Kenza eBookz

Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 - Chapter 8

Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 - Chapter 8

Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 Chapter 8: Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 Chapter 8. Da mamaki nake kallonsu dana ji sun ambaci ciki. "Rahama…

4,086 words

Da mamaki nake kallonsu dana ji sun ambaci ciki. "Rahama abun nema ya samu zama bai gammu ba. Lolo maza ɗakko mayafinki kizo muje asibiti a duba cikin muga na wata nawa ne." Amman Maigogul ba zaka bari muje da Alhaji ba, gashi su Rakiya da Hauwa suna hanya duk yadda akayi ma sun kusan ƙarasowa" "Dake baki da hankali ba ai dole kice a faɗa ma Alhaji. Kubi komai a sannu duk abinda na tsara shi za'a bi ku nutsu. Taso muje maza zan faɗa mishi mun fita" Haka Rahama ta ɗakko mun hijabina ta saka mun. Saifa data taimaka mun kana na miƙe tsaye ciwo ya cinyeni a tsaye. Asibitin kuɗi muka je aka Auna ciki wata har huɗu cib. Kuma wallahi inajin motsi kaɗan_ kaɗan haka amman dake halin ciwo nake ciki, al'adarma da banyi ba daga ni har Rahama bamu tuno komai ba ana ta lafiyata. Muna asibiti su Rakiya sukai kiran Maigogul sun iso Kano. A lokacin Hauwa basu daɗe da dawo da Aurensu ba. Alhaji Zaidu ne ya tsaya tsayiwar daka da shi da Gaza har suka shawo kan Maigogul ya amince ya dawo da Hauwa kafin iddarta ta cika. Tasha muka wuce muka ɗakkosu ɗaya daga cikin atampar da Hajiya ta saka mun a akwati itace a jikin kayi nayi harda gyalenta to mach da ɗan ɗankunnenta ƙarami na gwal data siya daga cikin arzikin sana'ar kayi nayinta. "Baka da aiki sai yawo da Ƴaƴa raɓe_ raɓe damma kamar kumbon naka yana can canada. Jiya ma ya kira mun daɗe muna magana dashi." "Ai ke ba'a rabaki da takalar faɗa da maganganu. Shige muje muah dallah" Motar suka shiga muka nufi gida. A falo duk muka baje Rahama ta kawo musu lemo da abinci. "To yarinyarnan lolo zamanta ya ƙare a gidannan na ɗan lokaci gaskiya dole zamu tafi da'ita dole ne wannan" Da sauri na kalli Maigogul Rakiya nama cike da bakinta tace. "A wanne dalili mijinta shi ba cewa yayi ya gaji ba, shi ba nunawa yayi komai ba. Sai kaine sabida ka samu waje zaka ce haka? Kada ka mance yafa biya mana aikin Hajji dani dakai har da lolon zamu je. Kada kayi abinda zaka yi mana salesalin tsiya wallahi. Ka bar yarinya a gidan mijinta, ai ita makirar sai tayi tunanin taci galaba a kanta ma" Numfashi yaja ya sauke. "Rakiya lolo cikine da'ita kin ganshi wata huɗu. Ganinmu da kika yi daga asibiti muke ko mijin baisan da cikin ba. Kuma ba sani zai yi ba lalata mana shiri zaiyi dan fasa abun zaiyi kowa yaji halin da ake ciki. In labarin cikinnan ya isa kunnen Hajiya to bamu san a wanne irin hali ita lolo zata kasance ba har dama cikin. Ki duba tulin tarin dukiyar da Alhaji ya tara ko iyakar kamfanin motocinshi ai shi kaɗai arzikine jibi Gaza lokaci guda ya canja. Sukenan a sintirin shigo da motoci suke. Ke ya kike ganin in Munubiya ta samu labarin wannan cikin Sabuwa ita ya zata kasance? Wallahi a irin baƙin ranta zata iya kasheta da abinda ke cikin wa akayima asara ba mu ba? Kinji wannan dalilin ne yasa dole lolo ta bar gidannan tun kafin Hajiya da dangin Alhaji Zaidu su ankare da cikin jikin Lolo labari ya shiga family house a cucemu" Ai duk sai muka tsorata muka gamsu da Maigogul. Hauwa ya ƙurama idanu Ƙur saida ta sauke kanta ƙasa tsabar kaifin idanunshi. "Hauwa idan wannan labarin ya fita nasan kece dan duk wajannan babu bare. Wallahi in kika fitar a bakin ragowar igiyoyin Aurenki dukka" "Bafa zata faɗa ba ma ai tayi laushi Hauwa sosai. Kuma makarantar su Mardiyya da muke zuwa babu laifi muna jin karatu. Rubutune Baba malam ya ɗauke mana dan mun kasa daga ni har itan, inma ta faɗa ni kaɗai na isheta riga da wando ai. Amman shi mijin lolon mai zaka ce mishi mu tafi da Lolon to ga azumi saura kwana biyu fa a soma tafiyarmu aikin Hajji ya kusa? " "Lolo ai ba lafiya bane da'ita yau ai anan yake ko Lolo"? Kai na ɗaga mishi halamun eh. " Ciwonne zaki nuna mishi yayi tsanani gaskiya ni kuma gobe sai inzo in koro mishi bayanin zamu tafi muyi jinyarki a gida ba shikenan ba? " A haka aka tsayar da zancan Maigogul ya tafi ya barmu muka ci gaba da tattauna matsalolin rayuwa iri_iri har dai Alhaji Zaidu ya shigo da tsiranshi him ya kawo ma su Rakiya aka gaggaisa ya shige ciki. "Tashi ki bishi maza, kin dai ji abinda Maigogul yace miki, kibi abinda yace miki sabida rayuwarki ake dubawa zaki iya rasa ranki in cikin kaɗai ma zaki rasa ai da sauƙi. Rahama miƙo mun wani tsinken tsiren. Ashe haka kuke cin daɗi? " Ni dai haka na shiga ɗaki na taddashi yayi shiru a zaune a bakin gado yana ta aikin tunani. Zama nayi a kusa dashi ya dubeni da kyau yace. "Wata rana sai labari ina fatan Allah ya baki lafiya. Goggo Amfana tace in gaisheki da jiki daga can wajenta nake taji labarin ciwonki. Yau tayi mun maganganun da suka tsaya mun a zuchiyata. Amman zanyi bincike da kaina in gano. Muddin abinda ta faɗa ya tabbata zuchiyata ƙila bugawa zata yi" Ajjiyar zuchiya na sauke kawai bance mishi komai ba na fita na kawo mishi abincinshi. A wannan daren ƙaramin hauka nayi na gangan harda sambatun gangan duk saida na tashin hankalin kowa. "Wannan ciwo na yarinyarnan dole fa sai an tafi da'ita neman magani zamanku haka bazai yiwu ba. Rahama riƙota muje ta kwana a cikinmu shima bawan Allah ya samu ya runtsa." Cewar Rakiya. Rahama ta riƙo hannuna muka shige ciki shi dai kusan a tafe ya kwana tsakanin ɗakinmu da ɗakinshi har garin Allah ya waye sassafe sai ga Maigogul harda Ci cib sun zo suka gabatarma da Alhaji zasu tafi dani. "To Alhaji Baba da dai an daure an barta dan Allah ai ina ganin duk maganin da za'ayi mata za'a iya mata anan. Ko nawane zan iya kashewa mai maganin yazo nan gidan yayi mata magani. Bana so ta bar gidanne" Sai ya mugun bani tausayi har rama yayi fa, ni kuma nayi likimo a kafaɗar Rahama idona ma a rufe ina hawayen baƙin ciki. "Kana ji Alhaji? Wannan ciwon dole sai mun tafi da Sabuwa sabida lafiyarta. Mu da so samu ne ma a haƙura da auren kaga fa a irin halin da take ciki" Cewar Ci cib ai Alhaji Zaidu dajin haka saiya amince a tafi dani maganan batun saki babu shi. "Amman wanne garinne za'a kaita maganin, sannan dani za'aje inta warke na dawo." Maigogul yace. "Ai tare da Rahama da Adama zasu tafi. Mai maganin macece maza basa zuwa gidanta kadai yi haƙuri zasu tafi in sha Allah inta warke nan da watanni zata dawo ɗakinta ni da kaina zan dawo da'ita. Can Agadez ne acan mai maganin take sai dai haƙuri Alhaji a yi haƙuri ƙaddarace" "To shikenan Allah ya bata lafiya bazan yi jayayya daku ba. Duk wani gudunmawa in sha Allah zan bayar ko da duk abinda na mallaka zai ƙarene. Kuma zansa aita mata sauka in sha Allah. Allah ya baki lafiya ɗorarriya Shalele." Saida aka gama haɗamun ƴan kayayyakin da zan buƙata na shiga na sameshi a tsaye idanunshi yayi jawur yana ta kai mari yana kai gwauro. Ina zuwa saina rungumeshi na fashe mishi da kuka wallahi. Dake jarumine sai ya shiga rarrashina yana bani kalma. "Shalelena Allah yana tare dake yana sane dake. Wannan wata jarabawane Allah yake mun akan matan da nake Aure domin ya gwada imanina. Ina hango sanda ko wacce ake fita da'ita cikin halin ciwo. Daga wannan tafiyar shikenan sai Aure ya ƙare. Gashi kema har an soma mun batun mu rabu. Allah ya bani komai na dukiya duk abinda na taɓa da hannuna Allah yana sama wannan abun albarka. Sai ya jarabceni da rashin samun magaji, ya kuma jarabceni da rashin kwanciyar hankali. Amman in sha Allah Goggona ta haskamun wani duhu daya daɗe a rayuwa da sannu zan gano bakin zaren. Shalelena ki kula da kanki, dan Allah duk tsanani da zafin ciwo kada ki bari a rabamu mutuwa zanyi in kika rabu dani. Bazan ɓoye miki ba wallahi a kaf matan da na rayu dasu nafi sonki da ƙaunarki sama dasu matsayinki na dabanne" Saina ɗago nace. Har Hajiyanka wacce ka yadda da'ita sama da kowa? " Cikin ƙarfin guiwa yace. "Har ita Shalelena sabida Hajiya a halin yanzu tabbas akwai ayar tambaya a kanta. Lokacine zai bayyana komai" Mun jima muna ma juna alƙawarurruka kafin daga bisani Maigogul ya ɗaukemu a mota muka tafi. A tsaye muka barshi a bakin get yana ɗaga ma motarmu hannu. Idanuna ƙur a kanshi sai nake ji kamar ƙarshen haɗuwata dashi kenan. Muna tafe ina kuka har muka iso Dutse. Ƴan uwanane suka tarbeni dukkansu muka shiga ciki, ciwona a wannan daren yayi tsanani sosai a hakan washegari Maigogul ya kwashemu zuwa Malam madori tare da kayan abincina da duk abinda zan buƙata har miyar situ yayi mun mai yawan gaske. Shi da kanshi ya roƙi mijin Adama akan zan zo in zauna nayi jinya anan kuma ya amince. Da Rahama muka zauna su Maigogul su kai mana sallama akan duk Juma'a zasu dinga zuwa su dubani Kunji fa halin da nake ciki. Gaga_gaga_gaga

BABANGIDA:.

Abubuwa da yawa sun faru a ciki harda haihuwar Ƴar Shuwa da tayi a gidansu da Haihuwar Hala, Sumy da Hameed kuma suma suna ɗauke da juna biyu anata laulayi. Tunda Ƴar shuwa tayi wannan abun Babangida ya korata gidansu sai dai yana ciyar da'ita yana shayar da'ita. Data haifi yarinyarta ma mace yaje ya dubasa sannan duk abinda uba yake yi yayi ƙoƙari yayi mata tsiransu sati biyu da Hala. Duk da kuɗin daya kashe wajen bikin Mardiyya hakan bai hana yayi bajinta ba. Sai dai labaran almara sun iso mushi dangane da labarin yadda sunan Ƴar shuwa ya kaya da irin manyan matan da suka halarci bikin da irin kayan data saka, kama daga irin gudunmawar data samu, da irin abincin da akaci alhalin ansan iyayenta ba masu dashi bane. Bayan suna da ɗan lokaci Baba Malam yace da Babangida horon ya isa haka ya dawo da matarshi. Dama ƴar shuwa sun yi asirin sunyi bikon babu abinda basu yi bama akan ayi suna a gidanshi yaƙi fur gashi ita duk duniyar data samu burinta dai ta rayu a ƙarƙashin inuwar Auren Babangida. Duk da tasan a halin yanzu babu soyayya sam a tsakaninta dashi dan ko fara'a bayayi mata. Tsautsayi bayan ta dawo gidan Babangida da kwana biyu sai tafiya China ta taso mishi sunyi sallama akan daga office zasu wuce. Ƴar shuwa tana zaune a Kitchen tana soya miyar kaji ga ɗiyarta a kan cinyarta tana shan mama da misalin ƙarfe biyar na yamma. Ɗakinta yasha gyara har fenti da sababbin kayan ɗaki saida ta sake damma tana tsoron tuhuma da abinda zata yi sai yafi hakan bajinta. Kwatsam ta jiyo sallamar Zarah ta shigo suna gaisawa da matan gida. Da sauri ta ɗago suka haɗa idanu. Fushi take yi da zarah tun ranar data kirata a waya wata budurwa ta ɗaga har suka zazzagi juna, to tun daga ranar Ƴar Shuwa ta kashe wayarta dalilin zuwan Zarah bagatatan kenan. "Aiki kike yi my love? " Zarah ta tambayi Ƴar shuwa. "Umm shi nake yi. Me yasa kika zo kinsan halin da nake ciki a gidannan auren sai girgiɗi kawai yake yi" Zarah bata ce komai ba ta shige ciki itace har uwar ɗakin Ƴar shuwa kan gado. Ita kuma saida ta sauke miya ta mayar da tukunya kana ta shiga ciki. A ƙasan kafet ta ajjiye yarinyar cikin gadonta na yara dake falon ta shiga ta samu Zarah. Dake duk cikin kewar juna suke sai suka farma junansu dama shi tsautsayi baya wuce ranarshi. Ranar tonan asiri itace rana mafi tsoro tare da nadama maras amfani. Kwatsam sai ga Babangida ya dawo gida tafiya bata yiwu ba. Dake dubun ta cika ba makawa yau ƙofarta a buɗe take, kuma shi kanshi Babangida da majalisa zai leƙa sai yayi isha sai ya shigo sai yake jin yana ɗan jin halamun mashasshara. Yana saka kafarshi ya shiga falon sai yaga yarinya ita kaɗai tana ƙananan kuka har zai ɗauketa sai yaji ihu da nishi a ciki. Ƙirjinshi ya dafe ya duba agogo da sauran lokaci kafin magriba tayi ma, to ihun waye a ɗaki da irin wannan nishi? " Sai ya soma bin hanya nishi na ƙaruwa da ihu dai har Allah ya bashi nasarar riskarsu. Ƴar shuwa tana ƙasan Zarah tana sha wa'iyazubillahi Zarah na ihu gasu tsirara haihuwar uwarsu da Ubansu. Ai take jikin Babangida ya shiga kakkarwa yana kaɗuwa yana jin wani irin juwa na ɗibarshi. Da bango ya jingina hawaye na zubowa a idanunshi. Lallai shi zina bala'ine ta ko wanne siga. Yau ga sakamakon zinar daya ta aikatawa a kan gadonshi Matarshi da mace suna maɗigo akan gadonshi na sunna yana kuma tsaye yana kallo. "Allahumma ajirni fi musibati.... " Suka jiyo muryar Babangida da wani irin amo mai kauri. A zabure Zarah ta ture Ƴar shuwa tayi saurin zura doguwar rigarta ta fice a guje jakarta na falo dama ta sura ta fice da gudu. Kallon Ƴar shuwa Babangida yake yi jikinshi na rawa. Ai batai aune ba ya afka mata da duka da zagi da hauka yana yi yana tarwatsa kayan ɗakin dama yasha gyara. Harfa saida matan gida suka zo. Suna shigowa da zummar ceto in suka ga yadda take sai su koma. Amman wallahi da duka yayi duka zanin gado ta jawo ta ɗaura ta fice da gudu taga yana shirin kasheta. Fita yayi baya ko ganin gabanshi kai tsaye sai wajen Baba Malam yana zaune a kujera ya gama ɗaura alwala kenan acaɓa ya sauke Babangida a ƙofar gidan. Dubu ɗaya ya miƙa ma mai acaɓar bai tsaya neman canji ba ya tunfari Baba malam zaman daɓaro yayi a gabanshi ya ɗaura kanshi a tsakankanin cinyar Baba Malam ya fashe da kuka jikinshi na wani irin rawa na fitar hayyaci yana cewa ya yafe mishi ya tuba ya gafarta mishi. Shiru Baba malam yayi yana sauraren amon kukan Babangida yana ratsa mishi jiki. Allahu Akbar yau ɗaya sai Baba Malam ya ɗaura hannunshi a kan Babangida yace. "Dena kuka Baban masu gida. Kaita ambaton Allah inka nutsu sai ka sanar mun damuwarka" A haka Kawu Manga yazo ya iske Baba Malam yana shafa kan Babangida ta shigar rarrashi. Ai kujera kawai ya ja zai zauna Baba Malam yace. "Manga ɗaga Babana ku je ya kwanta a ɗakina ganinan zuwa" Da mamaki a fuskar Kawu Manga Amman babu halin magana. Haka yasa hannu ya ɗago Babangida suka shiga ciki. Baba malam yace. "Allah ka shiga cikin lamarin yaronnan ya Allah ka taɓa. " Yana gama faɗin haka ya yafito magajin malam ya umarceshi ya bashi tawada da allo da alƙalami. Nan da nan malam ya rubuce ma Babangida wasu ayoyin Qur'ani ya wanke a ƙoƙo ya shiga mishi dashi. Babangida yana ciki a kwance idanunshi ɗaya na hawaye. Zama yayi a bakin gadon. Kawu Manga kuma illahirin mamaki ya hanashi ko da motsawane. "Babana tashi kasha rubutu ka shafe fuskarka da kanka dashi. Da dukkan halamu wani abun kaci karo dashi ya birgitaka tashi. " Tashi Babangida yayi ya amshi rubutunnan ya kafa kai yasha ragowar ya muttsuke a fuska da kanshi. Malam ya kamo kanshi ya dinga mishi tofi yana hura mishi iskar a kunnenshi sannu _sannu har saida nutsuwa ta saukarma Babangida. Wallahi sai ya rungume uban ta baya ya ɗaura kanshi a kafaɗar uban. Baba malam ya lumshe idanunshi yana jin kewar yanayin sosai irin shaƙuwar dake tsakaninshi da Babangida ba shaƙuwa bace ta wasa. Wata iriyar soyayyace daga Allah a tsakaninsu ga tsananin kamanni wanda ko ƴan biyu iyakar ƙarshen kamsnnin da zasu yi kenan. "Manga kaga ɗanka ko? " "Na ganshi Yaya kome ya sameshi oho da muka shigo baka ga yadda jikinshi yake rawaba wallahi." "Baba sakko ka sanar damu abinda ke damunka lokacin sallah yayi." A hankali Babangida ya sakko ya gurfana a gaban iyayen nashi kanshi a ƙasa. "Baba malam ka yafe mun dan girman Allah ka kuma yafe ma malama Babba a bisa saɓa umarninka da muka yi. Haƙiƙa ruɗin abokai da kururuwar shaiɗan su suka sanya na faɗa rayuwar da bata dace dani ba. Nasan na cunkusa maka baƙin ciki mai tarin yawa amman ka yafe mini ko zan samu haske fishinka masifane da bala'i. Duk da Allah yaga zuchiyata na tuba ina mai ƙyamatar rayuwar dana aikata a baya. Amman shirunka yana ƙona ruhina da gangar jikina a yafe mana dan Allah" Ajjiyar zuchiya Baba malam ya sauke tare da cewa. "Menene abinda ya firgitaka Baba? " Muryarshi na rawa ya labarta musu abinda idanunshi suka gani" "Assha ashsha wannan mata taka bata kyauta ba ta wani fannin. Ta wani fannin kuma kai sai ka iya ja mata faɗawa irin rayuwar sakamakon abinda mutum ya shuka na alkhairi ba yana nufin sai sak da abinda ya aikata ba. Ballantana kuma sharri. Daka sani baka daketa ba ka rabu da'ita ina amfanin abinda ka aikata Baba ka tozarta kanka dasu iyalanka baki ɗaya. Allah ya kyauta ya kuma kiyaye gaba." Babangida yace. "Kai mun umarni in saketa dan Allah" "Laaaa bazan umarceka ka saketa ba. Asalima a yau ɗinnan zata dawo ɗakinta ba zaka sake sakin ko wacce mace ba. Ka rungumi ƙaddara ka saka idanunka akan iyalanka. Ita kuma ka bata kulawa ta musamman ka kasance mai yi mata nasiha kuma kada ko da wasa ka tauye mata hakkinta domin zaka faɗa wata sabuwar jarabawar. Shi dama sharri ɗan aikene muddin ka aikeshi zai dawo, kuma in ya tashi dawowa baka san dame zai dawo ba ai. Hakkin Sabuwa daka tauye shi ya jagula lamuranka baiwar Allah ka zulunceta da yawa kayi amfani da tsoron saki da iyayenta suke yi ka wahalata. Gashi na fahimci sai dai sonta yayi ajalinka ko ranar da suka zo da mijinta naga sonta a tattare dakai. Kayi ƙoƙarin rungumar ƙaddarar kamar yadda a baya muka rungumi ƙaddarar daka rikito mana. Kaita adda'a a cikin Ƴaƴanka Allah yasa kada wani ya jawo maka abinda ba zaka iya jurewa ba. Yafiya da kake nema Baba daga kai har Babba babu wanda ban yafe ma ba. Kai kana tunanin da ban yafe maka ba zaka kai wannan labarinne? Na yafe maka tuni. Sannan duk abubuwan da nake yi maka sone ba ƙiyayya ba, ina horar dakaine domin ka sake nadamar abinda ka aikata mana. Amman har gobe ina jinka a jikina. Da ɗakinnan yana magana da zaiyi kullum sai nayi tunaninka duk matsalar da zata taso a gidanka ina iya raba dare ina roƙa maka Allah yayi maka mafita." Kuka Babangida ya saka mai gunji yaji soyayya da wajen Baba Malam kaɗai zai iya samun irinta. Kawu Manga yace. "Kayi shiru Baba. Haƙiƙa Yaya ka cika uban da ko wanne Ɗa zaiyi alfahari dashi. Kuma ka iya hora Ɗa haƙiƙa na koya daga gareka. Babangida ya horu iyakar horuwa duk wannan halin ko in kula da ka kwashe tsawon shekaru ashirin kanayi ashe kana mishi adda'a har kana damuwa da damuwarshi. Soyayyarku daga Allah ne." "Nagode Baba Malam kuma zan zame maka bawan da akan biyayyarka da cika umarninka zai mutu. Nagode ƙwarai da kula da su mardiyya da kake yi nagode da tsayuwarka akan su Aminu." "Baba kenan babu komai. Amshi wannan kin, kin gidanane dake kusa da Wawo ba'a daɗe da gama gyarawa ba da ƴan haya zan zuba. Kaje ka zauna iyakar rayuwarka a ciki kamar yadda naba su Bashiru dasu Ramadan suma suke zaune. Waɗanda suka mallaki nasu sun dawo mun dashi, waɗanda Allah bai hore musu ba suna ciki har yanzu" Kin Babangida ya karɓa ya dinga godiya yana share hawayenshi. "To bari in ƙara faranta maka wannan gida ka biya nera million uku a hankali a hankali har ya zama mallakinka zuchiyarka ta sake fari ko Baba? " Dariya suka saka Babangida idanunshi cike da ruwan hawaye yake godiya. Abun sha'awa tare suka tafi masallaci hannunsu a cikin na juna tamkar abokai. Ko da suka shiga sai Baba malam ya tura Babangida akan ya basu sallah. Haka ya ba da sallar magriba su wawo dasu Ramadan suna baya mamaki duk ya kama kowa harda almajiran malam. A wannan rana dai tare da Babangida Baba Malam suka ci tuwo suna yi Babangida na mishi hira zukatansu cike da farin ciki. Sai da akayi isha Babangida yayi ma Baba Malam sallama ya tafi kai tsaye wajen Malama ya labarta mata komai. "Hukunci sai mai tsaga ido. Lallai malam a gaisheshi. To naji daɗi sosai na kuma taya ka farin ciki da kuka daidaita da mahaifinka. Nima inda rabo sai in koma ɗakina da izinin Allah" Duk da girman abinda Ƴar Shuwa ta aikata cikin farin ciki da nishaɗi Babangida ya kwana. Washegari kuwa ya sanar ma matanshi zasu tashi daga wannan gidan dan haka mota zata zo da ɗaya da ɗaya ta ɗebe kayan kowa. Ya fita ya barsu suna ta haɗa kaya. Gidansu Ƴar shuwa ya wuce kai tsaye Mama tace ace ya shigo daga ciki. Ya kutsa kai ya shiga ta tusa Ƴar shuwa a gaba tai ta zagi harda duka sai shine ya ƙwaceta ma. "Babu komai Mama na yafe mata sannan ta koma ɗakinta yanzu. Gidanma tashi zamu yi yau ɗinnan sai ta tura a tattare mata kayanta babu komai" Ai kuwa haka akayi a ranar suka bar wannan gida zuwa gidan da Baba malam ya basu. Sai washegari dangin matan da dangin Babangida harda su Sa'a aka zo aka taya su jere ko ina ya fito fes Ƴar shuwa kuwa fuska duk a kumbure. Tun daga wannan rana alkadarinta ya karye bata da daraja bare fawa a idanun kishiya bare miji. Babangida ko dariya bayayi mata sai dai yana sauke dukkan hakkin daya rataya a wuyanshi. Ya hanata riƙe waya ya toshe duk inda za'a sameta. Tsugunne fa bata ƙarema ƴar shuwa ba. Dan Sameerah har sabon gidan su Ƴar shuwa tazo tayi mata hauka taji labarin ashe suna soyayya da Zarah. Ranar haka gidan ya cika da dandazon mata, Ƴar shuwa kuwa tana kulle a ɗaki tana kuka na fitar hayyaci. Da ƙyar matan layi suka fitar da Sameerah daga wannan gida unguwa ta cika da tsegungumi. An fita daga wannan sai kuma ta shiga sabon jarabawa ƙungiyar maɗigo data shiga dai ashe harda tsafi akeyi ita dake ƙaramace a ƙungiyar bata san wannan ba manyanne suka sani. Sai ya zamana babu dama dare yayi zata ji ana kiran sunanta ana cewa in bata dawo ƙungiya ba sai an haukatata, ko kuma an kasheta kamar yadda akaima wance da wance sai su shiga jero mata sunayen waɗanda suka fita a ƙungiya rayuwarsu ta salwanta. Abu dai kamar wasa sai lafiyar ƴar Shuwa ta soma taɓuwa yau ciwo gobe lafiya. Itace in abun ya tashi sai kishiyoyi sun daddanneta sunyi ta faman yi mata tofi tana cewa gasunan zasu kasheni. Banda rubutu da Babangida yake rubuta mata tana sha. Abubuwan dai sai sake tsananta suke yi saida aka danganta da gidan masu magani, duk dukiyar haram data tara saida ciwonta ya cinye tas bai bar mata komai ba Daman ance garin banza a farau_farau ɗin banza yake ƙarewa Shi kanshi Babangida saida dukiyarshi ta ƙare tas kafin Allah yasa komai ya daidaita suka fita a cikin rayuwarta sakamakon tsayuwar Baba Malam. Sai dai ta rasa ƙafa za'a iya cewa dan ƙafarta ta hagu bata iya ɗagawa sam sai dai ta dinga janta a ƙasa, hatta kamanninta saida suka canja idanunta suka firfito ta dawo abun tausayi kamar ba ita bace wannan Ƴar shuwan mai ji da izza da taƙama ba, ta zama musaka ƙarfi da yaji a hakannma ta Auna arziki sosai. Yau sai gaji Allah ya toni asirinta kab unguwa babu mai mu'amala da'ita cewa ma akeyi a unguwar ƴar ƙungiyar asirice ita, inta fito zata je makaranta yara sai su gudu, makarantar dole ita kam sai dai ta haƙura da zuwa sabida yadda ake gulmarta da yadda mata ke nuna ƙyamarsu gareta. Daidai da Zoɓo da Hamida take saidawa saida takai ta kawo ba'a siyan komai. Abinci kuwa Babangida baya iya ajjiye na wata guda a gidanshi albashin baya isarshi sai Baba malam ya tallafa mishi duk watan duniya Abubbuwa dai na jarabawa sukaita faffaruwa marasa daɗi. Wannan kenan Mrs Bukhari. [10/28, 11:53 AM] BADA'AT IBRAHIM: MRS BUKHARI 10

SABUWA:.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull