da tayi. anyi rikici a gidan sosai, harma shi babban ɗan Hauwa Masa'u wai zai sassareni ko ya turo a sace ni. To ni dariya ma ya bani, Allah na tuba wanne iya shege ne bamu gani ba. To ita Uwar taku dai har gidan uwar Ƴar shuwa taje aka raba garin tsiya, mu dai rigima bata lafa ba har yau ɗinnan. Itama Ƴar Shuwan wai ta dawo gida, ko da takadda, ko hutu aka turota tayi ba dai mu sani ba. Ka dai sake haƙuri dan Allah" Alhaji Zaidu yace. "Ashsha Alhaji Baba. Ko dan albarkacin yaran da an duba ba'a saketa ba. Ayi haƙuri a mayar da'ita dan Allah. Aba Mama Haƙuri itama duk a huce babu komai wallahi." "Ai fa baka sani ba Gaza har gidan Malam Habu ya burma dake ya raka ita uwar tashi, shi dama ba sonmu yake yi ba, ana faɗan ya fito yana aibatamu dawa Allah ya haɗashi da Gaza.. " Maigogul dare yayi ka barshi ya tafi" "Rai a ɓace Omri ya dubeni harda hararata, amman ta gargaɗice. " Toh hakane Alhaji da Alkhairi" Maigogul dai ƙin bamu waje yayi tare muka koma ciki Sai wajajen goman dare Maigogul da Hajiya Balaraba suka tafi Uzairu zuchiyata yace a barshi zuwa jibi in su Adama sun tafi ya dawo. Ai suna tafiya muka dasa hirar rikicin Hauwa da Maigogul da Kayi nayi. "Ke anyi abu. Kayi nayi har waje ta ja Hauwa suka fita dambe da ƙyar maƙota suka raba. Layuza dake bata da mutunci tace yau ɗinnan zata kama ma Hauwa gida su koma gabaki ɗayansu ke kiji neman fitina. Masa'u kuwa saida Gaza ya karza wuƙa yaga tayi walƙiya sannan ya fita a gidan. Cacar baki sukaita tatayi da Maigogul." Rahama ke bamu labari. Labbai da Uzairu zuchiyata kuwa kun ga dariya wai kuwa haɗe kai suka yi sukai ta ƙyaƙyatawa. Adama tace. "Rakiya ta ƙarama rigima maggi. Wai Gaza ne yai nata Rakiya layinmu na da. Ta faɗa gidansu Ƴar shuwa shi kuma ya faɗa gidansu Malam Habu daya fito yana ƙananun iskanci Suka raba abun kunya dai in faɗa miki dattijan anguwa dana maƙotan unguwama da ƙyar suka raba rikicin. Ƴar shuwa dai ana raɗe raɗin Babangida ya saketa amman babu tabbas gaskiya." Kunsan mune har biyun dare muna musu da dariya. Sai wajajen biyu da rabi Uzairu zuchiyata da Ma'aru suka shige ɗakin hagun ɗakina suka bi kafet sukai kwanciyarsu gida to babu. Su Labbai kuma gado suka haye, ni kam sai da nayi sallah na sha maganina na shafe jikina kafin na yi kwanciyata a ƙasa su na basu gadon sai tusa Adama take sakar mana ta cika ɗakin fal da wari. Murmushi nayi na tuno shekaru talatin baya a lokacin duk muna gida muna irin wannan gwamutsuwar ta bacci muita tusa abinmu. Rayuwa kenan. Gaga_gaga sai da muka kwana biyu cur dasu Adama, washegarin ranar da suka zo suka tafi kasuwa ai kuwa Labbai ma ta samo gyaɗa mai sauƙi rabin buhu ta siyo, Adama tayi tsince_tsincen kasuwancinta su Rahama kuma suka zama ƴan rakiya da su Uzairu zuchiyata daya aro motar Mum ta wajenshi. A ranar ƴan Rano a gidana suka wuni cur mukai zumunci sunata santin waje sosai. Washegari kwana biyu kenan su Rahama suka tattare kayayyakin dana rabar musu suka kama hanya Omri yai musu goma sha tara na arziki Maigogul ya kaisu har tasha. A kwana biyun na dafa mana magungunan haihuwa da Maigogul ya kawo mana, in Omri yazo da safe sai ya cika kofi tam ya shanye nima yace in sha ko babu komai zai gyara mun mahaifa tunda mahaifar dama tana da matsala. Da yamma ranar da Omri zai dawo gidana a ranar da su Adama suka tafi. Na gama komai na gyare gidana na banka ƙamshin turare, girkina na kammala na jera komai a ƙasan kafet ina gaban mudubi sai naji anata doka get wani irin duka da rashin mutunci dai. Hular dake ajjiye a gaban madubin na saka. Ina saye da riga da wando na kanti sun kamani tsam, fuskata na caɓa ado ga wannan azurfa a kunne da wuyana. Sanin babu mai gadi a gidan yasa na fita a yadda nake. Ƙofarnan dukanta akeyi. Waye yake buga ƙofa haka? " Hajiya munubiya ce. Kina ciki anata buga ƙofa bakya ji? " Sakatar ƙaramar ƙofa na ɓalle muka haɗa idanu da'ita tana tsaye da ƙawarta, ga motarsu a bakin ƙofar gidan. Haɗa idanunmu sai naji kaina ya sara na ɗanji juwa kaɗan. "Ko zaki iya buɗe mana get mu shigo da mota? " Inaga sai dai ku barta a wajen bazan iya buɗe wannan ƙaton get ɗin ba" Hajiya Mansa ke magana cike da taƙamar da zaka rantse itace a matsayin Rakiya ko Maigogul. Sai ita Hajiyace tace. "Bari mu bar motar anan. Ai ba zata iyaba" Waje na basu suka shigo na rufe gidana nayi gaba suna bayana. Har muka shige cikin falon. Numfashi naji Hajiya ta ja mai nauyi sosai. Ruwa na kawo musu na zauna aka gaisa babu yabo babu fallasa. Sai tambayoyin ina kayana suke to, taga na sake wasu yaushe yaushe da Aure. Ta leƙa Kitchen ta leƙa ɗakunan dake tsakiyan nawa, zata buɗe mun ɗaki na riƙe abun buɗewar nace. Nan ɗakin mijinane Hajiya" Sai ta wayance dai mukai dariya. Ko dana basu abinci basu ci ba, bafa su daɗe a gidan ba amman a ranar na shiga sabuwar jarabawa kunji wata ƙaddarar ko? Rimi_rimi Alhaji ya dawo muka tarbi juna cike da farin ciki muka ci abinci akai komai fa. Wallahi a wannan daren ni dai ƙaramar hauka nayi na dinga ihu ina fisgewa zan fita daga ni sai rigar bacci duk na firgice. Da Alhaji ya riƙeni sai nayi kukan kura na danna ihu in shaƙeshi da ƙyar zai ƙwace yana yi yana adda'a yana tofa mun. Wallahi kafin asuba duk na jij ji mai ciwo maƙota kuwa duk sun san abinda ke faruwa damu. Ana ƙwala kiran assalatu wallahi Allah sai naji kamar abu ya fita a jikina sai na dawo hayyacina. Ganin Alhaji duk na yakushe mishi fuska nima duk naji ciwo ga jikina duk tsami sai na fashe da kuka na faɗa ƙirjinshi. Kunji fa wata ƙaddarar. Haka ni dashi muka rufe na ranar farko, ya shirya muka tafi aiki tare, kafin muje aikin sai da muka je naga likita a wani asibitin kuɗi, magunguna dai ya bani bayan ya mun tambayoyi da gwaje_gwaje, sai muka wuce wajen aiki muka wuni lafiya. Da misalin shidan yamma muka dawo, muna shigowa ban zauna ba na shiga Kitchen. Zuwa bayan isha na sarrafa mana shinkafa da miya. Muka ci, na sha magunguna mu kai shirin kwanciya. A wannan daren abinda ya faru da irin ihun dana dinga yi wallahi saida maƙota suka fito. Ya fita ya samesu ma ya kasa. Abubbuwa a haka suka ci gaba da tafiya dole saida Maigogul suka san halin da nake ciki har Baba malam. Sai aka alaƙanta hakan da aljanune suka shafeni nan kuma hankula suka tashi na shiga shaye_shayen magani afujajan. Sai Rahama ce ta tawo ta zauna dani a cikin gidannan. Amman Maigogul da Baba malam basu zauna ba, Baba malam har sau biyu yana zuwa dubani, ina shan rubutu Ina sauraren Qur'ani, Alhaji Zaidu yanai mun tofi duk kwanan duniya. Ga saƙe_saƙin Maigogul da wasu magungunan karya sihiri. Amman wallahi ciwo sai girmama yake yi, da safe fa amma babu wata matsala sai da daddare ciwo yake tashi. Amman da Baba Malam yayo mun wasu rubutu ya kawo sai na dena ihunnan da fisgewa, amman fa nike nan firgita da ƙanƙame Rahama ko Omri in ranar kwananane yazo ga mafarkai masu tashin hankali. Kuma wani ƙudurar Allah da Hajiya da dangin Alhaji basu da masaniyar halin da nake ciki, ko da yake ita tafi kowa sani tunda ita tayi. Sai dai duk wanda ya ganni yasan banda lafiya idanuna sun firfito sosai. A haka bikin Uzairu zuchiyata yazo ina babu dama inaji ina gani akayi shagalin da akayi bana wasa bane. Sabida rashin lafiyata babu wanda ya iya raka Uzairu zuchiyata Canada hankulan dangina yana kaina kacokam Ita kanta Mardiyya biki ya ƙarato jikina ba daɗi sam. Gaza ma gari gari yake zuwa karɓo mun magani, amman abinda na yadda dashi lokaci Allah ya arama Hajiya. Akwai lokacin da ko ban sha komai ba zan warke da izinin Allah. A dangin su Alhaji dai wani biki suna ina daurewa in shiga taron a hakan, tunda ba magashiyyan nake kwance ba, ba dan faɗawar da nayi ba babu mai gane ina cikin halin ciwo ma, Goggo Amfana ita ma ciwonta ya tashi bata gane ma wake kanta baiwar Allah. Ita kuwa Hajiya da ka kalli fuskarta sai kaganta a cikin farin cikin ganin halin da nake ciki. Kana kallon makashinka baka da abinda zaka yi mishi wata shari'ar sai Allah. Tazo gidana a ƙalla yafi sawu goma tunda ita ba za aci gaba da ɓoye mata banda lafiya ba. Har ranar da suka haɗu da Anty Tani itama tazo Rahama ke sanar mata banda lafiya. Da Hajiya tazo sai Anty Tani tace. "Koma menene yake faruwa da matan Zaidu mu mun barma Allah ne bawai dan bamu da hankali ba" Ƙus Hajiya tayi ba amsa. A haka bikin Ƴan Tagwayen Anty Tani yazo daf dana mardiyya Sadiya ce ta rakani muka je akayi komai dani a daddafen. Da bikin Mardiyya yazo Alhaji sai ajjiye aiki yayi ya biyoni muka tare a hotel dan kawai ya kula dani. Allah sarki bawan Allah baya nuna gajiyawarshi sam wallahi. Haka akayi bikin Mardiyya a gidansu Baba Malam. A lokacin ma na ɗan ciko na sake haske ashe ɓoyayyen cikine a jikina babu wanda yasan da bawan Allah. Kunji ƙaddara a cikin ƙaddara ko? To wannan ciki yasa nayi kyau babu laifi haka muka shiga cikin su Sa'a akayi biki. Su Adama ne akan komai ni sai ido ga ciwo ga laulayi gashi bana son shiga mutane sam. Su Hameeda sune iyayen Amarya da su Sumy da Hala duk mun haɗu dasu gaisuwar mutuncice ta rabamu, Ƴar shuwa da danginta kuwa babu mutum ɗaya ma. Kwana biyu akayi aka gama biki duk abinda uwace ya kamata tayi to Alhaji Zaidu ya fansheni an yi mata komai Aure na gata sosai akayi mata. Baba malam yayi rawar gani, haka shima Babangida ya fitar da'ita kunya sosai. Ta tare a gidan mijinta daya gina nan kusa da su Sa'a Malama Babba ma naga duk ta rame tayi duhu wannan isar duk babu ita Rayuwa kenan kayan Allah. Maigogul dai kusan kullum sai yazo ya kawo magani ko yazo ganina. Ranar Juma'a ina zaune a falo na gama sheƙa amai na fito na zauna jagwab sai muka jiyo sallamar Maigogul ƙur yayi mun. "Lolo naga cikin ki kamar ya ɗaga kumburi yayi ne? Sai ni da Rahama mukai saurin duban cikin Rahama ta latsa sai ta zabura. "Maigogul ai cikine da'ita" "Tsarki ya tabbata ga Ubangijin kowa da komai" Mrs Bukhari ce [10/27, 8:49 AM] BADA'AT IBRAHIM: MRS BUKHARI 9

Kunyi ready ku koyi skill ɗin da ke kawo kuɗi! Idan kuna son ku iya yin voice over kamar masu tallace-tallace, ko ku iya video editing kamar professionals - to wannan class ɗin naku ne! 💪🏽

📚 Za ku koyi: 🎧 Voice Over (recording, editing, delivery) 🎬 Video Editing (cuts, transitions, subtitles & more!) 💻 Practical + Real Project Training

📍 Location: [TELEGRAM ]

Payment: 9163354359 Sa'adatu Adamu Opay

Send receipt via 📞 Contact: [07044292865] 🗓️ Registration ongoing - Limited space available!

💥 Kada ka tsaya jiran lokaci - ka shiga yanzu

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull